Showing 93001 words to 96000 words out of 350584 words
“Sai kuma ni dana shirya na kuma gabatar JANNART IDI SALE DAKATA. Nake, mana fatan mu hade awani sati Idan Allah ya kaimu a huta gajiya.”
Cuttt haka masu d’aukan shirin suka katse tare da kashe cameras dinsu.
Dai-dai lokacin ne Kuma anan gidansu Rayyern din Zuciyar Abba tayi wani irin bugawa, saboda sunan Yarinyar da yaji acikin kunnuwansa.
“Jannart Idi Sale Dakata!!”.
Abba ya maimaita sunan acikin zuciyarsa, cikin sauri kuma ya d’ago da kansa ya kalli Mamy, wacce ita dinma shi take kallo, fuskarta dauke da tsananin mamaki.
Atare kuma suka sake maida kallonsu ga tv,n.
“Idan har sunan da yarinyar ta fad’a shine sunanta na gaskiya, To Lallai kuwa, wannan itace yarinyar da Barrister Kabir yazo musu da maganarta.”
Abban ya fad’i haka azuciyarsa, fuskarsa cike da tsananin mamaki, hadi da tu’ajjudin faruwar hakan.
Tuno wani abu da yayi ne kuma yasa Lokaci daya ya saki wani irin murmushi, mai dauke da tsananin jin dadi, hadi da cin nasara.
Tabbas ayanzu ya sake gaskatawa, cewar Nesa tazo ta kusa.
Acan TV station din kuwa Zumbur haka Dr Rayyern din ya mik’e tsaye, wanda hakan yasa cikin sauri MD da kuma sauran assistance managing director hadi da manyan masu muk’amai na tashan suka nufo wajen Rayyern din kaitsaye, hannayensu suka dinga mik’a masa daya bayan daya suna gaisawa cikin mutuntaka.
Inda MD da farinciki yasa bakinsa kasa rufuwa yace.
“Mungode Kwarai Dr. Rayyern, Allah Ubangiji yasa kafi haka, nida sauran ma’aikatan wannan tasha, muna godiya agareka, daka samu daman zuwa wannan tasha.
Tabbas zuwanka ya sake daga darajar tasharmu.”
Yar sauk’ak’ekk’iyar Murmushi kawai yayiwa MD’n, Yayinda MD kuwa yasa a daukowa Dr. Rayyern din kyauta ta musamman, wanda sukayi dan nuna godiyarsu agaresa.
Salman, Aysha Lawal da kuma Aunty Fauziy D Sulaiman dake gefe kuwa, hannayensu suka d’agawa Jannart alaman jinjina, kowannensu fuskarsa cike da farincikin, irin nasaran da Jannart din ta samu, Domin kuwa ta kafa tarihin da akab gidan television’s din dake Nigeria babu wanda ya tab’a kafawa.
Ta kawo musu babban hazikin Dan kasuwa kuma Doctor, mutumin da kowa yake fatan ganinsa, yau gashi Jannart din ta kawosa ta kuma bayyanawa duniya fuskarsa, daya jima yana b’oyeta.
Murmushi Jannart din tayi musu, tare kuma da k’arasowa ta kalli Salman, wanda azahirance yana cikin tsananin farinciki, akasin hakan kuwa, shine Sam bayajin dadin zuciyarsa, saboda tun zaman Jannart da kuma Dr. Rayyern din daya gani awaje daya, yaji zuciyarsa ta karye, badan komai ba kuwa saidan tsananin matching din da yaga sunyi, sosai suka haska tamkar wasu taurari, sai kuma ayanzun ya sake tabbatarwa da kansa, cewar kwata-kwata ma Jannart Dakata ba sa’ar sa bace, Jannart matar manyan mutane ce.
Kana kuma Jannart zara ce acikin taurari, furta wani abu daya shafi so agareta, kuwa tamkar karambani ne, saboda ya sani bashi da wannan matsayin.
Haka dai jikinsa adan sanyaye ya juya suka rufawa su MD din baya, wanda tuni sun nufi hanyar waje, Dan raka Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara mota.
Cikin masu rakiyan kuwa harda Asiya, wacce takejin kamar ta fashe da kuka, ko tasa ihu.
Badan komai ba kuwa, saidan ta samu ko kallo daya ne Dr. Rayyern din yayi mata.
Jannart kuwa kaitsaye Office dinsu ta wuce, batare da tabi yan rakiyar ba, Sam ita rakasa ma baya gabanta, hasalima mamaki take akan yanda taga, y’an Office din nasu suna karramasa, Tabbas Koda ga wahalan da tasha wajen nemansa, tasan cewar shidin babban mutum ne.
D’an tab’e bakinta tayi alokaci da ta samu waje ta zauna.
Hakanan takejin zuciyarta wasai, tamkar an zare mata wani mashi dake sukanta.
“Alhamdulillah Allah, Kai katsaramin komai, yanzu bazan rasa aikina ba, bana kuma da wata fargaba, Thanks for everything Allah.”
Ta fad’i hakan abayyane Cikin kuma tsananin farinciki, dajin dadi.
Saboda duk wata fargabanta yanzu ya yaye.
Acan compound din tv station din kuwa, har wajen mota su MD suka rako Dr. Rayyern, bayan sun bashi kyautar karramawa.
Kasancewar kuma tun kafun su isa, Hadi'nsa ya bud’e masa murfin motar tasa ne, hakan yasa yana zuwa batare da wani b’ata lokaci ba ya shiga ya zauna.
Still harya rufe murfin motar kuma godiya su MD sukeyi masa, tare dayi masa fatan sauk’a lafiya.
Anutse kuwa Hadi yaja motar suka fice daga cikin gidan tv’n.
Fuska Asiya ta had’e tamkar zata had’iyi zuciyarta haka takeji.
Lallai tayi takaicin wannan ranan, saboda ko kallo daya bata samu daga wajen Dr. Rayyern din ba, hasali mai irin halittarta ma baisan tana wajen ba.
Dan Kallon kanta tayi, can cikin zuciyarta kuma taja tsaki, tare da cewa.
“Tayaya ma zai kalleni, tunda akwai irin waccar mayyar aduniya, natsaneki wallahi Jannart natsani ma Koda ganinki, saboda ke ne zaman office dinnan ya fara yimin kunci, kinzo kin hanani sakat, wai kawai saboda kina da kyau, mcheewww.”
Tak’are maganar nata da jan tsaki tare da juyawa ta koma Cikin office din, dan zuwa yanzu ita kad’ai aka bari awajen.
Acan cikin Office din kuwa, MD dakansa ya shigo cikin Office din su Jannart din, tare da bud’e hannayensa ya soma tafa mata.
Aikuwa Ganin haka yasa duk sauran ma’aikatan suma bud’e hannayensu suka soma tafa mata.
Cike da jinjina hadi da yaba k’wazonta MD yace.
“Congratulation Jannart, Lallai kin cika hazikar yar jarida, na kuma jinjinawa kwazonki, Tabbas samun irinki acikin aikin jarida abune mai kyau, ayau ta sanadiyarki tasharmu ta sake daukaka, kin shammace mu Kwarai, dole ne mu baki lambar yabo, zaku ma muyi miki karramawa ta musamman.”
“Kwarai kuwa Jannart hakika kinyi Namijin kokari, Tabbas kin cika hazikar Mace mai kishi da kuma son aikinta congratulations.”
Cewar Aunty Fauziya D Sulaiman.
Jannart din kuwa murmushin daya bayyana kyawawan hakwaranta tayi, cikin tsananin jin dadi tace.
“Congratulations to you all my colleagues, Domin duk wannan nasaran nasa meta ne da k’arfafawar guiwanku, musamman Salman, Thank you so much Salman.”
Murmushin Jin dadi duk sukayi, Yayinda Salman kuwa ya sunkuyar da kansa kasa yana murmushi.
Asiya dake gefe kuwa ji take kaman tayi hauka, tsabar k’unci takaici da kuma bak’in Cikin daya cika zuciyarta.
Haka dai suka ci gaba da tattaunawa atsakaninsu, Yayinda fuskar kowannensu ke dauke da tsananin farin ciki.
Amma banda na Asiya da har hawayen takaici saida suka tara.
MD kuwa yau din da kansa yasa akayi musu order’n delicious food, tare da kayan drinks.
Anan cikin babban falon da suke ajiye baki, suka gudanar da d’an kwarya kwaryan party.
Inda kuma sukayiwa Jannart din tanadin Karin matsa yi na musamman.
Bayan sun gama yar kwarya kwaryan Partyn nasu ne kuma ta dau Jakarta Kai tsaye ta wuce, gida zuciyarta cike da tsananin farinciki.
Yayinda daga can b’angaren Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara kuwa, daga tv station din kaitsaye gidansu ya nufa.
Suna isa bakin gate din kuwa Baba Hadi ya danna horn, cikin sauri da kuma azama Baba Maud’o ya karaso ya bude musu gate din, direct Baba Hadi ya tura motar cikin gida, tare da dai-dai-ta parking dinta a parking space.
Ahankali Rayyern din ya bud’e motar ya fito,
Kana ya juya ya nufi wurin da Baba Maud’o yake tare da ɗan longoɓar da kai alaman gaisuwa.
Murmushi Baba Mauɗo yayi tare da mishi sannu. kafun kaitsaye ya nufi babban falon gidan.
Inda Mamy da Abba dasu Ramadan ke zaune.
Shigowarsa cikin falonne kuma yasa duk suka d’ago Kai suka kalleshi, Riyyam-nsra ne ya taso da d’an hanzari ya rungumeshi, tare da cewa.
“Gaskiya ko Hamma Rayyern kaina musamman ne, ka iya amsa duk wata tambaya da akayi Ma.”
Kansa kawai ya Dan jinjina saboda duk ji yakeyi kansa a gajiye, karasa shigowa cikin falon yayi, tare da yiwa Abba da Mamy sannu da gida.
“Yauwa Rayyern sannu da dawowa.”
Mamy ta amsa masa, Yayinda Abba kuwa Da Kai ya amsa masa.
“Hamma Rayyern congratulation.” Ramadan ya fad’a k’asa k’asa yayinda yake Dan danne dariyarsa, badon komai ba kuma saidan sanin halin Yayan nasa da yayi, kwata-kwata baya son yawan magana amma kuma yau gashi wata tasashi yayi ta magantuwa.
Da kai kawai Rayyern din ya amsa masa, batare daya zauna acikinsu ba kuma kaitsaye ya wuce part d’insa.
Wanka yayi tare da dauro alwalan sallan magriba, bayan ya kimtsa kansa acikin wasu kaya marar nauyi ne kuma, ya fito inda dukansu suka had’a hanya wajen zuwa masallaci.
Koda sukaje masallacin kuwa kamar Koda yaushe basu dawo ba saida aka Sallame sallan Isha.
Suna dawowa gidan kuwa suka samu Mamy ta had’e musu lafiyayyen dinner, hakan yasa duk suka k’arasa kan dining table din suka zazzauna.
Yau din kuma Riyyam-nsra ne da kansa ya amshi Mamy wajen yin saving dinsu, shida kansa ya zubawa kowa abincin banda Abba da Mamy ta zuba mishi nashi, sannan da kansa ya had’awa Hamma Rayyern din tea.
Bayan ya kammala had’a musu ne kuma, kowa ya soma cin abincinsa, anutse Abba ya d’ago da kansa ya kalli Rayyern cikin jinjina da kuma ya bawa yace.
“Tabbas hirar da akayi da kai yau, tayi armashi da kuma ma’ana, sannan shawarwarin daka bayar shawara ne masu kyau, gaskiya na jinjina maka,”.
Sai kuma ya ɗan tsagaita kana ya ɗan kalleshi tare daci gaba da cewa. “Amma da kashawarce ni kafun hakan, To fa da bazakaje ba.”
Zazzafan tea din dake bakinsa ya had’iya, kana cikin yin kasa dakai yace.
“Kayi hakuri Abba nima banaje Dan son raina bane, naje ne kawai saboda nayi musu alk’awari, sannan banason wanda aka bawa kwangilar nema na din ya rasa aikinsa, kamar yanda manyansa suka bashi zab’i.”
Kai Abban ya jinjina, batare kuma daya ja zancen yayi tsawo ba yace.
“Shikenan To Rayyern Allah ya taimaka ya tsare min kai.”
Da Ameen duk suka amsa.
Bayan sun kammala cin abincinne kuma, kaitsaye Rayyern din ya wuce daki’n sa.
Yayinda Ramadan da Riyyam kuwa suka dawo Cikin falon suka ci gaba da hirararsu, daga karshe ma game suka had’a, suka soma yi.
Ganin hakanne kuma yasa Abba da Mamy wucewa sashinsu.
Rayyern kuwa yana shiga dakinnasa kwanciya yayi, Cikin mintuna kad’an bacci yayi nasaran daukarsa.
Acan falon kasa kuwa Ramadan da Riyyam, duk kowannensu saman kujera ya d’ale ya kwanta, su kansu ba zasu iya sanin tayaya nema bacci ya kwashesu ba, kowannensu da abun buga game din ahannunsa, haka sukayi bacci kasancewar dare ya nisa.
A sashin Jannart kuwa yau tun 9 tayi baccinta mai cike da nutsuwa, Yayinda takejin zuciyarta wasai babu sauran wani fargaba.
Washegari.
Friday.
Tun tashinsa karfe 7 ya gama shirya kansa, saidai shigarsa ta yaudin ta banbanta dana kullum.
saboda wani riga da wando mai Taushin gaske ya saka ajikinsa, sabanin suit daya saba sakawa akowacce rana.
Sosai kayan Yayi masa kyau, musamman daya daura boyfriend jacket mai kyau akan kayan.
Wasu bakaken shoe masu tsada da watch ya daura a tsintsiyar hannunsa .
Bayan ya gama kimtsa kannasa ne kuma, ya dauki wayarsa tare da duba sakonnin da suke ta shigo masa ta Twitter, saboda yanda duniyat Twitter din ta Dinke da hotunansa, gaba daya shi kawai ake watsawa, da kuma bayani akan hirar da akayi dashi.
Kashe data dinnasa yayi, tare da juyawa ya nufi k’asa kaitsaye.
Anan cikin falon ya samu su Abba, harma da Riyyam nsra wanda yake ta hamma da alama bacci bai ishesa ba.
Dan Koda asuba ma Abba ne daya fito yagansu kwance afalo, shi ya tashesu tare da saka su agaba suka wuce masallaci.
Karasowa yayi ya zauna akan dining table din, bayan kuma Mom tayi saving dinsa ne, ya soma cin abincin atsanake, saidai kuma bai wani ci sosai ba, ya mik’e tsaye.
Yaudin ma dai atare suka fita shida Ramadan, saidai kuma Riyyam-nsra ya dage kan cewar, tare zasu tafi Hospital shida Ramadan.
Hakan kuwa akayi inda Ramadan din ya dauki Riyyam din suka wuce Hospital, shikuwa Rayyern dama yau ba Hospital din zaije kaitsaye ba.
Bayan anwangale musu gate din gidan sun fito da tsalatsalan motocinsu ne, kaitsaye su Riyyam suka wuce Hospital, shikuwa Company’n sa ya nufa.
Koda ya isa company din kuwa ya samu, ma aikata madasa in juna suna ta aikinsu, Domin yau din injunan da zasuna had’a kwalaye da buhuna ake kafawa amazauninsu.
Sosai ya jinjina kansa ganin yanda aikin nasu ke tafiya yanda ya kamata.
Kasancewar kuma akwai aikin da zaiyi ne yasa, kaitsaye ya haura sama inda Office d’insa yake.
Acan gida kuwa Baba Maud’o na zaune yaji karan horn din mota, atunaninsa ko su Rayyern dinne suka dawo, hakan yasa ya wangale gate din gidan.
Barrister Kabir kuwa dake cikin motar, kaitsaye ya shigo da motar tasa cikin gidan.
Bayan ya gama dai-dai-ta parking din motar tasa ne kuma, ya bud’e ya fito, saidai kuma ayau din bashi kad’ai yazo ba, atare dashi akwai Dr.Sajo.
Karasowa wajen Baba Maud’on sukayi tare da bashi hannu sukayi musabaha.
Baba Maud’o kuwa fuska asake ya amsa musu, sannan kuma da kansa yayi musu iso zuwa cikin gidan, har cikin babban falon kuma ya kaisu.
Ganinsu ne kuma yasa Abba fadada fara’arsa, tare da sawa Mamy tayi musu tarba maikyau.
Bayan sun gaggaisa ne kuma, Barrister Kabir ya gyara zama, tare da Kallon Abban ya gabatar masa da Dr. Sajo.
Haka dai suka Dan tattauna, agame da abunda suke shirin had’awa.
Bayan kuma sunyi tattaunawa mai tsawo ne, suka yanke shawara akan cewar yau Idan an sauk’o daga sallan Jumm’a za’a daura auren.
Da wannan batun sukayi sallama.
Inda Abban ya rakosu har waje, bayan sun tafi ne kuma ya zauna anan awajen Baba Maud’o suka d’an soma tattauna wasu batu.
Acan Office din Rayyern kuwa. Ganin 11:30 am ne yasa shi mik’ewa. Tare da barin duk wani abu da yakeyi.
Kaitsaye kasa ya sauko, saboda yanason sake komawa gida saboda yin shirin zuwa masallaci.
Koda ya shiga motar tasa kuwa cewa Hadi yayi su wuce gida.
Take kuwa kaitsaye suka nufo gida.
Koda ya dawo gidan, wanka ya sakeyi inda ya shirya kansa cikin riga da wando da kuma babbar riga, ta hadaddiyar getzner’n da ak’alla kudinta ya haura sama da 100k, sosai kayan sukayi masa kyau kasan cewar kalarsu lemon green ne kana zaren da aka watsawa garen su kuma shudi ne da fari da baƙi sosai sukayi mishi kyau, musamman daya kafa hulan zanna bukar blue color Kansa, ga kuma wani tsadadden takalmin toms suma blue da agogo daya saka, Tabbas yayi kyau kwarai.
Domin shigar tasa bawai gama gari bace, shigace ta musamman, wacce ta kara bayyana kyau da kwarjininsa.
Bayan ya gama kimtsawa ne kuma, ya feshe jikinsa da turare tare da sauk’owa k’asa, saboda jiyo hayaniyar Ramadan da kuma Riyyam da yayi, wanda suma sun shirya ne tsab, Cikin sabin getzners dinsu, masu kyau.
Kallonsu Riyyam din kawai yayi kana a takaice yace.
“Ka kwaso kayanka ka dawo nan, ka dena kwana a hotel”.
Ya ƙare mgnar cikin bada umarni.
Cikin yanayin ba zata jin mgnar Riyyam-nsra ya kalleshi da alamun zaiyi mgn sai kuma yayi shiru.
Ganin tuni ya fice batare kuma daya ƙara ce musu komai ba.
kaitsaye ya fice daga cikin falon.
cikin sauri-sauri kuma ya nufi motarsa saboda bayason rasa hud’uba.
Bayan ya fita daga gidanne kuma suma suka fito inda suka shiga motar Ramadan daketa murna da farin cikin mgnar Hamma Rayyern ɗin nasu.
kaitsaye masallacin Alfruq’an suma suka wuce.
Acan gidansu Jannart kuwa hakanan tun tashinta yau din takejin zuciyarta na yawan tsinkewa, ga kuma wani irin faduwar gaba da takeji akai akai.
Sai-dai rashin sanin takamaimai abun yi, yasa ta fara ambaton sunan Allah a cikin zuciyarta.
Barrister Kabir kuwa, bayan yayi shirin zuwa masallaci, yau din ko motarsa bai dauka ba, da kafansa ya fito inda ya tako har bakin titi, taxi ya tara, tare kuma da yiwa mai taxi din bayanin inda zai kaishi.
Wanda kuma bako Ina bane face masallacin dake gefen gidan Dr. Sajo.
Koda mai taxi din ya saukesa a masallacin, kaitsaye wajen Dr. Sajo ya nufa, atare sukayi sallan Jumma’a, bayan sun idar da sallan ne kuma, Dr. Sajo ya fito musu da mota.
Kaitsaye suka nufi unguwar Nassarawa GRA.
Yayinda acan masallacin alfurq’an kuwa, bayan an sallame sallan jumma’an, Ramadan da Riyyam-nsra suka sulale, kaitsaye basu zame ko inaba kuwa sai kasuwa, saboda kafun su fita Abban ya basu kudi yace su sayo masa huhun goro da kuma katton katton na mintuna.
Sudai haka suka je suka sayo batare da sanin na meye bane.
Koda suka dawo gida, anan cikin falon Abban suka jibge huhun goron da kuma mintunan da suka sayo.
Dawowarsu kuwa yayi dai-dai da isowan su Barrister Kabir da kuma Dr. Sajo.
Inda Abba da kansa yazo yayi musu iso zuwa babban falon k’asa.
Bayan sun zazzauna ne kuma ya fita ya kira Baba Maud’o, inda yace.
“Baba Maud’o ka shigo, yau abun na musamman za’ayi acikin gidannan, Insha Allah yanzu za’a daura auren Rayyern.”
Idanu Baba Maud’o ya d’an fitar, lokaci daya kuma yaji wani irin farinciki ya lullub’e sa, wanda hakan yasa Cikin matuk’ar jin dadi yace.
“Masha Allah lokaci yayi kenan, yau dai Ranar Rayyernu ta tsaya, To Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.”
Da “Ameen.” Abba ya amsa.
Dai-dai lokacin kuma suka shigo cikin falon shida Baba Maud’o.
Acan waje kuwa yanzu motar Rayyern din ke isowa, Jin sunyi horn ba a bud’e musu bane kuma, yasa Hadi fitowa da kansa ya bud’e musu gate din suka shiga ciki.
Da mamaki Rayyern yake Kallon bakuwar motar dake fake afarfajiar gidan nasu, yayinda daga gefenta kuma motar Usman PA ne wanda yazo babu jimawa, kuma shima ya shigo yana can cikin falon Abban.
Ahankali ya bud’e murfin motar ya fito, Yana fitowa dinne kuma, Abba ma ya fito daga cikin falo, Kallon Rayyern din yayi, lokaci guda kuma ya hade fuskarsa, cikin tsare gida, ta yanda yasan Rayyern din bazai samu daman tambayarsa wani abuba yace.
“Hadi ka shigo daga ciki, kaima Rayyern ka biyoni.”
To Hadi yace tare da rufawa Abban baya, shima Rayyern din haka cikin daurewar Kai yabi bayan Abban nasa.
Suna shiga cikin falon kuwa, yaji zuciyarsa tayi wani irin harbawa, saboda yanda yaga mutane atare.
Daya bayan daya yake bin kowannesu da kallo, Koda ya sauke idanunsa akan Barrister Kabir, ji yayi wani irin abu ya tsarga mai.
“Oh My God meye kuma wannan mutumin ya sake zuwa yi agidan mu? Waishi bazai tab’a fahimta bane, nace masa ban shiryawa auren yartasa ba banasonta wai ko ana dole ne ai gaggawa dai bata da kyau.”
Yayi maganan azuciyarsa, tare da yin kicin kicin da fuskarsa.
Gudun kada yaji wata magana ta taso ne kuma