Showing 306001 words to 309000 words out of 350584 words

Chapter 103 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

tafi Company”.
Cikin sanyi yace.
“Toh kana ya miƙe ya tafi.”
Yana mgna ƙasa-ƙasa.

Ƙarfe bakwai da kwata dai-dai ya fito cikin wasu tattausan yaɗi mai masifar kyau, fari ƙal, sai baza ƙamshi yakeyi, kansa babu hula.
A tsakiyar falon ya tsaya tare da zubawa Jannart dake fitowa falon idanu kamar ya shekara bai gantaba.
Cikin tsananin bege da kewa, ya buɗa mata hannu alamun tazo, da sauri ta zaro idanunta tare da jujjuyasu ta nuna masa hanyar kitchen da corridor fitowa side ɗinsu Abba kana ta jujjuya mishi kai alamu a'a.
Cikin sauri ya tako zuwa gabanta, hannunta ya riƙo ya jawota jikinsa, tare da ruggume ta, cikin sassayan murya mai fallasa sirrin zuciya yace.
“Allah ya hanani sake ganin irin Daran jiya, domin yayi min tsoro, na rayu babu daɗi sabida rashin ɗuminki a kusa dani, na gaza bacci, na gaza samun salama Janna jiya kawai naji kamar shekara gudane Bama tare”.
Cikin yar dariya tace.
“Sorry Naanu sakeni to kada Mamy ta fito”.

Mamy kuwa dake tsaye a dinning area, kai ta juya da sauri ta koma cikin kitchen tare fara fasa kwan da zatayi amfani dashi.

Shi kuwa Rayyern hannunsa yasa ya tallabo haɓarta, cikin kulawa yace.
“Kina lfy dai ko? Baki sake yin Amai ɗin bako?”.
Da sauri ta gyaɗa mishi, kai tana ƙoƙarin kauda kanta ganin yana sunkuyo da kansa.
Shima da sauri ya ɗan ja baya kaɗan jin gyaran muryan da Abba yayi.
Shi kuwa Abba hango yadda yake riƙe da itane yasa, yayi gyaran muryan tun kafin ya iso.

Da sauri ta matsa can nesa, tare da rusunawa, ta gaidashi, shi kuwa Rayyern kitchen ya nufa.

Shi ko Abba waje yayi yana cewa.
“Hamzarta ka fito mu tafi kaga yau jumma'a mu samu mu dawo da wuri”.

“Toh Abba gani nan zuwa”.
Yace tare da kallon Mamy.
Kana ya juyo ya ɗan kalli Jannart dake bayansa.
“Barka da safiya Mamy”.

“Barka dai Babana ya gajiyar hanya?”.

“Alhamdulillah, Mamy na tafi”.

“Toh Allah ya bada sa'a ya kiyaye hanya”.

“Amin Ya Allah”. Yace yana mai juyowa ya, sauƙo.
Juyowa yayi ya kalli Mamy ganin baya ta basu, yasashi manna mata kiss a goshi, wanda sautinsa yasa Mamy juyowa, shi kuwa da sauri ya wuce waje tsaye ya samu Abba da Baba Mauɗo gaisawa sukayi kana ya shiga mota ya tafi.

Ita kuwa Jannart a kunyace ta shigo kitchin din tare da cewa.
“Mamy sannu da aiki”.

“Yauwa sannu Jannart”.
Ta ƙare mgnar tana kaɗan kwan data fasa.
Da sauri Jannart tasa hannu ta rufe hancinta tare da juya, baya wurin sink wani irin yunƙurin amai ta fara kamar maƙoshinta zai tsage.

“Ya Salam”. Shine abida Mamy ke faɗi tana ƙara matsota.
Ita kam Jannart yunƙuri kawai take, babu abinda take haraswa, to me taci da zata har.
Da sauri Mamy ta kamo hannunta tare da cewa.
“Sannu ko, muje waje”.
Cikin haɗa zufa suka fito dinning area,
numfashin ta fara sauƙewa tare, da danne yunƙurin dake taso mata, amman ina abin yaci tura, kasan cewar hannu Mamy da ɗan ƙarnin ai yunƙurin takeyi har jikinta na rawa tuni hawaye da zufa suke zubo mata dan yunƙurin yaƙi barinta,
cikin azaba tace.
“Mamy ki wonke hannunki ƙarnin kwai”.

Da sauri Mamy ta saketa ta juya tana wonke hannun tare da cewa.
“Allah sarki, kiyi haƙuri Jannart am na cuceki, kiyi haƙuri”.
Cikin hawala ta fara maida numfashin tare da cewa.
“A'a Mamy ba komai, nima bansan meyasaba naketa amai ni dai ƙarnin kwai baya sani amai fa”.
Kamota tayi tare da cewa.
“Muje falo, ai dama dole ki samu sauye-sauyen abubuwa, sai kuma in kinyi sa'a in ya rika zaki koma dai-dai sannu ko Jannart”.
Ta kare mgnar tana ajiyeta kan 3 str.
Da sauri ta kwanta sabida jirin da yawan kakarin ya jaza mata, lumshe idanunta tayi tare da fara sauƙe numfashi.
Gyara mata kwanciyar Mamy tayi tare da cewa.
“Banda zuwa kitchen na yafe, sam bana son tayin aikin ki bari zanyi komai dama wannan aiki nane”.
Ita dai Jannart shiru tayi sai zufan dake keto mata.

Ganin ta nitsune yasa Mamy komawa taci gaba da aikinta.

Ƙarfe takwas da rabi Ramadan ya sauƙo cikin shirin fita, zama sukayi a dinning table.
Amman duk yadda akayi taci abinci sam ta gaza, haka nan takejin bata son komai sai kunun nan, haka yasa shi kaɗai tasha.
Bayan sun gamane shi ya fita, su kuma suka dawo falo.

Rayyern kuwa A companyn suka samu Usman PA.
Dadi sosai Abba da Rayyern ɗin suke ciki ganin tarin ci gaba da kuma yadda hada-hadar ma'aikata da kuma yan kasuwan ke tafiya, kai Rayyern ya jinjina ganin yadda aketa cika manyan tirelili da kayyakin masarufi, wanda kasuwanni zai je, da kuma wasu jihohin wasu motocinma har ƙasashen maƙotanmu kamarsu Niger, Kamaru, Chadi. Zasu nausa.

Sune basu bar cikin campanyn ba sai ƙarfe biyu saura kwata, tuni anata huɗuba a masallatai wasuma sunyi salla.

Suna cikin mota ne ya kira Ramadan.
“Ni kam kunyi mgn dasu Riyyam-nsra kuwa?”.

“Eh Hamma Rayyern muyi mgn dasu kafin su taso”.

“Toh Allah ya kawosu lfy, kada kayi nisa zamu je Airport yanzu kana ina?”.

“Ina asibitine”.

Daga nan suka kayi sallama.

Shi kuwa Rayyern a hankali yake nazartan Abba da tun jiya ya kula dashi, time to time yana dafe ƙahon zuciyarsa alamun yana jin wani abune.
Cikin kulawa yace.
“Abba meke damunka ne?”.
Ajiyan zuciya yaja tare da cewa.
“Ba komai kawai dai ina yawan jin tsinkewan zuciya ne, tun shekaran jiya bansan me yasaba”.

Da sauri yace.
“Toh sai munyi salla mu wuce, pharmacy in gwada bp'nka”.
Daga nan dai suka wuce masallaci.

A gida kuwa dai-dai lokacin Barrister Kabeer ya sauƙe Aunty Dijat dasu Hafeez a ƙofar gidansu Rayyern ɗin kana, yace.
“Yauwa to ku, shiga ni zan wuce masallaci, sai an idar zan taho,”.
Ai tuni Hafeez da Hafiza kam sunyi cikin gidan.

“To Allah ya kiyaye hanya”.
Aunty Dijat tace, tare da bin bayan yaran.
Shi kuwa jam motar yayi ya fita, dan ganin Ari na tsaye alamun shima fita zaiyi, yasa suka tafi tare.

Da sauri Jannart ta miƙe tsaye tare da cewa.
“Laaaa Allah sarki Hafeez Hafiza”.
Sai kuma ta buɗe musu hannu tare da nufarsu.
Aifa da gudu suka faɗa jikinta, suna dariya cike da jin dadi suke cewa.
“i miss u so much Aunty Jannart”.

“Miss you to”. Tace tana sakesu da sauri ganin Aunty Dijat da yanzu ta shigo.
Mamy kuwa ido ta zuba musu tana murmushi.

“Allah sarki Aunty na, Ina kewarki, kai yau naji daɗi na Mamy ga Aunty Dijat matar Abba na da yaransa”.
Cikin karramawa Mamy tace.
“Masha Allah, sannunku da zuwa ku iso, marhabin lale da zuwa”.
Ita kam Aunty Dijat sai kallon Jannart take cike da so.
Zama sukayi bisa kujeru gaba ɗaya Hafiza ta kanainayeta, sai tsalle takeyi.

Mamy kuwa dinnin area ta nufa, Fridge ta buɗe tare da ɗebo musu, kayan sannu da zuwa.

A gaban Aunty Dijat ta ajiye, cike da kulawa tace.
“Bissmillah, yau kam Barrister ya cika mana alƙawarin”.
Cikin sakin fuska suka gaisa suna ta yabon sauyawar Jannart.

Kana suka sha ruwa.
Hafeez kuwa baisha komaiba, cikin kulawa Jannart ta miƙa mishi Appul tare da cewa.
“Ga mutuminka".
Kai ya jujjuya tare da cewa.
“Uhum”.

“To me kakeso?”.
Da sauri yace.
“Aunty Jannart kiyi mana a logoi-logoi”.
Dariya mai sauti tayi tare da cewa.
“Kace muyi hana baba tashi”.
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Mamy kuwa cewa tayi.
“Ai kuwa kam bari inyi wata ƙil kema kici,”.
Da sauri tace.
“A'a Mamy zanyi mana kekam ki huta”.

Hannunta Hafiza ta fara ja tana cewa su tafi.

Cikin Faɗa Aunty Dijat tace.
“Ka da Allah ki nitsu ku barmu, mu gaisa shegen iyayi”.
Kwaɓe fuska Hafiza tayi alamun zatasa kuka, haka yasa Jannart kamo hannunta da sauri tare da cewa.
“Ayyah my Aunty ki barmu, zo mu tafi”.

Daga nan suka wuce kitchen din.

Sauri-sauri ta haɗa komai na a hana baba tashin.

Ta sannan ta fara, tuya.
A ɗigon forko da ƙamshin ya bugeta, tayi saurin juyawa, tare da toshe hancinta.
Tuni yunƙuri ya taso.

Jin yadda ƙamshin ke ƙara rufetane, yasa tayi maza ta fito.
Da sauri Mamy ta miƙe tana cewa.
“Subahallahi Jannart aman kuma?”.
Ina ba mgn sai amai take zugawa, a duk kunun da tasha take keleyar dashi.
Tanayi harda shaƙuwa.

A tare Aunty Dijat da Mamy suka iso.

Hafeez kuwa da sauri ya kashe gas ɗin.
Kana suka fito, sannu suketa jera mata.
Amman babu bakin amsawa,
Tallabeta Aunty Dijat tayi cike da kulawa tasa mata ruwa ta wanke bakin ta da fuskarta.
Sai rawa jikinta keyi kamar mazari.
Falo suka dawo, Mamy kuwa gyara wajen tayi.

Sannan tazo ta zauna gefenta, tana mai kiran Ramadan a waya, yana ɗagawa tace.
“Kana ina?”.

“Asibiti”.

“Maza yanzu kazo wallahi aman nan fa yaƙi tsayuwa yau sau biyu tanayi”.
Da sauri yace.
“Toh Mamy bari in duba abinda ya dace in zo mata dashi.”

Su kuwa Aunty Dijat ne faɗa ta kama yiwa yaranta.

Jim kaɗan kuwa sai ga Ramadan ya shigo.
Da leda a hannunsa.
Gabanta ya ɗan tsuguna, cikin kulawa tace.
“Sannu my Aunty”.
Ya kare mgnar yana zaro ɗan ƙaramin ledan ruwan da yazo dashi, Alkurai ya ɗan haɗa kana, yace.
“Bari in sa miki ruwan nan zakiji ƙarfin jiki da kuma sauƙin aman zaki samu kuma kici abinci”.

Kai kawai ta jinjina mishi, sabida harga Allah tana son taji sauƙi dan zuwa yanzu, gaba ɗaya duniyar ba daɗi take jinta.
Hannunta ya kamo ya ɗan ɗaura mata robar nan, kana ya samu jijiya ya cusa allurar.
“Wachh”. Tace da ɗan ƙarfi.
“Sannu”. Sukace mata baki ɗayansu.

Haɗa mata ruwan yayi tare dasa alkuran.
Gyara mata kwanciyarta Aunty Dijat tayi.

A waje kuwa dai-dai lokacin Abba suka shigo cikin gidan, yayinda motar Barrister Kabeer ke biye dasu a baya.

Abba waya yakeyi da Baban Raihana.
Haka yasa suna fita, shi ya jingina da jikin motar shi kuwa.
Rayyern motar Barrister ya zubawa ido har yayi parking ya fito.

Gaisawa sukayi cikin mutuntaka.
Shima Abba ya gama wayar hakan yasa suka gaisa.
Baba Mauɗo daya nufosu ne Abba ya kalla kana ya juyo ga Barrister Kabeer dake cewa Rayyern.
“Eh gida lfy lau, duk gidan nawa ma ai suna ciki, ɗazu na sauƙesu kafin in wuce masallaci”.
Ɗan guntun murmushi yayi tare da cewa.
“Ah lallai kam mun gode kuwa”.
Juyowa sukayi suka kalli Abba da yace.
“Baba Mauɗo zamuje gidan Surkan Ramadan ne, sunce suna son ganinmu”.
“Toh Allah yasa lfy dai ko?”.
Cewar Baba Mauɗo.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Allahu alamu.
Barrister muje harda kai”.
Da sauri Barrister Kabeer yace.
“Ayi haka kuwa?”.
“Ah ba komai muje”.
Baba Mauɗo yace.
Haka yasa suka shiga motar shi Barrister Kabeer ɗin kana yaja suka tafi.

Shi kuwa Rayyern ciki yayi.

“Dai-dai lokacin kuma Ramadan ya gama haɗa mata komai ya koma gefe, yaja Hafiz da Hafiza.

Da sauri Rayyern ɗin ya ƙaraso tsakiyar falon, cike da alamun tambaya yake kallon Jannart dake kwance da ƙarin ruwa.
Gefenta ya iso, yana mai cewa.
“A'a Janna amanne Kuma?”.
A hankali ta buɗe idanunta tare da gyaɗa mishi kai.
Aunty Dijat kuwa, ɗan matsawa gefe tayi ganin yadda yake matsowa.
Hakan kuwa yayi masa daɗi, hannunsa ya kife kan goshinta kana ya gangaro dashi zuwa.
Kan wuyanta, cikin tsananin kulawa, tausayawa, yace.
“Baby kuma babu zazzaɓi fa”.
Still kai ta gyaɗa masa.
Mamy ce ta ɗan harareshi tare da cewa.
“Toh ai dai ka gaida surkar taka ko?”.
Cike da kunya ya ɗan sosai ƙeyarsa kana ya kalli Aunty Dijat sannan yace.
“Barka da yamma Aunty Dijat”.
Cikin jin daɗin kulawar da yake bawa Jannart tace.
“Barka dai Rayyern kun dawo lfy”.

Alhamdulillah yace yana zama bisa hannun kujerar da Jannart ɗin ke kwance.

Ramadan kuwa, whatsApp nashi yake dudduba akai-akai, dan ko zaiga saƙon Riyyam-nsra aikuwa yana dubawa yaga ya turo masa saƙonni har shida.

Aunty Dijat kuwa cikin sanyi tace.
“Toh amman dama haka take fama da amai hakane?”.
Da sauri Mamy ta jujjuya kai tare da cewa.
“A'a Wlh sukace batayi a can sai dai tunda suka dawo, in dai tururin wani abun mai ɗan mai da al'basa ya bugeta sai tayi ta amai, kin san sha'anin mai ƙaramin juna sai a hankali”.
Da sauri cike da tsananin mamakin Rayyern ya kalli Mamy jin wai mai juna.
Ita kuwa Jannart ƙara rufe idanunta kawai tayi.

Ita kuwa Aunty Dijat cikin jin daɗi tace.
“Allah sarki gsky ko zata rainin cikin da wahala, duk laulayi babu mai daɗi amman cikin dake sa amai yafi jikkatarwa”.
Shima kam Rayyern kamar gaula haka yake binsu da ido.
“To wai su a zatonsu cikene da ita Dako hakane da naji dadin duniya. Toh inama ta yarda na kusanceta bare in bata ciki yarinya da sai kwalele ta iya min ta barni in shiga muhallinka taƙi saidai ta dakatardani a bakin ƙofa”.
Sai kuma ya ɗago kansa da sauri jin Ramadan na cewa.
“Masha Allah, Alhamdulillah Hamma Rayyern su Riyyam-nsra sun iso yanzun nan yace jirginsu ya sauƙo”.
Cikin farin ciki yace.
“Masha Allah”.
Sai kuma ya kalli Mamy da tace.
“Toh maza kuje ku ɗaukosu”.
Da sauri kuwa Ramadan ya miƙe.
Shima Rayyern miƙewar yayi bayan ya shafa fuskarta.

Waje suka nufa.

Ganin la'asar tayine yasa, suka tsaya sukayi salla.
Kana suka wuce Airport.

Suna shiga cikin jama'a suka rinƙa kutsawa, tare da jujjuyawa.
Suna neman ta inda zasuga su Riyyam-nsra ɗin.
Riyyam-nsra kuwa dake bayan Mammy da zaiton ƙasa yayi da murya tare da cewa.
“Mammy bari mu gani ko jini da nono zaiyi musu jagora su ganeku”.

Rayyern kuwa idanu ya zubawa Mammy da Zaiton dake liƙe da niƙabi a fuskokinsu.
Cikin wani irin sassayan daɗi da yaji ya ziyarceshi ya saki murmushin mai haɗe da dariya cikin tarin jin daɗi yace.
“Mammy!”. Wata iriyar sassayar ajiyar zuciya Mammy ta sake mai ƙarfi tare da yaye niƙabin.
Kawai sai ta ruggume shi, wani irin sanyi mai masifar ɗadine ya rufesa yana maijin wata iriyar fitinenneyar iska mai daɗi na ratsasa.
Ita kuwa Mammy hannu tasa ta jawo Ramadan da ya zuba musu idanu.
Ruggume su tayi tsam-tsam a jikinta kawai sai taji hawaye na kwaranyo mata.

Zaiton ma yaye nata niƙabin tayi, tare da ruggume Mammynta ta baya.
Shi kuwa Riyyam-nsra cikin tsananin jin daɗin ya farayi musu video tare da cewa.
“Ko yau ko yanzu na mutu, na mutu da cikekken farin ciki, Mammy na cika miki burinki, na haɗaki da mafarkinki a zahiri”.
Sai kuma ya ruggume Ramadan da Rayyern ta bayansu.
Wani irin farin cike mai tarin yawa ya rufesu.

Da yawa mutane tsayuwa sukayi suna kallonsu.
Wata matace da tazo wucewa gefensu tace.
“Masha Allah uwa da ƴaƴanta”.
Kai Mammy ta jinjina mata tana mai sharce hawayen ta,
Kana ta sakesu gaba ɗayansu.

Su kuwa cikin tarin farin ciki suka ruggume Riyyam-nsra kana a ladabce Rayyern da baiji mamaki ko rashin dai-dai a ruggume su da Mammy tayiba ya kamo hannun Zaiton tare da cewa.
“Muna farin ciki da ganinku”.
Cikin jin dadi suma sukace haka.
Daga nan kuma Ramadan da Riyyam-nsra suka jidi jakkunan su, suka kai cikin mota, shi kuwa Rayyern bayan motarsa ya buɗe wa Mammy tare da cewa.
“Mammy shiga nan ban yarda da tuƙin Ramadan ba ya cika rawan kai”.
Cike da fara'a ta shiga kana ya maida ƙofar ya rufe.
Kana ya jawo hannun Zaiton kuma yasata a gaban motarsa.
Sannan ya zagaya ya shiga yana cewa.
“Ku kuma iyayen rawan kai ku tafi a hankali dai”.
Dariya Riyyam-nsra yayi tare da cewa.
“Yah Ramadan nine zan jamu”.

Haka kuwa akayi suma nufi gida cikin farin ciki.

Su Abba ma acan gidansu Raihana sukayi sallan ganin lokacin yayi, kana suka kama hanyar gida.
Suna isa, gida Baba Mauɗo yayi side ɗinsu.
Abba da Barrister Kabeer kuwa cikin gida sukayi.

A falon kuwa tuni Mamy ta cirewa Jannart ruwan dan ya ƙare kuma Alhamdulillah kuzarinta ya ɗan dawo dan har da tashi zaune suna hira.

Mamy ce ta ƙarasa musu suyan ta kawo musu sunaci suna hira.
Alhamdulillah kuma itama Jannart ta ɗan samu taci.

Tattare Wurin Mamy tayi.
Dai-dai lokacin kuma su Abba suka shigo.

Nan suka gaisa.
Cike da farin ciki Barrister Kabeer ya kalli Jannart da kyau tare da cewa.
“Eyyyeh masha Allah Mascow ta amshi ɗiyata ga yadda kika zamma balarabiya”.
Cike da kunya tayi murmushi.

Dai-dai lokacin kuma su Ramadan suka shigo farfajiyar gidan.

A can sashin Baba Mauɗo kuwa, fitowarsa da bayan gida kenan da alamun al'wala yayi, qura'an ɗinsa ya ɗauka, kana ya zauna kan sallayarsa ba tare da ya naɗa rawaninsa ba, suratul Khaf ya fara karantawa cikin dadɗan sauti.

Su kuwa su Riyyam-nsra, yana gama parking ya fito da sassarfa waige-waige yake yana cewa.
“Baba Mauɗoooo”.
Ganin babu alamunsa a wurin ne yasashi juyawa da sassarfasa ya
nufi cikin gida yana mai cewa.
“Mamy! Aunty Jannart!! Abba!!!”.
Dariya sosai Hadi da Ari sukeyi, dan su kansu sunyi farin cikin ganinsa.
Rayyern kuwa buɗe wa Mammy motar yayi tare da cewa.
“Mammy bisimilla mu shiga”.
Ramadan kuwa Hadi da Ari ya kalla tare da cewa.
“Yauwa ku shigo da kayyakin nasu”.
To sukace kana suka amshi key ɗin motocin.

Rayyern kuwa jagora yayi musu, yana gaba suna binsa a baya.

A can side din Baba Mauɗo kuwa, cikin ƙarfin hali yake karatun sabida wani irin masifeffen harbawa da zuciyarsa keyi.

Yayinda haka take a wurin Abban Rayyern ma.

Cikin murmushi Abba yake kallon ƙofar falon jiyo yadda Riyyam-nsra ke auna musu kira.
Mamy kuwa da sauri ta fito daga kitchen da taje ɗaukowa Barrister Kabeer ruwa.
Dai-dai lokacin kuma ya shigo.
Sai kuma ya isa gaban Abba yana ɗan sosai ƙeya yace.
“Oyoyo Abba”.
Murmushi Abban yayi tare da cewa.
“Har lau dai baka sauyaba”.
Kai ya jujjuya kana ya juyo ya kalli Mamy cikin sauri ya isa gabanta tare da cewa.
“Allah sarki Mamy na”. Sai kuma ya juyo ya kalli Jannart dake cewa.
“Uhum ina ka baro mana Mammy da Zaiton”.
Da sauri yace.
“Oho My Aunty ai bam ganekiba nayi zaton balarabiyar Saudia ce”.
Dariya sukayi baki ɗaya dai-dai lokacin kuma Rayyern ya turo ƙofar tare da shigowa kana yace.
“Mammy shigo mana.

A hankali tasako ƙafarta ta dama cikin falon.
Haka yayi dai-dai da wani irin harba da zuciyar Abba tayi wanda yasashi sauri ɗago kansa.

Ita kuwa Mammy a nitse ta kutso kanta cikin falon hakan ya bawa Ramadan da Zaiton damar shigowa.
Da sauri Jannart ta miƙe tsaye, ganin yadda Abba yayi wani zabura ya mike tsaye cikin tsananin kaɗuwa da zaro idanu a ɗimauce.

Mamy kuwa ganin yadda suka miƙa baki ɗayasu ne yasa ta ɗan tako zuwa gefen Riyyam-nsra daya ɗan tareta kaɗan.

Idanunta ta sauƙe kan fuskar Mammy da tun a airport data cire niƙabinta bata maidashi ba.
Wani irin zazzaro idanu Mamy tayi tare dajan wani numfashin mai haɗe da tarin al'ajabi, tsoro, kaɗuwa, da girgiza cike da ruɗani tace.
“Heeeehhhhh Addaaaaaa Aichaaaaaaa”.
Kawai sai luuuu ta tafi ƙasa a sun...!






By
*GARKUWAR MARUBUTA😉😂*




Ta tafi ƙasa luuu a sume,
Kusan a tare duk suka mimmiƙe tsaye baki ɗayansu.
Riyyam-nsra ne yayi wani irin juyi cike da hanzarin ya tarota ta faɗa jikinsa.

Ramada da Rayyern kuwa a guji sukayi kansu.

Barrister Kabeer kuwa, Abba ya nufa, ganin yadda ya tsaya ya tamkar an dasashi ya zubawa Mammy idanu tamkara ƙwayar idanunsa zasu faɗo ƙasa, wani irin azabebben karkarwa jikinsa ya kamayi tamkar mazari.
Kana fuskarsa ta cika da tsananin kaɗuwa, mamaki, tsoro, firgici, al'ajabi, da tarin ɗimuwa sam baibi ta kan Mamy da ta saki ƙara ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login