Showing 330001 words to 333000 words out of 350584 words

Chapter 111 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

dinta kuwa tuni sukayi jajur, dan ba kad’an ba sukasha tsotsa.

Jannart kuwa jin yanda ya matseta acikin bathtub din wankanne yasa ta, fashewa da wani irin kuka mai kama dana shagwab’a tare da soma tutturjewa, saboda Rayyern d’insa da taji tana gogan bayanta, Wanda har yanzu yake nuna alaman koda yaushe ashirye yake da sake komawa.

“Nidai ka k’yaleni, kabarni banaso saida na fad’a maka bacci nakeji, kabarni na tafi d’akina ni banason wannan d’akin.”

Tayi maganan tana bubbuga kirjinsa da hannayenta, Wanda hakan yasa shi sake matseta ajikinsa tare da lumshe idanunsa.
Domin ayanzun shi kadai yasan me yakeji ajikinsa.
Jinsa yake na daban kuma na musamman.

Ganin yanda take tayi masa rigimane kuma yasa, cikin lallami ya lallab’a ya gasa mata jikinta, tare kuma da bata baki yana tsaye akanta tayi wanka.
Har lokacin daya kammala nasa wankan kuwa batayi shiru ba.
Sai shagwab’a da koke koke takeyi masa.

Wannan yasa yana kammala wankan, ya nad’ota acikin towel, tare da fitowa daga toilet din.

Akan wata kujera dake gefe ya ajiyeta, kana cikin dan hanzari ya k’arasa ya yaye zanin gadon nasu, da duk ya b’aci da jini.
Wani sabon bedsheet din ya shumfud’a musu.

Duk da komai yanayinsa ne acikin dauriya, kasancewar zafin zazzab’in na k’ara shigansa.

Dawowa yayi ya d’auki Jannart din, tare da sata acikin jikinsa, Anutse ya kwantar da ita akan gadon, tare da matsawa shima ya kwanta agefenta, bayan yasa duka hannayensa biyu ya sak’alo ta jikinsa, tare da rufa musu blanket me taushi.

“Thank you Jannah.”
Ya fad’a yana me manna mata kiss akan goshinta, bayan ya lumshe idanunsa da suke cike da bacci.
Duk bayajin dadin yanayin nasa saboda fevern daya dirar masa.

Daga gefe guda kuma ga kukan Jannart din dake neman hautsuna masa kwakwalwa, saboda kasa kasa takeyi masa kukan shagwab’a, dan kamar yanda zazzab’i ya dirar masa haka ita dinma.
Sai karkarwa jikinsu keyi, duk da har yanzu suna mak’ale da juna, amma sam bacci ya kasa ziyartar idanunsu, bawai Kuma dan basa ji ba, kawai fevern ne ya hanasu sakat.

Acan b’angaren Ramadan da Riyyam kuwa, suna can d’aki batare da sunsan duk wani abu dake faruwa ba.

Musamman Ramadan dake manne da waya akunnensa, yana ta zubawa Rayhana k’orafin d’aga aurensu da akayi, Allah ya sani baiso hakan ba.
Dan ko yanzu ma gyara zaman wayar yayi akan kunnensa, tare da lumshe idanunsa cike da begen abar son nasa yace.

“Ni gaskiya banji dadin d’aga Auren nan da akayi har sai bayan Ramadan ba, ina buk’atar matata akusa dani, na k’osa Naji ki akusa dani My love, Please muyi musu tawaye ki bani had’in kai, wajen gaya musu cewar muna buk’atar junanmu anan akusa.”

Idanu Rayhana ta d’an zaro saboda jin abunda ya fad’a d’in, sanin yanda yake so da buk’atarta ne kuma yasa ta kwantar da murya, cikin tausasawa hadi da lallashi tace.

“Kayi hakuri Habibi ai bayan Ramadan din zaizo, yanzu idan mukace zamuja da maganarsu zasu ce bamu da kunya, amma nima I want....”

Kasa k’arasawa tayi saboda kunya, tare da cusa kanta acikin cinyoyinta kamar yana ganinta.

Murmushi Ramadan yayi tare da marairaicewa cike da shauk’i yace.
“Pls mana Rayhanna k’arasa kinji y’an mata na.”

Murmushin kunya Rayhanan tayi batare da ta k’arasa ba kuma suka ci gaba da hirarsu irin na masoya.

Yayinda daga can gefe kuwa Riyyam ne kwance, yana ta faman latsa wayarsa inda hankali da nutsuwarsa suka lula duniyar tiktok, tiktok dinsa yake shi kad’ai sai faman murmushi da dariya yake.
Wannan yasa sam hankalinsa baya kan Ramadan dake waya.

Har Ramadan din ya gama waya ya kwanta kuwa Riyyam nata faman shafa wayarsa, saboda live daya soma.
Bashine kuma ya kwanta ba har k’arfe 2:30 na dare.

4:30 am.

Ahankali Rayyern din ke bud’e idanunsa, Wanda gaba daya daren yaudin suka kasa samun bacci.

Idanu ya zubawa fuskar Jannart, dake fitar da numfashi ahankali, yayinda duk jikinta ya sake d’aukan zafi.

Hannunsa yasa ya shafi gefen fuskarta, cike da tausayin ta, saboda kiraye kirayen sallan Asuba da aka soma ne kuma yasa shi, d’an zare jikinsa daga nata ahankali gudun kada ya tashe ta daga baccin da takeyi.
Saidai abunda baisani ba shine Jannart din ba bacci takeyi ba.
Ta daiyi relax ne sbd bata da k’arfin da zata iya motsa Gabb’an jikinta.

Sunkuyowa yayi ahankali ya sumbaci goshinta, kana cikin rashin kuzarin da yake fama dashi ya wuce toilet.
Alwala ya d’auro, koda ya fito kuwa wata jallabiya ya zura ajikinsa, ahankali kuma cikin sand’a ya fice daga cikin dakin gudun kada ya tashi Jannart din daga bacci.

Kaitsaye masallaci ya wuce, inda yabi sahu akayi sallan asuban dashi.
Kamar koda yaushe kuwa koda aka idar da sallan, atare duk suka dawo gida, shi Baba Maud’o, ABBA, Ramadan da Kuma Riyyam nsra.

Saidai koda suka shigo cikin gidan, bai zauna acikin falon kamar yanda suka saba zama shan coffee ba, kaitsaye sama ya wuce dan yasan yabar Jannart din acikin mawuyacin Hali.

K’ofar d’akin ya bud’e ahankali tare da tura kansa ciki.
Asanyaye ya k’arasa gaban gadon tare da d’an sunkuyowa kan Jannart din, bayan yasa hannu ya kunna wutan d’akin.

“My Jannah. My Jannah.”
Yakira sunanta atausashe tare da sanya hannayensa duka biyu ya tallafo fuskarta.

Batare daya bari ta bud’e idanun nata ba kuma, murya k’asa k’asa tace.
“tashi kinji My Jannah bud’e idanunki pls.”

Wahalallen numfashi mai dumi ta fesar, tare da janye jikinta gefe, cikin yanayin wahalan da takeji, hadi da fushin da takeyi dashi murya, na kakkarwan zazzab’i had’i da kuka tace.

“Um um nidai ka k’yaleni,banaso ka sakeni, ko d’akinnan ma banaso.”
Tayi maganan hawaye suna me gangarowa daga kan fuskarta.

Wanda ganin hakan yasa Rayyern marairaice fuskarsa, Tabbas yasan cewar bai kyautawa Jannart din ba, amma shima bayin kansa bane, ita dince tazo ta daban.

“Kiyi hakuri Jannahta nine fa, Naan Hamma Nanun ki, taso muje ko kiyi wanka saina baki magani kisha.”

“Ni ka sakeni ka k’yaleni zafi nakeji, wayyyo Allah na Mammyna Nanu ya jimin ciwo.”
Ta f’ada agigice tana me yayyarfa hannunta, saboda yanda Rayyern din ya soma kok’arin d’agota wanda hakan yasa ta jin wani irin zafi a k’asanta.

Turjewan da takeyi d’inne kuma yasa idanun Rayyern sauk’a akan white bedsheet din dake kan gadon, Wanda duk ya b’aci da jini.

Wani irin bugawa kirjinsa yayi wanda har saida hakan yasan yashi zaro idanunsa waje, cike da tsoro had’i da tashin hankali ya zaburo, tare dasa hannnu ya d’ago bedsheet din.

“Jini! Janna jini ajikin bedsheet, Innalillahi Allah yasa kada abunda nayi ya zamo sanadiyar cikina, me kikeji yanzu ya kikejin cikinki? My Jannah fad’amin dan Allah, fad’amin cewar cikina na nan babu abunda ya sameshi, Wayyo Jannah zo in dubaki please..”

Abunda yake fad’a kenan cikin rud’u had’i da fargaba, sannan jikinsa na rawa ya soma kokarin kamo Jannart din.
Wacce ta soma fusgewa tare da turjewa.
Lokaci daya kuma tasa masa kuka.

“Nidai banaso ka kiranin Mamy na, kada ka sakemin komai, Mamy!!!”
Ta fad’a da yanayin d’aga murya.

Wanda hakan yasa Rayyern sake rud’ewa, da sauri kuma ya nufi hanyar fita daga d’akin dan k’iran Mamyn Kamar yanda ta buk’ata.

Tabbas ya rud’e wanda yasa tun kafun ya kaiga sauk’owa k’asan yake k’iran sunan Mamy.

“Mamy! Mamy!!.”
Yake fad’a yana me tsallake steps da bibbiyu.
Inda tuni kuwa sautin muryarsa ta karad’e duk falon.
Wanda hakan yasa Mammy da Mamyn wanda suke zaune a falon, tasowa arazane sukayi kanshi.

“Rayyern lafiya kuwa?.”
Suka had’a baki dukansu wajen fad’an hakan, tare da zubawa Rayyern din idanu.

Fuskarsa dake d’auke da damuwa ya kwab’e, still cikin rashin nutsuwa yace.

“Mamy Jannart, kizo muje Please Mamy Jannart ce.”

Yayi maganan yana me kamo hannun Mamyn, batare daya jira komai ba kuma, ya soma jan hannun Mamyn zuwa sama.

Wanda hakan yasa Mammy dake tsaye sakin ajiyar zuciya, tare da komawa ta zauna aranta take mamakin hali irin na d’an nata.
Dama tasan dole za’ayi hakan Tabbas, domin ihun Jannart din na jiya kawai da taji, tasan to baza’a wanye lafiya ba.

Mamy kuwa hankali atashe tabi bayan Rayyern, zuciyarta cike da fargaba kan abunda ya samu Jannart d’in.

Wannan dalilin yasa koda suka shiga cikin d’akin da sauri ta karasa wajen gadon, hankali ad’an tashe tace.

“Jannart.”

Jin muryar Mamy yasa Jannart din juyowa, tare da fashewa da kuka, had’i da kamo hannun Mamyn ta rike Acikin nata.

“Mamy!”
Ta fada cikin kuka.

Wanda hakan yasa Mamyn jawota ta d’aura kan Jannart din akan cinyarta.
Cikin tausasa murya tace.

“Na’am Jannart, yi shiru ki daina kuka kinji.”

Mamyn ta fad’a tana me shafa bayan Jannart din a hankali.

Yayinda Rayyern kuwa dake tsaye, matsowa yayi kusa da Mamyn cikin damuwa da rashin nutsuwa yace.

“Mamy cikina, inajin tsoron kada wani abune ya sameshi, kar ace shine ya zube Mamy dan Allah muje asibiti.”

Harara Mamyn ta watsa masa tare da kawar da kanta gefe, “wai cikina, hmmm sai kace ajikinsa cikin yake.”
Mamyn ta fad’i haka acikin zuciyarta.

Tare da d’ago Jannart din cikin kulawa hadi da tausasawa tace.

“Yi hakuri kinji Jannart daina kukan, muje toilet kiyi wanka, nasan hakan zaisa ki d’anji dama dama.”

“yauwa Mamy bari na had’a mata ruwan wanka, My Janna bari na had’a miki ruwan wanka kinji taso muje.”
Rayyern yayi carab ya fad’i hakan, batare kuma daya damu da kasancewar Mamy awajen ba, ya mik’o hannayensa da niyan d’aukan Jannart din.

Wacce tayi saurin mak’ale kafad’unta tare da soma yayyarfa hannayenta.
Alaman bazata je garesa ba.

“Sannu Jannart ki nutsu kinji, ki bari ya taimaka miki kiyi wanka, maza je ka had’a mata ruwan d’umi.”

Mamy ta fad’a tana me gyarawa Jannart din dogon gashinta wanda duk ya warwatse.

Rayyern kuwa jin abunda Mamyn ta fad’ane, yasa cikin hanzari ya wuce toilet, ruwan d’umi ya had’a kamar yanda Mamyn ta buk’ata.
Yana fitowa kuwa ya karaso wajen gadon tare da kamo hannun Jannart din.

“Muje please.”
Ya fada yana me marairaice fuska tare da matsowa gab da ita dan ya dauketa.

Ido ta lumshe jin ya ɗauke ta ya wuce Bathroom da ita.
Ita kuwa Mamy, jin dake jikin bedshit ɗin ta zubawa ido cike da tsoro.
Haka yasa da sauri ta nufi waje.

Shi kuwa Rayyern cikin tsoron ya taimaka mata, tayi wonka bayan ta wonke jikinta da ruwan ɗimin tai wonka tsarki,
Kana suka fito.

Wata tattausan riga ya zaro a durowarsa ɗaya daga cikin Rigunan da ya saya mata randa zasu dawo. Zira mata rigar tayi tare dasa mata hijabi kana ya shimfiɗa mata sallaya.
Ita kuwa Jannart cikin yanayin rawan sanyin zazzaɓin daya rufeta ta kabbarta sallan.

Gefenta ya zauna cikin rawan sanyin da zazzaɓin ya zuba mishin yana mai dannawa Dr Sulaiman kira.

Mamy ce ta shigo tare da sallama a bakinta, dai-dai lokacin kuma ta idar da salla.
Addu'a tayi tare da shafawa kana ta kalli Mamy data miƙa mata hannu tana cewa.
“Taho, taso ko Janna mu tafi asibiti”.
Ba musu ta kama hannun Mamy domin har yanzu sawunta rawa sukeyi, kuma jikinta ba ƙarfi, ga sukan zazzaɓi.

Da sauri yabi bayansu tare da cewa.
“Mamy bazamu kira azo a dubata a gidaba, naga tafiyar na bata wuya.”

Cikin yanayin kula Mamy ta kalli Jannart ɗin da yunwa, da zaƙular Naan da zazzabin da kukan da ta kwanayi yasata jiri da ganin duhu.
“To ɗagata mana, Ni nafi son muje asibiti, sabida jinin nan yana ban tsoro”.
Kafinma ta rufe bakinta, ya ɗagata, yayi gaba.

Ba kowa a falon kasa.
Haka yasa Jannart jin sauƙin fitinenneyar kunyar data rufeta.

A baya ya kwantar da ita kana Mamy ta zauna gaba a gefensa kana yana suka tafi.

Zaune suke gaban Dr Khaitar Hamza Ibrahim.
Tanayi musu bayani Mamy ta ƙalla cikin kulawa tace.
“Ba komai Mamy cikin yana nan, lfy lau, babu abinda ya sameshi, kamar yadda kuka zata, kuma nima kaina na zata, to amman kinsan dama ana iya fuskantar haka a dararen forko amare, musamman, in akaje musu da karfi”.

Wani irin munafukin kallo Dr Sulaiman yakeyiwa Rayyern tare da danne wata azabebbiyar dariyar dake taso masa.

Ita kuwa Mamy cikin sauke numfashi da kunya tace.
“Toh yanzu dai babu matsala ko?”.


“Eh babu wata matsala, yanzu ruwan nan, na ƙare wa zaku, tafi gida.
Dan zazzaɓin ma ya sauƙa”.
Cikin sauke numfashi Mamy tace.
“Toh Alhamdulillah”. Ta kare mgnar tana mai miƙewa ta fita.
Itama Dr Khairat bin bayanta tayi.


Suna fita kuwa Dr Sulaiman ya tuntsure da dariya, yanayi yana nuna Dr Rayyern ɗin cikin dariyar da yakeyi harda hawaye yace.
“Wai kai rawan me jikinka yakeyi ne!?”.
Harara Rayyern ɗin ya watsa mishi kana cikin muryar zazzaɓi yace.
“Banza dariyar me kakeyi kamar wani zautacce. Kayi min allura zazzaɓi nakeji”.

Cikin tsaida dariyar Dr Sulaiman yace.
“Uhummm yoh ai dole kayi zazzaɓi, tunda ka iya aikin riga malam masallaci ace ayi mutum kamar maye, duk abinda kayi sai ka samar da sakamako fiye da yadda akeso.
Kaiwa yar mutane ciki tun kafin, amarcewa.
Kana kazo ka bita da ƙarfi, kana son zazzago ɗan mu ka cucemu kai mana asarar ɗan baiwa”.
Ya ƙare mgnar yana haɗa ruwan allurar da zai masa.
Shi dai Rayyern fuska ya haɗe dan baida isasshen ƙarfin faɗa.
Haka yayi masa allurar yana tayi masa tsiya.

Mammy kuwa a gida, ita da Zaiton ne suka shiga kitchen.

Ƙarfe tara dai-dai suka dawo gida.
Alhamdulillah yanzu da ƙafarta ta shigo gida.
Domin taji sauki sosai.
A falon suka zauna baki ɗayansu.

Ganin haka yasa Zaiton kwaso duk kayan abincin da suka haɗa, musu da nufin kaiwa asibitin, ta kawosu tsakiyar falon, ta ajiye tana kallon Jannart dake kwance bisa kujera.
“Sannu my Aunty ya jikin”.
Ta faɗa cikin kulawa.
“Alhamdulillah”.
Jannart ɗin ta amsa a sanyaye dan bacci takeji.
Mammy kuwa jawo kwandon tayi gabanta.

Mamy kuwa cikin kulawa ta kamo hannunta tare da cewa.
“Tashi ki zauna kici abinci kisha, maganin sai muje ki kwanta”.
To tace kana ta yunƙura ta tashi zaune, ɗan ita kanta tasan tana jin yunwa.

Ramadan ne da Riyyam-nsra suka fito, daga side ɗin Riyyam-nsra ɗin.
Cikin fuskar dake nuna damuwa, da fushi da kowama, Ramadan ya gaidasu.
Riyyam-nsra kuwa cikin kumshe ido ya gaidasu.
Yayinda Rayyern kuwa ya zuba masa, idanu, yana nazartan yaron da kyau.
Mammy kuwa zazzafan ferfesun jan naman da yaji citta da yaji, like na masu jego dai.
Ta zubawa Jannart, tare da miƙa wa Mamy ta ajiye mata shi gabanta.
A hankali ta haɗi yawu sabida daddaɗan ƙamshin data zuƙa, Mammy kuwa cup mai ɗan girma, ta haɗa mata tea mai kauri da zafi, ta miƙa Mamy tare da cewa.
“Amshi ki bata, Jannart maza ki kafa kanki, ki shanye shi tas, ki bani kofin.
Zakiji ɗumi, hanjinki zai ware ki samu kici abinci da kyau”.
Hannu tasa ta amsa tare da gyaɗa kai.
Sai kuma ta riƙe cup ɗin tana ganin yadda yake zuba tiriri.
“Jannert kisha da sauri ba zafi”.
Mammyn ta kuma cewa.
Haka yasa, a hankali ta kai kofin bakinta.
Ido ta lumshe jin zafin dai-da misali ne, haka yasa ta kafa kai.
Ta shanye shi cikin bin umarni ta miƙawa Mammy kofin.
Tare dayin sassayan gyatsa.
Sai kuma zufa ta yanko mata.
Ita kuwa Mammy a cup ɗin ta kuma sake haɗa wani tea ɗin. Ta miƙa wa Rayyern da ya tsare Riyyam-nsra da kallo.
Shi kuwa kuwa Riyyam-nsra wayarsa yake lallatsawa.
Amsar cup ɗin yayi tare da cewa.
“Nagode Mammyna”.
Murmushi tayi cike da jin dadin ganin ta tsakiyar ahlinta.

Ita kuwa Mamy ƙara turawa Jannart plate ɗin zazzafan ferfesun tayi tare da cewa.
“Bacci fa kikegi kici muje ki kwanta”.
Kai ta gyaɗa, kana a hankali ta fara ci, tana tsoron kada ya sata amai, sai dai cikin ikon Allah sai taji babu aman haka yasa ta gyara zamanta.

Zaiton sauran wanda ta jera musu kan dinning table ta kwaso ta dawo dasu tsakiyar falon.
Ta ajiye musu tare da sawa Ramadan da Riyyam-nsra.

Shi kuwa Rayyern yana shanye tea ɗin ya miƙe a haura sama kujera ya kwanta yana mai lumshe idanunsa, tare da tafiya nazarin abinda ya dace yayi a kan Riyyam-nsra.

A hankali tayi gyatsa tare da cewa.
“Alhamdulillah Mammy”.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“To yayi kyau ɗiyata Allah ya ƙara sauƙi ko”.
Amin tace a hankali.

Mamy kuwa magunguna ta bata, bayan ta shane tace, to tashi ki haura sama kije ki kwanta kinji kiyi baccinki”.
Cikin kasala tace to. Kana ta miƙe ta haura saman.

A tsakiyar falon ta tsaya, tare da kallon ƙofofin ɗakunan duka biyu.
A hankali ta nufi, ɗaya ɗakin wanda da Ramadan ne a ciki.

Tura ƙofar tayi ta shiga, sabida sanin yanzu Ramadan ya koma ƙasa.

“Wow Masha Allah”. Tace lokacin data shiga ɗakin da yayi masifar tafiya da nitsuwarta sabida tsarin na musamman da akayi masa.
A hankali ta maida ƙofar ta rufe tare da murza key tana cewa.
“Bari ma in rufe nasan Naan yanzu zaizo ya takurani”.
Ta ƙare mgnar tana kwanciya bisa gadon tare da jawo blanket ta rufe jikinta.
Tana mai yin hamma, aiko cikin sakanni bacci tayi awon gaba da ita.

A falon kuwa, tana tafiya Abba da Baba Mauɗo suka shigo.
A nan a tsakiyar falon sukayi breakfast.

Bayan sun gama ne Ramadan ya kalli Abba tare da cewa.
“Abba bari muje mu gaida malam Mainasara”.
Yayi mgnar cikin yaƙin in ya kai ƙorafinsa shima zai samu ayi masa aure sa ya huta.
Murmushi Baba Mauɗo yayi cikin gano manufarsa yace.
“Kada ma kaje in dai akan batun aurenka ne, domin mun rigada mun gama mgn dashi, in ma kaga abinda Yayanku yayine”.
Cikin kwaɓe fuskarsa ya rusuna gaban Abbansa dakeyi dariya yace.
“Dan Allah Abba kuyi hakuri, aja ayi batun auren nan, wallahi tallahi a matse nak..”
Sai kuma yayi shiru ganin kallon da Abba yayi masa.
Kawai sai ga hawaye shar-shar na zuba cikin hakura yace.
“Ba komai Abba Allah ya kaimu bayan sallan”.
Amin sukace baki ɗayansu.
Shi kuwa Ramadan muƙewa yayi ya nufi ɗakinsa.
Da sauri Riyyam-nsra ya miƙe, sai ya kuma komawa ya zauna.
Jin Rayyern na cewa.
“Kai Riyyam-nsra zauna”.

Tashi zaune yayi, tare da miƙa masa hannunsa tare da cewa.
“Bani woyoyinka”.
Da sauri Riyyam-nsra ɗin ya kalleshi cike da yanayin tsarguwa.
“Nace ka bani woyoyinka”.
Rayyern ya faɗa a daƙile
Cikin yanayin tsoro yace.
“Hamma Rayyern me zakayi dasu, ba cajima”.
Ya ƙare mgnar cikin son waskewa.
Abba da Baba Mauɗo kuwo, ido suka zuba musu, Zaiton kuwa da sauri tace.
“Ai bashi da gsky, domin sam baya taɓa yarda ya bawa wani wayarsa”.
A hatsale Riyyam-nsra ya harareta tare da cewa.
“Toh munafuka waya kasa dake?”.
Cikin tsaresa da idanu.
Mammy tace.
“Kada ka sake cemata muna fuka, ka bada wayar kawai akace".
Cikin tura baki yayi ƙasa da kai.
Shi kuwa Rayyern cikin lumshe gajiyayyun idanunsa dake cike da bacci yace.
“Ka bani su, Zaiton shiga ki ɗauko min system nashi”.
Aifa da sauri ta miƙa tana cewa.
“Gata nan ma, kusa dashi”.
Hannunta Riyyam-nsra ya buge yana mai haɗa zufa yace.
“Hamma Rayyern ba caji fa”.
Da sauri yayi shiru, kuma tare da miƙa masa woyoyinsa duka biyu da system ɗin sa, sabida tsawan da Baba Mauɗo ya daka masa.

Komawa yayi ya zauna, gaba ɗaya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login