Showing 108001 words to 111000 words out of 350584 words

Chapter 37 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

ko me ta keyi kice mata ta bari, injini tazo mu yi breakfast.”

“To.” Momyn tace, tare da juyawa tasake nufan dakin Jannart din.

Tana zuwa ta tura kofar, but still Jannart bata ciki, da d’an mamaki Momy ta karasa jikin kofar toilet din, tare da kasa kumnenta.
Waiko zataji karar ruwa, saidai bataji komai ba, hakan yasa Momyn ta tura kofar tana me kiran sunan Jannart.

Saidai meye, idanunta ba abunda suka gane mata, domin kuwa Jannart bata cikin toilet din.

Mamaki ne ya kama Momyn, saboda Sam bata taba tunanin Jannart bata cikin toilet din ba.

Juyawa tayi cikin sauri ya dawo falo.


“Alhaji Jannart fa batanan, na duba bata dakinta kuma bata bayan gida.”

Cak Alhaji Idi Sale Dakata yatsaida duk wani abu da yakeyi, cikin yanayin mamaki had’i da razana yace.

“Bangane mekike cewa ba, wannan wani irin maganar banza ce, tayaya zakice bata dakinta kuma bata bayan gida, wannan gashi anan dinma batanan, To ko tana dakinki ne?”

Kai Momy ta girgiza da sauri, tare da cewa.

“A'a wallahi bata dakina, tun Safe ma banga sauk’owarta ba, zaiyi wahala ace ma tana dakina.”

“Kije ki duba ta yanzu.”

Dadyn ya fada cikin bacin rai.

Hakan yasa da sauri Momyn ta juya zuwa dakinta, kamar yanda ta zata kuwa hakanne, domin Jannart bata cikin dakinta.

Dawowa falon ta sakeyi, tare da Kallon Daddyn tace.

“Alhaji Jannart fa bata dakina.”

Idanu Daddyn ya zazzaro waje, Abdull kuwa da mamamki yace.

“Ha’a To Ina Aunty Jannart ta shiga ita da yawo ma bayinsa takeyi ba, amma bari na duba compound ko Garden ko tafita shan iska.”

Yana gama fadin hakan ya mik’e ya fita.

Kaitsaye garden dinsu ya nufa amma baiganta ba, hakan yasa ya dawo, fuskarsa dauke da damuwa yace.

“Daddy banganta ba.”

Kwafa Junaid yayi, tare dasa hannayensa a aljihun wandonsa, cikin bakar muguntan dake cinsa yace.

“Nifa Tunjiya na fada muku banganta ba, maybe yawon iskancinta ma ta tafi, dama ai ta saba tafiya kwanan gida.
Rijiyace kowanni dan iska yana iya zuwa ya zira gugansa yaja ruwa son ransa.”

Idanu Momy ta rumtse saboda har acikin zuciyarta bataji dadin bakar maganar da Junaid din ya fada akan Jannart d’in ba.

Daddy kuwa Wayarsa ya zaro daga cikin aljihun rigarsa, tare da lalub’o numbern Jannart din ya danna mata kira.

The first time akace masa wayan nata, is switch off, da Mamaki Daddy ya sake dialing airtel number dinta, still switch off, wani irin bugawa yaji kirjinsa yayi, cikin sauri yace.

“Junaid je maza ka duba side dina, watakila ko taje gaisheni ne.”

Juyawa Junaid din yayi, Inda kaitsaye ya nufi side din Daddyn, Koda ya karasa baiganta ba, har cikin bedroom na Dad din ya shiga amma babu ko alamarta.

Dawowa yayi yana ta kwafa, yace baiganta ba.

Mik’ewa tsaye Daddy yayi, cikin tsananin tashin hankali ya nufi kofar fita daga falon, batare kuma daya lura ba har tuntub’e yake.

Kaitsaye compound din gidan ya fito, tun daga nesa kuma ya soma k’walla kira.

“Ado! Ado!!”

Baba Ado dake bakin gate wurin Ashiru ne, Jin irin kiran da Alhajin keyi masa ne kuma yasashi tahowa da sauri.

Kallonsa Alhaji Idi Sale Dakata’n yayi, kana cikin dan daga murya yace.

“Jannart ta fita ne?”

Kai Baba Ado ya girgiza kana cikin girmamawa yace.

“A’a Alhaji Jannart bata fita ba, kwata kwata tunsafe Ina zaune anan banga wani ma daya fita acikin gidan nan ba.”

Shiru Daddyn yayi, na yan wasu mintuna, kamar kuma Wanda aka tsikara yasoma k’wala k’iran Guards.

Su kuwa k’attin banzan ma sai yanzu suka tashi daga nannauyan baccin daya daukesu.

Jin kiran da Ogan nasu keyi musu ne kuma, yasa cikin sauri duk suka k’araso.

Kallonsu Daddyn yayi tsab cikin hade fuska yace.

“Ina Jannart, dawa ta fita acikin ku?.”

Kai suka girgiza dukansu, kana suka had’a baki wajen cewa.

“A’a bamuga Jannart ba, mu yanzu ma tashinmu wata kila tana cikin gida.”

“Wani irin cikin gida kuma, bayan babu Inda ban duba batanan, maza ku zagaye duka gidan nan ko zaku ganta.”
Dadyn ya fada cikin bacin rai.

Nan take kuwa guard din suka bazu ako ina dake cikin gidan, amma ko alamar Jannart basu gani ba.

Hankalin Daddy yayi masifar tashi, musamman daya sake kiran wayanta yaji akashe.

Haka ya dawo falon afujajan, Yayinda Momy kuwa ta kasa zaune ta kasa tsaye, saboda abune kaman wasa amma yana neman Zamowa gaskiya.

Kallon Daddyn tayi, tare da Daukar wayarta tace.

“Bari na kira Barrister Kabir.”

Dialing number’n Barrister Kabir din tayi, bugu hudu kuwa Barrister Kabir ya dauka.

Bayan sun gaisa da Momynne kuma, cikin tashin hankali tace.

“Barrister bamuga Jannart bafa, munnemeta sama da kasa acikin gidan nan amma bamu sameta ba, munkira wayarta kuma akashe, Kodai tazo wajenka ne?”

Daga can b’angaren Barrister Kabir ya mik’e tsaye tare da daga muryarsa cikin nuna tashin hankali yace.

“What!! Wannan Wace irin magana ce, Ba’a ga Jannart ba, annemeta anrasa? Ita kudi ce da za’ace annemeta anratsa? Ko kuma ita din wayar hannu ce da za’ace an nemeta anrasa.”

Ya k’are maganar cikin yanayin tsawan, dake nuni da bazai iya tolerating nonsense akan Jannart ba.

Momy kuwa cikin tashin hankali tace.

“Wallahi Barrister bamuganta ba, body guards dinta da masu gadi duk sunce basu ganta ba.”

“Gani nan zuwa.” Barrister Kabir din ya fada agigice.

Tare da kashe wayar.

Bayan ya kashe wayartasa ne kuma ya saki wani irin murmushi tare da juyowa ya kalli Aunty Dijat dake zaune.

“Sakarkaru sai yanzu suka lura da cewar Jannart bata gidan, hmmm da sannu munafukan boye zasu fito fili, kowa kuma zai girbi abunda ya Shuka.”

Dariya Aunty Dijat tayi.
Yayinda shikuwa ya dauki key din motarsa ya fice.

Kaitsaye gidansu Jannart din ya nufa.

Yana isa gidan kuwa ko gama dai-dai-ta parking baiyi ba, ya fito.

Inda Daddy kuwa ke tsaye, gaba daya hankalinsa atashe yake sai safa da marwa yake, Yayinda kuma yake ta balbale guard din da fad’a, tankar zai hausu da duka, sai cewa yake, su je su nemo Jannart duk inda ta shiga ta fita.

Barrister Kabir kuwa agigice ya karaso, hankalinsa amatuk’ar tashe yace.

“Yaya ina Jannart? Waya dauke mana Jannart? Ina kuka kaita?.”

Kai Alhaji Idi Sale Dakata ya girgiza, cikin tsananin damuwar da yake ciki yace.

“Bansani ba Kabir, bansan Ina Jannart tayi ba, munduba ko ina amma babu ita babu alamanta.”

Hannu Barrister Kabir ya daura akai, lokaci daya kuma ya jujjuya idanunsa sukayi jajur, ahaukace ya soma neman Jannart din, tare kuma da soma zagaye cikin gidan yana leka har cikin followers, sunan Jannart din kawai yake kira da iyaka karfinsa.

Daddy kuwa bala’i da tashin hankali ne ke cinsa, cikin zafin nama kuma ya kalli Ashiru.

Afusace yace.

“Ashiru Ina Jannart waya bude mata kofa ta fita, ka fadamin nace ko kuma yanzu nasa bindiga na harbe kanka.”

Yakare maganar atsawace tare dasa hannu kuma ya dauke Ashirun da lafiyayyen Mari.

Kai Ashiru ya girgiza, cikin shanye zafin marin yace.

“Alhaji banganta ba, tun jiya gidannan akulle yake, gaba daya jiyama kowa ya sani bataje aiki ba, tunjiya bata fito ba, ga guards dinta nan suma shaidane.”

Sake hasala Daddyn yayi, Wanda hakan yasa ya sake gallawa Ashiru mari, tare da juyowa ya soma balbale Body guards din.

Cikin fushi yake cewa.

“Aikin banza k’attin banza kawai, angaya muku ahaka kawai na daukeku aiki ne, sokaye kun kwanta bacci sai kace matattu, yan iska kusan duk inda zaku ku nemomin y’ata.”

Barrister Kabir kuwa, zuwa yanzu har muryarsa ta Dishe, saboda yanda yake ta k’wala kiran Jannart.

Gaba daya lokaci daya jikinsa har karkarwa yakeyi, hankalinsa ya matukar tashi, inda yake reaction tankar da gasken gaske shima baisan inda Jannart din take ba.

Cikin kuma tashin hankalin daya nuna yana ciki ne kaitsaye ya nufi dakin Jannart din.

Yana shiga kuwa ya soma wargaza komai dake cikin d’akin, ananne fa kuma idanunsa suka sauka akan wayarta.

Da sauri ya dauki wayar dake kashe ya kunna, batare ma daya jira wayar ta karasa kawowaba ya dawo cikin falon, inda dukansu ke tsaye, cikin kuwa harda Junaid dake zukan shisha.

Wayar nata na kawowa Barrister Kabir ya shiga cikin dialing call dinta.

Aikuwa last sunan wanda tayi waya dashi Ne ya bayyana.

“Yah Junaid”

Idanu Barrister Kabir din ya zazzaro cikin matukar hasala, kuwa ya karasa cikin falon, batare da wata wata ba, ya Ware yatsunsa biyar ya zabgawa Junaid zazzafan Mari.

Tare kuma da juyawa afuce ya nunawa Dady screen din wayar Jannart din.

Cikin tsananin fushi yace

“Ba gashi ba, shine last mutum din da tayi magana dashi awaya, koma meye shi yasan inda take, Ina ya kaita? Yaya ka tambayeshi Ina ya kaita nace!!!!!!”.

Barrister Kabir din ya fada amatuk’ar tsawa ce, tsawan kuma daya saka hantar cikinsu kadawa.

Shi kuwa Barrister Kabir kuwa cikin fushi Ya...!





*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*

NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.

Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.


Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.

Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA)*

By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: Ya shak’o wuyan Junaid din, ransa amatukar b’ace, cikin kuma son d’and’anawa Junaid din thesame azabar da yake ganawa Jannart yace.

“Ina kakai Jannart! Kafadamin Ina kakaita, kasan inda take tabbas, ba kuma abunda bak’ar zuciyarka bazata iya sawa ka aikata ba, kafadamin Ina ka kai mana Jannart!!!?”

Barrister Kabir din ya k’are maganan cikin tsawa sosai.
Tare da sake makure wuyan Junaid.

Junaid kuwa idanunsa ya Dan zaro cike da mamaki yace.

“Wai Abba mekakeson fad’ane? Ni ban San inda Jannart take ba, ba kuma nina d’auketa ba, na d’auketa ma nakaita Ina, watakila tanacan ta tafi yawon banz......”

Wani irin wawan mari Barrister Kabir din ya zabgawa Junaid din akan fuskar sa, cikin tsananin b’acin rai da hasala, ya kuma sake zabga masa wani marin, wanda har saida hakan yasa fuskarJunaid din tayi jajur mgnar da yake son fitarwa kan Jannart ta makale, idanunsa ya zazzaro lokaci daya tare da somayin huci.

Barrister Kabir kuwa ji yake Kamar ya rufe Junaid din da duka, ransa yakai kololuwa wajen b’aci da irin mugayen furucin da Junaid din ka jefar Jannart dasu.
Cikin fad’a sosai ya juyo ga Daddy dake tsaye yace.

“Yaya ka fad’awa Junaid na bashi nanda anjima yaje duk inda ya kaita ya daukota, ni nasani shine ya sace ta, domin kuwa shine last mutumin daya kirata awaya.
Uban meya gaya mata a wayan?
sannan meye dalilinsa na kiranta awaya?
Shi ya sace ta, saboda ya cika banzan burinsa na dabbanci akanta, komai zaiyi kuma bakayi masa magana, gashi nan kaga illar da hakan ya jawo ko Yaya?, gashi nan ya saceta ya rabamu da ita, ya kaita inda zai cutar da ita.
Yaya kana mance Jannart marainiyace amma ya maida cutar da ita tamkar abinci da ruwan shansa, Allah ya wadaran hali irin naka Junaid.”

Barrister Kabir din ya kare maganar cikin muryar kukan daya zo masa”.

Momy da Abdull dake tsaye agefe kuwa, gaba dayansu kuka suka saka, saboda.
Sunsan cewa tabbas Junaid din zai iya aikata hakan, ballema jiyan Momy da kunnuwanta taji yana cewa saiya cika burinsa akan Jannart din.

Daddy kuwa ransa Idan yakai dubu to yayi masifar b’aci, akaron farko kuma cikin fushi, ya dawo da kallonsa ga Junaid, tare kuma da ta sowa ya nufi kan Junaid din.

“Ina kakaita Junaid, Ina kakai min Jannart?
Ka fad’amin Ina kakaita? Junaid me zakayi da ita.” Daddyn ya tambayesa atsawace.

Abunda Bai tab’ayiwa Junaid din ba kenan, musamman akan Jannart.

Ganin hakanne kuma yasa Junaid din soma girgiza kansa, cikin mamakin tuhuman da sukeyi Mishi yace.

“Wallahi Allah Daddy bani na dauketa ba, bansan inda take ba, bani na sace ta ba.”

Cikin nuna ɓacin rai a fili Barrister Kabir dake tsaye.
Cikin rufe idaunsa da kuma mance alak’ae dake tsakaninsu yace.
“Nabaka nan da awa 2 Junaid, Lallai-Lallai kanemomin Jannart, duk inda ka kaita, kaje ka daukota Idan kaki kuma nida kai bibbiyu, wallahi-wallahi saikayi dana sanin sace marainiyar Allah da kayi.”

Sake dawo da kallonsa ga Daddy yayi, kana cikin tafasar zuciyar dake bayyana zai iya aikata komai akan b’atan Jannart din yace.

“Yaya kasa baki kasake tuna masa, awa 2 na basa ya fito da ita daga inda ya b’oyeta, sannan yanzu zan.
Kaiwa y’an sanda report, bayan haka kuma zan zagaya cikin duk wani asibiti da nasan yana cikin garin nan, dole ayau asamo inda Jannart take.”

Yana gama fad’an haka ya juya kaitsaye ya nufi hanyar fita daga gidan.

Koda yazo bakin gate harara ya watsawa Ashiru, kana cikin takaici yace.

“Shashasha kana nan tsaye abakin gate Koda yaushe, amma ka kasa sanin fita da shigan mutane sakaran banza kawai.”

Ya Kai karshen maganan nasa yana me bankad’e Ashiru’n, Cikin pretending yasakai ya fice daga Cikin gidan.

Daddy kuwa zuwa yanzu saboda tsananin bakinciki, da takaici da kuma Tarin bacin rai, jikinsa har rawa ya somayi yayinda yake jin, tamkar yasaka hannayensa aka ya kurma ihu, saboda b’atan Jannart din.

Sanin bashi da wata makamane kuma yasa shi, soma balbale guards din, Jannart din.

Cikin fushi hadi da bala’in dake cinsa yace.

“Bantab’a nadaman ajiyeku
Acikin gidana ba sai yau, k’attin banza k’attin wofi kafuran arnan da basa sallah, tayaya ma za’ace yarinyar da nake biyanku mak’udan kud’i duk wata akanta, za’a nemeta a rasa, ashema k’attin wofi dana banza na tara, lusarai way’anda basu da aiki sai ci da kwanciya, ku fita ku barmin gidana yanzu basai anjima ba, dukka na sallameku, kada na sake.
Ganin Koda mummunar fuskar daya daga cikinku ne, ku fitamin agida.”

Daddyn ya kare maganan cikin bacin rai.
Dan har yanajin tamkar ya rufe guards din da duka.

Sukuwa k’attin banzan, sun matukar ji haushin zagin da Alhajin yayi musu, aso da niyarsu kuma shine su tanka masa, amma kuma saidai tuna cewar zai iyasa a dauresu ne, yasa basu tanka masa ba, sad’ab-sad’ab haka suka kwashe komatsansu suka fice daga cikin gidan.

Junaid kuwa zaman dirshan yayi, yana Mejin wani irin tafasar zuciya, saboda alluran nasa ta motsa, sosai matukan da Barrister Kabir ya sharara masa suka tsaya masa arai.
Lallai Barrister Kabir din yayi sa’a, kasancewar shi kanin mahaifinsa, domin yau da ace wanine daban Yayi masa hakan ba Barrister din ba, yayi rantsuwa bindiga zaisa ya harbe mutum.

Acan b’angaren Barrister Kabir din kuwa, yana fita daga cikin gidan, motarsa da yayi parking awaje ya shiga, bayan yayiwa motar key ne kuma, ya saki wani irin Murmushi, mai kama da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login