Showing 3001 words to 6000 words out of 350584 words
Sai kuma ya ɗan juyo yana kallonshi jin yana cewa.
"Ramadan ya kira ɗazu".
Kai ya gyaɗa mishi kawai.
Ganin haka Usman ya juya ya fita.
Yana ganin ya fita, ya matso ya rufe ƙofar.
Yana juyowa yana cire Suit ɗin, bisa kujera ya cillata, kana ya cire ta cikin.
Sunkuyowa ya ɗanyi yana kunce belt ɗin ƙugunshi.
Yana daga tsaye ya zare wando .
Yana son sakewa shiyasa yake jin daɗin rayuwar kaɗaici.
Sabida yana masifar kunya da suturce surar jikinsa.
Ko dan yanayin halittar jikinsa mai gargasa ne, baya son koda Ramadan ne yaga koda damtsen hannunshi bare sharaɓarsa bare aje ga cinyarsa, da tattausan gargasa yayi masu ƙawanya.
So Amman in shi kaɗaine yana sakewa, wasu lokutan daga falo yake fatali da kayyakinsa kafin ya shiga bedroom ma daga shi sai boxes zai shiga.
Tattare kayan yayi ya wuce dasu Bedroom, bisa gado ya ajiyesu.
Kana ya wuce Bathroom.
Bayan ya fitone ya kimtsa cikin wasu tattausan riga da wondo iya guiwa farare ƙal.
Turare ya ɗan fesa, kana ya ƙara gudun A'C sannan ya koma parlon ya ɗauko ƴar jakar da yasa Usman ya ɗauko mishi wanda yake cike da chocolates kala daban-daban.
Masu sanyi a daskare.
Sosai ya ci Galaxy Chocolate mai ɗan karen daɗi kamar yadda ya saba ta'ammali da kayan zaƙi.
Bayan ya gama ne, kuma yasha tea mara haɗi, wato coffee. Bayan ya kammala ne kuma ya dawo Bedroom riƙe da system a hannunshi.
Kashe wutan ɗakin yayi, kana ya kwanta.
tare dasa l system ɗinnasa a gaba.
Ajiyan zuciya ya sauƙe, Allah ya sani yana jin wani irin nishadi da sanyi na musamman in yana jin wa'azin Dattijon nan, Malam Mai-nasara, yana son tafsir din shi.
Baya gajiya da kallon fuskar tsohon.
Wannan yasa yake bibiyar shafin shi na You tube inda yake saka tafsiransa.
Lallatsa system ɗin yayi.
Jim kaɗan sai ga hoton ya bayyana.
Fuskar dattijon ya zubawa idanu.
Har bai jin abinda ake magana a kai.
Sai da yaji iska na ɗan cika mishi ido ne, ya ɗan lumshe idanun tare da sauƙe numfashi, kana ya buɗe su.
Kan rubutun dake ƙasan hoton Dattijo ya kuma kalla. Malam Mai-nasara".
Cikin sanyi can ƙasan zuciyarsa yake magana.
"Ƙarshen sunanmu iri ɗaya. Ni dai nasan Tubalin nawa sunan. Toh shi kuma menene TUBALIn nashi sunan Mai-nasara, menene asalin sunan?".
Wa zai amsa mishi waɗannan tambayoyin da zuciyarsa taƙi dena mishi su?
Numfashin gajiya ya sauƙe kana ya kauda tunanin yaci gaba da jin tafsir ɗin nashi.
Jin bacci zai kwashesa ne yasa ya rufe na'urar ya kwanta yana mai buɗe tafin fararen hannunshi yana addu'o'in.
Yana idawa ya shafa ya kwanta.
Kano Nigeria.
Sulaiman ne zaune bisa kujera matarsa, Sumayya na gefenshi.
Da sauri yace.
"Ikon Allah".
Juyowa Sumayya tayi tana cewa.
"Lfy?".
Da sauri ya matsota tare da cewa.
"Kiji ikon Allah wai Riyyam-nsra, wannan ɗan Ethiopia da nake ce miki yana masifar kama da Rayyern wai zaizo Nigeria".
Leƙowa tayi ta kalli fuskar wayarshi, inda yake TIKTOK yana bisa shafin Riyyam-nsra.
"Kai gsky kam Ni kaina ina ta'ajjudin kamanni Rayyern da yaron nan, kamar ta ƙazanta".
"Uhumm ni kaina na gaza daina mmakin kamanninsu.
To amman kin kuma ji wai zaizo Nigeria".
Riƙon da tayiwa yarsu ta gyara tare da cewa.
"Abban Nihal me abun mamaki don zai zo Nigeria, kasan celebrity’s da yawo kamar jirage".
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Sumayyah ba zuwansa Nigeria bane abin mamaki."
"Toh menene abin mamakin".
Ta tambayeshi cikin kulawa.
Juyo mata fuskar wayar yayi.
Da sauri ta zsro idonta waje cike da mamaki tace.
"Dama H...!
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*TUBALI*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
ASSALAMU ALAIKUM, Masoyana ma karantan littattafaina, ina mai farin cikin sanar daku, yau d’in nan MON, 18 OCT 2021 za'a fara biyan kud’in samun damar karanta littafin TUBALI akan farashi mai sauk’i Biya 500 k’aramin farashin na k’aramin group, kana sai *Special people Group* akan farashi mai sauk’i 1k kacal babban group a yawan posting babancinsu yake, zaku biya ta asusuna.
ACCOUNT NO 0661110170.
BANK NAME: AISHA ALIYU GARKUWA
BANK GTBank
sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan numben tawa da nakeyin whatsApp da ita 09097853276.
*PLS TAKE NOTE BAND VTU*
kada kiyi min VTU ko transfer'n katin ta wannan numben etisalat d’in idan kuwa kikayi wlh babu ruwana dan na fad’i miki. Please and please in dai da hali kada ki turo min katin, kiyi min transfer'n ruwan kud’i ta bank account na, in kuma babu dama to sayi katin MTN sai ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp.
Gareku mutanen jamhuriyar Niger ku tuntub’i Mommy akan layinta +22790899076, ta wurinta zaku biya, hoton katin zaku d’auka ku tura mata ta wannan numben a whatsApp, Special people group 1k ne (1000) k’aramin group kuma (500) kacal,
Please dan Allah babbar macece mai yara da tarin jikoki da y’ay’an jikoki mu kyautata lafazi da mu'amala gareta dan Allah don in ka girmama iyayen wasu wasu zasu girmama naki🙏🏻...
Littafin TUBALI littafine na musamman mai salo na musamman mai cike da abubuwa masu tarin yawa.
*Tausayi, Sark’ak’iya, jan hankali, Fadakarwa, Nishad’antarwa, ilimantarwa, al'ajabi, Sa'ar rayuwa, riƙon amana, cin amana, ribar kyautatawa, kana da sassayar soya mai salon narke jiki da zuciya*
Ga number wayata da nakeyin whatsApp da ita, 09097853276 idan kina son biyan kudin samun damar karanta littafin TUBALI sai ki biya ta wannan ac no din dai 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, dan Allah ki biya kafin kiyi min mgn kina turo shaidar biyanki ina gani zan saki a group, in Kuma baki da ac no ko yanayin zaman wani k’asa ko wani luggun ki sayi katin MTN na 1k in special group kikeso ki turo min. In Kuma k’aramin Group kike so ki sayi katin *MTN ki copy number's din ki turo min ta whatsApp number'n na 09097853276 kada kiyi min VTU ko transfer'n katin 9mobile dan layin nada matsala*
Za'ayi tsawon mako ɗaya ana biya ina kafin in fara update domin samun sassaucin aiyukan sauraron mutane, za'a fara biya yau *MON 18 OCT 2021. Kana zan fara posting ranar MON 25 OCT 2021 rana ita yau kenan in mai kowa mai komi ya kaimu bisa rai da lfy*
🙏🏻Na rokeki da girman zatin ubangiji in dai kin san zaki sayane dan ki fidda min littafina dan Allah ki bar kud’inki kiji tausayin marainiya, kada ku cutar da marainiyar Allah,😭🙏🏻🙏🏻🙏🏻.
Nasan daga yau har zuwa na gama littafin Chart zaimin yawa zai hausawa aiyuka zasu yawaita gareni, amman babu kamar makonni ukun forko zuwa biyar, Please ina neman al'farmar uzuri in kinga kinyi min mgn ban amsa mikiba, na tuba kiyi haƙuri ba raini bane ko wulak’anci face yawan mutane wata k'il ban isa kan Chart naki bane, Amman muddin na isa na kuma bud’e na gani tabbas zan baki amsa in katine zansashi yana shiga zan saki a group in bai shiga kuma in gaya miki, in Kuma ta account kika turamin ina ganin shaidar biyanki zan saki a group, 🙏🏻Dan Allah in kinsan ba littafi ko maganin gyara namu na mata kikeso ba to kiyi haƙuri da min mgn sai na d’an samu salama🤝🏻😘🙏🏻😂.
*Sayan na gari maida kuɗi gida sai kinzo*
By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:19 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*TUBALI*
PAGE 2
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
"Hausa ya keyi fa ko?". Cike da kaɗuwa Sulaiman yace.
"Eh abinda ya ban mamaki kenan.”
Sai kuma ya kalleta jin tana cewa.
"Koda yake ba mamaki wani ne ya rubuta mishi, tunda kaga ai yace.
Ethiopia Addis Ababa to Nigeria kano State. Kanawa zan zo muku.
Wata ƙil wani ne ya rubuta mishi".
Komawa yayi da baya ya jingina bayanshi da jikin kujera.
Numfashi ya ɗan fesar tare da cewa.
"Kai Sumayyah gsky da mamaki fa.
Kalli Comments ɗin mutane fa da amsar da yake basu."
Ya ƙare maganar yana shiga comments section ɗin ƙasan video'n da ya saka a shafin nasa.
Inda wani Abis Fulani yake cewa.
"Eyyeh Riyyam-nsra a Nigeria, kanawa nama fatan isa lfy".
Cike da mamaki Sumayyah ta kalli amsar da ya baiwa Abis Fulani.
"Ngd aboki na". da alamun musabaha.
Sai kuma tayi ƙasa ganin inda wani.
Ahmad MG ya fara mgn da zaro ido alamun mamaki tare da cewa.
"Riyyam-nsra da yin Hausa, ko mafarki nakeyi".
Dariya yayi tare da bashi amsa.
"Noh Ahmad zahiri ne".
Tofa wannan abun yasa comments ɗin mutane zubowa kamar ruwan sama domin shi dai ɗan ƙasar Ethiopia ne, kalarsa, harshensa, cimarsa, rayuwarsa, komai na canne, bai taɓa koda maganar Nigeria a shafinsa ba, sai gashi yau kuma yayi video cewa zaizo Nigeria, kuma yana rubutu da hausa yana kuma karantawa.
Cikin kaɗuwa Sumayyah taci gaba da bin comments ɗin mutane na farko-farko da ya iya basu amsa sabida yawan mutanen.
Cikin mamaki tace.
"Lah kalli tambayar da wani ya mishi."
Amsar wayar Sulaiman yayi.
Ya fara duba saƙon da Imran yayi mishi.
"Riyyam-nsra kasan Nigeria ne? Ko Ka taɓa zuwane? Ko wannan ne zuwan da zakayi na forko?".
Alaman murmushi yasa tare da cewa.
"Nasan abu da yawa kan Nigeria".
"Da sauri yace gaya min kaɗan daga ci."
"Ok kamar me kake son in gaya maka".
Da sauri yace.
"Ka iya taken ƙasa. Ko rantsuwar al'ƙawarin ƙasa."
Cikin lumshe ido, Riyyam-nsra dake kwance a ɗakinsa.
Ya rubuta mishi amsa, da bari in baka amsar a video."
Take kuwa ya tashi zaune yayi taken ƙasarmu Nigeria ƙasarmu ta gado kana da rantsuwar al'ƙawarin ƙasa.
Wannan video da ya saki
Yayi matuƙar jan hankali al'ummar Hausawa duniya baki ɗayansu more Especially ƴan Nigeria bama ya kanawa.
Da sauri Sulaiman ya fara rubutu.
A karo na forko a rayuwarsa da zaiyiwa wani comment a TIKTOK.
Rubutu yayi cikin harshen nasara.
"Hey Riyyam-nsra you knew much about Nigeria you are a patriot".
Yayi mgnar da gayya ne dan ya gano ko dai ɗan Nigeria ne basaja ne da karya yasa yake ciwa ɗan Ethiopia ne, wata ƙil karatune ya kaishi can.
Murmushi yayi tare da rubuta mishi amsa.
"Baƙon Nigeria dai mai kishin Nigeria amman ni ɗan Ethiopia ne.
Sai dai Nigeria ƙasar babban abokina ne da mukayi karatu tare a US."
So daga ganin wannan video, akai ta cewa.
"Haba shi yasa mana.
Nasir Ahmad ne wanda shine abokin nashi ya fito, yanata mishi tsiya a nashi shafin. Nanfa aka gane sanadin zuwansa da kuma inda ya koyi Hausa ras.
Ɗan gajeren tsaki Sulaiman yayi tare da cewa.
"Wadannan yaran gaba ɗaya TIKTOK ta haukata mana matasa wanda sune TUBALIn al'umma sai gashi kuma muɗin ma suna shirin haukatamu".
Dariya Sumayyah tayi tare da cewa.
"Dama haka ai Rayyern ɗin ke ce maka, in baka dena biyewa social media ba, zaka rasa lokacin kanka".
Kwaffa yayi tare da rufe datarsa kana yace.
"Nima fa Ibrahim ne ya sani fara wannan abun sabida, kamannin Rayyern da wannan yaron."
Daga nan sukaci gaba da hira kan kamanninsu.
Washe gari da safe ranar talata.
Gidan Alhaji Idi Sale Dakata.
Su kusan shida ne cikin falonshi.
Wanda huɗu daga cikin manyan yan kasuwane masu faɗa a ji masu juya sule ta koma million ɗaya ko tako wanne irin halin ƙaƙama ko talaka zaiji daɗi haka ko bazai jiba.
Biyu daga ciki kuma ƙusoshin gwamnati ne masu ƙarfin iko daga ta jiha zuwa ta ƙasa.
Alhaji Yawale ne ya gyara zamanshi tare da cewa.
"Yaron nan fa yanayi mana illa ba tare da mun ankare ba.
Gaba ɗaya ya rarake tubalin da mukayi tsawon shekaru muna ginawa muna samun wuri na jawo mana wuri."
Cikin tsananin takaici Alhaji Abdu Tababa ne yace.
"Tun-tuni nake gaya muku haka.
Mu kauda yaron nan a doron ƙasa shine kawai mafi sauƙin mu.
Kunaga yadda kasuwan cinsa ke haɓaka, kamfanonin sa suna bunƙasa daga Arewacin Nigeria har ya koma kudanci ya kafu.
Uwa uba yanzu duk ƙasashen Afrika yanada rassai.
Ya maida kayan abinci da araha tamkar ruwan sama cikin damuna.
Duk inda ka shiga a kasuwannin Mai-nasara race, ke cike.
A farashi mai sauƙi ta yaya za'ayi a saurari kayan kamfanonin mu".
Ɗaya daga cikinsu ne ya miƙe tsaye tare da cewa.
"Ni tambaya ta a kullum ma shine
menene Tubalin kasuwancin yaron nan?
Yaushema aka haifeshi? Sa'an yaran cikin mune fa!
Ta ina ya samu Wannan tarin dukiyar da har ya samu damar razana mana kasuwanci ya raunata mana Company's.
Yaushe yayi ginin duk a lokacin ɗaya menene Tubalin dukiyarsa da matakan ikonsa!?."
Ya ƙare maganar yana kallon Bala Tambari wanda shine shugaban tsare-tsaren ginin masana'antu a gwamnatance, dole sai yasa hannu za'ayi gini ya za'ayi ka bashi izini da damar yin gini a duk inda yake so a ƙasar nan".
Cikin takaici Bala Tambari ya fesar da numfashi tare da cewa.
"Tsohon yarjejeniya ne, yana da dukkan abin buƙata, yanada sa hannun da suka gabaceni kuma kan tsari suke.
Naso in ƙalu balanceshi.
Tun shekaru biyar baya lokacin da ya fara gina babban campany dake Nan birnin Kano wanda yanzu yake gab da kammalashi so naga komai da hujja yakeyi.
Yaron shegen taurin kai ne dashi, gashi da ɗan banzan tsaurin ido.
Kana mgna zai tsira maka waɗannan siraran idanun nashi masu kama da soyayyan gujjiya, tsakar idon ka ya baka amsa da hujjar da baka isa kayi mgna ba".
Dr.Lukman ne ya fesar da iska a baki tare da cewa.
"Ni ta ko ina ya tosheni
A fannin likitancin gaba ɗaya yana bi yana rarake privet Hospitals.
Ɗan banzan komai na asibitinsa mai sauƙi kuma ga kula ya za'ayi aje irin namu asibitocin."
Alhaji idi Sale Dakatane ya miƙe a fusacen shina kana yace.
"Nifa gaba ɗaya ya ta'azzara min campany na na shinkafa.
Sannan kafin kace ka motsa sai ka samu ya toshe ko ina.
Hegen yaro mai jajayen kunnuwa.
Yana nan tamkar Wahainiya, samun ganinshi ma ya zamewa mutun aiki."
Dr Lukman ne ya ɗan sauƙe numfashi tare da cewa.
"Cikin satin nan zai dawo Nigeria yanzu haka yana Ethiopia yaje, shugaban kasar can da kanshi da manyan likitocin sune, suka karrama shi.
Sabida taimakon da yayiwa wasu daga cikin mutanen ƙasar Ethiopia cikin Airport kan hanyarsa ta zuwa US, dan karramashi a matsayin ɗan kasuwan da yafi ko wanne sauƙin farashin kayan masarufi.
Kaga yana tafi kuma yazo wai kuma Ethiopia zasuyi mishi wata karramawar.
Yaro kamar ɗan ruwa, komai yasa kai sai Nasara".
Bala Tambari ne, ya kalleshi tare da cewa.
Toh yanzu dole kai zaka nema mana zama dashi.
Yana dawowa muna buƙatar shi mu gwada sayan farashinsa.
Muyi mishi tayin harƙallarmu yasan irin ribar da muke shigarwa, wata ƙil zai amince mu haɗa hannu in kuma yaƙi tabbas zamu gina mishi gadar zare.".
Da sauri Alhaji Idi Sale Dakata yace.
"Uhumm ai In Kuma yaƙi amincewa mu haɗa hannu.
Toh lokacin wasan zai fara, dan in taurin kaine da gsky da samun ƙarfin iko bai kai.
Mai-gaskiya da wasu ba, da muka gama dasu shekaru ashirin da biyu baya ba, danni cinnaka ne ban bar na gida Bama, bare shi baare."
Haka dai suka tashi a taron nasu.
A nufin sai ya dawo su zauna dashi.
A cikin gidan kuwa. Jannart ce ke
Tsaye a kitchen, inda take sanye da wani half gown mai masifar kyau wanda ya d’an bayyana fararen legs d’inta, rigar irin mai kauri da kama fatar jiki dinnan ne, wanda hakanne kuma yasa had’add’iyar Surar jikinta dan bayyana, kasancewarta y’ar gayu, Tabbas Jannart macece mai matuk’ar son fashion, shiyasa hatta suturun da take sawa ya banbanta da sauran na y’an Nigeria, saboda sometimes tafi yin shiga irin na wasu daga cikin larabawa, ko kuma shigar mutanen turkey🇹🇷.
Tsaye take a kitchine din cikin kuma nutsuwa take aikinta.
Yayinda Mom ke tsaye a gefenta.
Cikin kula Mom ta kalleta tare da cewa.
"Jannart kamar Yayanki ne ke kiranki".
Cikin bugawar zuciya tace.
"Yah Junaid!?."
Da sauri tace.
"Eh shi dai".
Bugawa zuciyarta ya kumayi, tare dajin wani iri acikin jikinta, saidai kuma babu yanda ta iya, haka ta juya cikin sanyi ta nufi falon.
Can tsakar falon ta hangoshi tsaye, saurayi ne, mai murd’addiyar Surar jiki da kuma tarin gashi akansa irin busu-sun nan, duk da cewar kyawun nasa bawani na zarce hankali bane amma baza’a tab’a k’iransa da mummuna ba, wata riga
marar hannuce ajikinsa, sai kuma wondon dake jikinsa wanda ya tsaya masa iya guywa.
Bisa alamu kuma yanzu ya tashi daga bacci.
saboda yanda idanunsa sukayi jazir.
Kallonta yayi, tare kuma da d’an cije labb’ansa, still Cikin binta da wani irin mayataccen kallo yace.
"Kije ki share min ɗakina".
Fuskarta ta d’an b’ata cikin kuma tsanar shiga ɗakin nashi tace.
"Yah Junaid breakfast nake haɗa mana".
A fusace ya juyo kanta cikin takaicin abubuwan dake haɗe mishi a kanta ya yarfa mata wani irin gigitaccen mari a kan kunneta na dama, saida ya bada wani irin sauti ƙauuuuu! Da ɗan karen ƙarfi.
A gigice tasa tafin hannunta ta tallabe ƙuncin ta.
Yayinda wasu taurari suka fara gilma mata a gani.
In da sabo yaci ace fuskarta ta saba da marukan Yah Junaid Wanda tun tana yarinya take shansu gashi sanadin su, kunnuwanta sun samu matsala jinta ya raunata.
Wasu irin hawaye ne masu masifar zafine suka silalo mata.
Ba tare da tace komaiba ta juya ta nufi ɗakin shi.
Ta yaya zuciyarta zata samu sauƙin ɗan uwanta da take bata da wani sama dashi tunda shine suke uwa ɗaya uba ɗaya amman yafi kowa tsanarta a duniya.
Ba shaƙuwa ko tausayawa a tsakaninsu.
Sannan mahaifinsu babu ruwanshi ko a gabanshi Junaid zai daketa babu ruwanshi sai yayi kamar baya wurin ma.
In Mom tayi mgna ya gwatsaleta yace babu ruwanta sunfi kusa.
Wannan ne ya ƙara tsananta zubda hawayen ta.
A haka ta fara tattara mishi falon da gaba ɗaya ya birkitashi.
Shigowa yayi ya zauna yana mai Binta da ido, duk inda tayi.
Wani irin abu yakeji a kanta.
A hankali ya miƙe yabi bayanta lokacin da ta shiga Bedroom.
Da sauri ta juyo jin shigowarsa.
Gefenta ya matso fuska a murtuke hakan ne yasa