Showing 258001 words to 261000 words out of 350584 words

Chapter 87 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

Mamy kuma dazu ma na nemi wayan Ramadan baya shiga.”

“Hmmm ai Ramadan kam basamunshi zakayi ba, domin tunda akasa masa ranan biki baida nutsuwa, ni har abun nasa ma tsoro yake ban, ban tab’a ganin mutum maison aurensa kamarsa ba, kullumfa yanzu agidansu yarinyar yake wuni.”

Mamyn ta fad’i hakan tana me Dan hararan Ramadan din dake zaune agefenta, Wanda kuma yanzu saukowansa daga sama, cikin shirinsa na zuwa zance.

Rayyern kuma jin abunda Mamyn ta fad’a ne yasa shi dan sakin murmushi, tare da gyara kwanciyarsa batare kuma da sanin Ramadan din na tare da Mamyn ba yace.

“Nifa Mamy asona dama adaga auren Ramadan sai after k’aramar Sallah, saboda akwai ayyuka da yawa a hospital dama company wanda suke bukatar nutsuwarsa kuma kinga ni sai bayan sallan zamu gama mu dawo.”

Wani irin zabura Ramadan dake zaune akan kujera yayi, sakamakon Jin abunda Rayyern din ya fada, kasance war a hands free Mamy tasa wayan.

Cikin kuma yanayin nuna damuwa da tsananin son auren da yakeyi, murya na amsa amo yace.

“What ad’aga aurena kuma Hamma Rayyern, wallahi ni babu Wanda zai d’aga aurena Haba Haba Dan Allah, shekaru nawa na kwashe inason aure, ai nutsuwar jiki nama shine Aure, ni inba Auren nan nayi ba ai aikinma dainashi zanyi, kullum fa yanzu kwana nake ina lissafin kwanakin da suka rage.”

Ya kare maganan with full confidence, Dan gaba daya ma ya manta da cewar agaban Mamy yake.

Rayyern kuwa jin abunda Ramadan din yafa d’ane, yasa shi sakin murmushi mai sauti, kasancewar shiba mutum bane da ya iya dariya sosai, shiyasa always murmushi ne dariyarsa.

Mamy kuwa baki bude take kallon Ramadan, cike kuma da mamakinsa tace.

“To kadaiji ko Rayyern da kunnenka, ko kunyana ma Ramadan bayaji, akan wannan auren ai saiya tayar mana da yak’i, yanzu ma haka ashirye yake zai tafi gidansu budurwar tasa, kullum zance ko gajiya da hiran ma basayi.”

Mamyn ta fada still tana me sake hararan Ramadan din, irin hararan nan ta wasa.

Yayinda shi kuwa ya sauke kansa kasa, Dan sai ayanzunne ma yakejin kunyan Mamyn nasa.

Rayyern kuwa ayanzun dariya yayi, duk da yasan wasa Mamyn take, amma sarai yasan halin Ramadan da son aure.

“Rayyern ina Jannart din take, ya kuma jikin nata?”

Mamy ta tambaya, domin dama dalilin dayasa takira din kenan.

Sassanyar ajiyar zuciya Rayyern din ya sauke, kana ahankali ya tashi zaune, cikin kuma muryarsa dake nuna girmamawa yace.

“Jikin nata da sauki sosai.”

“Masha Allah to hadani da ita mugaisa, Dan numbernta na fara kira amma baya shiga.”

“To Mamy.”

Ya fada yana me lumshe
Tsumammun idanunsa, Wanda basu gama washewa ba, lokaci daya kuma zanen surarta ya sake dawo masa.
Hakanan kuma yaji tsikar jikinsa na sake motsawa.

Saukowa daga kan gadon nasa yayi ahankali, batare kuma da ya kashe wayarba ya murda handle din kofar ya fita zuwa falo.

Fitowar tasa kuwa yayi dai-dai da nata fitowar itama, Wanda hakan yasa dukansu suka jefa idanunsu cikin na juna.

Da sauri tayi kasa da kanta, saboda Rayyern din bawai irin mutanen nanne da ake jure kallon cikin idanunsu ba musanman irin yanzu da ruwan jaraba ke yawo cikin kwayar idanun nasa.

“Gashi Mamy ce zaku gaisa.”

Ya fada yana me Mika mata wayar.

Jin abunda ya fada dinne kuma yasa ta amsar wayar da sauri, tare da karawa akan kunnenta.
Cikin sakin fuska da kuma girmamawa tace.

“Mamy na barka da dare.”

“Yauwa Jannart barkan ki dai, ya kike ya kuma kufayin jikin naki?”

Mamy ta tambayeta cike da kulawa.

“Alhmdlh Mamy naji sauki, ina Abba da Baba Maud’o da Ramadan?”

Tayi maganan tana me sakin Murmushin daya bayyana fararen hakwaranta.

Hakanne kuma yasa Rayyern din zuba mata ido, musamman innocent face dinta, da murmushin yayi wa kyau.
Ahankali kuma ya sauko da idanunsa zuwa kan, lafaffen Cikinta.

“Mutum sai karamin ciki, kaman ba’a cikin yakesa abinci ba.”

Ya fadi hakan acikin zuciyarsa.

Tare kuma da sauko da kallonsa. Zuwa kyawawan legs dinta da suka Dan bayyana.
Kasancewar rigar da tasanya din bata da tsawo sosai.

Jannart kuwa Sam bata ma kalleshi ba balle tasan da cewar ita din yake kallo, hasalima sauraran zancen Mamy kawai takeyi, inda take amsa mata da.
Tana mai nufar tsakiyar falon.
“Alhmdlh Jannart, Su Abbanku duk suna nan lafiya, haka ma Baba Maudo Dan shima yace yanemi wayanki Dan yi miki ya jiki amma wayar bata shiga.”

Dan murmushi Jannart din tayi, tare kuma da sunkuyar da kanta, cikin yanayinta na sanyi akoda yaushe tace.

“Ayyah ai tunjiya wayar take akashe shiyasa, kuma yau duk ban kunnata ba, amma idan na kunna zan kirasa insha Allah.”

“Masha Allah to badamuwa, Allah Ubangiji ya baku lafiya dukan ku, duk dama yanzun naga ciwon Rayyern din da d’an sauki, bai kuma sake tashi ba ko?.”

Jin anyi maganan ciwon nasa ne kuma, yasa Jannart din A hankali ta d’an d’ago kyawawan idanunta ta kalleshi.

Zaune yake akan daya daga cikin hannun kujerun falon, yayinda ya zubawa kyawawan yatsun kafanta idanu.

Fuskarsa ta d’an tsurawa ido, musamman lips dinsa da taga yana shining, hakanan kuma taji ta kasa d’auke idanunta akansa.

Dai-dai lokacin kuma ya d’ago idanunsa, Wanda hakan yasa idanun nasa fadawa acikin nata.

Da sauri tayi k’asa da kanta, tare da sake gyara zaman wayar akan kunnenta, cikin waskewa da kuma son janye idanunsa da takejin suna yawo akanta tace.

“Mamy ni kuwa Ina Riyyam nsra ne, almost 6 days bamuyi waya dashi ba.”

Daga can b’angaren murmushi Mamy tayi, kana cikin sakin fuska tace.

“Hmmm Riyyam nsra ne ko rigima, kullum bashi da zance saina sake dawowa Nigeria, ai muma munyi kewarsa sosai, amma yace zasu zo auren Ramadan dukansu harda Mammynsa.”

“Allah sarki Ramadan anata shiryen shiryen aure, lallai zamusha biki.”

Jannart din ta fada tana murmushi, tare da Dan matsawa gefe ta zauna.

“Gaskiya kam, tun da akasa bikin ai bashi da sukuni, kindai San shi dama.”

Yar dariya Jannart din tayi, Wanda har saida kyawawan fararen hakwaranta, da kuma dimples dinta suka bayyana.

Hakanne kuma yasa shi shagala da kallonta, yayinda yakejin wani abu na daban na tab’a wani sashi na zuciyarsa.

Kallo yakeyi mata mai dauke da ma’anoni na daban, kallo mai cike da tausayawa.

Tabbas har yanzu yana mamakin rayuwarta, domin kuwa ita yarinyace mai rauni, yarinyar da take rayuwa batare da tasan baya da kuma gabanta ba, yarinyar da ta kasance ta daban acikin mutane.
Haka kuma Yarinyar da SARKAKIYA ya cika gaba daya rayuwarta, sannan K’ADDARA ta cika rayuwarta da abubuwa daban-daban.
Uwa uba kuma ga MARAICI wanda ya lullube duk rayuwarta batare da ta sani ba ya yasan wannan abubuwan ne yasa zuciyarsa cika da tarin tausayinta mai kashe masa jiki!”.

Hakika ya gamsu cewa ita din mai tsananin rauni ce, irin raunin zuciyar dake karya zuciyar duk wani mai imani da tausayi.
Tayaya ta rayuwa har ta kawo I yanzu, a rayuwar da babu farinciki acikinta? Rayuwar da umarni kawai take karb’a ako da yaushe.
Tabbas Bata da zabi saidai abunda aka zaba mata ako da yaushe.
Rayuwarta ne amma sai yanda aka juyata haka take rayuwa tabbas ya kamata.

“ In sama mata farin ciki, in nuna mata tanada cikekken enci.
Babu tursasawa a kan komai Janna na ina son wani abu mai mahimmanci gareki amman nayi alƙawari bazan tursasa mikiba bazan miki doleba sai na tabbatar kin amince sani kin lamunce in zama sirrinki, nafi son ki soni so na haƙiƙa ba tursasawa ba kamar yadda Barrister Kabeer ya tsara kuma kike binsa a makanceba”.
Numfashi ya fesar a hankali kana yaci gaba da mgnar zuciya.
Waye Jannart? Mecece Jannart? Me ako boye a badinin baiwar Allah mai cike da rauni?”.

Allah ne kad’ai ya sani.
Yaji wata zuciyar tana bashi amsan tambayoyin da bai san dalilin yinsuba.

“Ga wayar.”
Ta fad’a a hankali, adai-dai lokacin kuma kenan da sukayi sallama da Mamy.

Idanunsa dake kan kyakkyawar fuskarta ya kawar, batare kuma daya karbi wayan ba, ya d’an Zame ya zauna acikin kujera.

“Kici abinci.”

Ya fad’a da wata irin muryarsa, wacce tayi sanyi sosai, kana kuma take fitar da daddad’an amo mai cike da kulawa, tausaya, lallaɓawa kana da riritawar da baisan na meneneba.

Yanayin yanda yayi maganan yana me jingina kansa da jikin kujerun, hade kuma da lumshe idanunsa ne, yasa Jannart din dan zuba masa ido.
Daga wuyansa zuwa fuskarsa.

Kwantattun gashin da suka kawata kasan hab’ansa ta zubawa ido, saboda yanda taga sunyi mishi kyau sosai.

Komai nasa mai kyaune, kuma gwanin burgewa, musamman black beard dinsa, da akullum shine abunda yafi daukar hankalinta akan fuskarsa, so take ace watarana ta tab’a taji yanda yake.

Ahankali ta kuma dawo da kallonta, ga jajayen lips dinsa, Wanda idanunta ke gane mata motsawansu ahankali.
Saboda yanayin yanda sukayi ja sosae ne kuma, yasa har wani shining sukeyi.
A hankali ta sauƙe numfashi tare da zama.

Kyawawan idanunta ta Dan zuba masa, bata ko k’yaftawa, yayinda har acikin jikinta takejin wani irin feeling, nason kusanta kanta da fuskarsa.

Numfashi yake shak’a ahankali, duk kuma da kasancewar idanunsa arufe suke amma hakan bai hanashi, sanin cewa kallonsa takeyi ba.

Ahankali Kuma cikin sanyin murya, mai dauke da kasala, irin wacce idan kajita zaka samu kanka acikin wata duniya cike da kulawa murya can ƙasa kamar cikin rad’a yace.

“Janna Nayi miki kyau be?”.

Da sauri ta janye idanun nata daga kansa, tare kuma dayin kasa da idanunta, saboda yanda sautin muryar tasa ta tayar mata da duk wani tsika na jikinta.

“Me kikeso? Ko akwai wani abinki ne a jikina, da kike nemansa da wad’anan mayatatyun idanun”.
Ya kuma faɗa a hankali cikin sigar tsokana da kuma sakon tattausan murmushi.
Da sauri ta fara jujjuya masa kai alamun a'a.
Shi kuwa Rayyern a hankali yace.
“To cinyeni zakiyi da wannan kallon naki?”
Da sauri ta tura baki cikin yanayin shogobarta dake kusan kashesa a zaune.

A hankali ya ƙara ɗan buɗe idanunsa kana cikin wata iriyar narkekkiyar murya mafi rauni yace.
“Janna kina sona!!!!”.
Still Ya fadi hakan yana me bude lumsassun idanunsa, Wanda sukayi tamkar sun tara ruwan wahaye acikinsu kana murya cike da rauni.

Kanta ta Dan girgiza ahankali, tare da kama y’an yatsun hannunta, ta soma murzawa cikin sanyin yanayi da kuma raunin daya zame mata sabo tace.

“Dama na gama wayanne, shine fa kawai...”

Ta kai karshen maganan tana me yunkurin sake miko masa wayar, saidai sam ayanzu bata bari sun kalli juna ba.

Shi kuwa Rayyern tamkar zaiyi kuka ya kuma yace.
“Janna kina sona?”.

Shiru tayi kamar bata jisaba,
Domin kalaman nasa sun zo mata a bazata.
Shi kuwa cikin tarin damuwar da bai san dalilntaba yace.
“Janna bakya sona ko?”.
Ya kare mgnar yana yunƙurowa, ganin tana mika masa wayanne yasa shi, Dan yunkurawa da niyar karban wayan, Wanda hakan yasa batare daya kula ba, ya sauke tafin hannunsa akan lallausan fatan hannunta.

A take kuwa duk sukaji wani irin abu ya tsarga musu, Wanda hakan yasa Jannart din tayi saurin sakar masa wayan.

Tare da d’an satan kallonsa, ganin cewar shidinma ita yake kallo ne idanun sa cike da hawaye, yasa ta karyar da wuyanta gefe.
Cikin sanyi tace.
“Ni kam ban tsane kaba Naan”.
Wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauƙe mai nauyi.
Kana a hankali ya zamo daga kan kujeran, tare da zama akan lallausan carpet din daya malale duk tsakiyan falon.

Ledan restaurant din dake gabansa ya jawo, tare da budewa ya ciro takeaways din dake ciki.

Ita kuwa cikin sauri ta jawo katon ɗin da Aunty Fauziyya ta aikomata, cike da son kauda yanayin da suke cikin tace.
“Laaa Naan kaya na ko”.
Ta ƙare mgnar tana gyara zamanta tare da kiciniyar farka gam ɗin.
Cikin yanayin mai cike da kulawa yace.
“Kawoshi nan in buɗe miki kada kiji ciwo”.
Da sauri ta miƙa masa tare da zama gabansa.
Key ɗin motarsa dake gefen wurin.
Yasa ya farko gam ɗin.
Kana ya buɗe katon ɗin.
Da sauri tasa hannunta ciki tare da fara fito da kayyakin cikin.
Da sauri ya karɓi wata gora data fito dashi cikin murɗe marfin yace.
“Ehyeh kinji dadinki mai Aunty Fauziyya ki gani fa Honey mai kyau ta aiko miki harda kuma riɗi a ciki.”
Ya faɗa tana jijjiga goran masifeffen raunin riɗi wanda shi a zatonsa.
Zumace.
Da sauri ta amshi gorar tare da cewa.
“Ni dai bani abuna na sanka da zaƙi yanzu zaka shanye min magani na”.
Yalwataccen murmushi mai sauti yayi tare dasa hannunsa ya kuma ɗaukan wani gora ya buɗe.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Gsky ban yardaba dani za'asha Janna kallli wannan fa shina zumace a ciki harda dabino, daɗi kan daɗi”.
Da sauri tace.
“Mu gani”.
Ta amshe kolbar kana ta medashi gefe.
Tsumin dabino ne mai matuƙar kyau.
Ɗaya gorar ya buɗe. Na tsumin goron Tula mai masifar yauƙi da kauri.
Yatsarsa ya ɗan sa ya dangolo.
Da sauri ya janye yatsarsan ganin yaukinsa.
“ Sweet heart me wannan?”.
Yayi mgnar da bai san ma da sunan ɗaya kirata ba.
Ita kuwa Jannart murmushin jin dadin da bata san dilinsa ba tayi tare da cewa.
“Naan duk magungunan Islamic ne, aka haɗa min kan ciwona suna da kyau sosai.
In ina shansu inajin sauƙin.”
Ta faɗi haka kamar yadda suka tsara da Aunty Fauziyya.
Kana ta kare mgnar tana ɓalle marafe gumbuna.
Ido ya zubawa gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, ita tayi kalan ja sosai.
Sai yake ganinta kamar Chocolate.
Sai dai abinda bai saniba sam bata da daɗin sha.
Gumbar madara ya kalla wacce itace kadai mai daɗin ci.
Sai kuma ya kalli koriyar gumar igiyar ruwa.
Juyowa yayi ya kalli garukan daka.
Garin mallaka shi korene.
Sai garin maɗi.
Da sauri ya jawo gumbar da ba'a bawa mai kishiya ganin duk saman gumbuna an zuba soyayyan inabi da kwakwa dasu dabino a zotonsa kayan daɗi ne.
Bai san suma da magani ake soyasu ba sauri ya ɗan gutsuri dunƙulen kwakumeti da inabi wanda ke haɗe da magani ya kai bakinsa.
Da sauri Jannart tace.
“Laaah Naan kaci, to Allah kuwa ni dai babu ruwan..”

Sai kuma tayi saurin katse mgnar tare da sakin dariya yadda taga ya yamutsa fuska tamkar zaiyi kuka.
Da sauri ya furzar dashi yana zaro harshensa waje, sabida yadda yaji magungunan na ratsashi.
Dariyar da take mushine ya sashi,
Ɗan kallonta don sosai tayi kyau.
Fizgota jikinsa yayi tare da cewa.
“Ok Janna mijinki kijeyiwa dariyar mugunta ko? To zo zo nan tare ki shanye abinki in bakya so Allah ya kamaki”.
Ya kare mgnar yana tallabe haɓarta duka biyu da tafukan nansa.
Ita kuwa Jannart har yanzu dariya takeyi.
Kanshi ya sunkuyar da sauri.
Ya manne lips ɗinshi akan nata.
Har lokacin kuma dariyar takeyi, dan tasan Rayyern da jarabebbiyar kwaɗayin kayan zaƙi.
Da sauri ta lumshe idanunta jin yadda ya zira mata tongue ɗinsa.
Yana mai ɗaura matashi kan nata, tare da sakin sassayan numfashi tare da murza yatsunsa kan gaɓar ta alamun ta tsotsa.

Haka nan taji tana mai bin umarnin sa.
Wani irin maraitaccen numfashin yaja mai tsawo.
Jin yadda ta kama harshensa tanayi mishi wani amintaccen kiss mai masifar sanyaya jiki da zuciya.
Wasu irin numfarfashin suka fara sauƙewa a tare a tare.
Ruggume tayi da hannunsa ɗaya kana ɗaya hannun kuma ya tallabe kanta.
Wani irin sassayan daɗi ne yake rufe masa zuciya da rayuwa, a wannan abu da Jannansa keyi masa.
Ita kuwa Jannart lumshe idanunta tayi tana maiyi mishi wani irin kiss da yake sata jin tamkar su tabbata a haka.
A ƙalla tsawon 3 minute, kafin a hankali ba zato ba tsammani yaji ta zare bakinta daga nasa.
“Heyyyyyyyyh Sweetheart”.
Ya saki sautin tare da jan sunan daya kirata da shi ɗin kana ya jingina bayansa da kujera, dan fitinenneyar kasala da yaji.
Cikin longoɓar da kai tare da tura baki murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Kalli fa ai bai gama fitaba”.
Ya kare mgnar yana ɗan zaro harshensa waje.
Idonta ta lumshe cikin yanayin kunya tace.
“Naan ya fita fa”.

Murmushi mai cike da jin dadi yayi kana yace.
“Allah ya miki al'barka ya jiƙan su Baba”.

Da sauri ta buɗe idanunta tare da cewa.
“Amin ya Allah ngd”.

Sai kuma ta gyara zamanta tare da sunkuyar da kai tana buɗe turaren Shu'umar humrar da turaren Al'ajabu a yan madaidatan kwalabe da kuma kulaccar sirri mai tarin jan hankali wanda AYSHA ALIYU GARKUWA ta haɗo mata su duka cikin 80k kacal da gumbuna da tsumi da komi, akwai kuma ƙanan sutin.
Cikin lumshe idanunta sabida daddaɗan kamshin data shaƙan tace.
“In kase kwaɗayin lasan wani abu ba, ruwana Naanu bazan goge maka ba”.

Wani irin sassayan numfashi yaja tare da zuƙan masifeffen ƙamshin da yaji yana kwantar masa da hankaki yar dariya mai sauti yayi tare da cewa.
“Sai kin goge kam”.
Ya ida mgnar yana mai ɗaukan kwalbar kulaccar sirrin yana sun-suna.
“Kai wannan turaren yayi min daɗi Janna”.
Ya faɗa da iya kar gaskiyar sa.
Murmushi tayi tare da cewa.
“In kana so to in number Aunty Aysha ALIYU Garkuwa. 09097853276, kayi mata mgn ta whatsApp duk ƙasar da kake zata tura in dai zaka iya kashe kudin zuwansu. Kana in a gida Nigeria ne kuwa duk State da mutun kayanta na zuwa”.
Ta ƙare mgnar tana ɗan shafa kullacar ta ɗan lakata a wuyanta da hannunta.
Murmushi yayi tare da bata kwalbar.
Da sauri ta amsa ganin yadda yaketa zuƙar ƙamahin.
Rufewa tayi kana ta tattaresu tasa a katon ɗin ta turesu gefe.

Murmushi yayi kana ya jawo ladan abincinsu.
Takeaway din farko ya bude tare da jefa spoon aciki.
“Zo kici abinci.”
Ya fada yana me Dan tura takeaway din gabanta.

Ahankali ta Dan kalleshi, tare kuma da kallon abincin, domin kamar yasan dama yunwa takeji, tun safe bataci abinci ba, duk da cewar tana da jure yunwa.

Ahankali ta d’an matsoshi tana gyara zmanta, tare da tankwashe k’afafunta, kana ta tsurawa abincin dake gaban nata idanu, saboda tasan bazata wani sake agabansa taci abincin sosai ba.
Domin lokuta da dama kwarjini yakeyi mata, wannan yana daya daga cikin dalilin dayasa bata iya jurewa kallon cikin idanunsa.

“Allah yasa dai yau kinsha maganinki?”.

Ya jefo mata tambayar, adai-dai lokacin da yake kokarin saka yankakken strawberry abakinsa, tare kuma da watsa mata idanunsa, da suke matukar di mautata.

Jannart kuwa tambayar da yayi mata dinne yasa ta d’agowa ta kalleshi, yayinda
D’agowan da tayi, dinne kuma yasa idanunsu sarkewa acikin na juna, Wanda hakan yasa da sauri ta lumshe nata idanun, sannan adan sanyaye ta girgiza kanta.

“Ummm Ummm ni bansha ba, bayan ma har yanzu wajen alluran zafi yake min.”

ta kare fadan hakan tana me cije lips dinta, tare da rumtse idanunta alaman da gaske tana jin pain.

For the first time kenan, daya kure mata kallon son acikin yan sakanni.
Wanda kuma abubuwan daya hango atattare da ita suna da yawa.

Numfashinsa ya fesar ahankali tare, kuma da tauna strawberry din dake bakinsa.

“Yah salam.”

Ya fad’i hakan acikin zuciarsa wacce


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login