Showing 6001 words to 9000 words out of 350584 words
bugun zuciyarta ya ƙara tsananta.
Har kana iya ganin yadda numfashin ta ke fita da yanayin tsoro.
Fuska ya kuma murtukewa.
Kana yace.
"Munafuka, sai kace da gaske haka kike tsoron maza, ji yadda kike tafiya ba bra kina wani karkakaɗa ƙirji irin ke gaki ƴar iska mai son maza ko?."
Idanunta ta rumtse da k’arfi cikin kuma ƙunan ran ƙazafin da Yah Junaid ke jifarta dashi murya na rawa tace.
"A'a".
Cikin haɗe fuska ya daka mata tsawa tare da cewa.
"Toh meya hanaki sa bra?".
Murya na rawa tace.
"Dr. Lukman ne yace in daina sa bra, sabida matsalar numfashin da Athsman ɗina ke jamin. In nasa ya matse min ƙirji sai numfashina yayi ta shaƙewa".
Wani irin dogon tsaki yaja tare da cewa.
"Ubanki zanci in baki dena raina min hankali ba, matse ƙirjin da ƙatti keyi bai shaƙe numfashin ba sai saka bra ne zai cushe miki numfashin."
Fice min da gani!!". Ya k’are maganar a tsawace.
Jin hakanne kuma yasa da sauri ta juya ta fita, hawaye na zubo mata sabida raɗaɗin marin daya yarfa mata da zafin kalaman zargi da yake binta dasu.
A falo ta samu Mom da sauri ta faɗa jikinta.
Cikin sakin sassayan kuka tace.
"Mom ki gaya musu wlh ni ba yar iska bace, Meyasa Mom Meyasa Ya Junaid ke jifana da mugayen maganganu, shifa yaya nane..”
Jawo hannunta Mom tayi suka zauna bisa kujera, a hankali tasa tafin hannunta tana share mata hawaye cikin yin ƙasa da murya tace.
"Na sani Jannart kuma Allah ya sani, ke ba ƴar iska bace. Yaushe ma kika samu sakewar rayuwar duniya kullum kina cikin takunkumi.
Ko ina zakije da masu gadinki.
Na rasa wannan masifar tsaron na menene kina girma ana ƙara killaceki kamar abun rashin gsky."
Cikin shessheƙan kuka tace.
“Mom shi Yah Junaid gani yake, su masu tsaron nawa dasu nake iskanci.
Daddy Kuma gani yake in ya cire masu tsaron da wasu zanyi iskanci.
Wlh na sani Mom bawai dan tsaron lfyata bane yasa Daddy ware min masu tsaro.
Shima zargina yakeyi ko Mom?".
Jin yadda numfashin ta ke fitane yasa mom gyara zamanta kana ta fuskanceta da kyau.
Allah ya sani tana son Jannart tamkar ƴar cikinta.
Amman duk yadda zatayi bata burge Alhaji Idi da Junaid, gani suke kamar so take Jannart ta lalace ne don ba ita ta haifeta ba.
Cikin kula da tausasawa uƙubar da suke shayar da ita tace.
"A'a Jannart Daddynku baya zarginki, shi ya bada masu tsaronkine sabida larurar ciwonki, kina buƙatar makusanci a koda yaushe, tunda abu kaɗan ke tada miki athsman ɗin wanda kinga tun da yana nimoniya, kina girma yana canzawa ya riƙa har ya zama asman shiyasa yake tsananta kulawa a kanki.
Sabida abu kaɗan ke tada miki shi.
Kuma Yah Junaid ɗinki yana sonki.
Ɗan uwa, uwa ɗaya uba ɗaya ya wuce wasa.
Sun haɗa da son da Mamanki zatayi mikine da tana raye".
Cikin zubda hawaye tace.
"Mom kin bani son da ya kamata uwa ta bawa ƴarta, ni banyi maraicin kyakkyawan tarbiyar uwa ta gari ba.
Kawai dai basa so nane".
Cikin kafeta da ido Mom tace.
"Jannart ki yarda dani, tashi muje kici abinci".
Cikin nitsuwa tasa hannunta ta share hawayenta kana ta miƙe.
Dinning area suka nufa.
Suna zama Daddy ya fito da hakama Junaid da Abdul.
Nan suka zauna sukayi breakfast.
A hankali ta sauke numfashi ganin Junaid ya miƙe ya bar wurin.
Sai kuma ta ɗan kalli Alhaji Idi Saleh Dakata.
Cikin takatsantsan da girmamawa tace.
"Daddy Ina son zanje gidan Aunty Rabi'ah akwai wani aikin da zamuyi a can".
Ido ya ɗan zuba mata.
Ita kuwa da sauri tayi ƙasa da kanta.
Tana tasbihi cikin ranta, da addu'ar Allah ya ɗaurata a kanshi.
Juyawa yayi ya fara sauƙa kan steps ɗin tare da cewa.
"Kada ki daɗe.
Kuma ƙafarki ƙafarsu Sunday."
Cikin sabo da hakan tace.
"Toh".
Kana ta miƙe ta nufi ɗakinta. Mom kuma ta fara tattara kan table ɗin.
Wanka tayi cikin nitsuwa da kuma sauri-sauri.
Tana fitowa, ta zauna ta tsane jikinta kana ta busar da tattausan suman kanta.
Ta shafa mishi mayuka, sannan ta tubkeshi.
Mai ta ɗan shafa kana ta Murja farar hoda, tare dasa man baki.
Sosai tayi kyau duk da bata cika kwalliya a fuskarta ba.
Wasu tattausan riga da wondo pallazo farare ƙal ta zaro,
Sai wata doguwar riga budaddiya mai igiya a tsakiya.
pantie tasa, kana ta zira dogon wondon daya kasance yayi tightin fatar jikinta.
Dole sa bra baya cikin jadawalin rayuwarta sabida larurar ciwonta.
Sai dai takan sa rigunan su ɗan matseta.
Rigar ta zura irin mai wuyanan nane wato, high neck, naɗe wuyan tayi ta gyarashi.
Cib-cib rigar tayi mata a jikinta gwanin burgewa ƙirjinta yayi cas a tsaye babu alamun ronƙofowa bare zubewa.
Lafaffen cikinta ya taimaka kwarai wurin bayyana tsayeyyun breast ɗinta.
Doguwar rigar kimono blue color mai ɗigon fari-fari'n ta ɗaura saman riga da wondon, cib kuwa kimonon yayi mata ajikinta, inda kuma har ƙasa yazo mata.
Igiyoyin dake sarƙafe tsakiyan rigar ta kama ta ɗaure.
Hakan ya bawa tsakiyar rigar haɗewa, sama can kan ƙirirjin ta kuma gefe da gefen ya rufu har ya samu damar rufe nimples ɗin ta.
Sai kuma tsakiyan bai ida rufuwa ba.
Sai kuma can ƙasa ta nan zaka gane riga da wondone a ƙasan doguwar rigar farin mayafi rigar ta dauko tayi Rolling kanta fuskarta ta fito a ciki kamar sifili (0) a ciki.
Sosai shigar tayi masifar mata kyau.
Wanda kuma sune suturunta na yau da kullum wanda tafi so da jin daɗin sawa, kasan cewar rigunan cikin masu taushine suna buɗuwa dai-dai jikinta.
Turare mai sauƙin ƙamshi ta fesa, sanin sa mai tsananin ƙamshin yana da illa ga baliga in zata fita da kuma lfyarta.
Wasu fararen takalma sau ciki masu taushi tasa.
Kana ta zari babbar wayarta kiran iphone11promax ta fito.
A bakin ƙofar shigowa falon tayi kiciɓis da Mom cikin.
Yanayin sakin fuska Mom tace.
"Kai masha Allah ɗiyata kinyi kyau".
Cikin yanayin jin daɗi tace.
"Ngd Mom bari inje da wuri in samu in dawo da wuri".
"Toh hamzarta ɗiyata, sai kin dawo".
Toh tace kana ta fita ta tafi.
Tana fitowa harabar gidan
Wadannan garadan marasa kan gado suka miƙe baki ɗayansu.
A hankali ta matso kusa da Driver'n'.
Cikin kula yace.
"Jannart yau kuma ina zamu je, naga yau ba ranar aiki bane?".
Cikin jin daɗin yadda dattijon ke mata mgn ta mutuntaka tace.
"Baba Ado, gidan Hajia Rabi'ah zamuje".
Marfin motar ya kama da nufin buɗe mata, da sauri tace.
"Baba Ado ka bari zan buɗe".
Murmushi yayi kana ya bude mata, ta shiga.
Suma sauran suka shiga sauran motocin suka tafi.
Suna isa gidan Hajia Rabi'ah.
Bayan sunyi parking ta nufi cikin gida su kuma suka zauna a waje.
Da sallama a bakinta ta tura ƙofar.
Da sauri taja da baya ganin Asiya dake fitowa.
Sai kuma ta shigo ganin taja gefe tana hararanta.
Da sauri tayi ciki jin Hajia Rabi'ah na cewa.
"A a Jannart kin iso ko.
Maza shigo daga ciki".
Cikin jin daɗi ta shigo.
Ta zauna inda Hajia Rabi'ah ke nuna mata.
Cikin girmamawa tace.
"My Aunty Ina kwana".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Lfy lau Alhamdulillah ya ƴan tsaron ki".
Cikin yin gajeren murmushi tace.
"Gasu can a tsaye a bakin gate tamkar dogaran sarki".
Dariya ta ɗanyi kana ta kalli wani ɗan matashi dake zaune can bisa kujarar Dinning area tace.
"Toh Mahmoud ga Jannart ɗin ta iso.
Tunda kaƙi bawa Asiya amsa ko ɗaya".
Da sauri ta juyo ta kalli inda aka kira Mahmoud.
Shi kuwa tasowa yayi ya nufo cikin falon yana mai cewa.
"Aunty naga kamar hasadace ke cinta, kuma ma bada ita nai wayaba.
Ita kuma wanna sai saiɓi.
Kin san tun safe ina nan kin ajiyeni kamar mara aikin yi".
Cikin nitsuwarta tace.
"I'm so sorry. Ina kwana".
Gefe ya zauna kana yace.
"Wuni dai tunda 12 tayi".
Nan suka gaisa kana Jannart ta fuskanceshu da kyau.
Cikin sani makamar aiki tace.
"Yaushe jirgin Ethiopia zai diro Nigeria a wanne gari ɗaya Abuja ko Lagos ne?".
Murmushi Mahmoud yayi tare da cewa.
"Wato zaki nuna min ke yar jaridace, tuni kin fara tambaya da wayo.
Jirgi zaki tambaya ko shi?".
Kwaɓe fuska tayi tare da kallon Hajia Rabi'ah kana a hankali tace.
"My Aunty menene ma sunan nashi?".
Cikin zuba mata ido Hajia Rabi'ah tace.
"Iyeh wato ma har kin mance sunan nashi. Kin manta cewa sunan nashi ne kawai makaminki."
Cewar Hajia Rabi'ah.
Ita kuma Jannart takwara kanta tayi bisa kafaɗa kana tace.
"Please my Aunty gaya min zan riƙe".
"Rayyern". Ta bata amsa a takaice.
Ita kuwa ido ta lumshe tare da fesar da numfashi can cikin zuciyarta tace.
*"RAYYERN! RAYYERN!! RAYYERN!!!* Ta maimaita sunan sau uku kana ta juyo ta kalli Mahmoud cikin nitsuwa tace.
"Mahmoud ranar yaushe zai dawo? Da wanne lokacin jirginsu zai iso daga Abuja ko Lagos zuwa Kano?".
Gyara zamanshi yayi kana yace.
"J....!
free PAGE .
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*TUBALI*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
ASSALAMU ALAIKUM, Masoyana ma karantan littattafaina, ina mai farin cikin sanar daku, yau d’in nan MON, 18 OCT 2021 za'a fara biyan kud’in samun damar karanta littafin TUBALI akan farashi mai sauk’i Biya 500 k’aramin farashin na k’aramin group, kana sai *Special people Group* akan farashi mai sauk’i 1k kacal babban group a yawan posting babancinsu yake, zaku biya ta asusuna.
ACCOUNT NO 0661110170.
BANK NAME: AISHA ALIYU GARKUWA
BANK GTBank
sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan numben tawa da nakeyin whatsApp da ita 09097853276.
*PLS TAKE NOTE BAND VTU*
kada kiyi min VTU ko transfer'n katin ta wannan numben etisalat d’in idan kuwa kikayi wlh babu ruwana dan na fad’i miki. Please and please in dai da hali kada ki turo min katin, kiyi min transfer'n ruwan kud’i ta bank account na, in kuma babu dama to sayi katin MTN sai ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp.
Gareku mutanen jamhuriyar Niger ku tuntub’i Mommy akan layinta +22790899076, ta wurinta zaku biya, hoton katin zaku d’auka ku tura mata ta wannan numben a whatsApp, Special people group 1k ne (1000) k’aramin group kuma (500) kacal,
Please dan Allah babbar macece mai yara da tarin jikoki da y’ay’an jikoki mu kyautata lafazi da mu'amala gareta dan Allah don in ka girmama iyayen wasu wasu zasu girmama naki🙏🏻...
Littafin TUBALI littafine na musamman mai salo na musamman mai cike da abubuwa masu tarin yawa.
*Tausayi, Sark’ak’iya, jan hankali, Fadakarwa, Nishad’antarwa, ilimantarwa, al'ajabi, Sa'ar rayuwa, riƙon amana, cin amana, ribar kyautatawa, kana da sassayar soya mai salon narke jiki da zuciya*
Ga number wayata da nakeyin whatsApp da ita, 09097853276 idan kina son biyan kudin samun damar karanta littafin TUBALI sai ki biya ta wannan ac no din dai 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, dan Allah ki biya kafin kiyi min mgn kina turo shaidar biyanki ina gani zan saki a group, in Kuma baki da ac no ko yanayin zaman wani k’asa ko wani luggun ki sayi katin MTN na 1k in special group kikeso ki turo min. In Kuma k’aramin Group kike so ki sayi katin *MTN ki copy number's din ki turo min ta whatsApp number'n na 09097853276 kada kiyi min VTU ko transfer'n katin 9mobile dan layin nada matsala*
Za'ayi tsawon mako ɗaya ana biya ina kafin in fara update domin samun sassaucin aiyukan sauraron mutane, za'a fara biya yau *MON 18 OCT 2021. Kana zan fara posting ranar MON 25 OCT 2021 rana ita yau kenan in mai kowa mai komi ya kaimu bisa rai da lfy*
🙏🏻Na rokeki da girman zatin ubangiji in dai kin san zaki sayane dan ki fidda min littafina dan Allah ki bar kud’inki kiji tausayin marainiya, kada ku cutar da marainiyar Allah,😭🙏🏻🙏🏻🙏🏻.
Nasan daga yau har zuwa na gama littafin Chart zaimin yawa zai hausawa aiyuka zasu yawaita gareni, amman babu kamar makonni ukun forko zuwa biyar, Please ina neman al'farmar uzuri in kinga kinyi min mgn ban amsa mikiba, na tuba kiyi haƙuri ba raini bane ko wulak’anci face yawan mutane wata k'il ban isa kan Chart naki bane, Amman muddin na isa na kuma bud’e na gani tabbas zan baki amsa in katine zansashi yana shiga zan saki a group in bai shiga kuma in gaya miki, in Kuma ta account kika turamin ina ganin shaidar biyanki zan saki a group, 🙏🏻Dan Allah in kinsan ba littafi ko maganin gyara namu na mata kikeso ba to kiyi haƙuri da min mgn sai na d’an samu salama🤝🏻😘🙏🏻😂.
*Sayan na gari maida kuɗi gida sai kinzo*
By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:19 PM - Auntyna: *TUBALI*
PAGE 3
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
*FREE PAGE*
*ƊANƊANO*
*NMETTARI enji men nfulɓe*
"Jibi". Ya bata amsa a taƙaice yana mai kallon Kyakkyawar fuskarta.
Ita kuwa gyara zamanta tayi tare dasa hannu ta amshi cup ɗin ruwan sanyin, da Hajia Rabi'ah ke miƙa mata-ta ajiye shi bisa Stoll din baƙin glass dake gabanta.
"Nagode". Ta faɗi cikin nitsuwa, sannan ta kalli Mahmoud dake bin fuskarta da ido.
Cikin yanayinta na nutsuwa da kuma bayyana zallan ajinta na y’a Mace tace.
“Akwai tabbacin jibi zai dawo? Sannan ta Abuja ko Lagos zasu sauƙa?".
Wayarshi ya zaro a al'jihun rigarsa yana mai lallatsata kana yace.
“In sha Allah jibi zasu dawo.
Dan last night muna tare da Deen ƙanin Usman PA'nshi.
Yayi magana da yayan nashi kan jikin mamansu ya tashi, yaushe zasu dawo.
Toh nan Usman ɗin ke cewa jibi zasu dawo.
Iya abinda na sani kenan, sauran bayani kuma sai dai in tuntuɓi Deen ɗin".
Ya ƙare maganar yana sa wayar a amsakuwa yadda duk zasuji.
“Hello Deen ya Gida".
Cewar Mahmoud.
Deen dake zaune gaban mamansu wanda yanzu ya gama magana da Usman ne yace.
"Lfy lau Alhamdulillah Mahmoud".
"Yah jikin Mama".
"Alhamdulillah jiki da sauƙi".
Ya bashi amsa yana miƙa mata maganin.
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Yah Usman ɗin yana dawowa ko?".
Ɗan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
"Eh to, zasu dawo, amman sai jibi fa kuma nan ma wata ƙil in sun iso su kwana a Abuja wata ƙil suda nan sai ranar jumma'a".
ya ƙare mgnar da sanyi.
"Ayyah ba komai ai in dai jikin da sauƙi, jumma'a kamar yaune Allah dai ya dawo dashi lfy. Ka gaida min Mama da jiki Allah ƙara ƙarfin jiki".
“Amin Amin". yace kana sukayi sallama.
Katse kiran yayi tare da juyowa ya kalleta.
Numfashi suka sauƙe ita da Hajia Rabi'ah.
Sai kuma tace.
"Alhamdulillah, toh Mahmoud ko zaka bani number Deen".
Da sauri yace.
"A a in fa yasan me kike bincika bazai saurareki ba".
Hajia Rabi'ah ne ta amshi zancen da cewa.
"Kada ki damu Jannart in sha Allah komai zai tafi dai-dai.
Shi Mahmoud ɗin shi zai rinƙa samo mana bayani.
Tunda kuna da number’n juna zaike miki bayani, ba sai kin fito kinzo nan ba, tunda fitar naki aikine mai zaman kanshi."
Cikin gamsuwa da hakan tace.
"Toh shike nan My Aunty, Ngd Matuƙa Allah ya saka da al'khairi".
“Amin Amin.” tace
Tana mai gudun kada aikin ya bar hannun yarinyar tunda kowa ya ganta dai yasan bawai tana yin aikin dan neman kuɗi ko suna bane, tana yine dan ra'ayin tane gashi du-du watanni huɗu tayi da fara aikin kuma suna jin daɗin mu'amala da ita, so dama sanyin da shirin yayi shiyasa aka canza wanda ke yinsa a baya.
Kuma da alamun tana matuƙar jin daɗin aikin.
Kiran Salman ne ya shigo wayarta.
Da sauri ta amsa tare da karawa a kunne.
"Assalamu alaikum".
Tace cikin sassayan sautin ta.
Daga b’angarensa kuwa murmushi yayi tare da cewa.
"Wa alaikissalam, Jannart kinbi diddigin Rayyern d’in? Kuma wane lbri kika samo mana a kanshi? "
Cikin yarda da kai tace.
"Duk motsinshi na cikin tafin hannuna!".
Dariya mai sauti Salman yayi.
Hakama Hajia Rabi'ah da Mahmoud.
"Karsashi’nki da ƙarfin guiwarki akan aiki yana burgeni Jannart”.
Cewar Salman.
Cikin sauƙe numfashi tace.
"Toh ba doleba Salman, tunda naji ana shirin korata, ai sai inda ƙarfina da hikimata suka ƙare".
Cikin wasa yace.
"Ke har wani ƙarfi a garreki da dai kin tsaya a hikimar na yarda".
Murmushin daya sanya beauty point ɗin ta lotsawa tayi.
Haka dai suka ɗan tattauna batun bayan ta mishi bayanin abinda ta ji kan dawowarshi.
Saida tayi sallan azahar ne kuma ta fito suka nufi gida.
A kan hanyarsu ta komawa ne, Baba Ado driver'nta ya ɗan juyo ya kalleta cikin kulawa yace.
"Jannart yanzu dai ciwonki da sauƙi ko?".
Numfashin ta ɗan fidda kana a hankali tace.
"Alhamdulillah da sauƙi dai zance, amman yana yawan motsa min a kwanan nan kamar yana son tashi."
Cikin tausayawa yace.
"Toh amman har yanzu babu wani maganin da ake baki sai allurar da akeyi duk watan ne?".
Kai ta gyaɗa mishi tare da cewa.
"Eh".
Numfashi ya ɗan fesar kana yace.
"Allah ya sauƙaƙa yasa zakkan jikine al'farmar Annabi da al'ƙur'ani".
Cikin jin daɗi tace.
“Amin Baba Ado nagode!".
A can Ethiopia birnin Addis Ababa, kuwa.
Riyyam-nsra ne tsaye gaban wayarsa daya tsaida.
Rawa yakeyi da murmushi a fuskarsa.
Sai kuma ya kalli gefensa.
Wata kyakkyawar budurwa wacce a ƙalla suyi sa'anni.
Murmushi yakeyi cikin harshen Hausa yake cewa.
"Jibi iwar haka ina hanyar Nigeria, su Zayton kuma sai dai ayi ta aikin zumbura baki.
Fan's ku gani, wai kishi takeyi dani".
Da sauri ta kai mushi bugu tare da matso ƙwallar idanunta, tana faɗin
"Mammy! Mammy!!".
Wata kyakkyawar matace mai Kekkyawar sura da jiki da shiga ta kamala, wacce kyan surarta ya iya boye ainihin shekarunta, ta fito daga cikin wata ƙofar da fuskantar inda ya kafa wayar tashi.
Ɗan gudu-gudu da tsalle-tsalle yake yana zagaya parlon Zayton na biye dashi a baya.
Da sauri yayi tsalle tare da ɗan sakin ƙara yace.
"Ohh Mommy".
Jin ta ɗan sa hannu ta bugi ƙeyarshi.
Tura baki yayi tare dasa hannunshi ya shafa ƙeyar yana mai zazzarewa Zayton ido.
Abin gwanin ban dariya da ka gani kasan akwai Kekkyawar shaƙuwa, ƙauna, tausayi, da son juna.
Ɗauke wayar tashi yayi ya sake video a