Showing 54001 words to 57000 words out of 350584 words

Chapter 19 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

lumshe idonta kana tace.
“bari naje saina dawo.”

Kai Momyn ta jinjina tare da cewa tagaishe da Abba Kabir din da kuma matarsa, da yaransa.

Da “to.” Jannart din ta amsa, kana tasa kai ta fice daga cikin falon.


Tana fitowa compound din gidan kuwa ta samu Baba Ado driver da guard dinta na jiran ta.

Domin tuntuni Daddy da kansa ya Gaya musu cewa Jannart din zata fita.
Yayinda kuma ya jaddada musu kulawa da ita.


Kamar Koda yaushe kuma tana shiga cikin mota, guard din nata ma suka shishshiga cikin tasu motar, tare da rufawa motar da Jannart din ke ciki baya.

Jin da tayi sunhau titi ne kuma yasa ta d’an jingina bayanta da jikin kujeran motar, tare da lumshe idanunta.

Ahankali take sauk’e ajiyar zuciya, Yayinda ayau din takejin kanta tamkar sakakkiyar tsuntsuwa.

Lallai watarana tana fata da burin samun yancin kanta, watarana tana fatan yin yawonta ita kad’ai batare da wani ko wata sun bibiyeta ba, haka kuma watarana tana fatan sauyawar rayuwarta gaba d’aya.

Yayinda kuma har acikin zuciyarta watarana take fata dason sanin kullin dake ƙule Cikin rayuwarta kamar yadda Barrister Kabir yasha faɗa mata.

Shin Meyasa Daddy’nta ya sanya mata tsaro maitsanani har haka duk da kuwa tana gamsuwa da irin soyayyar da yake nuna mata, ɗari bisa ɗari.

Meyasa Yah Junaid ke bibiyanta da munanan halaye? Da mugun manufa.

Yaushe ne canji zaizo cikin rayuwarta? Yaushe ne zatayi farinciki kamar kowa? Yaushe zataji kanta amatsayin Mace mai y’anci?

Lallai watarana zuciyarta kan gaya mata cewa Sauyin rayuwa zaizo.

Sai-dai yaushe zaizo? Da wani dalili zai taho a wanne yanayin duk bata sani ba.

Wani irin numfashi mai dumi ta fesar, adai-dai lokacin kuwa suka iso kofar madaidacin gidan Barrister Kabeer dake nan Nassarawa G.R.A

Wanda kuma isowarsu gidan yayi dai-dai da shigowar sak’o cikin wayarta.

Jin alaman shigowan Sakon da tayi ne kuma yasa ta d’ago wayartata ta duba.

Ganin sakon da aka rubuta mata dinne kuma yasa ta.
Jin wani irin bugun zuciya maitsanani.

Idanunta ta rumtse da k’arfi, cikin kuma muryarta da ke bayyana tsoro had’i da firgici Ta......



*GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya saya ba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota akai miki state ɗin da kike, Duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune TA *D.H.L Office*🤝🏻cikin mako ɗaya kayanki zai isa duk ƙasar da kike, sai dai akwai ɗan tsada cajinki da zasuyi
sayan na gari meda kudi gida.


GARKUWAR MA'AURATA


By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*TUBALI*

PAGE 14
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

*FREE PAGE NE*

*Littafin TUBALI na kuɗine ki biya kafin ki karanta dan Allah special Group 1k ne karamin group 500 bane kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, ko kuma ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp na 09097853276*



Ta buɗe idonta ganin sunan Yah Junaid na bisa screen ɗin wayarta ne yasa, ta fidda numfashin a hankali tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna'ilaihi rajiun Yah Junaid Kuma?”.
Cikin tsoro ta buɗe text ɗin dai-dai lokacin kuma mai gadin gidan Barrister Kabir ɗin ya buɗe musu gate.
Suka kutsa ciki.
"Dan ubanki ina kiranki bazaki amsa ba.
Maza ki ɗaga ko in ɓaɓɓllaki in mun haɗu".
Cikin ƙarfin hali ta zuge zip ɗin Baby hand bang din ta cilla wayar kana ta zuge ta rufe.

Da sauri Aunty Dijat tace.
"Lah Hafiz ga Aunty Jannart tazo".
Ta ƙare mgnar tana nufar inda motarsu Jannart tayi parking.
Hafiz kuwa da sauri ya juyo jin ance Jannart, cikin ware ido ya nufi motarsu a guje yana cewa.
"Oyoyo my Aunty, Hafiza ga Aunty Jannart tazo".

Murmushi mai cike da jin daɗi Jannart tayi kana ta ƙarisa fitowa tare da ware musu hannayenta.
A guje suka abka jikinta su duka biyu.

Cikin jin daɗi da son yaran ta ɗaga Hafiza da bazata wuce 7 year's ba.

Ruggume ta sukayi duka suna farin cikin ganinta.
Cikin kula, so, ƙauna, da tausayawa Aunty Dijat ta iso garesu fuska ɗauke da murmushi tace.
“Oyoyo Aunty Jannart, yau munji daɗin mu kin tunomo”.
Cike da happy tace.
"My Aunty kullum kuna raina".
Hannu tasa ta amshi Hafiza tare da cewa.
"Zo nan kada ki karya min ƴata maza mu shiga daga ciki."
Aifa tana faɗin haka Hafiz ya ɗiba a guje yayi cikin gida.
Ita kuwa Jannart juyowa tayi ta kalli Baba Ado dake gaisawa da Aunty Dijat.

Ita kuwa Aunty Dijat kamo hannun Jannart tayi suka juya suka nufi cikin gida.
Cikin murmushi ta juyo ta kalli Baba Ado dake cewa.
"Jannart muje ne ko mu jiraki".
“A'a Baba Ado ku jirani Awa uku Daddy ya bani".
Kai ya jinjina mata, kana ya koma wurin mai gadin gidan.
Su Sunday Kuma suka tsaya tamkar gumakan taɓo.

Daga bakin falon Hafiz keta rabkawa Barrister Kabir kira.
"Abba! Abba!! Kazo ga Aunty Jannart tazo".

Da sauri Ya miƙe tsaye, tare da katse wayan da yakeyi wanda kuma dama akan wani case ne da zasu shiga gobe,
Cike da farin ciki ya fara tako steps ɗin sauƙowa men falon su.

Ita kuwa Jannart Murmushin jin daɗi takeyi wanda ke bayyana tsantsan jin daɗin da take ciki.
Ita kuwa Aunty Dijat kitchen ta nufa.

fruits masu sanyi ta ciko mata plate dasu.
Kana da Bootle water.
Tana isowa Abba na ƙarasowa.
Kujerar dake gefenta ya zauna tare da sakin murmushi yace.
"Hafeeza zaki karya min cinyar ƴa ko".
Murmushi tayi tare da ɗan zamowa kaɗan tace.
"Abba ina yini".
"Lfy lau Alhamdulillah Jannart ya jikinki!?”.
Barrister Kabir ya faɗa cikin kulawa.
Yana mai kallon matarsa dake nuna tsantsan so ga Jannart murmushi yayi tare da cewa.
"A'a Khadijah kin mance Jannart ne da Asman kika kawo abu mai sanyi".
Ita kuwa Jannart a hankali tace.
"Abba nayi sauƙifa zan iya cin komai".
Kai ya jujjuya tare da cewa.
"A a ban yardaba".
Da sauri Hafiz Wanda zai iya kai shekaru goma sha shida yace.
"Abba yau kawai a barta taci".
Ina tuni Aunty Dijat ta juya kitchen.
Pepper chicken da yanzu ta gama aikinshi da zafinshi ta ɗebo, mata tare da haɗa mata tea mai zafi.

"Yauwa ci wannan bari su kuma na sa miki innabi da tufa ɗin a ruwa zasuyi ɗumi zuwa anjima sai kici".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ngd matuƙa my Aunty".
Haka nan sukayi ta nan-nan da ita tamkar suyi mata numfashi.

A can MAI-NASARA NIG LMT kuwa.
Dr Rayyern Mai-nasara ne zaune cikin nitsuwa yake duba bayananan da hukumar Road Safety, Suka turo mishi akan number motar daya tura musu.
Dan neman ƙarin bayanin.
Sanin waye shine yasa nan take suka turo mishi sunan mamalakin motar.

"Alhaji Idi Saleh Dakata."
Shine abin daya mai-mai-ta kan lips ɗin shi.
Numfashin gajiya ya ɗan fesar kana a hankali ya kuma ci gaba da ganin jerin jadawalin numbers ɗin motocin da suke mallakinsa kab.
Ido ya lumshe tare da meda bayanshi ya jingina jikin kujerar a hankali.
Ya fara jujjuya kujerar, cikin sanyi ya fesar da numfashi mai sanyi tare da cewa.
"Uhummm!”.
Kana ya gyara zamanshi tare da ajiye wayar da tunanin waɗannan tsoffin gefe.
System ɗin shi ya jawo ya ci gaba da aikin daya shafi Campany'shi na neman ma'aikata...


Yah Junaid kuwa yau ji yake tamkar ya kashe Jannart in ya kamata sabida, video'nta da Ushe ya turo mishi lokacin da Rayyern ke samata al'kyabbar.
“Wato dai shegiyar nan tasan maza tasan garɗinsu, ni takeyiwa tereren bankaɗa in na taɓata.
Yau kuwa tabbas sai na caccakaki shegiya ƴar iska mai idon cin maza.
Yoh dama ya za'ayi wannan zuƙeƙeyiyar. Tarwadan kyau ta zauna babu masu lasarta".
Kwafa yayi tare da ƙara yi mata text cewa yana kiranta fa.
Dan shi masifar feelings yasa ya mance da cewa bata nan ma.
Gashi ya leƙa falo yafi sau uku Mom na zaune...

A gidan Barrister Kabir kuwa.
Hira sosai Aunty Dijat da Jannart Da Abba dasu Hafiz sukeyi sunci sun Sha, sun kaiwa su Baba Ado ma, dan Aunty Dijat matar kwaraice.
Kiran sallan azahar da akayi ne, yasa Abba miƙewa shida Hafiz suka shiga sukayi al'wala bayan sun fito suka nufi masallaci.

Abba na cewa.
"Ku tashi kuyi salla, ko”.
To sukace.
Bayan sun fita Aunty Dijat ta miƙe tare da cewa.
"Muje muyi salla ko Jannart".
Kanta a sunkuye tana yiwa Hafiza kitson kalba ƴan ƙanana a tarin gashin ta tace.
"Nayi".
Tayi mgnar a hankali kana a gajarce.
Murmushi Aunty Dijat tayi tare da cewa.
"Oho kinyi da mutanen Makka kenan".
Cike da kunya tasa tafin hannunta ta rufe fuskarta cikin tsananin kunyar an gane tana fashin salla.

Ita kuwa Aunty Dijat murmushi tayi tare da wucewa Bedroom ɗin ta...

Bayan tayi sallan ne kuma ta fito ta sameta suna kitson.
Kitchin ta wuce Fruits ɗin ta kawo mata.
Kana ta zauna gefenta tare da miƙa mata fork.

Dai-dai lokacin Abba da Hafiz suka shigo.
Cikin kula Abba ya kalleta kana yace.
"Yauwa Jannart ku taso muje mall ku ɗan zazzaɓi abin da kukeso ko".
Cikin jin daɗi tace.
"Abba muna kitso komai ma aka kawo mana muna so".
Ya gane manufarta bazatace bazata jeba, amman ta bashi mgnar a dunƙule sanin tanada hujjar faɗin haka yasa yace.
"Daddy zaiyi faɗa ko?".
Kai ta gyaɗa tare da gyara zaman kan Hafiza bisa cinyarta kana tace.
"Kuma nan ɗin ma awa uku fa ya bani. Gashi yanzu naci biyu saura ɗaya".
Hannu ya miƙa wa Hafiz tare da cewa.
"Toh ba matsala kuyi kitsonku bari muje yanzu mu dawo, kada Daddy ya haɗa hardani ya tsire”.
Kai ta jinjina, har sunje bakin ƙofar fita kuma ya juyo cikin kulawa yace.
"Toh me da me kikeso in seyo miki?”.
Kai ta ɗan ɗago ta kalleshi tare da yin murmushi tace.
"Abba kayan hausawa".
Cikin gamsuwa yace.
"Masha Allah Ina ga dai ɗiyata ta canza salon shiga ko”.
Cike da kunya tace.
"Eh Abba naga waɗanan can ɗin basu da rufin asiri kamar namu.
Yauwa Abba da hijabai".
Ita dai Aunty Dijat murmushi kawai takeyi.
Shi kuwa toh yace kana ya fita.

Nan sukaci gaba da hira su kuma.
Da sauri Jannart ta ɗago kanta ta kalli Aunty Dijat jin abinda take cewa cikin hirar tasu.
"Uhm Jannart yanzu kam komai ya dai-dai-ta ai ko?”.
“Me ɗin fa My Aunty?". Ta tambaya cikin rashin fahimta.
Gyara zama Dijat tayi ta fuskance ta da kyau kana a nitse tace.
"Kamar ci gaban rayuwarki mana, yanzu kin gama karatu, har kin fara aiki yanzu wata shida kenanfa da fara aikinki.
Toh yanzu kuma sauran miki me!?”.
Ido ta ɗan jujjuya kana a hankali tace.

“Ohon musu”.
Tayi mgnar a hankali.
Cike da mamaki Dijat tace.
"Su waye ɗin?”.
A hankali tace.
"Daddy da Yah Junaid mana”.
Ganin yadda Aunty Dijat ta zuba mata idone, yasa ta ɗan muskuta kana a hankali taci gaba da cewa.
“Ban sani ba kam yanzu kam, sai kuma yadda Daddy yace ai!".

Numfashin mai nauyi Dijat ta fesar kana a hankali tace.
"Uhmm Jannart kenan shin ke baki da tsarin kankine a kan komai na rayuwarki. Dole sai abinda Daddy ya faɗa?”.
Da sauri ta gyaɗa mata kai alamun Yesss haka ne.
Apple ɗin data ɗauka ta ɗan ɓantara kana a nitse tace.
“Har auren ma, in baice kiyiba bazakiyi ba”.

Tada Hafiza tayi ta zaunar da ita gefe dan ta ida Mata kitson.
Cikin sanyi tace.
"Eh mana”.
Ta bata amsa da ɗan guntun murmushi, kana ta ronƙofar da kanta tace.
“Toh My Aunty Aure kuma! Ni kuma zanyi aure ne?”.

Da sauri Dijat tace.
"Mun shiga uku bazakiyi aure ba?”.

Nannauyan numfashin ta sauƙe kana tace.
“Yoh Ni na sani ne ai sai yadda Daddy da Yah Junaid sukace, Kuma ma ni ban taɓa tuno aureba, tunda basuma taɓa yimin mgnar aureba toh ni wake sona ma”.

Cikin tsananin tausayawa yadda ake juya rayuwar ƴarinyar ya zama bata tsarawa kanta komai ma sai abinda su Junaidu suka tsara mata, a takaice ma suke juya motsin rayuwarta.
A hankali tace.
“Toh wai babu mai zuwa gunki ne? Wanda kuke soyayya ko mgnar aure”.
Ta kuma jefowa Jannart tambaya.
Inabi ta tsinka tasa a bakinta kana a hankali tace.
"Ni kuma wa zaizo wurina, wayema ya sanni.
Nifa da zan samu Yah Junaid yayi aure ya bar gidanmu da shike nan wlh bani da matsalar komai a rayuwata zanci gaba da zama a gidanmu a haka har gaban abadan.
Ko kuma ace na dawo nan da bani da sauran damuwa a duniya wlh Ni banma san menene soba bare kuma soyayya bare batun aure.”

“Tirkashi”.

Shine abinda Dijat ta faɗa kana ta ture Hafiza daga jikin Jannart ɗin sannan a hankali tace.
"Uhmm koda yake ba mmki.
Toh dama ya za'ayi kiyi soyayyan waya isa ya isoki da kalmar so, yadda aka haɗaki da waɗannan bakaƙe kafuran ƙattin samudawan nan da ko yaushe suna biye dake tamkar inuwa.
Ina ai dama yana cikin manufar tosheki da akayi tako ina da gayya sabida kada wani ya kusanceki.”
Ta ƙare mgnar wasu siraran hawaye masu zafi na silalo mata.
Wanda haka yasa tuni itama Jannart idanunta suka cika da ƙwalla.
Cikin zubda hawaye Dijat taci gaba da cewa.
"A yadda Allah yayi miki cikekkiyar halitta mai nagarta wace ko mace ƴar uwarki bata gajiya da ganinki.
Ta yaya za'ace namiji kuma zai gaza sauƙe idanunshi a kanki da manufar so da ƙauna.
Toh ko nan wurin Abbankin adadin maza nawane suka zo da kansu dama waɗanda suka turo iyayensu kam sonki da neman aurenki wanda suke bada tabbacin tsoro ke hanasu fuskantar ki”.
Hannu tasa ta share hawayenta kana a hankali tace.
“My Aunty dole ne sai nayi aure? Ni kawai farin cikin rayuwa nake son samu”.
Cikin sanyi tace.
“Jannart duk wani farin cikin ƴa mace yana cikane in tana gidan mijinta kuma tayi dace da miji na gari.
Haka kuma duk farin cikin ƴa mace baya cika in batayi dace da miji na gari ba”.
A hankali tace.
"My Aunty Kenan dai dolen-dole saida aure farin cikin ƴa mace yake cika!?”.
Cikin sauƙe numfashi Dijat ta riƙo hannunta kana ta fara zaiyyano mata ni'imomin dake cikin aure da matsayin zaman aure dama manufar aure a musulci...”


Ramadan ne zaune a ƙasa kusa da kujerar da Mamy ke zaune.
Wayarsa ce saƙale a kunne a karo na bakwai ya kira Riyyam-nsra sai ace mishi yana bisa waya.
“Yanzuma bata shiga bako?”.
Mamy ta tambaya cikin kula.
"Uhum inafa ina ga dai ko dasu Zayton yake waya da Mammynsu.
Tun ɗazu waya taƙi ƙare wa".
Ramadan ya faɗa yana zura wayarsa a aljihu.
Gyara zama Mamy tayi tare da cewa.
"Toh Allah dai yasa lfy, kagafa yau ko breakfast baizo yaci ba, gashi yanzu har azahar ta gota bai kuma zoba".
Kai ya ɗan jingina da kujera kana yace.
"Bari in nayi wonka, kafin in wuce asibiti sai in biya in kai mushi abinci.”
Da sauri Mamy tace.
"Yauwa yafi kam”.
Da sauri suka kalli Abba da shigowarsa kenan cikin haɗe fuska yace.
"Har ke ɗin ma, shisshigewa lamarin da bai shafeki ba kikeyi, to ya za'ayi in iya control ɗin yaranki da yimin yayuɓe-yayuɓe suna kawo min cikin gida.
Toh me ruwanku dan bai zoba!?”.

Shiru sukayi baki ɗayansu
Saida ya tsagaita Ramadan ya ɗan longoɓar da kai tare da cewa.
"Afwan Yah Abba”.
Kai ya gyaɗa kana ya wuce falonshi na ciki.

A bakin gate kuwa Usman PA ne ya shigo da motarsa bayan Hadi ya buɗe masa.
Da sauri ya nufi wurin Baba Mauɗo bayan ya fito.
"Barka da yamma Baba Mauɗo”.
Cikin kulawa Baba Mauɗo yace.
"A'a Barka dai Usmanu! Kwana biyu shiru tunda kuka dawo bana ganinka ka bar Rayyanu shi ɗaya lfy dai ko?”.
Cikin son dottijon yace.
“Lafiya lau Alhamdulillah Baba Mauɗo, wlh da muka dawo ne Mama, ba lfy ashe ba ciwone matsalar ba, wai tayi kewan ƙannenta tofa dole ranarda muka dawo washe gari ta sani muka tafi Gombe bamu dawo ba sai jiya da dare da yake bamu taso da wuriba”.
Cike da kulawa yace.
“Masha Allah. Allah ya bada ladan ziyara, sai kuyi ta haƙuri damu, iyaye in an fara girma tamkar yara ake zama.
Allah yayi muku al'barka”.
Amin Amin yace.

Kana ya nufi cikin gida.
Da sallama a baki shi ya tura ƙofar falon.

Da sauri Ramadan yace.
"Wa alaikassalam, Yah Usman mutanen Gombe Kun dawo kenan".
Murmushi yayi tare da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login