Showing 39001 words to 42000 words out of 350584 words
da bayanka, ya kuma dauwamar da farinciki acikin zuciyarka da na ahalinka.”
Da “Ameen.” Duk suka amsa.
Inda Malam din ya sake d’ago Kai ya kalli Yayan nasa, cikin aminci yace.
“Tabbas Dr. Rayyern ya gwada mana karamcinsa, saboda haka kamar yanda ya daukeni amatsayin Kaka nima na daukesa amatsayin jikana, zan kumayi masa kyauta da karamci kamar yadda yayi mini, Ibrahim shiga cikin dakina, ka bude wajen da nake ajiye kayana na musamman ka d’auko masa sabbin alkyabba da hirami.”
Murmushin farinciki dukansu sukayi inda Alhaji Ibrahim kuwa ya mik’e cikin girmama maganan mahaifinnasu kaitsaye ya nufi dakin Malam Mai-nasara din dake cikin falon.
Har yakai bakin kofarne kuma ya juyo tare da Kallon mahaifin nasu, kana aladabce yace.
“Malam alkyabba da hiramin guda nawa za’a d’auko masa?”
“D’auko masa kala bakwai, saboda zasu fi isansa domin zai saka guda daya acikin kowacce rana, Kaga kenan kala bakwai zasu isar masa har sati guda yana sawa yana tunani.”
Kai Alhaji Ibrahim ya jinjina, tare da bud’e kofar dakin mahaifinnasu ya shige.
Cikin abunda bai wuce mintuna goma ba, kuwa sai gashi ya dawo hannayensa dauke da manya manyan alkyabba, da hirami irin wanda limaman makka suke sakawa ajikinsu, alkyabbu ne masu kyau da kuma tsadar gaske.
Mikawa Malam din Alhaji Ibrahim yayi, Yayinda shikuwa Malam din ya mikawa Rayyern dake zaune, wanda fara’a da kuma farincikinsa ya kasa b’uya.
“Wannan kyautace agareka Rayyern domin kuwa nasan zasuyi maka kyau sosai, shigace irin ta kamala.”
Kai Rayyern ya jinjina cike da tsananin jin dad’i kuma yace.
“Godiya nake maitarin yawa Malam, Allah ya kara arziki da lafiya.”
“Ameen.” Malam Mai-nasara din ya amsa cikin jin dadi.”
Dai-dai lokacin kuwa Ramadan Riyyam da kuma Naseer suka shigo cikin falon.
Karasowa Ramadan yayi ya mik’awa Hamman nasu babban ledan magungunan dake hannunsa.
Karb’an magungunan Rayyern yayi, hade kuma da mik’awa Ramadan alkyabba bakwai din daya same su amatsayin kyauta daga Malam.
“Kyauta na samu daga wajen Malam.”
Yafad’a adai-dai lokacin daya gama mikawa Ramadan din kayan.
Idanu Ramadan din yadan zaro fuskarsa cike da tsananin farinciki yace.
“Masha Allah Malam godiya muke.”
Hararan wasa Rayyern ya watsa masa, kana cikin sigar tsokana yace.
“Godiya muke kaman yaya, nawa nefa ba namu ba.”
Dariya kusan gaba dayansu suka sa, ciki kuwa harda Malam.
Riyyam kuwa jin hakanne yasashi, d’an shagwab’e fuska, tare da matsowa kusa da Malam din yace.
“Ayyah Kaka Malam toni Ina nawa alkyabban.”
Murmushi Malam Mainasara yayi, tare dasa hannu ya shafa kan Riyyama din.
“Kaima taka tananan tana jiranka amma sai ka ƙara girma, yanzu idan na baka yawa zasuyi maka.”
Malam din ya fada da matuk’ar kulawa.
Aikuwa Riyyam kamar dama abunda yake jira kenan, cikin yanayinsa na sakewa daya zame masa sabo, ya kalli Ramadan tare da cewa.
“Yeh za’abani ba za a bawa wani ba.” Ya kare maganan yana meyiwa Ramadan din gwalo.
Abunda ya matuk’ar bawa su Alhaji Ibrahim dariya kenan.
Shikuwa Ramadan durk’usawa agaban Malam din yayi, cikin sigarsa ta shagwab’a shima yace.
“Shikenan na fahimta yanzu wariyar launin fata za’a nunamin, da farko an bawa Hamma Rayyern alkyabba, yanzu kuma an shafa kan Riyyam amma ni ba a shafa nawa ba.”
Ayanzu kam Dariya Malam Mai-nasara yayi, har saida hakwaransa suka bayyana, cikin matsanancin kauna da kuma soyayyar yaran da yakeji acikin ransa, ya sa hannu ya dan jawo Ramadan din jikinsa.
Kansu ya shafa dukansu tare dayi musu addu’a, domin hakanan yakejinsu acikin zuciyarsa tamkar jikokinsa na gaske.
Rayyern kuwa duk abunda kannen nasa sukayi kallonsu kawai yakeyi, bayan kuma ya gama bare magungunan da ya kamata ace Malam din yasha ne, yasa Naseer ya miko masa bottle water marar sanyi.
Da kasan ya bawa Malam magungunan yasha.
Tare dayiwa su Alhaji Ibrahim bayanin yanda akullum Malam din zaina shan maganinsa.
Godiya sukayi mishi sosai, ganin da yayi kuma lokaci yadan ja sosai ne, yasa shi kallon su Ramadan tare da cewa su tashi su tafi.
Cikin aminci sukayi wa Malam din sallama, inda Rayyern ya shaida masa cewar zaidawo ya sake dubashi.
Koda suka tashi tafiya kuwa har wajen motocinsu Uncle Mustapha da kuma Alhaji Abdallah suka rakasu.
Basu koma cikin gidan ba kuma harsaida suka ga tafiyansu Rayyern din.
Daga b’angaren su Raayyern kuwa kaitsaye gida suka nufo.
Direct Rayyern dakinsa ya wuce, saboda yana son yin wanka, sannan akwai kuma wani aiki da zaiyi a laptop d’insa.
Yayinda su Ramadan da Riyyam kuwa, anan falo suka zauna inda Mom ta kawo musu abinci suka ci.
Bayan sun gama cin abincinne kuma suka wuce masallaci danyin sallan azahar, ciki kuwa harda Rayyern wanda ya sanja shigarsa zuwan wata farar jallabiya.
Jannart.
Kwance take akan makeken gadonta, wanda akoda yaushe yake shumfud’e da lallausan bedsheet na alfarma.
Irin kwanciyarnan ta rubda ciki tayi, Yayinda ajikinta take sanye da wata baby gown marar nauyi.
Lumsassun Idanunta ta ware ahankali tare kuma da sauke wani ajiyar zuciya mai
Cike da tarin damuwa.
Lallai Tabbas tana da buk’atar y’anci acikin rayuwarta, rayuwar da har yau ta kasa tantance wacce kalar rayuwa ce, rayuwar da kwata kwata babu haske acikinta sai tarin damuwa, kunci da kuma kadaici.
Mirgina wa tayi a hankali kana taci gaba da tunani.
Yayinda akowanni kwanan duniya da irin kalubalen da take fuskanta, acikin kowanni sa’a kuwa zuciyarta na bugawa da tarin tsananin tsoron abunda zaije ya dawo.
Lallai Tabbas tana da buk’atar haske acikin rayuwarta, haka kuma tana da buk’atar abokin rayuwar da akoda yaushe zai debe mata kewa, Sam arayuwarta batasan wani abu Waishi ingantaccen farinciki ba, akullum damuwa kawai da tsoro ta sani.
Haka kuma akowani bayan minti guda tsoronta yakan rub‘anya, tare da mummunan bugun zuciya akan abunda Yayanta Junaid ke neman aikata mata.
Saudayawan lokuta takan tambayi kanta, cewar shin Ya Junaid wani irin d’an uwane? Meyasa akoda yaushe bashi da fata ko buri saina keta haddinta?
Tabbas tunaninta yakan neman watsewa aduk lokacin da ta tuna cewar Ya Junaid din yayanta ne Uwa daya Uba daya.
Shin Meyasa Rayuwa take garari da ita?
Karar wayarta dake aje bisa bedsite ne ya katse mata duk wani tunanin da takeyi.
Ahankali tasa hannu ta share dan guntun hawayen dake kwance agefen Idanunta, wayartata dake ta faman tsuwa ta dauka, ganin kuma sunan Salman ne ke yawo akan screen din wayar yasata picking da dan hanzari.
“Y’ar Hutu wato kinanan kina hutawa agida ni kuma kinbarni da wahalan aikin ki ko.”
Cewar Salman.
Itakuwa Idanunta ta lumshe tare da d’an gyara kwanciyarta.
Cikin muryarta da tayi sanyi sosai tace.
“Sorry Salman gaba d’aya yau banajin karfi sosai ajikina ne, Impact ma nina fara sarewa da wannan aikin wallahi, I’m tired because mutumin nan kamar bazamu samu daman ganinshi ba.”
Murmushi Salman yayi tare da d’an gyara zamansa kana cikin son bata karfin guiwa yace.
“No Jannart don’t stress your self, Insha Allah yau zamu had’u dashi, kinsan na samo mana information akansa, so Yanzu dai anjima kishirya muje hospital d’insa, Insha Allah zamu samu ganinsa.”
Idanunta dake alumshe ta bud’e tare da sauke ajiyar zuciya.
“Thank you so much Salman Insha Allah zan shirya by 3 pm sai muje, zanzo office saimu tafi aboye batare da kowa ya sani ba.”
(Hattara garemu iyayen yara, yawan tsaro baya hana yaranmu yin abinda suke so. Tsananta addu'a da jawo yara a jiki yafi tsananta tsaro da zafi),
“To saikinzo.”
Salman din ya fada tare da kashe wayar.
Itakuwa Jannart bayan ta ajiye wayartata agogon dake sakale ajikin Bangon dakin ta kalla.
Wanda ya nuna mata 2:30 pm.
Zuro kafafunta kasa tayi daga kan bed din, batare da ta tsaya sanya ba kuwa ta shige bathroom danyin wanka.
Sanin da tayi cewar basu da enough time ne kuma yasa bata wani bata lokaci awajen yin wankan nata ba.
Koda ta fito mai kawai ta shafa ajikinta, sai kuma powder and oil lipstick.
Yayinda tabi zara zaran eye lashes dinta da mascara.
Bayan kuma ta feshe jikinta da sassanyan body spray ne.
Ta karasa gaban Sif din kayanta, inda ta zaro wani dogon wandon pallazo white and white colour roba t shirt wanda yake da ɗan fadi kaɗan ta kasa kuma yazo kusa da guiwarta.
Cikin nutsuwa ta sanya kayan ajikinta, tare da daukan wani hill shoe mai kalan blue ta saka ak’afanta, kana kuma ta yane kanta da wani dan vail shima mai kalan blue.
Akan tsintsiyar hannunta kuwa wani anklet ta saka mai kyau.
Wanda ya sake kawata kyaun kwalliyar tata.
Murmushi ne ya dan bayyana akan fuskarta, saboda Kallon irin kyaun da tayi acikin madubi, Yayinda kayan jikin nata kuwa sukayi matukar amsarta tana matuƙar son ƙananan kaya, ta gaza gano illar sasu a ko ina.
Tabbas ayau din ko makiyinta bazaiyi mata kallo daya ya dauke kansa ba sosai kam tayi kyau.
Wata yar madaidaiciyar handbag blue colour ta rike ahannunta bayan ta rike wayarta ahannunta na dama ne kuma ta juya ta fice daga cikin dakin.
Anan Cikin falo ta samu Momy da kuma Abdull zaune.
Ganin ta cikin shiri da sukayi ne kuma yasa Momy cewa
“A’a Jannart fita zakiyi ne.”
“Eh Momy zanje office amma bazan jimaba Zan dawo Insha Allah.”
“To adawo lafiya”
Da Ameen ta amsa, Yayinda Abdull kuwa yace idan tazo dawowa ta kawo masa abundadi.
Da to kai ta amsa masa kana tasa kai ta fice daga cikin falon.
Tana fita compound din gidan kuwa, kattin samudawan guard dinta suka tattaso.
Har acikin ranta Allah Yasani kwata kwata batason wayanann mutanen da suke tsaronta, saidai kuma babu yanda ta iya.
Haka ta shiga mota suka fice daga cikin gidan.
Direct Nasarawa G.R.A ta nufa inda anan wajen aikin nasu yake.
Suna isa kuwa ta fito daga cikin motar, kaitsaye ta wuce cikin Arewa 24 din ɗan madaidacin ma'akatane, wanda yake kamar irin manyan gidajen nan ne na al'farmar.
Sam wurin gidan TV'n bai cika girmaba, dan bazaifi wani gidanba, ma, sai dai zubi da tsarin wurin shine mai tafi da hankalin mai kallo, kota ina ka wulga shuke-shuke ne masu kyau da ɗaukar hankali kamar a kasashen turawa, Gate ɗinsu daya ne ta inda ka shiga ta nan zaka fita, can ciki kuma Office-office. Masu kyau ma dai-dai-ta na al'farmar da hall ɗinsu sai ɗakunan haska shirye-shiryen su.
Duk inda ta gilma kuwa sai abokan aikinta sun bita da ido, Yayinda kowa ke yaba irin baiwar kyau da Allah ya bata manya daga ciki irinsu Aunty Fa'iziyya D Sulaiman kuwa ƙuruciyarta suke gani a fili da illar shigarta da ta meda jikinta.
Direct office dinsu ta wuce kaitsaye.
Inda ta samu Salman da kuma Aysha Lawan suna zaune.
Nanfa ta tsaya gaisawa da Aysha kawartata.
Acan gidansu Rayyern kuwa.
3:00 am dai-dai ya fito daga wanka, inda ya shirya kansa cikin wani black tracksuit, masu kyaun gaske, da suka matuk’ar amsar jikinsa.
Yayinda ak’afansa kuwa ya saka wasu had’add’un sneakers shoe masu kyau da taushi.
Bayan ya gama kimtsa kansa ne kuma, ya shafa wani irin fitinannen turare mai tsananin kamshi.
Bud’e drawer’nsa yayi.
Shiru ya ɗan
Tsaya yana mai kallon Alkyabbun dake jere a saman kayanshi.
Haka nan yaji yana son gwada sa alkyabbar a jikinsa yaga ya shigar zatayi mishi.
Numfashi ya ɗan fesar a hankali inda anutse ya zaro daya daga cikin alkyabbun da Malam Mai-nasara ya bashi.
Warware alkyabban yayi tare da soma kare mata kallo baƙace mai kyau irin mai sheƙin nan gefe da gefenta an ƙawayashi da zare golding, kai ya jinjina saboda shi kansa ya yaba da kyau da kuma haduwarta, musamman daya fahimci cewar ba karamin kudi aka saka wajen sayan duk alkyabbun ba fuska ya dan yamutsa dan sun cika nauyi.
Addu’an sanya sabon kaya ya karanta, "Alhamdulillahil laxee kasani haxal saubah warazaƙani min gairi hauli minni walaƙuwah".
dai-dai lokacin daya ke daura alkyabban akan kayan dake jikinsa.
Tare kuma da daukan harami ya daura akansa.
Ya Allah!
Bakaramin kyau Dr.Rayyern Mai-nasara yayi ba, alokacin daya gama kimtsa kansa Cikin alkyabbar.
Kyau yayi sosai da sosai, wanda shi kansa saida ya sake yiwa Allah Godiya daya halittosa amatsayin bil’adama musulmi mai shiga ta kamala.
Koda ya kalli kansa amadubi numfashi ya ɗan fesar a hankali saboda yanda yaga ya fito tamkar Limami.
Wayarsa da kuma wata yar jaka dake gefen gadonsa, wanda ya kusan cika cikinta da chocolates ya d’auka, tare da rik’e jakan ahannunsa, kaitsaye ya fice daga cikin dakin.
Ahankali yake saukowa daga kan steps d’in...!
Uhum muje-muje dai sunan wata mota, lbrin yanzu anka fara.
By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*TUBALI*
PAGE 12
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
*FREE PAGE ne*
*Littafin TUBALI na kuɗine special Group 1k ƙaramin group 500 kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU,sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276. Ko kuma katin MTN*
Fawal beauty parlor sunai muku albashir da bude gidan Mata wato kigyara da kanki👩🏻🦰 da cewa suna gabatar da aiki na zamani kamar su gyaran jiki, spa kenan gyaran fuska wato facial,gyaran Kai, hair style , gyaran kafa pedicure,gyaran hannaye, manicure kitso,lalle ja da bakki,ba'a barsu abayaba suna saida kayan gyaran aure, turaruka,man shafawa, suna kwalliya wato makeup,turaren wuta, humrah,kulaccham dama abunda Baku sanshiba wato maida tsohuwa yarinya akankanin lokaci😄iya kudinka iya shagalinka💃kudai ku hanzarta zuwa ga wannan gida na mata zallah (FAWaL BEAUTY PARLOR)
Address: Main gate na fire service jimeta, opp sixty plaza.
kada kubari abaku labari😍 munai muku maraba a koda yaushe Mata yan kwalisa mace sai da gyara , yar uwa bora ba sunanki kizama mowar mai🏨 da taimakon FAWAL BEAUTY PARLOR 👩🏻🦰da kudinki qalilan kifita sab abunki ki baza kamci mai kama jiki.
Gamai buka contact CEO FAWaL BEAUTY PARLOR kan 09033901035 or 08078809930 sai kunzo, our time services from 8:am to 7pm, Monday to Saturday/ Sunday 10am to 6pm🪞🎁🛒🛍️🤝🏻
Kafad’anta wanda ya sauk’o ya rufe bayanta.
Batare kuma daya sake cewa komai ba, ya juya fuskarsar nan amurtuk’e.
Bottle water da kuma phone d’insa ya d’auka, kana ya zo ya wuce ta gefenta.
Itakuwa Jannart Idanunta ta rumtse da k’arfi, tare dasa hakwaranta ahankali ta cije lips d’inta.
“Duk wata macen da tasan ciwon kanta, bata yawo ahaka kamar yanda ke kikeyi, sannan mata da yawa suna sirrranta kansu, amma ke kina bayyana k’azantarki.”
Ta maimaita maganar daya fad’a mata d’in, wanda yasa tajin zafi har acikin zuciyarta, cikin kuma k’unan rai da b’acin ran kalaman nasa da wata iriyar fitinenneyar kunya mai masifar kashe ido da jiki tace.
“Waye shi da har yake fad’amin irin way’annan bak’ak’en maganganun, meya gani ajikina haka? Sannan akan me zai rufamin wannan abunnasa me shegen mayataccen k’amshi?.”
Ta fad’i maganar tana me d’an zame alkyabba’n ajikinta, dare da juya bayanta ta kalli jikinta, saboda tanason sanin mai ya gani ajikinta da har zai fada mata irin wannan maganan.
Karab kuwa Idanunta suka sauka akan jinin, dake jikin farin wandon ta, wanda da alama kuma daga jikinta jinin ya fito.
Idanunta tad’an zazzaro waje cike da mamaki da wata sabuwar kunya tace.
“What period dina kuma? Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un Period at this time, Oh My God!!”
Ta fad’a da d’an k’arfi, cikin kuma muryar dake bayyana tsananin takaicinta, saboda Sam bata tab’a tunanin period din nata zaizo a irin lokacin ba, kasancewar tasan da sauran lokacin daya rage masa, har na tsawon kwana uku kafun yazo.
“But amma why yazo yanzu? Meyasa Meyasa?”
Tayiwa kanta tambayar tana me b’ata fuska, domin sam bataji dadin abunba, cikin sauri kuma taja alkyabban daya rufa mata din ta sake rufe jikinta.
Lokaci d’aya kuma taji wani irin matsanancin kunya, da takaicin kanta na taso mata, duk da kuwa tasan cewar ba laifinta bane, period dinne ya sanja time wanda ko wacce mace kan iya fuskantar hakan musamman in tashin hankali da tsinkewar zuciya ya riski mutum, amma tayi matuk’ar takaicin ganin jinin period dinta da wani da bata sani ba yayi.
Tabbas taji kunya yanzu da wani idon zata sake kallonshi? kuma shi dinma ayanzu wani irin kallo zainayi mata karo na forko a rayuwarta da taji haushin irin shigar da takeyi.
“Wata macen da batasan ciwon kanta ba, bata iya ankilta kantaba.”
Zuciyarta ta bata amsa atake.
Idanunta ta rumtse cike da takaici.
Dai-dai lokacin kuwa Salman Ya ware idanunshi a kansu tare da dawo da kallonsa gareta.
Fuskarsa dauke da d’an mamaki yace.
“Ha’a Jannart lafiya kuwa kizo mutafi mana..”
Sauran maganar tasance ta mak’ale, alokaci da yaga jikin Jannart din lullub’e da Al'kyabban, da dazu ya ganta agefen mutumin da har yanzu baisan sunanshi ba.
Jannart kuwa fuska tad’an marairaice, kana cikin sanyin jiki ta soma takowa zuwa inda Salman din ke tsaye.
“Jannart wannan Al'kyabban fa? Kin sanshi ne?”.
Salman din ya tambaya, saboda yayi mamakin ganin ya sawa Jannart din da al'kyabban k’warai.
“Shi ne ya bani.”
Jannart din ta fad’a kaitsaye, bisa kuma sanin rashin dacewar Salman din yasan gaskiya abinda yasa yasa mata, shi yasa ta fad’a masa hakan, batare kuma da ta bada wata kofar da Salman din, zaiyi mata wata tambayar ba ta soma tafiya.
Salman kuwa idanunsa ya zuba mata, yana mai Kallon yanda al'kyabban tayi mata matuk’ar kyau duk da tayi mata yawa, saidai kuma Jin tace wancan mutumin ne ya bata, yasa shi jin babu dadi acikin zuciyarsa.
Saidai kuma bashi da ikon bayyana hakan.
Ab’angaren Dr. Rayyern kuwa Koda ya fito daga wajen wasan, kaitsaye Inda motarsa ke fake ya nufa.
idanun y’an tsirarun mutanen dake wajen ke kansa, duk da cewar kuwa basusan shi din asalin waye bane, amma kallo daya zakayi mishi kafahimci cewa mutum ne mai zarra.
Baya ga haka kuma ga tarin baiwar kyau da Allah Yayi mishi.
Tun kafun ya karasa isowa