Showing 84001 words to 87000 words out of 323952 words

Chapter 29 - Sakaci Book One Complete Hausa Novel

27 Sep 2025

2190

mahaifiyar rashida,
"Amin Amin... Tana kusa dake ne... " hajiya zainab ta tanbayeta, 
"aa... Inajin Tana dakinta... " ta amsa mata
"OK... Daman tasleem tace Tana kiranta bata daga waya shine na kira inji if she's alright,... "
"OK bari in leka dakinta.... Inazuwa... " ta fad'a bata kashe wayar ba ita kuma itama hajiya zainab vata kashe ba,  tafiya ta dingayi ta isa dakin rashida dake kwance head down sai kuka take har voice dinta bai fita at all,  Tana jin sallaman mum dinta tayi saurin daga Kai at the same time Tana goge face dinta, idanuwanta sunyi sutu sutu,
"meke damunki... " mum dinta ta tambayeta, da sauri tace
"nothing.. Kaina ke ciwo... " ta fad'a Tana nishi, 
"ga maman kawarki. She want to talk to who.. " ta fad'a Tana mika mata wayar,
"who mummy... " ta tambayi mum dinta while collecting the phone, hajiya zainab Tana jinsu,  banza mum dinta tayi daita ta fice daga dakin, face din wayar ta kalla taga hajiya zainab,  ta ma mance wacece hajiya zainab, kafa wayar tayi a kunne tare dayin sallama,  amsawa hajiya zainab tayi cikin faraa like nothing happened,  Tana jin voice din ta gane mahaifiyar tasleem ce, da sauri ta daidaita voice dinta Tana cewa
"mummy good evening... "
"evening.. Ya kike ya gida..."
"fine mummy.... Ban. Ma dade da Shigowa ba.... " ta fad'a trying to bring out her voice daya dishe saboda kuka,  shuru hajiya zainab ta danyi sannan tace
"daga ina kenan... " ta fad'a to be sure if rashida is something else,
"mummy har kin mance.... Bana je kaduna ba... Sai yau na dawo... " ta fad'a without thinking if mum dinta ta fadawa hajiya zainab gaskiya,
"oh... Well come back... Ya hanya tou... " inji hajiya zainab,
"fine mummy.. Ya biki anyi komai lafiya.... "
"fine my dear.... Lafiya lau... "
"Allah sarki... Bamu ma dade da gama magana da besty ba.... Naso inje gidanta yau amma na gaji sai gobe Insha Allah zanje... " ta fad'a sounding so cute and calm,
"oh kunyi magana kenan... Amma itace ta kirani tace in kira mum dinki saboda Tana kiranki baki dagawa... " hajiya zainab ta fad'a sounding a bit tense but trying to be calm,
"oh mummy... Nifa na kirata dazun kuma munyi magana... Kou dai ajiye wayarta tayi na kira wata ta dauka har na dauka itace... Ikon Allah... " ta fad'a Tana Dan dafa chest dinta,  shuru hajiya zainab tayi feeling kaman she should cut the phone sai kuma tace
"dear... Kina jina?.. " ta fad'a mata
"yes mummy... "
"Dan Allah ki fadamin da akwai abinda ya shiga tsakanin ki da tasleem ne Wanda ban sani ba?.. " ta tanbayeta cikin natsuwa,  da sauri rashida tace
" haba mummy no Mana... Me yasa zaki ce haka mummyna... "ta fadi haka,  da jin voice dinta kaji voice din mayaudariya,  before her voice sound so obedient amma now she hears the voice of a traitor,
"mummy wallahi babu abinda ya hadamu...pls ki bar tunanin hakan Dan Allah mummyna... " ya fad'a Kaman zatayi mata kuka,  ajiyan zuciya hajiya zainab ta saki sanann ta ce
"nidai kin san na haifeki kou... Tou ban son kiyi. Min karya... In d akwia abinda tasleem tayi maki just tell me now... Because ni Bazan taking bullshit ba... So tell me now... " ta daka mata tsawa,  kuka rashida ta farayi Tana cewa
"mummy Dan Allah kiyi hakuri... Babu abinda ya hadamu... " ta fad'a cikin kuka, shuru hajiya zainab tayi for a while kaman ta fado abinda ke ranta kuma kaman tayi shuru,  she's a person that is open hearted,  bata boye abinda ke ranta balle ta boyewa sa'ar yar da ta haifa abinda ke ranta
"tou in babu abinda ya faru why kina gari amma kika yarda tasleem despite you know how much she trusted you... You know how much I trust you too..." idanuwa rashida ta zaro while gabanta na faduwa sosai,  (that's how it is for bad people, kullum suna cikin fargaba, Kullum suna cikin tunani,  kou suna ci basu auki sai dai su dinga karewa kaman kudin guzuri.. Amma mutum Mai clean heart kou bai da kou sisi zaka ganshi cikin nastwua, kou bai samu Mai kyau yaci ba he will still gain weight because shi kwaciyar hankali gives everything, so the choice is yours,  be good or be bad but believe me, you can never regret being nice,  generous, selfless and above all being a good person) 
"Kinyi shuru kou... " hajiya zainab ta fadawa rashida dake faman kuka cikin serious fear of her plan being scattered, 
"wayyo mummy... Ba haka bane... " ta fad'a Tana kuka sosai,  her brain was thinking fast of what to say,  kawai Tana tunanin the kind of advice da Amanda zata bata, boom and she arrived,
"mummy.... Kawai ina jin kunya ne... Ba lallai inyi meeting class of sauran kewayenta ba.... " ta fad'a Tana kuka sosai  nan take hajiya zainab taji duk wannan haushi  da suspect din ya fita cikin ranta
"amma. Gaskiya ban san baki da wayau da hankali ba sai yau.... Ina maki kallon mai hankali Ashe am wrong... In ban da rashin hankali kaman naki who cares about class kou status... Anf for your information I bought you gold of 600k tunda kece kawar amarya... " idanuwa rashida ta zaro jin abinda hajiya zainab ta fad'a.
"fulani ta sayi duk kayan da yanmata zasu saka kuma naki is special and you have shoes to go with seven cloths da aka saya maki...nace ajiye maki dukda baki nan akayi biki you will still use them...amma kina nan saying rubbish,  am.l So very disappointed in you ...in hae muna tare da Kai if we can't make you blend with us then we won't insult you..nasan tasleem bazata ji dadi ba in har taji wanann dalilin nan naki.... " cikin matsanacin kuka rashida tace
"wayyo mummyna am sorry... Dan Allah kiyi hakuri..ki yafemin.. Dan Allah kar ki fadawa besty.... " ta fad'a cikin serious tears, shuru hajiya zainab tayi for a moment sannan tace
"promise me bazaki sake yi min karya ba... I know tasleem misbehave amma duk abinda zau fita daga bakinta gaskiya ce... Tou kema inason ki zama haka Don kou yanzu kin yi karya tunda har kikace kunyi magana alhalin ba haka bane... Pls kar in k'ara jin karya a bakinki.... " ta fad'a mata Tana kuka sosai,  sai taji ta bata tausayi,  nan kuma ta dawo Tana rarrashinta, sai da hajiya tayi mata alkawarin bazata fadawa tasleem sanann ta yarda tayi shuru,  kafin suyi sallama hajiya tacr
"duk sanda kike so kizo ki kwashi kayanki... "cikin wayau rashida tace
"mummy ki barshi pls...  "
"banson gardama... Am I clear   "
"yes mummy... Nagode.... " ta fad'a mata, 
"babu godiya... " sai lokacin  sukayi sallama,  duk da abubuwan arzikin da akayiwa rashida vai sa ta cire abinda ke zuciyar ta ba,  asalima son yarima ya fi mata komai,  suna gama waya ta dauki wayarta ta kira tasleem nan tayi mata karyar Tana hanya ne sai yanzu ta iso,  Don haka bazata zo ba yau sai gobe.

Tasleem na zaune falonta suna hira da masu aikinta kaman ba itace uwar dakinsu ba tukuicin ummah datayi mata alkawari ya iso,  har waje ta fita taga sabuwar Toyota keyless tsaye yana daukan ido, bata damu da masu aikin gida kaman su Mai gadi ba ta dinga daka tsalle Tana ihu har saida Hindu ta Dan tabota ta nuna mata wayanda ke kallonta,  sau lokacin ta dan tsaya, 
"dauko min wayata... " ta fad'a cikin so much excitement tana tsaye gaban motar,  da sauri daya daga cikib masu aikinta ta dauko mata wayar,  ummah ta fara kira Tana mata godiya Tana dire dire, dariya kawai ummah tayi ta kashe wayarta, kiran mum dinta tayi daga nan waje Tana ihu Tana fad'a mata kyautar da ummah tayi mata,  ta kira rashida ta fad'a mata sannan ta dauki picture din motar ta dora a both instagram da whatsapp status dinta tare da group dinsu na kawaye.  Duk wanda yaga wannan motar sai yaji bakin ciki,  wasu nan take suka fara kiranta suna congratulating dinta. Bude motar tayi ta dauki wata package dake ciki tayi cikin falon da gudu kaman gidansu babu mota,  she suddenly find happiness, inda ta san haka zata samu farin ciki da bata tsaya wahalal kanta ba.  Tana shiga ta zauna ta ware abubuwan da aka turo mata ba komai bane face abubuwan gyaran jiki daga Mai sai sabulu, wanann vai dameta ba sake fita tayi Tana kallon mota. 
Yauma yarima bai dawo gidan ba sau wajen karfe 10 na dare,  leda ya sake shigowa dashi kaman na jiya ya shiga har falonta,  babu kowa,  ajiyewa yayi ya Kama hanya kaman zai fita sai kuma yaga in Tana jin yunwa yaci amana kenan so it's better ya fad'a mata da akwai abinci if she want she eat if she doesn't want she starve, daga nan inda yake tsaye yace
"ke!!!... " ya fad'a da karfi,  shi sunanta ma shige mashi yake, tasleem dake kwance ta kanga waya a kunnenta bata ji ba because wayarta is on loud speaker sannan hajiya Tana karanta mata story book, idanuwata na budewa ahankali Tana maidasu Tana lumshe ahankali alaman She want to sleep,  sake kiranta yayi yaji shuru,  tsoki yaja ya nufi inda yaga mai aikinta ta shiga jiya,  kofa ya bude ya taka kaman Taki uku again sannan ya bude next door that lead to her bedroom,  da karfi ya bude kofa sai ga tasleem dake sanye da rigar bacci ta zubara ta mikewa zaune, ganin yarima ne tsaye yasa ta zaro idanuwanta sosai tare da rufe bakinta da hannunta sabida kar ihun dake neman fitowa ya kufce mata, she look so small as she sit in the middle of the wide bed,  kaman wata yar 12 ce zaune, 
"kinci abinci?.. " shine tambayar dayayi mata in  low voice yanda mum dinta bazata ji yana dakin ba as her mother's voice was coming out loud,  nan ya gane story take karanta mata,  da sauri ta daga mashi kai while covering herself with the huge duvet blanket,
"good... Kina bukatar... Wani abu?.. " ya sake asking in a low voice,  sake daga mashi Kai tayi
"tou daga yau.... Ki dinga cin abincin da zaa kawo... Bazasu gama ba sai nan da sati biyu... Daga nan zaki dinga abinci da kanki... Am I Clear..." ya fad'a sounding so official, baki cewa da matar shi yake magana,  he sound so straight forward,  kuma bai kalleta ba sosai Balle yaga abinda zai dauke mashi hankali game daita,  in short the room is not that bright balle yaga abinda ke jikinta. Kai tasleem ta daga mashi, bai k'ara cewa komai ba ya fita yana tunanin yanda maganar mum dinshi  ya dagula mashi komai,  wato gashi zai zama kaman bawanta,  haka ya fita daga bangarenta ya koma nashi,  to his surprise  yanda ya bar gadon shi haka yake ,babu alaman gyara,  zama yayi yana cire shoes dinshi, 
"wato I should repeat myself... " ya fad'a looking at the room,
"we shall see... " ya fad'a yana mikewa wanka yayi ya dawo ya kwanta.
Sai yau da karfe hudu rashida tazo gidan tasleem, Tana shiga ta tambayi hannatu wato daya daga cikin Mai aikin tasleem inda take,  nan ta rakata inda tasleem ke zaune Tana kallon zee cinema, sanye take cikin another doguwar riga amma na shadda red, she look so cute and young, in bq wnada ya Santa ba babu Mai cewa itace matar wannan aljannan doran kasa,   Tana ganin rashida ta daka tsalle ta Mike ta rungume ta,  kamshin jikin tasleem kawai yasa ta fara hawaye,  her heart is burning, jin shessheka yasa tasleem dake rungume daita daga Kai, 
"babe... Why kike kuka... " tasleem ta fad'a voice dinta na rawa about to break in to tears too, cikin matsanacin zafin da rashida bata san Za ji ba tace
"besty I miss you... Am happy for you... "ta fad'a Tana hawaye sosai,
"tou kuma sai ki Kama kuka?.. Nidai dan Allah ki Diana... " tasleem ta fad'a Tana turo baki kaman wata yar karamar yarinya,  rashida kasa daina kuka tayi saboda kishi, before Tana tunanin if har Tana iya zuwa kusa da inda yarima yake is OK for her but now she have an inch and she want a mile,  yanzu ta samun hanyar shiga inda yake amma kishi kuma na neman  lalata mata duk plan,  ganin tasleem gidan nan makes her want to dive knife into her,  bata san zataji hakan ba, jawota tasleem tayi Tana cewa
"wallahi kou ki daina kuka kou nima in farayi... " tasleem ta fada Tana kokarin fashewa da kuka,  ahankali rashida ta zauna Tana kallon falon da tunda take bata taba ganin inda aka zuba so much wealth ba,  lokaci guda kuma sai ta zabura Tana cewa
"ni banga zama ba...now zo ki bani tour a wannan gidan dake gari guda... "ta fad'a sounding kaman VA ita bace take kuka sosai few seconds back,   sai lokacin tasleem ta saki ranta Tana cewa
"hmmm besty ni ina na sani a gidan nan... Tunda na shiga gidan nan babu inda nake lekawa sai motata...kuma dana gani sai in koma nan... " harara rashida ta balla mata Tana cewa
"ya zaayi ke da gidan ki bazaki leka koina ki san inda gidan yake ba... Nidai muje Muga duk lungu da sako dake gidan nan... "  ta fad'a sounding so lively, 
"tou why not ki fara chan wani abu... " bata bari ta k'arasa ba tace
"haba wa ke ta abin sha ana maganar kashe kwarkwatan idanuwa... Now let's start with your own part.... "  ta fad'a hannunta cikin tasleem,  nan fa suka shiga bed room din tasleem,  rashida is a social person so she knows lots of expensive things tasleem doesn't know,  bags dinta lefen alone ta kurawa ido sabida tasan Millions nawa ne. Bata ankara ba tasleem ta bude dukkan closets dinta shake da kayan sawa,
"daman baki ga lefe ba... Gasu... " tasleem ta fad'a sounding so free, nan rashida ta wage baki Tana kallon irin sutura da akayi mata, abunta ya tashi daga not only wishing to have yarima but also jealous of tasleem, tasan kou duk abinda mum dinta Ke dashi bai isa a hada mata irin kayan falon tasleem ba, tun yanzu ta fara kishin tasleem ta fita kayan daki despite bata da assurance if she's even coming in or not, but one thing is Amanda ta bata so much hope that doesn't make her think of negativity sai zallan positivity,
"besty ke kanki kinsan in nace kayan nan zan tsaya kallo the whole time will go away.. So kawai muje in ga sauran wurare... Next time kuma sai in dawo mussanman Don kallon kaya... "ta fad'a mata, nan tasleem ta rufe closet dinta sanann suka fita daga bed room dinta zuwa sauran bed room dake nata Bangaren, kou dakin masu aikinta kawai abun kallo ne, suna da makeken Italian bed da babban closet kowa da nashi, suma sai da akayiwa kowacce daga cikin su new clothes masu tsada har goma each sanann ga shoes na gayu. Bayan sun gama ganin Bangaren tasleem suka fita main falo, daman ita rashida ba komai take son gani ba sai Bangaren yarima, tasan talseem is stupid and she won't hesitate to show her, suna fita rashida tace
"naga gida guda ne amma ina Bangaren mijin...ki... " ta k'arasa da kyar sabida takaici,
"Anya yana da Bangaren a gidan nan... Nidai ban sani ba... " tasleem ta fad'a sounding care free,
"haba don't talk like this mana... Mijinki ne fa.... At least ya kamata ki san some things game dashi... " inji rashida, baki tasleem ta tabe tare dacewa
"nidai muje muga gidan... " tafad'a heading to the door next to wanda suka fito, hannu ta saka ta bude, ita kanta sai da ta zaro idanuwa Tana kallon dakin shake da kaya, baki rashida ta bude Tana cewa
"wannan ma naki ne?... Chabdin... Yar gata... " ta fad'a Tana shiga dakin, shima dakin sai da suka zagayeta tas tare da duba bed room har da closets, nan MA da akwia kayan sawa da kuma kayan bacci na mata, Rashida rasa inda zata saka kanta kawai tayi, suna tafiya hawaye na taruwa idonta suna maidawa, nan suka shiga dakin tsakiya,tun daga falon suka gane dakin yarima na saboda shoes dinshi dake nan
"asshe nan ne dakinshi.... " rashida ta fad'a Tana shiga falon tare da lumshe idanuwa saboda sanyin dataji yau gata a dakin habibinta,
"pls besty ki zo mu koma... Kar yazo ya tarda mu... " tasleem ta fad'a daga inda take tsaye a bakin kofa Don Tana ganin palm sandlers namiji bata k'ara talking any step zuwa dakin ba Don tamkar taga dodo haka take ji, she feels kaman yana ciki,
"babe shigo ciki mana... Ba dakin mijinki bane?... Pls come in... " rashida ta fad'a Tana nufan wata kofa... " da sauri tasleem tace
"nidai ki fito... Wallahi kar ya tardamu nan... " ta fada jikinta na rawa,
"haba nidai wallahi yanda na duba dukkan sauran part din haka zan duba nan... " ta fad'a Tana bude wata kofa, tasleem kin shiga tayi saboda tashin hankali, babu abinda take sai kiran rashida ta dawo amma Sam bata dawo ba instead sai ta shiga bed room din data gani tare da lumshe idanuwa Tana kallon gadon that is a bit rough alaman an. Kwana Kai batare da an gyara ba, cikin matsanacin fargaba tasleem tace
"ni wallahi besty na koma falo... In ya tarda ki sai ki san abinda zaki fad'a mashi... " ta fad'a Tana komawa bangarenta da sauri tare da waige waige.

Thanks
[3/14, 6:28 AM] +234 703 008 7807: 28💚❤💙💜💛
Sakaci
🧡💚❤💙💜💛

®Zuwairat (ummumaryam)

2⃣8⃣

Bata wani damu kou kawo wata tunani ba ta je main falo ta zauna Tana kallon both kofar part din yarima dana shigowa ciki. Rashida kam ganin yau gata GA makwancin yarima yasa taji wani irin sanyi cikin ranta,  idanuwa ta lumshe while entering the bedroom


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login