Showing 177001 words to 180000 words out of 323952 words

Chapter 60 - Sakaci Book One Complete Hausa Novel

27 Sep 2025

2194

as the heart is on fire, she couldn't blink her eyes, haka kawai tayi zaune ta Kama yatsanta da hakoranta sai kuma ta dage sai yarfa dayan hannunta take, sai ka rantse the veins zasuyi cutting daga cikin hannunta saboda yanda suke moving abinka da slim fingers ba kaman namu masu kauri ba.
Hindu loves tasleem so much da ta dinga kallon window kou yarima ya fita Don tasan if tasleem is coming in soon, inda tasleem ke zama nan take zama, tana nan zaune sai taga yarima ya fita da waya a kunnenshi, sai da ta tabbatar ya fita daga Gate an maida gate an rufe ta Mike ta fita zuwa main falo hoping zasu hadu da tasleem ta taho amma shuru, she knew itace tayi pushing dinta Into his part Don haka ahankali ta bude kofar ta tarda tasleem zaune cikin yanayin da ya mugun firgita ta.

In kika karanta baki biyaba Allah yaisa, 300 is ur ticket, if you can't paydon't read, wayanda suka biya suna son kudinsu, kou ba komai zasu saka card.
Thanks
[3/14, 6:36 AM] +234 703 008 7807: ❤💙💛
Sak'aci
💚🧡💜💛❤💙

®Zuwairat (ummumaryam)


56





A gigice ta shiga dakin tana kallon yanda tasleem ta zaro idanuwa tana cizon yatsanta sosai kaman zata fasa sai kuma tana yarfa dayan hannunta in a horrific way,
"hajiya!.. " Hindu ta kirata as she moves closer to her,  taslem bata kou kifta idanuwa VA sanann bata daina abinda take ba, 
"hajiya... Lafiya?..?"ta tambayeta cikin gigicewa da tashin hankali,  ganin she's not talking nor reacting to her question yasa ta Kama mata hannu tare da kokarin cire hannunta dake cikin bakinta,  wani irin k'ara tasleem ta fasa lokaci guda Wanda yasa ta tsorata sosai tare da sake cewa
"hajjya meye haka... Me ya faru... " ta tambayeta as she's holding her two hands,  tana jin yanda  hannunta ke rawa sanann her hands seem very cold,  ihu ta saki again not saying a word but sai ihu,  idanuwanta duk waje amma kou daya babu hawaye saidai sunyi jajir kaman garwashi,  no one cab give the exact description of abinda ke cikin zuciyar ta,  as ahe sits there shouting so is all the love she have for rashida running out of her system and how she always talks about how bad yarima is rushing in, 
"wayyo ...ummahna... " was word daya fita daga bakin taslem dake rawa sosai, 
"Dan Allah hajiya ki fad'a min abinda ya faru" inji Hindu da bata taba ganin taslem haka ba,
"kin... Cuceni... " taslem ta sake fad'a cikij wani irin nishi da sai ja rantse she's in labor room about to put to bed saboda yanda take magana sai kace tana cikin azaban nishi,  Hindu da ta rasa abinda ke faruwa ta saki hannunta daya da sauri tasleem ta dora kan chest dinta tana cewa
"wayyo ...ciwo... Ciwo... Ciwo... " ta fad'a  tana dukan  chest dinta in a very terrible way, sake Kama hannun Hindu tayi ta daga idanuwanta ta zuba cikin na Hindu
"ciwo... " ta fad'a mata as tears na neman zubo mata for the first time  since she's heard her besty is becoming the wife of the man she have fallen in love with,  bata taba sanin kishi ba sai this instant,  the thought of Rashida tare da yarima alone is going to kill her,
"ina ke maki ciwo... " Hindu ta tanbayeta, 
"zu... Ci... Ya... Ta... " ta amsa mata kaman she's learning how to talk for the first time,.
"sannu... Tashi mu Koma... Bangarenki..." Hindu ta fad'a tana kokarin janta ta mike,  gani tayi kafarta Mai mikewa tsaye,  if she tries to stand her up sai legs dinta suyi shrinking kaman ba na mutum ba, wanann yasa Hindi sake shiga serious tashin hankali,  sake kokarin mikar daita tayi taga legs dinta sun lankwashe baya, 
"ciwo... " tasleem ta sake furtawa under serious and terrible voice,
"yanzu ya zanyi... " Hindu ta fad'a tana fashewa da kuka saboda tashin hankalin abinda tasleem keyi, 
"ciwo... "tasleem ta sake furtawa tana dora hannunta kan chest dinta in a serious  way that makes Hindu burst into another serious tears tana kallon taslem da hannunta dake kan chest dinta ke rawa sosai sabida tashin hankali, ganin tsayuwar ba Mai yuwa bane yasa Hindu komawa Bangaren tasleem ta dauko wayarta,  she wants to call hajiya zainab amma bata san yanda zatayi ba fitowa tayi da wayar ta dawo bangaren yarima tana cewa
"saka min wayar hajiya in kirata... " ta fad'a mata tana mika mata wayar, idanuwa tasleem ta daga ta mika hannunta dake rawa sosai kaman na tsohuwar datayi hundred plus, Hindu na dora wayar kan hannun ya fadi kasa she can't hold it, kou kadan bata da strength din da zata rike common phone dinta,  she's so taken unaware of the situation that the shock have taken over all her body,  daukar wayar Hindu tayi daga kasa ta sake mika mata ya sake faduwa,  hannunta sai rawa yake,  babu abinda take iya cewa sai ciwo, da gudu Hindu ta fita zuwa wajen masu gadi  luckily Umar na wajen,  cikin tashin hankali Hindu ta fad'a masu Umar ne ya dauki wayarshi ya fara kiran yarima amma sai yaji layin busy bai shiga,  he called him kusan sau shida all busy,  daga nan ya kira jakadiya ya fad'a mata matar yarima Aliyu bata da lafiya kuma ana kiran Aliyu bai daga ba,  suna gama waya jakadiya dake cikin fad'a ta je har chambers din ummah ta fad'a mata ga abinda ke faruwa,  salati ummhq ta farayi cikin serious tashin hankali tana daukar wayar ta Don kiran yarima taji busy,  nan ta kira number taslem lokacin Hindu ta dawo dakin da tasleem ke zaune tana cewa ciwo tare da dafa chest dinta,  Hindu daukar wayar tayi ta rasa yanda zatayi ta daga,  sau shafa face din wayar take Kama yanda take ganin sunayi if suna amfani da wayar,  in the process ta katse wayar, ummah sake kira tayi,  taslem  was looking at the phone amma kaman paralyze person babu abinda take iya yi,  this time luckily Hindu picked the phone,  cikin tashin hankali ummah tace
"gimbiyata... Me ke damunki... " ta fad'a sounding very very disturbed,  Hindu ce ta dora wayar a kunne as she hears magana tana kuka tana cewa
"gata nan... Bata iya komaj... " Hindu ta fad'a mata cikin serious tears,  salati ummah ta fara cikin voice dinta na rawa tace
"bata wayar... ""ta umarceta,  da sauri crying Hindu ta dora mata wayar a kunne  tasleem na jin voice din ummah na kiranta sai ga hawaye Mai zafi sun gangaro face dinta,
"gimbiyata... Tell me what's wrong... " ta tambayeta kaman zatayi kuka
"ummah.... " ta kirata da kyar
"naam gimbiyata... "
"ciwo... " ta furta mata kaman she's learning how to make her first words,
"Inna lillahi waina ilahi rajiun... Gimbiyata ina ke maki ciwo haka... " ummah ta fad'a as taji voice din taslem ya koma kaman ba nata ba
"zu... Ci... Ya... Ta... " ta amsa mata, ummah rasa abinda zatayi tayi,  da sauri ta fara cewa
"ke... Ki kaiwa masu gadi waya.." ta fad'a directing maganr ta to hindu, nan Hindu dataji abinda tace ta tashi da gudu rike da waya hannunta zuwa bakin gate,  har lokacin Umar bai har kokarin kiran yarima ba,  Hindu na zuwa ta mika mashi wayar ya amsa tare a sallama nan ummah ta tambayeshi if ya iya tuki mota ya amsa mata da eh,  nan ya fad'a mashi ya maidawa wacce ta kawo mashi waya, mikawa Hindu wayar yayi sannan ummah ta fad'a mata taje dakij taslem ta nemi makullin motarta ta kawowa Wanda suka gama waya dashi sanann ta koma ciki ta kira sauran masu aiki su ruko taslem su taho daita fad'a,  yanda ummah ta fada haka Hindu tayi,  tana kuka ta shiga ta dauko hijab din taslem tare da old key wato makullin motarta Wanda aka zo mata dashi daga gida,  nan dai suka kamata kaman wata gawa ita kawai sai cewa take ciwo tana kall0n faces dinsu with her dry face but red eyes aka saka ta bayan mota Umar yaja su zuwa fada, kafin su iso hajiya amina ta kira Dr daga palace hospital,  suna shiga daita bangaren ummah ta dinga kallonta tana jujjuya kanta tana cewa Ummah ciwo,  nan dai aka shiga bata taimako na gaggawa dukda Dr ya tanbayeta abinda ya faru amma bata iya magana.
Yarima na zuwa office ya cigaba da wayar daya fara tun yana fita daga gida, Bluetooth ya cire daga kunnenshi yayi relaxing da wayarshi yana juyawa ahankali  Kan kujera daya zauna a Kai sai hira  kawai suke maganar ba wani Mai amfani ba but he have to talk to her.  Incoming call yaji ya duka tare da rolling idanuwa yana cewa
"baby it's ummah... She havr been calling..bari in daga... " ya fadawa rashida,  nan yayi pickling wayar ummah
"what did you do to tasleem... " shine maganar da ummah tayi mashi
"wace tasleem... " was his reply
"you're very stupid... Nace me kayiwa taslem... " ta fad'a in a very harsh mood,
"ummah ni me nayi mata...ask mana if I did anything wrong to her... " ya fad'a yana hade rai
"gata nan kwance rai hannun Allah... Nasan it's not just like that... What did you do to her... " ta daka mashi tsawa
"wallahi ummah babu abinda nayi mata... Kawai I told her zan k'ara aure kuma it's rashida... That's all... " ya fad'a cikin sanyinmurya saboda wani Abu dayaji cikin ranshi,  he is old enough to know his very own feeling amma bai gane wannan abun da yake ji ba,  kawai dai gashi nan
"Aliyu so you want to Kill her... Ka fad'a mata kawarta zaka aura... Kuma. Baka damu da halin da zata shiga ba ka fita daga gida kana waya hankalinka kwance...ka kyauta kenan... Aliyu ka kyauta kenan... Aliyu if Nace naji dadin abinda ka aikata nayi maka karya... A haka zaka zauna da su biyu?... A haka zakayi adalci while your heart is in the same position?... " ummah ta fad'a kaman zatayi kuka,
"ummah sorry... ".ya fada calmly with his eyes closed, 
"ba zancen ummah sorry bane...aliyu Bazan iya bari ka shiga hallaka ba... If har kana ganin su biyu zasu zamr maka matsala since rashida kawai kakeso kana iya kawo takardan taslem sai ka auri rashida ita kadai, ..." da sauri ya Mike zaune tare da bude idanuwa yana cewa
"haba ummah... Bai kai haka ba... Ni ban san maganar zai saka mata wani ciwo ba... Am Sorry pls... " ya fad'a voice dinshi na rawa sosai, ummah rasa abinda zatafada mashi tayi as she sit right there watching tasleem dake kwance da Karin ruwa a hannunta, 
"Aliyu ina ganin bazakayi adalci ba... "
"ummah zanyi... Wallahi zanyi ummah am so sorry..." ya fad'a kaman shi ma zaiyi kuka, 
"ummah how is she... "ya fad'a cikin sanyimurya,  ummah was mad at him da bata amsa mashi ba ta katse wayarta kawai.  Nan ya ajiye wayar hannunshi yayi relaxing yana jujjuyawa ahankali with his eyes closed,  tunanin shi a dugule yake,  he wants to think about tasleem amma kaman someone is forcing his heart away from her,  yana a haka har kusan minti ashirin sai faman shafa gaban goshin shi kawia yake,  he is totally messed up,  kofar office dinshi aka bude sai ga baba sadik yashigo da sallama sanye da babban riga rike da big shasbaha Mai girman gaske,  zama yarima ya gyara tare da amsa sallama, kura mashi ido baba sadik as he is reciting some powerful surah a cikin ranshi,  yarima dake kallonshi saurin sauke idanuwa yayi tare da rufe idonshi as he is too hot for him to look direct into,
"baba.. Kai ne... Lafiya dai kou... " ya fada yana mikewa tsaye sanann kanshi kasa,
"lafiya lau... Daman nazo wucewa ta nan ne nace bari in shigo mu gaisa tunda kai baka zuwa gaidani... " ya fad'a yana zama dukda he have gotten the proof he is here for,  yasan da akwai sihiri jikinshi Don in da babu da zai cigaba da kallonshi har su gaisa amma he couldn't watch him, 
"aa ba haka bane aiki ne yayi min yawa... In kawo maka ruwa..." ya fada looking at his side instead of his front inda baba sadik ke zaune,  nan dai suka gaisa sanann ya Mike ya tafi.  Direct fada ya fadawa driver dinshi ya kaishi,  waje ya samu  ya zauna yana jiran Mai martaba,  bai martaba bai samu lone time ba sai bayan sallah asr sannan suka hadu da baba sadik,  Mai martaba was angry da bai shigo ba ya tsaya jiranshi, Bayan sun zauna baba sadik ya fara cewa.
"wato wannan yarom da akwai sihirin Mai karfi a jikinshi,...daya nayi mashi na gane... Sihirin dake jikinshi ba karami bane... " kallon mamaki Mai martaba yayi mashi yana cewa.
"sihiri kuma?...wato dai wannan yarinyar da zai aurace  .." mai martaba bai k'arasa ba baba sadik yace
"kar mu ambaci sunan mutum... Kawai abinda zamuyi shine adua... Amma zato zunubi ne kou da kuwa ya zama gaskiya... Sanann abinda zan fada maka shine.. Kar a hanashi auren wannan yarinyar... Don ina tabbatar maka da cewa da karfin sihirin dake jikinshi bai ganin kowa da arziki sanann kome zai iya faruwa indai aka hanashi... Yana iya barin kasar nan gabaki daya... Gwanda a barshi a inda zamu dinga ganinshi muna mashi magani cikin abincin da abunsha...don haka hakuri zakuyi dashi... Kuma. Ka fadawa fulani sakona kar taga bakinshi a wannan yanayin da yake ciki... " baba sadik ya fadawa Mai martaba,  sarki that look so furious ya ansa mashi da tou, baba sadik na kokarin tashi zuwa inda aka ajiye mashi abun ci da sha mahaifin rashida ya nemi ganin sarki,  sunan da aka furta mashi sounds familair that he thinks ina ya san wannan sunan,  bayan few seconds yace
"kaman uban yarinyar ce fa.. Yes shine uban matar abubakar... " inji sarki, 
"kou me ke tafe dashi?.. " inji baba sadik dake kokarin mikewa tsaye
"dan Allah baba ka zauna kaji abinda yake tafe dashi... Ina ji kaman in fad'a mashi ban yafe abinfa sukayiwa dana ba... Nasan dole suna da masaniya kan zancen... " da sauri baba sadik yace
"kar ayi haka... Kar kace masu komai... Ka kwantar da hankalinka... Kou Mai zaiyi daidai... Kawia muna bukatar yarima a kusa damu yanda zamu iya bashi abun karya sihiri... Kaman yanda na fada maka Abu kadan zai sa ya bar garin nan kuma da ita zai tafi wallahi kaji na ranste... Don haka hakuri shine maganin komai... " inji baba sadik dake kallon yanda Mai martaba looking like Aliyu in 70s,
"shikenan...amma ka zauna kaji abinda yazo dashi... Ni ban San manufar su ba... "
"na fad'a maka ka cire zargi daga cikin ranka... Ba lallai Wanda kakewa kallon makiyi ya zama makiyin ba... Wani a masoyi zai zaizo maka amma sam ba masoyin bane makiyi ne... Don haka ka cire zargi a ranka... " ya fad'a mashi cikin shawara, Mai martaba jinshi kawai yake amma he will deal with his whole generation when he got his son back,  nan akayiwa mahaifin Rashida iso ga sarki,  face din Mai martaba Sam babu walwala, kawai he is wondering their guts to temper with his family,  yasan shi ba mugun Mai mulki bane amma nobody touches his family and go Scort free,  cikin girmamawa mahaifin Rashida ya gaida sarki amma sarki bai amsa ba sai baba sadik ya dan kalleshi,  shi kadai yasan irin temper da yakeji Cikin ranshi,
"ranka shi dade... Wata magana ce ke tafe Dani... Yata ta fadamin suna kaunar juna da danka har take fadamin yace zai turo... " sarki kawai kallon shi yake as one gigantic enemy dake mashi magana cikin rainin hankali, 
" amma jiya Mai dakina ta shigo min da kuka tana cewa wai yar wajena kawar matar danka ce... Kuma uwar matar Dan naka wato surukarka tayi masu halaccin da bai kamata su bar yara suyi son zuciyar su ba...Don Allah Mai martaba ka bawa Dan wajenka hakuri kaman yanda zan bawa yata hakuri su hakura da wanann maganr... Turawa sunce a good name is better than silver and gold... " sarki dake sauraronshi kallon wnada yazo raina mashi wayau kawai yake, bai San yanzu sai ka haifi Dan da zai kai ka ya Bari ba, (rabbi kar ka bamu Dan da zai zama sanadiyar hawaye kou tozarta a garemu... Kar ka bamu yara masu son zuciya kou wayanda kansu kadai suka sani basu san ciwon wasu ba... Ya rabbi don't punish us with selfish and stupid children Don wallahi it's a big punishment to have a child who act with feeling for others, na wata American film dana kalla uwar take fadawa Dan iskan danta cewa da ta sani da ta juyar da mahaifyarta tayi adopting kare ya fiye mata sauki kan haihuwar shi) shuru ne ya Dan biyo baya na wani Dan lokaci before Mai martaba yace
"ai wanna maganar banza ce... Sam banga tudun dafawa a nan ba... Tunda suna kawaye bai hana su soyayya ba ai ba zai hanasu aure ba... Ita yarinyar da ta San halaccin da mahaifiyar kawarta tayi mata kuma dukda haka tayi soyayya dashi har ya kai ga maganar aure ai kuma Magana ta kare...kuma addini bai hana hadinsu ba... Don haka...ku shirya... Nan da sati guda a daura masu aure... " Mai martaba ya fad'a cikin anger da zaka gane Aliyu inherit some of his anger from his father, shi kanshi mahaifin rashida wonders why the king talks in such serious anger Don sam babu mutuntawa cikin yanda yake mashi magana sabanin sanda akayi bikin ummy da abubakar, bai San yarshi ta riga ta watsa mashi kashi a idon royal family ba,
"Mai martaba Allah ya ja da ranka... Amma ayi haka?.. " inji mahaifin rashida cikin girmamawa da sadda kai kasa, Mai Martaba zai bude baki yayi magaja suka hada ido da baba sadik dake mashi magana da ido kan yanda yake mashi magana hakan bai kamata ba, shuru Mai martaba yayi for a moment tare da sakin ajiyan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login