Showing 78001 words to 81000 words out of 350584 words
dan komai ba, saidan saka rai da kuma fatan cewa watakila zaku dubeni..”
Dan Jim yayi kana cikin k’ank’an dakai yace.
“Taimakon had’i da Alfarma nazo nema awajenku, Dan isar Allah da Manzonsa idan zaku iya.”
Shiru gaba d’aya falon ya d’auka, Yayinda kuma har yanzu zuciyar Abba keci gaba da bugawa, saidai kuma jin abunda Barrister Kabir din ya fad’ane yasa shi, sauk’e ajiyar zuciya, tare da kallon Barrister Kabir din cikin, kuma rashin gane inda kalamansa suka dosa yace.
“Inajinka Barrister wacce irin taimako kake nema awajenmu, Allah Dai yasa zamu iya sabida yadda ka haɗamu dashi da fiyayyan halitta in ban iya maka shiba zanji ciwo a raina.”
Idanunsa da suka d’an ciko da hawaye lokaci daya ya lumshe, cikin sanyin da jikinsa yayi ne kuma ya d’an zamo jikinsa daga kan kujeran, batare kuma dasu Abban sun farga ba, sai ganinsa sukayi ya durk’usa guiwowinsa biyu agaban Abban.
Cikin wata irin muryar dake bayyana karyewar zuciya da kuma tsananin damuwarsa yace.
“Dan Allah Dan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam. kuyimin taimako, da kuma alfarma kamar yanda na buk’ata a farko, saboda tseratar da rai da kuma lafiyar y’ar Adam.”
Again gaba d’aya falon shiru ya dauka, babu abunda ke tashi acikinsa kuwa face bugawan zuciyoyi, Yayinda kwakwalwar kowanne daga cikinsu ke kawo masa tunani na daban.
Bama kamar Abba da gaba d’aya kalaman Barrister Kabir din suka d'aure masa Kai, tare da juya masa tunaninsa izuwa wani waje na daban.
Yayinda shikuwa Rayyern gaba daya ya dauke kansa gefe, tare da hade fuskarsa.
Kallon Barrister Kabir din Abba yayi, cikin kuma rashin fahimta da kasa sanin makaman kalaman nasa, hadi da rudun daya samu kansa aciki yace.
“Barrister har yanzu dai ban fahimci inda kalaman naka suka dosa ba, bamusan me kake nufi ba? Rayuwar waye zamu tseratar, sannan me hakikanin zancen naka yake nufi?”
Idanu Barrister Kabir ya d’an lumshe, sannan kuma murya araunace yace.
“Tana tsananin buk’atar taimako, Tabbas Jannart tana buk’atar Garkuwa, had’i da ingantaccen mafaka, tana buk’atar haske acikin rayuwarta, wanda yake dauke da sarkakiya maitarin yawa, gaba daya duhu da bakinciki sunyi tasiri acikin rayuwarta, hakika tana buk’atar taimako, da kuma samun ceto daga irin azabar da d’an uwanta yake gana mata, Dan Allah ku taimaka ku bata mafaka, ku taimaka ku tayani inganta rayuwar marainiyar da Allah kejin kanta akoda yaushe.”
D’an tsagaitawa da maganan nasa yayi, tare da d’ago kansa akaro na barkatai ya kalli Abba daya zuba masa ido.
Saidai kuma awannan karon irin Kallon da yakeyiwa Abban ya banbanta dana sauran lokutan.
Bakinsa ya bud’e Ahankali cikin kuma fata da addu’an cikar burinsa yace.
*”Dan Allah Ina meneman alfarma agareku, Ina nemawa y’ata auren d’anka Dr. Rayyern Mai-nasara!!” zan bashi ɗiyata bisa yarda da gamsuwa da tarbiyarshi da gskyarsa da amanarsa*
Wani irin bugawa maitsananin karfi zuciyar Abba tayi, wanda kuma harsaida rud’u da kuma mamakin daya shiga ya kasa b’uya akan fuskarsa.
Idanunsa ya d’an zazzaro waje, da tsananin mamaki al’ajabi hadi da tu’ajjudi, yake Kallon Barrister Kabir din, saboda zai iya yin rantsuwa cewar maganan da Barrister Kabir din ya fad’a, ta daki zuciyarsa sosai, Yayinda kuma ta rarraba masa tunaninsa zuwa wani waje na daban.
Rayyern dake zaune kuwa idanunsa ya rumtse da k’arfi, adai-dai lokacin da maganan Barrister Kabir din ta daki dodon kunnensa.
“Aure! Aure!! Aure kuma!!!” Abba ya fad’a cikin bayyana tsananin mamakinsa, saboda shidai zaice tunda yake bai tab’ajin anyi irin hakan ba, sai awasu k’asashen kamar India, koda ma kuwa anan din anayi to ya sani ba acikin zuriyar Hausa Fulani ba gidan mata suje nemawa yarsu auren gidan maza.
Barrister Kabir kuwa Kai ya jinjina, fahimtar da yayi kuma cewar sun yiwa maganan nasa wata kalar fahimta ne yasa asanyaye yace.
“Kuyi hakuri banzo da maganar dan yin kaina, ko kuma wani abu na daban ba, saidai halin matsalar da nake ciki da kuma wanda nake shirin fuskanta yasa nazo muku da wannan buk’atar, nasan bakusanni ba baku kuma San komai akaina ba, amma Idan har buk’ata ta bazata samu ba, Dan Allah kuyi mini alfarma na kawo Jannart gidanku, ku b’oyemin ita, ku bata kariya kuma ku zame mata Garkuwa, ta yanda baza’a tab’a sanin cewa tana nan ba, kamar yanda na fad’a muku a farko, Jannart Marainiyace, marainiya kuma wacce take tsananin buk’atar taimako, amatsayinku na y’an uwa musulmai Dan Allah kuyi min wannan taimakon, ku zama kariya ga Jannart!!”
Barrister Kabir ya kare maganar yana me had’e hannayensa duka biyu waje d’aya, alaman rok’o.
Wani irin doguwar ajiyar zuciya Abba ya sauk’e, tare dasa hannunsa ya dafe zuciyarsa, da ayanzu ta rage yawan harbawan da takeyi tun lokacin da yaji sunan Barrister Kabir, maida bayansa yayi ya jingina da jikin kujerar da yake Kai.
Idanunsa ya lumshe, Yayinda yake amsar duk wani tunani da ke yawo acikin k’wak’walwarsa, wanda kuma har yakeji tamkar zasu hautsuna masa k’wak’walwa.
Tabbas ayanzu duk wani nazarinsa ya tsaya cak.
Yayinda Rayyern kuwa dake can gefe, idanu ya tsurawa Abban nasa zuciyarsa na bugawa, saboda sam bayason Abban nasa ya aminta da maganar Barrister Kabir din.
Domin shi agaba daya rayuwarsa babu maganan wata Mace acikin tsarinsa, ba kuma yajin zai iya auren wata, balle kuma ya karb’i wani ajiya ji rainin hankali wai ajiya!? Kamar a garin gaɓa-gaɓa.
Abba kuwa kusan mintuna 5 kenan yanzu da ya nutsa acikin duniyar tunanin da yake.
“Lallai Wannan shine k’arin dama, abubuwa nata kusantowa, nesa na matsowa kusa, Yayinda haske ke shirin bayyana ya mamaye duhun duhuwan daya danne kekkyawan Tubalin da yake gine tun da dadewa.”
Abban ya fad’i hakan acikin zuciyarsa, adai-dai lokacinne kuma ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi.
Ajiyar zuciya mai karfi ya sauk’e, tare kuma da dawo da kallonsa ga Barrister Kabir dake zaune agabansa.
Kwarai ya aminta da shawarar da zuciyarsa ke basa, ya kuma yi Na’am da hakan domin akwai wani ƙulli a tsakani.
Numfashi me zafi ya fesar, cikin kuma yarda da kai hadi da gamsuwa yace.
*Littafin TUBALI na kuɗine dan girman Allah da Manzonsa da darajar iyayenku kada ku karanta min littafina in baku biyaba, 1k ko 500 da kika biya ko zaki biya kuma bawai kuɗin mallakan littafin bane, kuɗin samun damar karanta Littafin ne, kiya girman zatin ubangijin daya bamu rai da lfy, kada ku fitarmin da littafin, dan darajar Allah kada kuyi ta posting na littafina. Special Group 1k ƙaramin group kuma 500 yawan posting ne babbancinsu, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in ba halin turowa ta account ki sayi katin MTN ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp number na*
*”Ni Alhaji Bashir Abban Rayyern na amince da buk’atar da kazomin dashi Barrister Kabir, saboda haka na amincewa d’ana Auren Jannart!!” bisa tsarin Musulunci mu zamu nemi aurenta*
Tamkar rugugin tsawa asararin samaniya haka Rayyern yaji fitan kalaman Abban nasa, hakanne kuma yasa shi mik’ewa tsaye agigice, hankalinsa amatukar tashe yake Kallon Abban nasa baya ko k’yafta idanunsa, wanda lokaci daya sukayi jajur.
Barrister Kabir kuwa idanunsa ya lumshe, zuciyarsa cike da matsanancin farinciki, hadi da jin dadi marar misaltuwa, saboda tsabar farincikin da yaji acikin zuciyarsa ne kuma, yasa wasu irin hawaye suka gangaro kan fuskarsa.
Hannayensa ya had’e waje guda, tare dayin shiru Dan yama kasa sanin da wacce irin kalmace zai godewa Abban.
Rayyern kuwa da gaba d’aya jikinsa ya d’auki rawa, kansa ya soma girgizawa cikin, wata irin murya dake bayyana gaskiyar abunda ke cikin zuciyarsa yace.
“A’a Abba Dan Allah kada.....”
Saurin dakatar dashi Abban yayi, ta hanyar d’aga masa hannu, mai dauke da alamun dakatarwa, wanda kuma hakan shiya tilastawa Rayyern din yin shiru tare da haɗiye ragowar mgnarsa.
Idanunsa ya rumtse da karfi, tare da taune jajayen labb’ansa, haka yakejin kansa na wani irin juyawa, arayuwarsa kwata kwata bayason jin wata magana da ta shafi mata, Babu mata atsarin rayuwarsa, saboda ya aminta cewa, zai iya rayuwa ko babu Mace a kusa da shi, Domin ko a addinance Aure bai zama dolen dole ba, matuk’ar zaka iya kare kanka daga aikata Zina da fasikanci toh shi bai kawo mace a rayuwarsa ma bare wani abu ya kwashesa.
“Kabamu wuri!!”
Abban ya fad’a atak’aice fuskarsa babu alaman wasa ko wargi.
Idanunsa da sukayi ja sosai ya bud’e ya kalli Abban nasa, saidai kuma yanayin da ya gani akan fuskar Abban nasa, yasa shi juyawa cikin sauri ya nufi stairs din dazai sadashi da part d’insa, ransa amatukar jagule.
Barrister Kabir kuwa ganin Rayyern din ya tafi ne, ya sashi juyowa ga Abba.
Kansa ya d’an sunkuyar fuskarsa dauke da tsananin farinciki yace.
“Tabbas Alhaji Bashir kayimin halacci, kayi min abunda bakowane zaiyi minshi ba, nagode matuka na gode sosai da sosai, nagode Alhaji Allah Ubangiji ya biyaka ya sanya farinciki mai dorewa acikin ahalinka.”
Kai Abban ya d’an girgiza Barrister Kabir din, tare da cewa.
“Bakomai Barrister Kabir ai duk yiwa kaine, Fatana da kuma burina shine Allah yasa hakan shine sanadiyar kawo haske acikin rayuwar da gaba da bayanta ke dauke da duhu da kuma rashin sani.”
Kai Barrister Kabir din ya jinjina, batare kuma daya zurfafa tunaninsa akan maganan da Abban ya fad’a ba ya ci gaba da yi masa godiya.
Haka dai suka dauki kusan 30mn suna maganganu irin tasu ta manya.
Kafun daga bisani Barrister Kabir ya mik’e da niyar tafiya.
Har bakin kofar falon kuwa Abba ya rakosa, ba tare kuma daya tsaya yaga tafiyarsa ba, ya maida kansa cikin falon.
Juyowarsa cikin falon kuwa yayi dai-dai da fitowar Mamy dake cikin kitchine, wanda kuma tun d’azu take tsaye tana sauraran maganganun da suke fad’a.
Kallon Mamyn Abban yayi, Yayinda ita kuwa Mamy keyi mishi Kallon mamaki.
Fuskarta d’auke da damuwa sosai tace.
“Duk naji abunda kuka tattauna Alhaji, amma kwata-kwata banajin hakan dai-dai ne, tayaya zaka amincewa mutanen da baka sansu ba? Tayaya zaka dauk’o wasu daban ka sakosu acikin rayuwar mu? Wayesu mene hadinmu dasu, da har ka amince akan Rayyern ya auri y’arsu?”
Ajiyar zuciya mai k’arfi Abban ya sauk’e, kana Ahankali ya shiga takowa har zuwa inda take.
Batare kuma daya amsa mata duka tarin tambayoyin nata ba, ya kama hannunta kaitsaye suka nufi falonsa dake cikin main parlor din.
Koda suka karasa falon nasa kaitsaye bedroom d’insa suka wuce, still kuma har yanzu yana rik’e da hannunta.
Suna karasawa cikin dakin kuwa, ya maida kofar ya rufe tare da murzawa kofar key.
Numfashi ya d’an fesar, kana Ahankali ya d’ago Kai ya kalli Mamyn, wacce har yanzu takeyi masa Kallon mamaki.
K’asa-k’asa yayi da muryarsa, yadda yasan koda akwai wani adakin To bazai tab’a iya juyo abunda yake fad’a ba, sai ita d’in kawai.
“Kiyi k’asa-k’asa da muryarki Ruk’ayya, kinsan komai babu wani abunda baki sani ba, Dama ce ta samu, hakika naji ajikina cewar komai yana gab da had’uwa waje d’aya, da yardar Allah abubuwa suna ta had’uwa waje d’aya.”
Idanu Mamyn ta zuba masa cike da d’an d’aurewar kai, cikin kuma muryarta da yayi sanyi sosai tace.
“Har yanzu bangane abunda kake nufi ba, meke shirin faruwa ne?”
Ajiyar zuciya Abban ya sauk’e tare da sake rik’o hannunta da kyau.
Again kuma Cikin yin k’asa da murya yace.
“Kintuna Barrister Abdulkarim Saleh Dakata?”
Kai Mamyn ta jinjina, cikin sauri kuma tace.
“Natuna shi mana, har abada kuma bazan manta shiba.”
Kai Abban ya jinjina cike da gamsuwa, yace.
“To wannan bak’on da yazo wajena k’aninsa ne, shima kuma Barrister ne, sunansa Barrister Kabir Saleh Dakata.”
Idanu Mamyn tad’an zaro cike da tsananin mamaki, tace.
“Ikon Allah, Allah mai iko, mai kumayin duk yanda yaso, Lallai Tabbas kuwa na amincewa maganarka, Nesa na matsowa kusa, kuma haske zai bayyana Insha Allah.”
“Insha Allah kuwa.”
Abba ya maimaita cike da k’warin guiwa.
Acan b’angaren Rayyern kuwa...!
*GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*
Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.
Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.
Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.
GARKUWAR MA'AURATA
By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: In Sha Allah kuwa.
Abban ya maimaita cike da k’warin guiwa.
Acan b’angaren Rayyern kuwa, koda ya koma part d’insa, gaba daya kasa zaune yayi, Domin kuwa abubuwa da yawa ne keyi masa yawo acikin tunaninsa.
Direct kuma saman balcony d’insa ya koma, yana nan tsaye ne kuma yaga Barrister Kabir din ya fito.
Hakan yasa cikin sauri ya juya, tare da nufan falon k’asan nasu kaitsaye.
Koda ya fito falon, rashin Ganin Abba acikin falon Yayi masa dadi, wanda kuma hakanne ya bashi daman nufan waje kaitsaye.
Fitowarsa compound din gidan, kuwa yayi dai-dai da mik’awa Baba Maud’o hannu da Barrister Kabir din yayi.
Cikin aminci suka sake gaisawa, inda Baba Maud’o yace.
“Masha Allah har kafito zaka tafi, To mungode sosai a gaida gida.”
Murmushi Barrister Kabir din yayi, tare da cewa.
“Nima Nagode Baba.”
Dai-dai ya juya zai shiga cikin motarsa ne kuma, Rayyern ya k’araso wajen.
Kallon-kallo suka danyi da Barrister Kabir din, Yayinda Barrister Kabir din ke kallonsa cikin sakin fuska.
Shikuwa Rayyern yaken dole yayi, kana anutse yace.
“Har zaka tafi?”
Kai Barrister Kabir din ya jinjina masa alaman.
“Eh.”
Shikuwa Rayyern kaitsaye bud’e murfin motar yayi, b’angaren mai zaman banza ya shiga ya zauna.
Ganin hakanne kuma yasa Barrister Kabir yin murmushi, tare da bud’e murfin motar shima ya shiga ya zauna.
saboda Lallai yasan cewa akwai magana.
Yana zama kuwa Rayyern ya fuskancesa.
Cikin muryar dake bayyana gaskiyar abunda ke cikin zuciyarsa yace.
“Bansan me kake nufi ba, Bansan me kake nema da rayuwata ba, Bansan wani k’ulline kuke nufina dashi, kaida y’an uwanka da kuma abokan kasuwancinka akaina ba, inayiwa fuskarka kyakkyawan gani , da kuma kyakkyawan zato, amma why zakayi min haka? kayi min bayanin yarinyar, kuma na saka baki anbata taimakon daya kama ta a Hospital dina? To yanzu kuma me kuke nema awaje na? Meyasa dole saini zaku zab’a mainayi muku? Ina da yakinin Akwai dubbannin mutanen, da zasu iya taimaka muku akan matsalarku, bawai dole sai lallai niba, To Meyasa kuke son takuramin? Meyasa kuke bibiyata? Meyasa zaka zo da wannan maganan mai kama da tatsuniya? Wanda ko’a labarai ko a fina finai babu irin wannan al’amarin, ni nakan cire kaina acikin duk wani abu danasan babu ruwana, Meyasa kukeson sakani acikin abunda baidace dani ba??”.
Juyowa Barrister Kabir din yayi, ya kalli Rayyern d’in.
Domin kuwa acikin kalaman da yaji sun fito daga bakinsa babu wanda bai fahimta ba ya fahimci Rayyern yanayi musu kuɗin goro shi dasu Alhaji Idi Saleh Dakata dasu Dr Lukman da Abdu Tababa.
Ajiyar zuciya mai karfi ya sauke tare kuma da kamo hannun Rayyern d’in, cikin fuskantar juna yace.
“Rayyern! Rayyern ka yarda dani, Rayyern ka aminta dani, bazan tab’a cutar dakai ba har abada, wallahi babu cutarwa tsakanina da kai, saidai ina tsananin neman taimakon ka, Ina neman taimakonka.
Dan tsiratar da ran Jannart, Jannart marainiya ce, Dr. Rayyern ba zaka gane halin da nake ciki ba, ba ni kuma da isashshen lokacin da zanyi maka bayanin da zaka fahimceni, fatana ayanzu shine Jannart ta kasance ak’ark’ashin inuwarka, ba naso asan ma tana tare dakai, Domin Kuwa auren da zakayi da ita, Aurene na sirri, haka kuma aure ne da zai zamo auren manufa, Dan Allah Rayyern ka amincewa buk’atata, ko badan niba Kodan maraicin Jannart..”
*”Manufa? Auren manufa Wanne irin manufa kenan?”*
Rayyern din ya tambaya, yana me tsare Barrister Kabir da ido.
“Manufa saboda ceto Rayuwarta, da kuma manufar fidda gaskiyar da take b’oye tsawon shekaru ashirin da biyu.”
Idanu Rayyern din ya lumshe, akaron farko cikin kuma halin ko inkula yace.
“To ni meye had’ina da wannan? Meya shafeni da hakan?”
Ajiyar zuciya Barrister Kabir ya sauk’e.
Kana cikin sanyi yace.
“Baka da had’i dashi, amma kuma abad’inance kana da had’i dashi, Domin idan kataimaketa Allah Zaibaka lada, kuma kayi taimakon musulunci.”
Barrister Kabir din ya fada idanunsa na ciko da k’walla.
Lips d’insa ya cije, tare da sake rumtse idanunsa, cikin yanayin dake nuna Kosawa da da maganan yace.
“Har dai yanzu bangane inda komai suka dosa ba.”
Still ajiyar zuciya