Showing 141001 words to 144000 words out of 350584 words
jiƙa min shi”.
Toh yace tare da amsa.
Manyan Robobin dake jere a wurin ta ɗan fara budewa.
Tana buɗe na forko ta samu tankadedden garin kunune, da alama ya dade ɗan har ya fara yin zare-zare.
Tana buɗe na biyu kuma ta samu markadedden gyada ne mai kyau, sai nason mai yakeyi.
Cikin jin daɗi tace.
“Lah markadedden gyaɗa ai ban saniba,In sha Allah kwannan zan mana miyar kase zan matse man inyi tunkuza.”
A roba ta ukune kuma ta samu barerren ɗanyen gyaɗa, ɗan ƙasa irin jajayen nan.
Ɗan ɗago kanta tayi ta ɗauki roba, gyad’an a diba gongoni huɗu.
Kana ta fito cikin Kitchen din, inda ta samu Riyyam-nsra tsaye ya wonke shinkafar ya jiƙata.
Sa gyadan tayi a tray'n roba ta bushesa tare da tsince duk wani ɗan daɗi.
Kana tasa ruwa ta wonkesu.
Sannan ta haɗesa da shinka fan.
Kujerar ɗan table ɗin dake tsakiyar Kitchen din Riyyam-nsra yaja ya zauna.
Ita kuma store ta koma, ta ɗan dudduba tsamiya, saidai kuma bata samuba.
Da sauri ta fito kitchine ɗin.
Fridge ta bude ɗan tuno akwai lemun tsami.
Guda biyar ta dauko manya, ta miƙawa Riyyam-nsra tare da cewa.
“Yauwa ga wannan matse min ruwansu.”
Aje wayarsa yayi tare da cewa.
“Toh bani cup.”
Miƙa mishi cup da wukawa tayi,
kana ta koma gaban Fridge din.
Kwakwa kwaya biyu da dabino ta ɗebo, mai ɗan yawa sai citta kwaya biyu rak, sai kanamfari cokali ɗaya,
tazo ta baresu tare da cire kwallayen dabinon da bawan kwakwan.
Kana ta watsasu cikin shinkafar da gyaɗan data jika.
Blender ta ɗauko tare da lallatsashi.
Kana tazo ta zuba kayan haɗin duka da yake kofin blender’n, babbane ruwa ta ɗan tarfa ciki,
rufewa tayi tare da kunnawa, ta markadeshi lukui.
Bayan tagama ne kuma ta ɗauko tukunya number uku.
Ta lallaye sannan ta dauki rariyar tatan koko.
Shina ta lalleyeshi.
Kana ta juye cikin tare dasa ruwa ta lallaye kofin blendern mai dan yawa ta lallaye ta meda shi wurin zamanshi.
Ta tace markaden.
Yayi wani irin fari tas tamkar madaran shanu.
Gas din ta kunna kana ta ɗan rage ruwan kunun a kofi, sannan ta ɗaura kan wuta, tare da dauko ɗan ƙaramin muciyarsu.
Ta matso kusa tasa cikin tukunyar, tana ɗan motsashi a hankali wutan naci, tana nan tsaye tana gaurayashi kuwa har ya fara kauri.
Tana motsashi tana tarfa wannan ruwan data diba tare da ruwan lemun tsamin.
Lokaci ɗaya ya fara wani irin masifeffen ƙamshi yayi kauri yayi fari tas, in ka gani zakace kinɗirmo ne aka burge.
Kashe wutan tayi tare da sauƙe tukunyar.
Riyyam-nsra kuwa aje wayarsa yayi tare da cewa.
“Har kin gama.”
Sai kuma ya matso ganin yadda kunun yake da sauri yace.
“Kai my Aunty wannan ko nono ne kikayi?”
Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.
“Kunun Gombawa kenan.”
Kai ya jinjina tare da miƙo ƙaramin cup yace.
“Samin in mana dandanel".
Murmushi tayi tare da sa mishi.
Kana ta ɗauko wani roba mai kyau ta juyeshi ciki.
Kana ta rage kaɗan tasa a ƙaramin flaks.
Tasa bisa tray'n tasa mug da spoon kana sai madarar gari a roba mai haɗe da set din flaks din.
Ɗayan kuma tasa zumar a ciki.
Kana ta mikawa Riyyam-nsra.
“Ajiye kam table a Dinning.”
To yace ya amsa.
Ita kuma ta jawo nashi kofin kunun, madarar ta saka mishi tare da zuma ta motsa da kyau.
Kana ta miƙo mishi tana cewa.
“Biri in sa wannan kuma a Fridge don in yayi sanyi yafi daɗin sha.”
Kai ya jinjina tare da amsa ya fita.
Ita kuwa ta buɗe Fridge ta sashi ciki.
Kana ta wonke komai ta fito.
(Gareku masu karatu.
Kunun yana sauko da ni'ima a jikin mace sosai kana da ruwan nono ga mai shayarwa, ga maza kuma yana sasu feelings yana kuma mgnin ciwon ciki in kin yawaita zuma da dabinon yana kuma gyara fatan jiki.)
Da sauri ta fito falon jin Riyyam-nsra na cewa.
“Wow masha ALLAH kai my Aunty wannan kunun duniya ne, yaseen yayi masifar daɗi.”
Yadda yayi mgnar da ƙarfine yasa Ramadan buɗe idonshi tare da yin tsaki.
Cikin murmushi Jannart tace.
“Kadama ka sake rufe ido la'asar tayi.
Tashi kawai.”
Miƙa yayi tare da cewa.
“Wallahi yajin nanne ya sani bacci.”
Juyowa sukayi jiyo takun.
Rayyern yana sauƙowa.
Kanta ta kauda daga kallonshi tare da nufar ɗakinta.
Shi kuwa Riyyam-nsra ya kalla tare da cewa.
“ku tashi kuyi al'wala mu tafi masallaci.”
“To.” Sukace kana duk suka miƙe sukayi al'wala suka mara mishi baya.
Ita kuwa Jannart tana shiga bathroom ta faɗa wanka.
Wonka tayi da ruwan sanyi dan cikin kwana biyun nan.
Duk zafi ake ɗanyi, alamun sanyi na tattara kayansa zai tafi ya bawa zafi wuri.
Al'wala tayi kana ta fito.
Bayan ta idar da salla ne, ta mike ta isa gaban dreesing mirror'nta, mai ta ɗan shafawa jikinta.
Kana ta ɗan murza yar fauda tare dasa kwalli sai man baki, da ta ɗan goga akan lips dinta, tare kuma da gyara gashin giranta.
Takowa tayi zuwa gaban durowar ta, Ido ta zubawa jerin kayan bayan ta buɗe durowar, ahankali tasa hannunta ta jawo ledar da taga wata tattausar atamfa, Black and green color sai ratsin red, wanda akayiwa dinkin riga da zani.
Underwear ta zaro fari ƙal da pant shima fari.
Bayan ta rufe drawern ne kuma, ta dawo bakin gadon ta tsaya, kana anutse ta zura kayan.
Cas kuwa suka zauna mata a jikinta, Musamman rigar da tayi cib-cib da jikinta, breast cup din da aka yiwa rigar tamkar an gwada mamanta ne.
“Kai tela maye ne.”
Ta faɗa lokacin da ta dawo gaban dreesing mirror'nta, ganin yadda ƙirjinta yayi cib-cib a cikin rigar.
Ɗaurin ɗan kwali ta murza tare da fito da jelan gashinta gefe.
Turare mai sanyin ƙamshi ta fesa ajikinta, kana ta zaro gyale red color ta yafa a kafad’anta kana ta fito.
Kitchine ta nufa, sabida jiyo motsin Mamy da tayi.
“Kai Masha Allah diya kinyi kyau".
Mamy tace lokacin da tayi arba da ita.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Ngd Mamy".
Ta ida mgnar tana shigowa ciki tare da cewa.
“Mamy ga kunu a fridge.”
Kai Mamy ta gyaɗa tare da cewa.
“Au kunu ne ni ai nayi zaton kimdirmo ne.”
miƙowa Mamy hannu tayi alamun ta bata aikin, suyan kayan miyan da takeyi tace.
“Haka Riyyam-nsra ma yace.”
Kai Mamyn ta jinjina tare da cewa.
“Ato bari in na gama zan sha,yanzu bar wannan ɗauko semolina kizo ki tuƙa mana tuwo, yau miyar kuɓewa da bandan kifi zamuyi da tuwo bayanshi bazamu ƙara komai ba mun gaji".
Toh tace kana ta ɗauki garin tazo ta fara tukawa.
Ita kuwa Mamy ruwan nama tasa a suyan kayan miyar nata, kana tasa tafasheshshen nama da kifi banda, da ɗan dakakken daddawa da citta da kanamfari.
Ita kuwa Jannart bayan ta gama tuka tuwon ta rufeshi yana turara.
Tace.
“Mamy kubewar fa."
“A gata can na gogata.”
Dai-dai lokacin Rayyern ya shigo cikin falon, da sallama a bakinshi tare da daurawa da kira
“Mamy! Mamy!!.”
“Na'am Rayyern gani nan fa”.
Tace tana juyowa tana kallon ƙofar Kitchine ɗin.
Shi kuwa cikin alamun gajiya ya shigo.
Kauda kanshi yayi daga kallon inda take.
Kujera yaja ya zauna tare da cewa.
“Kai Mamy daddawa yayi yawa a miyar nan, ji yadda duk Kitchine din ya dibke.”
Rufe tukunyar Mamy tayi tare da cewa.
“In ta tafasa zai ragu.”
“Mamy yunwa.”
Yace yana mai ajiye wayarsa gefensa.
“Jannart bashi abinda zaici.”
“Toh".
Tace tare da juyawa ta fita.
A hankali ya ɗan juyo kwayar idanunsa.
Jin motsin ta ajiye tray'n gefensa.
Yatsunta ya ɗan kalla kana ya kauda kanshi.
Ita kuwa bud’e flaks din tayi ta zuba mishi kunun a cikin mug mai dan girma.
Saida ta kusan cikashi, kana a hankali ta ajiye tare da sa spoon ta debi garin madara, cokali uku ta saka mishi, kana ta ɗaga robar zuma ta sulala mishi, tare da motsashi kana ta ajiye mishi a gabanshi.
Da sauri ya ɗan sunkuyo ido ya zubawa kunun ba tare daya fahimci menene ba.
Cikin kwaɓe fuska yace.
“Mamy me wannan kuma?”
Tana mai fita Kitchen din tace.
“Taɓa kaji.”
Sai kuma ta kalli Jannart tare da cewa.
“Kwashe abin cinnan haka.”
“Toh Mamy.”
Jannart din tace tana mai juyawa ta nufi wurin tukunyar.
Shi kuwa Rayyern idonshi ya lumshe sabida ƙugin yunwa da cikinsa keyi,
ahankali yasa hannunshi ya ɗauki spoon din.
Motsa kunun ya farayi wanda yake masu kallon nono, sai dai ganin yana tururine yasashi fahimtar ba nono bane.
A hankali ya ɗan ja guntun tsaki.
Sai kuma ya ɗan ɗebo cikin cokalin ya ɗan ɗago sama ya zubawa kunun ido,
sunkuyowa ya ɗan yi harshensa, ya ɗan zaro ya ɗan laso kunun.
Zir haka yaji yawun bakinsa ya tsinko kunsan Dakta da son zaki da gardi.
Da sauri yasa spoon din a bakinsa ya zuƙe kunun.
Idonsa ya lumshe sabida dandanon kwakwa da zaƙin dabino da zuma da gyadar da yaji sun gigita masa harshe.
Gyara zamansa yayi tare da d’ago mug din ya kai bakinshi.
Kasan cewar madara da zumar sun sa zafin kunun ya koma dai-dai misali.
Kafa kanshi yayi yana mai lumshe idonshi ya fara zukan kunun.
Yana mai jin garɗinsa, saboda d’umin kunun ya wadaci hanjin cikinsa.
A hankali ya ɗan janye mug din, yana mai jin dandanon lemun tsamin ya, gyara mishi bakinsa Kunsan bakin mara lfy.
Numfashi ya ɗan fesar tare da juyowa ya kalleta tana aikinta kamar bata Kitchine din.
Kafa kai yayi ya shanye sauran kana ya aje mug din, gyatsa yayi mai sanyi kana ya miƙe ya fita yana jin cikinsa tib-tib.
A falon ya zauna bayan ya kara karfin Ac sabida zufan data karyo masa.
Ita kuwa Jannart tana gama kwashe tuwon ta ida miyar, tuni kuma an fara kiran sallan magriba, tana gamawa ta fito.
Yayinda Ita kuwa Mamy tana can wurin Abba.
Washe gari da safe.
Kasan cewar asabar ce tuni u Ramadan sun shiga gari.
Rayyern kuwa sai karfe goma saura ya sauko cikin shigar tattausar jallabiya blue mai guntun hannun.
Kai tsaye wurin Abbansa ya wuce, bayan sun gaisa ne kuma ya tafi wurin Baba Mauɗo.
Ya dan jima a nan kafin ya dawo ciki.
A falo ya samu Mamy kwance tana kallon tv tuni sha ɗaya ta gota lokacin, gefenta ya zauna a ƙasa tare da jawo system dinsa da ya ajiye kafin ya wuce.
A hankali yace.
“Mamy me aka dafa?.”
Ba tare da ta kalleshi ba tace.
“Dumame mukayi na tuwon jiya dan bai ciwuba, kasan mu kuma muna son ɗumamen dasu Baba Mauɗo duka.”
Kai ya gyaɗa dan yasan time to time suna ɗumamen duk da shi dai ba ci yakeyi ba.
“Me su Riyyam-nsra sukaci?".
Ya kuma tambayarta.
“Waya san musu ni dai naji Ramadan yanata kwarwa da mita, wai Riyyam-nsra ya cika musu yaji, ina zaton indomie suka soya da kwai.”
Kai ya ɗan juyo ya kalleta tare da cewa.
“Toh Mamy yunwan da nakeji ni me zan samu?”
Cikin kauda kai tace.
“Tambayi matarka.”
Da mamaki ya kalleta ganin ita bashi take kallo bane ma, yasa shi yin kwaffa tare da jingina kansa.
Dai-dai lokacin kuma Jannart ta fito daga Kitchen din riƙe da roba da markadedden gyada a ciki, ta ɗan sa ruwa da yar ƙaramar muciya alamun matsan mai zatayi.
Ido Mamy ta zuba mata, ita kuwa Jannart zama tayi gefe a ƙasa.
Kana ta kuma kallon Mamy ganin har lau ita take kallo.
Da sauri tayi ƙasa da kanta ganin Mamyn ta meda kallonta ga Rayyern ɗin.
A hankali ta ɗan ɗago ta kalleshi cikin lumshe ido tace.
“Ina kwana?”
A hankali ya ɗago kanshi ya juyo gareta.
Ido cikin ido sukayi, haka nan ba zato ba tsammani bare niya, kawai sai yaji lips ɗinshi sun furta.
“B...!
By
*GARKUWAR FULANI*
“Ba abinda za'a bani kenan Mamy.”
Yayi mgnar yana sunkuyar da kanshi, ita kuwa Mamy murmushin dake son subce mata ta danne tare da cewa.
“Gaka ga matarka nan.
Rayyern ka fita idonafa ka dena damuna, ka tambayeta ita mana, ya zaka zo ka tsareni da mita kamar ɗan yaye.”
Kanshi ya juyo ya kalleta cikin kwaɓe fuska ya kontar da kai bisa kujerar.
Cikin sanyi yace.
“Shike nan Mamy na barki.”
Miƙewa tsaye Mamy tayi tare da nufar side ɗinta tana cewa.
“Bari ma in bar maka wurin.”
Ita dai Jannart jujjuya yar muciyar takeyi, tana haɗe markadedden gyadan.
Tuni kuma ya fara haduwa ya fara nason mai.
Shi kuwa Rayyern cikin haɗe fuska ya kalleta, kana yayi mgnar can ƙasan maƙoshinsa.
“Ke wai ce miki akayi ni bani da rabone a gidan nan?”.
Juyowa tayi ta ɗan kalleshi a fakaice kana ta meda kanta.
Dan bata jishi ba sosaiba ta dai ji alamun yayi mgn kam.
Shikuwa ganin hakanne yasa shi, jan tsaki tare da dan buɗe murya yace.
“Ba dake nake mgna ba? Kina jina kinyi shiru.”
Da sauri ta ɗago kanta tare da cewa.
“Ban jiba?"
A kufule yace.
“Kada Allah yasa kiji, idan kunu na na jiya yana nan, ai sai ki kawo min tunda ba ke kika dama minba.”
Jin abunda ya fad’a dinne kuma, yasa ta satan kallonsa, ta gefen Idanunta, batare kuma da tace masa komai ba, ta miƙe tsaye da robar a hannunta.
Kaitsaye dining ta nufa ta ajiye robar,
sannan anutse ta wuce cikin Kitchen,
mug ta ɗauƙa da spoon kana ta buɗe fridge, sassayan kunun ta tsiyaya mishi.
Kana tasa madara da zuma ta motsa, sannan ta ɗaura a dan tray.
Anutse ta fito daga cikin kitchine din, hannunta dauke da tray din, ta nufo inda yake.
Isowarta ne kuma yasa shi d’ago kanshi ya kalleta.
Jannart kuwa batare da ta kalleshi ba, ta d’an rusuna agabanshi, tare da ajiye try’n, cikin tafiyarta na nutsuwa kuma ta juya ta tafi.
Shi kuwa Rayyern baki ya taɓe tare da cewa.
“Aniyarku zata koma kanki, wato irin bari ki fara kasheni da yunwa dinan ko, dan kin samu an sake miki ragamar gidan.”
Ya ida mgnar nasa yana kai mug din bakinsa.
A zatonsa mai dumine sai kuma ya jishi mai ɗan karen sanyi harda ɗan kankara, da sauri ya lumshe idonshi dan sai yaji kamar yafi daɗi a hakan, sai yakeji kamar masoyinsa milkybar Chocolate dinsa yakeci, dan wani rin gardi yaji kunun yayi mishi.
Jannart kuwa komawa tayi ta ci gaba da aikinta, dan sosai ta tuka tukunzan nan saida ya haɗe da kyau mansa ya fito.
Tsiyaye man tayi a cikin kaskon mai, kana taja kujera ta zauna, tunkuzan ta fara gutsura tana mulmulasu ƴan ƙanana tana sasu kan tray mai ɗan girma.
Yayinda busan doyan da ta daura yake ta tururi alamun ya dahu.
Da sauri ta ida gama mulmula tunkuzan.
Kana ta miƙe ta kaishi cikin store ta ɗaurashi sama tare dasa rariya a kai yadda zaisha iska.
Tana fitowa ta sauke tukunyar ta kwashe doyar cikin, kula biyu manya daya nasu Baba Mauɗo daya nasu sai ƙaramar kuma ta Abba.
Dakakken yajin k’arakon da yasha kayan hadi tasa musu a robobi, kana tasa plates, sannan ta ɗaura wannan man data matse yanzu ta soya, ta sawa kowa.
Ganin kusan ƙarfe ɗaya ne yasa tasa kadan a plate, tare dasa yaji da mai, kana ta fito da salat da dafaffen kwai.
Inda ta barshi a nan ta sameshi ya dukufa kan system ɗin nashi.
A nitse ta wuce shi, shi kuwa yatsun ƙafarta ya ɗan bi da ido har saida ta ɓacewa ganinsa.
Bayan sallan azahar ne duk suna zaune a Dinning table.
Cikin zuba musu ido yace.
“Wlh za'a kasheku da yaji sai Ulcer tayi muku mugun illa, Ramadan kafa san illan yaji, jiya war haka kake cin danwake har kana kuka dan yaji, amma yanzu kazo kanacin wani abu daban kuma.”
Da sauri Ramadan yace.
“Wato harda kuka nayi jiyanko, to amman dai gsky wannan ba yaji, kuma wlh yamin daɗi yama fi min a soya doyan da kwai.”
Riyyam-nsra ne ya ɗan kalleshi yana sa farar doya da yajin k’arago, da yankekken kwai da ƴar al'basa da man gyaɗan a baki yace.
“Gsky nima yamin daɗi wlh, dan Mammy na yawan yi mana shi.”
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Okay aci daɗi lfy.”
Sai lokacin Mamy ta kalleshi a fakaice tace.
“Kai har zaka cewa wani yasan illar wani abu kuma yake ci, kaida kasan ciwonka kuma kake meda zaki abokin rayuwarka.”
Da sauri yace.
“No Mamy ciwo na bashi da alaƙa da zaƙin.”
Kai kawai ta gyaɗa tare da zuba mishi ido irin na tuhuma.
Ganin hakane yasa ya juyawa yayi ya nufi sama...
Haka dai al'amarin zaman gidan yayi ta tafiya.
Cikin kwanakin sosai Rayyern ya samu lfy ya koma kamar da.
A can tashar Arewa kuwa sosai Asiya tayi farin cikin jin lbrin bacewar Jannart daya zo mata da wani nasarar rayuwa.
Tunda gashi aikin da take son din ya dawo hannunta.
A gidan Barrister Kabir kuwa sosai hankalinsa ya kwanta yanzu, ya duƙufa kan fuskantar karar da zai shigar ka'in da na’in, nason tono tsohon zalumcin da aka binne, shekara da shekaru.
Alhaji idi Saleh Dakata kuwa sosai ɓacewar Jannart, ya gigita mishi lamuran rayuwa, wannan yasa ya dade rabonsa dasu Dr.Lukman ma.
Sai dai yau tun safe yake gidan Alhaji Bala Tambari.
Kasan cewar yayi tafiya ne, kusan na wata daya yasa suka jima basu gana ba.
Cikin tsananin takaicin abubuwan da suka faru,Alhaji idi Saleh Dakata ya kalli Alhaji Bala Tambari tare da cewa.
“Toh kaji dai duk abinda ya faru, ni kuwa kaji matakin dana ɗauka, da kuma kalubale da nasarorin dake cikin al'amarin, dole inyi wani abu dan tabbatar da abinda zai kiyaye min ahlina da mutuncina.”
Murmushi Alhaji Bala Tambari yayi kana yace.
“Wannan shirin naka yayi, kaga duk kulafacin mutun da nacinsa bazai cimma manufarka ba, amman inada shawara ta musamman da zan baka, ka bari sai na ɗan huta, zuwa jibi zanzo har gidanka, sai muyi maganan.”
Cikin jin daɗi da dukkan yarda Alhaji idi Saleh Dakata yace.
“Toh ngd matuƙa sai na ganka, ni bari in wuce Tababa Company.”
Daga nan sukayi sallama.
Kasancewar yau ɗin Lahadi ne, ya kama kuma gobe Monday Dr.Rayyern Mai-nasara da PA'nsa zasu tashi zuwa China.
Yau tun safe daya fita bai dawo gidaba.
Shida Abbansa dan suna Mai-nasara campany'n su da aketa kafa injinun kayan aiki.
Suna dudduba duk wata inji ko ƙarfen dakeda matsala.
Bisa jagoranci Engineer Bello, dan su san me-da-me suke da buƙatar sayan sabo, in yaje China.
Gaba ɗaya wurin masarrafin nasu, suketa dudddubawa yayinda PA ke biye dasu a baya, yana riƙe da woyoyin uban gidan nasa.
Shi kuwa Rayyern rike da system nashi yake.
Yana wasu ƴan rubuce-rubuce da alamu bayanan Engineer bello yake adanawa na abubuwan da suke buƙata.
“Wannan shine babbar matsalar data dakatar da komai, badon shiba da tun tuni an fara sarrafa al'kama zuwa fulawa, kana a medata macaroni indomie, da dai sauransu, ganan Cerelac ma da yayi k’aranci, kuma akwai buk’atar lallai muyisa.”
Engr bello ya faɗa yana nunawa, Dr Rayyern wani ɗan ƙaramin ƙarfen da bai taka kara ya karyaba.
Hannu Rayyern yasa ya amshi ƙarfe
Tare da duba numbers din jiki yace.
“Number 2%”.
Da sauri Engr bello yace.
“Eh to 3% ake bukata dan wannan campany'n ai yafi sauran baki ɗayansu girma da manyan kayan aiki,
na manta ne san da zaka tafi ban cema kada ka sayi kamar na wanda ka saba saya