Showing 180001 words to 183000 words out of 323952 words

Chapter 61 - Sakaci Book One Complete Hausa Novel

27 Sep 2025

2163

zuciya yace
"I have made up my mind... Rana irin ta yau a daura masu aure... Kaje gida gobe zaa kawo kudin neman aure da duk abubuwan da zaayi Wanda shariya ya tanada... Don haka the case is closed... " ya fad'a mashi atakaice sounding a bit calm than before. Haka mahaifin rashida ya tashi ya tafi looking surprised why this sudden decision, shi kuma Mai martaba ya bishi da harara a zuciye, only Allah knows what he is feeling as he sit there. He sees it as insult, inda zaa barshi his decision will be kou a warware abinda akayiwa danshi kou kuma yasa ayi masu hukuncin da sai sun gwammace mutuwa da rayuwa. Amma baba sadik ya hanashi hakan.
Taslem kam bata da magana sai ciwo har bacci yayi gaba daita, ummah na zaune a bakin gadon da take kwance tana kallon yanda ta rame kaman ba ita ba, taslem is too young for this, amma kuma ummah sees her fault, hannunta cikij na ummah har akayi sallah magrub, mikewa ummah tayi ta bar dakin tayi sallah ta dawo, she was expecting to see yarima amma shuru bai zo ba, abun ya b'ata mamaki, she calls him but busy, she wonder wane irin asiri ne zai maida mutum haka, wane irin asiri ne zai rikita mutum sosai haka ya manta komai nashi, she is sure yarima ya fara son taslem before all this, she remembers yanda yake satan kallonta ranar da suka zo nan, then tasan motar daya saya mata is out of love sannan he won't complain about ta rufe kofarta if he don't love her, amma gashi ya manta da duk wannan, she told him She's sick amma he can't see her, when she calls him today taji regrets a voice dinshi and she was thinking suna gama waya zai zo amma shuru, ita kam bata yarda cewa da akwai such sihiri da zai raba mutum da kowa nashi haka ba but Now she believes, sannan ta yarda ba rashin adua bane amma kaddara, rabbi kar yasa mugun kaddara ya jira mu a way of our life. Mun San it's not always going to be merriment for us but Allah kar ya jarabce mu da mummunar kaddara. hajiya amina kasa fadawa hajiya zainab halin da tasleem ke ciki tayi,
"da... gaske ...ne" voice din taslem ya maidota hayyacinta, da sauri ummah ta kalli taslem da face dinta ke jike da tears Tare da kama hannunta da babu canular.

Bati readers muje zuwa,🤣🤣🤣

Thanks
[3/14, 6:36 AM] +234 703 008 7807: 57masu sharing novel dina ban yafe ba, Allah ya maida maku intention dinku a kaina, I don't know what you mean but Allah knows best.

Masu reading basu biyaba suma Allah yaisa, bani kadai ke Allah yasa ba har da wayanda suka biya basu karanta ba amma sai dai su gani a wasu groups, suma basu yafe ba. In case you don't know ba kudin mallaka kika biya ba kudin karatu ne kuma da akwai agreement har nace Wacce b'ata yarda ba kar ta turo kudinta, duk wacce ta turo kudin ta amince kenan, so I take it as you knew. So the novel mallakina ne halak malak, if kika karanta banyafe ba, in da hakkinki kaina Allah yq bi maki in kuma nawa ne a kanku Allah ya bimu simple,






Da sauri hajiya ta shafa face dinta tana cewa
"gimbiyata... Kin tashi... " ta fad'a as tasleem dake kwance take hawaye then bakinta na rawa, 
"gimbiyata ki bar kuka kinji kou... Babu komai... Everything is time... Kishiya is not the end of life... Kowa da halinshi da zauna... " tasleem dake kokarin mikeaa zaune kai ta dinga girgizawa tana cewa
"ummah...kawata... Ce... " ta fad'a wasu zafafan hawaye na zuba daga idonta,  ummah rasa abinda zata fada mata tayi,  kou kadan she won't want to tell her that her friend use charm on her husband,  ita da kanta ta warware bakin zaren da kanta, 
"gimbiyata... Ki fadamin abinda ya faru ranar datazo gidanki na karshe.. " inji ummah, cikin kuka taslem ta fada mata how she came in a hurry just to help her prepare meal for yarima da kuma yanda tana gamawa tace ta dauko mata waya,  da sauran komai,  tana magana jikinta na rawa,
"gimbiyata... Babu abinda zan fada maki sai sakacinki ne ya jawo mana komai..."
"ummah sakacin me nayi?... Daman haka akeyiwa wacce ta aminta da mutum?.. " ta fada sounding very weak,
"my dear jewel... Ke da bakinkj kika fada mata in Tana sonshi zaki hadasu... Yanzu ita GA hada kanta dashi without needing your help... " ummah ta fada mata wannan Don kauda zargin wata magana daga cikin ranta,  cikin kuka tasleem tace
"ummah.... Ni ban... San haka komai zai kasance ba.... Ummah ta kwace min yaya Aliyu.... Ranar da kika ce in bashi hakuri wallahi na bashi kuma ya yafemin... Ummah har fadamin wakar da yake kauna yayi kuma yayi min wakar... Kuma yace in ya dawo zaiyi mana visa mu bar kasar...ummah shine yanzu kou inda nake bai kallo... Ummah Zuciyata ciwo yake min... " ta fad'a tana dafa chest dinta while crying out very loud, ummah ta mugum jin tausayinta,  she stares at her as she talks of how they spoke,  it's obvious ta gane ranar rashida ta zubawa favorite dinta magani a abinci,  she was there on mission
"my gimbiya wallahi  baa son da yana wa iyayenshi gardama Don a karshe Dan shi zaiyi nadama...sai na fada maki ki bar wanann yarinyar...tun ranar da kika fadamin ta shiga bangaren Aliyu duk da ta sani it's his na gane she's on mission... Amma kikayi kunnen kashi... Gashi tayi nasara kan abinda take nema a wajenmu..."
"ummahna... Am sorry... Ban Karawa... Ummah Inason rashida tsakanina da Allah.... Ina kaunar rashida kaman yar uwa da ban dashi.... I don't know she will do this to me... Yanzu yaya bai sona ita yake so... Ummah mutuwa zanyi... " ta fad'a cikin kuka har tana tsikewa, mikewa tsaye ummah tayi ta dora kanta a saman cikinta tana shafawa tace
"my dear babu abinda zau sameki... Kawai I want you to be strong... It's your own destiny... Kiyi hakuri kinji... "
"ummahna... Bazan iya hakuri ba... Ummah inason yaya Aliyu... " ta fad'a straight as she always says what she have in mind
"ummah me yasa tuntuni bai nuna min halinshi ba sai da ya ga na fara son shi na fara damuwa dashi?..wallahi ummah in da tun farko ne bazan damu ba... " ta fad'a sounding very bitter, 
"Shima yana sonki... Kou me zai maki a yanzu ba halinshi bane...aliyu shine wnada ya saya maki sabuwar mota ya kuma yi maki alkwarin baki rayuwa Mai inganci.... Kuma Insha Allah wannan Aliyun zai dawo ba da dadewa ba... Kawai ki dinga adua kinji gimbiyata " hannu tasleem ta zagaya waist din ummah dashi ta cigaba da kuka sosai, kanta ummah ta cigaba da rarrashinta ita kuma tana kuka straight from her heart  kou kadan bataga irin rarrashin da zaj hana zuciyarta kuka ba,  sai yau ta yarda that she have been a fool not to have given her husband her love,  she thought it's love da rashida je fad'a mata kar ta yarda dashi not knowing that tana kishin shi ne,
"I should have known... " ta fad'a cikin kuka while hugging ummah,
"pls ki bar kuka  Believe me komai zaiyi daidai... "
"ummah Dan Allah ki fada mashi ya auri wata... Kar ya auri Rashida...ita ta dinga zugani kanshi... "
"kuma dayake baki da wayau kika yarda kou?.. "
"ummah I thought sona take... Sai da ya kaiga I love her above all amma banda ke da mummy... Kuma shine zata auri yaya... Ni wallahi ban zama dasu... " ta fad'a crying sosai kaman ranta zai fita,
"haba dear na... Yayanki na sonki... In short kece yake so... " b'ata Bari ummah ta k'arasa ba tace
"amma bai zo ba ai kou... " tafad'a cikin kuka,
"ummah ina rike shi ya tureni... " ta sake fada mata taba kukan takaici,  cikin ran ummah tana tunanin ai ba yanzu zatayi kuka ba,  sai ta fara ganin best friend dinta da mijinta zata ji ainahin kishin da haushin.
"gimbiyata me zaa kawo maki kici Dan Allah... " ummah ta fada tana daga jaw din tasleem dake kan stomach dinta, 
"ni ummah kou ruwa ban sha... Ban cin komai... Indai har da gaske zai aureta.. Kawai gidan mu zan koma..." ta fad'a sounding so childish while crying,  dariya ummah tayi tace
"ki jirani...."ummah ta fad'a mata tana daina shafa Kanta, ahankali taslem ta koma ta kwanta tana hawaye,  the pain is unbearable for her,  wayarta dake  kan bedside locker ta mika hannu ta dauko tayi dailing number mum dinta,  hajiya zainab na picking tasleem ta fara Sabon kuka tana fad'a mata yarima yace rashida zai aura, 
"besty kiyi hakuri... Daman rashida tazo ne Don ta samu hanyar kusanci da shi ba Don tana sonki ba... Babu komai Allah ya saka maki... " ya fad'a mata kaman ita ma zatayi kuka saboda yanda tasleem ke kuka Mai ratsa zuciya,
"mummy da ciwo... Rashida ta yaudareni... Ta cuce ni... Wallahi ban yafe mata ba... Mummy guda zan dawo... Ban iya zama a kawo wacce na kira da kawata gidan da nake kira da gidan mijina... " ta fad'a sounding so tired
"my love kinsan ba ke kadai rashida ta yaudara ba... Ta yaudareni too... She wears the skin of an angel but She's not... Sai yanzu nake ganin sakacin mu... We welcome a total stranger without thinking twice... But babu komai... Da akwai Allah.. Pls kar ki damu kanki... Nasan in Allah ya yarda da akwai Sakayya Mai zafi... Allah zai saka maki kinji kou... " ta fad'a mata cikin rarrashi saboda yanda take kuka,
"tou mummy .." suna cikin magana ummah ta shigo sai wata Mai aiki biye daita da fruits cikin tray,  sallama tasleem tayi da mom dinta.
Babu irin magiyar da ummah batayi mata ba amma sam Taki amsa,  she begged her and call her with all sort of sweet names amma a banza,  she really believe she's in too much pain,  dole ta hakura ta barta,  sauka tayi daga kan gadon tana tafiya kaman iska na kadata ta shiga bathroom ta hado alwallah ta dawo tayi sallah da ake binta sanann ta dawo ta kwanta tana kuka,  wayarta na hannunta tana jin kaman ta kira rashida but she knows she will not pick her calls,  text ta shiga ta fara rubutu kaman haka
"rashida am disappointed in you... Ban san zakiyi min haka ba... Na aminta dake na sakar maki sirrin raina..amma kikayi min haka... Ban yafe maki ba... In da akwai Sakayya Allah zai saka min...nagode.. " ta rubuta ta tura mata.  Amma hakan does not make her feel any better,  nothing makes her feel better. She feels kaman her world have come to an end,  da akwai time da wani Abu zai sameka da zakaji in da mutuwa zakayi yafi maka duniya dadi,  haka tasleem take ji,  the feeling she's having is so bad and dangerous that she thinks it will be good if she relief herself of the burdens by killing herself, ahankali ta Mike zaune tana kallon kofar dake mosti,  she feels kilan yarima ne amma it was Hindu when the door finally opens,  da sauri ta mikawa Hindu hannu tana kuka Mai ban tausayi, nan ta shiga fad'a mata abinda yarima ya fad'a mata,  Hindu dora hannu tayi bisa Kai, 
"wallahi ban taba kaunar wannan kawar Taki... Nima na ja maki kunne kan fad'a mata komai da kike...amma baki ji... Inna lillahi waina ilahi rajiun... Gaskiya da akwai maciyar amana... Wai kana tare da mutum ya kasance Mai cin amanarka... Allah ya saka maki... " inji Hindu that is talking in serious anger,  tasleem kuka kawai take, 
"nasan yanzu ma kilan suna tare... "inji tasleem, 
"babu komai... In Allah ya yarda zata ga Sakayya... Baki da hakkinta amma ita tana da naki...ta yaudareki... Kuma mayaudari bai taba sakamako Mai kyau ba... Allah zai dubi halinki na gari ya saka maki... Dan Allah ki daina kuka haka nan... "  ta fad'a mata cikin rarrashi, karar message ne ya shiga wayarta tayi saurin dauka,  sai taga an rubuta
"ashe aure ya zama cin amana...kanki ake ji..." aka turo mata ta number yarima,  wannan abun ya sake kashe mata zuciya,  relaxing tayi kan gadon tana kuka to her satisfaction.

Yarima was together with his beloved rashida Don daga office wajenta ya wuce,  suna tare mahaifinta ya dawo daga palace,  he looks dull ya wuce bangarenshi,  hakan bai hana rashida da yarima cigaba da hirar su ba,  bayan kaman minti biyu da zuwanshi hajiya asiya ta shiga,  nan ya fad'a mata yanda sukayi da Mai martaba,  ahe was so surprise
"aure sati guda... Yaushe aka taba irin wannan..."
"ai Bakiga yanda yake min magana ba... Abun ya bani mamaki.. Je is indeed in a bad mood sanda naje Don Sam ba haka na sanshi ba..."
."yanzu meyw abun yi... "
"kawai ki fara fadawa  wayanda suka kamata su sanj sannan duk abubuwan da kike ganin tana bukata kiyi list Muga how much it will cost... " ya fad'a mata jiki babu kwari ta Mike ta fita,  falonta ta koma thinking of how to go about this whole thing,  she's so shy of hajiya zainab,  b'ata San ya zata ce mata da zata gane she havr nothing to do with this ba,  haka kawai sai ta yanke hukuncin zuwa gidan Dan iya the next day.  Don gani take it's better taje suyi magana kou kunyar da take ji ya ragu.
Wajen karfe 8 Mai martaba ya kira yarima da kanshi,  yana ganin kiran babanshi yayi saurin picking yayinda dayan hannunshi na cikin na rashida, 
"inason ganinka yanzu... " shine abinda ya fad'a mashi,
"baby zan tafi... " ya fad'a mata, rakashi tayi har bakin mota ya shiga kaman kar ya tafi ya kama hanyar palace. Rashida na shiga ciki mum dinta ta fad'a mata yanda ake ciki tsalle ta daka sai dakinta, b'ata San it's all plan to get their son back as soon as possible ba.
Wajen karfe tara Saura yarima ya isa palace, direct Bangaren dad disnhi ya shiga ,gaidashi yayi ya amsa mashi cikin faraa
"autan baba albishirinka..." mai martaba ya fad'a mashi, murmushi yarima ya saki not saying
"baka amsa ba... "
"abba goro.. " ya fad'a kanshi kasa
"nan da sati guda zan aura maka wannan yarinyar da kakeso... " idanuwa yarima ya zaro cikin so much happiness
"abba nasan I can count on you... Nagode abbah na.... I love you so much... " ya fad'a yana durkusawa nan gaban dad dinshi,
"Masha Allah... Kaji dadi kou... "
"eh abba... "
"amma banda wasa da aikk... Sannan banda shiga hakkin daya sabida daya... Kaji kou... " ya fad'a mashi.
"tou abba... " ya amsa cikin serious excitement,
"maganar lefe ina ganin a b'ata kudi ta sayi duk abinda take so... Gobe zan aika gidan da kudin neman aure dana lefe... Kawia sai ka jira a kawo maka mata... " d sauri yarima ya Mike ya rungume ubanshi sabida farin ciki,
"abba I love you sosai... "
"Nima I love you too Auta... " da sauri ya Mike yana cewa
"let me go to ummah in fad'a mata abinda ka fadamin... Daman tace babu kou sisinta ciki... Gashi an gama min komai... " ya fad'a yana barin wajen da sauri,  wajen ummah ya nufa yana shiga ya tarda b'ata dakinta,  kallon agogo yayi yana tunanin ina ummah zataje by this time ,sai lokacin ya Tuna da tasleem dake gidan, 
"oh... Na mance wallahi... " ya fad'a yana fita daga dakin, inda yake tunanin tasleem take ya nufa, bakin kofar ya tsaya feeling some how a bit sannan ya bude kofar,  ummah ce ta fara juyowa ta kalleshi,  tasleem was laying on praying carpet ita kuma tana zaune gabanta rike da mug,  da sallama ya shigo feeling a bit guilty which last for about  five seconds, 
"ummahan... " ya fad'a wa ummah while ita kuma tasleem ta bude idanuwa jin voice dinshi,
"sai yanzu ka taso kenan... " ta fad'a tana kokarin mikewa,
"aa I was a bit busy ne... Ummah ya jikinta... " ya fad'a yana Dan leko ta daga inda yake tsaye kaman he can't get close to her,  wanna abun yasa tasleem dake kallonshi fara new tears,
"ka tambayeta mana... " ta fad'a sounding angry, mikeaa tayi ta taka zuwa inda yake tsaye
"ke ya jikinki... Wai me yake damunki... Hope kin fad'a mata babu abinda nayi maki... " ya fad'a daga inda yake tsaye a bit far away from her, her voice was gone saboda shakewa but she she'd tears kaman it's her last,  the way he is acting towards her shows bata da sauran digon so a zuciyar shi,  it's like she's a total stranger to him. Mug dake hannun umma ta mika mashi yace
"ummah me zanyi dashi?.. " yafada yana Dan b'ata fuska,
"ka b'ata... I havr been telling her to eat b'ata ci... " ta fad'a mashi face dinta babu walwala,
"may be ta koshi kou... " ya fad'a calmly trying not to annoy her tunda yaga yanda take kallonshi,.
"baka da hankali... Na fada maka duk yau b'ata ci komai ba and you're here making stupid noise..."
"ummah.... Na... Koshi... " tasleem ta fad'a cikin voice dinta da bai fita sosai, 
"you see...i told you ta koshi... In har kaji mutum yace bai cin abinci ai koshi yayi... " ya fad'a atakaice, hajiya amina rasa inda zata saka kanta tayi  fita tayo daga dakin rike da mug da yarima ya maida mata hoping they will havr a private chat amma tana fita ya bi bayanta yana cewa
"umma albishirinki..." da sauri ta juyo tace
"wai biyoni kayi?.. "
"ummah pls say goro... "
"goro... " ta fad'a rasa inda zatayi dashi,
"my wedding is in one week... Kuma  abba zai kudin lefe da komai gobe... Hurray.... " ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login