Showing 189001 words to 192000 words out of 350584 words
yake nufi.
Kanta kawai ta girgiza, shikuwa cikin sauri ya juya ya nufi waje.
Yana shiga mota Ari ya bud’e masa gate, kaitsaye ya cilla hancin motar tasa waje, direct kuwa gidansu Rayhannan sa ya nufa, yana mejin wani irin shauk’i acikin zuciyarsa.
Koda ya isa gidan nasu tarba na mutumci ya samu daga wajen mahaifiyar Rayhannan, bayan Rayhannan ta fito ne kuma ya tsura mata idanu, baya ko k’yaftawa, kasancewar ta mai kunya ne kuma yasa ta sadda kanta k’asa.
Asanyaye tace.
“Please ka daina kallona hakanan.”
Murmushi yayi tare da gyara zamansa, cikin jin dadi yace.
“Tayaya zaki hana mutun kallon Matarsa? Ke dinfa yanzu gab kike da zama tawa.”
Murmushi tayi tare dasa hannu ta rufe fuskarta.
Haka dai suka sha hirarsu kafun daga bisani yayi mata sallama ya tafi.
Daga gidansu Rayhannan kuwa gida ya dawo.
Yana zuwa kuwa ya samu Baba Maud’o zaune abakin gate.
Da sauri ya k’araso wajen Baba Maud’on, cikin sakin fuska da dokin da har yanzu bai gama sake shiba yace.
“Baba Maud’o an bani Rayhanna, d’azun Abba yake fadamin.”
Murmushi Baba Maud’o yayi tare kuma da Kallon Rayyern din, jikin taya shi murna yace.
“K’warai kuwa Ramadan nasani, Abbanku ya fad’amin na tayaka murna sosai.”
Murmushi mai kama da Dariya Ramadan din yayi, tare da juyowa ya fuskanci Baba Maud’o, kana ransa asake yace.
“Baba Maud’o na kasa b’oye farinciki na, hankalina ya kwanta, yanzu bani da wani sauran fargaba, kana min addu’a please Baba Maud’o, Allah yasa albarka acikin had’innan.”
Murmushi Baba Maud’o yayi wanda har saida sautin ta, ya fito fili cikin sakin fuska yace.
“Insha Allah Ramadan, addu’a kuma kullum inayinta, Allah yasa matarka ce ya kuma kawar da duk wani fitina.”
“Ameen Ameen.”
Ramadan din ya amsa, tare da mikewa kaitsaye ya nufi cikin gidan nasu, kasancewar dare yayi kuma bacci yakeji.
Washegari.
*Mascow*
Ahankali yake driving motar da yanayinsa, dake bayyana tsananin gajiyar da yake d’auke da ita da yunwa.
Kaitsaye gida ya nufa, dai-dai ya hau wani titi ne kuma, wayarsa dake gefe ta soma kara alamun shigowar kira, share wayar yayi, kamar bazai d’aga ba kuma sai ya d’auki wayar, Ganin sunan Abbansa ne kuma ya sashi d’aga wayar da sauri.
Tare dayin Sallama.
Daga can b’angaren Abba ya amsa.
Shikuwa Rayyern din cikin sanyi yace.
“Abba yasu Mamy da Baba Maud’o.”
Abba dake zaune afalo gyara zama yayi, tare da cewa.
“Duk Suna lafiya, Mamynka tace agaisheka, ya Jannart take?”
sake gyara zaman wayar akan kunnensa yayi, kana cikin nutsuwa yace.
“Lafiyanta Qalau.”
Kai Abban ya jinjina tare da cewa.
“Masha Allah To bata wayan mugaisa.”
Jin abunda Abban ya fad’ane kuma yasa shi, danna Horn din motarsa, cikin dan ladabtar da murya yace.
“Abba bana gida, amma yanzu nake kokarin komawa.”
Daga can b’angaren kuwa jin Karan Horn din mota ne, yasa Abban yarda da abunda Rayyern din yace, cikin jaddadawa yace.
“Shikenan babu damuwa, Idan ka koma saika had’ani da ita.”
“To Abba Allah Yasa kada na manta.”
Jin abunda Rayyern din ya fad’ane kuma, yasa Abban yin shiru, Cikin d’an yanayin bacin rai yace.
“Rayyern!”
Da sauri ya amsa da
“Na’am Abba.” domin jin yadda Abban ya kirashi ba wasa
“Rayyyern!!”
Abban ya kuma kiranshi a dake.
“Na’am Abba.”
Still Rayyern din ya sake amsawa cikin fargaban umarnin da za'a bashi ko fada
Abban kuwa ransa ab’ace yace.
“Rayyern ni kake cewa, Allah yasa kada ka manta hadani da matarka?”.
Da sauri ya jujjuya kansa tamkar yana gaban Abban.
Shi kuwa Abba cikin dakile murya yaci gaba da cewa.
“Bansan Wacce irin rayuwa kakeso kayi da yarinyar nan ba, Wacce irin rayuwace haka Rayyern, Jannart matarka ce fa, wallahi wallahi Allah saiya tambayeka, akan hakkinta, baka kyautawa Rayuwarta Rayyern, akan ka afarayin aiki da kasuwanci da karatune? ko kaine kawai ma’aikaci a duka duniyar nan? Meye ka d’auki kanka da bazaka kula da matarka ba? kasani ko yau ka mutu Allah zai kama ka, da rashin sauke nauyinta dake kanka, kuma kasani ban baka ita ka tafi da ita don kayi ta wofantar da ita ba, tayaya zakana irin wannan sakacin, kullum Kai baka gida, baka da lokacinta kenan?”.
Lips d’insa ya d’an taune, cikin sanyin murya yace.
“Abba kayi hakuri...”
“Nayi hakuri dame Rayyern?”.
Cikin girmamawa yace.
“Abba kayi haƙuri akan komai ma na tuba”.
Cikin fada Abban yace. “Bani zaka bawa hakuri ba kasan Wacce zaka bawa hakuri, yarinya tana zaune ak’ark’ashinka amma baka San abunda ya dace ba, tunda ta tafi batayi waya da kowa ba, ka kulleta awaje daya, sannan yanzu Ina maka magana, kana cewa wai Allah yasa kada ka manta, shikenan yayi maka kyau Allah yasa ka manta ɗin!!!”.
Abban ya fadi maganan atsawace, kuma cikin fushi lokaci daya kuma ya katse kiran.
Da sauri Rayyern yabi wayar da kallo, lokaci daya kuma yaji duk zuciyarsa babu dadi, ajiye wayar agefensa yayi, domin dai-dai lokacin ya iso gida.
Yana gama dai-dai-ta parking, ya bud’e murfin motar ya fito.
Hannunsa rik’e da waya da kuma, ledodin takeaway din da yayi musu ya nufi cikin falon gidan.
Yana shiga kuwa ya zauna akan daya daga cikin kujerun falon.
Wayarsa ya dauka ya sake dialing numbern Abban.
Har saida wayan ta kusa katsewa kuwa, kafun Abban ya d’auka.
Jin Abban ya d’auki wayarne kuma yasashi, kwantar da murya cikin sanyi yace.
“Dan Allah Abba kayi hakuri, zanyi yanda kake buk’ata.”
Daga can b’angaren Abba azafafe yace.
“Hakurin me kake bani ne Rayyern?.”
Rayyern din kuwa sanin halin Abban nasu, Idan har yayi fushi ne yasa shi, sake yin k’asa da murya cikin tausasa harshe yace.
“Naji Abba kayi hakuri Dan Allah! In sha Allah zan kiyaye zanyi yadda kukeso”.
Idanunta ta bud’e da sauri, saboda jin muryarsa da tayi, da dukkan alama kuma tasan waya yakeyi.
Saurin tashi daga kwancen da take tayi, tare da Kai dubanta ga kofar dakin nata.
Duk yau zaman gidan bayayi mata dadi, saboda kadaici, ga kuma wani irin masifaffen kewa daya cika zuciyarta, tana matuk’ar son tayi magana da Abba Kabir dinta, wannan dalilin yasa ta yanke cewar, Idan ya shigo yau din zata rok’esa aron waya.
Da sauri ta zuro da k’afafunta k’asa, batare kuma da ta damu da shigar riga da wandon dake jikinta ba, kaitsaye ta nufi falon, kanta sanye da hulan sanyi, sai kuma wani bedroom shoe mai kyau.
Riga da wandon dake jikin nata kuwa, bak’aramin bayyana shape dinta sukayi ba, duk da cewar Suna da kauri, amma sunyi mata kyau sosai, Dan saita fito kamar irin y’an matan turawa dinnan, domin saboda tsabar zaman waje d’aya, har wani yellow da ja skin dinta yayi tsabar fari.
Ahankali ta bud’e kofar dakin ta fito.
Tana fitowa kuwa yana sauke idanunsa akanta.
Saurin yin kasa da kanta tayi, tare da karasowa cikin falon.
Shikuwa tun fitowarta ya kasa d’auke idanunsa, daga kallonta saidai fuskarnan tasa babu alaman Murmushi.
Ahankali ta zauna akan carpet, tare da nannad’e k’afafunta.
Rayyern din kuwa Ganin ta zauna ak’asan san ne, yasa shi gyara zamansa, tare da kwantar da murya cikin ladabi yace.
“Abba gatanan na shigo cikin gidan.”
Yana gama fadin hakan ya mik’a mata wayan.
Ai kuwa kaman jira take har hannayenta, na rawa wajen amsar wayar.
Tana karawa akan kunnenta, tayi Sallama.
Abban ne ya amsa mata, cikin kulawa da kuma sakin rai yace.
“Jannart ya kike ya gida, fatan komai da komai lafiya.”
Ajiyar zuciya ta sauke cikin tsananin jin dadi, tace.
“Lafiya k’alau Abba yasu Mamy, Ramadan da Baba Maud’o.”
“Duk Suna lafiya, gama Mamyn naku anan kusa bari na bata.”
Cikin jin dadi Jannart din ta jinjina kai, Jin Mamy ta karb’i wayanne kuma yasa ta karyar da wuya, cikin muryar shagwab’a tace.
“Ina wuni Mamy.”
“Lafiya kalau Jannart dinmu, wallahi munyi kewarki sosai, fatan dai kina nan lafiya.”
Mamyn ta tambayeta cike da kulawa, hadi kuma dajin dadin samun Jannart din.
“Nima nayi kewarku sosai Mamy, nayi kewarku sosai da sosai garin ba dadi sam Mamy, Ina Ramadan?”
“Ramadan yana can wajen aiki, kullum saiya tambayeki.”
Mamyn ta fad’a tana nazartar kalmar Garin ba dadi sam da Jannart ɗin ta fadi, shadar zaman doya da manja sukeyi kenan.
Jannart kuwa Kai ta kwantar kana cikin sanyi, tace.
“Ayya Mamy kice ina gaishe sa, Idan kunyi waya da Riyyam nsra ma kice ina gaishesa.”
“To Jannart Insha Allah zasuji, amma Ina dai babu wata matsala kam?”
Kai Jannart din ta d’an sunkuyar, cikin tausasa murya tace.
“Eh Mamy babu komai.”
“Masha Allah haka akeso ai, amma dai kina kulawa da sanyi, Dan naji ance sanyin garin daban yake dana kowacce k’asa.”
“To Mamy.”
Jannart din ta amsa, daga hakane kuma sukayi sallama da Mamyn, sosai Jannart taji dadin wayar da sukeyin, musamman taji zuciyarta tayi sanyi.
Acikin kaso 50 na damuwarta duka sun kau, dama matsalarta kewa ne kawai.
Ahankali ta zare wayar akan kunnenta, tare da mik’o masa.
Idanunsa dake alumshe ya bud’e tare kuma dasa hannu ya karb’i wayar.
Itakuwa Jannart maida kanta k’asa tayi, tare da sauke idanunta akan yatsun k’afarsa, wanda taga yana d’an motsa su Ahankali.
Idanu tad’an zubawa yatsun nasa, bakinta kuwa Ahankali yake motsi da alama, wani abu take son fad’a.
Rayyern dake zaune asamanta kuwa, Akasalance ya Kai dubansa gareta, karab kuwa idanunsa suka sauk’a akan saman kirjinta, kasancewar rigar da ta saka din mai d’an fad’in wuya ne, shi yasa saman kyawawan breast dinta suka bayyana.
Janye idanunsa gefe yayi, tare da maida kansa ya kwantar ajikin kujera.
Itakuwa Jannart d’agowa tayi ta kalleshi, Ahankali ta d’an had’e hannayenta waje d’aya.
Cikin daddad’an murya da kuma sanyin yanayi, mai kama da rok’o tace.
“Ummmm... Dan Allah kakiramin Abbana!!!”
Ta k’are maganan cikin seizing voice, lokaci daya kuma Idanunta suka kawo ruwa.
Yanayin yanda yaji sauti da Amon muryar nata ne, kuma ya saka shi bud’e idanunsa, tare da Kallon cute face dinta.
Ahankali ya mik’o mata wayar, ba tare kuma daya ce komai ba, ya maida kansa.
Itakuwa Jannart cikin jin dadi ta mik’e tsaye, da wayartasa ahannunta kaitsaye ta nufi dakinta.
Tana shiga kuwa tayi dialing numbern Abba Kabir.
Cikin sa’a kuwa bugu biyu wayar ta shiga.
Rayyern kuwa Ganin ta shiga daki ne, ya sashi tashi shima ya wuce nasa d’akin, bayan yayi al'wala ne kuma ya wuce masallaci.
Jannart Kuwa tanajin Abba Kabir ya d’aga kiran, ta kara wayar akan kunnenta, lokaci daya taji tamkar zatayi kuka, cike da matsanancin kewa, batare da ta iya amsa sallaman da yayi mata ba tace.
“Nayi kewarka sosai Abbana.”
Daga can b’angaren Abba Kabir kuwa, Jin muryar Jannart d’insa ya sashi lumshe ido, shima cike da tsananin kewa hadi da jin dadin, kiransa da tayi yace.
“Muma haka Jannart dina, munyi kewarki sosai, ya Mascow din, fatan duk kuma nan lafiya.”
“Lafiya K’alau Abbana, yasu Aunty Dijat dasu Hafeez, Allah nayi kewarsu sosai, har ma da Daddy na.”
Ta kare maganan cikin shagwab’a.
“Duk suna nan lafiya Jannart, suma kuma sunyi kewarki, Ina Rayyern din?”
Abba Kabir din ya tambaya, Dan waigawa bayanta tayi, kamar Wacce takesa ran ganinsa sai kuma tace.
“Yana lafiya Abba.”
Kai Abba Kabir din ya jinjina, cike da jin dadin jin muryoyin juna, haka suka sha hirarsu, bayan sun kammala wayar ne kuma ta tashi tayi Sallah.
Shikuwa Rayyern bashi ya dawo gidan ba, saida yayi sallan Isha, Koda ya shigo cikin falon, zama yayi akan sofa tare da d’aukan, abincin daya shigo dashi ya danci kad’an.
Bayan ya kammala cin abincinne kuma ya mik’e tsaye, direct dakinsa ya wuce, yana shiga ya soma rage kayan dake jikinsa.
Wani fari kal din towel ya d’aura akan waist d’insa, tare da nufar toilet kaitsaye.
Duk da cewar yana jin gajiya sosai ajikinsa, amma hakan bai hanashi yin wanka anutse ba, yana fitowa daga wankan direct gaban dressing mirror d’insa ya nufa.
Wani d’an k’aramin towel ya d’auka, tare da soma goge jikinsa dake jik’e da ruwa, sosai gargasan jikin nasa suka kwanta lub, ga wani hasken fatarsa daya sake bayyana.
Body lotion kawai ya shafa ajikin nasa, sai kuma turarensa mai dadin kamshi, bayan ya gama shafa mai dinne kuma, ya saka wani wandon boxer ajikinsa.
Duk da sanyin da ake yi kuwa, haka ya nufi kan gadonsa ya kwanta, batare da ya saka riga ko rufe kyakkyawar surar jikinsa ba.
Kwanciyar rub da ciki yayi tare da jawo laptop dinsa, ya soma dannawa.
Acan b’angaren Jannart kuwa, Koda ta idar da sallan nata, kwanciya tayi akan gado, zuciyarta cike da nishadi, saboda duk wani damuwan dake zuciyarta ya kau, yau tayi waya da Abbanta da kuma su Mamy, taji komai yayi mata wasai.
Gyara kwanciyarta tayi, juyawan da zatayi ne kuma Idanunta suka sauk’a, akan wayar Rayyern da ta ajiye akan bedside drawer dinta wayar na kawo haske alamun kira.
Da sauri ta d’an dafe goshinta, saboda ita gaba daya ma ta manta da batun wayar.
Sanin da tayi cewar zai buk’aci wayarne, kuma yasa ta tashi daga kwancen, wasu takalman ta saka tare da miƙa hannu zata jawo wayar.
Garin hakane ta amsa kiran.
Juyo fuskar wayar tayi da niyar taga wake kira sai taga ashema ta amsa kiran.
Sabon number ne, da sauri ta kalli rubutun dake ƙasan number Ethiopia ta faɗa cikin nazari, alamun daga can kiran yake.
Kiran na gab da sinkewa ta amsa da addu'ar ko Riyyam-nsra ne,
Da sauri ta kara wayar a kunne jin muryar Riyyam-nsra yana cewa.
“Asssalamu alaikum, Hamma Rayyern”.
Cikin sakin fuska da jin daɗin tace.
“Wa alaikassalam Riyyim”.
“Lahh My Aunty”.
Riyyam-nsra ya faɗi cikin jin daɗi da so da mutuntaka.
“Na'am Riyyam-nsra yasu Mammy da Zaytoon.”
“Duk suna lfy, mu Aunty nayi kewarku, kullum ina son in kiraku bani da number ku Hamma Radaman ɗan wulaƙanci sai yau ya turo min”.
Hanyar fita ta nufa tare da cewa.
“Allah sarki autan Mammy i miss u so much wlh”.
Cikin jin daɗi yace.
“wlh na fiku kewa gaba ɗaya yanzu Ethiopia ta daina min daɗi ma yaseen”.
Ya ƙare mgnar yana shiga falon Mammynsa.
Ita kuwa Jannart
murd’a handle din kofar tayi ta buɗe kana ta fito kaitsaye ta nufi dakinsa.
Suna masu ci gaba da mgn da Riyyam-nsra.
Ahankali ta murd’a handle din k’ofar d’akin nasa, tare dasa K’afarta ciki.
Cikin wani irin yanayi t...!
By
*GARKUWAR FULANI*
Sassayan numfashin ta fesar kana.
Tasa k’afarta na dama acikin d’akin, wani irin sassanyan kamshi daya daki hancinta ne, ya sata lumshe Idanunta tare da, turo kanta cikin dakin bakinta d’auke da sallama.
Sako kanta acikin dakin da tayi ne kuma, yasa idanunta sauk’a akanshi, inda yake kwance sanye da boxer ajikinsa, sai kuma laptop d’insa daya saka agaba da alama, wani aiki mai muhimmanci yakeyi.
Da sauri ta juya tare da kawar da kanta gefe, saboda wannan ne karo na farko acikin rayuwarta, da ta fara Ganin namiji haka dagashi sai yar finkilar boxer.
Rayyern kuwa dake kwance jin sallama, da kuma motsinta ne ya sashi jan blanket ya d’an rufe cinyoyinsa, tare kuma da juyowa ya kalleta.
Tsaye take amma ta kawar da kanta gefe, sannan tasa duka hannayenta akan kirjinta, da’alama kuma sanyin dake cikin dakinne yayi mata yawa.
“Meye?”
Ya fad’a yana me tsareta da idanunsa, saboda tunda suka zo bata tab’a shigowa cikin d’akin nasa ba sai yau.
Tsayuwarta ta d’an gyara tare kuma da juyowa ta fuskancesa, saidai bata yarda ta sake ajiye Idanunta akansa ba.
Cikin sanyin muryarta da akullum, take fitar da wani irin daddad’an sauti tace.
“Dama wayarka ake kira shine na kawo ma.”
Ta k’are maganar tana me d’an matsowa jikin gadon, a hankali saboda mik’a masa wayar.
“Gashi.”
Ta fad’a adai-dai lokacin da ta iso kusa dashi.
Hannunsa ya mik’a mata, still yana daga kwancen batare daya tashi ba, cikin wata irin murya yace.
“Give me.”
Mik’a masa wayar tayi, kasancewar ta sunkuyar da kanta k’asa ne kuma, yasa ta sauke Idanunta akan, wasu kwantattun gashin dake kwance akan kirjinsa, wanda kuma sudinne suka taho har zuwa, saman cibiyansa, gashi ne masu kyau da laushi, duk da cewar basu da yawa amma sun k’awata, farar fatar jikinsa sosai.
Tsaida idanunta tayi akan saman mararsa, wanda tananne gargasan sukafi yawa, kuma sun kwanta lub lub gwanin ban sha’awa, Kallon gashin jikin nasa ne kuma yasa, ta kasa sakar masa wayar da take mik’a masa.
Tana son gashin jiki sosai domin abun yana yi mata kyau, musamman awajen Namiji, duk da cewar ta saba kanin na legs din, Ya Junaid kasancewar ya saba zama da gajerun wanduna, amma bata tab’a ganin kyawawan gashi kamar na Rayyern din ba, saboda shi nasa har wasu shining sukeyi.
Rayyern kuwa dake mik’a mata hannu, Idanunta ya kalla saboda yaga ta kasa sakar masa wayar.
Ganin yanda take Kallon jikinsa ne kuma, ya sa shima ya kalli jikin nasa, saboda atunaninsa ko wani abun ta gani.
Fahimtar da yayi cewar hairs d’insa take kallone, kuma ya sashi dawo da kallonsa gareta, Cikin yanayin gajiyawa da Kallon nata yace.
“Wai duk wannan Kallon kam na menene Malama? ko cinyeni kikeson yi ne, Dan nasan zaki iya ko dai naci miki bashin wani abune kike kallonsa a jikina?.”
Maganan nasa daya fad’a ne yasa tayi saurin yin k’asa, da kanta tare da sakar masa wayar, lokaci daya kuma taji wani irin kunya ya lullub’e ta, saboda Sam bataso hakan ya kasance ba.
Jin ya karbi wayarne kuma yasa ta juyawa, da sauri ta fice daga cikin dakin.
Rayyern kuwa bakinsa ya tab’e, tare da bin bayanta da idanu, kasancewar tana tafiyar nata cikin sauri ne kuma yasa, duk wani gab’a dake jikinta motsawa, musamman big hips dinta way’anda suke da shape na burgewa, duk da cewar rigar bacci ne ajikinta, amma hakan bai hana hips din nata bayyana ba, saboda rigar jikin nata yana da santsi, ga kuma dogon gashin kanta daya sauko har bayanta.
Saurin kawar da idanunsa daga kan hips din nata, yayi tare da maida kansa ya ajiye akan pillow, akaron farko na rayuwarsa da yaji zuciyarsa na tsananta, bugawa akan wani abu na daban.
Idanunsa ya d’an lumshe tare da sauk’e Ajiyar zuciya.
Wayartasa ya kunna tare da duba mai kiran nasa, Ganin new number ne kuma ya sashi share kiran, saidai ko minti 1 ba’a rufa ba, wani kiran ya sake shigowa, Ganin kiranne kuma ya sashi d’agawa tare da kara wayar akan kunnensa.
Daga can b’angaren Riyyam yace.
“Hello Hamma Rayyern Riyyam-nsra ne.”
Ajiyar zuciya Rayyern din ya sauk’e, saboda Jin muryar Riyyam din, cikin muryarsa dake nuna d’an yanayin kasalan dake tattare dashi yace.
“Riyyam yakake yasu Mammy.”
“Lafiyanmu k’alau Hamma Rayyern, saidai nayi kewarka sosai, Mammy da Zaytoon sunce na gaisheka, kuma Hamma Rayyern mafa tuntuni nake cewa, Hamma Ramadan ya bani