Showing 30001 words to 33000 words out of 350584 words
da nade hannayensa akirjinsa, yana mai bin motar Rayyern da ta shige cikin gida da kallo.
Ramadan dake cikin motarsa kuwa, tun d’azu mutuwar zaune kawai yayi, tare da bud’e ido da baki yana kallon matashin saurayin, da yake ganinsa tamkar hoto copy din Yayansa Rayyern.
Lallai Tabbas wannan kamar da yake gani akan fuskar yaron, da kuma ta Hammansa Rayyern ta b’aci.
Cike da tu’ajjudi ya k’araso da motarsa zuwa bakin gate din gidan, tare dayin k’asa da glass din motar yana me sake Kallon yaron da har yanzu murmushi ke bayyane akan fuskarsa.
Ganin kuma yaron ya dan juya masa baya, ya kuma tare masa hanya ne, yasashi danna horn.
K’aran horn dinne kuwa yasa Riyyam-nsra da kuma Naseer juyowa, suka sauk’e idanunsu akan Ramadan dake kokarin tura hancin motarsa cikin gidan.
Idanunsu gaba d’aya suka zubawa fuskarsa, Yayinda lokaci daya Riyyam-nsra yaji wani irin abu ya daki kirjinsa, saboda Kallon fuskar Ramadan da yayi, ganin kuma kamar idanunsa na d’anyi masa gizo ne, yasashi sanya tafukan hannayensa yadan mutstsuke su.
Saidai kuma yin hakan da yayi ya sake tabbatar masa da cewar, bawai gizo idanunsa keyi masa ba, Lallai Tabbas fuskar wanda ke zaune acikin motar, tana shige da fuskar Mammy ce da kuma ta Zaytoon dinsa.
Wani irin mamaki ne ya lullub’esa, Yayinda Naseer kansa shima daya ga kamannin fuskar Mammyn Riyyam dana Zaytoon, akan ta Ramadan dake zaune acikin motar yace.
“Allahu Akhbar Allah Mai girma Riyyam kalli wani maikama da Zayton da Mammy’n ka, gacan kuma wani mai kama da kai, kodai y’an uwanku ne sud’in?”
Naseer ya kare maganar yana mai kallon, Riyyam wanda tuntuni ya nufi cikin gidan.
Ganin hakanne kuma yasa cikin sauri Naseer din rufa masa baya.
Riyyam-nsra kuwa yana k’arasa shigowa cikin gidan, Dr.Rayyern Mai-Nasara na fitowa daga cikin motarsa,
Haka ma Ramadan.
Cikin dan hanzari Riyyam din ya karasa, batare kuma da tunanin komai ba, ya ware duka hannayensa tare da fad’awa jikin Rayyern d’in, ya d’an rungumesa da k’arfi.
“Naji dadin ganinka sosai Hamma Rayyern, nanne gidanku?, waye wannan Hamma Rayyern?”
Riyyam-nsra yayiwa Dr. Rayyern duka tambayoyin, tare kuma da d’aga hannu ya nuna Ramadan dake tsaye, shima bakinsa d’auke da tarin tambayoyi.
Tsumammun idanunsa ya lumshe ahankali, tare kuma da sauk’e wata irin ajiyar zuciya, Tabbas kafun iyanzu yanajin zuciyarsa na matuk’ar tafasa, saidai kuma gashi yanzu lokaci daya yaji zuciyar tasa nayin sanyi.
Hannayensa yasanya ya d’an janye Riyyam daga jikinsa, kana ahankali yace.
“Eh. kanina ne, Ramadan.”
Murmushin matuk’ar mamaki da kuma Jin dadi Riyyam yayi, cikin halinsa na faram-faram da sakewa, ya rungume Ramadan din, kana da d’abi’arsa ta wayewa yace.
“Sunana Riyyam-nsra kuma naji dadin had’uwa dakai Hamma Ramadan.”
Murmushi mai dauke da wani irin Jin dadi, tare da zallan k’aunar yaron da yaji yana shigarsa alokaci guda Ramadan yayi, cikin kuma nuna zallan farincikinsa yace.
“Me too, amma wai a ina kasan Hamma Rayyern dina, da har kuke matuk’ar kama haka?”
Murmushi Riyyam-nsra yayi, kana cike da tsananin mamakin sautin muryar Ramadan irin tasa yace.
“Acikin jirgi muka hadu dashi jiya, nima nayi mamakin kamannin da mukeyi dashi sosai, amma kuma Allah babu yanda baya ikonsa, saboda haka ne ma ya zama Hamma na!!”.
Riyyam ya kare maganar yana me bin Dr.Rayyern da kallo, wanda tuni ya soma tafiya harya kusa isa kofar da zata sada shi da babban falon gidan.
Ramadan kuwa idanunsa yadan lumshe tare da sake rungume kyakkyawan matashin yaron ajikinsa, wanda ak’alla shekarunsa baza su wuce 21 to 22 years ba, Lallai yaji matsanancin son yaron ajikinsa, har yakai ga yanajin inama da ace yaron zai zamanto k’ani agaresa, kamar yanda shiya kasance kani ga Hamma Rayyern, Tabbas yaji gamsuwa da yaron acikin zuciyarsa, Yayinda kuma kamannin Hamma Rayyern din dake kan fuskar yaron, yasanya shi jinsa awani waje na musamman a zuciyarsa.
Hannun yaron ya kamo kana cikin kulawa yace.
“Masha Allah Riyyam-nsra mu shiga daga ciki, domin kuwa na kwad’aitu dason nunawa Abba da Mamy mu mai kama da Rayyern dinsu.”
Murmushi sukayi su dukansu, kana Riyyam ya sake rik’e hannun Ramadan k’am acikin nasa, Yayinda acikin zuciyarsa yakejin wani irin nishad’i, ji yake tamkar ba yaune farkon fara haduwarsu ba, yanajin kamar tuntun tuntuni ya sansu, acikin wani bari na jikinsa.
D’an juyowa Riyyam din yayi ya kalli
Naseer Ahmad dake tsaye, yana Kallon ikon Allah, tare da tu’ajjudin abunda ke faruwa.
Alama yayi masa akan ya biyosu, hakan kuwa akayi cikin dan sassarfa Naseer ya rufa musu baya.
Dr. Rayyern Mai-Nasara kuwa koda ya karasa cikin falon, direct part d’insa dake sama ya nufa, saboda ayanda yakejin kansa nadan sarawa, ba kuma yason wani abu da zaizo ya dameshi.
“Abba! Mamy! Abbana!! ku fito kuga wani abun ban mamaki!!!”
Cewar Ramadan dake shigowa cikin falon, hannunsa rike dana Riyyam-nsra.
Wanda kuma yanayin maganan nasa ne, cikin dan bayyana sautin muryarsa, ta yanda duk nisan dasu Abban suke zasu iya jiyosa, kasancewar kuma suna daya daga cikin bedroom din kasa, dake cikin falonne yasa, cikin sauri suka mik’e tsaye, tare da soma rige rigen fitowa asalin babban falon, saboda kiran da sukaji Ramadan d’in nayi musu, yadan tsinkar musu da zuciya.
Ai kuwa isowar su Ramadan din tsakiyar falon, yayi dai dai da fitowar su Abban.
Fitowar daya haifar musu da wani irin bugun zuciya, tare da matsanancin firgici hadi da zallan mamaki.
A matuk’ar mamakance had’i da tu’ajjudi, Mamy ta dafe kirjinta tare da sake, ware Idanunta akan matashin yaron da hannunsa ke sark’afe dana Ramadan, wanda idan ba k’arya Idanun nata keyi mata ba, Lallai Tabbas kamannin d’anta Rayyern ne, kwance akan fuskar yaron.
Cikin karfin halin daya kasa danne mamaki da tu’ajjudi’nta tace.
“Ramadan waye wannan? A ina kasa moshi? Kamar fuskar Rayyern nake gani akan tashi fuskar, ko kuwa dai idanuna ne keyimin gizon hakan?”
Murmushi Ramadan yayi, tare da sanya dayan hannunsa ya jawo Riyyam-nsra jikinsa, cikin kulawa kuma yace.
“Sam ko kad’an Mamy ba idanunki bane ke yi miki gizo, sunansa Riyyam-nsra, kuma tabbas yana matuk’ar kama da Hamma Rayyern dinmu, sannan Hamma Rayyern dinne ma ya samo shi, domin sun had’u ne a Ethiopia cikin jirgin da zai kawosu Nigeria.”
Shiru Mamy tayi tare da kafe yaron da ido.
Kamar dai yanda Abba ya kafesa da ido, baya ko k’yaftawa, domin tun Kallon farko da yayiwa yaron ya kasa dauke idanunsa daga kansa.
Wani irin bugawa yakejin zuciyarsa nayi, Yayinda wani abu ke tasowa tun daga cikin kasan kafarsa har zuwa tsakiyar kansa, Lallai Tabbas akwai kama aduniya, amma irin kaman Rayyern daya hango akan fuskar yaron tayi yawa.
Ramadan dake tsaye kuwa ganin irin yanda fuskokin iyayen nasu, ke cike da zallan mamaki ne yasa shi, sakin murmushi tare da jawo hannun Riyyam-nsra suka k’araso kusa da iyayen nasu.
Hannun Mamy Ramadan ya kamo, tare da d’an fad’ad’a murmushinsa, cikin kuma son basu cikakkiyar gamsuwa yace.
“Dan Allah Mamy ki kalli Riyyam da kyau, matuk’ar kama sukeyi da Hamma Rayyern dinki.”
Juyowa ya kumayi ahankali ya kalli Riyyam, wanda fuskarsa ke dauke da yalwatacciyar murmushi.
Shid’inma Murmushin yayi kana yace.
“Riyyam wannan itace Mamyn mu, Uwa d’aya tamkar da dubu, wannan kuma shine Abban mu, mahaifin daya kasance Garkuwa kuma jigo ga y’ayansa.”
Yak’are maganar yana meyiwa Riyyam nuni, da iyayen nasu shida Dr. Rayyern.
Yalwatacciyar fara’a ne ta bayyana akan fuskar Riyyam, Cikin matuk’ar ladabi da biyayya kuma yad’an durk’usa akan guiwowinsa, tare da bud’e bakinsa anutse yace.
“Abba da Mamy barkanku da gida, fatan zaku karb’eni kamar yanda su Hamma Rayyern da Ramadan suka amsheni, saboda daga yau Mamy kinzama mahaifiya agareni, haka ma Abba daga yau ka maye min gurbin Mahaifi.”
Kusan daina bugawa zuciyar Abba tayi, alokacin da yaji saukar muryar yaron acikin kunnensa, saboda tsananin yanda yaji muryar yaron tayi masa kama da ta Ramadan.
Yayinda daga gefe guda kuwa kwakwalwarsa ke neman juyewa, saboda wani irin tsohon tunani mai karfi dake neman dawowa cikin lissafinsa, da sauri sauri zuciyar Abban ke bugawa, musamman ayanzu daya sauke idanunsa akan yatsun kafan yaron.
Mamy kuwa da ayanzu taji zuciyarta nayin sanyi, hannayenta tasa ta d’an d’ago yaron, tare da sakar masa murmushi kana cikin tsananin kulawa tace.
“Insha Allah Riyyam mun karb’eka hannu bibbiyu kamar yanda su Hammanka suka karb’e ka.”
Murmushin tsananin jin dadi Riyyam yayi, sai alokacin ne kuma ya dago kai ya sake Kallon Abban su Ramadan d’in, da har yanzu ya kasa dauke idanunsa akansa.
Abban kuwa ganin Riyyam din na Kallon sa ne, yasashi dan sakin murmushi.
Ramadan kuwa hannun Riyyam din ya kama suka dawo cikin falon suka zauna, direct gaban fridgen dake cikin falon ya nufa, inda ya d’auko wa su Riyyam din bottle water da kuma fresh milk mai sanyi, ya basu suka sha shida Naseer da ya zama ɗan kallo.
Mamy kuwa da kanta ta k’arasa dining table, inda ta had’a musu lunch, saboda tuntuni rana tariga tayi.
Ramadan kuwa cike da soyayya yaja su Riyyam da kuma Naseer suka karasa kan dining table d’in.
Bayan kuma sun zazzauna ne Mamy tayi serving dinsu, inda ta zuba musu lafiyayyar jalop rice din da tayi, wanda yasha kayan vegetables, da pepper chicken.
Turawa kowannensu abincin tayi gabansa, tare dajan kujera itama ta zauna, anan kusa da Abba wanda shima yanzun ya karaso ya zauna.
“Rayyern fa ko bai dawo ba?”
Mamy ta tambayi Ramadan dake shirin kai loman abinci baki.
“Ya dawo amma ya haura sama, na daiga mood d’insa, kamar he’s tried, i think kuma stress din aiki ne.”
Ramadan ya fad’a yana mai hadiye abincin dake bakinsa.
Kai Mamy ta jinjina cikin gamsuwa kana kuma ta d’ago kanta ahankali ta kalli Riyyam-nsra, fuskarta dauke da murmushi tace.
“Masha Allah Riyyam kaiko daga wacce k’asa kake?”
Riyyam dake cin abinci gyara zamansa yayi, tare da fuskantar Mamy’n, kana aladabce cikin bagwariyar sausarsa yace.
“Ni d’an k’asar Ethiopia ne, acan mahaina da kuma y’ar uwata suke, acan aka haifeni kuma acan na taso nayi rayuwa, nazo nan Nigeria ne kuma saboda, abokina Naseer.”
Ya k’are maganar tasa yana me nuna Naseer dake shan Chapman din da Mamyn ta had’a.
Mamy kuwa still murmushi tayi tare da soma cin abincinta.
A Dai-dai lokacin ne kuwa Rayyern ya soma sauk’owa daga kan steps din falon, wanda ya sake shirya kansa cikin wasu had’add’un riga da wando, na normal jeans.
Sai-dai ganin da yayiwa su Abba da kuma Riyyam-nsra akan dining table ne, ya sashi tsayawa tare da zuba musu ido.
Abba kuwa da har yanzu baidainajin bugawar zuciya ba, d’ago kansa yayi ya kalli Naseer tare da cewa.
“Kai kuma a ina kake, su waye kuma iyayenka?”
Jin tambayar da Abban yayi ne yasa Naseer gyara zama, cikin dan girmamawa yace.
“Sunan Babana Alhaji Ahmad Dasuki, mu asalin yan Nigeria ne, kuma muna zaune anan cikin garin kano unguwar Rijiyar zaki.”
D’an Jim Abba yayi alamun dogon nazari, kana anutse yace.
“Sunan mahaifinka Alhaji Ahmad Dasuki, amma gaskiya bangane shiba.”
Murmushi Naseer yayi, tare da cewa.
“Eh gaskiya bai shahara sosai ba, saboda ba a b’angaren kasuwanci yake ba, saidai Mamana yar gidan Malam MAI-NASARA ce, ni jikansa ne.”
Lokaci guda walwalan dake kwance akan fuskar Abba ta kau, take duk wani annuri da murmushinsa suka gushe, badon komai ba kuwa saidan jin an ambata masa sunan Malam MAI-NASARA.
Ganin hakanne kuma yasa Ramadan, d’auke kansa daga Kallon Abban nasu da yake, inda ya sauk’e idanunsa akan Rayyern dake tsaye akan steps, wanda shi d’inma kuma Abban nasu yake kallo.
Sam gaba d’ayansu basu San dalilin daya sa, Abban nasu baison gani ko jin wani abunda ya shafi Malam MAI-NASARA’n, basusan wannan sirrinba, haka kuma basusan dalilin ba.
Kai Ramadan ya d’an sunkuyar ahankali cikin kuma rauni, dayin k’asa da murya yace.
“Abba yanzu ma abunda ya dawo dani gida kenan, dazu aka Kai mana Malam Mai-nasara hospital dinmu bashi da lafiya, hypertension and diabetes na damunsa, so akwai buk’atar Lallai lallai Hamma Rayyern ya duba sa, so Ya Sulaiman ya kikkira wayan Hamma Rayyern d’in amma kwata-kwata baya shiga, shiyasa na dawo gida saboda inasaka ran cewa zan iya samunshi, Dan gaskiya jikin Malam din ya tashi sosai!”
Fuska Abba ya sake had’ewa tamau, cikin kuma nuna halin ko inkula yace.
“Babu inda Rayyern zaije, ai bashi kad’ai bane Babban Dr. acikin garin Kano, akwai Doctors da dama, akaishi wani asibitin mana.”
Shiru gaba d’aya falon ya dauka, Yayinda Ramadan ya sunkuyar da kansa k’asa.
Shikuwa Rayyern dake tsaye idanunsa ya d’an rumtse, acikin zuciyarsa yana mai tambayar kansa, dalili da kuma hujjar da tasa Abban nasu bayason alak’arsu da Malam Mai-nasara, Tabbas da ace baisan waye mahaifin nashi ba, zuciyarsa zata iya sak’a masa abubuwa da yawa, saidai kuma amma yasan cewa mahaifinnasa mutumin kirki ne, babu yanda za’ayi wani mummunan tunani yayi tasiri acikin zuk’atansu sun san wayeshi mutun ne managarci daya ginasu kan kekkwan tubali nagarta.
Idanunsa da suke alumshe yadan bude, tare kuma da karasa saukowa akan steps din, kaitsaye ya nufo dining table din, duk da kuwa cewar har zuwa yanzu yanajin kansa nadanyi masa ciwo.
Isowarsa dining table dinne kuma yasa duk suka dago kansu suka kalleshi, Yayinda Abban cikin matsanancin kulawa yace.
“Masha Allah Rayyern ka dawo, ya meeting din naku?”
Kujerar dake gefen ta Abban nasu yaja ya zauna, kana aladabce yace.
“Eh Abba na dawo, meeting kuma Alhamdulillah komai ya tafi yanda ya kamata.”
Kai Abban ya jinjina cike da gamsuwa tare da fadin.
“Alhamdulillah haka akeso ai akoda yaushe.”
Gyara zamansa yayi, kana ahankali cikin kuma yin kasa da murya, hadi da sigar roko yace.
“Abba dan Allah kayimini al'farmar samun daman duba Malam Mai-nasara, tunda Ramadan yace yana da buk’atar taimakona sosai, please Abba dan Allah me zai hana bazaka bari naje na dubashi ba!!”
Ya k’are maganar tasa cikin k’ank’an da kai.
Yayinda Abba kuwa ya dauke nasa kan, tare da sake hade fuskarsa.
Ganin hakanne kuwa yasa Naseer zaro wayarsa, ya dannawa lamban Umminsa kira, cikin sa’a kuwa bugu biyu ta d’auki wayar.
Saidai kuma irin yanda Naseer din yaji sauti da Amon muryarta ne, yasa hankalinsa tashi.
Cikin fargaba yace.
“Ummi ya naji muryarki haka? meyake faruwa kodai jikin Malam ne ya tashi?”
Daga can b’angaren kuwa cikin sheshshek’an kuka Ummin tace.
“Eh Naseer jikin Malam ya tashi sosai, yanzu haka ankaishi Mai-nasara hospital, amma Dr da ya kamata ya dubashi bayanan, gashi kuma yanajin jiki sosai, domin sauran Doctors din da suka dubashi, sun tabbatar mana da cewar jininsa ne ya sauk’a, ga kuma diabetes.”
Idanun Naseer ne sukayi raurau lokaci daya kuma suka ciko da hawaye, ahankali yadan share k’wallan da suka zubo masa, kana yace.
“Kiyi hakuri Ummi Insha Allah Malam Mai-nasara zai samu lafiya, ki daina kuka muma zamu zo nan asibitin nida abokina Riyyam nsra.”
Daga haka kuwa bai sake cewa komai ba ya kashe wayar tasa, ya maida ita cikin aljihu.
Sai kuma ya dago kansa ya kalli Abba wanda har yanzu kansa ke gefe.
Dan jan kujerar da yake kai baya yayi, tare da mikewa tsaye ya iso har gaban Abban ya durk’usa, cikin muryarsa irin ta masu neman al'farma yace.
“Dan Allah Abba kayi hakuri kabar Hamma Rayyern yaje ya duba Malam, yanzu haka Mamana kuka takeyi, kuma tace jikin Malam din ya tsananta sosai, dan Allah Abba kayi mana al'farma, Malam shine duk wani hasken cikin familyn mu, rasashi dai-dai yake da yankewar farincikin mu.”
Still Kai Abba ya sake kawarwa gefe batare daya ce komai ba.
Ganin hakannen kuma yasa gabaki d’ayansu sukaji zuciyoyinsu sun raunata, babu ma kaman Rayyern da hakanan yakejin duk wani al’amuran daya shafi tsohon acikin jinin jikinsa.
Riyyam-nsra kuwa ganin yanda Abban ya kawar da kansa gefe ne, yasashi saukowa daga kan tasa kujerar shima ya durkusa agaban Abba’n.
Cikin sanyin da muryarsa tayi yace.
“Dan Allah Abba kayi hakuri, kabari Hamma Rayyern din yaje ya dubasa.”
Idanu Abba da ransa ke ab’ace ya rumtse, kamar kuma zaice wani abu saiya fasa hade da mikewa tsaye, kana yasa kai ya wuce bedroom d’insa kai tsaye...!
Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗
Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali
Ina masu pimples
Tabo(spot)
Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance
Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba
Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki
Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu
Sannan munada beauty kit wnd yk mayarda fata tadawo tamkar madubi wnd yajaraba shine zai tabbatar
Set din yakunshi Abu 6
Soap,body cream,face cream,scrub, cleanser, glow oil
Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself
100%tested nd trusted
Beauty kit:11k
Soap price:3k
Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free
Maiso kindly message 08062991549
Call 08064532391
Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏
Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝
Mg's skincare
By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*TUBALI*
PAGE 9