Showing 15001 words to 18000 words out of 323952 words

Chapter 6 - Sakaci Book One Complete Hausa Novel

27 Sep 2025

2231

dinta long gown dinta ya bayyana, gashinta babu dankwali so kana iya ganin long and silky hair dinta a bayyane, hajiya kallonta kawai take kaman sai yau ta fara ganinta,
"wato bazaki daina shan chocolate ba kou... Sai karshen wata ki ishi mutane da kukan menstrual cramp... Nasan kou bag dinki is full of it" hajiya ta fada saboda sanin yanda duk wata sai tayi wannan haukan ciwon cikin wani loakcin har da kwanciya take a hospital saboda ciwo. Murmushi kawai tasleem ta saki tana dawowa nan bakin gadon tace
"na daina.. " tana tura sauran bakinta, tissue ta dauka ta goge bakinta ta daidaita kanta sannan ta dawo ta haye gadon ta kwanta ta dora kanta kan kafar hajiya before saying
"ummah... Daman nazo ne in fad'a maki kiyiwa yaya fadan yaji tsoron Allah kar a wullashi a wuta Tam.... " tafad'a trying to start the conversation of why she's there. Idanuwa hajiya ta zaro ta shafa kanta jin ta ambaci wuta,
"wane yayan wai?.. " hajiya ta tambayeta,
"yaya Aliyu mana... "
"toufa... Me yayi maki?.. " da sauri tace
"ummah ni baiyi komai ba... Amma gaskiya ya bani mamaki... Dukda ni ba sonshi nake ba dole in damu saboda naga abinda yafi karfi na... Ya bani mamaki mutuka... Nidai kiyi mashi waazi Don kar a wullashi wuta wallahi... " ta fad'a jiran a tambayeta what he did.
Tasan she will surely want to know why she's saying all this, ummah was staring at her, tasan tasleem da making issues out of everything,
" tell me what did he do... " ta tambayeta, kwanciya tasleem ta gyara tare da kara relaxing kan kafar hajiya sanann tace
"ummah jiya kou?.. "
"eh... " ta amsa mata giving her undivided attentions,
"shi da yaya mahboob suka zo daukata a islamiya ...sai yaya Aliyu ya fiddo wayarshi,..ummah did you know what I saw kwanc e kan face din wayarshi?..." ta fad'a tana mikewa zaune making the whole thing looking and sounding very very serious,
"aa... Menene... " hajiya ta tanbayeta sounding normal Don it might not be as serious as she sounds, tasan halinta da exaggerating,
"nan nan din mace... " ta fad'a tana nunawa hajiya kirjin kanta, da yatsa, idanuwa hajiya ta zaro tare da rufe bakinta data bude da hannu guda looking surprise, tasan one thing for sure is tasleem don't lie, bata karawa kan yanda ta gani, amma for sure she will say exactly what she saw,
"you mean kirjin mace?.. " ta tambayeta cike da mamaki,
"eh wallahi... Ummah... Kuma manya... Gwanin ban tsoro... " ya fad'a idanuwanta duk waje alaman she's scared,
"subhanallah... " hajiya ta fad'a cikin sanyimurya alaman she's not happy to hear this,
"wallahi kam subhanallah... " tasleem ta fad'a tana komawa ta kwanta kan kafar hajiya hannu hajiya ta dora bisa kanta looking quiet for a moment sannan tace
"hope baki fadawa kowa ba... " ta fad'a tana shafa kanta,
"aa van fadawa kowa ba sai mummy da wani daya zo wajena jiya... Shima sai ya goyi bayan yaya... " irin kallon da hajiya tayi mata yasa tayi saurin Jan bakinta ta tsuke,
"how many times have I warned you kar ki dinga fadin duk abinda kika gani?.. " da sauri ta Mike daga kan kafar hajiya tace
"ummah am sorry ban karawa... " ta fad'a kaman zatayi kuka,
"good... Daga yau in na karajin Kinyi irin wannan halin sai nasa an zaneki...kuma Aliyu zan saka... " da sauri tace
"wallahi ban karawa... " ta fad'a voice dinta na rawa,
"good gimbiyata... Shi Kuma fav zanyi maganin shi... " ta fad'a mata, ahankali ta maida kai kan kafarta relaxing again, tasleem's character is some how,( if you always read my novels you will know I don't really love my female characters like my male stars amma I love tasleem saboda straight forwardness dinta...)
"yanzu bari kije kitchen ki fad'a masu a hada maki abinda zaki bukata a islamiya..." hajiya ta fad'a mata,
"OK ummah... Amma zaki karamin da kudi kou... Ban amsa wajen mummy ba... " ta fad'a tana mikewa daga kan gadon,
"babu damuwa... Ki. Fad'a masu bisa umarni na a dafa maki abu Mai shegen dadi yanda ke da kawayenki zakuci ku koshi... " inji hajiya,
"tou ummah... " ta fad'a tana Kama hanyar waje, ummah shuru tayi tana kallon bayanta da gashin kanta dake kwance gadon bayanta, Dan goshinta ta dafa not knowing what to think, it's a very difficult decision for her, she never felt so stranded with decision sai yanzu, ita dai har ga Allah tasleem tayi mata, zata fi kowa farin cikin ta ganta as her daughter in-law amma they might be consequences, tasan koda kuwa zata tsallaka ta and choose another person bazata damu ba because she's carefree person, asalima tasan bata damu da yarima ba. Bayan kaman minti goma tasleem ta dawo dakin rige da mug a hannunta na shayi Mai kamshin gaske alaman an zuba kayan yaji sosai, bakin gadon ta zauna ta dinga kurba har ta shanye tas sannan ta ajiye mug din wajen zata hau gado,
"maza maidashi kitchen... " shine umarnin da ummah tayi mata, babu musu ta Mike ta dauka tayi waje dashi, many people will think tasleem is not fit for the prince amma ita hajiya knows her imperfection can be perfect some day, koda nace yarima na Kama da mahaifinshi ba duka ba because he have some of he's mother's characters, ko kadan hajiya b'ata son iya yi, she love someone that is always himself nor matter what.


Wata yarinya ce zaune wacce bazata wuce shekara 20 zuwa 22 ba zaune a wata falo kusa da wata lady da zata kai kusan 30 plus tana rike da yaro a hannunta, magana take mata cikin lafazi Mai sanyi, daga nesa in kaga yanda takewa hannunta while speaking zaka san magiya take mata, sai da na tako kusa daita naji tana Cewa
"Dan Allah anty.. I beg you... Kawai kice Dan uwanshi ne ke son ganin shi... Nasan he will definitely come... Pls anty save a soul... "beautiful lady din ta fad'awa wacce ke rike da baby, da gani wacce ke rike da baby bata da interest kan abinda yarinyar ke cewa at all, because her face says it
"pls anty mutuwa zanyi... Ki taimaka min... " ta sake fad'a mata,
"amma rashida baki da hankali... Wato in nace mashi brother dinshi na son ganinshi sai yazo sai inyi yaya?... Kawai dai kinason ja min raini... "inji Mai baby a hannu, da sauri wacce aka kira da rashida tace
"no anty ummy... In yazo sai kice... " bata k'arasa ba ummy which is the second daughter inlaw din hajiya amina tace
"pls rashida get a life... Move on...sau biyu Kuna haduwa da Aliyu gidan nan amma kou inda kike yana kallo?.. I see no reason why zakiyi stressing kanki kan Wanda bai damu dake ba alhalin some people are dying to be with you... Wallahi wahala Zakisha a banza... Take a look at yourself... Wake up am Telling you if not wallahi zan fadawa mami tasa abu yayi maki auren dole,... " ta fad'a cikin matsanacin fushi, idanuwa rashida ta zaro cikin tashin hankali because tasan one word from her elder sister to her parent is all it takes and zaayi mata aure, kawai bata ankara ba sai ta fara hawaye, wato rayuwa kenan, yarima da tasleem ke kira da black mamba shine wannan yarinyar kewa hawaye, abincin wani gubar wani, she heard lot about him wajen mutane but never met him personally despite his elder brother is married to her elder sister, kou sanda akayi bikinsu wato yayarta da kuma yayan yarima she's only 14 which is 8 years back, bata damu da ta san who and who is present ba, amma seeing him five months back ranar da sister dinta ta haihu a hospital make her falls for him totally, ta shiga tsahun yanmatan that are dying for him amma nata is too much, ita kanta yar sarauta ce but under he's father, she tries all she could ta manta dashi amma he's handsomeness is not something one xan easily forget, har yau smile dinshi still linger in her heart, duk ta rame saboda tunanin ta, bata iya fadawa kowa amma she have to tell her sister Wato ummy, ita kuma tasan samun Aliyu might not be something easy saboda kou ita dake matar wanshi bata taba ganin smile face dinshi ba and bata taba ganin frown face dinshi ba either, kawai tasan he's not a social person and he's not into women,
"na shiga uku... " shine abinda rashida ta fad'a cikin hawaye sosai, baki ummy ta tabe tace
"baki shiga ba... Zaki dai shiga... Nadia son mason wani kika sawa kanki ba... You will suffer...wallahi it's better ki maida hankali ki gama service dinki ki samu daya daga cikin masu neman auren ki kiyi aure daga baya Allah ya sa maki sonshi than ji zauna kina hauka kan Wanda vai san if you're dead or alive ba... It's an advice.. If you like take it kou kuma leave it... Your business ..." ummy ta fad'a mata, rashida dafa chest dinta tayi sosai tana kuka,
"anty ummy do something... Wallahi mutuwa zanyi sabida yarima hydar.... In na mutu kina da alhaki wallahi... " ta fad'a cikin kuka sosai, wata yar karamar dariya ummy tayi tana cewa
"hehehe... Ashe ina da alhaki... Dayake ni na dora maki kou.... Na you sabi... Kinga na tashi ma..." ta fad'a tana San'a danta a kafada tana mikewa daga kan royal seat da take zaune,, wata budurwa ce tazo ta amshi yaron daga hannun ta, ta Kama wata hanya dashi,
"nidai zan fadawa yaya Muhammad... Nasan kilan he will do something... " a fusace ummy ta juyo tace
"wallahi one word from you to. Mijina zakiga abinda zai biyo baya tunda ana nema maki mutunci baki gani... Just try any stupid and see...wallahi sai na fadawa mami... " ta fad'a mata sounding firm and strong. Rashida rasa inda zata skaa kanta tayi saboda bakin ciki da damuwa, she feels like committing suicide kou ta huta da jarabawan rayuwa, she have her perfect life before she saw him, now yayi destroying everything for her.
"yanzu shikenan haka zan dinga wahala har in mutu?.. Will you watch me suffer yo death?.. " rashida ta tambayeta,
"ai bana son ki mutu shiyasa nake baki shawara... Just imagine ace kin samu kin fad'a mashi kina son shi and at last ya wulakanta ki... That will kill you faster.... Nasan it's hard for you ..amma kou kadan banson Kinyi anything that you will regret... " ummy ta fad'a mata,
"anty kilan ya tausaya Mani... Wallahi mutuwa zanyi... My heart is so heavy... Kou ruwa taste bitter a bakina... "
"wai in ba wawanci ba did you think ke kadai ce Mai sonshi?.. Da akwai dozens girls kaman ki masu mutuwan sonshi.... Aliyu is ranked the most eligible bachelor arewa, so Kinga dole ladies will be dying for him... Pls little sis take it easy on yourself... Banson ki shiga wata hali mara kyau... Kinji... " ta fad'a tana dawowa kusa da inda take zaune tare da zama gefenta, shuru rashida tayi sai hawaye na zuba,
"tou shikenan anty... " ta fadawa yayarta, ba wai because she give up ba, no, but it's because she will look for better alternative, tasan her sister is never going to help at all. Mikewa rashida tayi walking gently, tana da dirin da sai ka rantse she won't cry for a man, but unfortunately destiny have caught her in it's web, hanyar inda bed rooms dinsu take ta nufa ta bude daya ta shiga sannan ta wuce bathroom, tsayawa tayi Tasha kuka sosai har ta godewa Allah sannan ta wanke face dinta, her sister was in the bedroom listening to how she's crying, it really hurt her yanda sister dinta ke wahala saboda Wanda bai Santa ba, amma it's better for her she hurt her with her truth than to make her happy with lies. Shiyasa take fad'a mata ta rabu da tunanin shi Don tasan Sam ba hanya bace Mai bullewa face hanyar wahala da wulakanci. Tana fitowa ummy ta rungumi baby sister dinta suka fito falo tare, bag dinta ta dauka sanann ta yafa Vail dinta ta Kama hanyar waje sai shessheka kawai take, tana fita compound ta nufi Gate walking slowing zuwa waje, duk wnada zai ganta sai yasan something is bothering this beautiful girl, she was walking toward the main road yayi da wani makeken jeep yayi parking kusa daita yana wining glass din motarshi kasa, ciki wani cute guys ne yana cewa
"sister excuse me.... " ya fad'a with quite a firm voice amma kou inda motar ke tsaye bata kalla ba balle ta saurareshi, she gets lots of suitors amma ta dorawa kanta son yarima,.(ladies don't wallow in fantasy... Face the reality... Kar ku tsaya kaje kanku kan wanda bai san da zamanku ba.. Nasan it's not easy letting go but give it a try... Yan mata da dama suna kawo complain din suna san Wanda bai san su ba... Well dear ki. Rabu dashi and face those that wants you... Wannan shine taimakon da zaki iya yiwa kanki) wuce motar tayi ya sake binta da mota this time har fita yayi daga cikin motarshi yana binta da kafa yana magana amma tamkar he's invincible, bata kou kula shi ba, haka ya hakura ya kyaleta ya koma cikin motarshi. Sauran kadan da wani Mai Motan ya bigeta sai zaginta yake amma bata kou daga kai, wani Mai adaidaita ya tsaya yace
"hajiya tafiya ne?.." daga kai tayi ta kalleshi ta nufi inda adaidaitan take tashiga ta fad'a mashi sunan organization da take service. Daman wajen service dinta zata ta biyo ta gida sister dinta. Nan ya jata suka tafi.




thanks[3/14, 6:26 AM] +234 703 008 7807: 6🧡❤💛💚💜
Sak'aci
💜💚🧡💛❤💙




Zuwairat (ummumaryam)



6⃣




Happiness over load... Rabbi more thanks to you💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾




, yarima na kwance har karfe tara nan falo,   bude ido yayi waking up from the sweet sleep,  mika yayi ya koma ya zauna kaman minti biyar sannan ya Mike,  kofa dakin da mahboob ke kwance ya duba yaga har lokacin shi bai tashi ba, hamma ya saki heading back to his own room,  yana shiga ya cire long jallabiya dake jikinshi ya nufi closet da kayan hannunshi,  rataye jallabiyar yayi kusa da sauran kayan sannan ya nemo Jean da riga masu haske ya saka,  bai saka kaya Mai duhu saboda skin colour dinshi,  duk kayan dake cikin closet dinshi have bright colour,  fita yayi ya nufi Bangaren ummah while masu hidima suna ta up and down, wasu suna kula da tsaftar gidan while wasu kuma suna kula da flowers da dai sauransu,  falo ya shiga  yaji kamshin abinci,  yasan dai duk wannan abincin nashi ne sabida most Bangaren Mai martaba hajiya take breakfast da sauran kishiyoyinta,  wannan it's part of their culture.  Wata dake goge dining ta gaidashi ya daga mata hannu kawai with a smile sannan ya nufi bed room din ummah.

Tasleem kam tana maida mug ta dawo kan gado ta hau tare da dora kai kan kafar hajiya sai zuba take,  da ta fadi abinda ba daidai ba sai ta kwabeta,  in kuma ta fadi funny thing sai tayi dariya,  she so Much adores tasleem with her parrot mouth.
"gimbiya ki bari in shiga wanka in fito... " ummah ta fad'a mata,
"AI ummah nan da minti shabiyar za tafi... Kawai ki bari in gama ganin ki in tafi sai ki shiga wankan tunda ba lallai  ki fito Kafin in tafi ba... " ta fadawa tana baje kan gadon hajiya,  sai kawia hajiya ta biye mata,   tayi zaune while ta cigaba da bata labarai kala kala, hajiya na kallonta tana shafa kanta daga gaba zuwa baya feeling her silky hair, kofa aka bude yarima ya shigo smile a face dinshi amma ganin tasleem kafar hajiya yasa ya hada both gabas da yamma,  sai kudu da arewa kaman bai taba dariya ba,  tasleem najin voice dinshi tayi saurin mikewa Tare da dan komawa bayan hajiya alaman tsoro, jiya ta harareshi and she's sure bai mance ba,  karasowa yayi yacr
"ummah kafa yayi sauki kenan tunda har ana hawa... " yafada babu walwala a face dinshi, (rayuwa kenan,  mutanen that people are dying to Met suna chan wasu na ganin su a sanga,  kuma masu ganin nasu basu san value dinsu ba... Duk manyan Cele that were dying to met suna da masu ganin su at all time..they don't even value seeing them.. That's life...if Allah yasa Kana cikin such Cele don't be too proud for it's the will of Allah,  some of those people dying to met you are even far better than you in so many ways... Alhamdulillah )
"ashe ...kaima jiya baka hau ba?.. " inji ummah,  sake daure face yarima yayi yana zama kusa da ummah,  tasleem sai lekenshi kawai take, if you ask her waye dodonta she will tell you Aliyu kou black mamba,  yarima bai kara cewa komai ba  Don kar ummah ta sake yi mashi maganar da zai sa  raini ya shiga tsakanin shi da ita,  if  there's anything he hate is raini,  gyara murya ummah tayi sannan tace
"yanzu fav ka kyauta kenan?.. " da sauri tasleem tace
"ummah zan tafi... " ta fad'a tana sauka from the other side na gadon that is far away from inda yarima yake zaune,  yarima kasa kunne yayi yaji abinda mahaifiyar shi zata ce,  kou Kadan baiyi tunanin tasleem will tell hajiya about the boobs ba so ko kadan bai kawo hakan cikin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login