Showing 57001 words to 60000 words out of 350584 words

Chapter 20 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

cewa.
“Oyoyo Ramadan Alhamdulillah”.
Sai kuma ya juya.
Da sauri Usman ya nufi inda Abba ke tsaye rusunawa yayi tare da gaidashi.
Cikin kula Abba yace.
"Usman kwana biyu shiru”.
Cikin girmamawa yace.
“Wlh kuwa Abba sai jiya muka dawo”.
Ya faɗi haka tare da juyawa ya kalli Ramadan dake miƙo mishi hannu.
Musabiha sukayi kana ya kalli Mamy cikin mutuntaka yace.
"Barka da yamma Mamy".
Barka dai tace tana mai nunawa Ramadan Fridge alamun ya kawo masa abin motsa baki.
Da sauri kuwa Ramadan ya nufi Dinning area juice and bootle water ya kawo mishi.
Kana yace.
"Yah Usman bari in haura sama in ɗan watsa ruwa”.

Toh yace.
Kana ya haura.
Shi kuwa Abba ne ya dawo tsakiyar falon.
Mamy kuwa abinci ta kawo mishi.
Kana ta nufi Bedroom ɗin ta.

Yanaci suna hira da Abba.

A can tahir hotel kuwa.
Riyyam-nsra ne zaune bisa kujerar dake gefe.
Video call yakeyi da Mammynsu cikin sauƙe numfashi yace.
"Alhamdulillah Mammy duk abinda muke zato hakane, wlh kuma duk abinda ya tsananta tsawon shekaru yana gab da sauƙaƙa.
Sai dai ta ina? Ta yaya? Da yaushe? Zamu fito da manufarmu ta yaya za'a fahimcemu?”.
Ido Mammynsu ta limshe sai ga wasu irin zafafan hawaye kana a hankali tace.
"Riyyam-nsra nima kaina bani da sanin tudun dafawa
Kuma zuciyata ta ƙara kwaɗaituwa da tsatsonta.
Ta ina? Ta yaya? Yaushe? zamu samu nasara".
Cikin ƙarfin hali yace.
"Mammy keda kike da Riyyam-nsra, kada ki damu ki bada yaƙinin ki a kaina in sha Allah zan kusanto miki da nesa kusa dake cikin aminci".

Yadda yayi mgnar with full confidence ne yasata sakin sassayan murmushi.
Riyyam-nsra akwai ƙarfin hali da yarda da kai, idon ta ita nema da bazaima je Nigeria'n ba amman bisa ƙarfin halinshi yaje.
Kai ta jinjina mishi tare da yin murmushi, ganin ya sata farin cikine yasa shi cewa.
"Ina Deeda tsohuwa da Zayton?”.
Cikin sanyi tace.
“Sun tafi asibiti".
Ya buɗe baki da nufin yin mgna kenan kuma wani kiran ya shigo ɗaya wayar tashi.
Da sauri yace.
"Yauwa Mammy sai anjima zamuyi mgn”.
Kan ta fargama ya katse kiran.
Kana ya amsa wannan kiran wanda shima video call ne.

Wata iriyar fitinenneyar miƙa yayi tare da zaro harshensa ya ɗan lashi lips ɗin shi.
Sabida gamo da katar da yayi da wata kekkyawar baby mai cikar haiba kalar Ethiopia'n Girl's
Tana mishi Ethiopia'n dance.
Wanda take jujjuya mishi ƙirjinta da karkaɗa mishi su da karya kafaɗu irin dai rawar su nan ta sai kaci ka ƙoshi kan ka iya yinsa.

Ido ta jujjuya mishi tare da tsagaita wa da rawar kana cikin yin ƙasa da murya tace.
"I miss you very very very so much sweetheart”.
A hankali ya miƙe ya koma bisa gado.
Idanunshi da suke juye sabida ganin ɗaya daga cikin abokan masha'arsa da suka haɗu sanadin TIKTOK cikin sanyi da kasalar wani irin masifeffen feelings da ya ziraro mishi kamar zai tsinke mishi jijiyoyin jiki yace.
"Nace muzo Nigeria kika ƙi, sannan kuma kina son tarwatsa min kwanya da begenki”.
Cikin iya shege ta zame wuyan rigar ta ta ɗanyi ƙasa dashi.
Kana tasa hannunta cikin rigar ta zaro mishi... Tare da cewa.
"Lollypop"....! Ɗaga nan sukaci gaba da lalatacciyar hirarsu, haka yasa Ramadan nata kira bai amsawa.


A can gidan Alhaji Idi Saleh Dakata kuwa.
Cikin hatsala Junaidu ya leƙo falon yana mai rabkawa Jannart kira kamar zai yage bakinsa.
"Jannart! Jannart!! Jannart!!!".
Ya ida kiran da ƙarfi wanda yasa.
Mom dake Kitchen ta leƙo cikin taɓe fuska tace.
"Menene kake ta ihun kiran wacce bata gidan ma, sai ka tafi gidan Abbanku ai”.
Kwaffa yayi tare da watsawa Mom ɗin harara kana ya nufi Part ɗin Abbansu dan sai yanzuma ya tuno cewa bata gidanma.

Yana isa bakin ƙofar falon.
Dr Lukman da Alhaji Abdu Tababa suna isowa suma da alamun yanzu suka iso.
So kusan a tare suka shiga.
A falon suka samu Daddy wanda dawowarshi kenan shima nan suka zauna.


A gidansu Rayyern Mai-nasara kuwa, Ramadan ne ya fito riƙe da foodflakcs mai kyau. Usman na bayanshi.

“Eh ba asibiti ba yake Campany ya tafi tun safe bai dawo bama”.
Ramadan ya bawa Usman amsa wanda ya biyoshi da nufin zasu tafi asibiti.
Numfashi Usman ya sauƙe tare da cewa.
"Toh ni kam bari kawai in wuce can inda yake ɗin”.
Toh yace kana shi ya nufi hotel ɗin da Riyyam-nsra yake.
Shi kuma ya wuce campany.

Yana isa da mai a dai-dai-ta sahun ya tsaida shi bakin gate ya sallameshi.
Kana ya shiga cikin kamfanin.
Mai napep ya juya.

Kasan cewar duk ma'aikatan wurin sun san PA duk wanda yasan Dr Rayyern Mai-nasara zai iya saninshi da PA hakan yasa kai tsaye ya wuce Office ɗin sa.

Cikin gajiya ya ɗago kansa ya kalli ƙofar Office ɗin da ake bugawa cikin sauƙe numfashi gajiya yace.
"Yesss coming".
Cikin nitsuwa PA ya turo ƙofar.
Numfashi ya fesar tare da meda bayanshi ya jingina da kujera tare da kallon Usman murya can ƙasa yace.
"Sai yau?”.
Murmushi yayi tare da cewa.
"Wlh kuwa sai yau fa".
Ya ƙare mgnar yana ƙoƙarin zama.
Sai kuma ya tsaya ganin uban gidan nasa ya miƙe tsaye.
Hannunshi yasa ya tattare system din ogan nashi da wayarshi kana yabi bayanshi dan tuni ya tafi.

Da sauri yabi bayanshi.
Bisa. libta ya hangoshi tanayin ƙasa dashi, da sassarfa ya mara mishi baya.

A haka har suka sauƙo hawa na biyu.

Suna sauƙa yayi maza yabi bayanshi ganin ya nufi hannun damanshi.

Tafiya mai ɗan tsawo sukayi kana suka isa wani wuri mai ɗauke da manya-manyan store's masu masifar girma da faɗin gaske.

Wanda sun kai goma sha biyu.

Gaba ɗaya a rufe suke tsayawa ya ɗanyi kana ya juyo ya kalli PA tare da cewa.
"Muje ƙasa".
To yace kana yabi bayanshi.
Suna sauƙa ƙasan kuma wasu stores ɗin suka samu kamar na sama.

Sai dai waɗannan su anata loda buhunan shinkafa shanshera ne buhu-buhu".
Kai ya gyaɗa cikin gamsuwa kana suka sauƙo ƙasa gaba ɗaya.
Inda suka nufi can gefen baya wani ƙaton hall ɗin cike da enginer's anata kafasu da haɗasu babu ƙaƙƙautawa.
Cikin nitsuwa yace.
"Lokacin salla yayi abar aiki aje ayi sallan la'asar”.
To sukace cike da jin daɗin kana suka bar aiyukansu.
Kana suka firfito.

Shi kuwa yayi gaba PA ya mara masa baya.

Suna isa parking lot Usman ya buɗe mishi mota gefen baya.
Kai ya jujjuya mishi kana ya shiga gaba mazaunin driver'n kana ya nunawa Usman gefenshi.
Yana son yayi tuk’i da kansa ne dan sanin akwai masu bibiyarsa.

Ana buɗe musu gate ya fita a nitse.
Karatun ƙurani ya saki sautin muryar Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Joɗa, (GARKUWA) Sassanyan sautinsa mai sauƙar da nitsuwa ya saki.
Kana ya saita hancin motar bisa titi ya fara takata a guje.
Dan so yake su samu jam'i sallan la'asar a Masallacin ƙofar gidansu.


Ana tada iƙama suna isowa.
Da sauri sukayi al'wala kana sukabi jam'i Allah yasa ba'a kere musuba.

Ana idar da sallan suka shiga cikin gida.
Tare da Abba da Baba Mauɗo, Hadi, Ari da Ramadan da Riyyam-nsra wanda suka juyo tare.

A bakin gate Usman ya zauna wurinsu Baba Mauɗo.

Su Ramadan kuwa a babban falon suka zauna.
Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara bayan Abbansu yabi har falonsu na ciki.
Gefenshi ya zauna tare da sauƙe numfashin gajiya kana ya kalli Abba dake cewa.
"Ya ka samu aiyu kan?”.
Cikin nitsuwa ya tonƙoshe sawunsa kana a hankali yace.
“Alhamdulillahi komai na tafiya dai-dai da izinin ubangiji.
Shinkafar nan ma da muka saya ta manoman Adamawa can wajajen Gurin ta iso, kuma shinkaface mai kyau da in ganci dan Jamila ce sai kuma mahanga kaɗan ita tafi kyau a barta a ɗaya.”



Uhumm yanzufa wasan zai fara daga PAGE din gobe.


*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*

NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.

Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.


Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.

Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike,

Kana duk ƙasar da kike zan iya aika miki kaya ta D.H.L amman yana da ɗan tsada,
in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA)*



By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*TUBALI*


PAGE 15
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

*FREE PAGE ne kuma suna gab da karewa*

*Baiwar Allah Hajia yan mata uwar gida, 🙏🏻😭 ROK’EKU DA GIRMAN ALLAH DA SOYAYYARKU DA MANZON ALLAH DA DARAJAR IYAYEN DA SUKAYI SANADIN ZUWANKU DUNIYA, DAN ALLAH KADA KI KARANTA MIN LITTAFINA IN KINSAN BAKI BIYA, DAN GIRMAN ALLAH DA ZATINSA DA RANA TA KARSHE DA MUKE TSUMAYI KADA KU FITAR MIN DA LITTAFINA DAN KUN BIYA 1K KO 500 WANNAN KUDIN KARANTAWA KUKA BIYA BA KUDIN MALLAKAR SA BANE, DAN ALLAH DA ISARSA BAYIN ALLAH KADA KU FITAR MIN DA LITTAFINA KADA KU KARANTA IN KUNSAN BAKU SAYABA🙏🏻🙏🏻😭😭😭😭 wlh duk wanda yamin hakan bazan yafe hakkina*

_Ki biya 1k in saki a special Group, ko kuma ki bada 500 in saki a ƙaramin group wanda bonus ne wa fans na kullum PAGE ɗaɗɗaya asalin kudin littafin 1k ne in gamashi in ya zama Complete 1kne. Turo kudin damar karanta Littafin TUBALI ta asusuna na GTBank 0661110170 AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 in ba halin biya ta account kuma ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp dina_


Kai Abba ke jinjina masa cikin tarin gamsuwa kana a nitse yaci gaba da cewa.
"Kuma mun samu al'kama aciki sosai kusan buhu dari bakwai”.
Gyara zama Abba yayi tare da cewa.
"Ita al'kamar ba duk stores din hawa na biyu ita bane, bazatayi yawa ba?”.
A hankali ya ɗan kalli Abba tare da cewa.
“A'a bazatayi yawaba Abba sabida abubuwan buƙatunta da yawa, ita za'a sarrafa ayi fulawa kana a juyata ayi Sufageti da makaroni da indomie sannan za'a barta ita ɗaya ma.
Kuma yanzu anfi ta'ammali da irin abincin kana zamu fidda buhunan don buƙatun cikin gida kamar su hidimar ababen biki da masu ƙananan sana'o'in duk suna buƙatar fulawar”.
Gyara zama Abba yayi fahimtar yana tare da gajiya da yunwa ne yasa shi cewa.
“Je kaci abinci kayi wonka zamu ƙarasa mgnar gobe da yamma”.
Kai ya gyaɗa kana ya miƙe ya fito.
Kai tsaye side ɗin sa ya wuce.
Wonka yayi mai rai da lfy ya shafa mai.
Kana ya zaro.
Wasu tattausan yadin voyel mai masifar taushi mai gidan dara-dara baƙi ne mai sheƙi ya saka.
Wanda yayi masifar mishi kyau farar fatarshi ta ƙara bayyana a ciki matuƙa gaya.
Wasu tattausan toms yasa Nevy blue masu masifar kyau kana ya kafa hular zanna bukar itama Nevy blue mai ratsin Black da royal blue.
Sajenshi ya konta lib sai sheƙi yakeyi tamkar yadin jikinsa fararen ƙananan kayan dake jikinsa suka ƙara haska kalar kayan inda ana iya ganinsu kaɗan ta dara-daran wani sassayan turarensa ya fesa.
Kana ya zari wayarsa ya zura a al'jihunsa kana ya nufo falon.
Cikin zumuɗi Riyyam-nsra yace.
"Wow Masha Allah, Hamma Rayyern dama haka kayan hausa fulani keyi maka kyau tubar kalla kai duk kayan da kasa sai sunyi maka kyau”.
Ya ƙare mgnar yana ƙoƙarin ɗaukarsa hoto.
Da sauri yasa hannunshi ya shafa ƙeyarsa lokacin da Rayyern ya ɗan ɗaka mishi mari cikin tura baki yace.
“Dan Allah ɗaya kawai”.
Bai kulashi ba.

Sai juya da yayi ya fuskanci Mamynshi,
hannunshi ya ɗaura kan cikinsa yana shafawa tare da kallon Mamy kana ya longobar da kai.
Murmushi Mamy tayi tare da miƙewa ta nufi Dinning table saninsa yasa ba sai yayi mgna ba take fahimtarsa.
Bayanta yabi yana kallon Ramadan tare da cewa.
"Me kakeyi a gida”.
Cikin tsoron kada ya korasa asibiti yace.
"Na gaji ne Hamma Rayyern kuma Dr Imran da Yah Sulaiman da Dr iley duk suna can”.

"Shine kuma yanzu Sulaiman yake cewa inje ana buƙata ta?”.
Kai ya ɗan shafa tare da fara inda-inda.
Shi kuwa tsaresa da ido yayi tare da nazartarshi kana a hankali yace.
"Kada ka zama maƙaryaci!”.
Da sauri yace to.
Wayarsa ce ta kuma ringing ganin Sulaiman ne yasashi miƙewa tare da buɗe Fridge Chocolate masu yawa ya ɗiba daskararru kana ya zaro goran ruwa da sauri haka yasa bai san wanda ya daskare ya ɗaukoba.

Cike da mamaki Mamy ta bishi da ido jin yana cewa.
"Mamy sai na dawo ana nemana a asibiti, Mamy abu mai ruwa-ruwa nake so in na dawo”.
Kai Riyyam-nsra ya jujjuya kana a hankali yace.
"Allah sarki Hamma Rayyern sam baya samun hutu, lokacin cin abinci ma rasawa yakeyi bawan Allah.
Dan Allah Hamma Ramadan muje ka tayashi”.
Kwaffa Ramadan yayi tare da dungure mishi ƙeya kana yace.
“Dan Allah Barshi shi baida wani uzuri sai aiki ni kuwa ina fama da uzurin soyayya.
taso mu tafi kaga Auntynka yaro”.
Ai kuwa da sauri ya miƙe.

Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara yana fitowa Hadi da PA suka miƙe.
Da sauri yace.
“Noh Hadi bari. PA mu tafi”.
Da sauri PA yace “Toh”. kana yabi bayansa.
Yana shiga motar yaja.
Hadi kuma ya buɗe musu gate, suka fita.

Saida suka fita sun hau titin da zai kaisu Mai-nasara Hospital ne ya ɗan miƙawa PA goran ruwan alamun ya buɗe mishi.
Amsa PA yayi tare da cewa.
“A daskare yake fa”.
Hannu yasa ya amshi gorar ya ɗan jijjiga tare da jan tsaki sam rabinsa duk a daskare yake.
Aje goron yayi kana ya ɓalle ledan Chocolate ɗinsa ya fara taunawa da yawa-yawa sabida azabebbiyar yunwar da yakeji.

A nitse ya zurawa motoci uku dake bayansu idanu.
Binshi sukeyi gadan-gadan kamar masu niyar takashi.
Da sauri yayi kwana ya shiga hannun damansa.
Ga mmkinsa sai gashi sun biyoshi a guje har na gaban na gab da buga mishi motarsa.

Cikin ransa yace.
“Okay!!!” sai kuma ya juya hagu da gudu.
Cikin nitsuwa yace.
"PA ko zaka sauƙa!”
Da sauri PA yace.
“A'a muje in ba matsala, naga motocin nan binmu sukeyi fa, ba halin tsayuwa”.
Kai ya gyaɗa mishi kana ya juya akalar motarsa dan canza hanya.
Sabida sanin ana buƙatarsa a asibiti in ba don hakaba zai tsaya yaji dasu.
So amman ganin duk inda yayi suna biye dashi kamar inuwa ne yasashi juya akalar motarsa kai tsaye titin da zai kaishi Jan bulo ya nufa.
Ganin haka ne kuma yasa motocin nan uku suka tsagaita da binshi.

Gaba ɗaya ransa ya hatsala ya tafasa sabida yadda suka sashi dole ya fasa zuwa inda akeda buƙatarsa da neman taimakonsa ya nufi inda baya son zuwa.
Wani irin masifeffen tsaki yaja tare


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login