Showing 69001 words to 72000 words out of 350584 words
bacci, an daura mata drip ajikinta.
Karasowa Cikin dakin Abba Kabir din yayi, cikin tsananin kulawa hadi da tausayawa ya sa hannu ya shafi goshin Jannart din dake bacci Cikin kwanciyar hankali.
“Insha Allah Jannart farinciki yana nan zuwa acikin rayuwarki, Domin ba zaki tabbata acikin kunci ba har abada, Tabbas watarana makiyanki sai sunji kunya, kunya irin Wanda ba zasu taba iya daga Ido su kalleki ba, Insha Allah watarana zaki zama y’antacciya nan bada jimawa ba.”
Abba Kabir din ya fad’a, cikin tabbaci da kuma sanin lokacin hakan na k’aratowa sabida yasan dole watan-wata rana gsky zatayi halinta.
Sanin da yayi kuma cewar Dr yace abarta tasamu ishashshen hutu ne yasa shi matsawa can gefe, tare da zaro wayarsa kaitsaye ya dannawa lamban Dr Sajo Kira.
Cikin sa’a kuwa bugu uku kacal Dr Sajo ya d’aga wayan.
Bayan sun gaisane kuma Abba Kabir din ya gyara zamansa tare da cewa.
“Yaya Sajo jikin d’iyarku Jannart ne ya tashi, yanzu haka muna cikin Mai-nasara Hospital an bata gado, saidai kuma ba Dr. Rayyern ne ya duba ta.”
Daga can b’angaren Dr. Sajo yace.
“Subahanallah yanzu Ina fata jikin natan da sauki.”
“Eh.” Abba ya bashi amsa.
Dr. Sajon kuwa cewa yayi.
“Karka damu Barrister Kabir Indai kuna Cikin Mai-nasara Hospital, koba Dr. Rayyern bane ya duba ta, To Ina tabbatar maka da zata samu isashshen kulawa, Domin gaba d’aya likitotin dake cikin asibitin sunsan aikinsu, kuma dukansu k’wararrune kamar yadda suke da lafiyayyun kayan aiki, sannan maganar Dr. Rayyern dinma zaku samu ganinsa Idan kukayi booking Insha Allah.
Cikin samun karfin guiwa yace.
"In Sha Allah kuwa zamuyi booking”.
“Yauwa sai munzo”.
To yace kana sukayi sallama da juna.
Yana katse kiran ne kuma ya kira Matarsa Aunty Dijat ya Sanar da ita halin da ake ciki, nanfa tace gatanan zuwa ta k’are mgnar da cewa.
“Yanzu ya jikin nata?”.
Juyowa yayi ya d’an ya kalleta.
a hankali take fesar da numfashi alamin baccinta yayi zurfi.
“Da sauki.”
Ya bata amsa, Domin kuwa harzuwa lokacin Jannart din bacci take bata farka ba.
“Allah ya ƙara sauki”.
Amin yace kana sukayi sallama.
K’arfe 5 dai-dai ne kuma yana nan zaune, kiran Yayan nasa, wato Alhaji Idi Sale Dakata ya shigo cikin wayarsa.
Bayan ya d’aga wayarne kuma Daddy da hankalinsa ke tashe yace.
“Wai Kabir ina kuka shiga ne? Wani asibiti ne ka kai Jannart, duk na karad’e asibitoci mafi kusa damu amma babuku babu alaman ku, kuna Ina sannan ya jikin Jannart din?”
Daddyn ya had’ewa Barrister Kabir duka tambayoyin awaje d’aya.
Barrister Kabir kuwa ajiyar zuciya ya sauk’e, tare da cewa.
“Kayi hakuri Yayah, gaba daya sha’anin ciwon Jannart dinne ya rudar dani, shi yasa bankira na sanar dakai komai ba, yanzu dai haka muna Cikin Mai-nasara Hospital, kuma jikin nata da sauki sosai Dan tun da doctors suka duba ta take bacci har yanzu kuma bata farka ba.”
Shima Daddyn ajiyar zuciya ya sauk’e, nan take kuwa yace.
“Okay ganinan zuwa Mai-nasara Hospital din”
Yana gama fadin hakan kuwa ya kashe wayan.
Mom dake kallonsa ne kuma tace.
“Bari na dauko mayafi na muje, Domin dama na gama abinci, Idan yaso saina tafi musu dashi.”
Kai kawai Daddyn ya jinjina mata, Domin kuwa hardai yanzu, Jin zuciyarsa yake a Jagule.
Koda Mom ta d’auko mayafin nata, kitchin ta wuce tare da daukan basket din da ta shirya food flask acikinsa.
Kaitsaye waje ta nufa, saboda tuni Daddyn ya fice.
Tana fita compound din gidan kuwa ta sameshi zaune acikin motarsa, bayan ta shiga kana driver yaja suka fice daga cikin gidan.
6:12 pm dai dai suka iso cikin asibitin, wanda kuma zuwannasu yayi dai dai da zuwan Aunty Dijat.
Domin kusan atare ma suka shiga cikin d’akin da Jannart din ke kwance bisa jagorancin Barrister Kabir.
Bayan sun gaggaisa da junansu ne kuma, Aunty Dijat ta zubawa Barrister Kabir din kunun data dama musu ya sha kasancewar itama tayi girki na musamman ta taho dashi.
A lokacin da aka soma kiraye kirayen Sallah magriba ne kuma, Daddy da Abba suka fice dan zuwa masallaci.
Yayinda su Aunty Dijat da Momy kuwa anan cikin d’akin asibitin sukayi nasu sallan.
Dawowar dasu Barrister Kabir din sukayi a masallaci kuwa, yayi dai-dai da shigowan wasu nurses guda biyu.
Ledan ruwan dake jikin Jannart din, wanda ya k’are nurses din suka cire, tare kuma da sake yi mata wasu y’an gwaje gwaje.
Bayan sun kammala duba lafiyar Jannart d’inne kuma, suka juyo inda d’aya daga cikin nurses din tace.
“Kuyi hakuri patient din batason hayaniya sosai, kuma ak’a’idar aikinmu Idan dare yayi, bama barin kowa acikin Hospital din sai masu kula da majinyata, saboda haka dole duk zaku tafi, saidai za a bar mutum guda d’aya kawai da zaina kulawa da ita, ma’ana wanda zai kwana da ita.”
Kai Duk suka jinjina, cikin gamsuwa da bayanan Nurse din Aunty Dijat tace.
“Shikenan To Abban Hafeez kuje, Idan yaso ni zan kwana da ita”
Saurin girgiza Kai Mom tayi tare da cewa.
“A’a Dijat baza’ayi haka ba, duk kuje ni zan kwana da ita, Domin ba wani d’awainiya ne akaina sosai ba, ke kuwa nasan dole su Hafeeza zasu nemeki.”
Murmushi Aunty Dijat din tayi kawai, saboda tasan maganan da Mom'n ta fad’a gaskiya ne.
Hakan kuwa akayi kamar yanda Momy tace, ita dince ta zauna awajen Jannart din , yayinda Barrister Kabir, Daddy, da kuma Aunty Dijat suka koma gida.
Mom na zaune kuwa har wajajen k’arfe 11 zuwa 12 amma Jannart bata farka daga nannauyan baccin da takeyi ba, wanda kuma hakan ya samo asaline saboda, k’arfin alluran dasu Dr. Sulaiman sukayi mata.
*Littafin TUBALI na kuɗine ki biya kafin ki karanta cikin salama special Group 1k ne karamin group 500 kacal kuɗin karantawa ne bawai kuɗin mallakan littafin bane, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 in ba halin turawa ta ac no kuwa ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp*
Acan gidansu Rayyern kuwa, gaba d’aya babu wani wanda zaka kalla kace yana cikin farinciki, musamman ma da ayanzun suka ga, Rayyern din ya kwashe sama da awanni bakwai bai farka daga baccin daya daukeshi ba.
*11:30 pm*
Dai-dai ahankali ya soma bud’e idanunsa da sukayi masa nauyi.
Inda yana gama waresu kuwa ya sauk’esu, tarwal akan Abbansa dake zaune agefe, ya k’ura masa ido, da dukkan alama kuma jiran farkawan nasa yake.
Idanun nasa ya sake bud’ewa da kyau, cikin kuma dan kuzarin da ya saura masa, ya soma yunkurin tashi zaune.
Ganin hakanne kuwa yasa Abba sakin numfashi, tare da cewa.
“Alhamdulillah Rayyern ka tashi ko, sannu ya jikin naka? Ya kakeji yanzu?”
Idanunsa ya d’an lumshe tare da k’ak’alo murmushin karfin hali, kana murya asanyaye yace.
“Alhamdulillah Abba, yanzu banajin komai naji sauki.”
Murmushin Jin dadi dukansu sukayi, Yayinda Riyyam da har yanzu yake cikin gidan, ya matso kusa da Rayyern din da sauri.
Hannun Rayyern din ya kamo, tare da d’an langwab’ar da kansa gefe, kana cike da soyayya hadi da kulawa yace.
“Masha Allah Hamma Rayyern, Naji dadi daka ji sauki, sannu ya jikin naka?”
Kansa yad’an jinjinawa Riyyam din, tare da dan gyara zamansa, Ahankali yace.
“Da sauki.”
“Hamma Rayyern sannu ya jikin naka?.”
Cewar Ramadan daya taso ya matso kusa da Hamman nasa.
Kai Rayyern din ya jinjina alaman da sauki, dai-dai lokacinne kuma idanunsa suka sauka akan agogo.
Ganin lokaci ne kuma yasashi dan fiddo idanunsa, tare da Kallon Abba da Mamynsa cikin marairaice fuska yace.
“Abba 11:30 pm, narasa sallan magriba, da Isha, Ayyah Abba mai yasa baka tasheni ba.”
Kai Abban ya girgiza tare da cewa.
“Tayaya zan tasheka Rayyern? Ai rashin lafiya ya kauda komai, yanzu ba gashi ka tashi ba, kuma Alhamdulillah ciwon naka da sauki, sai kaje ka rama sallolin da ake binka, tun kafun 12 am ya cika.
Kansa ya jinjina alaman “To.”
Inda Kaitsaye Ramadan ya wuce sama ya had’a masa ruwan wanka acikin bathtub.
Da taimakon Ramadan din kuma ya haura sama yayi wanka.
Koda ya fito daga wankan, wani brown din jallabiya ya saka, tare da shumfud’a sallaya ya tada sallah.
30mn kuwa cas ya dauka yana sallan, bayan ya gama biyan duka sallolin nasa ne kuma ya sauk’o k’asa.
Inda har yanzu suna zaune a falon.
Gefen Abbansa ya zauna ya d’an kallon mamynsa dake cewa.
“Sam Rayyern, baka kula da kanka saboda kwata kwata bakacin abinci, d’azu ma haka kafita bakasa komai acikinka ba sai kayan zak’i.”
Kaitsaye kitchine Mamyn ta wuce, batare kuma da taji ta cewarsa ba, ta hado masa ferfesun kaza, da kuma gasashshen kifi, hadi da ruwan tea mai kauri.
Ganin kuma yanda iyayen nasa suka sakashi agaba ne yasa shi dagewa yaci, duk da cewar bayajin dadin bakinsa, amma haka yaci sosai.
Koda ya kammala cin abincin sama ya haura, saboda still wani sabon bacci yakeji a idanunsa.
Haurawansa sama dinne kuma yasa, Riyyam-nsra mik’ewa tsaye.
Cikin alamun bacci da kuma gajiya yace.
“Abba Mamy Yah Ramadan ni zan tafi, dama na zaunane kawai saboda inason naga tashin Hamma Rayyern.”
Kai Ramadan ya dago tare da Kallon Riyyam din, Cikin nuna damuwarsa ga Riyyam din kuma yace.
“Gaskiya ba zaka tafi yanzu ba Riyyam, ka ko san k’arfe nawa? Yau kam dai ka kwana anan kabari gobe da safe Idan mukayi breakfast saika tafi.”
“K’warai kuwa Riyyam dare yayi yanzu shabiyu fa, Ina zaka samu abun hawa ma, ka kwana anan kawai, yanzu ai duk munzama daya”
Cewar Mamy da ta cab’i zancen.
Abba dake zaune, kuwa baice musu komai ba.
Ganin hakanne kuma yasa Ramadan kama hannun Riyyam din suka haura sama.
Koda suka isa saman direct dakin Ramadan din suka nufa
*Mainasara hospital*
Abba ne da Aunty Dijat suka turo kofar d’akin da Jannart take, a nitse suka kutsa kai ciki.
Dai-dai lokacin kuma Jannart ta ɗan fara motsa kwayar idanunta.
Wanda kuma ganin hakan yasa dukansu cikin sauri suka k’arasa shigowa cikin dakin.
Barrister Kabir da farin cikinsa ya kasa buya ne yace.
“Alhamdulillah Masha Allah Jannart ta farfad’o, Alhamdulillah.”
Jannart kuwa jin sautin Abban nata acikin kunnuwanta ne, yasaka ta kara Ware idanunta tare da yunkura ta tashi zaune.
Kallon Abban nata tayi tare kuma da sakin sassayan ajiyan zuciya mai cike da burbushi kuka, kana Ahankali tace.
“Abbana.”
“Na’am Jannart ya jikinki? Ina da Ina keyi miki ciwo?.” Abba Kabir din ya amsa mata yana me shafa kanta.
“Babu inda yakemin ciwo Abba saidai banajin karfi ajikina.”
Jannart din ta fada tana me Zuro kafafunta k’asa.
Dai-dai wannan lokacinne kuma Daddy ya turo kofar dakin ya shigo.
Yana Ganin Jannart din azaune ya saki murmushi, tare da karasowa cikin dakin, kaitsaye wajen Jannart din ya nufo, cikin nuna so da kauna hadi da tsantsar kulawa yace.
“Allah abun godiya Jannart ya jikin naki?.”
Murmushi Jannart din tayi tare da langwabar dakai cikin sanyi tace.
“Daddy jikina da sauki sosai.”
Kanta Daddyn ya ci gaba da shafawa, cikin kuma muryar dake bayyana rararrashi yace.
“Kiyi hakuri kinji Jannart, kwata-kwata bansan me yake damun Yayanki Junaid ba, Sam Junaid baida wadataccen hankali, duk lokacin daya shawo giyarsa akanki yake huce duk wani haushinsa, bansan ya zanyi dashi ba Jannart, amma na d’auki samunsa amatsayin k’addarata wacce bazan taba iya sauya taba.”
Ya kare maganar yana mai matsan k’walla daga cikin idanunsa.
Wanda hakanne kuma yasa Jannart girgiza masa, Kai kana cikin sanyi tace.
“Karkayi kuka Daddy kaifa mahaifinmu ne, kuma zubda hawayenka asanadiyar Yah Junaid ba karamin masifa zai haifar masa ba.”
Shiru gaba daya dakin ya dauka, inda hakanne kuma yasa Momy zubawa Jannart din abinci.
Saidai kuma bataci abincin ba saida taje tayi brush tare dayin wanka kana ta kimtsa kanta da kayan da Aunty Dijat ta kawo mata wanda harda pand. Anan cikin toilet din dake cikin dakin ta gama kimtsawanta.
Bayan ta fito ne kuma ta zauna taci abincin, Duk da cewar batajin dadin bakinta kuma haka ta daure taci sabida yadda iyayen nata suka matsanta.
Kafun ta gama cin abincinne kuma Momy, tayi shirin komawa gida, acewarta zata je ta dawo.
To shima dai Daddyn kasancewar ba jimawa zaiyi bane yasa Mom'n na tafiya shima ya tafi ba jimawa, acewarsa akawai wani aiki da zaiyi.
Hakan yasa dakin ya rage daga Jannart sai Abba Kabir da Aunty Dijat da kuma Hafeeza.
Wanda Hafeezan ne kuma ta kamo hannun Dijat, tare da cewa
“Momy taso muje kiga waje.”
Yadda take tajan hannun tane tana d’aga sautin cewa su fitane yasa Dijat din ta mike kasancewar tasan ba'a son cika hayaniya kan mara lfy.
Koda suka fito harabar wajen kuwa, akan wani kekkyawan kujeran silver Dijat din ta zauna.
Ko mintuna 3 ba ayiba da fitar tasuba.
Barrister Kabir ya gyara zamanshi tare da jawo kujerar da yake kai ya ƙara matsowa kusa da Janbart
Zama yayi agefen Jannart din.
Wanda hakan yasa ta d’ago Idanunta dake cike tab da hawaye ta kalleshi.
Kai ya fara jujjuya mata yana mai jin rauni.
Gaba daya fuskarta ne ya sauya, Yayinda rauni da kuma matsanancin damuwa ya bayyana akan fuskarta.
Cikin kuna da kuma ciwon da takeji acikin zuciyarta ta ɗan gyara konciyar da tayi murya a sanyaye tace.
“Abba”.
Cikin tarin kulawa yace.
“Na'am Jannart”.
Ɗan yunƙurowa tayi ta ɗan tashi ta jingina da jikin gini.
Murya can ƙasa hawaye na kwaranya tace.
“Abba Yah Junaid ya tsaneni. Yah Junaid shine babban matsalata aduniya, Yah Junaid baya k’aunata Koda kad’an, Abba sai yaushe ne nima zan zama y’a kamar kowa? Sai yaushe ne zan samu ingantaccen farinciki? Sai yaushe zuciyata zata huta da kuncin rayuwa? Yaushe Daddy zai fara daukan mataki akan abubuwan da Yah Junaid keyi min Abba ka rabani da gidan Daddy mana dan Allah ka medani gidanka...”
Dan tsagaitawa da maganan tayi tare da dafe saitin kirjinta dakeyi mata zafi.
Cikin kuma muryar kuka tace.
“Abba zuciyata tana gab da bugawa, matukar rayuwata taci gaba da tafiya ahaka,Abba mutuwa zanyi, Domin wata kilan hakan shine zai zamo silar farincikina.”
Saurin rufe mata baki Barrister Kabir yayi, cikin kuma muryar dake bayyana tsananin takaicinsa da tausayawa da son fara fahimtar da ita wani abun da bata saniba sabida fara shirin kawo mata sauyi a rayuwarta yace.
“Bazaki tabbata ahaka ba Jannart Insha Allah haske yana nan zuwa, sannan ki rabu da maganan Junaid dana Daddynki.
Domin kuwa Dadynki *HANKAKA NE*...!!!”
Littafin TUBALI na kuɗine ki biya kafin ki karanta cikin salama special Group 1k ne karamin group 500 kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276.
*GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*
Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.
Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.
Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.
GARKUWAR MA'AURATA
By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*TUBALI*
PAGE 18
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
*WANNAN PAGE D’IN SHINE K’ARSHEN FREE PAGE, DAGASHI BABU WANI FREE PAGE IN KIN GANSHI A WOJEMA TO SATA PAGE NE daga wannan PAGE 18 na gama free PAGE, dan sonku da Allah da Manzonsa kada ku fitarmin da littafina 1k ko 500 da kika bada bawai yana nufin kin biya kin mallakeshi bane kuɗin karantawa ne, dan Allah nace ba don niba, in Zaki saya ga ac no 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in baki da damar tura ta account ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo minshi ta WhatsApp 09097853276.*
_Masu karanta Audio books kuyiwa girman Allah ku kiyaye min littafina domin zama lafiya yafi zama ɗan sarki, ga number birjik a pages idan ki/kana so ki/kayi min mgn mu dai-dai ta masu posting a wasu shafukan kuyi girman Allah ku barmin