Showing 48001 words to 51000 words out of 350584 words
kamarta dinnan ba ace daga gidan talakawa ta fito ba, Sam Kwata-kwata ma batayi kama da hakan ba bare kuma waye bai san sunan mahaifintaba Alhaji idi Saleh Dakata.
Sake gyara zamansa yayi, tare da cewa.
“Badamuwa zan taimaka muku Insha Allah, yau Wednessday kuma duk ranan wednessday at this time Dr. Rayyern yakan je wajen wasan Polo, ba kuma ya barin wajen sai 5 na yamma, saboda haka zan baku Andreas din wajen, zakuma ku iya zuwa kusa meshi.
Wani irin sanyi Jannart taji acikin zuciyarta, Yayinda Salman kuwa yayiwa Dr.Sulaiman din Godiya.
Shikuwa Dr. Sulaiman a paper ya rubuta musu adress din wajen, tare kuma da yi musu fatan nasara.
Godiya sosai sukayi masa kafun sukayi masa sallama, cikin hanzari suka fito daga cikin asibitin.
Direct wajen da motar Salman din ke fake suka nufa.
Suna shiga kuwa ya tada motar suka nufi wajen buga wasan Polo’n kaitsaye.
Tafiyar da bata wuce ta 20mn sukayi ba, sai gasu abakin kofar babban mashigar wajen wasan Polo’n da yake duka a unguwa ɗaya ce.
Bayan kuma Salman yayi parking motar ne suka fito, direct mashigan wajen suka nufa.
Amma sai guard din dake tsaron wajen suka dakatar dasu, had’e da cewa bazasu shiga ba, anyi clossing wajen na two hours, suje anjima su dawo.
Rau-rau Jannart tayi da ido, Yayinda Salman kuwa ya zaro ID card d’insa ya nuna musu, cikin sanin makamar aikinsa kuma yace.
“Mu y’an Jarida ne, ankuma tabbatar mana da cewar mutumin da muke nema yana cikin wajen nan, please dan Allah kubari mugansa, abune na gaggawa.”
Dan Kallon juna guard din sukayi, kaman zasu hanasu kuma sai suka matsa musu alaman su shige.
Aikuwa wani irin sanyi Jannart taji zuciyarta tayi, cikin sauri kuwa suka sakai suka wuce cikin wajen.
Y’an tsirarun mutanen dake wajen suka soma wuce wa, ganin kuma kamar babu alaman yalwan mutane awajenne yasa sukayi tsaya, saboda su kansu basu San ta Ina zasu fara nemansa ba.
Jannart dinne ta kalli Salman kana zuciyarta akarye tace.
“Anya kuwa Salman kana ga zamu sameshi anan wajen?”
Shiru Salman din yayi, alamun nazari dai-dai lokacin kuwa wani ma’aikacin wajen yazo gilmawa ta gabansu.
Salman dinne ya tare mutumin, tare da cewa.
“Dan Allah Malam muna tambaya ne,".
"Allah yasa na sani."
Ya basu amsa yana kallon Jannart.
Numfashin gajiya Salman ya sauƙe tare da cewa.
"Please Dr. Rayyern Basheer Mainasara muke nema.”
Idanu sauran ma’aikatan wajen da sukaji abunda Salman din ya fada suka zuba musu.
Shikuwa wanda Salman din ya tambaya, kansa ya girgiza cike da mamaki kuma yace.
“Dr. Rayyern Bashir Mai-nasara kuma anan wajen? gaskiya bana tunanin hakan, saboda muma bamu sanshi ba, sunansa kawai dai mukeji, amma dama yana zuwa nan dinne.”
Baki Jannart ta cije tare da sanya hannayenta ta kama waist dinta.
Cike da takaici tace.
“Again na sake rasa damata.”
“Calm down Jannart, mu k’arasa can cikin wajen mu duba ko zamu dace.”
Salman ya ce mata.
Fuskarta ta kwab’e saboda zuwa yanzu ta fara gajiya da gantalin neman mutumin tunda shi ba kuɗi bane.
Amma da yake ta San wannan din shine last hope dinta, hakan yasa tabi bayan Salman suka shige cikin inda ake gudanar da asalin wasan Polo din.
A dai-dai lokacin kuwa Rayyern yayi nisa acikin wasan nasa, sai sukuwa yakeyi akan doki cike da k’warewa da jin daɗin yanayin wurin shiru ba hayani ba mai takura mishi.
Yayinda kuma ya kasance shi kad’ai ne awajen yake sashi karsashi.
D’an shigowa su Jannart da Salman sukayi Cikin wajen, Saidai kuma ganin da sukayi babu kowa awajenne yasa Jannart jingina bayanta da jikin wani k’arfe.
Akasalance tace.
“Salman zuwa yanzu Tabbas inaji ajikina cewar na kusa rasa aikina, wannan ɗan is ɗin mutumin ba saukin ganine dashi ba, kalli wajen nan fa babu kowa sai wancan mutumin daya bamu baya yana ta sukuwa akan doki shima ɗaya kamar mara aikin yi.”
Takai karshen maganan nata tana me Kallon bayan Dr Rayyern, da yake nesa dasu sosai.
Dan kallonta Salman yayi cikin kuma son k’arfafa mata guiwa yace.
“Karki damu Jannart Insha Allah zamu hadu dashi, Yanzu dai mukarasa wajen wancan mutumin sai mu tambayeshi koya San wani abu dangane da wanda muke nema.”
Still fuskarta ta kwab’e tare da cewa.
“shikenan muje.”
Hakan kuwa akayi inda suka k’arasa shiga can cikin wajen wasan dake malale da koriyar ciyawa mai cike da damshi.
Suna kara kusantan cikin wurin wasanne kuwa Rayyern din ya juyo da akalar dokinsa.
Sai-dai kuma Sam baisauke idanunsa akansu ba.
Idanu gaba dayansu suka zazzaro, Yayinda Jannart kuwa cike da mamaki tadan matsa bayan Salman.
Tana fadin
“Laaa Salman wannan mutumin nefa da na fasawa waya a airport, wayyo Allah Salman nikam kazo mu gudu, tun kafun ma ya ganmu.”
Kai Salman din ya girgiza tare da cewa.
“Mu gudu kuma Jannart? saikace marasa gskiya muje dai ki bashi hakuri dama ai aranar baki bashi hakuri ba, daga ganinsa ma Babban mutum ne watakila ma zai iya taimaka mana muga Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din.”
Fiki-fiki tayi da idanunta, kana adan tsorace tace.
“Shikenan muje.”
Nanfa suka nufi wajen Rayyern d’in.
Dai-dai lokacin kuwa Rayyern dayake matuk’ar gudu akan doki, batare daya d’ago ko waiwaye ba ya taho aguje.
Kaitsaye kuma direct inda su Jannart d’in ke tsaye ya nufa.
Gadan gadan.
Su Jannart din kuwa kansu basu ankar ba, saida dokin ya kusan zuwa gab dasu.
Wani irin k’ara mai cike da tsoro da firgici Jannart ta saka da karfi, tare kuma da daura hannayenta akanta ta rumtse Idanunta k’am, domin ta gama sadak’arwa akan cewar dokin ya nuk’urk’usheta ma angama lokaci ɗaya numfashin ta ya fara fizgan firgici.
Domin hatta Salman dake gefenta shima yayi surrender.
Rayyern kuwa Sam bai Ankara ba saida ihun Jannart din ya shiga dodon kunnensa, wanda hakan yasa cikin sauri ya dago kansa.
Ganin yana gab da bi ta kansu ne, yasashi saurin.
Damƙe igiyar linzamin dokin da ƙarfi ya tsayar dashi cak.
Saboda ganin macen da yayi agabansa ne kuma ya sashi dirowa daga saman dokin.
Bayan ya juyashi.
Wani irin dogon tsaki yaja.
Tare da Kallon Salman wanda keta sauk’e ajiyar zuciya, kana ya watsawa Jannart din dake gabansa wani kallon da yasa cikinta ya murda ya haɗe da numfashin dake sauya salon fita da shiga.
Cikin tsuke fuska yace.
“Bakwa ganine, yanzu idan da nabi takanku fa?”
“Kayi hakuri dan Allah!” Salman ya fad’a asanyaye.
Itakuwa Jannart sai ayanzu ta bud’e idanunta, Yayinda gaba daya jikinta ke kakkarwa.
Hannu tasa ta dafe ƙirjinta.
Rayyern kuwa y’ar gajerar tsaki yaja, batare kuma daya sake ce musu komai ba ya juya ya nufi inda kayayyakinsa suke.
Yana zuwa kuwa ya zauna akan wata kujerar silver mai daukar mutun uku,
Sunkuyowa yayi tare da bud’e jakan daya shigo da ita ya zaro bottle water, b’alle murfin goran yayi, kana ya soma zubawa akan tarin sumar dake kansa wanda yake jin zufa na tsastsafo mishi.
Jin da yayi baisamu gamsuwa bane kuma yasashi karkad’a gashin kannasa dan yadda ruwan zai taɓa fatar kansa, wanda hakan yasa har ruwan dake kan nasa ya watsu akan fuskar Jannart.
Salman dake tsaye kuwa dan matsowa yayi, tare da gaishe da Rayyern d’in.
Batare kuma daya dago ba ya amsawa Salman d’in atakaice.
Idanu Salman yayiwa Rayyern dake tsaye, alaman ta gaishe shi.
D’an k’aramin bakinta ta turo gaba tare dasa hannunta ta goge ruwan daya watsa mata, kana asanyaye tace.
“Ina wuni.”
Shiru yayi bai amsa taba, tare dayin kamar ma baijita ba.
“Ina wuni.”
Jannart d’in ta sake fad’a akaro na biyu.
still shiru yasakeyi kamar baijita ba.
“Kibashi hakuri.”
Salman dake tsaye ya fada kasa-kasa.
Karamin bakinta ta sake turowa, cikin kuma wata irin murya mai kama da shagwab’a, sakalci, sanyi da kuma tsoro tace.
“Kayi hakuri please, ranan nayi maka b’arna amma bada sanina nayi hakan ba, Dan Allah da Manzonsa kayi hakuri.”
Idanunsa yadan lumshe saboda jin ta had’asa da sunan Allah da Manzonsa ne kuma, yasashi gyaɗa mata kai alaman yayi.
“Nagode.” Ta fad’a asanyaye.
Shikuwa Salman ganin hakanne ya sashi dan matsowa, cikin neman alfarma yace.
“Dan Allah ranka ya dad’e tambaya mukeyi.”
D’ago Kai Rayyern din yayi ya kalli Salman din afakaice.
Batare kuma dayace komai ba ya maida kansa k’asa tare da ɗaukan ɗan karamin towel ɗin dake gefe ya fara goge suman kanshi zuwa wuyanshi da fuskarshi da sajenshi da ruwan ya jiƙa.
Salman kuwa ganin hakanne yasashi Kallon Jannart, wanda gaba d’aya mood dinta ya sanja,tun lokaci da taga kamar dokin zai takesu ta soma sakin wani irin numfashi sama-sama a hankali.
Wanda da dukkan alama kuma tsoritan da tayi dazunne yakeson tayar mata da ciwon ta.
Sanin yanda ciwon keyi mata idan ya tashi ne kuma yasa, Salman din cewa.
“Subahanallah Jannart ciwonki ko?.”
Kai ta gyaɗa mishi cikin jawo ajiyan zuciya da take son yi.
Cikin kula ya nuna mata gefen Rayyern dan babu wata kujerar a nan kusa dasu.
"Maza ga waje ki zauna.”
Ya kare maganan yana meyi mata
Nuni da d’an gefen Rayyern, wanda kuma dama wajen zaman daya rage din bai wuce na zaman mutum daya ba sabida ya ajiye tarkacensa a wajan zaman mutun ɗaya gashi kuma a ɗaya wojen.
Jannart kuwa kasancewar dama ta gaji da tsayuwa kuma ga numfashin ta dake fizga ne yasa, batare da ta musa ba ta zauna awajen sanin in ta zauna zai iya dai-dai-ta.
Shikuwa Salman ƙara matsosu yayi.
Tare da sake maimaita maganarsa ta dazu.
“Dan Allah ranka ya dad’e tambaya mukeyi.”
“Inaji.”
Rayyern din ya fada agajarce, nan ma saboda yaji Salman din ya hadashi da Allah ne.
"Dan Allah wani mutum muke nema".
Uhum ya kuma cewa a taƙaice.
Gyara tsayuwa Salman yayi tare da cewa.
" Sunan shi Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara.
Shi muke nema, munje Hospital d’insa ne aka tabbatar mana da cewa Lallai-Lallai yana nan, shine muke tambaya dan Allah koka sanshi?”
Ad’an fakaice Rayyern din ya kalli Salman, saidai kuma cikin halin nuna ko inkula yace.
“Meyasa kuke nemanshi me zai muku? Wa yace muku yana nan?.”
Jannart dake dan haki ne taja ajiyan zuciya ta fizogishi da ɗan ƙarfi kana tace.
“Mitssss mutun sai rashin gsky, gaba ɗaya ya wahal damu."
Ta wutsiyar idonshi ya ɗan kalleta a fizge.
Ita kuwa ci ga da cewa tayi.
"Nemansa kawai mukeyi, wallahi daga yanzu kuma ni nagaji,
Dan bazan zauna inyi ta neman wani can ƙato baƙi mummuna mai ƙaton tumbi ba dan yayi kuɗi yana jin kansa waya masan TUBALI kuɗin nashi ko na haram ne shiyasa yake tsoron yin ido huɗu damu ƴan jaridu.
Kada ya gaza amsa mana tambayoyinmu."
Numfashin ta fesar a hankali jin ya dai-dai ta.
Salman nata jujjuya mata kai ina bata ganiba bare tasawa bakinta linzamin.
Tsaki ta ɗan ja tare da ci gaba da cewa.
"Mutumin nan ya wahalar damu sosai, na farko dai shiba kudi ba, amma na lura kudi yafi saukin samu akanshi.”
Alama Salman ya mata akan tayi shiru, da yin gyaran murya.
hakanne kuwa yasa tayi shirun.
Shikuwa Rayyern tunda ta fara maganan yake kallonta ta wutsiyar idanunsa baki cai-cai.
Salman kuwa gyara tsayuwarsa yayi, tare da fadin.
“Mu yan jarida ne kuma ma’aikatan tashar Arewa24, munzo nanne domin samun daman yin hira dashi, Lallai kuma muna da buk’atar ganinsa.
Domin rashin samun tattaunawa dashi ɗin, dai-dai yake da rasa aikin mu.”
Fuska Rayyern din yadan tab’e tare da cewa.
“Uhummm.” Atakaice.
Jin hakanne kuma yasa jikin Salman yin sanyi, still cikin yanayin dake bayyana damuwarsa yace.
“Dan Allah In dai kasan hanyar da zanbi wajen ganinsa ka taimaka min, Banason rasa aikina, inason aikina sosai, Dan Allah Idan ka sanshi, ko kuma kasan inda zan sameshi ka fad’amin, domin da wannan aikin kad’ai na dogara, dashi ne kuma nake ciyar da iyalaina da iyayena, dan Allah ka taimaka kada in rasa aikina.”
Tabbas Salman ya karyo lagonsa tunda ya hadashi da Allah da kuma nuna masa aikin shine mafogararsa, Idanunsa yadan lumshe ahankali, batare kuma daya kalli daya daga cikinsu ba yace.
“Naji badamuwa amma dai yanzu kam bayanan, Zan gaya masa idan ya amince shikenan, zan kawoshi har cikin tashan Arewa24 din kuyi mishi duk tambayar da kukeso.”
Farinciki da tsananin jindadi ne ya lullub’e cikin zuciyar Jannart da Salman.
Cikin bayyana zallan jin dadi Salman yace.
“Mungode sosai ranka ya dad’e, mungode kwarai, saidai amma dama ka sanshi ne?”
Kansa ya jinjina tare da cewa.
“Eh nasanshi uban gidanane zan gaya masa Insha Allah kuma zaizo zan roƙeshi in gaya masa uzurinka bisa tausayawarsa kan kada ka rasa aikinka da kake kula da ilanka zaizo in Sha Allah.”
Murmushi Jannart dake gefe tayi, tare da lumshe idanunta saboda wani irin sanyi da taji acikin zuciyarta sai kuma ta ɗan gyara zamanta.
Shikuwa Salman cikin tsananin jin daɗi yace.
“Sir! Nagode! Nagode!! sosai!!! Dan Allah kayi mishi magana, ni kuma zan tsumayeka har zuwa nan da y’an wasu kwanaki, wallahi Banason rasa aikina yau kuma saura kwana takwas za'ayi hirar dashi ranar Alhamis na sama.”
Kai Rayyern din ya jinjina, tare da sake cewa.
“Insha Allah zaizo.”
“Ka tabbatar zaizo?”
Jannart da nutsuwa ya dan fara sauka azuciyarta ta fad’a.
Dan juyawa yayi ya watsa mata harara, cikin zuciyarsa kuwa cewa yayi.
“Oho bansani ba shegen baki.”
Salman da farinciki ya cika zuciyarsa kuwa, cewa yayi.
“Mungode sosai amma dan Allah in ba matsala ka bamu numbern ka saboda idan zaizo din musani.”
Kansa yadan girgiza, cikin kuma rashin sabonsa da yawan magana yace.
“No kai dai ka bani taka numbern.”
To Salman yace Cikin gaggawa kuma ya bashi numbernsa.
Mikewa tsaye yayi fuskarsa cike da farinciki yace.
“Alhamdulillah Jannart taso mutafi Insha Allah yanzu kam na samu full confidence.”
Yayi maganar yana me soma tafiya, saboda tsananin farincikin da yake ciki kuwa bai majira Jananrt dinba.
Jannart kuwa ganin Salman din ya soma tafiya ne yasa ta mik’ewa tsaye itama.
Tashin nata kuwa yayi dai-dai da juyowan Rayyern inda ya sauke idanunsa Akan bayanta.
Da sauri ya rumtse idanunshi da ƙarfi tare da kame jikinsa sabida yadda yaji tsikar jikinshi na mimmiƙewa yana tashi tsaye.
Sabida a bunda ya gani ajikinta.
Yadda yaji tsikar jikinshi na tashi ne ya kuma sashi buɗe idanunsa.
Damatsan hannunsa ya kalla gaba ɗaya tattausan gargasar jikinsa ta miƙe tsaye.
Ita kuwa Jannart taku ta farayi da nufin bin bayan Salman wanda haka yasa ta ƙara matsowa gabanshi tana takun dake juya kyawawan mazaunanta.
Fuskarshi ya kuma yamutsawa.
Tare da saurin kawar da kansa gefe.
“Meye haka?”
Ya fad’a azuciyarsa yana mai jin kamar ana tsikarinsa
Jannart kuwa da batasan komai ba, ahankali ta soma dan takawa.
"Ta yaya mace zata kasa sanin ranakun al'adar ta? Ko ta kasa kimtsa kanta har ya fito ya ɓata mata sutura?".
Yayiwa kansa tambayoyin a jere.
"Miteeeew". Ya kuma jan gajeren tsaki.
"Daga nan zuwa parking lot mutun nawa zata sa suga jininta, maza nawa zasu ganta a haka, yanzu ita in an barta wai mai hankali ce ko? Waɗanne irin iyayene gareta da zasu barta kara zube da irin wannan shigar, na tabbatar da suturarmu ta hausa fulani tasa baza'a gane lalacewar kayan jikinta da wuriba kamar wannan tsukekken farin wondon pallozo ɗin ko ya ɓata mata jiki hijabinta zai kareta."
Yayi kalaman a saman harshensa.
A hankali ya ɗan juyo ya kalleta tana mai ci gaba da tafiya.
"Ko ba komai musulmace yana da kyau ta suturce kanta".
Ya faɗa yana kallon yadda take jujjuyawa tamkar Wahainiya.
Sai-dai bai wuce taku goma tayi ba zuwa sha biyu.
Taji muryarsa ta ratsa dodon kunnenta.
Inda yace “Stop.” Cikin wata irin kakkauran murya.
Aikuwa cak ta tsaya saidai kuma Sam ta kasa juyawa ta kalleshi.
Shikuwa Rayyern fuskarsa ya sake had’ewa, tare da yamutsaawa dan ji yake tamkar zaiyi amai kana ahankali ya juyo ya kalli alkyabbar shi dayake gefenshi.
A hankali yasa hannunshin ya d’auki alkyabban.
Ya tashi tsaye kana ya fara taku a nitse.
Har lau bata juyoba kuma bataci gaba da tafiya ba.
Salman kuwa juyowa yayi ya zuba musu ido.
Kauda kansa gefe yayi lokacin daya kara taku ɗaya ya iso kusa da Jannart ɗin.
Ƙara matsowa yayi kusa da ita yana mai ware alkyabbar.
Kanshi ya ɗan ronkofar cikin yamutsa fuska yace.
“Duk wata Macen da tasan ciwon kanta, bata yawo a haka kamar yanda ke kike yi, sannan mata da yawa suna sirranta kansu, amma ke kina bayyana kazantarki in kika sani nayi amai bazan yafeba.”
Cike da mamaki ta ɗan juyo yana kallonshi.
Hakan ya zama kamar irin hirar masoyane irin ana kallon juna nan.
Wani saurayi ne dake can ta bayane yana kallonsu ta cikin raga,
Ya zaro wayarsa da sauri ya fara ɗaukar su hoto, domin ya gano ƙanwar Junaidu ce.
Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara harara ya watsa mata tare da cewa.
"Mitssssss Ni ki dena kallona ko in tsokale idanun".
Ya fad’i maganar yana me zagayeta tare da dago alkyabban ya d’aura mata akan K...!
Fawal beauty parlor sunai muku albashir da bude gidan Mata wato kigyara da kanki👩🏻🦰 da cewa suna gabatar da aiki na zamani kamar su gyaran jiki, spa kenan gyaran fuska wato facial,gyaran Kai, hair style , gyaran kafa pedicure,gyaran hannaye, manicure kitso,lalle ja da bakki,ba'a barsu abayaba suna saida kayan gyaran aure, turaruka,man shafawa, suna kwalliya wato makeup,turaren wuta, humrah,kulaccham dama abunda Baku sanshiba wato maida tsohuwa yarinya akankanin lokaci😄iya kudinka iya shagalinka💃kudai ku hanzarta zuwa ga wannan gida na mata zallah (FAWaL BEAUTY PARLOR)
Address: Main gate na fire service jimeta, opp sixty plaza.
kada kubari abaku labari😍 munai muku maraba a koda yaushe Mata yan kwalisa mace sai da gyara , yar uwa bora ba sunanki kizama mowar mai🏨 da taimakon FAWAL BEAUTY PARLOR 👩🏻🦰da kudinki qalilan kifita sab abunki ki baza kamci mai kama jiki.
Gamai buka contact CEO FAWaL BEAUTY PARLOR kan 09033901035 or 08078809930 sai kunzo, our time services from 8:am to 7pm, Monday to Saturday/ Sunday 10am to 6pm🪞🎁🛒🛍️🤝🏻
*By*
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*TUBALI*
PAGE 13
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*