Showing 270001 words to 273000 words out of 350584 words
ya ɗan rage wani abin to amman kamar ingizasa akayi.
Kifa kansa yayi a jikin glass din jaccuzei'n ya saki wani irin kuka mai sauti tare dasa hannun damansa ya damƙi Naan ɗin tamkar zai karyashi.
“Why!? Why!!? Whyyyyyyyyyy!!!? Janna na me nakeji hakaaaa? Huyyhhhhh".
Ya ƙarasa mgnar da ƙarfi da kuma sakin kuka.
A ƙalla 40 minute yayi a haka a kasan ruwan sanyi kafin.
Ya fara sauƙe ajiyan zuciya akai akai kana ya funkuyo ya kalli Naan ɗin shi da still har yanzu dai tana tsaye ne sai dai ta rage kumbura, hakan ne yasashi rufe ruwan kana, ya fito.
Sai lokacin yake tuhumar kansa kan yana zubda mutuncinsa yafi dacewa daya tabbatar da ta soshi kafin komai.
Kana ya kimtsa.
Wasu datsastsun suit yasa rea collor masu azabar sheƙi.
Sosai yayi kyau a ciki saidai fuskarsa da tayi jazir kana idanunsa suka ɗan kumbura alamun dai yayi kuka.
Wayarshi ya zaro a aljihun jallabiyar tasa ya ɗauka.
Kana ya fito falon, fuska a tsuke.
Yana isa kuwa yaji ana buga ƙofa, da sauri ya nufi can bakin ƙofar sanin breakfast nasu da yayi other ne ya iso.
Bayan ya amsa ne, ya dawo tsakiyar falon.
Bisa santer table dake tsakiyar falon ya ajiye ledan.
A hankali ya zauna bisa kujera tare da meda bayan shi ya jingina kanshi da kujerar,
Idanunsa ya lumshe adai-dai lokacin da yaji suna gab da ciccikowa da hawaye.
Jannart kuwa a ɗakinta,
Hannunta tasa tana fifita lips ɗinta sabida wani irin zogi da suke yi mata,
Dan sai wani zut-zut sukeyi mata sabida yadda yayi mutsu tsotsan huce takaicin su.
Hannun tasa ta sharce hawayen ta,
Cikin sanyin murya da rauni tace.
“Mugu kawai Allah zai saka min duk ya sa Caɓɓullena ciwo”.
Sai ta kuma kifa kanta bisa pillow taci gaba da kuka, a haka bacci yayi awon gaba da ita.
Shi kuwa Dr Rayyern a falo.
Duk sonshi daya tankwara kansa ya sarrafa tunaninsa ya kasa.
Ya rasa meke yawo a jiki da zuciyarsa,
Yasan shi dai bai taɓa shiga makamcin wannan yanayin ba a rayuwarsa ta duniya.
“To meyasa yanzu rana tsaka komai yake sauya min? to ko dai dama tuntuni nima jarabebben ne kamar Riyyam-nsra?, koko zuwanta rayuwatane yasa haka, dan tun ranar da yarinyar nan tayi ta shafa min marats
Da ciwon cikinna ya tashi ne duk ta sauya min rayuwa ta medani wani jarabebben mara haƙuri”.
Yana cikin hakane yaji wayarshi na ringing,
taune lip enshi na ƙasa yayi tare da rumtse idanunsa da masifar ƙarfi.
Cikin zuciyarsa yace.
“Na gaji da wannan ajiyar zan meda musu yarsu tunda bata sona, bana son na fasa bazan zauna tsawon shekara da itaba, ya kaita duk ma inda yakeso yanzu a wata takwas ma tana gab da kasheni kuma tace bata sona! Wai bata sona!”.
Taune lip inshi ya kumayi jin kira na uku ya kuma shigo masa wayar,
Ya sani bazai iya mgn a dai-dai ba.
A kufule ya zaro wayar tasa da nufin katse kiran, sai kuma ya amsa cikin makantar ido.
Saida ya amsa kuma yaga Barrister Kabir ne.
Cikin danne hali da yanayin da yake ciki ya kara wayar a kunnesa.
Cikin sarkafewar murya da shessheƙan raunataccen kukan dake gab da kubce masa yace.
“Salamu alaimu Barrister barka da safiya”.
Shiru Barrister Kabir yayk tare da fiffito da idanunsa woje cike da mamakin yanayin muryar Yaron yace.
“Rayyarn! Lafiya kuwa”.
Idonsa ya rumtse da karfi hakan ya bawa hawayen sa damar zubowa murya a dake yace.
“Eh lfy”.
Cikin rashin gamsuwa Barrister Kabir yace.
“Ka tabbatar?”.
“Uhummm”. Ya bashi amsa cikin maƙoshinsa.
“Rayyern!.”
Barrister ya Kuma kiransa cikin kulawa.
Cikin Muryar dake nuna asalin halin da yake ciki yace.
“Na'am”.
Zuwa yanzu kam Barrister ya gane tabbas Dr yana cikin yanayin matsi domin muryasa kadai ta fallasa halin da yake ciki.
Wani irin murmushin dake tare da manufofi Barrister yayi kana a hankali yace.
“Meke damunka?".
“Babu”.
Ya kuma basa amsa a takaice.
“Toh Jannart ce bata da lfy”.
Ya kuma tambaya cikin hikimarsu ta Lawyers.
Cikin sakin shessheƙan kukan can ƙasan maƙoshinsa da dannesa da makararriyar jarumtarsa yace.
“Tana lfy”.
Murmushi Barrister ya kumayi kana yace.
“To ko dai itace tayi maka wani laifin".
Cikin kufular da bai san yanada itaba yace.
“Eh wai bata sona”.
Da sauri Barrister yace.
“Subahallahi gaya min me tayi maka in Sha Allah kuma zanyi mata mgn kuma inada yaƙinin bazata ƙaraba”.
Sai lokacin ya dawo cikin nitsuwa kaɗan a hankali yace.
“Bata son shan mgni kuma bata son allura, gashi jikinta ya tashi bata son cin abinci, sai tayi ta guduna, banaaaa soooooohhh”.
Yaja ƙarshen mgnar can ƙasan maƙoshinsa kana hawaye na kwaranya.
Murmushin ƙeta Barrister ya saki cike da jin dadi tabbas yasan tarkonsa ya kama kurciya.
A fili kuma sai cewa yayi.
“Kayi haƙuri in Sha Allah zan mata mgn kuma zata bari”.
Tamkar yaro ƙaramin haka ya gyaɗa kansa.
Ajiyan zuciya Barrister ya sauke kana a hankali yace.
“Dama na kiraka ne in shaida maka Azeez yace in Sha Allah jibi jumma'a zai zo muku yaga jikin Jannart din in ka amince tun randa kuka haɗu yake matsimin zaizo na dai ƙi amincewa sabida ban san ra'ayinka ba”.
Cikin sanyi yace.
“Allah ya kaimu, zan tura maka address namu ka tura masa”.
Da sauri yace.
“A'a na tura masa number ka zai kiraka”.
“Ok”. Daga nan sukayi sallama.
Meda wayar yayi cikin aljuhunsa kana ya miƙe tsaye,
idanu ya zubawa ƙofar ɗakin nata,
yanaji kamar tunaninsa na hautsinewa.
Kwaffa yayi tare da juyawa ya nufi woje a kasalance ya shiga motarsa yaja ya bar gidan.
European medical center Mascow.
A karo na barkatai Dr Sulaiman ya kuma kallon Dr Rayyern da idanunsa sukayi lu-lu kana fuskarsa tayi jazir.
So yake yayi matsa tsiya to Amman kansu ya ɗauki zafin aikin da sukeyi.
Domin tun tara na safe da suka shiga har yanzu biyu saura basu fitoba.
Biyu da kwata dai-dai suka fito a jere.
Daga nan ɗan masallacin dake gefensu suka, shiga sukayi salla kana suka fito cikin yanayin alamun yunwa da gajiya.
Cikin sanyi ya juyo ya kalli Dr Imran dake gefen Dr Sulaiman.
Gajiyayyun idanunsa ya zuba musu jin abinda suka haɗa baki wurin cewa.
“Dacta wai meke damunka ne?”.
Cikin kauda kai yace.
“Abinda yake damunku”.
Da sauri Dr Sulaiman yace.
“Ya zakace haka yanayinmu ya banbata da naka.
Kalli yadda idanunka suke a kumbure ga fuskarka tayi jazir alamun ka kwana kuka ne.
Please Dr Rayyern tell me true”.
Wani irin sassayan tsaki yaja tare juyawa ya nufi. Motarsa baice musu komaiba dan yasan Sulaiman ba mutuncine da shi ba yanzu zai kwance masa wondo a kasuwa.
Leffe cafe ya wuce kai tsaye, sam bayajin sha'awan cin komai duk da masifeffiyar yunwar dake zagularshi wacce itace kuma ta taimaka mishi wurin kashe kaifin azabebben sha'awar dake wujujjugashi.
Sheey yaja numfashi sabida sanyin dake ratsashi.
A hankali ya shiga ciki bayan yayi parking.
Coffee mai zafi kawai ya rinƙa zuƙa ba sassauci har saida ya cika cikinsa da ruwan kana yaji sanyin ya ragun masa.
Kana kuma kaifin yunwarsa ta mutu.
Sai uku da kwata ya bar wurin yana shiga asibitin sukayi sallan la'asar.
Daga nan suka koma aikin su na gaba wanda zai kaisu karfe biyar.
Ethiopia Addis Ababa.
Riyyam-nsra ne zaune gaban Mammy rike da waya a kunne cikin tsananin jin daɗi yace.
“Alhamdulliah Mamy kice mu fara shirin zuwa Nigeria nan kusa”.
Daga can ɗaya sashin cikin shakuwa Mamy tace.
“A sosai ma kam Riyyam-nsra dan in Sha Allah ranar jumma'a za'a kai kayan aure da sadaki kuna sai da ranar kuma kafin Azumi za'ayi komai”.
“Wayyo Mamy kice Hamma Ramadan daɗi kamar ba mutuwa, jibi kenan fa, za'a kai ko”.
“In sha Allah kuwa”.
Cewar Mamy daga nan ya mikawa Mammynsa waya suka ci gaba da hira.
Russia Mascow.
A hankali ta buɗe kofar ta fito falon, sabida wani irin kishin ruwa da takeji.
Saɗab-saɗab haka take tafiya a hankali duk tasan da wuya in yana gidan.
A hankali ta sauke numfashi tare da wucewa kitchen kai tsaye, goran ruwa mara sanyi ta ɗauka, tare da ɓalle marfin, kana ta kafa baki sabida sosai takejin kishin,
Saida ta shanye rabin gorar kana, a hankali ta ajiyeshi kan fridge,
ido ta zuwa window'n kitchin tana mai kallon yanayin sararin samaniya da tayi dib alamun da yiwuwar a tsula musu sanyi harda dusan ƙanƙara.
Jikin window ta matso tare da manna tafin hannunta jikin Glass din.
Ido ta lumshe a hankali tana mai tuno kalamansa.
“Chocolete yafi min mace sau dubu”.
Ta rasa manufarsu.
Wa zan tambaya ya min ƙarin bayani a kai.
Da sauri ta juya ta nufi falo sabida amsar da zuciyarta ta bata,
“Aunty Fauziyya D Sulaiman ta tabbatar zata faiyace mata zare da abawa”.
Inda tabar wayarta a safiyar yau din ta zauna aiko tana nan.
Hannu tasa ta ɗauka.
Tana ɗagawa kuwa kiran Aunty Fa'iziyya na shigowa.
Cikin happy ta amsa kiran tare da cewa.
“Assalamu alaikum my Aunty yar halas ki ƙi ambato, wlh dama yanzu ke zan kira”.
Cikin kulawa da mutuntaka Aunty Fauziyya tayi murmushi mai kama da dariya tare da cewa.
“Ayyah Jannart na nima kina raina kwana biyu bamuyi mgn ba, ya gida ya maigidanki ya sanyin Russia,”.
Cikin happy tace.
“Kai my Aunty duk ni ɗaya toh duk komai lfy”.
“Toh kefa ya jikinki bai tashi dai kam ko kin fara shan mgninki”.
“Alhmadullilah da sauki, my Aunty nayi kewar aikina, eh zan fara”.
Cikin sauke numfashi Aunty Fauziyya tace.
“Aikin kima damu duk munyi missing naki, more especially nida Salman da Aysha lawal yanzu Asiya ce ke aikin tare da Salman kullum sai sunyi faɗa ita ta nuna mishi tafishi iyawa shi kuwa yace kin fita iyawa”.
Murmushi mai sauti tayi tare da cewa.
“Ina nan dawowa verry soon”.
“In mijinki ya yarda ko”.
Cikin sauri tace.
“Zaima yarda shi ne ruwansa ma dani”.
Sai kuma tayi saurin cewa.
“Yauwa my Aunty Ina da tambaya”.
Wanda fadin hakan ne ya hana Aunty Fauziyya samun damar yi mata izina kan furucinta na shi mema ruwansa da ita.
Cikin nitsuwa da halin girma tace.
“Na'am ina jinki my Jannart”.
Numfashin shaka ta ɗan sauke tare da gyara zamanta,
Jujjuya kanta tayi ta kalli gefen hagu da damanta kamar dai mai tsoron ko akwai wani a gefenta.
“Uhumm ina sauraronki Jannart! Menene tambayar?”.
A hankali tace.
“Uhummm yauwa dama ba wai...”.
Sai kuma tayi shiru tana nazarin yadda zata furta kalmar”.
“Damaba wai me”.
Aunty Fauziyya ta kuma tambayarta
Tare da daurawa da cewa.
“Jannart kada ki damu gaya min me kike son sani in Sha Allah zan sanar dake matuƙar na sani”.
Numfashi ta kuma fesarwa kana tayi ƙasa da murya tare da cewa.
“Uhum My Aunty wai kina Shan Chocolate kuwa”.
Shiru Aunty Fauziyya tayi tana nazartar kalamanta wanda kuma a take ta tuno kwanaki suna mgn Jannart ɗin ta ce mata mijinta bai damu da abinciba kullum chocolate ya bawa amanna'
To me take son sani, hakan data tuna ne yasa a hankali tace.
“Yess ina ci”.
Cikin jin dadi tace.
“Yauwa my Aunty to wai mace nada wani daɗi nada banne?”.
Anzo wurin Aunty Fauziyya ta faɗa a ranta a fili kuwa kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Dadin na musamman ma kuwa musamman a wurin na miji, ke bakya cin chocolate ne?”.
Da sauri tace.
“Eh ni tun ina ƙarama Daddyna baya barina inci chocolate.
Amman my Aunty wai chocolate yafi mace daɗi”.
Da sauri Aunty Fauziyya tasa tafin hannunta ta rufe bakinta dan dariyar dake gab da kwabce mata,
Zuwa yanzu kuma ta fahimci Jannart abunka da kwakwalwar marubuciya mai cike da falsafa.
Cikin tausasawa tace.
“Waya ce miki hakan?”.
Cikin sanyi tace.
“A'a bani aka gayawa hakaba naji ana gayawa wani hakane a waya?”.
“Waya faɗi hakan?”.
Ba tare data shiryawa amsaba taji bakinta yace.
“Naan”.
Da sauri Aunty Fauziyya tace.
“Waye Kuma Naan”.
Da sauri ta jujjuya kanta cikin yanayin sirrintawa musamman tuno mgnar sa na cewa meyasa bazata sirranta sirrin mijinta ba, a hankali tace.
“Wani maƙocinmu ne matarsa ƙawata”.
Tayi mgnar cikin waskewa da ganin bai dace ta fadi waye Naan ɗinba, sai daifa ta mance da marubuciya take mgn.
Ita kuma Aunty Fauziyya ta gane sarai amman sai ta tayata sirranta sirrinta dan tasan Jannart bata taɓa yin ƙawaba a rayuwarta kana a hankali ta gyara zama tare da cewa.
“Amaryace matar tasa”.
Da sauri tace.
“Bamaya sontama akayi musu auren”.
Cikin hikima tace.
“Toh suna kwana tarene,”.
Cikin nauyin mgnar tace.
“Sau biyar kawai suka taɓa kwana daki ɗaya”.
Miƙewa Aunty Fauziyya tayi ta wuce bedroom ɗin ta tare da cewa.
“Toh ya taɓa kusantan tane?”.
Shiru tayi alamun nazari.
“Hello Jannart bakya jina”.
“A'a ina jinki”.
“Nace ya taɓa kusantan tane?”.
Da sauri tace.
“A'a”.
Tsaki taja tare da cewa,
“Toh ita ƙawar taki macece kuwa?”.
Da sauri tace.
“Eh macece mana”.
Cikin yanayin faɗa tace.
“Muna mace dai Jannart, mace zata yardane tayiwa mijinta riƙon sakainar kashin da har zai kwatanta ta da chocolate da zai kasance tamkar maɗaci in an misaltashi da macce, anya kuwa Jannart kawar kin nan tasan me ake nufi da mace da zaman aure da kuma haƙin miji akan mata da hakkin mace akan mijinta.
Shin nakashesshiyace bata da ƙirjin da zaija hankalin na miji ko mazaunan da zata iya gigitasa dasu.
Koka ƙazamace koko bata kasance masa mace mai kula da lamuransa bane”.
Cikin sanyi tace.
“Duka ba haka bane my Aunty, shi ba ruwansa ne da ita sai dai in bata da lfy zai kula da ita, kuma shima in baida lfy yanada rakin narke mata bayason tayi nesa dashi. Kuma tace kwanakin duka sai ya rinƙa yi mata wasu irin abubuwa masu bada tsoro jiya kwana yayi yana kuka data gudu daga ɗakinsa sabida yadda yake shige mata jiki kuma jiya har rantsewa yayi tayi wai yana sonta, ita kuma tana ce mishi bata sonshi”.
Da sauri tace.
“Toh Jannart kice mata ta nemi yafiyarsa domin ta kwana cikin fushin ubangiji da tsinuwar Mala'iku ki shaida mata mace ta gari bata gujewa buƙatar mijinta shimfidarsa,
Sannan shawara mahimmiya ta tabbatar da soyayyarsa gareta ta gamsu da sonta da ya faɗawa cikinta tuni sai dai ta sashi a hanyar da zai san ita mai cikekken enci ce kafin ta sallamasa budurcinta, hakan kuma bazai faruba har sai in ta juye zuwa mace mai jan hankali ta gigitashi da surarta taja hankalinsa ta yadda zai gane kurensa a furucinsa kirsa, da kisisina, tsabta, shogowa, ki koya mata irin shogoɓarki da ke taki halittacema.”
Cikin wayon wai ta kauda hankali Aunty Fauziyya a kanta tace.
“Inama maɗa mgnar ki in ta shigo zan saka mata taji”.
Murmushi tayi tare daci gaba da koyar da ita dabarun jan hankali da gigita lafiyyan namiji da samarwa kai daraja.
Saida kuɗinta suka karene suka ƙare wayar.
Sosai kuwa ta ɗauki zazzafan darussan da anka koyar da ita.
Ido ta lumshe tare da fesar da numfashi,
da sauri tace
“Laa Abba ma yayi ta kirana ashe”.
Da sauri ta danna masa kira,
Bugu ɗaya kuwa ana biyu ya amsa.
Cikin kulawa so ƙauna yace.
“Jannart ya gida ya jikinki”.
Cikin jin dadi tace.
“Alhamdullah Abbana jikina da sauƙi ina su Hafiz Ina Aunty Dija”.
.“Duk suna lfy, kina dai shan mgnin ki ko?”.
Da sauri tace.
“Eh Abba”.
Dariya ya ɗanyi tare da cewa.
“A'a kam ban yardaba bakya sha, ai mijinki ya gaya min bakya son shan mgnin da cin abinci.”
Da sauri tace.
“Toh Abba zan kiyaye”.
Cikin jin dadin sauƙin kanta yace.
“Yauwa ɗiyata. Toh kuma meyasa kike gudunsa kawai dan zai baki mgni”.
Da sauri ta jujjuya kai tamkar tana gabansa.
Kana a hankali tace.
“Abba ni badan bada mgnin nake gudunsa ba, Shima irin Yah Junaid ne”.
Cikin kauda kai da kunya duk da yasan ita bada wata manufa tayiba tunda yasan tabbas Jannart bata san cikekken rayuwan aureba dan a kife akabar rayuwarta,
Ba ƙawa ba amini ga tsaro gashi ko ɗan abun social media nan saida ta fara zuwa aikine aka barta ta farin whatsApp kuma ko shima bata da group ko ɗaya,
Bata karance-karance littatafai bare tasan wani abu an hana Mom shaƙuwa da ita, ta azo a gani,
Ita rayuwar ta zaman auren normal zamane.
Toh Amman Alhamdulillah ko shima baya son Dr Rayyern ya maida mishi ita bazawara tunda yana sane da sharaɗinsu.
Haka yasa cikin sanyi yace.
“Kada ki damu Jannart ai shi ba kamar Junaid bane,
Amman kada ki yarda dashi”.
Ba tare da fahimtar sa ba kawai tace to.
Daga nan sukayi sallama.
Jin ana kiran sallan mangarib ne yasa ta miƙa ta nufi ɗakinta.
Shi kuwa Rayyern daga asibitin wani cafe ya Kuma zuwa yasha coffee kafin ya wuce masallacin.
Daga nanne kuma bai dawo ba saida akayi sallan isha.
Daga can ya biya ya saya musu abincin kamar yadda ya saba.
Takwas dai-dai ya shigo falon.
Shiru babu motsin komai kai kace babu mutum a gidan.
Cikin kasala ya rufe gajiyayyun idanunsa kana ya ajiye ledan kusa dana safiyar yau wanda yaga gashi bata taɓa shi ba,
juyowa yayi ya kalli ƙofar ɗakinta kana a hankali ya taɓe bakinsa sannan ya wuce bedroom ɗinsa.
A hankali ya fara zare kayan jikinsa kamar yadda ya saba.
Kafin ya shiga bathroom dagashi sai boxes.
Wanka yayi da ruwa mai zafi sosai.
Kana ya sako bathtub mai taushi.
Wani irin masifeffen gajiya, kasala, wahala, da bashin baccin daren jiya da baiyiba ne duk sukayi mishi taron dangi.
Karamin towel ɗin dake hannunsa yasa ya tsane jikinsa.
Kana ya shafa mai da fesa turare a jikinsa.
A hankali yako zuwa gaban sip ɗinsa.
Wani towel sabo dal pink ya jawo.
Bathrobe din ya zare a jikinsa tare da saƙalashi kana,
ya ɗaura towel ɗin.
A hankali ya juyo ya nufi gado.
Yana hamma ya zauna tare da rage hasken ɗakin.
Cikin wani irin sanyi ya kwanta a kife rub yayi kan cikinsa tare dayin fuskar tausayi.
Lokacin ɗaya bacci yayi awon gaba dashi.
Ita kuwa Jannart jin yunwa na kwakularta ne, yasata fitowa a hankali kitchin ta wuce.
Tupa da inabi ta ɗiɓo a plate kana ta dawo ɗakinta. Kana ta ɗebi gumbunan da garukan dakan cokali ɗaɗɗaya ta da masu da madarar ruwa, ya zama kamar fura da nono kai ta kafa ta shanye su tas. Kana taci gaba da cin inabin,
Tanaci kuwa ba jimawa tayi bacci.
Washe gari ranar al'hamis.
Zaune yake a falon cikin shirinsa na fita.
Ledodin ya zubawa idanu.
Wanda harda na yanzu da aka kawo musu.
Siraran idanunsa ya zubawa ƙofar ɗakin nata,
Kana yana mgnar zuciya.
“Uhummm bataci na jiyaba da safe da dareba sannan yanzuma gashi bata fitoba.”
Hannunsa yasa bisa ledan magungunan ta da sauran alluranta biyu da anyi jiya in anyi yanzu an gamsu.
Gashi ba'a tsallakewa duk sauran ma sun zuɓe yanzu sai an sake daga forko.”
Kwaffa yayi kana a fili yace.
“Gata da shegen tsoro da raki”.
Kanshi ya jinjina kana ya miƙe jiki a mace kitchin yaje plate da spoon ya ɗauko yazo ya ɗan zuba abinci sama-sama ya ci.
Kana ya koma kitchin chocolate nasa ya ɗauka kwalba biyu kana ya fito ya nufi asibitin.
Dan yanzu aikin ya ɗau zafi dan dudu wata biyu ne ya rage musu,
Sunci fiye da rabin lokacin su shiyasa yanzu ba sauki.
Ita kuwa Jannart sai kusan bayan azahar ta fito falon.
Tea ta haɗa mai kauri tasha tare da ɗebo inabi tazo ta konta a falon tanasha tana kallon tv.
Yoh inda sabo ai dama haka suke zama.
Ƙarfe shida dai-dai Suka fito asibitin.
Kai tsaye masallaci ya nufa kamar jiya.
Yana kan hanyarsa ne kiran Azeez ya shigo masa waya.
Ganin yadda aketa kira