Showing 282001 words to 285000 words out of 350584 words
zai huda k'irjinshi yasakata,
Saman yalwataccen gashin kanta da yasha gyara ya cusa fuskarsa yana shak'ar k'amshin da ke fita akanta,
A hankali yasakar mata kiss a tsakiyar kanta, hannunshi yad'ago cikin kasalar da tagama rufeshi yad'an d'ago wuyanta yana shafawa cikin wani irin salo me rikitarwa still dai fuskarshi na cikin gashinta yana sakar mata da kiss ta ko'ina har ya gangaro da kanshi a goshinta yana cigaba da kissing d'inta...
Ji tayi gaba ɗaya numfashinta yana shirin rabuwa da jikinta saboda yanayin da yasakata a ciki, cikin kasala batare da ta bud'e idanunta ba tashiga girgiza mashi kai murya can ƙasa take cewa.
“Uuhm uhm uhm uhm Naaan”.
Cigaba yayi da abinda yakeyi sabida ya fara fita haiyacinsa.
wani irin shock takeji aduk shafawar da yakeyi ma wuyanta jin hannunshi tayi daga wuyan nata yana yo k'asa dashi ahankali zuwa k'irjinta, cikin sauri ta aro jarumta tatureshi tare da k'wace jikinta takoma gefe tana kiciniyar gyara rigarta tana sauke numfashi dak'arfi.
Bud'e rinannun idanunshi yayi da suka koma kamar rushi cikin rashin k'arfin jiki da kasala yaja k'afafunshi yazauna bakin gado gabad'aya jikinsa karkarwa,
Dafe kanshi yayi da duka hannuwanshi biyu, ganin yadda yake karkarwa ne yasa ta ƙara jan baya jikin bango tajingine kanta tana cigaba da sauke ajiyar zuciya cike da tsoro da mamakinsa..
Sun kusan minti biyar a haka babu wanda ya cewa ɗan uwansa komai.
Da ƙarfi-ƙarfi yake sauƙe numfarfashi,
Na tsawon lokaci sai yanzu ya fara jin numfashin sa na sauƙa a hankali,
dak'yar yasamu nutsuwa ta fara tasauƙar masa gyara zamansa yayi tare da danne D ɗin da dake zillo d'ago rigannun idanunshi da har lokacin basu koma ainahin kalarsuba yakalleta saida yad'an saita kansa sannan dak'yar ya iya bud'e bakinsa cikin wata iriyar murya da yake mata magana da ita wasu lokutta mabanbanta yace.
“Yayanki Azeez ne ya zo”.
Cikin mamaki ta kalleshi ido waje tace.
“Ya Azeez nan yana ina?”.
Da yatsarshi ya nuna mata hanyar falo.
Dan ya kaasa bata amsa saidai yad'aga mata kai dan koda yayi mata magana ba k'aramar jarumta ya auro ba har ya iya bud'e baki yayi magana.
Wani ɗan tsalle mai cike da jin dad'i da farin ciki tayi lokaci guda tayi saurin juyawa zata nufi falo.
Cikin wani irin zafin nama yamik'e tare da ruk'ota,
da sauri ta juyo takalleshi cike da mamakin tsaidata da ya yi.
Idanunshi ya zuba mata a cikin nata cikin muryarsa da har lokacin bata koma dai-dai ba yace.
“Jannah ahaka zaki fita?”.
Kallon jikinta tayi sannan taturo d'an k'aramin bakinta cikin muryar shagwa'ba tace.
“Ya Azeez d'ina ne fa”.
Wani irin kallo yayi mata wanda ita kanta bata gane fassarar kallonba da yafi kama da harara yace.
“Toh inma Ya Azeez d'inki d'inne sai akace kifita gabanshi a haka ya kalle min mata,
Wai bakisan cewa ke a yanzu matar aure bace da da yanzu ba d'aya bane bafa Janna ki kiyaye min mallakina ban amince ki bari ya ruggumeki ba, ko hannunki ya taɓa wlh Allah ya isa bazan kuma yafeba dan na lura shi baisan irin matatan da suke dai-da shi da suka dace ya rugguma ba”.
Batare da ya jira jin abinda zata ceba yajuya yajawo hijab d'inta da yake ajiye gefen gado da kanshi ya yasaka mata, gashin gaban kanta da yad'an fito ne yasa hannu yagyara mata shi sannan yakama hannunta ahankali suke takawa su dukansu jikinsu a mace suka fito falo.
A dai-dai lokacin da Azeez ya katse wayar da sukeyi da Abba yad'ago kanshi batare da ya janye wayar daga kunnenshi ba yasauke idanunshi akansu.
Tamkar wata da tauraro haka ya gansu, wani irin fad'uwar gaba ne yaziyarceshi wanda shi kanshi baisan dalilin hakan ba lokacin da yaga sun fito hannunsu sark'afe da na juna Rayyern yana jifanta da wani irin shu'imin kallo me wuyar fassarawa.
Kallon mamakine yake binsu da shi har suka iso tsakiyar falon, sai a lokacin Jannart tad'ago kanta da yake sunkuye tana kallon yadda Naan yake murza yatsarsa manuni cikin tafin hannunta.
Ganin yayan nata yasa ta janye hannunta daga cikin na Rayyern cikin tarin farin ciki tace.
“Oyoyo Ya Azeez na”.
Murmushi yayi tare da miƙa mata hannu.
Cikin sauri taje tazauna bisa kujerar da take fuskantar wadda Ya Azeez yake zaune a kai.
Shi kuwa Rayyern kai ya jinjina cikin jin sanyi a ransa da bata kama hannun Azeez ba wani kallon takaici yakewa Azeez ɗin dan har yau yana jin ciwon ruggume mishi Janna da yayi.
Shi kuwa Azeez ido ya zuba mata.
Cikin matsanancin farin ciki da take jinta a ciki tace.
“Ya Azeez ina kwarka”.
Sai a lokacin Azeez yasauke hannunsa daya miƙa mata, aro jarunta yayi tare da sakin murmushi yace.
“i miss you so much my Jannart”.
Murmushin yaƙe tayi ganin yadda Rayyern yayi kici-kici da fuska.
“Ayyah Azeez na ya kwana biyu”.
“Alhamdulillah Jannart da fatan na sameki lafiya?”.
Ya faɗa yana matsowa bakin kujerar.
Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi tare da cewa.
“Lafiya lau muke, ya su Daddyna da Abbull ina Mummy na?”.
“Duk suna nan lafiya lau Jannart”.
yafad'a still dai idanunshi suna akanta dan ta kasa sakewa dashi kamar yadda suke tun tasowarta, duk da yaga farin cikin ganinsa cikin kwayar idanunta.
Sai a lokacin Rayyern yamatso shima fuskarsa d'auke da murmushi mai cike da kishin Azeez ɗin yasake mik'a masa hannu sukayi musabaha kana yace.
“Sannu Ya Azeez ya k'asar taku da gajiyan tseren bin Matata?”.
Murmushi yake Azeez yayi tare da cewa.
“Toh Alhamdulillah gamu a cikinta,
Yoh naga wani can da ban saniba da yar kekkyawar ƙanwata data ɓace mana ba dole inyi tseren bibiyaba”.
Wani murmushi isa Naan yayi tare da ɗan juyowa ya kalleta cikin juya murya a narke yace.
“Sweet heart kice mishi ya kwantar da hankalinshi mijinki na kula dake da kyau”.
Kamar sokuwa haka kalamansa suka medata, sabida tarin mamaki kawai sai ta zuba mishi idanun.
Shi kuwa Azeez wani irin maƙoƙone ya tokare masa zuciya.
dai-dai lokacin wayarsa tayi k'ara alamun shigowar text nan yad'auko wayar yana dubawa.
Shi kuwa Rayyern cikin wani irin taku ya juyo zuwa inda take,
A kan hannun 1 seater d'in da take zaune ya zauna samansa.
Cikin tsareta da maraitattun idanunsa yakamo tafin hannunta yahad'a da nashi yarike tare da ɗaga mata girarsa ɗaya.
Kana ya karkaɗa mata harshensa.
Wani irin yarr taji lokacin da taushin tafin hannunsu yahad'u da na juna, k'ara sunne kanta tayi cike da jin kunya tana mai kiciniyar zare hannunta,
Murmushi Rayyern yayi yad'an sunkuyo da kanshi yana lek'a fuskarta yana mai mata mgna raɗa-raɗa yadda Azeez zai ɗan iya jinsu.
“Sorry Babyna, na gajiyar da ke ko, na hanaki bacci ko, kiyi haƙuri zan goyaki kiyi baccinki in biya bashi”.
Yadda yayi mgnar ne yasata dole ta narke idanu tare da zuba masa su.
Dai-dai lokacin Azeez yad'ago kanshi ya kalleshi.
Wani irin bugun zuciya ne yaziyarceshi lokaci guda yanayin fuskarsa tad'an canza, gyaran murya yayi tare da k'ok'arin saita nutsuwarshi sannan yamik'e tsaye.
Su dukansu d'ago kai sukayi suka kalleshi, cike da shagwa'ba Jannart tace.
“Ya Azeez ya naga ka mike?”.
Murmushi yayi cikin ɓoye damuwarshi yace.
“Zan tafine K'anwata ana jirana”.
ledojin da yashigo da su ne yad'auko yamik'a mata yana cewa.
“Ga wannan ƙanwata ki kula da kanki kinjiko kin san matsalarki banda shan sanyi”.
Ya ƙare mgnar yana jujjuyawa ya kalli tsakiyar falon nasu.
Yayinda Rayyern kuwa ya taune lips ɗinshi na ƙasa yana mai tsaresu da ido.
Azeez kuwa,
Cikin juya kai yace.
“Gashi gidan naku sam babu tsarin tsare lfy daga sanyin ƙasar”.
Cikin yin fiki-fiki da ido Rayyern ya kalleshi tare da cewa.
“Ina wadar da ita da ɗumin jikina ne shiyasa ba buƙatar hita ko hura wuta a cikin falon ko ba hakaba my life?”.
Ido ta zura mishi kamar yar yaye.
Shi kuwa Azeez rumtse idanunshi yayi tare da miƙa mata ledan.
Hannu tasa ta amsa tana me Marairaicewa tace toh.
“Ya Azeez ammah dai zaka dawo ko? Kuma kaga ko ruwa baka sha ba fa?”.
A karo na biyu yayi murmushi yace.
“Eh Jannart idan nasamu lokaci zan dawo muyi hira, yanzu me kikeso inzo maki da shi idan zan dawo?”.
Da sauri ta kalli Rayyern sabida jin yadda ya matse hannunta,
Sai kuma ta kalli Azze da yayi gyaran murya,
Itama murmushin tayi tace.
“Bana buk'atar komai Ya Azeez zan dai saurari lokacin da zaka zo”.
Jinjina kai yayi yace.
“In sha Allahu”.
sannan yamaida kallonshi ga Rayyern da har lokacin hannunshi yana cikin na Jannart yana d'an murzawa,
Wani irin takaici ne yaji ya cikashi ammah yadaure ya'boye 'bacin ranshi yace
“Toh Rayyern ni zan wuce. A kular min da ƙanwata kada sanyin Mascow ya illatamin ita”.
Sai a lokacin Rayyern yad'ago yakalleshi fuskarsa d'auke da murmushi keta yace.
“Tun yanzu mun d'auka wuni kazo mana kada ka damu in dai ina raye babu abinda zai cutarmin da ita Al'jjanata ce fa ta duniya dole in kula da ita ko My Janna?”.
Rai a jagule Azez yace.
“Nima haka naso Rayyern saidai jiran da akeyi min ne zai sa intafi yanzu ammah insha Allahu zan dawo wata rana”.
“Toh shikenan muna nan muna jiran dawowarka Ya Azeez”.
Murmushi Azeez yayi yace.
“In sha Allah”.
Mik'ewa Rayyern yayi har a lokacin hannunsu suna sark'afe da na juna nan ita Jannart tamik'e, cikin sauri Azeez yawuce gaba suna biye da shi a baya suka rakashi har wajen k'ofa, sukayi bankwana bayan ya d'aukar ma jannart al k'awalin sake dawowa gidan nasu, saida suka sake musabaha da Rayyern sannan yatafi Jannart tana d'aga mashi hannu.
Bayan ya tafi suka dawo falon suka zauna nan tabud'e ledojin da yabata riguna ne tagani irin na sanyi masu kyau ciki farin ciki tad'aga tana gani sannan tajuya takalli Rayyern tace.
“Naan!”.
Bai kulataba sai tura baki da yayi kamar yaro ƙarami ya kwaɓe fuska.
“Naan kalli rigunan da Ya Azeez yakawo min masu kyau.
Allah yayi mashi al'barka kamar ya sani daman sanyi na damuna a garin nan, kalli wannan rigar!”.
Tafad'a a lokacin da take d'aga wata rigar sanyi me kyau
Sai a lokacin yad'ago yakalleta fuska yad'an 'bata kad'an yace.
“Rigunan ma basu da kyau”.
Cike da mamaki tace. “Naan basu da kyau fa kace? Kallesu fa”.
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Eh basu da kyau”.
bai jira jin abinda zata ce ba yamik'e yanufi bedroom d'inshi.
Wordrobe d'inshi buɗe bude yad'auko wata leda, kana ya juyo yafito.
Inda ya barta ya sameta a tsaye a yadda yabarta rik'e da rigunan.
Amsar na hannunta yayi yamaida a cikin ledarsu yawurga a bayan kujera kana yace.
“Bana son wannan”.
Da idanu tabi kayan da yawurga shima kallonta yake yamik'a mata ledar da yafito da ita, yace. “Amshi wannan kisa”.
Amsa tayi cike da mamaki da sanyin jiki tace.
“To na wanene wannan ɗin?”.
Batare da ya janye idanunshi akanta ba yace.
“Duba kigani da wannan da na yayanki wane yafi kyau?”.
Batare da ta ce komai ba tabud'e ledar tafito da rigunan sanyi ne masu masifar kyau da taushi kala ukku, pink, brawn nd black irin masu gashin nan, ita kanta sosai taji rigunan sun burgeta.
Dagowa tayi takalleshi har lokacin idanunsa suna kanta, hannuwansa hard'e a kirjinsa ya d'an karkata kai gefe yana jira yaji abinda zatace,
Sunkuyar da kanta tayi tana kallon k'asa cikin tausasawa da muryarta irin ta shagwa'ba tace.
“Duk suna da kyau sosai ka iya zaɓi ammah ina son na Yayana”.
Ciza lips d'inshi yayi sannan cikin sanyin muryarsa yace
"Na Yayanki kikeso ko na mijinki?”.
Ɗago kai tayi takalleshi ganin ya tsareta da idanunshi,
hannuwanshi suna hard'e a k'irjinshi.
Murmushi tayi batare da ta bashi amsar tambayarshi ba tace. “Nagode sosai Naanu Allah yak'ara bud'i”.
Lumshe idanunshi yayi cike da jin dadi sannan ya jinjina mata kai, batare da ya ce komai ba yawuce bedroom d'insa.
A bakin gado ya zauna yana mai sakin tattausan murmushi, ya d'auko system dinshi yana fara aiki da aka turo mashi ta email daga campany yanayin aikine cike da farin ciki.
Ita kuwa Jannart.
Cikin sanyinta tad'auki ledar tawuce bedroom d'inta tana shiga ta'adana kayan cikin wardrobe.
Juyowar da zatayi ta hango wayarta da ke saman bedside tana haske da tafara ringing, cikin sanyinta taje tad'auko wayar ganin sunan Aunty Fauziyya ya bayyana a screen d'in wayar yasa tayi murmushi saida tazauna bakin gado sannan tayi picking tare da yin sallama
Daga chan 'bangaren aka amsa
Gaisawa suka da Aunty Fauziyya.
Gyara zama jannart tayi tace.
“My Aunty ya aiki?”.
"Alhamdulillah Jannart, ya mijin naki?”.
Saida takalli k'ofa sannan tace.
“Yana nan lafiya lau my Aunty”.
“Masha Allah, Jannart ya labarin k'awarki wadda mijinta ke cewa chocolate ya fiye mashi mace”.
Yar dariya Jannart tayi kana tace.
“Umhum ya fara canzawa Aunty”.
Sauke numfashi Fauziyya tayi tare da gyara zama dan tana son bata shawarwarin da takeda yaƙinin zai ƙona ruwan kan duk na mijin da mace kamar Jannart zatayi mishi su.
“Uhm toh Jannart ki kai mata saƙona kice mata lallai tabbas ya kamata tafara juya matakinta na 'ya mace tanuna mashi ita macece tana da banbanci sosai da chocolate.....!”.
Shawarwari masu zafi da ratsa zuciya Aunty Fauziyya tabata akan yadda mace zata ja hankalin mijinta ta sashi ya banbance tsakanin aya da tsakuwa.
Sannan kare mgnar da cewa.
“Yanzu ma kikirata kice tadaina raba makwanci da shi ta kiyaye kada taji tsoronsa domin tsoron zai hanata neman matsayinta”.
Cikin sanyin murya Jannart ta sauke dogon numfashi kana tace.
“Toh ai yana bata tsoro akan yadda yake mata abubuwa my Aunty”.
Dariya Aunty Fauziyya tayi tace.
“Toh ai rayuwar auren kenan, Jannart kawai dai kar tayarda tabashi kanta har sai ta tabbatar da ya kamu da sonta kafin tamallaka mashi kanta,
ta garashi ta yadda sai ya lashe aman da yayi da kansa, tadage tadinga shiga wadda zata ja hankalinsa da tafiya me jan hankali, sannan tadinga kasancewa a kusa da shi a duk lokacin da yake gida ki samata turarukan dana aika miki, kar suraba makwanci dan kwanciya a tare yana k'ara kusanci da juna, tacire tsoronsa a ranta ahaka har shak'uwa zata shiga a tsakaninsu”.
Cike da gamsuwa da maganar Auntyntata tace.
“Toh Aunty insha Allahu zan yi mata bayani in sha Allah sai ta gigitashi gigicewar da zai gane banbanci tsakanin Macce da Chocolate.”...!
Sun dade suna waya da Aunty Fauziyya Sulaiman, ta bata shawarwari masu tarin yawa.
Daga bisani dai sukayi sallama.
Tana ajiye wayar ta saki wani irin tattausan murmushin mai cike da manufofi,
A hankali ta juya ta shiga bathroom, wanka tayi da ruwa mai ɗan karen ɗauki sabida anayin sanyi sosai yau ɗin al'wala tayi kana ta fito bayan ta saka bathrobe mai kauri,
Kai tsaye gaban dreesin meeror ta tsaya karamin towel ɗin dake hannunta tasa tana tsane ruwan jikinta,
Man kullaccar sirri ta shafa a duk luggun da sako na jikinta, kana ta juya da auri ta bude akwatin kayanta, wasu riga da wondo da mayafi ta zaro ta kimtsa kanta aciki.
Wando mai kauri irin na sanyin nan, cib ya matseta,
Sai rigar mai ɗan sawo har kan guiwarta tazo mata kana daga sama dai-dai da jikinta daga ƙugunta zuwa ƙasa kuma a buɗe yake.
Wasu manyan boturane a jere gaban rigar sai gefe da gefen riga kuma da igiyoyo, gaba ɗaya kalansu nevy blue ne mai masifar kyau da sheƙi,
Sauri-sauri ta dawo gaban dreesin meeror hoda ta ɗan shawa fuskarta kana ta shafa siraran lips inta lipstick mai sheƙi.
Turare ta fesa.
Kama ta tubke gashin kanta.
Ɗan mayafin da yakeda fuskar hijabi red color ta ɗauko tasa a kanta tare dayi Rollin nashi fuskarta ta fito 0 sifili a tsakiyar.
A can ɗakin Dakta Rayyern mai nasara kuwa.
Aikin yakeyi cike da jin dadi da farin cikin da shi kansa baisan na menene ba.
Numfashi ya fesar tare da kallon agogon hannunsa.
Ganin lokacin salla'n la'asar yayinda yasashi,
miƙe tsaye tare da wucewa bathroom nashi.
Al'wala yayi kana ya fito.
Kai tsaye masallacin su ya wuce.
Ita ma Jannart ganin lokacin salla yayinda yasa ta shimfiɗa sallaya ta tada salla.
A hankali ya fesar da numfashi bayan ya dawo daga masallacin.
Cikin shauƙi ya nufi ƙofar ɗakinta yana mai kallon agogon hannunsa inda yaga ƙarfe huɗu da kwata na yamma.
A hankali ya tura ƙofar ɗaki. Tare da sa kansa bakinsa ɗauke da sallama.
“Assalamu alaikum Jannaaaa!”.
Ya ƙare sallamar da kiran sunanta can ƙasan maƙoshinsa.
Ita kuwa Jannart dake ninke sallaya.
A hankali ta juyo ta kalleshi.
“Masha Allah”.
Ya furta ba tare daya shiryawa hakanba, ita kuwa jujjuya kwayar idanunta tayi cikin alamun bacci tace.
“Na'am Naan”.
Wani sassayan numfashi ya fesar kana a hankali ya fara takowa zuwa tsakiyar ɗakin.
Murya a tausashe yace.
“Baki amsa min sallamata ba”.
Cikin sanyi tace.
“Afwan Wa alaikassalam”.
Numfashi ya ɗan fesar tare da sunkuyowa kan goshinta ya manna mata kiss,
da sauri ta lumshe idanunta.
Yatsarshi manuniya yasa ya lakaci tsinin hancinta kana yace.
“Baby face ɗinki yayi kyau, kizo muje musha Chocolate ko ki ɗan ga garin”.
Idanunta dake cike da lamun bacci ta ɗan buɗe kana a hankali tace.
“Naan bacci”.
Hannunshi yasa ya kamo nata kana murya can ƙasa yace.
“Zo muje kisha Chocolate zakiji duk wata bukatarki da bacci zata tafi, dan shi Chocolate yafi komai daɗi”.
Da sauri ta kalleshi.
Shi kuwa kai ya jinjina mata tare da jujjuyawa alamun abu yake nema.
Ƙafarsa yasa ya jawo takarmanta sau ciki masu tsini. Suma red collor ne.
Jawo hannunta yayi sukazo har inda takalman suke.
A hankali ya rusuna yayi ƙasa.
Jawo takalman yayi gabansa, kana ya ɗago kanshi ya ɗan kalleta, ido ɗaya ya kashe mata tare da cewa.
“Saka”.
Ya ida mgnar yana ɗago ƙafarta, wanda hakan yasa tayi saurin dafe kafaɗarsa, sabida jin kamar zata faɗin.
Shi kuwa juyowa yayi ya ɗan kalli hannunta a hankali ya manna haɓarsa bisa bayan hannunta, ya fara goga sajensa akan fatar hannun nata a hankali,
Yayinda ya meda hankalinsa kuma kan sa mata takalmin,
Ita kuwa Jannart cikin lumshe ido tasa hannunta ɗaya ta dafa ɗaya kafadar tasa tare da manna babbar yatsarta kan sajenshi a hankali ta fara jujjuya yatsar,
Tanayi mishi wani irin gigitaccen yanayi mai kassara tunanin namiji, kasake yayi yanajin yadda take watsa da sajensa.
Ita kuwa Jannart batama fahimci ya gama saka mata takalmin ba,
Sabida yatsunta da take motsawa kan tattausan sajensa.
Shiru yayi baiyi yunkurin hanataba bare ya janye fuskarsa.
saima gyara durkusonshi da yayi wanda hakan ya bata damar wasa da sajensa duka gefe biyu.
Wasu irin masifeffen abubuwa yakeji suna biyo jijiyoyin jikinsa,
a hankali ya ɗago kanshi ya zuba mata idanu.
Ita kuwa jin wani irin masifeffen harbawa da zuciyarta ya farayi ne yasata fara dawowa hayyacinta.
Da sauri ta kalleshi tare da janye hannayenta.
Kana taja da baya tana kallonsa.
Cikin