Showing 63001 words to 66000 words out of 350584 words

Chapter 22 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

Kabir din ya fad’a yana me.
Kallon Yayan nasa, wato Alhaji Idi Saleh dakata, cikin matsanancin tashin hankali.

Shima kuwa Alhaji Idi Saleh Dakata'n tashin hankali ne, kwance akan fuskarsa, cikin yanayin rud’ewan da yayi, ya kalli Dr Lukman dake tsaye, tare da cewa.

“Dr. Lukman ka duba mana ita dan Allah.”

Jin hakanne kuwa yasa Dr Lukman dake tsaye, d’an matsowa kusa dasu,
dan duba Jannart din, wacce ita yanzu bata masan duk wata Waina da ake toyawa acikin gidanba.

Idanu Barrister Kabir ya d’ago tare da watsawa, Dr Lukman din muguwar harara, cikin kuma yanayin fushi da tsananin b’acin rai yace.
“Kada kayi kuskuren tab’a min y’a.
Domin kuwa na jima da sanin muguwar cutar da kakeyi mata ta karkashin k’asa.”

Cak Dr.Lukman din ya tsaya, tare da matsawa gefe batare kuma daya karaso wajen ba, saboda jin abunda Barrister Kabir din ya fad’a.

Barrister kuwa sungumar Jannart din yayi, kaitsaye kuma cikin sauri ya nufi hanyar fita daga cikin gidan.

Da hanzari kuwa maigadi ya bud’e masa dan madaidicin kofar dake jikin gate din gidan ya fice.
Koda ya fito kuwa murfin motarsa na gidan baya ya bude, tare da tura Jannart din ciki ya kwantar da ita.

Batare kuma daya jira komai ba, ya zagaya ya shiga b’angaren driver, ahanzarce ya tada motar, tare kuma da cillata kan titi, kaitsaye yabi bayan motar Dr Rayyern Mai-nasara dake ta sharara gudu, akan shumfud’add’en titin kofar gidan daya mike santa yana mai jin jijiyoyin kansa na tsananta harbawa sabida ihu da hayaniyar da akayi tayi a kanshi .

Shi kuwa Barrister biye dashi yake a hamzarce.
Wanda kuma yayi hakanne saboda sanin matsayin Rayyern da yayi, na likita zai iya taimaka musu.

Yayinda ab’angaren Rayyern kuwa tuk’in motar yake, yana maijin wani irin b’acin rai acikin ransa, badan komai ba kuwa saidan b’ata masa rai da lokaci da akayi agidan Alhaji Idi Salte Dakata, Tabbas yasan cewar.
Koda ace yaje asibitin nasa yanzu, babu wani abu da zai iya aikatawa, Domin yafi kowa sanin kansa Idan ransa na b’ace baya tab’a iyayin komai, koda ma kuma ace yayi din bisa dole, to abun bazai zama hundred percent yanda yake so ba ga kuma alamun ciwon kansa da yake ji.

Y’ar k’aramar tsuka yaja, tare kuma da d’an buga kan steering motar tasa, kaitsaye ya sanja akalar tafiyar tasa, inda ya saki hanyar asibitin nasu daya kama, direct ya shari kwana tare da hawa kan titin da zai sa dashi da gidansu.

Ganin hakanne kuma yasa P.A d’agowa ya kalleshi, kamar zaice wani abu kuma saiya fasa, saboda yasan halin maigidan nasa, da yawan lokuta bayason adameshi da yawan magana.

Barrister Kabir dake bayan su Rayyern din kuwa, shima gudu yake shararawa, still kuma har yanzu yana mebin ba yansu, sai-dai duk bayan mintuna kad’an yana juyawa ya kalli Jannart dake kwance flat agidan baya, babu alaman numfashi ko d’igo ajikinta.
Wanda hakan kuwa shi yake k’ara sanya Barrister Kabir din acikin tashin hankali.

Tafiyar da bata wuce ta 30mn ba sukayi, isowarsu wajen wani jection ne kuma yasa, Usman P.A d’an d’ago kai ya kalli Rayyern din.
Sake Kallon bayansu Usman P.A din yayi, still kuma ganin motar da tun d’azu yake ankare da ita, na binsu abayane , yasa shi d’an muskutawa cikin kuma yanayin mamaki yace.

“Sir kaman fa binmu wannan motar dake bayanmu takeyi.”

Idanu Rayyern din ya d’aga, tare da maida kallonsa ga madubin motar wanda yake haska musu duk abunda ke bayansu.

Tabbas shima ya lura da motar, saidai kuma bai d’auki hakan amatsayin wani serious abuba, batare kuma daya tankawa Usman P.A ba, kaitsaye ya hau kan titin daya shigar dasu layin gidansu.

Suna isa bakin gate din tamfatsetsen gidan nasu ne kuma, barrister Kabir ya taka wani irin birki.

Wanda kuma hakan yayi dai-dai da tsayawar motar Rayyern din shima, cikin kuma zafin nama da zafin ciwon kan sa yakeji ya bud’e murfin motar ya fito, saboda duk atunaninsa Alhaji Idi Sale Dakata ne, bai daddara da gargadin daya yi masa ba, ya sake turo masa wasu mutanen dan su bibiyeshi.

Fitowarsa daga cikin tasa motar ne, kuma yasa Barrister Kabir fitowa shima cikin hanzari, kuma ya nufo Dr. Rayyern d’in.

Muryarsa na rawa yace.

“Dan Allah Dr. Rayyern ka taimakamin, kada Jannart ta rasa ranta, Dan Allah ka taimakawa rayuwarta, wlh itace kaɗai babbar *HUJJATA,* ita kad’ai ce Hujjar da zan nuna anan gaba, please ka taimaka min!!”
Barrister Kabir din ya fad’i haka cikin tsananin tashin hankali, da kuma muryarsa wacce take fitar da sautin kuka.

Dr. Rayyern din kuwa Jin amo da kuma sautin, muryar Barrister Kabir din dake fita cikin kuka ne, da kuma amo mai shiga kunne, yasa shi rumtse I danunsa, tare dasa hannunsa na dama ya dafe kansa, dake wani irin sarawa, dan lokaci daya yaji kaman ana buga masa gudu ma a tsakiyar kannasa, abu na farko da bayaso arayuwarsa shine, yi masa magana cikin sigar kuka da kuma d’aga murya, sannan kuma aduk sanda wani ya buk’aci taimako afujajan awajensa, ya kanji zuciyarsa ta karye.
Balle kuma Barrister Kabir din da yake ta had’ashi da sunan Allah.

*Inama ace makaranta zasu kasance kamar Dr Rayyern in an had’asu da Allah zasuyi abu ko zasu bari, dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenku idan Free PAGE ya kare kada ku fitarmin da littafina, in kinsan kin sayane dan ki fitar dan Allah ki gaya min in meda miki kuɗinki Dan girman Allah da tsarki littafinmu akwai karami. Group 500 ne kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 ko ki sayi katin MTN ki copy edin ki turo min ta WhatsApp*

“Usman!”
Rayyern din ya kira sunan Usman P.A da wata irin murya.
Jin amo da kuma sautin muryar Rayyern din cikin wani irin yanayi na dabanne kuma yasa, cikin sauri Usman ya fito, tare da k’arasowa yana Kallon Ogan nasa.

“Ka kaishi hospital Usman kacewa Sulaiman ya duba patient din, please kuje Usman kutafi daga nan please.....”

Rayyern din ya fad’i hakan, cikin wani irin yanayi marar dadi dayakejin kansa aciki, tare kuma dasa hannayensa duka biyu ya kama kansa.

Usman kuwa fahimtar halin da Ogan nasa ke cike ne yasa shi, saurin kallon Barrister Kabir.

Ahanzarce yace.
“Muje na rakaku hospital dinsa akwai Doctor's zasu dubata in sha Allah zata samu lfy.”

Ko jiran abunda Barrister Kabir din zaice kuwa baiyi ba, ya bud’e murfin motar barrister din, nan b’angaren mai zaman banza ya zauna.

Ganin hakanne kuma yasa Abba Kabir din shima komawa cikin motar, a 360 ya murzawa motar key tare da cillata kan titi, kaitsaye suka nufi asibitin Mai-nasara Hospital, saboda dama Barrister Kabir din yasan asibitin.

Ganin sun miki hanyar asibitinne kuma yasa Usman P.A ciro wayarsa ya dannawa Dr Sulaiman Kira.

Bugu biyu kuwa Sulaiman ya dauki wayar, bayan sun gaisa ne kuma Usman P.A ke fad’awa Sulaiman din cewa.
“Gamunan a hanyan Mai-nasara Hospital zamu kawo emergency patient, bisa umarnin Dr Rayyern.”

Da “to.”
Kawai Dr. Sulaiman ya amsa, Yayinda shi kuwa Usman P.A ya katse kiran.

Rayyern kuwa da har yanzu ke tsaye abakin, motar tasa hannayensa duka biyu yasa ya cigaba da rike kansa dake sarawa.
Jin da yayi cewar bazai iya jurewa tsayuwar bane, yasa shi nufar gate din gidannasu, koda ya isa jikin gate din, hannunsa ya daura akan y’ar karamar kofar dake jikin gate din, tare da tura ta ciki.

Baba Maud’o dake zaune abakin kofar dan Part ɗin sa, yana me sauraran radio ne ya d’ago kansa, saboda ji da yayi an tab’a kofar shigowa gate din.

Aikuwa yana d’aga kansa ya sauke idanunsa akan Rayyern, da har yanzu yake dafe da kansa da hannuwansa duka biyu.

“Rayyern!!!”
Baba Maud’o ya kira sunansa, cikin yanayi na mamaki da kuma zallar damuwa.

Batare kuma daya bari Rayyern din ya amsa masa ba, ya d’aura da cewa.

“Subahanallah Rayyern maiya sameka? Lafiya kuwa? Meke damunka? Bugewa kayi akan naka ne? Ko kuwa wani abune ya same ka?”

Baba Maud’o yayi masa duka tambayoyin cikin bayyana tsananin damuwarsa.

Shikuwa Rayyern da ayanzu, yakejin idanunsa sun fara yi masa nauyi, kai kawai ya iya girgizawa Baba Maud’on, batare kuma daya iya cewa komai ba, kaitsaye ya wuce cikin gidannasu.

Hakan da yayi dinne kuwa yasa Baba Maud’o, Jin wani iri acikin zuciyarsa, take kuma damuwa maitsananin yawa ta bayyana akan fuskarsa, saboda ya sani ba karamin abubane zai sa Rayyern din dawowa acikin irin wannan yanayin, Lallai akwai abunda yake damunshi.

“To kodai awajen aikin nasa ne aka bata masa rai? Kodai kuma ciwon kansa ne?”

Baba Maud’o yayiwa kansa tambayar da bashi da mai amsa masa ita, sai Rayyern din.

Ganin da yayi zancen zuciya bazai kaishi bane kuma, yasa shi dan bud’e kofar gidan ya lek’a waje, ganin motar Rayyern din da yayi fake akofar gate dinne kuma yasashi saurin fitowa, tare da leka cikin motar, ganin akwai key ajikin motar ne kuma yasa, da kansa ya wangale makeken gate din, tare da dawowa ya shiga cikin motar, da kansa ya shigo da motar ciki, saboda a lokacin shi kad’aine ya rage agidan, Hadi driver da kuma sauran masu bawa flowers ruwa duk basanan.

*Dan Allah da Manzonsa idan free PAGE sun kare kada ku fitar min da littafi, ina rokon nanne da yakinin duk Musulmin kirki mai cikar imani da sanin darajar Allah da Manzonsa da darajar iyayensa nasan bazai fitarmin da shi ba, ko ya karanta na watan*


Rayyern kuwa Ahankali yake tafiya, yana me d’an jujjuya kai tare kuma da rumtse idanunsa, da yakejin sunyi masa matukar nauyi.
Isowarshi jikin kofar da zata sadashi da babban falon gidanne kuma, yasa shi d’aura hannunsa akan handle din kofar.

Dai-dai lokacin kuwa Abba da Mamy ne ke zaune acikin falon da alamun tattauna abu mai mahimmanci sukeyi.
Inda Abba ya d’ago kansa ya kalli Mamy, cikin yanayin yin ƙasa da murya da alamun tsawatarwa yace.

“Kinsan abunda yake bunne, wanda kuma har yanzu bamu shirya tono shi ba. Meyasa kikeson ki bada kofa da abubuwa da yawa zasu iya wakana ba tare da mun shirya musuba.
Wannan sirrin mai karfi ne da cikar rauni, Tono shi kuma dai-dai yake da tsayawar bugun zuciyar wasu mutanen, musamman Rayye......”

Sauran maganan dake bakin Abban ne kuwa, suka mak’ale, asakamakon jin motsin bud’e kofar falon da akayi,
Wanda hakan yasa cikin sauri duk suka maida kallonsu ga bakin k’ofar.

Ganin Rayyern din da sukayi dafe da kai ne kuma, yasa duk suka mimmik’e,

“Rayyern lafiya kuwa?”
Abba ya tambaya hankalinsa atashe.

Kai Rayyern din ya d’an girgiza musu, batare daya ce komai ba, kuma ya k’arasa shigowa cikin falon, tare da nufan kan 3 seater, din leather cushion dake Cikin falon ya kwanta.
Still kuma hannayensa ya sake maidawa duka biyu ya rik’e kansa.

Al’amarin daya sanya hankalin su Abba da Mamy matukar tashi kenan.
Da sauri Abba ya k’arasa inda Rayyern din ke kwance, hannunsa ya d’aura akan Rayyern din, cikin muryar dake bayyana zallan damuwarsa da farga yace.
“Rayyern me yake damunka, kodai ciwon kanka ne ya tashi!?”

Kai Rayyern din ya jinjina alaman “Eh.” Saboda ayanzu yakai wani stage da bayajin zai iyayin wata magana.

Zazzafan numfashi Abba da Mamyn suka sauƙe, cike kuma da alhinin tashin ciwon kannasa, Abba ya zaro waya dan kiran Ramadan.
Yayinda Mamy kuwa ta matso kusa da Rayyern d’in, anutse ta zauna tare da soma shafa masa tarin sumar dake kansa.

A dai-dai wannan lokacin kuwa, Ramadan ne ke zaune acikin wani had’add’en lambu, dake cikin wani katafaren gida, yayinda ya k’urawa wata fara kyakkyawar matashiyar budurwar dake zaune agefensa idanu.
duk da cewar kuma ak’alla budurwar dake zaune agefen nashi, ba zata wuce 20 years ba, amma tana da cikar halitta mai kyau, da ganinta kuma kasan cewa yar manyan mutane ne, Rayhanna kenan kyakkyawar matashiyar budurwar mai alkunya.

Yayinda ad’an gefe da Rayhannan kuwa Riyyam-nsra ne zaune, yanata yiwa Hamman nasa tsiya.
Cikin kuma ya bawa da zab’in Ramadan d’in yace.

“Gaskiya Hamma Ramadan ka iya zab’en kyakkyawar budurwa, tamkar daga saudiya aka sassak’ota.”

Murmushin Jin dadi Ramadan yayi, tare da sanya hannunsa na dama ya dafa kafad’an Riyyam din, again kuma cikin kasa dauke idanunsa daga kan Rayhanna’n nasan yace.

“Angaya maka cewar ni na wasa ne, ai kwata kwata bana sanya, ko da ka d’auka cewar ni irin suma Hamma Rayyern ne waliyai.”

Dariya Riyyam nsra ya saka, Yayinda ita kuma Rayhanna ta sanya mayafinta ta rufe fuskarta, wanda tayi hakanne kuma saboda Sam bazata iya jurewa, irin Kallon da Ramadan din keyi mata ba, Domin kallone da yake bayyana tsananin kauna da soyayyarsa agareta.

Baki Ramadan din ya bud’e da niyar cewa wani abu, amma kuma sai k’aran wayansa dake tashi, acikin aljihun rigarsa, ya hanashi furta komai.

Zaro wayartasa yayi, ganin sunan Abba na yawo akan screen din wayar ne, kuma yasa shi d’agawa da sauri.

Daga can b’angaren kuwa Abba dake tsaye agefen Rayyern ne yace.

“Ramadan, Rayyern! Rayyern ciwon kansa ya tashi!”

Idanu Ramadan din ya dan zazzaro tare kuma da, mik’ewa tsaye cikin tashin hankalin daya samu kansa aciki yace.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un, Abba maiya samu Hamma Rayyern din, yaushe kuma ciwon kan nasa ya tashi?”
Ya tambayi Abban cikin tashin hankali, gami da tsananin damuwa.

“Bansani ba Ramadan, Domin yanzu dawowanshi gida, yanzu haka gashinan a kwance sai faman rike kan na yakeyi.
Maza Ramadan kabar duk abunda kakeyi ka dawo gida, sannan ka biya ta pharmacy ka had’o masa magunguna.”

Abban ya fad’i hakan, cikin muryar dake bayyana cewa, kwarai yana cikin damuwa.

Ramadan kuwa idanunsa da suka ciko da k’walla, saboda tausayin dan uwannasa yad’an lumshe, kana cikin muryarsa da tayi rauni sosai yace.

“Shikenan Abba ganinan zuwa.”

Yana gama fadan hakanne kuma Abba ya katse kiran.

Riyyam-nsra da tun d’azun shima ya mik’e tsaye hankalinsa atashe matuka, yace.

“Hamma Ramadan mai yasamu Hamma Rayyern? Dan Allah karkacemin wani abu na cutarwa ne ya sameshi.”

Idanu Ramadan din ya bud’e, cikin yanayin sanyi yace.

“Ba abunda ya sameshi Riyyam, kawai dai ciwon kansa ne ya tashi, wanda dama kuma yana dashi, saidai bai cika tashi ba, harsai da dalili, Idan ciwon kannan ya tashi Riyyam, Hamma Rayyern yana shan wahala, saidai duk da haka gwara ciwon kan, akan matsanancin ciwon cikin da yake tashi mishi, awasu mabanbanta lokuta.”

D’an rank’wafowa yayi ya kalli Rayhanna, da itama gaba daya damuwa ta bayyana akan fuskarta, saboda tasan matsayin Dr Rayyern din awajen Ramadan, tasan yanda Ramadan ya dauki Rayyern, da kuma yanda yake girmama duk wani abu daya shafesa, haka kuma tasan yanda Ramadan din ke daukan duk wata matsala ko damuwar yayansa, Domin sauda yawan lokaci Ramadan din, kan fad’a mata cewar Hamma Rayyern dinshi, shine duk wani Garkuwa’rsa, shine kuma wanda ya tsaya masa akan jindadi da farincikinsa.

“Hanna zantafi, Hamma Rayyern bashi da lafiya, zamuyi waya later.”

Ramadan din ya fada murya asanyaye.

Mik’ewa tsaye Rayhanan tayi, tare da cewa.
“Shikenan badamuwa, Allah Ubangiji ya bashi lafiya, yasa zakkan jikine.”

Da “Ameen.” Ya amsa, har wajen da motarsa kirar Benz ke fake kuma Rayhanan ta rakosu, inda tayiwa Riyyam-nsra sallama.

Saida taga ficewarsu daga cikin compound d’in gidan nasu, kuwa kafun ta koma ciki.
Duk zuciyarta babu dadi, saboda duk wata damuwa da tagani akan fuskar Ramadan to ta shafeta.

Ramadan kuwa suna ficewa daga cikin gidansu Rayhannan, wani irin gudu ya soma shararawa akan titi, wanda hakan yasa cikin mintuna kadan suka iso, babban pharmacy dinsu.

Ko gama dai-dai-ta parking din motar baiyi ba, haka ya fito ya shiga cikin pharmacy din, duk wasu magunguna da yasan Rayyern din zai buk’ata ya had’a, tare da fitowa agurguje yaja motar suka nufo gida kaitsaye.

Isowarsu bakin gate din gidanne kuma yasa, Ramadan soma danna horn.

Wannan yasa cikin sauri Baba Maud’o dake zaune abakin gate din, yayi jigum, yazo ya bud’e musu, gaba d’aya bayajin dadi acikin zuciyarsa, saboda sai ayanzunne ma yake tunawa da cewar, halan ciwon kai din Rayyern dinne ya tashi, saboda aduk cikin gidan babu wanda baisan da cewar, Rayyern na fama da ciwon kai dana ciki ba.

Ramadan kuwa yana shigowa cikin gidan yayi parking motar, cikin sauri kuma shida Riyyam suka fito, kowannensu fuskarsa dauke da matsanancin damuwa suka shige cikin gidan.
Tunkafun su karasa shiga cikin babban falon gidan kuma, Ramadan ya soma b’abb’alle magungunan da zai bawa Rayyern din.

Wanda hakan yasa suna shiga cikin falon, direct Riyyam-nsra ya k’arasa gaban deep freezer, tare da dauko bottle water marar sanyi kasan cewar ba'a jima da sasuba.

Koda ya dawo goran ruwan ya mik’awa, Ramadan wanda zuwa lokacin harya gama b’are magungunan, inda da kansa ya tallafo Hamman nasa, tare da zuba masa magungunan, kana ya had’a masa da ruwan faro.

Atake kuwa Rayyern ya had’iye magungunan, saidai kuma cikin radadin ciwon kan nasa da yakeji, ya sake komawa ya kwanta, Yayinda sannu Ahankali yake ci gaba da d’an jujjuyawa kan nasa.

Idanu duk suka zuba masa, kana cike da tsananin tausayawa sukeyi mishi sannu, Riyyam-nsra kuwa zama yayi dab’as ak’asa, idanunsa da suka cicciko da hawaye ya zubawa Hamma Rayyern d’in, acikin ransa kuwa yana me addu’a, da fatan Allah Ya bawa hamma Rayyern dinnasu lafiya.

Rayyern kuwa dake kwance kannasa ya sake rikewa, tare da lumshe idanunsa, wanda sukayi jazur, saboda tsabar wahalan da yakeji kuwa, hatta jijiyoyin dake kwance akan goshinsa saida suka fito rud’u rud’u.

*Dan girman Allah masu sayan littattafai dan su fitar su watsashi kuyi hakuri kada ku saya littafina dan Allah nace in kin saya kuma ki gaya min in meda miki kuɗinki*

Bayan kaman mintuna 15 dashan maganin nasa ne kuma, ya soma sauke wani irin wahalalliyar ajiyar zuciya.
Yayinda sannu ahankali yakejin relief nad’an saukar masa.

In a 20mn kuwa batare da zato ko tsammani ba, bacci mai nauyi ya daukesa.

Jin yanda numfashinsa ke fita da d’an fusga ne kuma, yasa su Abba gane cewar yayi bacci, ajiyar zuciya suka sauk’e dukansu, Yayinda Abba kuwa ya d’an rankwafa tare da gyarawa Rayyern din kwanciya.

Bayan ya koma ya zauna akan kujera ne kuma yasa hannunshi duka biyu yayi tagumi cikin alamun tarin fargaba, tashin hankali, so, da tarin tausayin d’an nasa .
Ido Ramadan ya ɗan zuba mishi kana a hankali yace.
“Abba ba komai fa in sha Allah zai samu lfy”.
Numfashi ya ɗan sauƙe a hankali kana murya asanyaye yace.

“Hakika yanzu aduniya babu wani abu da yake, damuna da kuma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login