Showing 309001 words to 312000 words out of 350584 words
Chapter 104 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete
faɗi sumeba kana bai bi ta kan Rayyern da Ramadan da keta jijjigata suna auna mata kiraba.
Zaiton kuwa, cikin tsananin rawan jiki itama ta saki kuka tare da bin bayan Mammynsu data nufu kan Mamy.
Cikin Sauri Barrister Kabeer yayi hamzarin riƙo Abba ya ajiyesa.
Jannart kuwa a gigice ta saki kuka ganin yadda gaba ɗaya Mamy ke kwance kamar matacciya.
Wani irin tsorone ya rufeta, jin Rayyern yana cewa.
“Innalillahi wa innailaihi raji'un Abba, Mamy bata motsifa, Ramadan ka duba mana Mamy, Mammy ki taimakemu”.
Gaba ɗaya ma shi ya mance cewa, shi likitane.
Shi kuwa Ramadan kuka kawai ya saki da azaban karfin sauti yana jijjigata.
Hakan ya tsananta kukan Jannart, yayinda kukan Jannart ɗin kuma yasa su Hafeez saki kuka da karfi.
Ita kuwa Mammy kitchen ɗin su ta nufa sa sauri.
Aunty Dijat kuwa kamo Jannart tayi tare da ruggume ta, tana maimaita.
Innalillahi wa innailaihi raji'un.
Riyyam-nsra kuwa yau shine ya zama na miji
Domin dama can shi yanada zaton hakan zai iya faruwa, hakan yasa cikin ƙarfin guiwa da ƙarfafawa su Rayyern guiwa yace.
“Hamma Rayyern Mamy fa tana raye, Please ka nitsu, ka dubata, tana da raye, sumane tayi”.
Ina gaba ɗaya falon ya dibke da koke-koke duk gidanma ya hargitse.
Dai-dai lokacin kuma Hadi da Ari, suka shigo riƙe da jakkunan su Mammy.
Ganin yadda gaba ɗaya suke a hargitse ne, yasa, Ari sakin jakukkunan Hannunsa, a guje ya koma baya.
Side ɗinsu ya nufa, a matuƙar gigice.
Yana tafe yana aunawa Baba Mauɗo wani irin hargitsestsen kira.
“Baba Mauɗo innalillahi wa innailaihi raji'un Kazo kaga halinda Alhaji da ahlinsa sukeciki, Baba Mauɗoooooo!!!!!”.
Cikin tsananin gigita Baba Mauɗo ya ajiye ƙura'an ɗin hannunsa kana miƙe tsaye a hargitse.
Dai-dai lokacin kuma Ari ya shigo.
Ganin yadda Ari yake a matuƙar gigicene, ya sashi.
Ƙara kiɗiminewa cikin tashin hankali yace.
“Kai Ari meke faruwa”.
Cikin hargitsi Ari ya fara nuna muna masa, hanyar cikin gidan yana cewa.
“Rayyern! Ramadan! Riyyam-nsra! Jannart! Namynsu”.
Innalillahi, jin yadda ya jera masa kiran sunayen su Rayyern shine tashin hankali mafi muni a garesa.
Allah ya sani da wani mugun abu ya samesu gwara ya samesu.
Wannan dalilin yasa gaba ɗaya ya firgice jikinsa ya ɗabi wani irin mazari.
Ba tare daya tuna baisa rawanin da yake kare surar fuskarsa ba, ya nufi cikin gidan a hargitse.
A can cikin gidan kuwa, cikin Hanzarin Mammy ta ɗauko ruwan sanyi a Fridge ɗin data samu a dinning area.
Tana ɓalle marfin goronan, ta iso inda Mamy ke kwance kan cinyar Riyyam-nsra.
Da sauri ta watsa mata ruwan a fuska, cikin Sa'a watsawa ɗaya, Mamy taja wani irin firgitacen numfashi tare da yunƙurawa a zabure ta miƙe zaune kamar wacce zata arta a guje, ganin hakane yasa.
Rayyern yin wani irin zabura ya kamota ya ruggume ta a jikinsa da ƙarfi cikin gigita yace cewa.
“Innalillahi wa innailaihi raji'un Abba Mamy na, Mammy Help me”.
Cikin tsananin sauri Mammy ta sunkuyo kan Mamy hannunta ta kamo ta riƙe da karfi, cikin tsananin rauni tace.
“Ruƙayya ki buɗe idonki, kada ki zauce, nice Adda Aichanki ki buɗe ido, kinga Rayyanunnki ya shiga ɗimuwa, kalli Ramadan ɗinki yadda yake kuka”.
Wani irin zurawa Mammy idanu tayi, wasu hawaye masu azabar zafi nankwaranyo mata.
Abba kuwa har yanzu ya gaza daina kallonta.
Barrister Kabeer dai na riƙe dashi.
Yayinda Aunty Dijat ma ke riƙe da Jannart.
Dai-dai lokacin kuwa Baba Mauɗo ya kutso kansa cikin falon, yana mai cewa.
“Rayyanu! Ramadan! Meke faruwa”.
Jin sautin muryarsa ne, yasa Mammy dake durƙushe, wani irin zabura tare da miƙewa tsaye,
Ido cikin ido sukayi da Baba Mauɗo.
Cikin tarin kiɗima, gigita, hautsunewar tunani, ta fara nunashi da yatsa murya can sama a hargitse tace.
“Ya ilahi ya mujibattada'awati ya hayyu ya ƙayyum birahamatika astaƙisu. *Mujed* ta kira sunan da yasa jikin Baba Mauɗo sakin wani irin masifeffen karkarwa.
Ita kuwa Mammy luuu tayj
Ta faɗa kan Ramadan a sume.
“Innalillahi wa innailaihi Mammy!”.
Zaiton ta saki azabebben kuka.
Abba kuwa ganin fuskar Baba Mauɗo ne, yasashi yin wani irin zabura ya kwace hannunsa da riƙon da Barrister Kabeer yayi masa.
Kawai sai yasa hannunsa duka biyu ya riƙe kansa da azaban ƙarfi cikin hartsewar murya cike da kuka yace.
“Ya Allah kada in rasa hankalina, ya Allah idan mafarki nakeyi, ka farkar dani ka kuma tabbatar min da mafarkina ya zama gsky al'farmar Annabi da al'ƙur'ani dan girman zatinka”.
Shi kuwa Riyyam-nsra da sauri shima ya zubawa Baba Mauɗo ido, wanda ya gane sanadin ganinsa ne ya sumar da Mammynsu.
Goran ruwan dake hannunta yazare.
Tare da yayyafa mata.
Amman ina bata farfaɗoba
kuma yayyafa mata yayi da ƙarfi, cikin Sa'a ta farfaɗo da wani irin maraitaccen kuka mai cushe numfashin, ta meda kanta jikin Ramadan.
Shi kuwa Baba Mauɗo zamewa yayi ya zauna a tsakiyar falon bisa carpet cikin wata iriyar fitinenneyar murya mai cike da ababe masu tarin yawa yace.
“Ya Salam, Yau a raye nake ko a mace? Ya Allah mafarkine ko zahiri? Aicha a mafarki nake ganinki ne kamar kullum koko ido biyu ne?”.
Ya kare mgnar yana sakin kuka kamar yaro.
Wannan al'amarin ya magaga ya kuma dunguzuma tunanin kowa,
Barrister Kabeer kuwa kai kawai yake jinjina yana nanata kalmar.
“Alhaji Bashir Muhammad Mai Gaskiya! Ya salam, inama ace nima zanga yah Abdulkareem a wannan duniya da nake ciki”.
Sai kawai ya saki kamo Jannart dake kuka ya ruggumeta cikin sautin kuka yace.
“Kiyi kuka Jannart, bazan hanaki yin kuka a wannan ranarba, kiyi kukan da ba'a barki kin yishi ba tsawon rayuwarki.
Jannart kiyi kuka domin kece kikafi cenccenta dakiyi kuka fiye da kowa a yau”.
Ita kam Jannart zuwa yanzu kanta ya fara juyawa.
Ita kuwa Mammy rarrafe ta farayi kamar yarinya.
A haka ta isa har gaban Baba Mauɗo, kawai sai ta kife kanta, bisa sawunsa.
Cikin wata iriyar sassayar murya tace.
“Nice Mujed nice, Aucha nice, ɗin dai”.
Hakan ne yasa Baba Mauɗo ɗaga Hannunsa sama tare da cewa.
“Alhamdulillah alakulli halin, Aicha gaya min Riyyam-nsra ɗanane?”.
Cikin zubda hawaye ta gyaɗa masa kai tare da cewa.
“Eh shida da Zaiton duk yayanka ne Mujed yayankane na cikinka kuma na halattatu”.
Jin wannan kalmar ce, tasa, Riyyam-nsra janye jikinsa daga jikin Mammy da rarrafe shima ya taho jikin Baba Mauɗo.
Shi kuwa Baba Mauɗo, hannu ya miƙawa Zaiton tare da cewa.
“Zo nan Mamana zo nan Aicha kin cika min burina”.
Aifa cikin kuka Zaiton ta faɗa, jikinsa, ita da Riyyam-nsra duk sun gane, cewa Baba Mauɗo shine mahaifinsu tun daga fuskarsa, dan sun mishi farin sani a hoto.
Da sauri suka juyo duk suna kallon Barrister Kabeer dake kuka ruggume da Jannart, cikin sanyi Abba yace.
“Barrister kayi haƙuri, ni nasan kukan me kakeyi, amman dan Allah kayi haƙuri”.
Da sauri cike da mamaki Barrister Kabeer ya tsagaita da kukan yanayiwa Abba kallon tambaya.
Kai Abba ya jinjina masa.
Alamun “eh na sani”.
Rayyern kuwa a hankali ya miƙe dinning area ya nufa, gororin ruwan sanyi ya ɗebo masu yawa.
Yana dawowa, ya ɓalle marfin goro ɗaya, yasawa Mamy a baki, ba musu, ta amsa, ajiyan zuciya ta fara sauƙewa bayan ta gaba shan ruwan.
Abbansa ya kuma bawa, sannan ya bawa Mammy amsa tayi tasha, sannan ya bawa Baba Mauɗo.
Haka sai ya basu baki ɗayansu.
Kana a hankali ya kamo hannunta janyeta yayi daga jikin Barrister Kabeer.
Bisa kujera ya ajiyeta.
Ɓalle marfin goro yayi tare dasa matashi a bakinta.
Yadda takejinta a gigice yasa ta amshi ruwan.
Shi kuwa Rayyern jawo Hafeez da Hafiza yayi ya mannasu a jikinsa yana shafa kansu.
Hakan da yayi musu yasa gaba ɗaya nitsuwa ta fara sauƙar musu.
Kallon Jannart yayi cikin tattausan murya yace.
“Kiyi haƙuri ki dena kukan haka nan kinji, kinga baki da lfy”.
Meda kanta kawai tayi ta jinginar a kujera bayan ta zame ƙasa.
Abba ne yayi gyaran muryan tare da kallon Mamy dake sauke ajiyan zuciya.
Cikin sanyi yace.
“Ruƙayya kinga ikon Allah ko?”.
Kai ta jinjina masa kawai.
Shi kuwa Barrister Kabeer, wayarshi ya zaro.
Alhaji Bala tambari ya kira, yace yana son ganinsa a gidansu Dr Rayyern.
Kana ya kira Dr Sajo.
Sannan su kuma falon kab, ɗinsu kowa ya koma mazauninsu.
Riyyam-nsra kuwa murmushi kawai yake tayi.
Gaba ɗayansu a ƙasa suka Zazzau na.
Babu abinda ke tashi sai sauƙe ajiyoyin zuciya.
A hankali Abba ya matso gaban Baba Mauɗo cikin tarin girmamawa mutuntawa, sunkuyar da kansa yayi ƙasa murya a raunace yace.
“Kafin ince komai, in kuma yi komai.
Zan fara da neman afuwarka a bisa ajiyeka da mukayi a matsayin maigadi, a muhallinka, wallahi bamj ganeka ba, ka gafarceni ubangidana, da kai tsaye zan iya kiranka da ubana”.
Da sauri Baba Mauɗo ya fara jujjuya mishi kai tare da cewa.
“Bashiru dan Allah kada kace komai, domin da duk al'ummar duniya kowa zai samu mutun mai amana irinka ahlinsa to da tabbas da babu wani batun cin amana da zai rage a duniya, Bashiru kai mutun ne managarcin da samun irinka zaiyi wuya, domin irinku suna ƙaranci a duniya, to Ni kuma Bashir me zanyi maka takwarana da zan iya biyanka a duniya, ka cika ɗan halas”.
Mamy kuwa a hankali ta iso gaban Mammy cikin rauni da kuka tace.
“Adda na kuma uwata kin min komai a duniya, ni kuwa me zan miki?”.
Da sauri Mammy ta rufe mata baki tare da cewa.
“Ai ni kika yiwa komai a duniya, bani da abinda zan biyaki dashi tabbas jin cika amintacciya”.
Cikin rauni Ramadan yace.
“Mamy ki dena kuka, koma menene abarshi sai mun gaisa dasu”.
Hakan ne kuwa yasa duk suka rinƙa gaisawa da juna.
Dai-dai lokacin kuma Dr Sajo da Alhaji Bala Tambari suka shigo a tare. Dr Sajo kam yayi masifar kaɗuwa da ganin fuskar Baba Mauɗo, yayinda Alhaj Bala Tambari kuwa yaketa murmushi.
Nan aka gaggaisa dasu. Kana duk suka Mamy ta gabatar musu da ɗan abin taɓawa. Amman ina babu wanda yayi iya cin komai.
Musamman Rayyern da Ramadan dake cikin kaɗuwan son sanin Meya firgita musu iyaye harda suman wasu, irin Rayyern da Abba tun safe babu abinda sukaci.
Gyara zama sukayi tare da fuskarta Abba da Barrister Kabeer ya jefa masa tambayar da amsoshinta keda yawa.
“Abban Rayyern, su waye waɗannan da ganinsu ya gigitaku ya firgitaku har ya kai iyalinka da suma? Sannan me alaƙarku dasu? Sannan ya akayi Alhaji Bashir Muhammad Mai Gaskiya, da akeda cikakkun rahotannin rasuwarsa shekaru ashirin da biyu zuwa da uku ya kasance a nan a gidanku kuma cikin bada kamanni?”.
Kai Baba Mauɗo ya jinjina tare da saurin cewa.
“Ƙannena su”.
Da sauri Abba yace.
“Kayi haƙuri Alhaji, barni in gaya musu gsky, kodan Rayyern da Ramadan, domin zuwa yanzu nagane cewa Riyyam-nsra kam da yar uwarsa Zaiton sun san komai”.
Da sauri Riyyam-nsra ya jinjina masa kai alamun eh.
Shi kuwa Barrister cikin sanyi ya kalli Hadi da Ari dake tsaye bakin ƙofar, yace.
“Da kun bamu wuri”.
Da sauri Baba Mauɗo yace.
“A'a barsu babu komai su mutanene masu aminci, ku shigo ciki ku zauna”.
To sukace kana suka shigo ciki suka zauna.
Barrister Kabeer ne ya kuma cewa.
“Abban Rayyern kai muke sauraro”.
Jin hakan ne yasa Abba Rayyern, sunkuyar da kansa, tare da rumtse idanunsa hawaye masu zafi suka silalo masa.
Sai kuma ya kalli Rayyern da Ramadan kana cikin tsananin rauni da tunowa da tsohon tabo mai ciwo a ransa ya buɗu baki a hankali ya fara basu lbrin da shine Tubalin komai cikin raunatacciyar murya yace.
*“Gembu Membilla”.*
Sai kuma ya sharce hawayensa kana yaci gaba da cewa.
“Shekaru ashirin da uku zuwa da huɗu baya, mun kasance a cikin garin Gembu da yake tushenmu asalin mahaifa mu ni da Rukayya.
Mu asalin fulanine, kuma makiyaya.
Alhaji Bashir Mai Gaskiya, gashi nan Baba Mauɗo kenan. kuwa baƙone a garinmi ba nanne asalin garinsaba.
Daga nan Kano yake a yadda ya sanar mana yanayin kasuwancinsa ne na binciken ma'adan ƙasa dana ruwane, da haɗa hannu da manoma wurin ganin sun bunƙasa harkarsu, ne ya kaisa Gembu.
Matarsa ɗaya Hajia Aicha.
Gata nan Mammyn Riyyam-nsra kenan.
A lokacin yaransu biyu ne, Rayyern da Ramadan”.
Cikin wani irin ɗimuwa da kaɗuwa, Rayyern da Ramadan suka zazzaro idanunsu waje tare da kallon Baba Mauɗo da Mammy kana suka kuma juyo suka kalli Abba cikin son tabbatarwa.
Shi kuwa Abba kai ya jinjina musu cikin tabbatarwa yace.
“Yesss Rayyern ku ɗindai kai da Ramadan, ku ƴaƴan sune na cikinsu. Sune suka haifeku”.
Ya salam tashin hankali da ba'a sa masa rana.
Gaba ɗaya Rayyern da Ramadan gigicewa sukayi.
Yayinda Jannart kuwa da Aunty Dijat da Dr Sajo suka zama kamar an dasasu ana basu labaran al'mara.
Yayinda Mamy kuwa ta saki wani irin raunataccen kuka.
Haka yasa Ramadan sa tafin hannunsa yana sharce mata hawayen.
Hafiz da Hafiza kuwa kwalamarsu kwai sukeci.
Alhaji Bala Tambari da Baba Mauɗo da Mammy kuwa Kai suke jinjina musu.
Barrister Kabeer kuwa zama ya gyara tare da cewa.
“Ci gaba”.
Numfashi Abba ya ɗan fesar kana yaci gaba da cewa.
“Lokacin dududu shekaruna sha 16, yayinda Ruƙayya kuwa lokacin shekarunta 12 ne kacal a duniya.
Rayyern kuwa lokacin shekarunsa 6 ne rak a duniya.
Kunga kenan da shekara 6 kacal nema Rukayya ta girmi Rayyanu ina tunawa lokuta da dama Rayyanu kan cewa.
Abba kayi Sa'a wlh Mamynmu bata tsufa, Ramadan kuwa lokacin shekaransa uku ne.”
Da sauri Rayyern ya riƙe kansa da hannu biyu kana cikin birkitaccen yanayi yace.
“Dan Allah kayi mgnar da zan iya ganewa, kaina bazai iya ɗaukaba tunanina zai hargitse”.
Ramadan kuwa shi zuru-zuru ma kawai yayi sa idanunsa.
Shi kuwa Abba murmushi mai ciwo yayin kana yace.
“Bari kuji yadda abun ya ya kasance, lokacin da suka ƙauro Gembu.
Ni ina yawan shiga cikin gari in mun dawo kiwo, in na shigo ina saida Su Fiya inabi da dai sauransu.
Kuma a bakin kwafar gidansu nake zama da ɗan teburunina.
Wannan dalilin yasa muka saba dasu sosai.
Har ya zama suna kwasa min aminci Alhaji Bashir amintaccen mai kuɗune mai mutunta talaka.
Haka nan Allah ya jarabceni da son yaransa Rayyern da Ramadan.
Mun shaƙu dasu sosai.
Har ya zama nike kaisu Makarantar boko, da islamiyya.
Sannan in zaune a ƙofar gidansu muddin suna gida to sai suzo wurina.
Wata rana Rayyern karatun Alqur'ani sai ya ɓata, nayi masa gyara, ashe Alhaji na jinmu.
Sai yake takvayata nayi karatun ne, nace mishi eh nayi na allo, sosaima.
Anan yake cemin ayyah ai babanshi ma na karantar da allaho dan haka in fara karantar masa dasu Rayyern mana.
Naji dadin hakan kuwa nan na fara karantar dasu, kuma Alhamdulillah kansu na ɗauka.
A lokacin
Ruƙayya kuma na tallan nono,kasan cewar gida, gida take shiga, shiyasa ta shiga gidansu.
A ranar forko suka saye nonon. ta duka to daga nanfa kullum sai tazo gidan.
Itama ta saba dasu Rayyanu sosai.
Muna cikin haka akayi faɗan ƙabilun Gembu da fulani.
A wannan faɗan ne na rasa kowa a duniya, nima din abinda yasa na tsira, dan ina cikin Gembu ne.
Ruƙayya ma haka abin ya kasance a wurinta.
Ta zama marainiya gaba da baya, dan gaba rugagenmu babu wanda ya tsira, sunyi mana illamafi muni a rayu warmu.
Mun shiga tashin hankali fiye da zaton ma sauraren.
Alhaji Bashir da matarsa, sun tausaya mana lokacin da abin ya lafa mukaje rugagenmu dasu, sosai Adda Aicha tayi ta kuka sabida ita macece mai rauni, ina tuna yadda ta ruggume Ruƙayya tana cewa.
Ruƙayya ki dena kuka ni zan zamemiki komai na duniya da kika rasa, ki kalleni matsayin tayarkin kuma mahaifiyarki, ki kalli su Rayyern kamar kanneki, ko kuma yayanki, ki kalli Babansu a matsayin babanki yayanki.
Zamu riƙeki dake da mai sunan Abban Rayyern”.
Da yake haka take kiran kasan cewar suna Bashiru sunan mijinta kenan.
To daga wannan ranarfa, muka dawo da zama gidansu.
Aka ware ɗaki akabi, ata waje.
Ita kuwa Ruƙayya daga ranan ɗaki ɗaya take kwana dasu Rayyanu.
Hakan ya sanar da wata iriyar amintacciyar shaƙuwa taban mamaki a tsakiyarsu.
Ni kuwa daga ranar Abba suke ƙirana dan karar inada sunan mahaifinsu.
Dan mahaifinsu da Baba suke kiransa.
Mahaifiyarsu kuma da Mammy suke kiranta.
Ramadan kuwa shiyasawa Ruƙayyah Mamy.
Daga nan muka zamo ahli ɗaya.
Cikin shekara ɗaya muka zamo tamkar yan uwa na jini.
Tuni Baba Mauɗo ya koya min mota,ya zama nazama kamar PA'nsa.
Sai dai banyi karatun bokoba,
Lokuta da dama, Baba Mauɗo sunayin baƙin musamman wani bawan Allah Barrister Abdulkareem Sale Dakata, yana yawan zuwa, kuma daga nan Kano yake tun forkon ƙauriwarsu da yazo ya fara soyayya da Zainab dudu cikin wata ɗaya akayi aurensu.
Na fahimci duk wani sirrin Alhaji Abdulkareem ya sani.
Kuma Alhaji yana ji dashi.
Sukayi duk mgnar sirrinsu a gabana ba tare da wani ɗarba.
Akwai wata ranar jumma'a da Barrister Abdulkareem yayi isowan dare, baima zo da motarsaba.
Da motar haya yazo, hana yasa Alhaji tadani mukaje ɗaukosa.
To muna dawowa a cikin motar.
“Barrster lafiya kuwa wannan zuwa na bazata”.
Kai jingina kana yace.
“Kamar yadda na gaya maka tun lwanaki, akan barazar da abokan tawagar abokanka sukeyi min, na in kasance cikinsu, in kuma basu dukkan bayananka na sirri, domin suna son mallakar wani sashi na musamman.
Bazan ɓoye maba harda ɗan uwana Yah Idi, shi yayi min barazana da raina dana Zainab”.
Cikin tashin hankali Alhaji yace masa.
“Zainab kuma to me tayi musu, da sayi maka barazana da ita, meyasa zasu sa mace a ciki, macema mai tsohon ciki”.
Cikin rauni yace.
“Nima sun raunatani dayin barazana da Zainab, domin cikinta ya tsufa haihuwa Yau ko gobe. Shiyasa na tattaro maka dukkan bayanka na sirri da dukkan takardunka da komai, na dawo maka dashi.
Sabida ina tsoron kada barazanar su ta raunata imanina su sani inci amanarka in basu shi”.
Cikin yanayin ɗumuwa.
Alhaji Bashir yace.
“Haba Barrister ya za'ayi kayi haka, bunada sama da iyalanmu, injidai akan Company da ake kafa Tubalinsa a kanone ya tada musu hankali.
Sukega kamar zan gurgunta musu basu da suke ganawa,
Toh kaje da takardu. Ka bawa Alhaji Bala Tambari, ya soke sa hannunsa, a dakatar da ginin, ko ma samu kwanciyar hankali.”
Haka kuwa akayi, washe gari da safe, nida kaina na kaishi gidan surkansa.
To yana gaida surkansa ya kama hanya ya koma kano da dukkan takardun sirrin dake hannunsa da komai na companyn.
Bayan ya koma da kwana biyune, kuma aka kira Alhaji taron a nan cikin Taraba.
Toni a lokacin duk inda zaije tare muke zuwa in muna gida kuwa, a bakin gate nake zama, wasu lokutan in anyi baƙi ina buɗe musu gate.
To wata rana da yamma, haka da sauri naga ya fito.
Ya shiga mota, koda na taso, sai cewa yayi in bari.
Rayyern kuwa dake gefena da sauri ya taso yaje ga mahaifin nasa, tare da cewa.
“Baba nima zanje”.
Ganin yadda yaron ya tsareshi da idanune yasashi cewa.
“Toh Mauɗo na muje”.
Da yake mafi akasarin lokuta haka yake kiransa.
Ramadan kuwa lokacin bacci takeyi.
Haka dai suka tafi tare,
Har zuwa ƙarfe sha ɗaya na dare basu dawoba, hakanne yasa.
Mammyn ta fito wajena ita da Ruƙayya, dan har lokacin Ramadan yana wurina.
Amsar Ramadan tayi a hannuna kana, ta juya tayi ciki.
Ita kuwa Mammynsu cikin fullacin da bata gama iyawaba, dan ita asalin ƴar ƙasar Ethiopia ce.
“Abba Rayyarn yau kuma lfy kuwa har yanzu Baban Mauɗo da Rayyern basu dawoba.
Gashi nayi ta