Showing 219001 words to 222000 words out of 350584 words
yace.
“To Meyasa kike fushi dani?”
“Nifa Naan bana fushi...”
Ta fad’i maganar cikin sigar shagwab’a, tare kuma da turo d’an k’aramin bakinta gaba.
Lips din nata ya kuma kallo, still yana mejin wani irin abu nayi masa yawo acikin jikinsa, in a silent voice yace.
“To Meyasa yau bakizo kin bani mgnina ba, bakince kina gadina ba, kuma dama ai kince saboda gadi na ne, kawai Abba ya turo ki, yanzu har kin gama gadinne ko kuma umarnin Abbanne ya k’are ummmmm?”.
Ya Kai karshen maganan nasa, cikin wani sautin daya sata d’agowa ta kalleshi.
Saidai kuma ganin yanda cikin idanunsa, suka sauya launi izuwa na maye ne yasa tayi saurin k’asa da kanta.
Asanyaye kuma tace.
“To baka ce ka samu lafiya ba.”
“Ummm.”
Ya amsa mata ahankali, tare da zura duka hannayensa acikin aljihun rigarsa.
“To Allah ya kara sauki.”
Jannart din ta fad’a ashagwab’e, tare kuma da kawar da kanta gefe, saboda matukar numfashinsa, ya ci gaba da sauk’a akan fuskarta, To babu makawa zata iya sume masa.
Shikuwa Rayyern ganin hakan da yayi ne, yasa shi jinjina kansa, had’e da cewa.
“Ameen.”
ahankali kuma ya janye jikinsa baya, tare da juyawa batare da ya sake ce mata komai ba ya fice daga cikin dakin.
Jin alamun takun tafiyarsa, da kuma yanda ya fad’i Ameen din, acikin rashin dad’in yanayi ne, yasa ta d’ago Kai ta kalleshi.
Amma kuma sai taga ko juyowa baiyi ba, direct ya fice daga cikin d’akin.
Asanyaye tabi bayansa da kallo, tare da sauk’e ajiyar zuciya, cikin sanyi kuma ta lumshe Idanunta, tana me sake shak’an kamshinsa mai matuk’ar dadi.
Shikuwa Rayyern yana fita daga d’akin nata, direct cikin falo ya fito, ahankali ya zauna akan d’aya daga cikin kujerun falon, tare da jingina jikinsa da kujeran ya lumshe idanunsa.
Almost 10mn Ahankali ya sauke ajiyar zuciya, tare kuma da zamewa ya kwanta akan kujeran.
Hakanan yakejin tamkar babu wani abu akusa dashi, like yayi losing wani important abu nasa.
Jannart kuwa Ganin ta fiyar nasa ne, ya sata koma ta kwanta, akan gadonta hade
da lumshe Idanunta, Ahankali take sauraran yanda zuciyarta ke bugawa, sanadiyar kusan cin da suka samu atsakanin junansu d’azun.
Rayyern kuwa Ganin da yayi zaman falon ya ishesa ne, ya sashi komawa d’aki, ya d’auko system d’insa.
Jin da yayi dakin Yayi masa sarari da maraicine kuma, ya sashi sake dawowa falon.
Anan kan kujera ya zauna, tare da d’aukan laptop din nasa ya soma duba bayanan sabon companyn su.
Wanda zuwa yanzu komai na companyn yana tafiya dai-dai, domin sun samu share holders da yawa, baya ga haka kuma ana nan anata, sarrafa kayan masarufi, ba kuma iya alkama kawai suke sarrafawa ba, harma da shinkafa shanshera, wanda yanzu haka managernsa ya tafi, Gombe Dan saro musu shinkafan.
Kusan mintuna 20 ya share yana duba, yanda harkar companyn nasa ke tafiya, bayan ya kammala ne kuma ya shiga, cikin mails dinsa saboda amsar sakonnin da ake tura masa arana, kusan sama da 1000.
Kamar Koda yaushe kad’an daga cikin sak’on ya duba.
Sakon last daya duba kuma shine, wanda ya kama dole sai yayi reply, saboda wasu code ne zai turawa d’ayan companynsa.
Kansa ya d’an dafe Ahankali saboda, tunawa da yayi cewar code din suna cikin karamar wayarsa, Wacce ke hannun Jannart.
Ahankali ya d’an juyo da kansa ya kalli, kofar dakin nata, duhun da yagani ta tsakankanin kofa ne kuma, yasa shi fahimtar cewa harta kwanta.
D’an k’aramin tsuka yaja, tare da rufe laptop din, Ahankali ya maida jikinsa ya kwantar akan kujeran.
Numfashi ya d’an fesar, tare kuma da lumshe idanunsa, kwata kwata baisan Meyasa yakejin kansa, kamar ba’a daidai ba haka nan yakejin sa kamar yana cikin maraicin kaɗaici.
Haka kuma baisan dalilin da yasa shi, yake yawan jin kasala ba, Yayinda bakin abubuwa ke bijiro masa acikin Y’an kwanakin, gaba d’aya yasan ba haka yake ba.
Sake gyara kwanciyarsa yayi, tare da rumtse idanunsa way’anda keyi masa gizo da kyakkyawan surar jikin Jannart din, musamman kirjinta wanda akoda yaushe Idan ya kalla, sai yaji tsikar jikinsa ya tashi.
Kasancewar tun kallo dazu da yayi mata, har zuwa yanzu tsikar jikinsa baidaina tashi ba.
Haka kuma yakejin wani irin abu na yawo acikin jikinsa, musamman jijiyoyin dick d’insa dake mommotsawa.
Matse jikinsa waje d’aya yayi, tare da d’aukan trow pillow ya d’aura kansa akai.
Da k’arfi ya kuma rumtse idanunsa, tare da fatan Allah yasa bacci yayi gaggawar d’aukarsa.
Kasancewar kuma yasa maganinsa, mintuna 30 da suka wuce, shiyasa bai wani sha wahala ba baccin ya d’aukesa ahaka, Yana nan kwance akan kujera batare daya shiga cikin bedroom d’insa ba.
Ab’angaren Jannart kuwa sam bacci ya ki d’aukarta da wuri, saboda hakanan takejin duk jikinta yayi sanyi, Yayinda zuciyarta ke raya mata cewar, kamar Rayyern din yayi fushi ne.
Sake gyara kwanciyarta tayi hade da lumshe Idanunta, wanda sukeyi mata gizo da nasa idanun.
Tananan ahaka bacci ya d’auketa, saidai har acikin zuciyarta da tunaninsa tayi bacci.
*Washegari.*
Kamar yanda ya saba tashi akowacce rana haka yau dinma.
Ahankali ya dan bud’e idanunsa tare da tashi ya zauna.
Acikin bakinsa yake ambaton sunan Allah, tare kuma da d’an k’arewa falon kallo.
Duk da kasancewar babu isashshen haske acikin falon, amma hakan bai hanashi Ganin lokaci, ajikin agogon dake kafe ba.
Sanin da yayi cewar Idan ya tsaya zai iya rasa jam’ee ne, yasa shi mikewa tsaye tare da nufan d’akinsa.
Koda ya shiga alwala yayi, kasancewar yanajin karfin jikinsa yau dinne kuma, ya sashi daukan carkey d’insa, tare da bud’e kofar dakin ya fice.
Koda ya fito compound din gidan motarsa ya shiga,ba tare daya tsaya wani b’ata lokaci ba kuma, kaitsaye ya nufi masallaci.
Jannart kuwa jin Karan fitan motarsa ne, yasa ta bud’e Idanunta ahankali, tare da mik’a hannunta sama ta kunna wuta.
Agogo ta kalla, Ganin lokacin sallah yayi ne, kuma ya sata saukowa daga kan gadon, direct toilet ta wuce ta d’auro alwala.
Tana fitowa kuwa ta shumfud’a Sallaya ta tada sallah.
Koda ta idar da sallan komawa tayi ta kwanta, saboda duk ji take baccin bai isheta ba.
Acan b’angaren Rayyern kuwa, Koda suka idar da sallah bai bar cikin masallacin ba, har saida gari ya fara haske.
Bayan yayi musu ordern abinci ne kuma, ya kama hanyar dawowa gidan.
Kaitsaye dakinsa ya wuce, bayan ya rage kayan jikinsa ne kuma, ya shiga wankan da mintuna 20 kacal ya b’ata wajen yinsa.
Ahankali ya murd’a handle din kofar, toilet din ya fito hannunsa rike da Dan karamin towel yana tsane jikinsa.
Bayan ya kammala tsane jikin nasa ne kuma, ya shafa body lotion mai kamshi, tare da bud’e drawer ya ciro, wani had’add’en suit mai tsadar gaske.
Anutse ya saka boxer da singlet d’insa, kana cikin dan hanzarin kada ya makara ya shirya kansa cikin suit din nasa, mai kalan army green wanda yayi matukar yi masa kyau.
Cikar haibar kwalliyan nasa ya sake fitowa ne kuma, musamman daya saka takalmin sau ciki army green, da kuma agogon kamfanin Rolex ahannunsa.
Briefcase da kuma wayarsa ya d’auka, cikin takunsa na alfarma ya fita zuwa falon.
Dai-dai lokacin ne kuma delivery ya kawo masa ordern abincin da yayi.
Karb’an abincin yayi, tare da komawa Cikin falon ya zauna.
Bud’e ledan yayi tare da ciro takeaway d’aya ya bud’e, Kallon abincin dake cikin takeway din yayi, kana ahankali kuma ya d’ago da kansa ya kalli kofar d’akin nata.
Idanunsa ya dan zubawa kofar domin baiga alaman cewa an bud’eta ba, na yan wasu mintuna ya kalli kofar, lokaci daya kuma ya dauke kansa, tare da daukan spoon ya soma d’an tsakalan abincin dake gabansa.
Kwata kwata kuma bai wuce loma 4 yayi ba, ya ture takeway din gefe saboda har yanzu bawai yana wani jin dadin bakinsa bane Chocolate din daya ɗebo ya fara gutsara yana taunawa a hankali saida yaji ya ɗa koshi kana yaja ledan maganibsa.
Bayan yasha maganinsa ne kuma ya mik’e tsaye, still ya kuma Kallon kofar dakin nata, kamar wani wanda ke tsammatan wani abu, dai-dai lokacin kuma wayarsa dake cikin aljihunsa ta soma k’ara.
Zaro wayar daga cikin aljihun nasa yayi, Ganin da yayi sunan Abbansa na yawo akan screen din wayarne kuma ya sashi, picking call din tare da kara wayar akan kunnensa, cikin dan yanayin girmamawa yace.
“Assalamu Alaikum Abba Ina kwana.”
Daga can b’angaren Abba dake zaune akusa da Mamy, Jin muryar Rayyern din wasai ne ya sashi, Dan fadada murmushi kana cikin kulawa yace.
“Wa’alaikassalam, lafiya kalau Rayyern ya jikin naka?”
“Alhamdulillah Abba naji sauki sosai, Dan yanzu haka ma wajen aiki zan tafi.”
Rayyern din ya fada yana me janye idanunsa daga Kallon kofar dakin Jannart din.
Abba kuwa Ajiyar zuciya ya sauke, saboda ko daga sautin muryar Rayyern din, kasan Masha Allah yaji sauki.
Cikin jin dadin hakan kuwa yace.
“Masha Allah haka akeso ai, Allah ya kara maka lafiya, amma kada ka manta da shan magunguna akan lokaci, ina Jannart fatan tana lafiya?”
Idanunsa ya dan lumshe ahankali, kuma cikin sanyin murya yace.
“Lafiyanta kalau.”
Kai Abban ya girgiza kana cikin gamsuwa yace.
“masha Allah to adawo lafiya amma Rayyern ka kula da kanka sosai, ka daina sakaci akan cin abinci da kuma shan magani.”
“To Abba.”
Rayyern din ya fad’a atsanake, jin Abban ya kashe wayanne kuma, yasa shima ya zare wayar akan kunnensa, tare da maida ita cikin aljihun rigarsa.
Gudun kada ya makara ne kuma yasanyashi, d’aukan Briefcase d’insa ya fice daga cikin falon.
Koda ya fito waje motarsa ya shiga, cikin dan hanzari yayi mata key, tare da cillata kan titi kaitsaye ya nufi, babban hotel din da acikinsa zasuyi lecture din yau.
10:00 pm
Ahankali ta bud’e murfin kofar dakin nata ta fito, saidai kuma daddad’an k’amshin turarensa da ya gauraya da numfashinta ne, ya sata lumshe ido tare da shak’an wani sabon numfashi.
Ahankali kuma ta bud’e Idanunta tare da soma k’arewa falon kallo, wanda komai na cikinsa tsab tsab yake.
Idanunta da suka sauk’a akan ledodin takeaway din dake kan table ne, ya sata karasowa cikin falon.
Sanin da tayi kuma cewar Rayyern din baya gidanne, yasa ta nemi waje anan cikin falon ta zauna, batare da ta damu da irin shigar dake jikinta ba.
Ahankali ta jawo ledodin takeaway din, abunda taga yayi mata ta d’anci kad’an, bayan ta kammala cin abincinne kuma, ta koma ta kwanta tare da lumshe Idanunta, tana me sauraran wak’an film din Kalho Naho, dake tashi acikin babban tv’n dake falon.
Azahirin gaskiya wakan take saurare, saidai kuma amma abunda ke cikin zuciyarta daban yake, domin gaba daya tunaninta ya tafi ne izuwa ga rayuwarta.
Sau da yawan lokaci takan ji ta wata ta daban acikin wannan duniyar, takanji kanta amatsayin wata halitta wacce bata da gata, halittar da rayuwar ta ta kasance tamkar haja a kasuwa, ko kuma kwallo ta yanda kowa ke bugata yanda yake so.
Tabbas tasan k’addara na iya zuwarwa bawa, ayanda bai tsammata ba, amma ita tata k’addarar akullum da salon wasa da rayuwa take zuwar mata.
Kamar dai yanzu da take rayuwa awata duniyar ta daban, wanda babu iyayenta akusa da ita.
Ada ta fuskanci takura kad’aici da kuma tsangawa ma, awajen Yah Junaid, takanyi kuka sosai aduk sanda Junaid ya musgunawa rayuwarta, haka kuma takanyi takaici da mamaki aduk sanda, yayi yunkurin kusanto da kansa gareta, ta sani cewar shidin Yayanta ne na jini, amma har yau tambayar da takeyi wa kanta shine, Meyasa Junaid din da ya kasance dan uwa agareta, ke kokarin keta haddinta akoda yaushe?
Ajiyar zuciya ta Dan sauke ahankali, cikin sanyi kuma tasa hannu ta sharce hawayen, daya gangaro ta gefen fuskarta.
Sakamakon tunawa da tayi cewar, ayanzu wata kalan rayuwa takeyi daban, cikin kuma k’addarar da ta d’aukota daga gidansu, ta raba ta da Mahaifinta, da kuma y’an uwanta.
K’addarar da ta kawota wannnan k’asar da take ganinta amatsayin sabuwar duniya.
Numfashi ta kuma fesarwa, tare da gyara kwanciyarta akan kujeran, ahankali ta kuma lumshe Idanunta.
Tana kwance ahaka da tunani kala kala, acikin zuciyarta bacci b’arawo ya d’auketa.
Acan b’angaren Rayyern kuwa tun 8:00 pm suke lecture, basu ne suka fito ba sai 1:00 am, nanma breaktime ne da suka samu, domin bayan sunci abinci zasu sake komawa wani lecture din.
Kasancewar kuma akwai musulmai da dama, acikinsu ne yasa sukayi amfani da breaktime din sukayi Sallan azahar, bayan sun idar da sallan azahar dinne kuma, suka wuce cafe dan cin abinci.
Shidai bai wani ci abincin sosai ba, sai drinks kawai da yasha kan Chocolate ɗinsa da yaci.
Kasancewar kuma agefen cafe din akwai, wani sasanyan furanni da swimming pool ne, yasa ko ina dake wajen ya d’auki sanyi, daga inda su Rayyern din ke zaune kuma, suna iya jiyo koke koken tsuntsayen dake shawagi awajen.
Saboda daddad’an sanyin dake ratsa sa ne, kuma yasa shi d’an lumshe idanunsa ahankali.
Wani irin yanayi yakejin kansa aciki, ma’ana yanayi mai kama da shauk’i, akaro na farko kuma acikin rayuwarsa daya fara tunanin wata mace.
“Naan! Naanu!!”
Ya maimaita sunan da take kiransa dashi, Yayinda acikin kunnuwansa kuwa, yakejin tamkar sautin muryar nata ne keyi masa gizo.
Idanunsa dake alumshe kuwa, salon shagwab’arta suke hasko masa, musamman yanda takeyi Idan tana magana, Ahankali yake ganin lips dinta na motsawa, Idan acikin fushi take kuwa, to lips din nata take turowa gaba, then saita dan karyar da wuyanta gefe.
Sassanyar Ajiyar zuciya ya sauke, ahankali kuma yake sauraran sautin bugun zuciyarsa dake tafiya kadan kadan, batare da ya ankara ko sanin abunda yakeyi ba, kuwa yaji heart din nasa tayi sanyi sosai.
Take kuma wani bakon yanayi mai kama da farinciki, ya ziyarcesa.
D’an bud’e idanunsa yayi Ahankali, ya saukesu akan wasu kyawawan tsuntsaye dake shawagi asaman wasu fararen furanni wani yalwataccen murmushi ya subce masa.
“Rayyern.”
Dr. Sulaiman dake zaune agefensa ya kira sunansa, fuskarsa d’auke da mamaki saboda, wannan ne karo na farko aduk rayuwarsu, daya taba ganin Rayyern din ya nutsu yana tunani, wanda da’alama kuma abu mai mahimmanci yake tunawa.
Jin sautin muryar Dr. Sulaiman acikin kunnuwansa ne, yasa shi juyowa batare kuma daya kalli Dr Sulaiman dinba yace.
“What happened?”
Idanu Dr. Sulaiman din ya zuba masa, saidai duk yanda yaso karantar yanayin Rayyern din bazai iya ba, saboda Miskiline na k’arshe, Dan kuwa gashi yanzu yanzun ya sanja mood din fuskarsa.
“What Happened?”
Rayyern din ya sake tambayar Dr. Sulaiman.
Jin hakanne kuma yasa Dr. Sulaiman girgiza kansa, cikin kuma kawar da tunanin dake ransa yace.
“No dama naga lokacin komawa lecture yayi ne.”
Agogon dake daure atsintsiyar hannunsa ya duba, Ganin lokaci na tafiya ne ya sashi mikewa, batare kuma daya jira su Dr. Sulaiman din ba yayi gaba.
Kaitsaye hall din nasu duk suka koma, tare da ci gaba dayin lecture.
Kamar kullum haka yau dinma 5:30 am dai-dai suka tashi daga lecture din, kasancewar kuma hazo ya bayyana agarin da kuma sanyi mai tsanani, shiyasa basu wani tsaya ba anatashi kowa ya kama hanyar masaukinsa.
Ahanyarsa ta dawowan ne kuma ya tsaya yayi musu takeaway, kamar dai yanda ya saba yi musu akowacce rana.
Cikin ikon Allah kuma yana isowa gida, aka fara yi musu ruwan dusan k’ank’ara.
Koda ya shigo cikin falon rigar suit d’insa da dusan k’ank’aran ya sauka akai ya cire, tare da ajiye ta akan kujera, Ahankali kuma yake karewa falon kallo.
Sauke idanunsa da yayi akan hulan Jannart din, dake yashe ak’asan carpet ne kuma, yasa shi fahimtar cewa ta d’an zauna afalon.
K’ofar d’akinta dake arufe gam ya kalla, kana cikin dan hanzari ya wuce d’akinsa, bayan ya ajiye ledan takeway din anan cikin falon.
Koda ya shiga bedroom kayan dake jikinsa ya rage, tare da daura towel akan waist d’insa, kaitsaye ya wuce bathroom yayi wanka had’e da d’auro alwala.
Koda ya fito daga toilet din har 6:20 tayi.
Ruwan dake jikinsa ya dan goggoge, bayan ya shafa mai ajikin nasa ne kuma, ya karasa gaban drawer’n sa, tare da ciro kayan da zai saka.
Kasancewar kuma ana sanyi sosai ne, ya sa shi saka wani dogon wandon jeans mai kauri, tare da long sleeve t shirt kana kuma ya daura babban sweater akan shigar tasa.
Bayan ya kammala kimtsa Kannasa ne kuma, ya d’auki key din motarsa ya fice.
Duk da cewar kuma har yanzu ba’a gama ruwan dusan kankaran ba, haka ya fita ya shiga mota zuwa masallaci, domin dama su y’an garin sun saba da irin yanayin.
Bayan an idar da sallan ne kuma ya zauna acikin masallacin, har saida akayi sallan Isha.
Wanda zuwa lokacin kuma sosai garin ya sake yin sanyi.
Hakanne ma yasa bai wani tsawaita addu’a ba ya nufo hanyar dawowa gida.
Duk da kuma cewar shidin yana cikin mota, amma hakan bai hanashi jin fitinannen sanyin dake tashi acikin garin ba.
Koda ya iso gida ko gama dai-dai-ta parking baiyi ba, da Dan sassarfa ya fito ya shige cikin falon.
Ajiyar zuciya ya dan sauke, kana ahankali kuma ya sauke idanunsa akan ledodin daya kawo, wanda suke nan kamar yanda ya ajiyesu, saboda babu alaman an tab’a.
Idanun nasa ya daga tare dakai dubansa izuwa kofarta.
Tsaida idanunsa akan kofar yayi baya ko kyaftawa, Yayinda shi kansa ya rasa me yake kallo, da tsammani.
Saidai kuma har acikin zuciyarsa abu d’aya yakeson sani, shine rashin cin abincin da baiga tayi ba, wanda baisan dalili ba, cause kullum Idan ya kawo abincin kafun ya dawo daga masallaci yake Ganin taci nata.
Numfashi ya fesar kana ahankali kuma ya dauke idanunsa daga Kallon kofar nata, batare kuma daya waiwayi abincin ba shima, kaitsaye ya wuce d’akinsa.
Koda ya shiga cikin dakin sweater din nasa ya cire, bayan ya rage hasken wuta ne kuma, ya koma ya kwanta akan lallausan gadonsa.
Kamar yanda yake kwance akan gadon nasa kuwa, haka itama Jannart ke kwance, Yayinda ta kanannad’e Kanta acikin blanket.
Saboda sanyin da akeyi ne kuma yasa, tunda yamma da ta shigo cikin dakin bata sake fita ba.
Ko yanzu ma batajin zata fita saboda batajin yunwa, kasancewar taci abinci da rana sannan tasha fruits salat.
Atana kwancen kuma wayarta ce ke rike ahannunta, tana Dan latsawa, game takeyi wanda da’alama kuma tana Jin dadin game din sosai.
Kasancewar ana sanyi sosai ne kuma, yasa tana rik’e da wayan ahaka har bacci ya dauketa batare da ta shirya masa ba.
*Rayyern.*
Ajiyar zuciya mai k’arfi ya kuma sauk’ewa akaro na barkatai, kana cikin dan yanayin kasalan da yakejin kansa aciki ya lumshe idanunsa.
Ahankali yakejin mood d’insa na sanjawa, ga kuma tsikar jikinsa da yakejin yana tashi.
Sannu ahankali kuma idanunsa dake lumshe, suka soma yi masa imagining nata, wanda hakan yasa take duk wata