Showing 150001 words to 153000 words out of 350584 words

Chapter 51 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

damanshi.
Bottega ya faɗa a hankali kana ya ɗan kaikace ya zaro katinshi, ya miƙawa PA tare da cewa.
“Shiga ka saya mana, ni pizza ma ya isheni,kai kuma ka sai abinda kakeso, ka sayawa wannan ma.”
Ya ida mgnar yana nuna masa Driver'n'sun.

Toh yace, ya amsa kana ya bude ya fita.

Jim kaɗan ya dawo riƙe da ledodi.
Kana ya shiga suka tafi.

Bayan kwana biyar ya gama har had’a komai, ya kimtsa kayansa kana ya kaisu Airport, dan yana son kayan su rigasu tasowa.

Yau ta kama satinsu biyu cur da zuwa.
Yau ne kuma jirgin kayansu ya tashi sai dai ta Lagos zai sauƙa.
Daga can kuma ya wuce Kano.

Kasan cewar yau ɗin Lahadi ne, shine a.lissafi kuma sunyi kwana goma sha huɗu.

Tunda safe yayi musu order’n abinci ta online a Frongji Restaurant, kasan cewar komai nasu da tsari, yasa Delivery available ne ko yaushe.
Kuma free delivery ne, cikin abinda baifi 40 minutes ba sai gashi sun kawo musu har ƙofar dakinsu.

Jin ana buga ƙofar ne yasa.
Ya ɗanyi miƙa daga kwancen da yake, ido ya ɗan rumtse sabida kartawar da yakeji cikinsa nayi masa tun daren jiya.
A hankali ya yunƙura ya taso jin anci gaba da bugawar, ya sani bazai iya cin komai ba, sai dai yayi musu order ne sabida PA.

A hankali ya miƙe tsaye sai dai ya kasa ida miƙewa zat, sabida yadda yaji cikinsa na tsananta ciwon in ya gwada tsayuwar, hannunshi yasa ya dafe cikin, kana ya fara taku a hankali.

PA kuwa dake falon kasan cewar ya fara yin bacci ne, yasa toh sai yanzu yaji bugun da sauri.
Ya miƙe tare da nufar ƙofar yana buɗe wa.
Ma'akkacin Halal Frongji restaurant, din ya miƙa masa ledodin hannunsa kana ya juya ya fita.
Sabida dama yayi musu transfer'n kuɗin su.

Yana juyowa ne kuma ya hango Rayyern ɗin yana fitowa daga cikin Bedroom din.

Ido ya zuba mishi ganin a ɗan sunkuye yake tafiya, kana yana dafe da cikinsa da hannun damanshi, da sauri ya nufo gareshi, cikin kulawa da fargaba yace.
“Sir lfy kuwa?"
Cikin rumtse idanunshi ya zauna bisa kujerar dake gefenshi.
Ba tare daya buɗe idonba murya a hankali yace.
“Usman ƙara gudun AC'nnan”.
Da sauri Usman ya juya, ya ƙara gudun ACn kana ya dawo inda yake.

Cikin kulawa yace.
“Sir cikin ne?”
Lip ɗinsa na ƙasa ya taune,
tare da ƙara rumtse idanunshi kana a hankali ya miƙe kan kujerar,
baya son yin mgn sabida ko numfashin ya fesar sai yaji wani irin masifeffen ciwon cikin ya karu.
Ido P.A ya zuba mishi ganin lokaci ɗaya wata iriyar fitinenneyar zufa ta keto mishi tako wanne hudan gashin jikinsa.
Duk da sanyin garin da kuma na'urar take busawa.

Gaba ɗaya hankalin Usman ya tashi sunkuyowa yayi kansa cikin tsananin tsoron kada dai ciwon cikin nasa ne zai tashi yace.
“Hamma Rayyern ko zamu tafi asibiti ne?”.
Cikin sanyi murya can ƙasa yace.
“P.A kaci abinci”.
Ya ƙare mgnar da ɗan ƙarfi alamun baya son mgnar.
Shi kuwa P.A a hankali ya ɗan ja da baya cikin taraddadi yace.
“Toh tashi muci.”

Da sauri ya buɗe idanunsa da tuni sun gama rinewa sunyi jazir sabida ciwo.
A faɗace yace.
“Dan Allah ka zauna kaci abinci.”

Jin hakane yasa P.A aje ledodin kana shima ya zame ya zauna a wurin.

Shi kuwa Rayyern juyawa yayi ya kwanta a kife.
Tare dasa hannunsa duka biyu ya dafe cikinsa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani'imanwakil, la'ila ha illa'anta subahanaka innikuntu minazzalumin”.
Waɗannan sune yaketa maimaitawa a hankali, yadda P.A ma bayaji kana ya matse cikin yayi shiru.

Hakan ne yasa hankalin P.A ya ɗan kwanta,
har ya samu yaja abincin ya fara ci.
Yanaci yana juyowa yana ɗan kallonsa.
Haka dai har ya gama ci.
Kana ya tattare wurin.

Sannan ya wuce ɗakin kwanansa ya ɗauko wayarsa, kana ya fito falon.
Dakin Rayyern ɗin ya wuce,
Woyoyinsa ya dauko duka biyu kana yazo ya zauna kusa dashi.

Zuwa lokacin kuma cikin ya ɗan lafa,
hakan yasa Ya buɗe idonshi ya kalleshi a hankali yace.
“Me zakayi da waya?”
Da sauri ya kalleshi tare da cewa.
“Dama zan kira Ramadan ne ko Dr Sulaiman in gaya musu halin da ake ciki.”
Tsareshi da ido yayi, hakan yasa yayi shiru.
Hannun ya miƙa masa ya amshi woyoyin kana a hankali yace.
“Kada ka faɗa musu domin zaka tada musu hankali, kuma in nayi Sa'a haka zai keyi yana lafawa har ya bari, so kada ka gaya musu”.
Cikin yanayin rashin gamsuwa yace.
“Okay Sir”.
Shi kuwa a hankali ya miƙa ya tsaya tsakiyar tamfatsetsen falon na al'farma.
Kana ya nufi ɗakinsa.
Kai tsaye Bathroom ya wuce.
Wonka yayi kana ya fito.

Wasu tattausan riga da wondo yasa Pink panther masu sheƙi.

Kana ya gyara labulayen sannan ya ƙara ac sannan ya kashe wutan ɗakin ya dawo ya kwanta.

A nan gida Nigeria kuwa.

Bayan sallan isha'i Abba ne
Zaune bisa kujera, Ramadan na gabansh, Yayinda Mamy ke gefensu.

Jannart da Riyyam-nsra kuwa suna can main falon suna kallon wani India'n Film a zee world.

A Karo na barka tai Ramadan ya kuma gyara zamanshi,
Abba kuwa ido ya zubawa TV kamar yana gane me sukeyi.
Yayinda Mamy kuwa ta zuba musu ido.
Cikin kwaɓe fuska da shogobe fuska Ramadan yace.
“Uhum Abba dama..”
Sai kuma yayi shiru.
“Dama me?”
Abba ya tambaya ba tare da ya kalleshi ba.

Cikin sanyi yace.
“Eh dama gidansu Rayhana ce, sukace in tura”

A fakaice Abba ya kalleshi tare da cewa.
“Ka tura me?”
Kamar zaiyi kuka yace.
“Wai in tura manya na ayi mgnar aure in da gaske nakeyi, dan su gidansu daga yarinya ta gama Secondary School bazataci gaba ba, sai an aurar da ita taci gaba a gidan mijinta, to gashi ita Rayhana har taci gaba sabida, batun Hamma Rayyern baiyi aureba, shine sukace toh ai yanzu dai yayi auren sai ayi batun namun ko?”

Ya ƙare mgnar yana kallon iyayen nasu.
Mamy kam kai ta kauda tana mamakin zalama, irin ta Ramadan sam baya iya ɓoye maitarsa akan san aure.
“Wannan dai anyi jarabebben yaro”
Ta faɗa cikin ranta
Abba kuwa numfashi ya ɗan fesar tare da cewa.
“Toh su sukace ko dai kai kace?"
Da sauri yace.
“Su”
Kallonshi yayi tare da cewa.
“Banbancinka da Rayyern kenan Ramadan, kai kakan ɗan taɓa ƙarya shi kuwa duk ɗacin gsky zai faɗeta, yanzu da shine cewa zaiyi shine ya faɗa”
Da sauri yace.
“Toh Abba nine na faɗan.”
Mamy kam dariyar dake cintane ta dan subuce mata.
Ido ya ɗan zuba mishi kana yace.
“Wato kai dai ayi maka aure kake so ko?”
Da sauri yayi ƙasa da kansa.

“Toh ba damuwa tashi kaje zamuyi mgn da Baba Mauɗo.”

Wayyo Ramadan kamar ya mutu dan daɗi ai da sassarfa ya fito.
A falo ya tsaya kusa da Jannart cikin happy yace.
“My Aunty ki shirya kun kusa kai kayan aure.”
Da sauri Jannnart din tace.
“Kai haba dai iye, lallai kam abin nema ya samu kenan matar ma tsunci ta haifi kogi.”

Riyyam nsra kuwa Jujjuyawa yayi tare da cewa.
“Eh matar falke ta haifi sanda,
kai lallai akwai casu a ƙasar Kano”
Sai kuma suka bishi da ido jin ya kira Rayhana ya fara mgn da ita ya haura sama.
Murmushi Jannart tayi tare da cewa.
“Kai Riyyam wai kai baka gajiya da rawane?”
Dariya mai sauti yayi tare da cewa.
“Nida Hamma Rayyern duka ƙugunmu kamar roba yake Bama gajiya da karairayashi”
Harara ta ɗan cilla mishi tare da cewa.
“Ji sharri”.
Da sauri yace.
“Wallahi kuwa my Aunty”.
Cikin hararan wasa tace.
“A'a wlh kada kayi mishi sharri, wannan kuma da son jiki ma abu kaɗan ya kama raki yaushe zai iya jujjuyawa kamar yadda kake”

Dariyar Mamy da suka jine yasa, Jannart miƙewa da sauri ta nufi ɗakinta cike da kunya.
Ita kuwa Mamy tafiya takeyi tare da cewa.
“Gskyarki dai kare mijinki diyata”

Shima Riyyam dariya yayi tare da cewa.
“Aifa kam tana kareshi.”

Nan dai sukaci gaba da hira.

A can China kuwa gaba ɗaya wunin ranar a daki Rayyern yayi shi.
Koda ruwa bai sa a bakinsa ba,
sabida matsa mishi da cikinsa yayi duk bayan 10mnt sai ya lafa na tsawon 10mnt ɗin kana ya sake tashi.
Salla kwai ke tadashi, shima sai in ya samu ya lafa.

P.A kuwa haka ya wuni zirga-zirga a kansa.

Dare nayi kuwa ciwo yace Assalamu alaikum.
Ya tashi gadan-gadan.

Shi kuwa P.A yayi baccin gajiyan zirga-zirgan, da yayi yau din.

“Ya ilahi ya mujibadda'awati.”

Sune kalaman da bakinshi ke iya furta wa, yayinda gaba ɗaya jikinshi ke wani irin masifeffen karkarwa,
zuface take keto mishi tako ina tamkar wanda ake watsawa ruwa.

Juyi yakeyi a kan gadon yana mai yin duk wata addu'ar da tazo bakinsa.

“Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Yayi addu'ar cikin wani irin azabebben numfashin, da yake ja tamkar ransa zai bar gangar jikinsa.
Kar-kar haka jikinsa ke rawa, so yake ya jawo wayarshi ya kira asibiti, amman ina ya kasa hakan sabida ko numfashinsa, in yaja kamar zai suma haka yakeji, cikin ya kulle yayi wani irin tauri da zafi.

A hankali ya mirgino dan matsowa zai jawo wayarsa, cikin akasi ya ture woyoyin duka biyu suka fadi ƙasa daga kan bedside drower.

Dai-dai lokacin kuma yaji cikin nasa yayi wani irin damƙa mai cike da azaba.
Wani irin duhune ya rufewa ganinsa.
A hankali yaji kamar gadon na jujjuyawa dashi...


P.A kuwa yanata baccinsa, sai asuba ya tashi, alwala yayi bayan ya fito yayi sallan asuba.
Sabida ganin kamar ya ɗan makara yasa Rayyern yayi ta tadashi kenan bai tashi ba.

Yana idawar ya fito falo.

Shiru ya tsaya tsakiyar falon.
“Bai tashi ba, ko ya fitane, bari in duba dai?”
Yayi mgnar zuciya yana mai nufar dakin.

A hankali ya dan ƙonƙosa kofar.
Shiru ba alamun mgn haka yasa ya kuma bubbugawa yana mai kiransa still shiru.

Dan tura ƙofar yayi tare da sallama a bakinsa.

Cikin yanayin firgici ya zaro ido tare da nufo kan gadon, sabida hango Rayyern ɗin da yayi a yashe bisa gadon tamkar matacce.
Cikin kidima ya haura gadon tare da ruggumeshi yana jijjigashi da kiran sunanshi da ɗan ƙarfi.
“Sir! Sir!! Sirrrrrr!!!!".
Ya ida kiran da ƙarfi cikin tsananin tashin hankali, domin gaba d’aya jikinsa ya sake yayi sanyi tamkar wanda ya mutu, sai iya cikinsa ne yake da ɗumi.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani'imanwakil Hamma Rayyern tashi".
Gaba ɗaya jikinsa rawa da karkarwar yakeyi.
Cikin tsananin tashin hankali ya debo ruwa ya yayyafa mishi amman ina.
Haka yasa ya buɗe ƙofar ɗakin ya fita da gudu.
Sauka kasa yayi.

Jim kaɗan sai gashi ya dawo da ma'aikatan hotel ɗin.
Kana da Driver'n' taxi.
ID card din Rayyern ya nuna musu.
Tare da Receipt's din kayayyakin da suka saya da kuma takardun Campany da matsayin nasa companies din da kasan cewarsa likita.
Haka yasa da sauri sukasa hannu suka ciccibeshi suka sauƙo aka sashi a mota, P.A ya shiga tare da jan marfin ya rufe kana Driver'n yaja.


Daga nan kai tsaye
Puhua International Hospital and clinic (PIH) Suka nufa.

A cikin motar kuwa cikin tashin hankali P.A ya kira. Dr Sulaiman yana ɗagawa yace.
“Dr Usman P.A ke mgna”.
Cikin kaɗuwa Sulaiman yace.
“Yesss na gane meke faruwa ne Usman”.
Murya a karye yayi mishi bayanin abinda ya faru ya ɗaura da cewa.
“Yanzu haka yana sume gamu a hanyar zuwa asibiti, yauwa gashi ma mun iso”
Yayi mgnar ganin sun shiga cikin asibitin.

Suna yin parking nurses Suka nufosu.
Da irin wannan gadajen ganin Ambulance ce kuma da tambarin hotel ɗin a jiki.
Suna isa driver'n na buɗe musu.
Da sauri P.A ya fito yayinda Sulaiman ke ce mishi.
Ina kun isa ka haɗani da Doctor ko nurse, duk wanda ka samu kana kada ka gayawa su Abba sai ya farfaɗo kaji ko Usman”.
Da sauri yace to kana ya fito.

Daurasa sukayi a kan gadon kana suka nufi Emergency room.
Yayinda tuni likitoci suka rufawa Nurses din dake tura gadon baya.

Da sauri P.A ya miƙawa daya daga cikin Nurses din wayarsa.
Ƙarawa a kunne tayi.
Kai take ta jinjinawa jin cikekken bayanin matsalarsa, haka yasa da sauri ta miƙa babban Doctor'nsu wayar.

Sosai Sulaiman yayi mishi duk bayani, wannan yasa suka fara bin matakan bashi taimakon gaggawa.
Bayan ya bawa nurse din wayar ta dawowa P.A da ita.

Wasa-wasa kusan awa uku ba'a fito da shiba,
hankali P.A yayi matuƙar tashi.
Sulaiman kuwa ya kirashi yafi sau goma.
Sosai shima ya karaya jin shiru ba'a fito da shi bane.
Yasa yace.
“P.A kira Ramadan ka gaya masa halin da ake ci, ni gsky abin ya bani tsoro”.

Cikin karaya P.A yace.
“To.” kana ya katse kiran.

Number Ramadan ya kira.
Shi kuwa Ramadan lokacin duk suna falon, sun gama karyawa kenan.
Kasan cewar jiya a asibiti ya kwana shiyasa yau zai wuni a gida duk da Monday ne.

Jin wayarsa na ringing ne ya kalli Jannart, dake kusa da wayar inda ya sakalata a caji.
“Waye ne”. Ya tambaya.

Dan leƙa fuskar wayar tayi tare da cewa.
“P.A ne”
Haka nan sai yaji zuciyarsa ta tsinke.
Mamy ma haka abin yake gareta.
Sai suka zubawa wayar ido gaba dayansu.
Riyyam-nsra ne ya ɗan jujjuya ya kallesu.
Yayinda sai kuma yace.
“Hamma Ramadan ka amsa mana”.

“Miƙo min wayar”.
Yace yana kalloshi
Da sauri ya miƙo masa wayar bayan ya amsa kira na biyu.
“Hello P.A ya akayi ne?”
Cewar Ramadan.

P.A kuwa Murya a sanyaye yace.
“Ramadan Hamma Rayyern ba lfy ciwon cikinsa ya tash...”

Da sauri duk suka juyo suna kallon Ramadan din daya miƙe tsaye yana cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun, hasbunallahiwani'imanwakil,
P.A, ina yake? Wanne hali yake ciki? Kuna ina yanzu? Bashi wayar!"

Gaba daya Ramadan din ya gigice.

Jin abinda yake faɗa ne kuma yasa Mamy miƙewa, jiki na rawa take cewa.

“Menene Ramadan meya faru da Rayyern? Ina yake bani wayar”.

Juyawa yayi cikin yanayi tashin hankali jin P.A na cewa.
“Muna asibitine Ramadan, a sume muka kawoshi tun safe, kuma har yanzu bai farfad’oba, nima kaina ban san halin da yake cikiba”

“Yah ilahi ya mujibadda'awati”.
Ramadan ya faɗa murya na rawa.
Mamy kuwa da sauri ta nufi side ɗinsu tana cewa.
“Abban Rayyern, Rayyern! Rayyern!!!”.
Da sauri Abba ya miƙe ya nufo kofar falon su.

Riyyam-nsra kuwa a main falon.
Gaba ɗaya jikinshi rawa ya fara.
Yayinda Jannart kuwa take binsu da kallo.
Shi kuwa Ramadan bin bayan Mamy yayi yana cewa.
“Abba Hamma Rayyern ciwon cikinsa ya tashi, tun jiya da dare yana sume har yanzu bai farfadoba, Abba ya zamuyi.”
Da sauri duk suka tsaya cirko-cirko a tsakiyar falon.

“Kira min P.A maza bani wayar”

Cewar Abba haka yasa Ramadan sake kiran P.A.
Bayanin da yayiwa Ramadan din shi yayiwa Abba.

Tashin hankalin da ba'a sa masa rana.
Jannart kuwa shiru tayi tana kallon Riyyam-nsra daya kira Mammy a waya yana gaya mata abinda ke faruwa yadaura da cewa.
“Mammy kiyi masa addu'a'n samun lfy kin san addu'arki gareshi bata da hijabi, Mammy yana cikin tsananin hali wuya bakiga yadda ciwon ke wahal dashi ba kamar zai ɗauke mana ransa”.
Ya ƙare mgnar murya na rawa hawaye na zuba.

Ita kam Jannart abubuwan sun raunata-ta.
Domin ganin hawayen Riyyam.
Dan ita haka Allah yayi idonta muddin taga hawaye idon wani to nata zai zubo, dan irin idon GARKUWA ne fareta.
Haka kuma tana da rauni abu kaɗan ke sata hawaye.
Bare kuma wannan al'amarin da tasan yana masifar sasu cikin tsananin tashin hankali.
Sautin muryar Abba tajiyo cikin rauni yana cewa.
“Rukayya ki dena yi mishi kuka, addu'arki yafi buƙata, Ramadan tashi maza dauki E-passport dinmu, Ka fara mana shirin tafiya.”
Ya ƙare mgnar suna fitowa main falon a jere.
Yayinda shima idanunsa sunyi jazir alamun tashin hankali.

Waje ya nufa.

Mamy kuwa zamewa tayi ta zauna bisa kujera hawaye na shatata tace.
“Yah Allah kaji tausayin wannan bawa naka, ka jikanshi ka yaye masa wannan azabar ka bashi lfy.
Ya Allah ka zama gatansa a kasar da ba ta saba bashi da kowa sai kai ya Allah”
Cikin raunin murya da sanyi ido na ciko da hawaye Jannart tace.
“Amin ya Allah, Mamy ki dena kuka kici gaba da yimishi addu'a”.

Riyyam ya kalli Ramadan da ya sauƙo yanzu da E passport a hannunsa.
Da sauri Riyyam yace.
“Hamma Ramadan bazakayi muku booking ta online ba ai yafi sauki.
Ka duba ka gani ina za’afi samun jirgin China da wuri Abuja ko Lagos kaga baka da nitsuwar yin tuƙi”.
Da sauri Jannart tace.
“Eh hakanfa zaifi”.

Hakan kuwa shi yasa Ramadan komawa zaune jiki, a mace ya fara bincike kan sifirin jiragen sama na kasa da kasa.
Cikin sa'a kuwa ya samu akwai jirgin zuwa China ta Abuja nanda kwana biyu.

Haka yasa ya fara hidimar neman visa nan take a wurin yayi komai.
Sabida yanzu duniya ta zama a tafin hannu.

A can harabar gidan kuwa.
Gaba ɗaya hankalin Baba Mauɗo yayi matukar tashi da jin wannan lbrin.
Hadi da Ari ma jikinsu yayi sanyi.

Suna nan Sulaiman ya shigo.
Bayan sun gaisane ya kalli Baba Mauɗo cikin kulawa yace.
“Ba komai fa, ya farfaɗo P.A ya ganshi ma, sai dai sun hanashi shiga dakin da yake”.
Toh abunka da nesa in kaji baka gamsuwa in ba gani kayi ba.

Koda suka shiga cikin gida.
Nan yayi ta kwantar musu da hankali.
Haka dai suka wuni a ranar da zulumi bini-bini su kira P.A.

Washe gari ma hakan suka wuni.
Toh da Yamma Ramadan ya tafi Abuja.
Dan Sulaiman da P.A sunce ba sai Abban yaje ba.
Tafiyar Ramadan yasan gidan ya ƙara zama shiru kamar ba mutane.

P.A kuwa shima har yau bai ganshi ba.
Sai da dare ne da ya sake zuwa asibitin sai gobe da safe yazo.
sunce ya koma masauƙinsu ne a cewarsu ma'aikatansu ke kula da maralafiya.


Ranar da Ramadan yazo Abuja da dare washe gari da safe.
Jirginsu ya daga zuwa kasar China.

Gab da magriba jirginsu Ramadan ya sauƙa.
Daga Airport ɗin kai tsaye Puhua International Hospital din yace mai taxi ya wuce dashi.
Cikin sa'a kuwa suna zuwa bakin gate din P.A na fitowa.
Nan ya sallami mai taxi shida PA Suka nufi ciki.
“Kayi sauri P.A ta ina zamu bi? Ya jikin nasa? Yana mgn?”.
Ramadan ya jerowa Usman tambayoyin.
Cikin sanyi Usman yace.
“Ko munje bazasu barka ka ganshi ba, amman sunce gobe da safe zamu ganshi. Sai dai in nuna maka dakin da yake ciki kawai."
Hakan kuwa akayi duk da kasancewar Ramadan likita basu barshi ya shigaba sabida wai ƙare a gidansa zakine.

Dole suka koma masauƙinsu.
Usman din yayi musu order'n abinci.
Bayan sunyi wonka sunyi sallane.
Suna cin abinci Ramadan ya kira Abba wanda lokacin suna tare da Baba Mauɗo nan ya ɗan ƙarfafa musu guiwa.
Kana ya kira Riyyam yace ya bawa Mamy waya.
Toh sun danji sanyi dai.

Washegari

Ƙarfe takwas dai-dai ta samesu tsaye a bakin dakin da Rayyern ɗin ke ciki.
Wanda yau kwana shi uju kenan a na hudu.
Bayan Doctor ya fitone.
Ya kalli Ramadan tare da cewa ya biyosa Office nasa.
Haka kuwa akayi.

P.A kuma yana tsaye a wurin
Tsawon kusan ,35mnt kafin Ramadan ya dawo jiki a mace.
A hankali yace.
“P.A mu shiga”.
Da sauri P.A ya mara masa baya.

Suna shiga suka hangoshi can kwance kan gado.
Lumshe ido Ramadan yayi sai ga wasu hawaye masu zafi sun zubo mishi.
Sabida tausayin Hamman nashi.
Shi kuwa Rayyern cikin yanayin mamaki yake kallon Ramadan tare da buɗe baki a hankali yace.
“Ramadan yaushe kazo”.
Hawaye na zuba yace.
“Jiya nazo Hamma Rayyern”.
Cikin tausayawa P.A yace.
“Sir ya jikin?”.

A hankali yace.
“Alhamdulillah”.
Ina hawaye Ramadan sun gaza tsayuwa, sabida ganin wani irin masifeffen rama da Hamman nashi yayi.
Cikin nan a ɗakale tamkar babu hanji a ciki.
Ya rame yayi fiyau.
Yayi wani irin sanyi ko mgn a hankali yakeyi.
“Abba ya gaisheka da jiki


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login