Showing 78001 words to 81000 words out of 323952 words

Chapter 27 - Sakaci Book One Complete Hausa Novel

27 Sep 2025

2165

tana cikin fushi dashi, yana ganin ta zuba mashi ido ya Mike ya komo kusa daita tare da sadda Kai kasa,
"tun dazun ina ka tafi.. " shine abinda ummah da mood dinta ya sauya tunda taga yanda tasleem ta Koma ta fad'a mashi,
"ina nan... Banje koina ba... " ya fad'a kanshi kasa,.
"nan ina?.. " ta sake asking, 
"bacci nayi... Ji nayi kaina na ciwo... Shine na dan kwanta in huta... "
"ranar daurin aurenka shine zaka ce ka kwanta ka huta?... Aliyu wato you want to show your stubbornness kou...dole sai ja nunawa kowa baka son wanann auren.... Wallahi banyi regretting wanann hadin da akayi ba sai da naga tasleem dazun.... " ahankali yarima ya daga Kai ya kalleta,
"I regrets it so much but I know babu abinda zan iya yi because it's meant to be.... Amma zan yi maka wata magana for the last time.... " ta fads tana gyara zama,  idanuwa Aliyu ya lumshe tunda yasan inda ta dosa,  yasan ba komai bane sai warning da aka saba mashi kaman an bashi the most expensive crate of egg ya Kai wani waje,
"in ka cutar da tasleem ban yafe maka ba... Yanda yarinyar nan ta koma saboda wanann auren wallahi if you make things worst for her Bazan yafe maka ba kou da kuwa bayan raina ne... " idanuwa Aliyu ya daga ya zuba cikin nata tare dacewa
"haba ummah... Shikenan ni ban da iko da ita?..ai wanann kalaman sunyi min zafi da yawa.... " ummah b'ata Bari ya k'arasa ba tace
"ban damu ba... I don't care how hot they are... Dole in fad'a maka abinda ke cikin raina saboda nasan halinka... Bance taslem bazatayi maka abinda mata zatayi miji ba... Sanann bace kar ta sauke nauyinka dake bisa kanta ba... Bace kar kayi abinda ya kamata daita ba... Amma sam kar ka zalunci wannan yarinyar... Nasan ba komai  yasa wannan yarinyar ta koma hakan ba sai Don fargaban zama da Kai... Tou wallahi da kaina zan dinga zuwa Don ganin irin zaman da kuke daita... Nasan you will say kar ta fad'a... Amma ka sani if you hurt her ban yafe ba... " ummah ta k'ara maimaita mashi, shuru yarima yana sauraron abinda mahaifiyar shi ke fad'a mashi, she always warn him amma yau she's hotter, 
"ummah... Bani da hakki... Kanta... Amma zan b'ata nata dake kaina... " yafada kanshi kasa,  ummah ta gane da abinda yake nufi bashi da hakki kanta,  wato bazai kusance ta ba
"wannan kuma matsalar kace... Kou kadan bai dameni ba... " ta fad'a kaman she's not talking to her fav.  Ba komai ke saka mata hakan ba sai yanda taga tasleem,  dole ta nuna mashi she's very important to her, b'ata taba jin ranta ya bace irin na yau ba and dole tayi protecting dinta.
"ina iya tafiya   " ya fad'a cikin sanyin murya, shuru ummah tayi, ganin tayi shuru yasa bai tashi ba, shuru tayi for  moment trying to calm her nerves, kafin hajiya amina ta fara magana sai yar uwarta ta fara cewa
"kar ka biyewa  abinda fulani take cewa..matarka ce kuma kowa yasan cewa miji shine head of the family... Kar abinda take cewa yasa ka zama cold husband.... Take charge... Kaine shugaba itace karkashin ka so do your thing..." ta fad'a mashi,  shidai shuru yayi,  hajiya dake zaune babu abinda take sai hararan sister dinta,  ita kam b'ata damu ba sai da ta Kai inda take so sannan tayi shuru,  ahankali hajiya ta dora hannunta kan yarima tana cewa
"my fav... Kar kace ummah b'ata damu Dani ba... "
"AI Hakane ummah...sam baki damu Dani ba... " b'ata Bari ya k'arasa ba tace
"haba fav... Damuwa da Kai din ne ya jawo haka... You're my two special people put together.. So I have to make sure everything is alright..."
"shine kike ta jera min Allah yaisa?.. " inji yarima kaman zaiyi kuka.
"ai nasan tunda kana tsoron Allah yaisan bazaka yi abinda zai sa ta Bika ba...so pls my fav... Kayi hakuri da auren nan... Nasan insha Allah da bakinka zaka ce nagode da kuka bani tasleem... " b'ata k'arasa ba yace.
"hummmm" alaman that is never happening,
"yes... I know.... Nothing good ever come easy... Many marriages da akayi base on love doesn't last... Yarinya ita zata kawo miji shi MA na namiji ya tura iyayenshi out of so much love amma lokaci kadan sai kaga komai ya watse... But a naku case din.. She's now your wife...you don't know her much kawai dai kana ganin ta... Now kana da daman da zaka Santa... Ta sanka ku gane junanku while being married to each other... So pls  keep calm and see the good in her..." ta fad'a tana shafa kanshi, shuru yayi yana sauraronta,  bawai because he want to keep calm and know her ba but because yanzu anyi mashi katangan karfe daita,  he wanted her to see what he is made of,
"ummah... " ya kirata ahankali
"Naam my fav.. " ta amsa mashi,
"yanzu dai ki fadamin abubuwan da ya kamata tasleem ta dingayi min Don wannan baki yafe ba might make me not to say one word with her... " ya fad'a mata,  dan murmushi ta saki tace
"haba nifa ba ina nufin katanga nayi maka daita ba... Aa... Kawai zalunci ne banso... Kuma Kai kanka in kana abu na zalunci ka sani... kuma ka san Wanda ba zalunci ba... " inji ummah,
"naji... Amma hope dai in nace zan auri wata shi ba zaluntar ta nayi ba kou... " ya sake asking dinta
"aa ai wanann abune Wanda addini ya tsara... So don't even go there... " ta fad'a mashi,  zai bude baki yayi magana tace
" ka tashi ka tafi... Dare na karayi... " ta fad'a mashi alaman ta sallameshi,
"tou sai da safe... " ya fad'a yana mikewa. 
"Allah ya kaimu.... " ta fad'a mashi,  nan ya fice daga dakin yana jin bakin ciki, wajen dad dinshi ya sake lekawa amma still da akwai mutane,  har zai koma yaji ciroma yana cewa
"ka shigo ciki mana... " ya fad'a mashi,  sai lokacin ya shiga ciki,  bayan Mai martaba ya sallami wasu ta rage dafa shi da wasu cabinet dinshi ya kalli yarima yace
"wai Kai ta akayi kana ango amma kana yawo Kai kadai babu abokai.... " ya tambayeshi yana kallon yanda ya hade rai, shuru Aliyu yayi baice komai ba, 
"ai wannan angon daban ne... Chan na ganshi yana tafiya kaman mara gaskiya shi kadai... " inji ciroma wato crown prince, nan dai Mai martaba da mutanen shi suka dinga bashi advice kan zamantakewar aure.  Ya kai kusan minti arbain nan zaune sannan aka sallameshi,  haka ya fita shi kadai babu aboki kou guda sai ka rantse bashi ne angon da akayiwa gaggarumar biki ba,  wajen motarshi ya nufa ya shiga ya Kama hanyar waje,  bayan kaman minti talatin yana driving yayi parking a wajen da banda fruits babu irin fruits da zaka nema wajen da bazaka samu ba,  har da Wanda ban taba gani ba duk suna dashi,  nan ya mika kudi yace a bashi fruits, 
"wane irin fruits zaa baka... " Mai wajen ya tambayeshi yana kallon yawan kudin dake hannunshi,
"anything that is not poison kawai hado min.... "ya fad'a mashi,  nan aka fara cika leda da fruits,  kowanne leda da akwai kalan fruits din dake ciki,  sai da aka cika mashi kusan leda bakwai da Fruits, bayan mota ya bude aka zuba mashi sannan ya figi motar ya bar wajen,  bai nufi koina ba sai inda ake saida Nama nan MA ya saya kaman zai ciyar da akalla mutane ashirin suci su koshi. Gidanshi  ya nufa,  babu abinda yake tunani sai shi yau ya zama Mai dayab abu kawai Don wanann yarinyar taci, 
"what a life... " ya fad'a heading to makeken parking space da aka tanada Don ajiye motoci not less than 5, gjdan yasha haske har baa magana,  gidan ya ginu har iya ginuwa, da sauri Mai gadi da security suka nufo inda yake fita daga cikin mota, cikin total respect suka gaidashi,  hannu kawai ya daga masu sannan y nuna masu abinda ke bayan seat dinshi,  nan suka bude suka fara fiddowa, yana kallo aka. Fiddo kayan duka,  yasan yanda Dan Adam yake,  he knows carrying this items might make then salivate, 
"ku ajiye wasu daga cikin kayan sai kuyi amfani dashi   " ya fad'a masu,  nan suka nuna godiyarsu suja bishi fa sauran kayan,  gidan is round in shape,  da glasses dake gidan yafi blocks yawa,  yawanshi  gidan glasses ne,  ginin Sam ba nan bane,  irin gidan turawa da in an bude curtains zaka GA abinda ke faruwa ciki kou kaga waje farau din nan haka yake,  part biyar ne dungule waje guda, ciki har da nashi part inda shine ke kallon kofar shigowa falo, gidan shares a general parlour da general dining Wanda shine abu na farko da zaka gani in ka shiga ciki,  general falo din na da girman gaske,  sai a  gina 3 bed room flat da girman general falo din,  bai san a saka kaya ba sai da ya shiga ciki, set din manyan royal seats ne guda biyu sai manyan curtains Wanda suka rufe glasses din, curtains din suna da tsawo sosai Sannan suna da kauri,  yanda kujeru ke kala biyu haka suma curtains din ke kala biyu,  kowannensu  suna matching da sets. Falon ya mugun hadu,  baki ya tabe alaman babu abinda ya burgeshi,  shi he's the kind of man da bai son tarkacen kaya... Inda zaa bashi dama yayi decorating falonshi da kawai zai samu expensive cushions ya ajiye, he don't mind two or three sofas for as long as they are expensive.  Masu gadin dake biye dashi da leda ya juya ya kalla sanann yace
"Kuna iya ajiyewa nan... " ya umarce su,  cikin girmamawa suka ajiye suka juya tare da barin wajen.   Bai k'ara dumwa ya kalli wani waje ba ya bude first door by he's left, yana budewa yaga it is well decorated, to he's believe zai ganta nan dakin,  kowanne Bangaren na dauke da 4 bedroom flat,  duk bin dakunan da suka sha manyan gadaje yayi amma b'ata nan,  ficewa yayi daga nan ya koma next one,  shima yasha kaya amma duk ya gama zagayewa babu ita ciki,  fitowa yayi general falo yayi tsaye alaman yana tunani,
"wato three whole part for her.  Lallai MA... " ya fad'a yana kalle kalle,  wannan abun VA karamin haushi ya bashi ba, wato ita kadai ta amshe koina kenan bayan b'ata da matsayi kou guda a wajenshi,  face dinshi daure ya koma right hand side.. Yana bude kofa yaga wata budurwa zaune,  falon sai kamshi kawai yake,  shiga ciki yayi Hindu tayi sauri sauka daga kan kujera ta durkusa nan kasa Tana gaidashi,  inda kasa ba dashi ake ba... Kou kallon inda take baiyi ba ya ya tsaya for about 30 seconds,  da sauri Hindu ta Kama hanyar inda anty maryam ta nuna masu as dakinsu,  juyawa yayi yace
"Tana ina... " ya tambayi Hindu dake faman sauri zata bar wajen,  cikin girmamawa ta nuna mashi dakin da tasleem take, 
"ki kirata.. " ya sake fad'a mata babu musu ta Kama hanyar dakin da tasleem ke kwance,  lokacin tasleem na kwance wayarta on loud speaker,  babu abinda ke tashi sai voice din hajiya zainab,  story take karanta mata while tasleem na lumshe idanuwa,  sallama Hindu tayi in a low and respective voice, dukda tasleem ta iya magana hakan bai hana su b'ata girman ta ba because na gaba yayi gaba kou da kuwa dan cikin ka ne, shuru tayi baa amsa ba,  sake maimaita sallama tayi a bit louder than before still tasleem data lafe a jikin pillow alaman bacci na neman daukata b'ata ji ba,  maimaitawa tayi da karfi tare da Dan yaye curtains din,  sai lokacin tasleem ta daga Kai gabanta na mugun faduwa,  amsawa tayi Tana mikewa zaune,  kallon wayarta tayi tace.
"mummy give me a second.... Hindu ce ta shigo... " ta fadawa mum dinta dake kan waya sanann ta kalli Hindu,  murmushi Hindu tayi tace
"shine yace in kiraki.... " da sauri tasleem tace
"shi wa?.. "ta fad'a voice dinta na rawa,  hajiya najin abinda ke faruwa ta katse wayarta,
"mijinki mana... Yana jira  ."Hindu vata jira abinda tasleem Zatace ba sai ta fita daga dakin,  Tana zuwa falo taga yarima tsaye ya rike waist yana kallon falon,  dukda mood dinshi sai da ya yaba da falonta,  it's full of most expensive items bai taba ganin irinsu ba amatsayin shi na Dan sarki that have been to places.
Hannuwa tasleem ta fara yarfawa Tana kallon wayarta Don yiwa mum dinta magana sai taga ta  yanke call din,  cikin matsanacin fargaba ta sauka daga kan gado sanye da doguwar rigar lace Wanda zaiyi hundred plus a kasuwa
,"na shiga uku..." ta fad'a Tana kokarin kuka,  cikin kasala ta Kama hanyar waje Tana  aduar dayazo ranta, da kyar legs dinta ya kaita falo,  yarima ya bawa kofar baya, jikinta na rawa ta iso kusa dashi,  haka nan yasan she's behind him  juyawa yayi cikin kasaita ya kalleta,  kan tasleem kasa, she's trying so hard to stand but it became impossible,  kawai sai ta zame ta zauna kasa,
"ke kar in k'ara jiranki... Am I clear... " da sauri ta daga mashi Kai,. "good... Abincin ki na chan... " ya fad'a yana nuna Mata hanyar falo,
"and duk abinda kike bukata ask... Or kina iya amsar number wayata kiyi min text....and ki sani zaki dinga gyara bangarena but make sure ban ciki before you enter...hope kin gane" ya fad'a mata,  tasleem datayi suman zaune sabida yau gata GA Wanda tafi tsana kuma tafi jin tsoro duk duniya kusa da juna a gida  daya sanann a inda babu Mai cetonta kou da kuwa Kasheta zaiyi,
"ke in ina maki magana kina shuru zan cire few minutes ciki time dina inci uwarki..." da sauri ta daga mashi Kai dukda in banda zagin dayayi mata babu abinda taji sabida fargaba da tsoro,  bai k'ara cewa komai ba ya fice daga dakin, tasleem  Sakin wani irin ajiyan zuciya tayi because ji tayi like she just escape from a lions den.  Yafi minyi biyar da fita sannan ta samu ta iya mikewa,  abun nasu ya zo da bambanci, baka cewa amaryace,  babu dokin komai cikin ranta wai fargaba,  she feels so free at this moment,  kawai a tsoron ta yana kiranta zai fara daukan ta da Mari,  it was a lot easier than sje thought  cikin kankanin lokaci taji wani irin natsuwa, nan take all loose strength dinta ya dawo,  mikewa tayi ta ware hannuwa  Tana sakin ajiyan zuciya da ita kanta ta dade rabon da tayi irinshi.  Da sauri tayi pinching kanta Don ta sani if she's dreaming or not, 
"wai Allah... Narrow escape... " ta fad'a Tana dafa chest dinta, daga inda take tsaye takwalawa Hindu kira,  da sauri Hindu ta fito cikin tsoro saboda yanda ta kirata,  Tana zuwa taga tasleem tsaye kaman ba amaryar da aka kawo gidan miji yau ba,
"Kinga ikon Allah!!..." ta fad'a idanuwanta duk waje,
"meye... " ta tanbayeta,
"wai bai bugeni ba... Yace duk abinda nake so in tambayeshi... Can you believe that... " ta fadawa Hindu cikin so much excitement,  kou kadan baka cewa itace ta kusa mutuwa sabida fargaban abinda yarima zaiyi mata a yau,  kou kadan bata kawo anything intimate cikin ranta ba,  because it's very far from her brain,  kawai tsoronta ya dinga zaluntar ta, amma she was so surprised,  murmushi kawai Hindu ta saki bata ce komai ba,  tsalle tasleem ta daka Tana cewa
"ihuhuhu.... Am. So happy... Wallahi ya bani mamaki... Zan. Fadawa ummah da besty da kuma mummy na... " ta fad'a cikin farinciki, now she's back to  her former self, where she says what ever she see,  where nothing pass her eyes and judgement, daman zancen auren nan ne ya ladabtar da ita and now that it's not as bad as she thinks zata koma her former life,  now it's even better.  juyawa tayi ta Kama hanyar bed room sai kuma tayi saurin juyawa Tana cewa
"GA abinci chan... " ta nuna mata inda yarima ya nuna dukda bata San exactly where ba,
"in Kuna ci kuje ku dauko kici..." ta fad'a Tana shigewa dakinta Don kai rahoto as usual...


Thanks
[3/14, 6:28 AM] +234 703 008 7807: 26💚💜❤💙💛
Sak'aci
💚🧡💜💛❤💙

®Zuwairat (ummumaryam)


2⃣6⃣






follow me on instagram@zuwairatummumryam)


on wattpad@ummumaryam29 for those that want my old novel.




Tana shiga ciki ta dauki wayarta,  duk ta rasa wanda zata fara kira,  number mom dinta tayi dailing,  hajiya zainab na ganin kiranta sai Taki picking, kawai fargaban ta taji tana kuka ta tada mata hankali kou kuma ta fad'a mata yayi mata wani abu naughty Don tasan tasleem ba hankali gareta ba, sake dailing tayi Tana Dan dire dire kan gadon da take zaune saboda murna,  tankar taga dodo bai cinyeta ba hka take ji,  she feels so excited and happy,  still hajiya zainab bata daga ba,  da ta sake calling a karo na uku sai taji ta kashe
"Babu rabon kisha labari... " ta fad'a Tana neman number ummah,  bata damu ta san ce wa karfe goma ya wuce ba, sai da wayar ya kusa katsewa ummah da hankalinta ya gama tashi tayi picking,  har ta kwanta ta fara bacci saboda gajiyan hidima,  Tana ganin kiran hankalintabya mugun tashi, cikin ranta babu abinda take cewa sai
"dukda warning din dana yiwa dan nan... " ta fad'a yayin da take picking wayar, 
"ummah... " taji voice din tasleem a kunnenta,
"Naam gimbiyata... Baki kwanta ba... " ta fad'a Tana sauraron how she sound Don ta gano if da akwai matsala,
"ummah kin San me?... " ta fada cikin kwanciyar hankali, wani irin sanyi hajiya taji cikin ranta jin voice din tasleem ba yanda ta sa ran zata ji ba
"menene gimbiyata... " ta tanbayeta,
"ummah wai ya shigo... Kuma wallahi bai dokeni cewa... Cewa ma yayi duk abinda nake so in tambayeshi... " ummah murmushi kawai ta saki tana lumshe alaman she want to go back to sleep,
"ummah  nasan ke kikayi mashi magana... Naji dadi sosai.. Dan Allah ki dingayi mashi magana kullum


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login