Showing 99001 words to 102000 words out of 323952 words

Chapter 34 - Sakaci Book One Complete Hausa Novel

27 Sep 2025

2180

gayu sosai cikin expensive lace sannan ta saka long hijab dinta tare da daukan matching bag da shoe masu kyau ta saka ta fito, kafin ta fito duk masu aikinta sun shirya,  haka suka jera suka fita,  har Allah Allah take ta shiga motar ta,  masu gadi na ganinta zata shiga mota sai da sukayi mamaki Don amaryar da aka kawo ranar Saturday ta fara fita ranar Wednesday looks some how but haka suka bude mata gate ta ja motarta Hindu na zaune gaba,  suna fita Umar dake dakinshi ya dauki wayarshi ya kira yarima,  yasan ba auren so sukayi ba kuma yana ganin Aliyu bai da masaniyar fitar datayi,  hakan yasa ya kira yarima. 
Rashida kou karfe bakwai baiyi ba ta kira Amanda taji jnda suke,  nan ta fada mata motarsu ya lalace suna hanya,  haka ta dinga kiranta a waya Don jin inda shke8,  tana jin tace sun wani local government that is about an hour drive zuwa cikin gari rashida ta shirya ta dauki bag dinta ta fadawa mum dinta an kirata a wajen service,  daman suk fitar da take most babu abinda take cewa sai wajen service,  kou wajen tasleem zata bata cika fadi ba Don kar ummy ta ankara da akwai wani abu dake tafiya,  ita kuma mom dinta give her so much trust that bata binciken abinda take,  bata san her daughter is into serious business ba,  no trust should stop you from monitoring what ur child does Don with bad influence wallahi wata rana sai su baka mamaki.  Bakin gate  na Estate din da Amanda take rashida taje ta zauna tana jiranta. Bayan kaman hour guda ta hangeta ta taho saman abun hawa,  har wani irin ajiyan zuciya Mai karfin gaske ta saki.

Thanks
[3/14, 6:29 AM] +234 703 008 7807: 32🧡💛💚💙❤
Sak'aci
💜🧡💛💚💙❤


®Zuwairat (ummumaryam)

3⃣2⃣




Mikewa tsaye Rashida tayi as Amanda na sauka daga cikin abun hawa,  wani irin ajiyan zuciya kawai take saki  dariya Amanda tayi tana cewa
"wallahi kina da matsala...you have to see your face yanzu.... Duk Kinyi zuru zuru... "
"sister bazaki gane ba...yau kou bacci banyi ba.... Shi yasa kika gani haka... "ta fads tana bin bayan Amanda dake shiga cikin estate din, sauri kawai Rashid's take yayin da take biye da Amanda,  Amanda ba bude kofar dakinta ta shiga Rashida ta shiga ta zauna,  da ka ganta kasan ba a hankalinta take ba,  Amanda kam ciki ta shiga da dan bag dake hannunta, few minutes later ta fito daure da towel tana cewa
"hope bazaki damu ba in dan yi wanka in nemi wani abu inci... " ta fadawa rashida da babu abinda take jira kaman results, shuru kawai rashida tayi bata ce komai ba alaman she have no choice,   komawa ciki Amanda tayi ta barta nan zaune tana counting seconds.

Yarima was a bit busy so bai samu daman daukan waya ba har Umar ya gaji da kira ya hakura,  sai da ya gama duba files da wasu abubuwan zuwa wajen karfe sha biyu sanann ya samu natsuwa, sai lokacin yayi breakfast da ummah ta aiko mashi tare da daukan wayarshi,  miss calls din Umar ya gani kaman biyar,
"what sort of stupidity is this... In har ka kira mutum sau daya zuwa biyu bai dauka ba sai kayi mashi uzuri.. Kasan bai kusa... " ya fada yana redailing number Umar,  bayan ringing kaman uku Umar ya dauka yana ceww
"ranka shi dade ina wuni... Kayi hakuri dazun na isheka da waya..."
"me ya faru?.. " shine tambayar da yarima yayi mashi,.
"daman ina son in tambaya ne in ka yarda a budewa matarka gate... Naga zasu fita ne.... "
"ban gane ba... "
"fita sukayi tun dazun... "
"da wa naji kana plural...su suwa?.. " ya sake asking,
"ita da masu aikinta ne kilan.... " inji Umar,
"OK shikenan... " inji yarima,  kashe wayar yayi ya cigaba da harkokin shi,  he pretend cewa vai damu ba,  Afterall shi ta fada mata in har ummah ta amince kawai ta fjta amma sai ya kasance he want to know if really ummah ta amince, shi kanshi he doesn't know how comes yake son sani, 
"it's not as if I care..." ya fada yana daukan wayarshi,  number ummah yayi dailing,  bayan tayi picking sun gaisa yace
"ummah ke kika amince yarinyar nan ta fita kenan... Duka fa ranar Saturday akayi mata aure.... "  ya fada sounding a bit disturbed,
"nifa ban gane what you're talking about ba... " inji ummah,
"ummah jiya tayi min maganar zuwa school.... Shine nace ta tambayeki... " bai k'arasa ba ummah tace
"Don ubanka aliyu ni zan bawa matar ka umarnin fita Don ka raina ni?... Aliyu rainin ya Kai haka?.. "
"wayyo no ummah... Am sorry... "
"keep quite.... Kayi min shuru.... Wato tunda ni na sa akayi maku aure ta zama matata kenan kou.... ".
"pls ummah ba haka bane..."
"haka nr mana...gaskiya Bazan boye maka ba ka bata min rai... "
"Allah sarki ummah am sorry... Bazan k'ara ba.. Pls... Kika san kou mutuwa zanyi yanda ban jin dadin jikina din nan ba... " ya fad'a cikkn sanyin murya, sai lokacin ummah ta dan saurareshi, 
"then what happened... Ta fita ne... " ta tafada calmly
"eh Umar ya kirani yace ta fita tun da safe..."  ya fada a bit disturbed
"then why kake kirana... Ba dai kana wasa da damarka as her Husband ba?.. Kar kace ina maka baki but you won't like abinda zai biyo baya... Time might come da kakeson zama mijin ta nuna maka ita bata San wannan zancen ba..."
"Ummah yanzu haka zan saka mata ido?... ""ya fada kaman zaiyi kuka saboda takaici, 
"your business... " inji ummah
"nidai wallahi sai na zaneta...da aurena kanta zata dinga yawo tun baa je koina ba?.. " ya fada cikij fushin da bai San kishi bane
"kaji sakarci... An fada maka Mai hankali na dukan mace?.. Small thing I will beat her... Go and kill her ai matarka ce... Kaine kake wasa da damarka... Har yarinyar tazo ta fada maka zata fita Don ka raina min hankali kace ta tambayeni.... Ai ga irinta nan... Kuma I won't talk to her... " inji ummah cikin fushi,
"ummah sorry.... Nidai kiyi lifting Allah yaisa kaina so that I will be a better husband... " ya fad'a mata calmly, 
"being a better husband na cuta da zalunci kou... If that is what you mean no.... Bazan Bari ba... "
"ummah babu zalunci.... Babu cuta kuma.... Kawai zanyi abinda ya kamata ne... Wanann yarinyar da kou magana akayi mata sai kuka me zaa zalunta nan... " ya fada wearing a smile  yayin da ya tuna yanda take kuka in akayi mata Magana, he wonder if da akwai tank zaune a kasan idonta that tears flow easily,
"naji... Daman kou da kuwa na fada maka Allah yaisa kou ince ban yafe ba,  daga baki na ne kawai.... Amma ba wai I mean it ba... " wani irin kasaitaccen murmushi Aliyu ya saki jin abinda tace,
"kuma Don na fada maka doesn't mean kayi misbehaving daita.... Don't hurt her.. Kadai San I love that girl... "
"I know ummahna... Kawai ina son ta daina wanann sangarta da kuka koya mata ne... Koy magana zata furta kaman tana koya... It's annoying... "ya fada amma smiling,
"AI haka ake son mace.... "
"nidai ummah ban son... " ya fada yana dariya. 
"Kai ka sani AI... Talk to you later... " ta fada mashi tare da katse wayarta.  ajiye zuxiya ya saki Don tamkar anyi lifting wani makeken curse daga kanshi haka yake ji,  yanda yake jin takaicin wanann kukan banza da take
"hmmm.. " kawai ya fada.

Tasleem kam tunda ta shiga school babu abinda take sau budewa friends cikin motarta, wayanda suka shiga cikin motar suka tuka round the school sunfi goma,  kou lectures bata shiga ba sai labari take bawa wayanda suka biye mata,  klu kadan batayi tunanin her level kou class,  GA masu aikinta biye daita,  lokacin lunch mutanen da ta sayawa abinci basu irguwa,  wajen karfe biyu ta bar school, bata Kama hanyar koina ba sai hanyar gidan iyayenta.

Rashida na nan jugum har Amanda ta hadowa kanta plantain da kwai sai ruwan tea,  fitowa tayi ta ajiye kan dining dinta ta kalli rashida datayi jugum tace
"join me... " idanuwa kawai rashida ta daga ta kalleta ta sauke kanta alaman raina mata hankali take,  tasan she cant drink kou ruwa ne balle kuma abinci,  Amanda vata k'ara kallon inda rashida take ba ta cigaba da cin abincinta,  sai da ta cinye tas sanann tace
"sai yanzu na dawo...bari ina zuwa... " ta fad'a tana mikewa rike da plates data ci abincin dasu,  few minutes later ta dawo da wannan kwallin da aka bata,  zama tayi rashida ta ware idanuwa tana kallonta, 
"yauwa yanzu ki bude kunnenki kiji abinda zan fada maki... Baba ya gama komai...abinda ya rage shine kawia ki hada ido dashi bayan kin saka wanann kwallin.... " ta fad'a tana mika mata abinda ke hannunta,
"ban gane ba... " rashida ta fada voice dinta na rawa
"Meye abinda baki gane ba?.. Nace zaki saka wannan kwallin... Sai ki tabbatar kin hada ido dashi.. Thats all... Ba zai k'ara ganin kowa mace ba face ke... " jiki na rawa rashida tace
"ni ya zaayi in hadu dashi har in hada ido dashi?... Wayyo na shiga uku... " ta fada tana kuka saboda abinda heart dinta keyi mata,  she really need to she'd some tears so that ta samu sauki,  wani irin zafi take ji,  she feel so disappointed already,  kallon haushi da takaici Amanda tayi mata tana cewa
"Meye haka zaki zo kina min kuka bayan duk wahalal dana sha...kou India yake kina iya zuwa ki same shi in dai he's important to you balle mutumin dake kasar nan... " cikin kuka rashida tace
"wanann mutumin is a VIP... Ganinshi ba sauki bane.... Tunda nake zarya gidanshi ban taba ganin shi ba... Kaicona... " ta fada tana kuka sosai kaman it's the end of life,  a nata tunanin zaa zo mata da wani abu ace ta turara ta kira sunanshi or something like that amma Aliyu data sani won't be easy to make an eye contact,
"that means you're not serious.... Duk yanda yake VIP if you want to get him you will... Kou president sai ka mallaka if you want... All you need to shine kawai ki sakawa zuciyarki you will have him and you will do all you have to do... Yanzu dai ya rage naki... If you want do it if baki so ki ajiye maganin... Nidai na yi maki alkawari kuma I have fulfilled it... " ta ajiye mata kwallin tana kokarin mikewa cikin tashin hankali ta rike Amanda tana cewa
"sister help mana... Dan Allah kar ki barni haka nan... Wallahi na zama very confused ne... " ta fada tana rike da Amanda,  tsayawa Amanda tayi ta kalleta tace
"wai ke me zanyi maki kuma bayan ke da kanki have given up... In ba Don you're not thinking ba why do I ask you to be close to his wife... Ba Don ki zama close to him ba?... "da sauri rashida tace
"I know amma na rawa abinda zanyi ne... Dan Allah advice me... " ta fada tana kuka,  Amanda na tsaye while rashida na rike da kafarta,  ta ma rasa abinda zata ce mata
"tunda nake zuwa gidan ban taba haduwa dashi ba.... He is hard to. Met... "
"listen pls my friend... Kina jin abinda zan fada maki?.."
"yes... " rashida ta fada cikin serious exaggeration, 
"kinsan duk yanda na miji yake indai ba kasar ya Bari ba yana weekend gida?... " da sauri rashida ta daga mata Kai, 
"good... Let me show you something... " ta fada heading to the door,  fita tayi daga sakin ta rufe kofa sai kuma bayan kaman second biyu ta bude kofa da karfi  ta shigo,  da sauri rashida ta daga Kai suka hado ido
"Kinga yanda kika kalleni haka duk Wanda zaa budewa kofa da karfi zai kalleka... If kinje gidan weekend sai ki saci jiki ki shiga Bangaren shi... In bai falo dole ki shiga har bed room dinshi and bang his door.. Believe me kou bacci yake zai tashi yaga who it could be... And as his eyes meet yours shikenan an gama... Now is it difficult?.. " ta tambayeta,  da sauri rashida ta girgiza nata Kai saboda tasan tasleem is easy to convince, so zata jya shiga Bangaren yarima ba tare da tasleem ta San nan ta shiga ba, 
"and another option... Duk namijin Muslim indai Mai addini ne zai fita ziwa wajen sallah... Kina iya zama inda kikasan zan wuce,  dayazo zai wuce you can make a noise da zaisa ya kalli inda kike... That's all... " ta sake fada mata,  nan take murmushi ya bayyana kan wet face din rashida,  da sauri ta dauki maganin ta saka cikin bag dinta, 
"nagode nagode nagode.... " kawai take Mai maitawa as tana mikewa, 
"I don't think ina iya hakuri sai week end.... " bata k'arasa ba Amanda tace.
"you have to... Weekend end is here already..... "
"ni so nake inje yau kou zanyi saa .."
"pls aa.. Kar zaryarki yayi yawa har sister dinki ya gane before komai ya kammala... Ki Bari zuwa Saturday or Sunday... Sai kije...daga wannan zuwan am 100% sure bazaki sake komawa gidan ba sai a matsayin matarshi.... " wannan statement yayiwa rashida dadi sosai da bata San lokacin da ta daka tsalle ba
"everything you want zan baki in har na gan kaina tare fa Aliyu..." ta fada out of desperation,  dariya kawai Amanda tayi
"ai wanann is assured.. " ta fada cikin ranta while wearing a smile dake bayyana all is alright, da sauri ta fita tana cewa
"wallahi wannan week end din zaiyi min nisa amma it's alright... Zanyi hakuri..." ta fada kaman wata sabuwar mahaukaciya, 
" I pray you don't run mad before everything pull off... " inji Amanda dake binta da harara.

Tun daga gate masu gadi suka farayiwa tasleem oyoyo, amma fa suna mamakin why she's here so soon,  tana shiga gate tace
"baba kusa kazo kaga motata... " ta fadawa babbab Mai gadinsu tana wace baki, shima baki ya washe ya taho yana jera mata aduoi, Bangaren hajiya Asabe ta fara shiga tana salllama da karfi,  hajiya Asabe dake zaune falo tayi saurin mikewa tana cewa
"lafiya?.. " ta fada tana kallon yanda tasleem ta shigo
"yo mummy lafiya lau... "
"Bangane yo mummy lafiya lau ba... Me ya kawo ki?.. " ta tambayeta,
"mummy lafiya lau... " ta fada cikin shagwaba
"tou if lafiya lau it's better ki kama hanya ki koma inda kika fito... Salon ki jawa mutane magana daga kaiki Saturday sai ki Kama hanya ki zo gida yau... If baki son Ranki ya baci better go back now... " ta fada mata babu wasa,  tasleem gani take bata sonta
"tou .." kawai ta fada tana barin part dinta da sauri don kar ta bugeta,  da sauri ta fita zuwa Bangaren mum dinta  tana waige waige,  hajiya zainab na dakinta taga an bude kofa,   ganin tasleem tsaye yasa kirjinta bugawa da karfi kaman zai fito,   tasleem sai kallon baya take gudun kar ace hajiya Asabe ta biyota,  wanann reaction din yasa hajiya zainab k'ara shiga tashin hankali, 
"besty... " ta fada tana mikewa Don leka inda ta fito if someone is behind her, 
"naam my mummy... "
"lafiya... Waya koro ki... " ta fada mata tana kallon yanda take nishi
"mummy babu kowa... Nazo ne.. Shine small mummy tace in koma... "
"ban gane kin zo ba... Kinzo yin me?.. " ta tambayeta tana kallonta,  marairacewa tasleem tayi tace
"mummy school naje... Nace Bari inzo in ganki... I miss you... "  ta fada kaman zatayi kuka,  idanuwa hajiya zainab ta zaro tana cewa
"so kike ki bani kunya tasleem ?.." ta kira sunan ta directly,  nan take tasleem ta gane da akwai matsala because she  hardly call her by her name, 
"kafin in rufe idanuwana in bude ki bace Min daga nan gidan... Wallahi in ba haka ba da khalifa zan hadaki...now out... "ta daka mata tsawa,  kuka tasleem ta farayi zata bude baki tayi magana hajiya zainab tace
"kalma daya ban son ji... Kou kadan banason jin komai daga gareki... Now tashi ki bar gidan nan... " ta fad'a tana nuna mata hanyar waje, tana kuka tana cewa
"shikenan... Daman baki sona.. Since you don't miss me shikenan... " ta fada tana tsaye inda take,  hajiya zainab sakin ajiyan zuciya tayi tare da yin shuru,  bayan kaman minti daya ta Kama hannunta tana cewa
"besty kin San ba haka bane... Tunda sisters dinki suke aure kin taba ganin wacce bayan kwana uku tazo gida?... Baa zuwa sai in mutum ya Dan. Kwana biyu... So pls ki koma kinji babyna... Kar dad dinki ya kamaki gidan nan... " ta fad'a mata cikin rarrashi,
"ni yunwa nake ji ki bani abinci inci kafin in tafi... " ta fada cikin shagwaba. Kaman wasa sai da hajiya zainab da Kanta ta dafa mata abiinci ta koshi tace zatayi bacci kadan,  nan hajiya zainab ta kusa dukanta sannan ta yarda ta bar gidan. 
Haka nan yarima ya bar office wajen karfe uku, he want to see if ta dawo gida, despite his feeling empty he want to see, shi dai kawai yanason yaga if zata yi mashi karya or something, kawai yana son jin ya tsareta investigating dinta, it's going to be fun, yana tuki yana murmushi, yana zuwa gjda yaga motarta bai nan, dariya ya saki yana cewa
"yau da akwai shagali," ya fads wearing a very broad smile, today is the first day daya dawo daga office ya wuce gidanshi directly ba tare da yaje gidan ummah ba, kawai farin cikin ummah tayi freeing dinshi kawai yake, yana fita ya shiga shiga ciki yayi alwallah ya wuce masjid, daga nan ya dawo ya zauna compound da masu gadi, sai. Magana suke amma shi yayi shuru, baifi minti talatin da zama ba sai ga horn a bakin gate, kawai sai ya sake sakin murmushi, da sauri ya daya daga cikin masu gadin ya bude mata gate motarta ya kuso kai, gefe daya ya kau da kai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login