Showing 252001 words to 255000 words out of 350584 words

Chapter 85 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

wayarsa dake gefe ta soma k’ara.

Wanda hakan yasa shi janye jikinsa da sauri, agogon dake daure atsintsiyar hannunsa ya duba.
Ganin da yayi lokaci ya tafi ne kuma, yasa shi mikewa da sauri tare da d’aukan briefcase d’insa.
Haka ya d’auki wayar tasa batare kuma, da yayi picking call din ba, ya fice daga cikin falon da sauri saboda yayi latti sosai.

Jannart kuwa jin alamun ficewarsa daga falonne yasa ta bud’e Idanunta.
Wanda sukayi ja saboda ɗan kukan da tayi.

Kofar falon tabi da kallo mai kama da harara, lokaci daya kuma cikin haushin kanta tace.

“Ni meyasa ma na daina kukanne? Wallahi Allah saiya sakamin, kuma bazan sake fitowa falon ba balle harka Ganni kamin allura na gaya ma Abba na ya hana amin allura.”

Ta kare maganan tana me dawo da sabon sheshshek’an kuka, tare da zamewa ta kwanta awajen.

Rayyern kuwa yana fita agurguje ya shiga motarsa, kaitsaye ya nufi Paradontal hospital, Dan acan zasu gudanar da Kidney Surgery yau din.

*Kano Nigeria*

Alhaji Idi Sale Dakata.

Gaba d’ayansu zaune suke acikin wani katafaren falon, da kaitsaye za’a iya kiransa da aljannar duniya.

Domin kuwa falone daya amsa sunansa.

Alhaji Idi Sale Dakata, Doctor Khamal, Alhaji Abdu Tababa, sai kuma Enginer Alkali Baba da Alhaji Bala tambari.

Way’annan mutane biyar sune ke zaune acikin falon, Yayinda kowannensu da abunda yake sakawa acikin ransa.

Dr. Khamal ne da duk yabi ya had’a gumi duk da sanyin A/C n dake tashi acikin dakin, ya d’ago ya kalli abokan zaman nasa.

Hankalinsa atsananin tashe yace.

“Agaskiya bazan b’oye muku ba na fara tsorata da wannan al’amarin, komai namu sake lala cewa yake kullum, muna fuskantar barazana tako ta ina, daga gefe ga wancan d’an iskan yaron Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mainasara, company d’insa sai kara bunk’asa yake akowacce rana, duk share holders dinmu sun tafi izuwa companynsa, still Acan Moscow din daya tafi, nasarori kawai yake samu, domin duk wani labarin nasararsa yana zuwa kunnena, na rasa yanda zanyi nikam narasa yanda zanyi na kawar da Dr. Rayyern daga doron duniyar nan.”

Shiru ne ya gifta atsakaninsu, kaman na yan wasu minute Alhaji Abdu Tababa ne ya gyara zama, tare da fuskantar Alhaji Idi Sale Dakata.

Cikin yanayin damuwa yace.

“Ina matukar jin tsoron ace shirin da mukayi shekaru 20 baya ya tar watse, dukanmu nan zamu shiga tashin hankali marar misaltuwa, shin menene mafita Alhaji Idi Sale Dakata? Menene mafita.”


Idanu Alhaji Idi Sale Dakata’n ya rumtse, cike da takaici hadi da b’acin rai kuma yace.

“Tabbas tarkon da muka d’ana ne ya kauce, Munkiwata abun harinmu da kanmu amma ayanzu yazo ya b’ace mana, da way’annan hannayen shekaru 22 nayi ina kiwata abun harina, bawai Don ya girma ya amfana dani ba, saidan Nina amfana dashi, tayaya zannemi abun hari na na rasa? Tayaya? Lallai Tabbas akwai wanda yake ankare da takuna, akwai kuma wanda yake dasa hannu akan rasa lu’u’un dinaren dana jima Ina adanawa da b’oyewa.”

D’an tsagaitawa da maganan nasa yayi, tare da d’agowa ya kalli abokan nasa.

Cikin k’una da kuma zafin zuciya yace.

“abun harina ayanzun guda biyu ne, wanda kuma kunsani basai na fad’a ba, Lallai kuma lokaci yayi dazan tauna tsakuwa dan aya taji tsoro, ashirye nake dana kawar da duk wani wanda yace zai shiga gabana.”

“Kwarai kuwa hakan shine dai-dai kuma muma muna bayan hakan, amma wani hanzari ba gudu ba Tayaya ne zamu samo abun harinmu?”

Cewar Engineer Alkali Baba.

Wani irin shu’umin Murmushi mai dauke da tsananin mugunta, Alhaji Idi Sale Dakata yayi.
Ahankali kuma ya mik’e tsaye tare da zura hannayensa acikin aljihun rigarsa.

Cike da isa da kuma yarda da abunda ke cikin zuciyarsa yace.

“Ta yanda muka rasa abun harinmu tanan zamu sake samoshi, Lallai wanine yayi wasa da hankalina ya sanjamin taku, nima kuma zanyi wasa da hankalinsa wajen sanja nawa takun, Yanzu wasan ya fara ni Idi Sale Dakata babu wanda ya isa yamin shamaki da cikar burina, kujira kuga abunda zai faru nanda wattani biyu rak.”

Dariya duk suka kwashe dashi.

Dai-dai lokacin kuma sukaji anbud’e k’ofar falon sirrin da suke ciki, wanda hakan yasa cike da tsananin mamaki hadi da razana duk suka d’ago kansu, inda suka sauk’e idanunsu Akan...!







By
*Garkuwan Fulani*



Akan Barrister Kabir, Wanda shigowansa kenan cikin falon, duk da kuwa yaji abunda suke fadad’in amma saiya yi kamar bai ji komai ba.

Ganinsa da sukeyi dinne kuma yasa Dr Lukman da kuma Alhaji Abdu Tababa yin shiru, tare da soma kallon kallo atsakaninsu, Wanda kuma hakan alamace dake nuna zallan rashin gaskiyarsu.
Alhaji Bala tambari kuwa wani irin kallon ƙasa-ƙ’asa yakeyiwa Barrister Kabir ɗin mai kunshe da alamomi masu tarin yawa.

Alhaji Idi Sale daka ta kuwa wani kallo ya shiga yiwa k’anin nasa, irin kallonnan mai d’auke da ma’anoni daban daban.
Saidai kuma gudun kada Barrister Kabir din ya zargi wani abu, yasa Alhaji Idi Sale dakatan ya d’anyi gyaran murya yace.

“Barrister kazo adai-dai domin kuwa magana muke akan yanda zamu fad’ad’a kasuwancinmu, musamman company’s dinmu, way’anda ayanzu shareholders dinmu suka soma janyewa, badan komai ba kuma saidan sabon Companyn Mainasara wanda ayanzu mafi yawan y’an kasuwa dake cikin jihar Kano, dama na sauran garuruwa, harda mak’otanmu, suka zuba hannayen jarinsu acikin companyn, Wanda hakan kuma bak’aramin tawaya ya kawo ga namu companyn ba.”

Ya k’arasa maganan a dai-dai lokacin da Barrister Kabir ya gama, k’arasowa cikin falon tare da neman waje ya zauna, akan d’aya daga cikin kujerun falon.

Ajiyar zuciya Barrister Kabir ya sauke, kafun ahankali ya d’ago ya soma kallon kowannensu d’aya bayan d’aya.

“Hakan yana da kyau tabbas, domin ni kaina nafahimci cewar, shareholders din companies dinmu sun soma ja baya, musamman kamfanoninmu na kayan masarufi.”

Ya ida maganar yana me kallon Dr Lukman da yake sharce gumin daya kwanta agoshinsa, Wanda kuma Gumi ne na tsananin rashin gaskiya da tashin hankali domin haka nan yake jin fargaba in ya kalli ƙwayar idon Barrister Kabir ɗin.

Alhaji Idi Sale Dakata kuwa, hannunsa yasa ahankali ya dafe zuciyarsa, cikin wani yanayi mai wuyar nazarta yace.

“Shin ka samu wani labari adangane da b’atan Jannart kuwa?”

Yanayin yanda yayi tambayar ne, yasa Barrister Kabir d’ago Kansa ya kalli Yayan nasa.

Tsawon mintuna biyu kafun ya girgiza Kansa, kana cikin nazartar fuskar yayan nasa yace.

“Babu wani labari akan b’atan Jannart, amma dai nasan y’an sanda na bayyane da kuma ss suna nan suna aikinsu akan hakan.”

“Allah yasa aganta, domin kuwa mahaifinta yana cikin tashin hankali da alhinin rashinta, kuma ganinta ne kadai zaisa ya warke daga wannan ciwon daya kamashi.”

Engineer Alkali Baba ya fad’i hakan, yana me kallon Alhaji Idi Sale Dakata.

Barrister Kabir kuwa Kansa ya sunkuyar, tare da sakin wani b’oyayyen murmushi.

Acikin ransa kuwa cewa yayi.

“Lallai watarana Gaskiya za tayi halinta tabbas, watarana fuskokin da suke dauke da murmushi ayanzu, sune wanda zasu kasance cikin bakin ciki da danasani mara amfani da tarin kunya.”

Da alama kuma su Alhaji Idi Sale Dakata’n, sun manta cewar da Lawyer suke tare, Wanda ko yaya aka fadi maganar daba gaskiya ba zai iya gane ta hanyar nazartan ko wanne harafi da ƙididdigansa filla-filla.

Daga haka kuwa Shirune ya biyo baya atsakaninsu, inda kowannensu ya kasance da abunda yake sakawa acikin zuciyarsa.

Musamman Alhaji Idi Sale Dakata, Wanda zuciyarsa ke ci gaba da tsara plan din dake yawo acikin tunaninsa, shi kad’ai yasa tsarinsa haka kuma shi kad’ai yasan inda ya dosa.
Abubuwa uku dake cikin zuciyarsa lallai tabbas saiya cimmasu, koda kuwa hakan yana nufin rasa wasu rayukan.

Yayinda Dr Lukman kuwa babu wani abu dake sukar zuciyarsa akullum, face nasara da kuma d’aukaka had’i da cigaban da Dr Rayyern Bashir Muhammad Mainasara ke samu, musamman akan aikin likitancinsa.
Tabbas wuta ne keci a zuciyar Dr Lukman, Wanda ayanzu bashi da wani buri da ya wuce, kawar da Dr Rayyern a doron k’asa kamar yanda ya alk’awarta wa kansa, cewar watarana tabbas za’a wayi gari babu Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mainasara.

Shi kuwa Barrister Kabir abunda ke cikin zuciyarsa, ingantaccene wanda ya tabbata watarana sai ya faru, matukar yana raye to Tabbas saiya Bayyana b’oyayyen sirrin da aka bunne tsawon shekaru.

*Ethopia*

Riyyam nsra.
Munafukan idanunsa da sukayi ja sosai ya lumshe, tare da sake gyara kwanciyarsa, kana ahkanli kuma ya sake tura hannunsa cikin mararsa.

Batare da an d’au koda minti daya ba kuma, ya sake bude idanun nasa inda ya sauke ganinsa, akan wata kyakkyawar yarinya wacce hoton videon ta ya cika gaban wayarsa.

Sosai yake kallon yanda yarinyar ke motsa duk wata gab’a najikinta da sunan wai rawa.

“Shonah!”
Ya karanta sunan da yarinyar ke amfani dashi, wacce kuma da dukkan alama musulmace, saidai wayewa da kuma rudin shaidan hadi da sharri da illan dake cikin TIKTOK yasa ta koma tamkar y’ar arna marassa tarbiya da al'k’ibballah.

Sake gyara kwanciyarsa yayi, tare da kurawa breast dinta idanu, kasancewar shatinsu ya fito ta cikin t-shirt din dake jikinta.
Duk da cewar yau yafara ganinta a TIKTOK din, amma tayi masa sosai, domin all videos dinta duk na banza ne, Dan ko sau d’aya babu inda ta saka kayan kirki wanda duk tawagar ibilasan TIKTOK d’in kanyi haka wai dan a samu Follower dan yin tutiya da al'ummar da zasuyi ta ingiza su ga hanyar halaka mai fad’i musu gsky suyi mishi taken Allah ka aika munafukinmu can nesa... Sun mance daga bakin magautanka ko mahasadanka kake saurin gane kurenka har ka gyarashi in kana da shi ɗin in kuwa hasadace kawai tasa a sukeka ko a ɓatanci gareka to ai su mahasada gishirine na ci gaban rayuwan ɗan Adam, domin idan Ubangiji yayi nufin ɗaukaka wani bawa nasa to a harsunan magautanka mahasadansa zai ɗaukaka shi!

Bio dinta daya karanta ne kuma yasa shi, following dinta saboda yaga tasa tutar Nigeria, Wanda kuma hakan alamace dake nuna cewar y’ar Nigeria ce.

Take kuwa yaga tayi following dinsa back, before 10 second kuma saiga DM dinta ya shigo wayarsa sabida ganin sunanshi yayi following nata kawai ya isheta abin al'fahari domin sanuwarsa da shuhurarsa ya wuce zaton mai zato.

Idanunsa yad’an zazzaro take kuma yasaki wani irin shu’umin murmushi, ko kusa baikawo aransa cewar zatayi accepting nasa haka ba dan shi kansa yaga kanta yana hayak’i shaidan na kad’a mata tana juyawa da bin linzaminsa.

Shiga cikin DM din nata yayi, inda ta rubuta masa sak’o kamar haka.

“Hey handsome how are you?”.
Inda akarshen rubutun tasa masa wani d’an banzan Emoji dake nuna kwarewarta a iskanci.

Ganin emojin ne kuma yasa Riyyam sake sakin murmushi, cike da shauki ya rubuta. “Sexy.” tare da tura mata, Dan yasan zata fahimci abunda yake nufi dan yasan mafi akasari duk kanwar jace, tabbas akwai na gari a TIKTOK amman basu da yawan watsastsun more especially in akayi duba da shigar mutun da kalamansa sabida mafi aksarinsu tawagar TIKTOK sun zama tamkar rainon karnuka.

Aikuwa take tafahimta.

“You want?”

Ya karanta sakon da ta turo masa, inda jikinsa na b’ari yayi mata reply da.

“Yeah I want.”

Emojin murmushi ta turo masa, take kuma saiga wasu bad videos dinta sun shigo wayar tasa, tare da message na “Where are you living?”

“Oh My God she’s hot”

Riyyam din ya fada da d’an karfi, tare da zaro harshensa ya lashi labb’ansa, tare da kurawa videon da yake kallo din idanu.

Yanda yaga yarinyar naked ya masifar tayar masa da hankali, take yaji yanason yin video call da ita.

Hakan yasa cikin gaggawa ya tura mata number dinsa, tare da sawa ta turo masa nata.

Da hanzari yayi dialing numbern nata to face time.

Dai-dai lokacin kuwa Zaitoon ta turo kofar dakin nasa, bakinta dauke da sallama.

Amatukar zabure ya kifa wayartasa, tare da juyowa yana kallon Zaitoon din, da munafukan idanunsa na rashin gaskia.

Itama Zaitoon din kallonsa tayi, ganin da tayi duk yana zabure ne kuma yasa ta, watsa masa harara tare da cewa.

“Are you okay?”

“Yea I’m okay, mekika shigoyi dakina?”

Riyyam din ya tambayeta yana me hade fuska, tare dayin rau rau da idanunsa.
Alamun dai rashin gaskiya.

“Oho mezanzo nayi ad’akin dan rawan TIKTOK? Mammy ne tace nazo nakiraka.”

Zaitoon din ta fada tana me hararansa, batare kuma da tajira maizaice ba, ta juya tayi tafiyarta.

Tana fita kuwa Riyyam din ya zaro wayarsa, tare da ci gaba da watching videon yarinyar.

Sam kwata-kwata ajikinsa baya majin cewa, hakan da yakeyi badai dai bane, bayan kuma ada ba haka yake ba, fitowar TIKTOK ne duk ya sauya masa rayuwa, kuma ayanzu yanajin cewa yakai Namiji, yaje stage din da yakejin Mace ne cikon rayuwa.
Subahanallah saboda waya kawai arana, baisan irin yawan zunuban da yake dibarwa kansa ba, nau’in Zina babu Wanda bayayi kamar dai yadda matan TIKTOK ke bada dama ta wurin bayyana surar jikinsu, yayi zina da ido sannan yayi na baki, still kuma yazo yayi na gaskiya.
Wanda a zahirin gsky taɓararsa ma da d’an sauk’i akan wasu da suka meda man hajar dandalin yad’a fasadin luwad’i da maɗigo ya subahanallah.

Haka dai ya b’ata lokaci yana kallon videos din yarinyar, batare daya tuna cewar Mammy nakiransa ba.

Wannan itace banzar d’abi’ar Riyyam nsra wanda, Mammy dama y’an uwansa basu san yanayi ba.

Wanda kuma hakan k’addarace kana kuma rubutaccen Al’amari wanda Allah Ya rubuta, dole kuma saiya faru.
Ta k’ark’ashin sakacin iyaye da sakarwa yaransu wayoyi kara zub’e suyi tsiyar da suke so.

Kano Nigeria

Murmushin Mamy tayi tare da kallon Ramadan da yake gyara zaman hulan kanshi sai k’amshi yakeyi.
“Toh naga dai alamun sauri kakeyi, kaje kawai sai ka dawo muyi mgnar!”.
Cikin jin dad’in hakan ya saki murmushin da fuska tare da cewa.
“Dad’ina da ke Mamy na saurin ganuwa, sai na dawo”.
Ya ida mgnar yana mai fita.
“Allah ya kikaye hanya, ka gaida min surkar tawa”.

“Amin zataji”.
Ya faɗi yana fita.

Yana fita kai tsaye side d’in Baba Maud’o ya nufa,
Kai tsaye cikin d’akinsa ya nufa, yana mai sallama a saman lips ɗinshi.
Wani irin masifeffen bugun zuciya Baba maud’o yaji, lokacin ɗaya cikinsa ya fara ɓari miƙewa yayi cikin zafin nama, ya juyawa ƙofar shigowa baya,
da sauri Ramadan ya tsaya ganin alamun yanzu Baba Maud’on ya fito wonka don dashi sai gajeren wando,
shiru yayi baiyi mgna ba haka shima Ramadan sai dai idanunshi da ya zubawa k’eyan Baba Maud’on cikin wani irin yanayi,
Shi kuwa Baba Maud’o hannunshi yake miƙa wa gefen gadon inda rawanin buzayensa yake, yana mai son jawowa,
Da sauri ya kuma kauda kanshi jin muryar Ramadan na cewa.
“Afwan Baba Maud’o dama zan sallamekane zan tafi gun Rainaha”.
Cikin daburtacciyar murya ba tare da ya juyoba yace.
“Masha Allah Ramadan sai ka dawo”.
Kasake Ramadan ɗin yayi ganin sam Baba maud’on yaƙi juyowane yasa ya juya ya fita.
Mota ya shiga kai tsaye ya nufi gidansu Raihanan.

*RUSSIA*

Mascow.

5:30 pm.

Dai-dai daya bayan daya suke fitowa, daga cikin babban theatre room din, da suka kwashe sama da awanni 4 acikinsa, suna gudanar da Kidney surgery.

Ahankali yake tafiya yana me kokarin Zare, hand gloves din dake hannayensa.

Wassai yakejin zuciyarsa, babu wani damuwa domin yayi archiving duk wani abunda yakeso, domin kamar koda yaushe yauma yayi nasara akan surgery din da sukayi, kuma shi yayi winning.

Wanda hakan yasa matsayinsa ya zama na musamman akan sauran Doctors, din da sukeyin aikin tare.

Dr Pola Denemith wanda shine babban shugaba awajen. ne ya karaso inda Rayyern din yake, tare da mika masa hannu, cikin jinjinawa yace.

“Congratulations succeeder”.

Murmushi Rayyern din yayi, Wanda ya bayyana tsananin kyawunsa, hadi da zallan kwarjini da kuma haiban da yake dashi.

Cikin muryarsa ta nutsuwa akoda yaushe yace.

“Thank you Sir.”

Sauran Doctors din da sukayi aikin tare ne, kuma suka zo suna yi mishi congrats.
Saboda ya samu sakamako mai kyau, domin sosai surgeryn da yayi din yayi kyau.

Ahankali yakai dubansa ga tsadadden agogon dake daure akan tsintsiyar hannunsa.

5:45 dai-dai daya ganine yasa shi furzar da iska mai sanyi ta bakinsa.

Ahankali kuma ya lumshe gajiyayyun idanunsa, saboda fad’o masa arai da tayi.

Kukan shagwab’anta ne ya shiga yi masa yawo acikin brain, Wanda hakan yasa ahankali ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya.
Still agogon hannun nasa ya sake kallo, for the first time da yaji zuciyarsa ta karbi tunaninta.
Yasan bata da lafiya tun safe kuma daya fita bai sake bin takanta ba, haka kuma yasan zuwa yanzu dole tanajin yunwa.
“Ko taci abincin rana? Uhum na safen ma da ya taci”

Zuciyarsa tayi masa tambayar, da baida amsarta yana mai jin zaƙuwan komawa gida.

“Zamu iya wucewa ko naga dare yanayi.”

Muryar Dr Sulaiman ta katseshi daga tunanin da yakeyi.

Numfashi mai dumi ya d’an fesar, batare kuma daya kalli Dr Sulaiman din ba yace.

“Eh muje.”
Ya kare maganan yana meyin gaba, Wanda hakan yasa su Dr Sulaiman din rufa masa baya, domin kuwa sudinma duk agajiye suke.

Kamar yanda suka saba kuma, koda sukazo compound din asibitin, direct motarsa ya shiga, sukuwa already dama taxi najiransu, shiyasa bawani b’ata lokaci duk suka fice daga cikin asibitin.

Sannu ahankali yake driving motar, tare da bude glass din window‘ dake kusa dashi, yana me shakan daddd’an iskan dake busawa, gefe guda kuma ga tsananin sanyin da ake na ratsa jikinsa.

Kasancewar kuma glass din windown motar nasa asauke yake ne , yasa duk jacket din dake jikinsa bai hanasa jin daddad’an sanyiba

Wani irin yanayi yakejin kansa aciki yaudin, yanayin da baisan dame zai kirasa ba, baisan meyasa yakejin yanason ya koma gidan ba.

Idanunsa ya kuma dan lumshewa ahankali, sakamakon tunawa da yanayinsu na jiya da yayi, yanda kirjinsa ya had’e da nata, da kuma hucin numfashinta dake sauka akan fuskarsa da yanayinsu na safiyar yaud’in.

Take yaji tsikar jikinsa tayi wani irin zubawa, dai-dai lokacin kuma ya iso, wani katafaren Cafe, Wanda anan yakeson yi musu takeaway yau din.

A kasalance ya bude murfin motar ya fita

Direct cikin Cafe din ya shiga, cikin mintuna kalilan kuma yasa akayi musu takeaway, saidai yau Arab dishes ya saya musu, da kuma kalan abincin yan Russia’n.

Bayan ya kammala ne kuma ya dawo motarsa, tare dayi mata key direct ya nufi hanyar Mosque saboda yafiso sai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login