Showing 312001 words to 315000 words out of 350584 words
Chapter 105 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete
kiransa yaƙi shiga”.
Cikin alhini nace mata.
“Toh kinsan kuna cewa, wannan abun shi neturom ne ko netyuk ɗin har yanzu baida ƙarfi a nan jihar tamu, naga shima kansa Alhajin wasu lokutan sai ya hau kan wancan dutsen yake samu yayi mgn”.
Shiru naga tayi sai kuma can ta ɗan kalleni tare da cewa.
“Nifa ina tsoro domin ya shaida min abokansa ne da sukeyin komai tare sun kuma san abubuwa da dama a kansan sun juya mishi baya, asalima har barazanar hallakashi sukeyi damu duka.
Gsky hankalina ya tashi, ina tsoron mutanen kasar nan”.
Da sauri nace to ta bani wayar inje in hau kan ɗan dutsen da nake ganin Alhaji na hawa yayi mgn da mutanensa, dan a lokacin duk faɗin Gembu membila mutun uku ne kacal keda wayar hannu kuma sai sun hau dutse suke kira, a lokacin kuma layi yafi waya tsada.
Koda na amshi wayar sai ta koma ciki.
Ni kuwa nayi ta gwada kiransa amman sam baya shiga.
Nima kaina hankali na ya tashi, haka yasa nayi ta zama a wurin har dare ya fara nisa har na yunƙura zan tashi sai kuma naji ƙaran wayar, da sauri na danna inda ta nuna min,
Ina kaiwa kunne kuwa naji murtar Alhaji cikin wani irin gigitaccen yanayi mai bayyana azabar da yake ciki, cikin yanayin wasiyya yace.
“Aicha!”. Da sauri nace.
Ba ita bace nine Bashiru”.
Cikin wani irin numfarfashin naji yace.
“Bashiru ina take?".
“Tana gida, bari in kai mata”.
Na bashi amsa sai kuma naji yace.
“Da wuya ka isa inda take ina raye, kayi sauri dai kaje, ka ɗaukesu ku gudu, Bashiru ni bazan rayuwa, sun turani cikin ramin kogi, yanzuma ɗan zaren bakin gaba na samu na riƙe, kuma yaushe zai iya tsinkewa,
Rayyanuna kuwa na wurgashi can gefe, kazo ko ni ban rayuba Rayyern ya rayu.
Bashiru kayi maza kaje gudu dasu.
In in ka ɓoyesu ka kuma samu dama, kazo ka ɗauke Rayyern a daren nan.
Sannan ka tuna gidan da mukaje da kai a Kano, a wannan ƙaramin sashin na waje, gidan a ciki duk wasu takardun abinda na mallaka da duk wata dukiyana suna, ciki”.
A takaice dai anan ya gaya min dukkan sirrukansa tare da damƙa min amanar yaransa, ya shaidamin akwai tarin dukiyar ɗaya ware na aikin campanyn suna ciki wannan sashi, ya kuma roƙenin da in bawa su Rayyern kekkyawan ilimin boko, ya kuma cemin baya son yaransa suyi maraici.
Ya ɗaura da cemin tun ɗazu fa wanda ya turasa cikin ramin yayi nufi gidansa dan yaji yana cewa zaizo ya kashe sauran yaransa, yacemin ya goya Rayyern a jikin bishiyane a bakin gaɓar, kuma an bubbuga bishiyar amman dai baiga faɗowan Rayyern.
Ni kuwa dai-dai lokacin na iso ƙofar gidan.
Ga mamaki na sai naga gidan yanaci da wuta.
Makota duk sun fito sun tsaya cirko-cirko an rasa yadda za'ayi su shiga gidan.
Haka yasa na saki kuka ina cewa.
“Innalillahi wa innailaihi raji'un, sunbi sun kashe su”.
Dai-dai lokacin kuma naji Alhajin yayi mgn da ƙarfi a cikin wayar yace.
“Sun kashemin mata ɗan Bashiru?”.
Sai kuma naji suuuuuuu zinɗim alamun ya faɗa cikin azabebben ramin.
Wannan abun ya gigitani yasani.
Kurma ihu na nufi cikin gidan ina cewa.
“Sun kashe Alhaji da Rayyanu sannan sunzo sun bankawa gidan wuta, wayyo Adda Aicha.
Can najita, tana amsawa tana nufar ɗakin Ruƙayya tana cewa.
“Ruƙayya! Ruƙayya!! Fito keda Ramadan”.
Ina muna iso bakin ƙofar wuta ya rufe ɗakin nasu.
Ihu Adda Aicha tasa tare da juyawa ta fice daga gidan tana faɗin shike nan, sun hallaka min ahlina gaba ɗaya, mezanyi da Nigeria garin mugaye.
Daga nan ban kuma ganintaba, ban kuma jintaba.
Dai-dai lokacin kuma aka kece da ruwa kamar da bakin kwarya.
Duk da wannan ruwan wutan saida ya kara kusan awa biyu yanaci kafin ya mutu.
Washe gari da safe aka shiga ciki, toh fa nan muka samu Ruƙayya da Ramadan a sume a cikin Bathroom, bisa alamu hayakine ya sumar dasu,
hakane yasa muka tafi asibitin cikin taraba dasu.
Bayan an basu gado, ni kuwa na sake dawowa bakin gada, inata dube-dube cikin ikon Allah naga Rayyern a goye a jikin bishiya saidai a sume yake. Kuma kanshi ya fashe yanata zubda jini, har lokacin yayi wani irin fari fat alamun jininsa ya ƙare, kwancesa nayi na kaisa asibitin.
Sanin anyi gobarane yasa aka amsheshi a sibiti.
Watanmu ɗaya kafin suka samu lfy, cikin ikon Allah Sarkin Gembu shine ya ɗauki nauyin niyyar.
Alhamdulillah duk sun samu lfy, sai daifa Rayyern ya samu matsalar kwakwalwarsa ta mance baya.
Shiyasa ya taso bai iya tuna abinda ya faru dashi daga haihuwarsa zuwa shekara bakwai.
Ramadan kuma a hankali ya mance iyayensa.
Haka nayi ta zama dasu a Gembu cikin gidan Sarkin Gembu.
Harda Ruƙayya, wacce nai tunanin ita kaɗai ce zata tayani rike amanar da aka bani domin munyi neman duniya babu lbrin Adda Aicha.
Nan nace ina son muyi aure da ita, dan mu rani yaran.
Haka yasa aka ɗaura mana aure.
Daga baya muka shirya muka taho kano, koda mukaje Kano kai tsaye wannan gidan muka nufa.
Kasan cewar gidane da ya ginawa a sirri dan ko iyayensa basu saniba.
Kuma dama takardun gidan da key ɗin duk da wasu tarin takardunsa nasan inda yake ajesu.
Shiyasa na ɗauka mukaje muka zauna a ciki.
Nasa Rayyern da Ramadan a Kekkyawar makaranta, na kuma saya mana motar da nakeyi musu dukkan hidima dasu.
Ni kuwa na zama kamar mai gadin gidan Ruƙayya kuwa mai gyaran gidan da rainon, aikin da muke ne muka warewa kanmu albashi kamar yadda mukaji ake biyan masu irin aikimu da wannan kuɗin nakeyi mana komai na aiki.
Su kuwa su Rayyern inayi musu komai da dukiyar mahaifinsu. Dan ko mota dana saya dan kaisu makarantane.
Su kuwa sun taso a duniya su basu san kowaba sai mu.
Dan ko gambu bana kaisu.
Na kuma ƙi kaisu wurin dengin mahaifinsu wato gidan Kakansu Malam Mai Nasara ne sabida inaga kamar magautan zasu iya ganesu ta sanadin zuwan su biyomu su kashesu.
Gashi mukuma Allah bai bamu haihuwa ba, sai suka zame mana yayanmu.
Bana harka da kowa dan gudun kada a ganomu, na hanasu yin abota da kowa.
Saida suka girmane Sanadin karatu dole Rayyern yayi abota da Dr Sulaiman.
Ramadan kuwa har yau baida abokin ko ɗaya.
Usman PA maigadin maƙocinmu ne ya haɗani dashi da wutanmu ya ɓaci ya gyara man sanadin haka suka saba da Rayyern har ya zama PA'nsa.
Na gina su Rayyern kan ƙin yarda da kowa, shiyasa baya sakin jiki da kowa a rayuwarsa.
Baya amsa gayyatan hiran yan jarida ko ta inane.
Sunyi kekkyawan karatun likitanci, dan nasan burin mahaifinsu ne dan shima likitane, to amman yafi bawa kasuwanci himma.
Nasan idan su Rayyern suka gane Malam Mai Nasara kakansune to gaba ɗaya ko wanne asirin zai tonu.
To amman duk da haka inada niyar dole watan-wata rana zan gaya musu gsky.
Ɗan tsagaitawa yayi tare da sauƙe numfashi.
Yayinda saura kuma kab sukayi shiru.
Rayyern da Ramadan kuwa,
Hawaye kawai suke zubdawa.
Shi kuwa Abba Barrister Kabeer ya fuskata a hankali yace.
“Tun randa kazo min da batun zaka bawa Rayyern auren Jannart ka kuma gaya min sunanka, na gane tabbas kanada alaƙa da Barrister Abdulkareem Sale Dakata, domin ksunanku.
Koda na kwakkwafi Jannart bayan aure kuma na gane ɗan uwanka ne.
Yanayin yadda bada auren Jannart da yadda komai ke tafiya, da tuno kalaman Barrister Abdulkareem, na gane duk abinda kake boyewa akan Jannarr, na kuma gane akwai wani abinda ka sani a kanmu shiyasa na amince a sauƙaƙe”.
Cikin sauƙe Numfashi Dr Sajo yace.
“Barrister Kabir shaida musu”.
Cikin sanyi yace.
“A'a muji yadda akayi Alhaji Bashir ya rayuye dai tukun da yadda Hajia Aicha ta rayu”.
Jin hakane yasa Baba Mauɗo gyara zama tare da fara basu lbi
“Ni a waccar naran koda naje, cikin Gembu membila sai na samu, ashe harda su Alhaji Bala Tambari dasu Alhaji Audu Tababa da kuma Alhaji Ahmed Tinkau da Alhaji Idi Sale Dakata, da kuma Dr Lukman, da dai sauransu za'ayi zaman. Nayi mamaki domin wannan taron iya na mutanen tarabane.
Sunyi duk yadda zasuyi da in haɗa hannu dasu naƙi, wanda hakan ya tunzurasu, sukayi ta gayamin duk abinda sukaga dama.
A karshe dai da faɗa aka tashi, yayinda duk abinda mukeyi Rayyern na kan cinyarta.
Ina fita wurin Alhaji Idi yace.
Ba sai na rayuba kan inyi musu turji, yace dani da Lawyer na duk sai su ɗai-ɗai tamu.
Furucin daya bani tsoro kenan.
Saidai ban kulaba na shiga mota na kama hanyar Gembu, duk da dare yayi.
Ina tafiya Alhaji Bala Tambari ya kirani a sirrance kamar kullum shike sanar dani duk shirinsu.
Ya shaida min cewa fa, an turo mai babbar mota kan ya takani, ya kasheni ya kuma je da fetur ya ƙona min gida.
Hakan yasa na ƙara gudun mota, ga kuma hadarin da iska da akeyi.
Tafiya kaɗan kuwa nayi Baga mai babbar mota na bina, duk inda nayi sai ya bini hakan yasa na gane shi aka turo
A haka dai ya samu ya turani cikin ramin to kafin in faɗa sai na fita cikin motar lokacin daya tokareta da bishi.
Gaba ɗaya naji ciwo, hakama Rayyern to sai na cire rigata na goya Rayyern a jikin wata bishiyar dake ɗan gefe kaɗan da wacce ta tokari motata.
Na juyo zan dawo bayan Rayyern ɗinne kuma, tsantsin ya ɗebeni na tafi cikin ramin to ban faɗaba, na riƙe sirarun jijiyoyi bishiyar.
A haka ina reto na kira Bashiru nayi mishi dukkan bayanan sirri na.
Hankalina ya tashi lokacin da naji yana cewa, an bankawa gudana wuta, babu wanda na tuna sai Ramadan da Ruƙayya, dan sai nakeji Aicha zata iya tsaratar da kanta, amman su yarane.
Wannan kaɗuwanne tasa na faɗa cikin ruwan Kogi mai masifar zurfi, daga nan kuma ban sake sanin inda nakeba, sai farkawar nayi na ganni a wani babban asibiti Alhaji Bala Tambari na gefena.”
Shiru yayi alamun ya gama.
Murmushi Alhaji Bala Tambari yayi ganin yadda duk suka zuba mishi idanu alamun neman ƙarin bayani.
Zamanshi ya gyara tare da kurɓan ruwa kana yace.
“Tun da na gaya masa ana binsa nima na biyo bayansu ba tare dana gayawa munafukan banzanba da nufin in dakatar da direban babbar mota sai dai ina na makara.
Domin ina zuwa motar na faɗawa, cikin ramin shi kuwa ya wuce cikin gari,
Tashin hankali yasa na kasa tuna ya dace in bisa in tseretar da yaran.
Sai daga baya na tuna hakan.
To koda naje cikin garin sai na samu tuni an ƙona gidan.
Haka yasa kawai na wuce cikin jama'ar ina cewa a nuna min gidan Sarkin ruwa.
Nayi sava kuwa aka kaini, dan duk a tunani an rigada an gama da waɗannan kam, shiyasa nake son a ceto Alhaji Bashir da yaƙinin nasan yana da baiwar iya riƙe numfashinsa na wasu lokutan.
Koda aka haɗani da Sarkin ruwa, ce masa nayi motar ɗan uwanane ta faɗa cikin ruwa muna zuwa, dan Allah ya taimaka min.
A nan yacemin gsky baya tsammanin ɗan uwana zai rayu, domin babu wani wanda ya taɓa faɗawa cikin ramin nan ya tsira, domin ruwan bai cika gudu Bama.
Amman irin ranar ruwan zai iya gudu ya amayar da abin cikin ramin sabida yadda ake ruwa kamar da bakin kwarya.
Anan yace min, sai dai a tsammaci gawar ɗan uwan nawa, dan haka inje in sanar a matatar ruwan kiri dam.
Kana ya haɗa da kiramin Sarkin ruwan dake can ya sanar musu da gashi-gashi abinda ke faru ya ƙara da cemin.
“Sarkin Ruwan kiri dam dashi da aljanu marabarsu kaɗan, domin shi yakan iya yin kwana hamsin cikin ruwa, kuma babu matatan ruwa da baya zuwa, zai iya taimaka min sai dai zai cajeni kuɗi da yawa, jin haka yasa nace babu komai ko nawa ne zan biya.
Toh a daren na kama hanyar kiri.
Cikin ikon Allah kuwa kafin asuba na isa.
Kai tsaye bakin dam ɗin na wuce.
Allah mai yin yadda yaso a lokacin da yaso.
Kafin in isama an tsamoshi a cikin ruwan saidai baya da maraba da gawa.
Kwanana goma sha ɗaya a can, kafin muka samu ya farfaɗo daga dogon sunan da yayi,
To sai dai fa ya rasa tunaninsa.
Haka yasa a sirrance na ɗaukoshi na dawo dashi, gidana dake Gombe acan akayi ta jinyarsa har ya samu lfy, amman tunaninsa bai dawoba.
Kasan cewar yana yawan zama da Mai gadin gidama na can da yake buzune suka saba sosai.
Har da zai tafi garinsu sulaje tare,
Saida yayi shekara Goba sha uku acan amman ni ina zuwa ni kuwa naji daɗin zamansa can sabida yafi sirri zamansa acan yasa ya koyi duk yarukansu da kuma shigarsu d ta zame masa jiki.
Sai shekaru goma baya ya dawo, nan mukaci gaba da zama dashi, har tsawon shekara ashirin ba ɗaya.
Kawai ranar ya fita yaje masallaci yana dawowa mota ta bugeshi.
Bugunma bana kirkiba sai dai ya suma, tofa yana farfaɗowa ya farfaɗo da tunaninsa kwakwalwarsa ta dawo ras.
Babu abinda yake cewa sai.
Rayyanuna Ramadan ɗina, Bashiru ka kula min dasu, ka kula da maraicinsu dana Ruƙayya kada ka bar Aicha ta ƙasarsu da yarana”.
Wannan abun shi yafi komai yimin daɗi.
Daga nan aka sallamemu nan nayi masa bayanin komai.
Tofa daga ranar ta tada hankali sai munzo Kano.
Yayinda a wurin su Alhaji Idi Sale Dakata kuwa, nake cikinsu dan sanin duk ƙullinsu.
To koda muka zo Kano kai tsaye nan gidan yace muzo.
Muna zuwa kuwa ya ganka a ƙofar gidan kaida Rayyern da Ramadan bisa alamu masallaci zaku tafi.
Yana ganinku yace ga yayansa.
To kuma ni kaina na gamsu dan tsananin kamar da Rayyern keyi dashi.
Ramadan kuma da an ganta ansan Aicha ce ta haifesa.
To dole muka koma mukayi sabon shiri, haka yasa yazo muku a suffan buzu yana neman aikin gadi. Kai kana ganinsa sai kayi ta kallonsa har saida yayi ta maimaita maka mgn cikin muryar buzaye sannnan ka girgiza masa kai, da alamun jikinka na rawa a lokacin.
Rayyern kuwa sai yayi saurin cewa.
“Dan Allah Abba mu ɗaukehsi aiki ka dena buɗe mana gate dayi gadin ƙofar gida bamajin daɗin haka.”
Ni kuwa duk mgnar da kukeyi a waya nake jinta.
A karshe dai yaran ne suka dage dole ka ɗaukeshi. Shi kuwa ya rayu cikinku domin ya gane wanne yanayi kuke ciki.
Yasha zuwa wajena a boye muyi mgnar sirri.
Kai kuwa ka yarda dashi yasa har ka nemi shawarsa kan aikin campanyn, ya baka shawarar a fara ginisa kuma ka yarda, cikin hikima yasa akeyin komai cikin gaggawa.
Koda Riyyam-nsra yazo kawai cemin yayi wallahi ɗansa ne”.
Ya ƙare mgnar yana dariya.
Cikin sanyi Mamyn Rayyern ta kalli Mammyn tare da cewa.
“Dan Allah Aicha ya akayi kika bar ƙasar nan”.
Cikin sauƙe numfashi farin ciki Mammy tace.
“Lokacin da naji Abinda Bashiru ke cewa sanda gidan yaketa ƙonewa yana cewa.
An kashe Alhaji da Rayyanu sannan an kashe su Ramadan.
Daga lokacin na fita gidan to a ganina Meta rage min da Nigeria, da a mahaifiyata batason aurena da Abbansu Rayyarn wanda kasuwancine ya kaisa ƙasarmu Ethiopia har muka kulla soyyaya, kasan cewar dama mahaifina ya rasu, kuna Ni kaɗai suka haifa shiyasa Didi na batason auremu, a ƙarshe dai bada yardarta akayi aure ba, randa muka taho Nigeria tayi kuka kamar zata mutu niko son da nakewa mijina yasa na daure muka zo.
Alhamdulillah ahlinsa kab suna sona. Cikin aminci muke zama da kekkyawan zaman lfy.
Har na haifi Rayyern da Ramadan kafin mukaje Ethiopia lokacin shekaran Ramadan biyu a duniya.
Muna dawowa ne muka koma Gembu membila.
To shiyasa wannan abin na faruwa na tattara na koma ƙasata ta haihuwa kuma a lokacin inada cikin Riyyam-nsra da Zaiton har na wata huɗu.
Shi ya sani.
Naƙi in sallami iyayensa ne dan naji gaba ɗaya ƙasar na tssneta bana son komai ma ƙasar gani nake ƙasace da babu amana, a nan diganmu dake can bayan gida babanshi naje na ɗauki E password na da komai nawa, a ciki kuma nayi ta zama ba tare da sanin kowaba, har komai na tafiyana ya kammala.
Na tafi, gidan babansa kuwa duk sun shiga tashin hankali jin labarin rasuwarsa dan har can ƙaninsa Mustahpa yaje to amman dan ba'a sansaba anki a sauraresa. Dole ya dawo sukayi ta zaman makoki, amman Malam yaƙi amincewa shi cewa yake shifa Ɗansa da jikokinsa na raye, su kuwa yaransa sai dukega mutuwarce ta gigitashi.
Nima a zatona su Rayyern basa raye, shiyasa banda bin ta kan Nigeria ba sai dai ina yawan gayawa su Riyyam-nsra cewa su asalin ƴan Nigeria ne ina basu lbrin komai.
Sai ranar da naga gidajen tv'n da jaridun ƙasarmu suka rinƙa haska hoton fuskar Rayyern ne a matsayin wanda ya taimaki ƴar wani babban ƙusam gwamnati, ina ganinsa naji a jikina ɗanane, ganin sunansa ya ƙara bani ƙarfin guiwa, musamman in na duba kamarsa da Riyyam-nsra da kuma kamannin mahaifinsu, haka yasa na amince da nacin Riyyam-nsra na son zuwa.
Kana shi kuwa dake ɗan rawan kaine yana bibiyan mutanen ƙasarnan a shafukan sada zumunta.
Anan yaga Ahmad Nasir har suka saba, sai daga baya muka gane shi ɗan ƙawar babansune.
Shi yan ywansane shiyasa nace muku.
Ta ƙare mgnar tana shafa kansa.
Jannart kam har yanzu hawaye take zubdawa.
Shi kuwa Baba Mauɗo cikin fargaba yace.
“Alhaji Bala Tambari kullum tambayarka nake ina Barrister Abdulkareem Sale Dakata amman kaƙi gaya min komai a kansa yau tsawon shekara uku kenan ina tambaya, tunda kaƙi sanarmin barin in tambayi Kabiru”.
Ya kare mgnar yana fuskantar Barrister Kabeer.
Shi kuwa Alhaji Bala Tambari wani irin raunataccen kukane mai sassayan sauti ne ya subce mishi.
Shima Barrister Kabeer kukane mai sassayan sauti ya saki.
Yayinda tuni Aunty Dijat ma ta kife kanta bisa cinyarta.
Cikin tsananin tashin hankali Baba Mauɗo ya matso gaban Barrister Kabeer murya na rawa yace.
“Kabir ka tunani ko?”.
Kai kawai ya gyaɗa masa yana mai sakin shessheƙan kukan da yasa jikin Jannart fara wani rawa mai haɗe da tasowar kuka.
Shi kuwa Baba Mauɗo cikin taraddadi yace.
“Kabiru ina Barrister Abdulkareem inayake? Ina Zainab? Me ta haifa?”.
Cikin tsananin kuka Barrister Kabeer ya ɗago kansa tare da nuna masa Jannart...!
Ban samu nayi editing ba sabida zazzaɓin mura ɗaya rufeni, zakuga kurakurai da yawa, duk na san zaku kage in sha Allah.
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*
NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa