Showing 123001 words to 126000 words out of 350584 words

Chapter 42 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

kallonsa, cikin kulawa yace.

“Rayyern fita zakayi ne.”

“Eh Abba”.
Ya bashi amsa a takaici.
Cikin tsaresa da ido Abba yace.
“Ina zakaje”.
Ya ƙare tambayar da alamun son cikekken bayani ina zaije me kuma zaiyi.

Hannunshi ya ɗan d’ago.
Tare da saidashi kan wuyanshi.
Ya ɗan shafa wuyanshi har zuwa kan ƙeyarsa kana a hankali yace.
“Inason zanje company ne, saboda P.A yamin waya, wai akwai wani inji da ba’a gane kansa ba, like dai baya aikin daya dace kana Engineer bello yana can yana jirana shima.”


Kai Abban ya jinjina, kana cikin gamsuwa yace.

“To Allah Ya bada sa’a.”

Da “Ameen.” Ya Amsa.

Barrister Kabir kuwa, ledan dake hannunsa ya mik’awa Jannart dake zaune akasa, cikin kulawa yace.

“Jannart ga waya nan na sayo miki, akwai new sim acikinsa, bayan number na kuma bansa miki numbern kowa ba, sannan kada ki fara amfani da laptop dinki yanzu, kina dai charging nasa amma kada ki yi using dashi,domin hakan zai taimaka wajen gujewa duk wani shaida.”

Karb’an ledan da yake mik’o mata din tayi, cikin jin dadi tace.

“Nagode sosai Abba Kabir Allah ya kara budi.
Amma fa jiya Abba ma ya sayamin sabuwar waya.”

Ta kare maganan tana meyi masa nuni, da Wayar dake hannunta.

Barrister Kabir din kuwa murmushi, yayi cikin jin dadi yace.

“Masha Allah waya tayi kyau sosai, Allah yasanya al'khairi ya kuma saka da alkhairin.”

Da “Ameen.” Duk suka amsa, saidai banda Rayyern wanda ya kawar da kansa gefe yana kallon Riyyam-nsra daketa lallatsa woya ya kifa kai har kamar zai hade goshinsa da wayar haka yasa ya tsareshi da ido yana nazartarsa.
Dan ko kasa inda take dinma bai kalla ba sai dai yana jin amon muryarta.

Barrister Kabir kuwa Mikewa tsaye, yayi tare da Kallon Jannart din, cikin tausasa murya yace.

“To Jannart ni zan wuce, dama sakon da nazo kawo miki kenan.”

Murmushi Jannart din tayi, cikin sanyi tace.

“Abba ka gaida gida, ka gaishemin da Aunty Dijat dasu Hafeeza.”

“Zasuji Insha Allah.” Abban ya fad’a, tare da juyawa yayiwa Mamy sallama.

A gaida gida Mamyn tayi masa, sannan suka fice shida Abba.

Ganin hakanne kuma Yasa Rayyern ma mik’ewa tsaye.

“Rayyern katsaya kayi breakfast tukun kafun ka fita, gacan abinci akan dining.”

Cewar Mamy tana me kallonsa.

Fuskarsa ya d’an ya mutsa, tare da Kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa, adan kasalance yace.

“Mamy banajin yunwa sosai, kuma Idan na tsaya break zan makara, saina dawo kawai ki ajiyemin lunch.”

Ya k’are maganan yana me nufar hanyar fita daga falon.

Wanda hakan yasa Mamy da Ramadan suka Bishi da kallo, Mamy kuwa har cikin ranta tana mamakin, yanda Rayyern din yake tafiyar da rayuwarsa, gaba daya sam cin abinci bai damesa ba sai dai wasu lokuta isasshen lokacin zaman cinnema yake rasawa, shiyasa idan ya tara yunwar tofa in ya samu ya ya zauna zaici da dama.

Rayyern kuwa Koda ya fito compound din gidan, ya samu tuni harsu Abba da Baba Maud’o sun tafi, Yayinda shima Barrister Kabir Yayi nasa tafiyar.

Motarsa ya shiga, Yayinda Hadi ya jasa suka fice daga Cikin gidan.

Acan falo kuwa, har Rayyern din ya fice Jannart bata iya sake dago Kai ta kalleshi ba, saboda tun Kallon farko da tayi masa, taji zuciyarta na bugawa, wanda kuma batasan dalilin hakan ba.

Bayan fitan nasa ne kuma ta d’ago kanta tare da Kallon Mamy, ad’an ladabce tace.

“Mamy yau me zamu dafa da rana.”

Murmushi Mamyn tayi, kana atausashe tace.

“A’a Jannart yau kam kihuta, ina nan zanyi komai, basai kin wahalar da kanki ba wannan fa aiki nane!!!.”


“Mamy ba wahalar da kai bane zanyi, na saba ko agida ma duk ranar da babu aiki Ina taya Momy duk wasu aikace-aikace gida, Dan Allah Mamy ki bari Ina tayaki ki dena cewa na bari.”

Jannart din ta fad’a cikin tausasawa.

Hakanne kuwa yasa Mamy jin sanyi acikin zuciyarta, saboda tasan Itakam tayi sa’ar suruka.

“Shikenan Jannart babu damuwa, na baki wuk’a da nama ki dafa mana duk abunda kikeso.”

Mamyn ta fad’a cikin sakin rai.

Riyyam nsra kuwa, cikin dokin cin abincin Auntyn tasa yace.

“Yauwa Aunty Jannart muje kitchine din, ni yau da kaina ma zantayaki aikin, amma mezaki dafa mana me dadi haka?”

Murmushi Jannart din tayi, tare da cewa.

“Muje zaka gani.” Yanayin yanda tayi maganan tana me mikewa tsaye ne, yasa Riyyam din rufa mata baya suka shiga kitchine.

Shida kansa yayi mata wanke wanke, Yayinda ita kuwa tayi greetting kwawa, saboda abunda ta tsara zata dafa musu shine.
Coconut rice, and onion sauce, sai kuma gas meat mai kayan kamshi, da salad cream, ab’angaren drinks kuma, Banana Milk shake zatayi musu.

Anutse ta fara aikinta, Yayinda Riyyam keta yi mata hira, daga gefe guda kuwa yana tayata da y’an wasu ayyukan, kama daga kan yanke yanke zuwa yan kananun abubuwa masu sauk’i dai.

Haka dai sukayi aikin cikin nutsuwa, almost 1hour kuwa ta kammala komai, tare da jeresu akan dining table.

Gaba d’aya gidan kuwa haka ya gauraye da kamshin girkinta.

Bayan sun kammala jere komai a dining table dinne kuma, ta kunna boner tare dasa turaren wuta mai dadin kamshi.

Mamy kanta ta yaba da aikin Jannart din, bayan sunyi sallan azahar ne kuma, suka zo kan dining table din sukaci abincin.

Saidai kuma Jannart din bata wani ci abincin sosai ba, ayanda Mamy ta fahimta kuwa shine, Jannart din irin Rayyern ce, kwata kwata basu dauki cin abinci serious ba sai dai tasan shi Rayyern in ya zaunawa abincin bai mishi da wasa ko dan yakan dade baici bane, ta lura ita kuma Jannart irin mutanen ne da zasuci kaɗan yanzu anjima su kuma cin kaɗan.

Bayan sun kammala cin abincinne kuma suka dawo falo, hira suka Dan tab’a, lokacin da Ramadan da Riyyam suka fita yawo ne kuma, Jannart ta tashi ta koma side dinta, tana kwanciya afalonta kuwa bacci ya dauke ta.

A can gidan Alhaji Idi Saleh Dakata kuwa.
A gajiye ya dawo gida, daga Tashar Arewa 24 TV da yaje, yanzu ya samu MD da kansa ya mishi bayanin ɓacewar Jannart da kuma hukuma da suka shiga lamarin kana yasa gidajen Rediyo su cekinta su kuma ya bawa gidan tv nasu cekiyar gaggawa.
Daga nan kuma asibitin Dr Lukman ya wuce inda anan sukayi tattaunawa mai yawa kana ya nufo gida.
Da sauri Mom tabi bayanshi.
Tana cewa.
“Alhaji anji lbrin Jannart kuwa?”.
Da sauri ta matsoshi ganin yadda ya dafe kanshi da hannaye bibbiyu yana mai jujjuya kanshi.
Kana ya tafi lu alamun zai fadi.
Cikin tsananin tashin hankali da kidima Mom ta saki ihu tare da isowa gareshi ta tallabeshi murya na rawa take kwarmawa Abdul kira.
da gudu Abdul ya shigo cikin tashin hankali tace.
“Abdul kira min Barrister Kabir Abbanku kace Daddynku ba lfy”.
Kafin ta ƙare mgnar kuma Alhaji idi Saleh Dakata ya sake gaba ɗaya naushin ya jata suka tafi kasa bisa carpet.
Ganin haka ne yasa Abdul gigicewa tare da zaro wayarsa ya kira Barrister Kabir.
Wanda shi kuma lokacin ya fito daga gida shi kenan.
Koda Abdul ya gaya masa abinda ke faruwa.
A firgici ya dauko ya wuce asibitin Dr Sajo ya dauko shi.
A gidan Alhaji Idi Saleh Dakata'n kuwa, suna cikin gigin suka jiyo muryar Dr Lukman yana sallama hakane yasa Mom sakin dogon numfashi tare da cewa.
“Dr ka shigo, kayi sauri shigo ka taimaka mana Alhaji zai fadi”.
Jin hakane yasa Dr Lukman kutsa kai cikin main falon nasu da hanzarin.

Daga nan shida Abdul suka tallabeshi suka a mota suka wuce asibitin Dr Lukman din.

Suna tafiya ba jimawa.
Barrister Kabir da Dr Sajo suka iso.
Bayan Ashiru ya musu bayanine suka nifi asibitin Dr Lukman ɗin.


A nan gidansu Rayyern kuwa.

Bacci Jannart tayi sosai dan Koda ta tashi tayi sallan la’asar sake komawa tayi ta kwanta.

Ahaka dai har magriba.


9:30 pm dai-dai ya shigo gidan, wanda kuma tun fitan da yayi da safe sai yanzu yake shigowa.

Da sallama abakinsa ya tura kofar main falon ya shigo.
Jin da yayi ko ina shiru babu alaman motsin kowa ne, yasa kaitsaye ya wuce sama, saboda yasan zuwa yanzu su Mamyn nasa sunyi bacci.

Yana haurawa saman kuwa, anan cikin falonsu ya samu Ramadan da Riyyam, ko wannensu rungume da waya ba abunda sukeyi sai chatting.
Kana ga TV a kunne tashar Arewa 24 TV.
Yayinda su basuma san me akeyi a TV'n ba.
A hankali ya ɗan juyo ya kalli TV'n sabida ganin program ɗin da Jannart tayi dashi ake haskawa.
Idanunshi ya zubawa rubutun dake tafiya kasan hotonsu mai motsin da yake fuskar TV'n.
*Daya daga cikin ma'aikatan wannan ma'aikata Mai gabatar da shirin Baƙon mako mai suna Jannart idi Saleh Dakata ta bata tun daren jumma'a, kana har yau babu ita babu lbrin ta, a madadin tashar Arewa 24 TV muna cekinta Tata ga duk wanda Allah yasa ya ganta ko yaji lbrinta, ya taimaka ya nemi ɗaya daga cikin wadannan numbers din... akwai tukuici mai girma ga duk wanda ya kawo ta ko lbrinta kimanin Naira million 5. Muna addu'a Allah ya baiyana ta ya kuma bawa mahaifinta lfyar jikinsa wanda sanadin batanta ya tada masa ciwonsa*
Wani irin numfashin ya fesar a hankali tare da mai-maita karanta rubutun a karo na barkatai.
Can cikin zuciyarsa yake nazari.
“Tabbas akwai gadar zaren da ake sakawa, wanda ake neman mai ruftawa a ciki.
Dole suna da manufa a kaina.
Amman manufar Barrister Kabir tafi ta kowa girmama a kaina, tabbas ba haka kawai ya zaɓeni ya lika min wannan mayataccen aurenba, nasani haƙƙun nasan akwai wata boyeyyiyar manufa da niyarsa ta liƙamin auren ya kawo diyarsu ya ajiye mana a cikin gida.”
Idonshi ya lumshe tare da buɗe kana yaci gaba da nazari.
“Wani wasane suke son bugawa dani, yarsu ta zamo yar leken asirinsu kenan itace zata basu duk wata damar cimma nasarar turani kan gadar zaren da suke saƙamin ko meye.
Itace mai iya buɗe musu kofa ta su shigo rayuwata.
Meyasa Abba na bai gane hakabanba ya akayi Abba na yayi saurin yarda dasu?”.
Numfashi mai nauyi yaja ya sauƙe tare da yin kwaffa.
Wanda sanadin hakane su Ramadan suka gane ya shigo.
Kallonsu kawai yayi tare da amsa sannu da dawowan da sukeyi masa.
Idonshi ya kuma maida kan TV inda ake haska fuskarsa data Jannart.
Batare daya ce musu komai ba, ya wuce zuwa dakinsa.

Yana shiga ya soma rage kayan jikinsa, tare ci gaba da nazari.
“Me Barrister Kabir yake nufi dani? Alhaji idi Saleh Dakata dai ɗan uwansa ne uwa ɗaya uba ɗaya.
Kana ita kuma wannan Jalila ne ko jalilu ne, yarsa ce ta cikinsa.
Haƙƙun Barrister Kabir medani tsanin hawa yake son yi!.”
A hankali ya tura ƙofar shiga toilet.
A fili yace.
“Me yasa Abbana ya yarda dashi, ya akayi yayi saurin gamsuwa dashi.
Bayan kuma shine ya dauramu kan turbar kebanta kai da mutane da gudunsu da rashin yarda dasu.
Sanadin haka muka taso ba abokai ba kawaye bama sakin jiki da kowa, daga ni har Ramadan, sabida horaswar Abbanmu ta gudun mu'amala da mutane,
Yasha cemin.
Rayyern ɗan adam abin tsorone kada ka yarda da kowa, mutun duhun darene Allah kadai ke saninsa!
To ya akayi yayi saurin yarda da Barrister Kabir?
Tabbas shima Abba na akwai manufar yardar sa”.
A hankali ya ɗago ƙafarsa ta hagu ya sa cikin Bathroom din.
Hannunshi duka biyu yasa ya matse kanshi da ƙarfi.
Dan yadda yakejin kansa na jujjuyawa nazarurrukansu na hautsinewa suna haɗe zaren suna curkudeshi.
Duk da azabebben sanyin da akeyi.
Ruwan sanyin ya sakarwa kansa.
Sabida jin kan nashi ya fara sarawar.

Bayan ya fito ne kuma, ya shirya kansa cikin wasu tattausun kayan bacci.
Wondon iya guiwa rigar irin mai hular nan.
Fridge d’insa dake cike da kayan ciye ciye ya bud’e, Apple goran swan water da kuma ledan diary milk ya d’auko.

Tare da komawa kan gadonsa ya zauna cikin sanyi yace.
“Ta yaya zan yarda da ita, a wani sashin ma zan ajiyeta bayan nasan ita ɗin makamin magautanane sun turora cikin rayuwata ne dan cin nasarar kansu a kaina.
Meyasa Abba na bai fahimci hakaba.
Itama da mugun nufinta a ranta fa, iyayenta zatayiwa aiki”.
Yayi mgnar yana mai ajiye Jannart a sashin da yake ajiye magautansa a cikin zuciyarsa da rayuwarsa da waɗanda yake zargi.

A hankali ya jujjuya kansa.
Kana ya ɗan gatsi apple din ya soma ci bayan ya gama ne kuma, ya daura chocolate d’insa da ruwa akai.
Numfashi ya ɗan fesar
Kana ya kwanta yana mai nazari.


A nan asibitin Dr Lukman kuwa.
Barrister Kabir ne da Mom ke zaune gaban table ɗin Dr Lukman.
“BP'nsa ne ya hau sama sosai, sabida tashin hankali rashin yarsa.
Kana kuma rashin baccin da baya samun yi, sai nazari da damuwa yasa zuciyarsa ta kumbura.”
Dr Lukman ya ƙare mgnar yana mai yin ƙasa da idonshi sabida wani irin tsareshi da ido da Barrister Kabir yayi.
Cikin zubda hawaye Mom tace.
“Innallahi wa innailaihi rajiun, zuciyarsa kuma ta kumbura?”.
Cikin murje ido yace.
“Hakkun kuwa, sabida damuwa tayi mishi yawa, Jannart ta bata kana shima Junaid yana hannun hukuma, wanda kuma ƙaninsa uwa ɗaya uba ɗaya yasa aka kama ɗan nashi da wanne abu ɗaya zaiji?”.
Cikin haɗe fuska Barrister Kabir yace.
“Shine yace ma ni na kai Junaid hannun hukuma?”.
Da sauri ya girgiza kai alamun a'a
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
“Toh ka tsaya iya matsayinka, ka tabbatar da abu kafin kayi mgn”.
Yana faɗin haka ya mike ya fita.

Dakin da aka kwantar da Daddy ya nufa a bakin ƙofar shigowa yayi kiciɓis da Dr Sajo.
Hannunshi Dr Sajo yaja kana suka juya suka nufi parking lot.
Cikin motar Dr Sajo suka shiga.
Wani dogon numfashi Dr Sajo ya sauƙe kana a nitse yace.
“Dr Mina da Dr Lukman yayi aikin duba Alhaji tare da ita, ƙanwatace cousin sister na.
Na samu duk bayanin komai a wurinta”.
Da sauri Barrister Kabir yace.
“Dan Allah menene gskyan abun dake damun Yayana?”.
Kai Dr Sajo ya jinjina tare da yiwa Barrister Kabir duk abinda Dr Mina ta sanar masa...

A nan Office din din Dr Lukman Kuma Barrister Kabir na fita, itama Mom ta fita.
Ta koma wurin mijin nata.

Ba ji mawa Barrister Kabir ya dawo akan dole a sallami yayanshi zasu sauya asibiti.
Kuma dole haka akayi.
Aka medashi asibitin Dr Sajo.

Washegari.

Kamar dai jiya yaudinma Jannart ce ta-taya Mamy duk wasu aikace-aikacen gida, bayan sun kammala ne kuma suka zauna suna dan tab’a hira.

Kasan cewar yau Monday ne tushen aiki.
Yasa tuni Ramadan ya tafi.
Riyyam-nsra kuma Ahmad yazo sun tafi gidan Malam Mai-nasara.

Takwas saura kwata. Ya sauko falon.
Cikin shigar Suit red color masu masifar kyau.
Hannunsa riƙe da wayarsa yana mgn.

Cikin sauri ya kalli Mamy tare da cewa.
“Mamy na tafi”.
Kafin ma tace wani abu tuni ya nufi hanyar fita.
Kawai sai ta bishi da ido.
Har ya fita kuma sai ya juyo ya leƙe fuska ya kwaɓe tare da cewa.
“Mamy na tafi”.
Murmushi tayi dan dama tasan tabbas zai juyo muddin batace mishi.
Allah ya bada sa'a yayi muku al'baka.
Cikin sauri ya kuma cewa.
“Mamy zan tafi”.
Fuska ta tsuke tare da cewa.
“Ka dawo kayi breakfast”.
Cikin kwaɓe fuska yace.
“Mamy sai na dawo, kinga Ramadan keta kirana, wai akwai matar da aka kawo haihuwa yaƙi kuma dole sai anyi mata CS, dan Allah Mamy ce Allah ya bani Sa'a yayi min al'barka Please Mamy say something".
Ta sani in dai yace bazai ciba ko ta matsa mishi bazaici yadda take sonba.
Hakane yasa tace.
“Toh Babana Allah ya bada sa'a ayi aiki lfy rabbil yayi maka al'barka”.
Da sauri ya juya yana mai cewa.
“Yessss Mamy Amin Amin”.

Da ido ta bishi tana murmushi tana tuno wasu abubuwa masu tarin yawa.


Jannart kuwa dake cikin Kitchen tana wonke-wonke rumtse idanunta tayi tana mai jin yadda bugun zuciyarta ke harba a duk sanda sautin muryarshi ya sauka kan kunneta.
Duk da bata hangoshi ba, ita robonta da shima tun jiya da safe zuwan Barrister Kabir nanma bataga fuskarsa ba, kuma haka yanzuma.

Sai dai yanayin alaƙarsa da mahaifiyarsa yasata jin maraicin rashin tata mahaifiyar da jin bege.
Domin a gidansu babu irin wannan tarbiyar shaukin mahaifa da Kekkyawar shaƙuwar.
Haka dai taci gaba da aiki ita da Mammynsu.


Alhamdulillah komai yana tafiya dai-dai, domin Jannart ta samu nutsuwa acikin gidan.

Kasancewar yau tsawon kwananta biyar kenan da zuwan ta gidan.

Akullum kuma sabonsu k’ara-k’arfi yake, da Mamy, Ramadan da kuma Riyyam, harma kuma Abba da take samun kulawa awajensa sosai ta kuma take jin daɗin zama dasu.
Takan kalli Mamy matsayin Mom da Aunty Dijat dan duka biyu ta meye mata gurbinsu.
Abba a matsayin Daddy kana Riyyam-nsra ya meye mata gurbin Abdul Ramadan kuma gurbin Yah Azeez yayinda tasa a ranta cewa wato duk inda kake a duniya sai ka samu kalubalen makiyin dan gashi nanma Rayyern ya zame mata gurbin Yah Junaid a cewarta kenan.

Acikin kuma way’annan kwanki biyar din, sau biyu tak kawai Jannart da Rayyern din suka ga juna.

Tun gaisuwar da tayi masa ranan farko kuwa, wata magana bata sake hadata dashi ba tunda bazai amsa mataba a zatonta bazata kara gaidashi ba Dan matsalar kunneta yasa bataji amsawar da yayinba.


Rayyern kuwa kasancewar yau laraba, tun sassafe ya fita, saboda akwai wasu patients da suke da appointment din ganinsa.

Bashi ne ya dawo gidan ba kuwa sai 2:00 pm, inda ya tsaya yayi sallan azahar d’insa a Darul Hadith Masque.

Yanzun kuwa Shigowarsa Cikin gidan kenan, hannunsa rike da suit dinsa, ya murda handle din kofar falon ya shiga bakinsa dauke da sallama.

Mamy dake zaune ne ta amsa masa.

Ganin kuma yanda yake da'alaman gajiya atattare dashi ne yasa ta zuba masa ido.

Shikuwa k’arasowa cikin falon yayi, tare da zama akan kujera, idanunsa ya lumshe, kana cikin sigar shagwab’a da bayyanar tarin gajiya da yunwar dake cinsa yace.

“Mamy nagaji, kuma yunwa nakeji sosai.”
Ya ƙare mgnar yana juya kwayar idanunshi da sukayi jazir.
Ido Mamy ta dan zuba mishi cikin tausayawa tace.
“Badole kaji yunwa ba Babana, kwata-kwata bakason cin abinci, saika wuni ka kwana batare da kasa abincin kirki acikin ka ba sai kayan zaki da Fruits.”

Mamyn ta fad’i haka tana me K’are masa kallo, saboda har wani dan rama taga yayi, saboda rashin cin abincin da bayayi akai akai dan abin nashi ya karune tun zuwan Jannart gidan.

“Kazo kaci abinci.”
Mamyn ta fad’a cikin kulawa.

Shikuwa Rayyern idanunsa ya d’an bud’e akasalance yace.

“Mamy me aka dafa.”

“Coconut rice, with onion sauce, gas meat, and salad cream, sai kuma milk shake, and plaintain da kuma fish.”

Mamyn ta bashi amsa atakaice.

Fuskarsa ya d’an kwab’e, tare da rausayar da kansa gefe, cikin sanyi yace.

“Shike nan Mamy ku kullum abu ɗaya.
Kwananfa naga shi kukayi kukayi taci ba sauki”.
Da sauri tace.
“Yoh ya mana daɗi Ramadan da Riyyam-nsra sukace a sake yinshi, nima kuma naji daɗinsa”.

Cikin tarin gajiya yace.
“Mutane ayi ta sasu tsatsagar shinkafa ba sauki kamar tsuntsaye.
Gsky ni bazan ciba,
abu mai dan ruwa ruwa nakeso, banason abinci mai nauyi.”
Jujjuya kai Mamy


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login