Showing 9001 words to 12000 words out of 323952 words
"farida?.. " ya tambayeshi, kai kawai yarima ya daga mashi alaman eh,
"kasan kaima fa kana da laifi...why did you ask in the first place... " ya fad'a yana kai grape bakinshi, hararanshi yayi without saying another word, sake katse wayar yayi, few minutes later sai ga blink daga wayar alaman shigowan message, yasan it's still her don haka bai bude ba. Kafin su tashi daga kan dining saida aka bashi miss calls sun kai ashirin amma babu Wanda ya daga.
"farida na ruwa... " mahboob ya fad'a yayinda da yake goge bakinshi da tissue Mai taushin gaske. Falo suka dawo suka ga hajjya ta Mike ta shiga ciki. Hanyar waje sukayi. Suna fita basu tsaya koina ba sai chambers din yarima, a bakin nashi kofar ma da akwai Mai bude mashi kofa, gaisawa sukayi da wannan saurayin Mai suna Umar is he's personal worker, duk wata hidima dake Bangaren yarima shi keyi mashi, shine Mai kula da wankin kayanshi dukda bashi ke yi ba, shine zai kaisu kuma ya amsosu, shine Wanda zai keyi mashi hidima, he washes he bathroom, cleans his bed rooms da falo, suna shiga ciki naga falon so neat and tidy, komai da ake bukata a falon yan gayu yana dashi, saurayin na biye dashi har cikin falon, direct daya daga cikin bedroom dinshi ya shiga Don ya kuskura baki before going to masjid, shima mahboob dayan bedroom din ya shiga Shima ya kuskura baki, kusan tare suka fito da yarima, Umar kallon yarima yayi cikin respect yace
"ranka shi dade nan zaa kawo maka abinci?.. " bai k'arasa ba yarima yace
"munci... Kana iya tafiya for today... " ya fad'a mashi, a kaidar maaikatan gidan babu Wanda zai tafi gida amma yarima do permits Umar yaje gida kullum sai ya dawo the following day,
"baka bukatar komai?.. " Umar ya sake tambayan yarima because yasan gobe bai zuwa bisa umarnin yarima, ya bashi Sunday ya huta sannan yayi nashi hidimomin, he's the only person that have this heart cikin yanuwanshi, sauran maaikatan always wish sunawa yarima Aliyu aiki saboda bai da matsawa kaman sauran yan gidan, sannan in har ya saka sutura kusan sau hudu kou biyar Umar ya ke kwasarwa kayan, in ka hadu da Umar cikin gari when he's off zaka sha mamaki saboda shiga yake ta kece raini as a results of kwancen kayan da yarima ke bashi, sannan duk wani Mai aiki a fada yana da albashin shi wanda ake basu duk karshen wata, yarima yana bawa umar dubu daya kullum na transport, hakan yasa Umar bai hada yarima da kowa ba, at times in ya zauna da sauran masu aikin gidan ana hira sai yace
"duk abinda zai samu yarima na sharri rabbi ya kauda shi..." he always pray for he's well-being. Duk maaikatan gidan babu Mai fadin bad habits dinshi, kawai the only thing they know is baya magana kaman sauran yanuwanshi.
"eh kana... iya tafiya... " ya fad'a yana saka hannu cikin aljihunshi, dari biyar ya dauko guda biyu fari tas ya mika mashi, durkusawa saurayin yayi ya amsa yana mashi godiya da adua kaman yanda yake mashi kullum. Tare suka fita su suka wuce masjid shi kuma Umar ya tafi gida.
Tasleem na kwance kan Doguwar kujera kanta kan kafar mom dinta ita kuma mum dinta ta dora hannunta kan gashin kanta sai shafawa take,
"Kinyi sallah kou... " mahaifiyar ta ta tambayeta,
"mummy zanyi... Bari kunun nan ya sauka kar inyi amai... " tafad'a cikin shagwaba,
"kusan minti talatin bai isa ya sauka ba?.. Na lura this days sallah magrub da ishai kike hadawa... " inji mom dinta
"no mummy... Bai sauka ba... Taso min yake... Mummy a daina saka min madara da yawa.... Kaman inyi amai nakeji... " ta fad'a cikin shagwaba, hajiya zainab zata bude baki tayi magana sai wayar tasleem ya fara ringing, kaman bata so ta dauki wayar ta ga Mai kira, daga nan inda take kwance tayi picking calls din
"baby... " naji voice din namiji ya fad'a mata cikin wayar, Dan baki ta tabe tace
"good evening... "
"baby ya kike.. Ya gida... Na dawo kasar... Nace yau j must see you... " aka Fad'a mata
"OK... Welcome.... " ta fad'a ahankali,
"yanzu gani nan cikin compound dinku... " ya fad'a mata, bata kara cewa komai ba ta katse wayar tana daga kanta,
"mummy nayi bako... " ta fad'a tana mikewa,
"tou... Kar ki dade... Kinsan dad dinki baiso wannan hiran daren...dukda bai gari kar ya samu labari kinji kou?.. " ta fad'a mata cikin extra calm voice,
"OK mummy... " tafad'a tana Kama hanyar wurinta,tana shiga ciki ta sake kaya zuwa doguwar ruga sannan ta saka long hijab ta fito, imagine wacce tace bazata iya sallah saboda kar kunun gyada ya dawo mata ba gata walking quickly to meet a visitor. Sai kamshi take ta fita compound dinsu da babu mutane sai masu gadi da securities dake zaune a duty post dinsu,motar dake daukan ido gefe guda ta nufa walking majestically, Wanda ke cikin motar na ganinta shima yayi saurin fitowa wearing a smile, saurayin fari ne tas, yana Da kyau sosai kaman mace, sallama tayi mashi ya amsa looking straight into her large eyes,
" ahmed sannu da dawowa... Saukan yaushe?.. " ta fad'a da sauri sounding like a real talkative, murmushi ya saki Wanda ya bayyana how handsome he is yace
"I told you yau na dawo...nace dole sai na ganki zan samu sukuni.... "
"welcome.. Muje ka zauna..." ta fad'a mashi
"aa.... Daga nan ma yaisa.. Except in ke kina bukatar zama... But am OK... " ya fad'a mata, ahmed is one of her numerous friends who so Much love and adores her, tasleem Nada shiga rai because bata da damuwar komai, she don't frown kou feel sad, da wuya ta shiga damuwa dukda she easily get scared of things.
"bari insa a kawo maka abun sha... " ta fad'a mashi,
"Dan Allah baby kar ki damu kanki...ganinki kawai nazo yi... Sati biyun nan kaman wata biyu haka nake ji... Ya karatu both boko and arabi?.. "
"lafiya lau... Ana tafama... " ta amsa mashi, nan fa hira ya barke tsakanin su, Don rashin wayau irin na tasleem she told about what she saw a wayar yarima, babu abinda yace sai
"Allah ya kyauta... " wannan amsar ya mugun bata mata rai
"Allah shi kyauta kadai zaka ce?.. Lallai ma..."
"ya kikeson ince.... " tsoki taja tana cewa
"kilan ma halinku guda.. Nidai kaga tafiya ta.... " tafad'a cikin fushi tana juyawa, da sauri ya rike hannunta, dadin hira yasa tasleem bata San an bude gate ba, dukda gate din bai kara while opening amma anyi horn kafin Mai gadi ya bude, amma duk bataji ba, alhaji mussadiq that is just coming in from abuja bai hangi komai da ya shigo gidanshi ba sai tasleem da ahmed ke rike da hannunta, hasken motar alhaji ne ya dallesu yayi saurin sakin hannunta, sai lokacin tasleem ta lura that her dad is back, ji tayi gabanta ya mugun faduwa, ba sau daya basau biyu ba he have warned her kan hira da samari a gidanshi, especially da dare, amma gashi abun ya kai ga har Kama mata hannu ake a cikin gidanshi, yana zaune bayan mota sai huci yake yayin da driver ya nufi parking lot dashi, yasan b'ata da laifi kaman mahaifiyar ta, always yana kiran tasleem ya zaunar daita yana advising dinta ta maida hankali kan karatunta tunda she's in 3 level a buk amma b'ata ji, Allah kadai yasan decision that he's going to make this time around, he feel insulted ga yarshi a compound dinshi rike da hannun kato, despite har kallon malami ake mashi saboda yanda he's God fearing sannan yana da tarin gemu irin na malamai. AI tunda tasleem ta hangi motar ubanta ta baje da gudu zuwa Bangaren mahaifiyarta, if you see yanda hankalinta ya tashi kasan bai wasa da ita like her mother use to,
"lafiya?.. " shine tanbayan da hajiya tayi mata, dukawa tayi da hannunta kan chest dinta tana nishi kaman wacce tayi hours tana gudu tace
"mummy... Mummy... Daddy... Ya dawo... " ta fad'a cikin haki sosai,
"you mean your dad is back?.. " hajiya ta tambayeta,
"yes mummy... Kuma yaga ahmed... Ya kamamin hannu... " ta fad'a still bending AMD breathing pretty fast,
"why zai Kama maki hannu... " ta fad'a cikin damuwa sosai,
"mummy... Don na bashi labarin black mamba... Shine ya goyi bayanshi.... Sai nayi fushi zan tafi sai ya kamamin hannu... Ni kuma ban lura dad ya shigo ba...."
"shima in ba iskanci ba sai ya goyi bayan yarima... " was hajiya zainab's statement,
"don't mind him Mummy... Kilan halinsu guda.... Nidai mummy pls kar kisa daddy yayi mani fad'a.... Kinsan banason fad'a pls.... " ta fad'a kaman zatayi kuka,
"shima alhaji kullum. In zai dawo daga tafiya bai informing mutum sai da yayi zuwan bazata... Go inside and pray... " ta fad'a mata, tasleem dake nishi mikewa tayi daga bending da tayi ta Kama hanyar part dinta.
Har ilah yau INA maku tallah wannan ingantaccen maganin mai suna rainsoul, ga wayanda basu sanshi ba it's a qualitative medicine dake maganin different cuta dake damun mu a yanzu, mata masu Neman maganin infection kou wayanda basu releasing lokacin sex try rainsoul zakayi mamaki it is tested and trusted, bazan iya fada maku abubuwan da rain soul keyi ba but it's effective and will relief you of so many illness da Wanda ka sani da Wanda baka sani ba, but its 30k per kwali mai dauke da 30 sachets, if kana da halin saye contact mummy a kan 08063328903. Ina amare it's good u use rain soul da kayan mata, zai yi maki maganin infection sosai, mata da dama suna da infection kina iya ganin ke budurwace baki dashi but most yanzu suna dashi basu ganewa sai sunyi aure, in har mace tayi university tana shiga public toilet sai dai fatan Allah ya kiyaye.
thanks
[3/14, 6:25 AM] +234 703 008 7807: 4๐๐๐งกโค๐
Sak'aci
๐๐๐งกโค๐๐
ยฎZuwairat (ummumaryam)
4โฃ
Free page
Alhaji na fita daga cikin mota yayi part dinshi yana tafiya da sauri, da ka gan yanda yake tafiya kasan he's angry, bayan kaman minti biyar yaran gidan suka fitowa har da matanshi zuwa bangarenshi domin yi mashi sannu da zuwa, duk suna falo while he's inside freshening up, cikinsu har da hajiya zainab, duk yaran that are present suna part dinshi as usual kaman yanda sukeyi duk sanda ya dawo daga tafiya, amma yau banda tasleem because tasan tayi tsiya, bayan kaman minti ashirin alhaji ya fito sanye da jallabiya fari tas,duk sai sannu da zuwa ake mashi face dinshi babu walwala yake amsa masu, daga kai yayi yana kallon faces dinsu kou zai gan tasleem amma babu ita, kallon hajiya zainab yayi with an unpredictable look ya dauke kanshi, yaran mikewa sukayi suka barshi da two wives dinshi,
"alhaji me zan hado maka... " small wife dinshi ta tambayeshi, shuru yayi for a moment sannan yace
"kawai kawo min shayi... " ya fad'a mata, mikewa tayi ta bar dakin hajiya zainab na zaune kanta kasa, tasan yau da akwai budurin magana because she will definitely hear from him,
"ya hanya?.. " ta tambayeshi cikin calmness,
"ki kiramin tasleem... " was the only things he told her,
"lafiya dai?.. " ta amsa mashi, wani irin kallo ya watsa mata yacr
"bani da right din ganinta at my own wish sai Kinyi questioning dina?.. " ya fad'a sounding angry,
"sorry ni ba abinda nake nufi bane.... Kawai naga yanzu ka dawo.... "
"you don't have to tell me that... Now get her...." ya fad'a atakaice, bata kara cewa komai ba ta Mike, fita tayi ta dawo part dinta, tasleem ta gama sallah ta dawo falo sai mazurai take, da sauri tace
"mummy did he say anything?.. Dan Allah kar ki bari yayi Mani fad'a... Pls... .."ta fad'a tana komawa kusa da mom dinta
"besty kwantar da hankalinki... Kindai san am With you kou...now tashi muje... " ta fad'a mata, aikam hannu tasleem ta dora bisa kai ta fara kuka tana cewa
"wayyo mummy dukana zaiyi?.. "
"meye na duka?.. Pls muje... "
"mummy I can't face daddy... Dan Allah ki fad'a mashi nayi bacci.... Am Scared.... " ta fad'a jikinta na rawa, yanda hankalin tasleem ya tashi yasa hajiya zainab tace
"tashi muje ki kwanta... Kar ki damu kanki kinji kawar mummy.... " dadi tasleem taji, tayi saurin kama hanyar part dinta ita kuma hajiya na biye daita, bata tsaya koina ba sai bed room dinta, jikinta na rawa ta sake kayan jikinta zuwa na baccida sauri ta hau gado ta kwanta hajiya ta zainab ta dauko story book ta dinga karanta mata in a sweet tune Wanda yasa kou minti Ashirin tasleem batayi ba bacci yayi gaba daita as usual. Sai da ta tabbatar tayi bacci sannan ta Mike ta koma wajen alhaji, daman he knows she won't call her,
"alhaji tayi bacci... Daman she's having headache... " ta fad'a atakaice while kishiya ta na zaune wearing a normal face,
"I know AI.... Don't worry... Everything is coming to an end soon.... " ya fad'a atakaice. Ita dai bata gane abinda yake nufi ba amma she felt seriousness a voice dinshi and it scares her.
Bayan su yarima sun dawo daga masjid yaso ganin mahaifin shi amma sai ya tarda he's very busy da mutane, Bangaren shi ya koma inda ya tarda mahboob na waya da babe dinshi, lokacin kam shi ya samu over 50 miscalls sai kuma messages daga farida and wasu da bai ma San su ba, kashe wayar kawai yayi ya ajiyeta gefe guda yayi relaxing a falo for like thirty minutes sannan ya Mike ya kalli mahboob That is still on the phone yaxe
"good night " bai jira reply dinshi ba ya shige bed room inda yake kwana most of the time. Yana shiga ciki ya sauya kayan jikinshi zuwa ba bacci sannan ya haye gado ya jawo laptop dinshi ya saka wata karatun alqurani, yana sakin ajiyan zuxiya tare da lumshe idanuwa, while he's listening he's thinking, he wonders why yace ya zaba mashi mata, he don't want to end up not happy with he's mother's decision, sai kuma ya tuna his mom always want the best for him, idanuwa ya lumshe yana kokarin cinko who his mom will select for him sai kuma yace
"don't think about it... Let's Just wait... " ya fad'a calmly, kawia he prays he doesn't regrets it, saboda ko ma wacece zaa bashi bazai iya kallon mahaifiyar shi yace baiso ba, he's the last born amma kou kadan baa sangartashi ba, da akwai respect da sanin ya kamata. Kawai he can't wait to be married, he knows his wife will be a lucky girl because he always thought of the kind of romantic life he's going to live when he's finally married, murmushi ne ya bayyana a face dinshi, pillow daya ya dauka ya dora kan ruwan cikinshi ya rungumi pillow kaman mutum, Yana cikin sauraron alquran bacci yayi gaba dashi
Wajen karfe 11 daya na dare Mai martaba shi kadai ya shiga bangaren hajiya amina, sai yanzu na gane inda yarima yayi inheriting bakinshi, his father is very dark in color, dashi yarima ke kama, in ka ga yanda shi kadai yake tafiya sai ka rantse ba sarkin bane because nobody is following him, kou masu bude kofofi duk sun kwanta, sanyi yake cikin shadda Mai shegen tsada Wanda da akwai manyan aiki a jiki, kou button din wuyar rigar bai a balle yake, duk yau bai samu ganin matanshi ba saboda bakin da yayi, da sallama ya shiga chambers dinta. Babu kowa ciki bai tsaya wasting lokaci baya shiga inda yasan zai sameta, kwance take cikin blanket mai taushin gaske, sallama daya tayi ta bude ido tare da amsawa tana mikewa zaune, kaman ba Mai bacci ba ta sauka ta gaidashi cikin girmamawa, amsawa yayi yana cewa
"ya jikin naki?.. "
"da sauki abbah.... " tafad'a kaman wata yar yarinya,
"Allah ya kara sauki.... I have been in different meeting yau... Shiyasa ban waiwayeki ba... "
"I know... kar ka samu damuwa ranka shi dade..." ta amsa mashi ahankali,
"kina shan magungunanki dai kou?... " ya sake tambayan ta cikin kulawa,
"eh sosai MA... Yanzu kafar alhamdulillah.... "
"Masha Allah.... When is your next check up?.... "
"sai nan da wata biyu... lokacin da gama shanye drugs dina... " ta amsa mashi,
"tou madalla.... Kina bukatar wani abu?... " ya tambayeta kaman yanda yake tambayar ta for the pass 40 years plus, kullum sai ya tambayi matanshi if there's anything they need, bai taba fashin wannan tambayan ba, bai yarda wata jakadiya ta fada mashi halin da matanshi ke ciki ba, ba wai Bai da jakadiya ba yana da ita amma bai bada daman a shiga tsakanin shi da matanshi ba as ya gani yanda suke yanda suke gandama a royal houses wajen hada husuma kou kawo matsaloli daban daban. Yasan babu irin makircin da baa iya hadawa da su.
"babu matsala... Amma naso in tattauna wata magana Mai muhimmaci da kai... " ta fad'a mashi, zamanshi ya gyara yana cewa
"OK ina sauraonki ummah... "
"daman it's about Aliyu.... "
"tou what about him... Shima yau bamu samu ganawa dashi ba..."
"dazun ya shigo yake ce min a zaba mashi mata... Wai shi ya gaji da nema... " shuru yayi for a moment as bai taba zaba masu mata ba kou mijin aure ba,