Showing 117001 words to 120000 words out of 350584 words
cikin motar ne kuma, Ramadan, Riyyam da kuma Hadi suka shiga jidon kayan da suka sayo din, suna shigarwa zuwa babban falon k’asa.
Bayan sun gama shigo da kayanne kuma, Hadi ya koma waje.
A tsakiyar falon suka ajiye kayyakin tare da kimtsasu wuri daya kayan masu yawane, domin duk wani abu na amfanin Mace babu wanda basu sayo ba hatta audugar mata Mamy ta saya mata, ga kuma wasu had’add’un akwatuna set masu kyau da suka sayo.
Mamy kuwa wanda shigowarta cikin falon kenan, jakan dake hannunta ta ajiye, tare da wuce wa kaitsaye ta nufi bedroom dinta, saboda Ganin da tayi lokacin sallan azahar na kokarin gotawa.
Ramadan da Riyyam kuwa, anan cikin bathroom din dake cikin falon, suka d’auro alwala, tare da jerawa atare suka wuce masallacin, dake jikin gidan nasu.
Bayan sun idar da sallan azahar dinne kuma, suka sake dawowa cikin gidan, gaba ɗaya a sokane suke tafiya, wanda da dukkan alama kuma yunwa sukeji da tarin gajiya, saboda zagayen da suka sha a cikin Shoprite din, wai danma sun dan saya biscuit, sunci acikin Shoprite din.
Dawowarsu cikin falonne kuma suka samu, Mamy zaune, wanda itama idar da sallanta kenan, ta dawo falon ta zauna.
Akusa da Mamyn suka zauna.
Yayinda Riyyam kuwa ya langwab’ar da kai, tare da karyar da wuyansa gefe, cikin yanayin shagwab’an wanda in yanayi, tsananin kamanninsu da Rayyern ke k’ara bayyana yace.
“Wash Allah Mamy yunwa nakeji, har inaji kaman babu hanji acikina.”
“To Riyyam, yanda naji gidannan gaba daya, ya gauraye da kamshi, ai nasan abinci na musamman Auntynku ta girka mana.”
Mamyn ta fad’i haka tana murmushi, saboda sosai maganan Riyyam din ya bata dariya.
Jannart dake kwance anan cikin falonta kuwa, cikin dan bacci Marar nauyin daya d’auketa ne, ta soma jin tashin hayaniyarsu, bud’e idanunta tayi, tare kuma da tashi ta zauna.
Shiru tayi na y’an wasu mintuna, Jin da gaske maganan su Mamyn ne ke tashi acikin falon, yasa ta d’aukan mayafinta ta rufa, ahankali ta mike tsaye, kana cikin takunta na nutsuwa, ta nufi falon nasu kaitsaye.
Ahankali ta murd’a handle din kofar falon nata ta fito, tozali dasu Mamyn da tayi ne kuma yasa ta sakin dan murmushi, tare da karasowa ta durkusa a gaban Mamyn..
“sannunku da dawowa Mamy.”
Jannart din ta fad’a tana me duk’ar da kanta k’asa.
“Yauwa sannunki dai Jannart, ya fama da kad’aici.”
Mamy ta tambaya cike da nunawa Jannart din kulawa.
Jannart kuwa Murmushi tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah amma da bakwa nan gidan ba daɗi Mamy”. Tayi mgnar cikin fito da gskyr zuciyarta.
Mamy kuwa murmushi tayi tare da cewa.
“Meyasa baki taso Rayyern yazo ya tayaki zamaba”.
Tayi mgnar cikin son nuna kusancinsu.
Ita kuwa Jannart da sauri tayi ƙasa da kanta.
Kana cikin nutsuwa ta mike tsaye, direct gaban fridge ta nufa, inda ta bud’e ta dauko ruwa, da kuma tamarine juice maisanyi, bayan ta shiga kitchine ta dauko cups ne kuma, ta sake dawowa cikin falon, tare da ajiye juice da ruwan agaban Mamyn, cikin nuna tsantsar kulawa tace.
“Mamy ga ruwa kusha, nasan kunsha hanya, sannan ga abinci ma, tun d’azu na gama.”
Murmushin Jin dadi Mamyn tayi, tare da karb’an ruwan, da Jannart din ta tsiyaya a kofi Tasha,
Zuciyarta kuma cike da annushuwa tace.
“Masha Allah Jannart Allah ya miki albarka.”
“Ameen.”
Jannart din ta amsa cikin jin daɗi.
Yayinda shikuwa Ramadan dake zaune, ya tankwashe k’afafu Kallon Jannart din yayi, cikin dan sigar gajiya yace.
“Aunty Jannart wallahi yunwa nakeji, tun breakfast din safe, sai wani dan biscuit da naci, abamu abinci please.”
Murmushi Jannart din tayi, kana cikin sakin fuska tace.
“Sorry akwai abinci zakuje dining ko kuma akawo muku abincin nan.”
“Kai Anya kuwa, gaskiya dai Jannart kawo mana shi nan muci, saboda dukanmu agajiye muke.”
Mamy ta cab’i zancen domin itama kanta yunwa takeji.
Jannart kuwa kaita jinjina tare da cewa.
“To bari nakawo muku abincin nan.”
Tana gama fad’an hakan kuwa, ta mik’e tsaye, tare da nufan dining table din, food flasks din da ta zuba abincin aciki ta d’auko, atsanake kuma ta shiga jere musu shi agabansu.
Bayan ta kammala haka dinne kuma, ta d’auki plates tare da fara saving ko wannensu, had’add’iyar jollop rice and coleslaw din, ta zubawa Mamy, sai kuma pepper chicken onion soup din da ta zubashi acikin wani plate da ban.
Kamar yanda ta zubawa Mamyn kuwa, haka ta sakawa su Ramadan da Riyyam ma, way’anda sukayi zaman dirshan.
Saboda ma tunkafun su saka abincin abakinsu, kamshi duk ya cika musu hanci.
Turawa kowannensu abincin agabansu tayi, yayinda na Mamy kuwa ta kai mata har gabanta.
Tare da d’aukan cup ta zubawa kowannensu Shaka’n da ta had’a.
Ramadan da Riyyam kuwa, tun a Loman farko da sukayi, duk suka lumshe idanunsu, saboda wani irin dadin abincin da sukaji, tun kafun su gama tauna abincin kuwa suka soma jijjiga kansu, cike da gamsuwa, Ramadan yace.
“Masha Allah, nice taste gaskiya Aunty Jannart kin iya girki, ko daga aroma dinma kin biya.”
“Sosai kuwa Aunty Jannart, gaskiya abincinki akwai dadi, wayyo Allah kaman kunnena zai tafi.”
Cewar Riyyam-nsra daya cab’e zancen.
Ba’iya Mamy dake dariya ba kuwa har Jannart saida tayi murmushi.
Ahankali kuma ta mik’e tsaye, tare da sunkuyar da kanta k’asa cikin sanyi tace.
“Mamy bari na koma d’aki.”
Saurin Riko hannunta Mamy tayi, kana cikin kulawa tace.
“A’a Jannart Ina kuma zaki, ki zauna mana muci abincin tare, ko wani abu zakiyi a dakin?”
“A’a.” Jannart din ta fad’a ahankali, tare da soma wasa da y’an yatsun hannunta.
“to zauna kinji, kada kice zakiji kunyan mu, duka munzama daya.”
Mamyn ta fada mata cikin kulawa.
Jin hakanne kuma yasa ta zama, tare da bud’e food flask din Fan cake din, ta soma kokarin saka Musu acikin plate.
Ramadan da Riyyam kuwa tuni suke ta zuba santi akan abincin.
Wanda hakan yasa, Mamy daukan pillow ta saka musu, amatsayin waiji, sabida yanda suka cikasu da surutu.
Acan compound din gidan kuwa, Abba da Rayyern dinne suka shigo, atare kasancewar su sai yanzu ne suke dawowa daga masallaci, saboda Koda aka Idar da sallah basu bar masallacin da wuri ba.
Dab da zasu k’arasa jikin kofar falonne kuma, Rayyern yaga Abba na kokarin wucewa gaba.
“Abba Ina kuma zaka?”
Rayyern ya tambaya, da dan mamaki.
Hakan ne kuwa yasaka Abban sakin murmushi, kana cikin kulawa yace.
“K’ofar baya zanbi Rayyern”.
Da sauri yace.
“Meyasa?”.
Yana mai ci gaba da tafiya yace.
“Sabida surkata daga yau ma tacan zanna shiga da fita.”
Fuska Rayyern din ya kwab’e, kamar zaice wani abu kuma saiya fasa, Yayinda Abba kuwa kaitsaye ya nufi hanyar da zata sadashi da kofar falonsa na baya.
Rayyern kuwa fuskarsa ad’an tsuke yake mgnar zuci.
“Ba ga irin ta nanba kuma kanku takura zata zame muku”.
Ya ƙare mgnar yana tura kofar falon ya shiga, bakinsa d’auke da sallama.
Jin sautin muryarsa ne kuma, yasa Mamy dasu Ramadan d’agowa suka kalleshi, tare kuma da amsa masa sallaman nasa.
Idanunsa ya d’an zuba musu, musamman Ramadan da Riyyam, wanda yaga sun maida gaba daya hankalinsu wajen cin abinci, musamman ma Ramadan wanda ya ritsa pepper chicken, babu abunda kakeji atsakaninsu sai kat-kat k’aran spoons.
Idanunsa ya d’an lumshe, tare kuma dasa hannunsa ya dafe cikinsa, dan ƴar yunwar da yake ji.
buɗe idanun nasa da zaiyine kuma ya sauk’e ganinsa akan Mamy, wacce ta d’an zuba masa ido.
Idonshi ya kauda tare kuma da karyar da wuyansa gefe.
yanayin yanda Mamyn taga yasa hannayensa akan lafaffen cikinsa ne, kuma yasa ta gyara zamanta, kana cikin tausasa murya tace.
“Kwata kwata bakason cin abinci Rayyern, kana son barin kanka da yunwa bana son hakan
Kai kullum rayuwarka ta ƙare a cimar zaki, duda kasan matsalar da ke damunta, da anyi mgn sai kace.
Ba zaƙine matsalar ciwon kaba.
Zo kaci abinci kaji, gashi nan da d’uminsa kaci tun kafun ya huce, saboda nasan bakason cin abinci mai sanyi.”
D’an kwab’e fuskarsa yayi, had’e da kawar da kansa gefe.
Yayinda Ramadan dake ta cin nama kuwa ya d’ago da kansa ya kalli Hamman nasa, kana cikin santin abincin yace.
“Hamma Rayyern abinci yayi dadi, ka gwada ci kaji pepper chicken dinnan kuwa, badai dadi ba.”
Ya k’are maganar yana me yagan cinyar Kazan yasa abakinsa.
Riyyam-nsra kuwa, juyawa da kallonsa yayi ga Jannart, wanda take zubawa Mamy juice na pineapple and Orange din da tayi, kanta ak’asa yake, domin tun shigowar Rayyern din bata ma d’ago kanta ba.
“Nasara miki Aunty Jannart, wallahi kin iya dafa abinci sosai, tunda na shigo Nigeria banci fancake mai dadin naki ba, please kullum kina yi manashi kinji..”
ya k’are maganar yana me rausayar da kansa gefe, alaman rok’o.
Jannart kuwa da har yanzu kanta ke k’asa murmushi tayi, batare kuma da tace komai ba, ta zuba musu shaka a cup shida Ramadan.
Mamy kuwa Rayyern dake tsaye yana Kallon wani waje daban ta kalla, still kuma cikin kulawa tace.
“Babana zokaci abinci kaji, ka daina zama da yunwa.”
Kansa ya d’an girgiza alaman “A’a.”
Batare kuma daya ce komai ba, ya zagaya ta gefensu, kaitsaye ya nufi hanyar steps din da zai kaishi zuwa sama, ko kusa kuwa bai kalli inda Jannart take ba, impact baisan da cewar tana acikin falon ba.
Mamy kuwa da kallo ta bisa, harya soma haurawa saman stairs dinne kuma ya Dan tsaya, tare kuma da juyowa ya kalli Mamyn nasa yace.
“Mamy Abba fa ya shigo, yana side d’insa.”
Kai Mamyn ta jinjina, Yayinda shikuwa Rayyern din kaitsaye ya haura sama.
Jannart kuwa har dai zuwa yanzu ta kasa d’ago kanta, saidai jin alaman tafiyarsa yasa ta sauk’e b’oyayyar Ajiyar zuciya.
Mamy kuwa food flask din abincin ta d’auka, bayan ta mik’e tsaye ne kuma tace.
“Barin kaiwa Abbanku nasa abincin.”
Bayan ta wuce sashin Abban ne kuma, Jannart din ta d’an gyara zamanta, tare da d’ago kanta, ta kalli babban tv’n dake cikin falon, inda taga tv channel dinsu, wato Arewa24 suna haska film din, Nisan Kwana.
D’an maida hankalinta ga tv’n tayi, Yayinda su Ramadan kuwa har yanzu cin abincin nasu yaki k’arewa, santi kawai sukeyi, shakan da ta had’a kuwa tas suka shanye shi.
Acan b’angaren Rayyern kuwa yana shiga cikin falon nasu, jacket din dake saman rigarsa ya cire, tare kuma da karasawa gaban fridge dinsa, bud’e murfin fridge din yayi.
Hade da d’auko babban kwalban chocolate d’insa, wanda saboda tsabar sanyi harya fara daskarewa.
Murfin kwalban ya b’alle, tun kafun ya zauna kuwa ya saka spoon acikin kwalban, tare da d’ebo chocolate din ya soma sha.
Idanunsa ya lumshe, alokacin da yaji zakin chocolate din na mamaye bakinsa.
Cikin nutsuwa kuma ya zauna akan daya daga cikin kujerun falon, bayan ya daura kafafunsa akan rug ne kuma ya ci gaba da Shan chocolate d’insa.
Yana girgiza k’afa alaman yana enjoying mood dinnasa.
Mamy kuwa Koda ta isa part din Abban, zaune ta sameshi a falon, ganinta ne kuma yasa Abban sakin murmushi.
Kana cikin sakin fuska yace.
“Banyi tunanin zuwanki yanzu ba ai, naga kaman yaran naki sun rik’eki da zance saboda daga nanma inajin tashin maganganunku.”
Murmushin Mamyn tayi, adaidai lokacin da take k’arasowa gabansa ta durk’usa, kana muryarta atausashe tace.
“Barka da dawowa.”
“Yauwa, kuma sannunku da dawowa, fatan kunyi sayyaya lafiya?”
“Lafiya lau Alhamdulillah, munsayo duk wasu abu da suka dace gacan kayan ma acikin falo, ko kuncesu ba mu yi ba.”
Mamy ta amsa tana me kokarin zuba masa fried rice acikin plate.
Abban kuwa Kai ya jinjina cike da gamsuwa, kuma yace.
“To Allah ya Amfana.”
“Ameen.” Mamyn ta amsa tana me ajiye masa plate din abincin agabansa, hade kuma da zuba masa juice, and fancake.
Juice din Abban ya d’auka ya d’an kurb’a, cikin rashin son tauyeta kuma yace.
“Kije ki gama da yarannaki ko, ni Idan yaso kyaji dani anjima.”
“To.” Mamy tace tana murmushi, kana kuma ta mik’e ta fice daga Cikin falon.
Koda ta dawo falon,harsu Ramadan sun kammala cin abincin.
Inda Riyyam da kansa ya tartare wajen,. Tare dakai plates din da suka b’ata kitchine.
Mamy kuwa zama tayi tare da jawo kayyyakin da suka sayo.
“Jannart zokiga kayayyakin da muka sayo.”
Mamyn ta fad’a tana me bubbud’e kayan.
Inda ta fara ciro wasu tsala tsalan laces, da kuma atamfofi masu kyau, Hadi da materials da shadda laces.
Jannart kuwa ganin yanda kayan suke da kyau sosai ne yasakata sakin murmushi, tare da cigaba da Kallon kayayyakin da Mamyn ke fitowa dasu.
Bayan Mamyn ta faka su laces din agefe ne kuma, ta soma ciro had’add’un Turkish, and Dubai abayas and kimonos, masu kyau da tsadar gaske, kasancewar kuma abayas din irin new design dinnan ne yasa suka dauki hankalin Jannart.
Mamy kuwa sauran shoes bag and vails, da kuma sauran abubuwan da suka sayo duk ta nunawa Jannart, kana cikin kulawa kuma tace.
“Jannart ga kayayyakin naki, Allah yasa sunyi miki.”
Murmushi Jannart din tayi, tare da d’an sunkuyar da Kanta, tana kallon datsassun abayas masu masifar kyau da laces din cikin sanyin murya kuma tace.
“Komai yayi, nagode sosai Mamy Allah Ya saka da al'khairi.”
“Ameen Summa Ameen Jannart, ba komai ai yiwa kaine.”
Mamy ta amsa, tana me zaro wayarta, inda ta dannawa number’n, tailor din da ta amince da k’warewar sa kira.
Bugu biyu kuwa tailorn ya d’auka, bayan sun gaisane kuma Mamy ta shaida masa cewar tanason ganinsa.
Kasancewar yasan inda Naira take ne kuma, yasa take yace.
“Toh Hajjajo. Ganinan zuwa.”
Kashe wayan Mamy tayi, tare da Kallon Jannart cikin kulawa tace.
“Yauwa Jannart wani irin dinkuna kikeson ayi miki, kinsan ku y’an matan zamanin nan yanzu baku cika son riga da zani ba.”
Sadd’a kai k’asa Jannart din tayi, ladabce tace.
“Ni Mamy komai akayi ma inasawa.”
Murmushin Mamyn tayi tare da cewa.
“Shikenan To bari tailan yazo.”
Nan dai suka shiga d’an tab’a hira, Yayinda Riyyam-nsra da Ramadan keta jan Jannart din da hira.
Suna nan azaune kuwa, cikin abunda bai wuce 15mn ba saiga tailorn yazo.
Bayan sun gaisane kuma Mamy ta basa, k’atuwar ledan da ta Ware kayayyakin dinkin aciki, kana cikin sakin fuska tace.
“Fahad ga y’atanan dan Allah kayi mata dinkuna masu kyau, way’anda zasu sake fito da ita sosai, sannan kuma akan kari muke buk’atar kayan.”
Murmushi Tailan da Mamyn ta kira da Fahad yayi, kana Cikin bata girma yace.
“Insha Allahu Hajiya za’ayi mata dinki dai-dai da zamani, kafun nan da sati biyu kuma zaku samu dinkin Insha Allah.”
“Yauwa to Allah yasa, yanzu za’a baka size dinta ne, ko zaka gwada ta?”
Mamyn ta fad’a tana me Kallon Jannart da kanta ke sunkuye.
Kanshi ya ɗago ya ɗan kalli Jannart kana yace.
“A’a basai na gwada taba, ai naganta kuma Insha Allah zanyi mata komai yanda ya dace.”
Fahad din ya kare mgnar yana sake harhad’a kayan waje daya.
Mamy kuwa kaita jinjina cike da gamsuwa tace.
“To nawa ne kudin dinkin naka.”
D’anjim Fahad din yayi, saboda shi kansa baisan nawa zaice ba, kasancewar kayan suna da yawa, dole sai ya nutsu ayi total tukunna.
Fahimtar hakanne kuma yasa Mamy mik’ewa tsaye, tare da cewa.
“Kad’an jirani inazuwa.”
Kaitsaye sama ta haura, tana shiga cikin falon saman kuwa ta hango Rayyern zaune, ya daura kafarsa daya kan d’aya, Yayinda idanunsa kuwa ke lumshe, sai kuma goran swan dake rike a hannunsa.
“Rayyern.”
Mamy ta kira sunansa.
Jin sautin muryar Mamynnasa ne kuma yasashi bude idanunsa.
Tare da gyara xamansa yace “Mamy.”
“Na’am tunanin mekakeyi?” Mamyn ta tambaya cike da kulawa.
Kansa ya dan juya, kana cikin sanyi yace.
“Babu komai Mamy, kawai dai nagaji ne.”
“Da kyau.
dama kudin dinki nazo karb’a awajenka, yanzu na kira taila kuma yazo, zai tafi da kayayyakin da muka sayo zaije ya dinkosu.”
Mamyn ta fad’a tana me tsaresa da idanu.
Wanda hakanne kuma yasashi shagwab’e fuska, tare da karyar da wuyansa gefe, kana akasalance yace.
“Eyyah Mamy ai duk kun kwashemin y’an kud’ad’ena, kuma fa bana da wani kudi sosai, sannan ba atm dina yana hannunku ba naga shima yadda kuka yasheni kamar ba gobe.”
Murmushi Mamy tayi, saboda tasan maganar cewa ma bashi da kudi ba gaskiya bane.
Sai dai al'adarsa ce bai cika son almobazaranci ba, yana fadin hakanne kawai saboda kaucewa mgnar da suke ta lika mishi
“Cash mukeso yanzu ba wai transfer ko wani abuba, tailor ne yazo, ko atm card din kakeso mu bashi yaje ya cire?”
Cewar Mamyn.
Rayyern kuwa da sauri ya kalleta tare da cewa.
“Atm card na din zaku bawa wani, uhumm lallai Mamy abun ya magaga”. shi bawai kudin bane bayason bayarwa, a'a kawai dai shi ayanda aka lika masa auren ne baiso ba, saboda dama yasan dolene sai antakurasa akan hakan.
Ita kuwa Mamy ido kawai ta zuba mishi.
Mik’ewa tsaye yayi, tare da nufan d’akinsa, kaitsaye gefen bedside drawernsa ya nufa, Koda ya ya karasa bud’e drawern yayi ya d’auko, bandir din kudi, Rafa daya inda kuma kowani Rafa daya 50k ne.
Juyowa yayi ya dawo falon, tare da damk’awa Mamyn kudin.
Cikin shagwab’a da kuma turo baki yace.
“Mamy gashi yanzu a barni in huta ko. Kuma a kamo min ATM na kin san Ramadan ba mutuncine dashi ba, in ya samu kudi.”
Karb’an kudin Mamy tayi, batare kuma da ta sake ce masa komai ba, ta juya ta fice daga cikin dakin.
Koda ta sauko kasa, duka 50k din ta bawa Fahad.
Da ya tashi tafiya ne kuma ta had’ashi da Hadi ya kaisa har zuwa babban shagonsa.
Sauran kayan da suka rage din kuwa, Mamyn da kanta ta Taya Jannart suka shigar dashi, can cikin bedroom din Jannart din.
Cikin kulawa kuma haka Mamyn ta Taya ta suka shirya duka sauran kayan acikin wardrobe, kayan shafa kuwa anan kan dressing mirror Jannart din ta jere su.
Bayan sun kammala komai ne kuma, suka sake dawowa nan cikin main falon.
Zama sukayi inda Riyyam da Ramadan kuwa suka shiga sana’arsu ta buga game, ganin yanda Game din ke dadi ne kuma yasa, Jannart maida gaba daya hankalinta garesu.
Mamy kuwa kallonsu take fuskarta d’auke da yalwataccen murmushi, saidai kuma ganin yanda hankalinsu duk ya tafi akan game dinne yasa, ta mik’ewa.
Anutse ta nufi sashin Abba.
Ahankali ta tura kofar dakin ta shiga, bakinta dauke da sallama.
Abba dake rike da wani littafi na Tafsir, ne ya amsa mata sallaman tare da d’ago kansa ya kalleta.
Itakuwa Mamy fuskarta dauke da murmushi ta k’arasa shigowa cikin falon, cikin muryar dake nuna tautasawa tace.
“Allah yasa bankatseka daga abunda kakeyi ba.”
Murmushi Abban yayi, cikin fadada fara’ar dake kan fuskarsa kuwa yace.
“Sam baki katseni ba, kamar kinsan cewar kuma dama ina nemanki.”
Abban ya fad’a yana me jawo wata leda dake gefensa.
Mamy kuwa k’arasowa inda yake zaunen tayi, tare da durkusawa ta zauna agabansa.
Abba kuwa Ledan dake hannunsa ya mik’a mata, atausashe yace.