Showing 45001 words to 48000 words out of 350584 words

Chapter 16 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: šŸ“šŸ‡šŸ‡šŸ‡šŸ‡šŸ‡šŸ‡šŸ‡šŸ‡šŸ‡šŸ‡

*TUBALI*


PAGE 11
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

šŸ‡šŸ‡šŸ‡šŸ‡šŸ‡šŸ‡šŸ‡šŸ‡šŸ‡šŸ‡šŸ‡

*FREE PAGE ne*

_Littafin TUBALI na kuɗine hamzarta ki biya ki karanta cikin salama special Group 1k ne karamin group 500 kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, ko kuma ki sayi katin MTN ki copy number's ɗin katin ki turo min_

*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*

*NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ʙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.

Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones šŸ˜) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🄰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.


Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki Hajia yan mata. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da ni'imantaccen kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.

Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

šŸ¤šŸ»šŸ„°šŸ˜˜ Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA)*


Sautin takun takalminsa dasu Ramadan sukaji ne kuma yasa su maida hankali zuwa gareshi.

Idanunsu gaba daya suka zuba mishi, tare da had’a baki gaba dayansu suka ce.

ā€œMasha Allah! Tsarki ya tabbata ga sarkin daya halicce mu ya kuma halicci Hamman Rayyern dinmu.ā€

ā€œInnalillahi kai Hamma Rayyern kayi kyau sosai, wallahi kamar daga Saudiya kazo.ā€

Cewar Riyyam-nsra daya hangame baki da hanci yana Kallon Rayyern d’in.

Shikuwa Rayyern karasa saukowa cikin falon, yayi ganin Abba da Mamy zaune ne kuma yasashi, d’an rusunawa ahankali yace.

ā€œMammy a bani Bootle water mai sanyi.ā€

Mamy da ita kanta ta yaba da tsananin kyawun da al'kyabban jikin nasa tayi masa ne ta saki murmushi, tare da fadin.

ā€œMasha Allah Rayyern kayi kyau, wannan suturar tayi maka kyau, Lallai kuwa ashe Rayyern din nawa ya kerewa sa’a.ā€

Ɗan guntun Murmushin yayi, Cikin kuma alaman jin kunyar yabonsa da Mamyn nasa tayi yace.

ā€œNagode sosae Mamyna.ā€

Abba daya kafe Rayyern din da ido kuwa baya ko k’yaftawa, fuskarsa cike da mamaki yace.

ā€œRayyern wannan shigar fa yaushe ka fara ta? sannan a ina ka samo alkyabba mai tsananin kyau haka?ā€

D’an sunkuyar da kansa k’asa yayi, tare da kama y’an yatsun hannunsa ya soma murzawa.
Sam arayuwarsa shi bai iya k’arya ba, impact ma arayuwarsa babu abunda yafi tsana kamar k’arya, bayayin k’arya bakuma yaso ayi masa.

Duk da kuwa yasan Abban nasu bazai so abunba so gskyar da zai fada ba, amma ya zama dole ya gaya masa gaskiya, saboda karya ba d’abi’arsa bace.

ā€œKayi hakuri Abba Malam Mai-nasara ne ya bani kyautan Alkyabbu guda bakwai.ā€

Idanu Abba ya kankance cikin kuma nuna rashin jin dadin hakan ya kawar da kansa gefe.

Ganin hakanne kuma yasa Rayyern d’in, ya d’an rank’wafar da kansa.

Kana cikin sigar ban baki yace.

ā€œKayi hakuri Abba, idan bakason shigartawa sainaje na cire.ā€

Ajiyar zuciya Abban ya sauk’e kana ahankali yace.

ā€œA’a ni Bance Banason shigarka ba, kayi kyau Tabbas kuma shigar alkyabba shigace da take da matuk’ar mutumci, gashi kuma ta bayyana tsananin haiba da kwarjininka, saidai amma ka kiyaye nan gaba bafa na son wata alaʙa a tsakaninku.ā€

Kai Rayyern din ya jinjina kana cikin girmama zancen Abban nasu yace.

ā€œNagode Abba kuma Insha Allah zan kiyaye.ā€

ā€œShikenan.ā€ Abban ya fad’a atakaice.

Riyyam-nsra kuwa cikin kasa kosawa da Kallon yanda Hamadan nasu yayi kyau yace.

ā€œPlease Hamma Rayyern Ina zakaje.ā€

ā€œPolo.ā€
Ya bawa Riyyam din amsa a taʙaice kuma dai-dai lokacin da yake kokarin fita daga falon.

Da sauri Riyyam din ya tashi yabi bayansa, yana me fad’in.

ā€œTo Hamma Rayyern tsaya muyi video dan Allah.ā€

Ramadan dake zaune ma mik’ewa tsaye yayi yabi bayansu.

A compound din gidan suka tsaya, inda Riyyam sarkin tiktok ya saita wayarsa ya soma yi musu video dukansu uku.
Harda sa musu wata y’ar wak’a, shidai Rayyern Kallon Yaron kawai yakeyi, domin a wuni biyu kawai da sukayi da yaron, ya fahimci wani abu, da kuma irin d’abi’a da yaron yayi shura akai.

Saidai kuma baisan Meyasa ba yakejin yaron acikin zuciyarsa hakan yasa yake kasa yakiceshi.

Gama k’arasowarsu compound din gidan kuwa, yayi dai-dai da fitowan Baba Maud’o daga cikin d’an madaidacin Part ɗinsa dake gefen gate.

Yana fitowa dinne kuma ya sauk’e idanunsa akan Rayyern, dake sanye cikin al-kyabba.

Wani irin tsayuwa Baba Maud’on yaji zuciyarsa tayi, take kuma wasu irin abubuwa suka shiga dawowa cikin tunaninsa.
Saidai kuma Ina ayanzu kwakwalwarsa bata da wani buk’atar amsar kowani irin sak’o, wannan dalilin yasa zuciyarsa ke cigaba da bugawa da harbawa a hankali.

D’an matsowa kusa dasu Baba Maud’on yayi, tare kuma da sauk’e idanunsa akan Riyyam wanda keta faman bin wak’ar Justin Bieber me suna (Peaches) dake tashi awayarsa.

Idanu Baba Maud’o ya tsurawa yaron baya ko k’iftawa, Yayinda zuciyarsa ke cike da zallan mamakin, kamannin Rayyern dake kwance akan fuskar yaron.

ā€œBaba Maud’o barka da yammaci.ā€

Cewar Rayyern.

Wanda maganan nasa ne kuma yasa Baba Maud’o dawowa cikin tunaninsa.

Murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa, duk da kuwa cewar rabin fuskartasa arufe take, amma hakan bai hana Rayyern din gane cewar Baba Maud’on murmushi yayi ba.

ā€œYauwa Barka dai Rayyern, yau kuma inazaka je haka naga kayi shigar da ta bayyana kyau da cikar haibarka.ā€

Murmushi Rayyern din yayi, tare da dan matsowa kusa da Baba Maud’on kana yace.

ā€œWurin wasan polo zanje Baba Maud’o".

Kai ya jinjina alamun gamsuwa.
"Shin ko akwai wasu abubuwan buk’ata naka da suka k’are, idan nazo dawowa saina sayo maka.ā€
Rayyern ya tambayeshi cikin mutunta ma'aikatan gidan nasu.
Again Murmushi Baba Maud’o yayi, cikin kuma Jin dadin kulawan da su Rayyern din sukeyi dashi yace.

ā€œA’a Alhamdulillah ayanzu kam bana buk’atar komai, saidai nace kayi kyau sosai cikin wannan shigar, amma baka daura hiramin naka dai-dai ba, Bari na gyarama irin yanda samarin makka suke saka nasu.ā€

Murmushi Rayyern din yayi, kana ya matso Baba Maud’o d’in ya gyara masa sakun hiramin.

Riyyam-nsra kuwa da d’an mamaki ya kalli Hamma Rayyern dinnasu, tare da cewa.

ā€œHamma Rayyern waye wannan mutumin, naga jiya da nazo banganshi ba.ā€

ā€œSunansa Baba Maud’o.ā€

Ramadam ya bashi amsa.

Saurin jinjina Kai Riyyam yayi, kana ahankali ya matso kusa da Baba Maud’o din.

Fuskarsa dauke da murmushi yace.

ā€œRawanin da kasa akanka zuwa fuskarka yayi kyau sosai Baba Maud’o, Dan Allah Hamma Rayyern kuzo mu d’auki hoton selfie tare dashi, saboda Idan na koma Ethiopia zan nunawa Mammyna, na kuma bata labarin yanda wasu daga cikin yan Nigeria sukeyin shigarsu.ā€

Ya fad’i hakan saboda baisan cewa Baba Maud’o’n shigar buzayen Niger šŸ‡³šŸ‡Ŗ yayi ba.

Kamar yanda ya buk’ata kuwa matsowa Rayyern da Ramadan sukayi, inda suka saka Baba Maud’o da Riyyam din atsakiya.

Hakanne kuwa yasa Baba Maud’o da Riyyam din ke iya jiyo sautin bugun zuciyar kowannensu, saboda yanayin yanda sukayi kusan ci sosai da juna, domin Riyyam dan sarkin son jiki, har rungume Baba Maud’on yayi ajikinsa.


Yayinda Ramadan ya karb’i wayar Riyyam d’in, yayi musu hoton selfie har kala biyu.

Bayan ya mikawa Riyyam din wayarsa ne kuma,
Rayyern ya juya ya shiga motarsa, driver’nsa yaja suka fice daga cikin gidan.

Ramadan da Riyyam kuwa zama sukayi dab’as Akan wani dan dogon Bencin da Baba Maud’o ke zama, haka kuwa suka sa Baba Maud’on agaba sunata hira, musamman Riyyam daya bud’e baki ya dinga shararawa Baba Maud’on labarai kala-kala, wanda duk rabinsu na abun dariya ne.


*Arewa 24 TV*

Jannart ne da Salman ke tafe acikin babban corridor din, da zai sadasu da compound din gidan tv'n nasu.

Anutse Jannart take takunta, Yayinda time to time take Kallon fuskar wayarta dake rike ahannunta.

Salman dake biye da ita kuwa, idan hankalinsa yakai dubu to duk akanta yake.

Baisan meyasaba hardai idan Jannart tana waje, baya tab’a iya dauke kansa daga gareta, koda kuwa yaya baya iya gajiya da Kallon tafiyarta mai kama data hawainiya.

Yayi Imani azuciyarsa cewa Jannart macece ta gasken gaske, ko acikin mata irinta basu da yawa.

Isowarsu jikin motarsa ne kuma yasa Jannart fakon idanun guard dinta ta shige cikin motar, kana cikin sauri tace.

ā€œPlease Salman kayi sauri mubar nan, Domin idan wayannan kattin suka ganni dakai ina mai tabbatar maka cewar akwai matsala.ā€

ā€œNikuwa nasan da cewar akwai matsala ai Jannart, abu mai sauki ne ma su samin bindiga akaina su harbeni, tsoron da ake baki agidanku ko Gwamna iyakaci.ā€

Salman din ya fada adaidai lokacin da yake ta da motar suka bar wajen.

Suna hawa titi kuwa Jannart ta sauk’e ajiyar zuciya tare da fad’in.

ā€œAllah Yasa dai mudace mu samu ganinsa yau, amma mutum dan ya zama richest man shikenan kuma ganinsa saiya zama wahala.ā€

Shidai Salman murmushi kawai yayi kaman zaice wani abu kuma saiya fasa.

Kaitsaye suka nufi Mai-nasara Hospital.

Tafiyar mintuna kad’anne ya kawosu bakin kofar katafaren asibitin.

Kasancewar kuma ba ashiga can Cikin hospital din da mota, matuk’ar ba emergency bane, yasa Salman parking motar anan babban parking lot na asibitin, wanda shi kansa ya kusan kwatan wata karamar unguwa.

Bud’e murfin motar Jannart tayi ta fito, tana me k’arewa kyau da had’uwar asibitin kallo.
Lallai privet Hospital ne daya amsa sunansa, saboda daga ginin asibitin ma kasan ba kananan billions aka kashe masa ba.

ā€œMai-nasara Hospital! Lallai asibitin ya had’u.ā€

Jannart din ta fad’a tana me Kallon Salman.

Shima Salman din kallonta yayi, tare da cewa.

ā€œTo Kema da bakinki kin fad’a, yanzu kiyi imagine tayaya za ace kinsamu ganin mamallakin wannan wajen acikin sauki? karki manta kuma bawai iya Hospital dinnan ya mallaka ba, yana da companies, bama a iya Nigeria ba, wallahi Jannart wannan mutumin *Richest Man* ne na k’arshe.ā€

Kai Jannart d’in ta jinjina, domin ita kanta ayanzu ta yarda da hakan.

Kaitsaye kuma suka kutsa cikin asibitin.

Acan b’angaren Rayyern kuwa kaitsaye Wajen buga wasan polo suka nufa.

Koda suka isa wajen da haduwarsa da kuma kyawunsa ya darawa kwatance.

A parking lot driver’nsa yayi parking.

Bayan ya fito daga motar nasa ne kuma kaitsaye ya nufi cikin wajen.
Da kwata-kwata babu mutane acikinsa.
Duk da tsananin girman wajen kuwa, amma bakajin motsin komai saina tarin dawakai da kuma tsirarun masu kula dasu.

Wanda kuma hakan ya faru ne saboda zuwan Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, kasancewar idan har zaizo wajen To yakan biya mak’udan kud’ad’e ne, ta yanda ranar baza'a amshi kuɗin wasuba, harsai yayi wasansa ya gama ak’alla na tsawon awa 2, bayan ya tafi ne kuma sauran jama’a zasu dawo su cigaba da harkokinsu bawai kuma yana haka dan isa bane, sai dan sosai hayani kan iya sa mishi ciwon kai, yana kuma jin daɗi wasan polo a jikinsa.

Shigarsa cikin babban wajen wasan buga Polo dinne kuma yasashi, zare alkyabban dake jikinsa ya ajiye, tare da wayoyinsa harma da y’ar bag din da yasaka bottle water mai sanyi aciki.

K’arasawa yayi wajen tarin dokunan da akeyin wasan dasu, tare da zab’o wani farin doki, wanda mafi yawanci idan yazo shi yake hawa.

Batare da wani bata lokaci ba kuma ya dale saman dokin tare da rik’e Sandar buga k’wallon nasa ya soma sukuwa, tare da gabatar da wasan.


Mai-nasara hospital.

Salman da kuma Jannart dake tsaye abakin k’ofar office d’inne suka tsaya suna Kallon juna.

Salman ne ya gyara tsayuwarsa tare da cewa.

ā€œPlease Jananrt mushiga mana, kinfi kowa sanin irin wahalan da muka sha, kafun mu samu aka nuna mana wannan office din, wannan ita kadaice daman mu ta karshe, kada muyi wasa da ita.ā€

Kai Jannart ta jinjina kana asanyaye tace.

ā€œTo.ā€

Knocking kofar Salman yayi, inda Dr Sulaiman dake zaune akan wata hamshakiyar kujera ya bada izinin shigowa.

Hakanne kuwa yasa suka kutsa Kai suka shiga bakinsu d’auke da sallama.

Amsa musu sallaman Sulaiman yayi, tare da dago kansa ya kallesu.

D’an Kallon juna suka tsayayi na tsawon sakanni, kafun daga bisani Dr.Sulaiman din yace.

ā€œBismillah’nku.ā€
Ya kare maganan yana meyi musu nuni da wasu kujeru guda biyu dake gabansa.

Yayinda kuma acikin mintuna kadan na Kallon daya musu, ya fahimci cewar sudin ba marassa lafiya bane.

Zama sukayi akan kujerun daya nuna musu d’in, Salman ne ya mik’awa Sulaiman din hannu suka gaisa, Yayinda ita kuma Jannart ta gaidashi da sassanyar muryarta, wanda har hakan yasa shi kasa jurewa saida ya dago ya sake Kallon ta, Yayinda azuciyarsa yake mamakin jin ta gaishe shi da Hausa, domin sam baiyi mata Kallon y’ar Nigeria kuma maijin Hausa ba, kasancewar yanayin kamannin ta da kuma shigarta da tsarinta dabanne, bawai irin normal mata da kowa ya sani bane, ita din akwai abu na musamman atattare da ita, wanda kowanni irin Namiji idan ya kalleta saiya gane hakan.

ā€œMeke tafe daku? Ko kuma patient kuka kawo?.ā€

Salaiman ya tambaya.


Jin hakan ne yasa Salman d’an gyara zama, tare da fuskarta Sulaiman d’in, kana atausashe yace.

ā€œSunana Salman Aliyu, wannan kuma abokiyar aikina ce sunanta Jannart Idi Sale Dakata, Mu y’an Jarida ne, ma’aikata Tashar Arewa24.ā€

ID Card d’insu suka zaro tare da nunawa Salaiman daya zuba musu ido.

Salman ne ya cigaba da cewa.

ā€œMunzo nanne bisa dogaro da kuma fatan, dacewar samun ganin Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, Dan Allah Dr. Idan akwai taimakon da zakayi mana, ka taimaka muganshi, wallahi ganin nasa nada matuk’ar muhimmmanci, musamman ga Jannart.ā€

Ajiyar zuciya Sulaiman ya sauke, tare da maida hankalinsa ga Jannart, domin kuwa idan har abunda tunaninsa ya basa gaskiya ne, to Lallai ya kamata ace ya taimaka musu.
Domin ya raya aransa cewa aiki aka basu domin su tattauna da Dr.Rayyern d’in.

Zamansa ya gyara kana anutse yace.

ā€œBabu damuwa tunda dai harkunzo nan Insha Allah zaku gansa, duk da cewar ayanzu baya cikin hospital d’in, amma Ina da tabbacin inda zaku sameshi, saidai kuma ganin nasa ba shine ba, dan Ina da tabbacin ba lallaine Dr. Rayyern ya amince kuyi hira dashi ba, saboda aduk k’asarnan babu wani gidan Jarida daya tab’a amincewa sukayi hira dashi.ā€

Idanu Jannart ta d’an lumshe ahankali, Yayinda ajikinta takejin Wannan shine last chance dinta, akasin haka kuwa zata iya rasa aikinta, wanda kuma shine ke sata acikin farinciki.

D’an cije labb’an bakinta tayi, kana cikin siririyar muryarta tace.

ā€œPlease Dr. I need your help please!! Banason nayi losing job d’ina!!!ā€

Takai k’arshen maganan muryarta araunane.

Wanda hakan yasa Dr.Sulaiman Jin tausayin yarinyar, saidai kuma har acikin zuciyarsa yayi mamakin, Jin tace bataso ta rasa aikinta.
Domin yasan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login