Showing 186001 words to 189000 words out of 350584 words

Chapter 63 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

wayar ku gaisa, bansan Meyasa Rayyern yake haka ba, da gasken gaske na fahimci cewar, zama da Mace ne bazai iya ba, saboda baisa abun acikin zuciyarsa ba shiyasa, amma babu komai na zuba masa ido, awannan karon zanga iya gudun ruwansa a gari irin Mascow mai yanayi na musamman da kuma mace kamar Jannart da kuma keɓantaccen wuri zan bishi da ido inga iyakar yaudar da zuciyarsa ke masa na cewa zai iya rayuwa ba mace.”

Ajiyar zuciya Mamy dake gefe ta sauk’e, cikin nazartar maganganun mijin nata kuma murmushi tayi tare da cewa.

“Tabbas nima dai sau dayawa ina mamakin yanda yake cewa baya gida, amma da fari na yarda da maganganunsa, saboda kasan Rayyern bai cikayin k’arya ba, Dan banace baya k’arya ba kwata kwata arayuwarsa, saboda babu wani d’an Adam d’in da baya k’arya a dai wannan ƙarni namu, saidai na wani yafi na wani amman dan nasan karya ba dabiarsa bace, amma gaskiya nidai kam jikina yayi sanyi, kada fa Rayyern yaje ya ajiye y’ar mutane ne, kawai ya fita harkarta.”

K’wafa Abban yayi tare da d’aukan kofin coffee din nasa, cikin yarda da hukuncin da zuciyarsa ke yanke masa yace.

“Hmmmm zanyi magananinsa kuwa Idan har hakan ta kasance, saboda matarsa ce ko da ace bayasonta kuwa akwai, hakkinta da ya rataya awuyansa, amma ki barni dashi kawai.”

Abban ya k’are maganan yana me Kai kofin bakinsa.

Mamy kuwa shiru tayi, saboda tasan idan abun da tayi yakini gaskiya ne, to kuwa Rayyern bai kyauta ba.

Ganin da tayi kuma Abban ya ci gaba da shan coffee dinne, yasa ta tashi ta wuce kitchine Dan k’arasa had’a abincin dare, domin bata son Ramadan ya dawo ya samu bata gama had’a abincin ba, kasancewar yanzu duk hankalinsa, ya koma kan hospital dinsu, tun safe Idan ya fita sai bayan magrib yake dawowa, hatta yau Weekend ma bai zauna ba.
*Moscow.*

Gaba d’aya cikin d’akin da suke gwaji din, ya d’auki shiru babu abunda kakeji kuwa, sai k’aran na’urori da kuma sanyin, AC dake tashi duk da sanyin dake garin kuwa, amma yanayin aikin da sukeyi din yana tsananin buk’atar sanyi.

Yanayin test din nasu kuwa ya kasu kashi biyu ne, domin kanana daga cikin Doctors din suna gwada aikinne, akan robot ma’ana wasu halittun da aka kirkira ma tsakaita kuwa, akan halintun kananan dabbobi sukeyi nasu gwajin.

Yayinda manya manyan Doctors din, da suka amsa sunansu masu experience ke gwada, aikin akan mutane majinyata way’anda, suke fama da lalurar kidney.

Acikinsu kuwa harda Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, wanda ya bada gaba d’aya attension d’insa, akan wanda yakeyiwa aikin, agefensa kuwa Dr. Sulaiman ne da kuma Dr. Nick Michel, wanda shima Babban Dr. ne ak’asar France.

Saidai duk da k’warewansa idanu ya zubawa, Rayyern alokacin da yake aikin dashen k‘odan.

Saboda su iya nasu mik’o masa kayan aiki ne.

Adai-dai lokacin da Rayyern ya kammala, dasa k’odan bayan ya d’inke cikin mutumin dake kwance, ne ya sauk’e wani irin nannauyar Ajiyar zuciya, tare kuma dasa hannu ya dafe saitin zuciyarsa.

“Yah Rabbi”

Ya k’ira sunan Allah abayyane,
Cike da gamsuwa hadi da samun k’arfin guiwa, da yarda akan cewar Allah’n ne maiyi, shine kuma mai bada sa’a akoda yaushe shike rayawa ya kuma kashe.

Kashe wutan theater room din da yake ciki yayi, da kansa kuma ya turo gadon da mutumin ke kwance har zuwa wani extra room, wanda acikinsa ne za’a jere way’anda akayiwa surgeryn, saboda a tabbatar da lafiyarsu.


Kusan Atare Doctors din suka kammala aikin nasu.

Yayinda zuciyoyinsu ke cike da alhinin, yanda way’anda sukayiwa aikin zasu tashi.

Dukansu kuwa Fatansu shine, patients din su tashi lafiya batare da wata sabuwar matsala ba.

Almost 1hour suna zaune cikin zullumi, saboda har yanzu babu d’aya daga cikin majinyatan da ya farka.

Ak’a’idan aikin nasu kuwa, wanda patient d’insa ya fara farkawa batare kuma da wata matsala ba shine yazo first.

Cikin sa’a kuwa Patient din Dr. Rayyern Muhammad Mainasara ne ya fara bud’e idanunsa.
Inda kuma ya tashi garau batare da juyewan, brain ko haddasuwan wata matsalan ba, Dan Koda ya bud’e idanunsa acikin hayyacinsa yake sai yan kananun surutan da suke dole, bayan ƙaƙkanin lokaci kuma ya zama dai-dai.

Wani irin farinciki na ya cika zuciyar Rayyern, lokaci d’aya kuma ya shiga godewa Allah, saboda yasan bayin kansa bane, kowacce Nasararsa daga Allah ne.

Gaba daya Doctors din sun Taya Rayyern farinciki, tare kuma da mamakin k’warewarsa, musamman Envigelators da suka kasance consultant's ne, saboda basu tab’a tunanin wani
Daga cikin Doctors din zai k’ware da sauri akan abun har haka ba, musamman ma shi da yake d’an Nigeria, basu tab’a tunanin shi zaiyyi wining ba.

Domin faruwar hakan alamace dake, nuna musu babban nasararsa, shine kuma zai karb’i award na ban girma, tare kuma da certificate din da zai nunawa duniya, cewar shi babban likita ne, amintacce kuma yardajje akowacce k’asa.

Tabbas Rayyern yaji dadin hakan azuciyarsa, domin ko babu komai zai kankaro mutumcin k’asar sa.

Alhamdulillah Sauran
Patients dinma, da akayiwa operations din sun bud’e idanunsu, cikin sa’a kuwa kowanne da hayyacinsa ya dawo hakama nasu Dr Sadiq da sukayi gwajin su kan ƙananun dabbobi suma na Dr Sadiq ya tashi lfy bisa alamu gaba zai taka matakin da Rayyern ya taka a yau.

Sosai Doctors din sukayi kokari, harma way’anda suka gwada nasu akan mutum mutumi.


3:00 pm Dai-dai suka kammala, duk wani abunda zasuyi, Ganin garin nata k’ara gumewa da snow ne kuma, yasa duk suka watse, kaitsaye Rayyern ya nufo gida.

Saidai kuma kafun ya k’araso saida ya tsaya, amasallaci yayi Sallan La’asar, kana ya biya Halal restaurant yayi musu takeaway, na Arab dishes kafun ya nufo gidan kaitsaye.


Gaba d’aya yau din jin zuciyarsa yake wasai, badon komai ba kuwa saidan wannan nasarar daya samu.

Shigowa cikin falon yayi, tare da neman waje ya zauna, bayan ya zare jacket din dake jikinsa, kasancewar duk ta b’aci da dusan k’ank’ara dake dan sauka.

Kallon d’an table din dake cikin falon yayi, rashin Ganin ledodin daya bari awajen ne kuma, yasa shi gane cewar Jannart din ta fito, domin ta hakanne kawai yake gane fitowarta, ko rashin fitowarta, kasancewar Idan ta fito takan kwashe ledodin takai kitchine.

Ledan daya shigo dashi din, ya d’auko tare da d’aukan chicken kebab ya soma ci, bai wani ci sosai ba ya ajiye, sai kuma pizza da drinks din daya d’ansha.

Bayan ya kammala ne kuma kaitsaye ya wuce bedroom d’insa, saboda yana so ya d’an watsa ruwa.

Koda ya shiga bedroom din kayan jikinsa ya rage, tare da fad’awa bedroom ya sakarwa kansa ruwa.

Bayan ya fito awankanne kuma ya shirya, kansa cikin wasu Sabin riga da wando, tare da d’aura wata jibgegiyar rigar sanyi akai.

Still kuma car key d’insa ya d’auka, direct ya fice daga Cikin gidan.

Daga gidannasa kuwa kaitsaye wani babban shagon saida kaya ya nufa.
Mall Yevropeyskiy ya wuce kai tsaye dan yafi kusa da inda yake.
kayan sawa da kuma sweaters Chocolate's
masu yawan gaske ya saya.

Har ya juya zai tafi ne kuma, idanunsa suka sauk’a akan wasu, womenswears masu azabar kyau, wanda dukansu kaya ne da zasu tare sanyi.
Domin irin jibga jingan rigunan nanne da y’an k’asar suke sawa.

K’arasawa wajen clothes din yayi, tare kuma dasa hannunsa ya zaro wasu manyan jacket masu kyau, guda biyu ya ciro jacket din, sai kuma wasu wanduna masu kyau, way’anda ya ibosu sama da guda biyar haka nan yake kallonsu yana murmushin, a hankali ya lumshe idanunsa da alamun yana so tuno wani abune.

Zuba su yayi acikin basket din dake hannunsa, kaitsaye kuma ya nufi wajen biyan kudi.

Koda akayi masa bill bai damu da yawan kudin ba, haka ya mik’a musu atm card d’insa suka cire.

Daga mall din kuwa, kaitsaye wajen sport ya nufa, saboda yana son dan motsa kafafunsa.

Acan gida kuwa Jannart tunda ta k’ule d’aki bata sake fitowa ba, ko da kwanciyar ma ya isheta bacci ne ya d’auketa, ba ita ta tashi ba kuwa sai dab Sallan Magriba, bayan tayi Sallah ne kuma, ta d’auko wani book dinta, ta soma karantawa.

Tana nan azaune har aka kira Sallah’n Isha, tana idar da Sallan kuwa ta haye kan gado, saboda sanyin garin ya sake yawaita.


Rayyern kuwa tunda ya fita bai dawo ba sai yanzun.

Ahankali ya bud’e murfin motar ya fito, tare da Kwaso manya manyan ledodin kayan daya saya, kaitsaye ya nufi cikin gidan.

Yana shiga cikin falon kuwa, idanunsa suka sauk’a akan, ledan abincin daya sayo d’azun, babu alaman an tab’asa.

Kauda kansa gefe yayi, for the first time kuma kenan daya d’aga, idanunsa ya kalli kofar dakin nata haka nan yaji kamar ba dadi.

Bakinsa ya d’an tab’e kana kaitsaye ya wuce dakinsa.

Yana shiga ya dire ledodin dake hannunsa, tare da wucewa toilet yayi wanka, bayan ya fito ne kuma ya shirya kansa, cikin wasu kayan bacci masu nauyi.

Hayewa saman gadonsa yayi, tare da kunna laptop d’insa, ya soma receiving sakonnin da ake turo masa, kaitsaye sakon maganer’n Companynsa ya fara dubawa, inda yake shaida masa yanda abubuwan companyn suke tafiya, da kuma yanda manyan y’an kasuwa, ke zuba hannun jari acikin companyn, komai dai yana tafiya normal.

Domin Koda ya duba details na companyn, ya ga abun na tafiya akan dai-dai.

Iya sakon da yasan suna da muhimmanci yayi replying, sauran sak’onnin kuwa ko duba su, baiyi ba ya kashe laptop din nasa.

Idanunsa ya d’an lumshe, dai-dai lokacin kuwa wayarsa dake gefe ta soma k’ara.

Ganin sunan Ramadan na yawo akan screen, din wayar ne kuma ya sashi d’agawa, tare da kara wayar akan kunnensa.

“Good Evening Hamma Rayyern, I hope you’re okay.”

Daga can b’angaren Ramadan din ya tambaya.

Idanunsa ya d’an lumshe tare kuma da gyara kwanciyarsa, Cikin kulawa yace.

“I’m Okay Ramadan, you? Ina Mamy da Abba?”

Murmushi Ramadan yayi tare da cewa.

“Same to you Hamma, Mamy da Abba kuma suna lafiya, Ina Aunty Jannart?”

Idanunsa ya d’an lumshe, kana cikin yin kasa da murya yace.

“Tayi bacci.”

Kai Ramadan ya jinjina, Jin kamar Hamman nasa agajiye yake ne kuma, yasa shi danne dariyarsa, domin shi wani tunani na daban zuciyarsa ta basa.

“Okay Hamma gud night, but please ka gaishemin da Aunty Jannart Idan ta tashi.”

“To.”
Rayyern din ya fad’a agajarce, domin bayason Ramadan ya sake yi masa wata tambayar, daga haka sukayi sallama.

Ahankali ya zare wayar daga kan kunnensa, tare da mik’ewa tsaye, ya k’arasa gaban fridge din dake cikin dakin.
Koda ya bud’e fridge din dan siririn tsaki yaja, saboda ganin da yayi babu ruwa aciki.
Gashi kuma yana buk’atar ruwa, saboda tunowa da yayi baisha maganinsa ba.

Kaitsaye ya nufi kofar fita daga cikin d’akin.

Dai-dai lokacin kuwa Jannart, da fitowarta daga, d’akinta kenan ta nufi kitchine, saboda Itama ruwan take da buk’ata.

Saidai kuma ganin duhu da tayi afalonne yasa ta, d’an tsayawa tare da soma laluben inda makunnin wutan falon yake.

Dai-dai lokacin kuwa Rayyern din ya fito, ko kad’an kuwa duhun bai tsorata shi ba, kasancewar yasan kan gidan shiyasa, baya wani buk’atar haske kaitsaye, ya nufi kitchine din.

Dai-dai ya kawo tsakiyar falon ne kuma, itama Jannart din ta iso wajen, wanda Jin motsin mutum da tayi, ya saka duk ta tsorita, juyowan da zatayi ne kuma sukayi karo, inda take kafad’ansa ya bugi hab’arta.

Wani irin k’ara ta saka tare da saurin, sanya hannayenta ta kama hab’ar nata.

Rayyern kuwa d’an ware idanunsa yayi, saboda bai tab’a kawowa aransa cewar tana cikin falon ba.
Jin yanda tayi k’ara ne kuma yasa shi, matsawa cikin sauri ya kunna, wani dan blue din hasken wuta dake cikin falon.

Idanunsa ya sauk’e akanta, wanda har yanzu tana rik’e da hab’ar nata, ta kuma rumtse Idanunta, da alama ya bugeta sosai.

Ahankali ya soma k’arewa shigar dake jikinta kallo, wata doguwar riga ce mai kauri, sai kuma hulan sanyin dake kanta, Yayinda dogon gashin kanta ya sauk’o kan kafad’unta.

Duk da cewar hasken daya kunna din, bayi da karfi sosai, amma hakan bai hanashi kallon yanda fuskarta, tayi fayau ba, ga kuma shatin nipples dinta da suka bayyana, kasancewar gaban rigar nata akwai tsagu ne, kuma yasa yake iya ganin tsakiyan kirjinta, ma’ana tsakiyan breast dinta.

Idanunsa ya mayar kan fuskarta, tare da soma takowa ahankali ya shiga matsowa inda take.

Dai-dai yazo kusa da ita ne kuma ya tsaya cak, kyawawan hannayenta ya kalla, akaron farko a iya tsawon rayuwarsu, ya sake matsowa kusa da ita sosai, har hakan ya bawa hucin nufashinsa dama sauk’a akan kirjinta.

“Meye?”

Ya fad’a da wata irin husky voice, din dake bayyana baccin da yakeji.

Jannart kuwa dake tsaye, Jin muryarsa da tayi akusa da ita ne, yasa ta saurin bud’e Idanunta da suka cika da k’walla, ta sauk’esu akansa.

Shek’in ruwan hawayen da idanun nata keyi ne, ya sashi jefa nasa idanun acikin nata, still cikin wata irin muryar daya kusan sata rud’ewa yace.

“Meye? Kinada damuwa ne? Me kikeso, uhummmm tell meeee.”
Yaja ƙarshen mgnar cikin kasalalliyar murya a tausashe
Hawayen dake cikin idanun nata ne suka gangaro, lokaci d’aya kuma tayi k’asa da kanta, tare da had’e yatsun hannunta waje d’aya.

Shi kuwa Rayyern a hankali ya m...!






By
*GARKUWAR FULANI*
Motsa kafafunshi ya danyi baya kaɗan domin ji da yayi bugun zuciyarsa na tsananta.

“Ruwa zan sha.”
Ta fad’a cikin wata muryar shagwab’a.

Idanunsa ya d’an lumshe saboda wani fitinannen, kamshinta daya bugi hancinsa.

D’an matsawa gefe yayi, batare kuma daya ce mata komai ba, ya rab’a ta gefenta, wanda har hakan yasa jikinsa d’an gogan nata jikin, kaitsaye kitchine din ya wuce.

Yana shiga kuwa ya bud’e murfin fridge, goran ruwa guda biyu ya d’auko, kana ya dawo cikin falon, Tana nan tsaye ayanda ya barta, saidai ta kuma rik’e hab’arta.

K’arasowa wajen nata yayi, tare da mik’o mata goran ruwan, cikin silent voice yace.

“Take it, then go to sleep now, ko na jimiki ciwo ne?”

Yanayin yanda yayi maganan nasa ne cikin tauyawa da tausasawa, yasa duk taji tsikar jikinta na mimmik’ewa, Ahankali ta girgiza masa Kai, kana cikin sanyin murya tace.

“Zafi nakeji.”

Ta k’are maganar tana me nuna masa gefen lips dinta, da ya d’anyi ja.

Idanunsa ya d’an tsurawa Lips din nata, saboda yanda yaga Suna shek’i, d’an kawar da idanun nasa kuma yayi Ahankali, kana cikin sanyi yace.

“Babu ciwo awajen, zuwa anjima zai daina zafi sannu ko sorry ban san dake a wurin bane.”

Yayi maganan yana me Kallon wuyanta.

Ita kuwa Jannart jin abunda ya fad’ane ya sata karb’an bottle water’n, da yake mik’o mata tare da juyawa, cikin sanyi ta nufi bedroom dinta.

Da idanunsa ya bita, har saida ya ga ta shiga cikin bedroom dinta, kafun ya juya shima ya nufi nasa bedroom din.

Yana shiga ya sawa kofar key, maganinsa ya b’alla yasha, kana ya koma ya kwanta.

Koda ya lumshe idanunsa still k’amshin turaren nata yakeji, acikin hancinsa, dan gyara kwanciyarsa yayi, batare kuma daya baya wani tunani daman shigowa, cikin kwakwalwarsa ba bacci ya d’aukesa.

Haka itama Jannart tana shan ruwan, kwanciya tayi cikin mintuna kad’an kuwa bacci ya dauketa.

Acan b’angaren Ramadan kuwa Koda suka gama waya, da Hamman nasa Whatsapp dinsa ya shiga, Ganin Riyyam da yayi a online ne, kuma yasa suka fara chat, ananne kuma ya turawa Riyyam din numbern Rayyern, Wacce yake amfani da ita anan Mascow din.


Washegari.

Yau ya kama Sunday, tunda Rayyern ya bar gidan kuwa bai dawo ba, domin can cikin garin ya shiga, Saboda akwai wasu Frnd’s d’insa da sukayi karatu tare, yaje sun danyi wani taro.

Jannart kuwa yauma ad’aki ta wuni, saboda duk kwana biyun da ciwon Mara take wuni shiyasa fitan ma, bai wani dameta ba duda bata jin hakan don al'adarta zata zo tayi mmkin hakan daya fara mata yanzu.

***

After five days ago.

Ahaka sukeyin rayuwarsu ta yau da kullum, komai na tafiyawa Rayyern yanda yake so, saidai zuwa yanzu gaba daya abubuwa sunyi masa yawa.

Haka ma Ab’angaren Jannart rayuwarta take ita d’aya, tun daga daren ranar kuwa bata sake saka Rayyern din a Idanunta ba.
Iyaka ya ajiye mata abinci tazo taci.
Da hakanne kuma kowannensu yake sanin, lafiyar d’an uwansa ta haka suke sanin zaman juna.

Acan gida Nigeria kuwa, abubuwa duk suna tafiya yanda ya kamata, musamman a company babu wani mishkilan da ake samu dan Rayyern yana aikinsa da kyau ta yanar gizo-gizo kana ga amintattun ma'aikata, haka asibitin ma Ramadan yana iyaka kokarinsa sosai.

Ko yanzu dawowansu daga masallaci kenan, shida Abban nasa.
Bayan sun shigo cikin falon ne kuma, Ramadan din ya nufi sama.

“Ramadan.”
Abba ya k’ira sunansa.

Jin kiran Abban ne kuma yasa Ramadan juyowa, tare da dawowa ya zauna acikin falon.

Kallonsa Abban yayi kana Cikin sakin fuska yace.

“Karna manta ban Gaya maka ba, dazu iyayen Rayhanna sun kirani, sun kuma shaidamin cewar, sun baka auren yarsu, kamar yanda muka buk’ata, sannan kuma sun bamu lokaci, amma Idan son samu ne ayi bikin kafun watan Ramadan yazo.”

Idanu Ramadan ya dago ya kalli Abban nasa, cikin tsananin jin dadi da farinciki yace.

“Alhamdulillah Allah Nagode ma.”

Yayi maganar cikin manta cewar, agaban Mamy da kuma Abban yake.

Mamy dake gefe kuwa murmushi tayi, saboda ta sani dama Ramadan din yana son aure.

Ramadan kuwa cikin zumudi ya kalli Abban nasa, tare da cewa.

“To Abba yanzu yaushe za’akai kudin sa rana da kayan lefe?”

Kallonsa Abban yayi, baice komai ba saidai aransa yana mamakin, yanda Ramadan din ke tsananin son Aure.

Ramadan kuwa Ganin irin Kallon da, Abban keyi masa ne ya sashi mikewa da sauri, cikin kunya ya haura sama.

Ganin hakanne kuma yasa Abba yin dariya, kana ya mik’e ya wuce part d’insa, inda yabar Mamyn zaune itama tana dariya.

Tana nan zaune kuwa Ramadan din ya sauko, cikin shirinsa tsab, inda yayi kyau acikin riga da wandon jumpern dake jikinsa.

Kallonsa Mamy tayi, gaba daya farincikinsa abayyane yake, fuskarta dauke da murmushi tace.

“To yau kuma sai ina?”

Murmushi yayi, tare da Dan matsowa cikin yin kasa da murya yace.

“Ayyah Mamy am zanje gidansu Swe....” saurin gimtse bakinsa yayi, saboda ya kusa yin b’aran b’arama.

Mamy kuwa dariya tayi saboda Sarai, ta fahimci abunda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login