Showing 42001 words to 45000 words out of 323952 words
shopping din duk kayan kitchen da kikeso ..." idanuwa tasleem ta zaro Tana cewa
"ummah me zanyi da kayan kitchen kuma... "
"oho... " ta amsa mata, haka suka dinga hira da tasleem Tana b'ata advice cikin dabara, b'ata bar gidan ba sai wajen karfe biyar na yamma with agreement din cewa zata dawo ranar Saturday ta dafa mata new food Mai dadi.
Yarima kam yana chan Mai martaba garden abokai sun sakashi gaba sai zolayanshi kawai suke, ya Sara abinda zai fad'a masu sai ya sadda kai kasa to let them talk to their satisfaction Don ya lura babu abinda zai fad'a masu that will get in to their thick skulls
Wanann yace shi zaiyi organising barbecue wanann yace shi zaiyi organising picnic, ganin maganar bai karewa ya fiddo wayarshi yana latse latse, hankalinshi seem a little lost, he's just thinking yanda yaga tasleem Dazun, he don't know exactly what he's thinking amma dai Allah kadai yasan abinda ke yawo cikin ranshi, still yana godewa Allah da b'ata san ya ganta a haka ba, gani yake zata iya rainashi. Haka dai suka sha hira da planning events dinsu Don shagali da nuna farin cikin yarima zaiy Aure, shi kam Wanda ake planning saboda shi bai kou ce uffan ba balle yasan Sunayi Da, daga baya suka watse zuwa gidajensu.
Monday.
Rashida ce zaune a wata yar office kanta kan desk, da gani kuka kawai take, the thought of the man she so. Much love and adores with another woman is killing gradually, tunda ta samu labarin yarima zaiyi aure komai ya ida watse mata, she don't sleep eat or drink, banda kuka babu abinda take, iyayenta basu fiya bincika halin da yaransu ke ciki ba, kou kuma ince basu tsananta bincike balle su san abinda ke faruwa, kullum shiga kitchen ta debi abinci a gaban idon kowa Don suyi tunanin Tana cin Abincin, amma Tana shiga dakinta take juyewa cikin leda ta zubda. Kou kadan b'ata son abinda zai sa a tambayeta what's wrong with her, hakan yasa she will look OK when with people but cry when she's alone, yau Tana zuwa wajen service dinta ta samu wata empty office ta zauna sai kuka take, daga nesa na hango wata yarinyar dake sanye da doguwar wando na yan nysc wanda ya Kama mata jiki Sosai kanta babu dankwali, her fingers are well punished sai Tana sanye da riga T-shirt shima na yan bautar kasa, sai dube dube take alaman she's looking for someone, ta leka nan ta leka chan, the girl look Very classy and sexy, ahaka ta iso inda rashida take,
"I have been looking for you every where .... " ta fad'a Tana shiga dakin, ganin yanda bayan rashida ke moving yasa ta gane she's crying,
"babe what'sup...why are you crying... " ta fad'a Tana dafa bayanta, da sauri rashida ta daga kai Tana goge face dinta wai Don kar a gane she's crying, yarinyar dake tsaye kanta zata kai a kalla shekara 28 Don she look well matured,
"nothing... " ta fada cikin voice da bai fita sosai,
"stop saying nothing pls... You're crying... What's wrong?.. "ta tambayeta cikin damuwa sosai, ita dai rashida dagewa tayi ta goge face dinta fas sannan tace
"nothing..."
"pls stop nothing... " ta fad'a Tana jawo kujera ta zauna,
"tell me... What's wrong... " ta fad'a cikin kulawa sosai, da ganin yarinyar b'ata jin Hausa at all Don kou kadan b'ata da alama tashin arewa stare da ita, da ganinta irin mutanen nan ne da ake aiko dasu zuwa bautar kasa arewa, rashida shuru tayi don tunda tashiga wanann rayuwa na son Wanda baisan kou Tana da rai ba b'ata taba fadawa kowa ba sai ummy, itama ummy abinda yasa ta fad'a mata is because Tana ganin zata iya taimaka mata tunda she's in their family amma she regret telling her, rashida is a kind of person that keeps to. Much secret to her self, Tana da kawayen da dama amma babu wnada yasan halin da take ciki, kullum basu da magana sai na yanda ta rame amma her only response is stress, gani take in ta fadi abinda ke damunta hakan zai ja mata bacin suna da kuma rasa ajinta, sannan batason abinfa zai sa a yayata cikin kawaye, haka yasa she keeps all her pains to her self, idanuwa ta daga ta kalli Amanda dake kallonta sai kuma ta saukesu yayinda new tears ke forming,
"pls tell me... Problem shared is a problem solved... " ta fad'a Tana shafa bayanta ahankali,(NB duk giran da zasuyi a nan zai kasance cikin turanci tunda Amanda b'ata jin Hausa amma zamu dingayin wasu da Hausa saboda wasun mu su fahimta...)
"zaki tsaneni... " rashida ta fad'a cikin sabon kuka Mai nuna ta gaji,
"haba me zai sa in tsaneki?... Dan Allah fad'a min abinda ke saka ki kuka haka... Yanzu watan mu 8 a nan wajen...i study people very well.. Amma the way you're changing yana damuna... Fadamin abinda ke damunki kou zan iya taimaka maki.. You never can tell who can wipe your hidden tears away...." ta fad'a Tana shafa bayanta in a circular motion,
"Bazan iya fadi ba... Kawai zan mutu da abinda ke damuna... " ta fad'a cikin matsanacin tired tears,
"nidai na rokeki ki fadamin... Nayi maki alkwari da kabarin mamana Bazan fadawa kowa ba if you think I will publicize you... Ni nan garin ma wa na sani... Ba kowa... Tell me pls... " ta fad'a cikin rarrashinta, rashida is feeling she should say it to relieve herself of the pain and agony amma she's so Shy, buda bakin Amanda sai cewa tayi
"kou kina da ciki ne?.. " da sauri rashida ta girgiza mata kai,
"did you kill anyone... "
"pls stop quessing ..it's non of them... Kawai ina jin kunya ne... Amma zan fad'a maki... "ta fad'a Tana gyara zamanta, itama Amanda zama ta gyara Tana sauraronta,
"wani ne... Bai san ni ba... Na ganshi sau daya... Tun daga wanann ransr ban kara samun sukuni ba... I love him... And now he's getting married... " ta fad'a cikin matsanacin kuka, wani irin dariya Amanda ta saki Tana mikewa at the same time Tana clapping hannunta Tana cewa
"wonder shall never end... Ewooo... "ta fad'a Tana dariya sosai Tana alaman abinda rashida ta fad'a surprises her, rashida shuru tayi Tana kallon yanda take dariya then Tana clapping hannu,
"wato in this century ana samun mace ta zauna Tana kuka saboda tanason wani?.. I thought that era is gone... " ta fad'a Tana kallon rashida data zura mata ido Like she's seeing her for the first time,
"why young girl like you with everything zaki zauna kina kuka saboda wani abu wai shi na miji... Haba kin bani kunya... "
Tou me zanyi In banyi kuka ba... Wallahi abinda ke rage min zafin raina shine hawayena... " rashida ta amsa mata,
"pls. Ki bar wanann maganar kaman we not in 21 century..."
."wai me kike ganin zanyi?.. "
"baki taba jin snatching ba... "
"haba anty Amanda.. Snatching... Ya zaayi inyi snatching wnada bai sani ba... Wanda kou ganina bai taba yi ba... " ta fad'a sounding so confused,
"well My Dear ki bar kuka... All it takes is a snap of a finger and he will be all yours... " da sauri rashida tace
"kaman yaya... " ta fad'a jikinta na rawa,
"kawai feel free... Kar ki k'ara kuka... In mun tashi... Muje gidana... Muyi magana... I will tell you how it's done... " ta fad'a mata, nan take rashida taji sanyi cikin ranta, she feels she's real and not fake, kunsan da akwai maganar da mutum zaiyi maka ka yarda even without knowing the person, haka maganar Amanda yayi tasiri a rayuwar ta lokaci guda, tamkar Wanda ke cikin rigiya a mika mashi wuka ne, nan take zai Kama without thinking twice,
"Dan Allah ki fadamin how yanzu...can't wait sai mun tashi... " rashida ta fad'a Tana Kama hannu Amanda, dariya kawai Amanda tayi tace
"wanann ba abun sauri bane.. Kawia ki kwantar da Hankalinki... Tashi muje muyi abinda ya kawomu ..." ta fad'a mata Tana mikewa, da sauri itama rashida ta Mike Tana cewa
"give me a hint kou zan samu sukuni... " ta fad'a mata Tana tunanin abubuwa da sama lokaci guda,
"pls in kinason in samo maki mafita then kiyi hakuri mu tashi... Kinsan ance even walls have ears... You dint know who might be listening... So relax... " ta fad'a mata, sai lokacin rashida ya yarda ta kwantar da hankalinta Tana jiran su tashi taje gidan Amanda da b'ata taba zuwa ba kawai Don taji abinda zata fad'a mata.
Ita kuma maryam Tana dawowa daga lectures ta sake kaya zuwa simple shirt ta fito falo ta kalli mum dinta sannna tace
"mummyna am. Ready... Duk Da akwai ingredients din?" ta tambayeta looking weak,
"yes my love... What's wrong with you... " ta tanbayeta Tana mikewa,
"nothing.. Kawai jikina baiyi min dadi ne... " ta amsa mata Tana Kama hanyar kitchen,
"why tou.. Kou zaki huta gobe sai muyi..." hajiya ta fad'a mata,
"no mummy... Kinga Saturday da sunday zanje yiwa ummah girki... Dole in fara koya daga yau tunda kayan da zaa sha kala biyu zan koya da kuma abinci kala biyu... I want to practice sosai yanda bazanyi mistake ba... " ta fad'awa mum dinta dake biye daita. Dadi hajiya taji, cikin ranta babu abinda take sai yiwa hajiya amina adu'ar Allah ya b'ata lafiya mai daurewa, nan fa suka shiga kitchen, yau hajiya da kanta zata koya mata abincin, hajiya amina is making it easy for her sosai Don a nata tunanin zata sha wahala kafin tasleem ta koyi abubuwa, tasan ba abinci kadai bane abinda ya mace zata koya amma yana cikin jigon zaman aure. Kan kitchen table dinta ingredients ne kala kala suna jiran a fara aikatasu,
"babyna yau zan koya maki cabbage rolls da watermelon lemonade... " ta fad'a mata, idanuwa tasleem ta lumshe Tana cewa
"I love it mummy... " ta Fad'a sounding matured and weak,
"First abubuwan da zamu bukata shine cabbage, sai mince meat, fara shinkafa da aka dafa, sai kwai, da su Maggi da kayan kamshi irinsu ginger, onions, garlic da sauransu... " ta fad'a Tana nuna mata duk kayan, shuru tayi Tana kallonta tare da lumshe idanuwa kaman Tana jin bacci,
"now dora mana ruwa kan wuta... " hajiya ta umarceta, babu musu ta debe ruwa ta dora kan gas,
"Kinga in bakison ki zama lazy good kou inje slow cook dole in kina wannan sai kiyi wani abun at the other chance you get.. So while muna jiran ruwan mu ya tafasa sai mu fara hada kayan filling dinmu wato abinda zamu saka a cikin cabbage dinmu..." ta fad'a Tana Dauko bowl
"mummy what's wrong in mutum ya zama slow cooker... " ta tanbayeta
"ai mijinki na iya dawowa so Hungry kou ya dawo ba lokacin da kike tunanin zai dawo ba... Or ya zo da abokai.. Sai a dinga jiranki har a gaji da jira... Amma if you're a fast cooker shikenan at anytime yoire ready... Abincin dake daukan wasu minti talatin yana iya daukan wasu 1 hour depending on the procedure they use... "
"wai mummy why kuke min maganar miji this days ne?.. Ummah tace miji kema kice miji..duk shiyasa banajin dadin jikina... Dazun ma dana fadawa kawayena cewa sukayi kilan aure zakuyi min... " tafad'a Tana turo baki,
"pls ki maida hankali muyi abinda ya kawo mu nan... " tafad'a Tana dauko sarchet of tomato paste sannan tace
"Kinga kowa yasan tomatoes na cikin leda dafaffe ne.. Don haka zaki Dan zubashi ciki bowl dinki sanann ki zuba mata ruwa yanda zaiyi ruwa ruwa... " ta fad'a Tana yanka bakin tomato din da kitchen scissors, juyeshi tayi cikin wata bowl sannan ta zuba ruwa daidai ta saka whisk ta kadashi Sannnan ta ajiye gefe. Katon cabbage dinta ta dauko ta yanka hancinshi, sannan ahankali ta saka wuka Mai kaifi tsakiya Tana Dan Zagayawa wajen da itacen cabbage din yake har ta ciroshi ta jiye gefe guda
"hope you're watching... "ta tambayeta,
"yes mummy.. " ta fad'a Tana turo baki,
"very good... Yanzu zamu hada kayan filling din.. " ta fad'a mata, wata neat bowl ta dauko ta fasa kwai ta zuba ciki ta kada sosai, markadadden naman ta dauko danye ta zuba cikin kwai din, sannan ta zuba fara shinkafa Wanda ya dahu, dagashi ta fara zuba su albasa da tafarnuwa da dai sauran spices sai kuma maggi,
"yanzu kinga hannuna babu datti amma dole zan sake wanko hannuna tunda dashi zanyi mixing yanda zai hadu da kyau... " ta fad'a mata Tana kunna tap, hanunta ta wanke ta kalli ruwan dake kan gas daya fara tafasa tace.
"baby saka mana small salt cikin ruwan sai ki saka cabbage cikin ruwan... " ta fad'a mata, yanda tace haka tasleem tayi sannan ta dawo ga mum dinta data saka hannunta cikin hadin dake cikin kwano Tana motsawa, sai da ta tabbatar hadin yayi sannan ta cire hannunta ta wanka, ta dauki spoon ta tura cabbage din cikin boiling water din da kyau sannan tace
"Kinga ki tabbatar cabbage din ya samu ruwa kaman na minti uku zuwa biyar sai ki fidda... " ta fad'a mata, few minutes later ta fidda cabbage din cikin ruwa,
"zamu Bari yahuce tukun kafin mu fara balla ahankali..." ta fad'a mata, ita dai tasleem ta maida hankalinta sai kallo kawai take, b'ata ga wahalan komai ba cikin wanna aikin, it's something she can do except if da akwia wani abu da b'ata sani ba, katuwar bakin pan ya dauko daga cikin oven Tana cewa
"zamu zuba wanann tomatoes din da muka zubawa ruwa dazun cikin pan din nan sai mu danyi spreading dinshi.." tafad'a Tana juye half of wannan tomatoes din cikin pan din sannan ta dauki chokali ta bazashi yanda koina zaiji sannan ta dawo GA cabbage ta fara cire bayan ahankali Tana ajiyewa cikin tray, saida ya gama ajiyewa sanann ta dauki wuka ta yanke sauran hancin dake sama kadan, Tana yi Tana kallon if tasleem is watching.
"now zaki debi filling dinki ki zuba cikin cabbage din sai kiyi rolling ki ajiye cikin pan dake dauke da tomato din.. " ta fada tana zuba filling din Tana gamawa ta daukeshi ahankali ta dora kan tomatoes din, ahaka har tayi guda biyar sannan ta dauki sauran tomatoes ta juye samanshi tace
"now zaki rufe da foil paper Don kar samanshi ya bushe... "ta fad'a Tana dauko foil paper Mai kyalli ta rufe rolls din dashi sannan tace
"yanzu zaki saka a oven @ 360 degrees sannan zaki barshi yayi hour guda kou fi.. "idanuwa tasleem ta zaro tace
"mummy hour guda... Nifa am hungry ..." tafad'a kaman zatayi kuka,
"baki ganin danyen Nama ne?.. Dole zaa barshi ya dahu har ciki sosai yanda komai zai hade... " ta amsa mata,
"hmmm bai da wahala sai dai dadewa... "
"ai in kin San zaku ci in two hours time sai ki shiga kitchen..." b'ata k'arasa ba tasleem tace
"ku kuma mummy... Ni Da wa?.... "idanuwa hajiya tayi rolling tace
" ba ku ba... Mu nake nufi... " ta amsa mata atakaice, b'ata Bari ta kar wata magana ba tace
"yanzu sai muyi watermelon lemonade din mu.. Shi kuma kawai zamu bukaci kankana, sugar, cinnamon power or sticks, sai lemon ba lime ba,..tare da ginger fresh on" ta fad'a mata, juyawa tayi ta dauko kankana ta ajiye sannan tace
"zamu hada syrup da sugar dinmu.. "
"kaman ya?.. " inji tasleem,
"kawai zaki debi ruwa daidai sai ki zuba cikin tukunya tare da zuba sugar dinki.. Sai ki dora a wuta ya tafasa sosai, Kinga bazaki samu matsala da sugar ba, ..." ta fad'a Tana dauko small pot ta zuba sugar daidai sanann ta zuba ruwa ta dauki cinnamon stick guda biyu ya zuba ciki ta dora kan wuta, nan take kitchen din ya dauki kamshin. Kankana ta yanka tare da zubawa cikin blender Tana cewa
"sai ki zuba citta kadan kar ki saka da yawa... "
"mummy in yayi yawa me zai faru?.. " ta tambayeta, bazata iya fad'a mata cewa in aka zuba citta da yawa cikin kankana aka markada yana maganin man power ba, (tou mata masu complaining mazanjensu basu dadewa on bed kunji...ba dole sai yasan me yake sha ba... Kawai ki dinga dura mashi yana sha sai yayi firing dinki yanda kikeso, some people will be like this is good.. Well try it today Insha Allah you will love it)
"kawai yana sakashi yaji ne... " ta fad'a Tana yanka small amount Tana zubawa cikin blender shima.,
"mummy bazamu cire yayan ba?.. " ta tambayeta
"aa.. It's very important.. Yayan kankana suna da matukar amfani Don haka kou ci zakiyi kar ki zubda yayan... " ya fad'a mata, sugar dake tafasa sosai ta kashe Don ya huce sannan ta dauki lemon dinta ta matse ruwan cikin cup ta ajiye gefe, blender ta tada ta markada kankanan sosai sannan tayi sieving dinshi zuwa cikin bowl ta juye lemon juice din, saida ta Bari sugar dinta ya Dan huce sannan ta zuba ciki ta motsa ta saka masu a fridge Tana cewa
"yafi dadi If serve chill... "
Thanks.
[3/14, 6:26 AM] +234 703 008 7807: 14💙💚💛💜❤
Sak'aci
💙💚💛💜❤🧡
®Zuwairat (ummumaryam)
1⃣4⃣
Haka suka falo har abincin ya dahu sanann suka ci, it so delicious, sai santi tasleem take Tana cewa
"mummy gobe zan hada nawa... Nasan sai yafi naki dadi... " ta fad'a mata, murmushi hajiya tayi tace
"ai haka nakeso... Nafison naki yafi nawa ai... Gobe bazan ci komai ba har sai kin dawo kin dafa mana abinci... " ta fad'a sounding so encouraging.
Wajen karfe biyu su rashida suka tashi daga wajen service, sai bin Amanda rashida take kawai Don taji what she have for her, sai da suka fita daga gate din ministry da suke service rashida tace
"sister pls tell me mana... Jikina sai rawa yake... " ta fad'a Tana kalle kalle kaman mara gaskiya,
"dear relax let's go to my house... " ta fad'a mata Tana tafiya ahankali, a haka