Showing 138001 words to 141000 words out of 350584 words

Chapter 47 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

maganan cikin dan nuna tausayawa.

Abba Kabir kuwa da sauri yace.
“Subahanallah Rayyern din?”.

Kai ta gyaɗa kamar tana gabanshi.
Sai kuma ta daura da cewa.
“Eh Mamynsa nata kuka da Baba Mauɗo”.

“Innalillahi Jannart meyasa baki gaya min ba”.
Cikin sanyi tace.
“Abba na manta ne”.
Cikin faɗa yace.
“Jannart ki mance ciwo da lfyar mijinki? Kada ki sake yin haka kul kinji ko?".
Cikin biyayya tace.
“Toh Abba"

Barrister Kabir din kuwa dan gyara zamansa yayi, tare da cewa.
“In sha Allah da yamma zan zo, akwai wani abu da kike buk’ata ne?”

Kai Jannart din ta jinjina, kana cikin sanyin murya tace.
“A’a Abba babu abunda nake buk’ata.”

“To shikenan sai nazo.”
Daga haka sukayi sallama.

Bayan ya katse wayarne kuma ta mik’e, tare da fitowa waje suka shiga Kitchen da Mamy.

Da yamma misalin ƙarfe biyar da da rabi na yamma.
Abba da Barrister Kabir din Suka shigo a jere.
Kasancewar shigowar Barrister’n ya samu Abban a wurin Baba Mauɗo ne.

Ganinsu ne kuma yasa, Mamy yin murmushi, fuska asake tace.
“Sannu da zuwa Barrister".

Shidin ma Barrister Kabir din murmushi yayi, kana cikin mutuntaka yace.
“Yauwa sannu Hajiya, fatan na sameku lafiya ya mai jiki?”

“Lafiya k’alau Barrister, jiki kuma Alhamdulillah dan yana ta samun sauki, ya iyalai?”

“Masha Allah Iyalai Alhamdulillah.”
Ya fad’a adaidai lokacin da yake zama akan kujera.

Yayinda ita kuwa Mamy juyawa tayi kaitsaye ta nufi, d’akin Jannart tana cewa.
“Jannart ga Abbanki yazo”.

Jin abunda Mamyn ke fad’ane yasa Jannart dake zaune, saurin mikewa tsaye tare da nufo falon tana gyara mayafin doguwar rigar jikinta.
Murmushi Mamy tayi tare da juyowa.
Ta nufi falon ita kuwa ta rufa mata baya.

Suna fitowa ta nufi kusa da Abban tana murmushi.
“Abba sannu da zuwa”.
Tace tana zama agefenshi.

Yayinda ta hango Abban Rayyern kuma yana haurawa sama.

Mamy kuwa Dinning area ta nufa.
Goran Ruwan sanyi dana Nutri milk tasa a ɗan ma dai-dai-cin tray da cup, kana Akan santer table ɗin dake gabanshi, ta ajiye tray tare da zama bisa kujera.
“Sannu Barrister Bismillah ga ruwa”.
Ta faɗa cikin kulawa.

“To nagode.”
Barrister Kabir ya amsa.
Tare da daukan ruwan ya d’ansha kadan.

Jiyo alamun ana sauƙowa ne kuma, yasa Mamy maida kallonta ga stairs din.
Ganin kuma Rayyern ne yake takowa a hankali, yana sanye da wata tattausar jallabiya baƙa mai masifar sheƙi.
Irin mai guntun hannu ne jallabiyar,
gabanta kuma ta sama ank’awatasa da aninaye.

Abba na biye dashi a baya.

Sosai ya ɗan rame duk da jallabiya ce a jikinsa, kuwa amma ramarsa ta ɗan fito, sai wani irin fari da yayi yayinda sajenshi yake ɗan hargitse.

Cikin jin daɗi Mamy tace.
“Alhamdullahi lallai yau kam jiki da sauƙi, tunda har Babana zai sauƙo ƙasa."
Jin hakane yasa Barrister Kabir juyowa, ya kalli gefen damanshi ganin Rayyern ne, da yadda yake tafiya a kasalance alamun ba isashen ƙarfi ajikinsa ya sashi cewa.
“Ayyah Alhaji da ka barshi ai, Idan yaso ni saina haura in ganshi, gaskiya yaji jiki”.
Dai-dai lokacin kuma suka iso kan steps ɗin ƙarshe.
Cikin yanayin gajiya da maida nufashi ya zame, ya zauna kan step na biyu tare da jingina kansa, da jikin ƙarafunan gefe da gefen steps din, cikin lumshe ido yace.
“Abba na gaji.”

Ya ƙare mgnar yana kallon tsakiyar falon.

Ita kuwa Jannart jin muryarsa ne, da kuma abinda Mamy da Abbanta suka fadane, yasa ta ɗago kanta tare da ware manyan idanunta,ta kalli hanyar sauƙowan.
Wanda yanzu kusan satinta uku a gidan, amman bata taɓa zuwa ko kusa da wurinba.
Ido cikin ido sukayi dashi,
Wanda hakan yasa tayi maza tayi ƙasa da kanta.
Tare da lumshe idanunta tabbas ya rame sosai fuskarshi tayi wani irin haske.
Sajenshi ya hargitse kaɗan alamun babu isasshen ƙarfin jiki da nitsuwar lfya.

Dib-dab-dib-dab haka taji bugun zuciyarta na harbawa.

Shi kuwa Rayyern fuskarshi ya tsuke tare dayin mgnar zuci.
“Eh dole mana a Barka ka haura sama, tunda gaka ubana, kasan da ka gani ka karanta duk bai isheka ba ai, sai kaga makwancina".
Mtswwww yaja ɗan gajeren tsaki cikin bakinsa.

Mamy kuwa cikin jin daɗi tace.
“Sannu ko Babana.”
Kai ya gyaɗa mata cikin sanyin jiki.

Abba kuwa gefenshi ya ɗan ratsa tare da cewa.
“Toh huta sai ka ƙaraso ko”.

Kai ya kuma gyaɗawa.

Barrister Kabir kuwa gyara zamansa yayi tare da cewa.
“Rayyern ya jikin naka?”.
Da sauri yace.
“Alhamdulillahi ni nama worke.”
Murmushi Barrister yayi domin ya gane cewar.
Har yanzu Dr.Rayyern bai yarda dashi ba, asalima zarginsa yakeyi.
Cikin kulawa yace.
“Masha Allah. Haka ake so.
Allah ya ƙara lfy da karfin jiki.”
A takaice yace.
“Amin.”

Shi kuwa Abban Rayyern da Mamy cikin jin daɗi sukace.
“Amin Amin Barrister mun gode matuƙa, Allah ya bar zumunci.”
Amin yace yana mai kallon Jannart data sunkuyar da kanta ƙasa, tana wasa da wayar hannun ta.

Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
“Toh Alhaji bari in wuce gida, Allah ya ƙara sauƙi.”

Miƙewa shima Abban yayi tare da cewa.
"Amin Amin Barrister mun gode sosai”

Daga nan suka fita tare.

Suna fita itama Jannart ta miƙe ta nufi ɗakinta.

Da wani irin masifeffen kallo Rayyern ya bita dashi, kallon da yafi kama da harara.

Mamy kuwa shi ɗin ta zubawa ido, Jin ana kallonsa ne kuma, yasa ya ɗan juyo ya kalli Mamy ganin yadda ta tsareshi da ido ne, yasashi kwaɓe fuskarsa tare da miƙewa ya dawo kan doguwar kujera.
A hankali ya kwanta tare da ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya kana
Yace.
“Mamy Riyyim fa?”
Numfashi ta sauke tare da cewa.
“Ya tafi yi mana cefene shida Hadi.”

Kai ya gyaɗa tare da fuskantar TV.

Ita kuwa Jannart tana shiga part dinta.
Wonka tayi tare da al'wala kana ta fito dan magriba ta gabato.

A falon kuma a tare Ramadan da Riyyam-nsra da Abba suka shigo.
Gaba ɗayansu riƙe da manyan ledodi.
Kitchen suka wuce.
Kasan cewar kayan miyane.
Yasa duk suka diresu nan.
Kana duk suka je sukayi al'wala.
Shi kuwa Rayyern dama ya koma ɗakinsa dan yin wonka.

Bazai iya zuwa masallaci ba, dan d’an haurowan da yayi duk jikinsa rawa yakeyi.
Haka yasa yayi salla a ɗakinsa.
Su kuma suka wuce masallacin.

Basu dawoba saida sukayi isha'i.

A haka dai Rayyern yayi jinyar ɗan motsawa kaɗan da ciwon cikinsa yayi.
Cikin ikon Allah cikin mako ɗaya ya samu lfy, sosai yanzu ƙarfin jikinsa ya dawo.
Yau Monday har asibiti yaje sai dai sam bakinsa ba daɗi shi yasa bai iya cin abinci.

Jannart kuma bata wani ganinsa bare wata mgn ta haɗa su.

A can sashin Alhaji idi Saleh Dakata kuwa.
Duk yadda Barrister Kabir ya zaci takun yayan nasa ya wuce zatonsa.
Hakan yasa ya tsananta matakan irin bi diddigi.
Da taimakon Baba Ado da Ashiru.

Duk yadda yaso gano ainihin zuciyar yayan nashi ya gaza ganewa.

Yah Azeez kuwa sosai ya shiga tashin hankali.
Wanda saida yayi jinyar ciwon da tashin hankalin yasakar masa.

Mom da Abdul kuwa gaba ɗaya gidan ya juye musu.
Domin abun ya musu yawa, ga Daddy da hawanjininsa ke yawan tashi, bini-bini ciwon kai an tafi asibiti.

A can tashar Arewa 24 TV kuwa.
Gaba ɗaya Aisha Lawal da Aunty Fauziyya D Sulaiman da Hajia Rabi'ah, dama sauran ma'aikatan hankalinsu yayi matuƙar tashi, da jin labarin ɓacewar Jannart.

Musamman Salman da gaba ɗaya ya gigice ya ɗimauce.
Dan abun ya daki zuciyarsa sosai, hakan yasa ko aiki yanzu ya dena zuwa, dan shi a zatonsa akan shirinsu aka sace ta sai yake gani shine next target din masatan.
Ganin tashin hankalin da yake cikine kuma yasa.
MD neman Barrister Kabir yayi mishi bayani.
Dole yazo har gidansu shida MD.
Nan sukayi mishi duk bayanin abinda ke faruwa.
Toh Alhamdulillah ya samu nitsuwa sai dai kuma ya shiga ruɗani.
Nan MD ya gyara zamanshi tare da cewa.
“Yanzu dai sai ka kwantar da hankalin ka.
Ka fara zuwa aiki”.
Da sauri yace.
“Toh Ni da waye zamuyi aikin?".
Cikin sauƙe numfashi MD yace.
“Yanzu zamu bawa Asiya riƙon kwaryar shirin zuwa, lokacin da komai zai dai-dai-ta.”
Cikin tarin ruɗani yace.
“Toh ita Jannart fa?”
Da sauri Barrister Kabir yace.
“Kada ka damu da mgnar Jannart komai zai dai-dai-ta da izinin ubangiji.”
A hankali yace.
“Toh Allah ya yarda.”
Amin Amin sukace kana suka sallameshi suka tafi.


A gajiye ya dawo cikin gidan.
Ko yanzun fitowarsa kenan daga cikin mota, Yayinda Usman PA ke riƙe da marfin motar.
Cikin kulawa yace.
“Sannu”.
Kanshi kawai ya gyaɗa kana ya raɓa ta gefen Usman ya wuce.

Shi kuwa Usman binshi a baya yayi, riƙe da jakar laptop dinsa da ɗaya wayarsa, sai wasu files dake hannunsa.
A hankali ya kalli Baba Mauɗo dake yi masa ya jiki, fuska ya ɗan sake tare da cewa.
“Jiki da sauki Baba Mauɗo”.

“Masha Allah. Allah ya ƙara sauki”.

“Amin Amin.”
yace tare da wucewa.

PA na biye dashi a baya.

“Wa alaikassalam”.
Mamy tace lokacin da suka shigo tare da sallama a bakinsu.

“Masha Allah Babana sannu da dawowa ya Office”.
Mamyn ta Kuma faɗa.

Shikuwa Rayyern numfashi ya ɗan fesar tare da cewa.
“ALHAMDULILLAH Mamy”.
Juyowa tayi ta kalli PA dake gaidata tare da, ajiye kayan uban gidan nasa agefenta.
“Lfy lau Usman ya Umma da jiki”.
Mamyn ta amsa masa tana d’an murmushi.

“Jiki da sauƙi, tace ma in gaidaki”.
Ya faɗa yana kallon Rayyern ɗin daya nufi Dinning area.

Kai ya ɗan juyo tare da cewa.
“Riyyam fa, nasan Ramadan kam mun barshi a asibiti”.

“Riyyam yana sama yanayi musu gyare-gyare.”
Murmushi Usman yayi tare da cewa.
“Toh wai sai yaushe zai koma ne, yanzu fa yafi wata ɗaya da zuwa har ya shiga na biyu, kuma banga yana wani aikinba.”

Da sauri ya kalli Riyyam-nsra dake saukowa yana cewa.
“Toh P.A ko dai korata zakayi ne, wai dan Allah ma me na tare maka ne, nafa gane tun a jirgi ba sona kakeyi ba, to yawo nazo ko kana da mgna?".
Ya ida mgnar yana turo baki.

Dariya sosai PA yayi domin dama akwai yar tsama tsakaninsu cikin dariya yace.
“A'a ni kuma in koreka, to a kaina kake ne?"

Cikin taɓe bakinsa da salon ƴan samarin TIKTOK da sukafi kama dana ƴan daudu yace.
“Toh waya sani”.
Murmushi Usman ya kumayi tare da cewa.
“Mamy ni bari in wuce gida”.

“Toh ka gaida Umma ko Usman”.
“In Sha Allah zataji”
Ya bata amsa.
Har yaje bakin ƙofar fita kuma ya juyo tare da cewa Riyyam-nsra.
“Nest week fa zamu wuce China, dan haka ka shirya mu sauƙeka a ƙasarku.”
Ya ƙare mgnar cikin tsokana.

Shi kuwa Riyyam-nsra murmushi yayi tare da cewa.
“Ayyah to dan Allah ka bari in zamewa Hamma Rayyern PA'nsa mu tafi tare”.

Dariya Usman yayi kana ya juya ya fita.
Shi dai Dr Rayyern bai kulasu bama,

Shi kuwa Riyyam-nsra System ɗin da wayar ya ɗauka ya koma sama dasu.

Mamy kuwa shiru tayi ta kasa kunneta can kitchine, dan tasan Jannart na ciki taga kuma Rayyern ya nufi can.


A hankali ya sako ƙafarsa ka step ɗin Dinning area.
Ƙamshin da yake jin ya ɗan shaƙa.
Ba tare da tunanin komai ba ya kutsa kai cikin Kitchen din.

Ita kuwa Jannart dake tsaye miyar taushe da man shanu take haɗawa, Yayinda tamaida gaba d’aya nutsuwarta, ga aikin da takeyi din, wanda hakan yasa ita sam bata ma lura da shiba.


Shi kuwa Rayyern yana shigowa cikin kitchine din, idanunsa suka sauk’a akan bayanta.
Wanda dogon gashin kanta ya sauk’o har tsakiyan gadon bayan ta, kasancewar kuma turkish gown ne ajikinta, shiyasa tayi kyau sosai yaudin, duk wani kuruciya da yarintar ta, I mean innocent dinta ya bayyana.

Kallo d’aya yayi mata ya d’auke kansa, tare da tab’e bakinsa, batare kuma da ya aiwatar da abunda ya shigo dashi cikin kitchine dinba, ya juya tare da ficewa, Kai tsaye ya nufi falon Abbansa.


Da sallama a bakinsa ya shiga.
Gefen Abban nasa ya zauna.
Bayan sun gaisane kuma ya ɗan gyara zamanshi, kana cikin nitsuwa yace.
“Abba batun tafiya ta China fa na gama komai, Insha Allah Ranar Monday mai zuwa zamu tafi.”

Cikin zuba mishi ido Abba yace.
“Rayyern baza’a bariba kuma, sai ka kara samun lfyar jikinka?”

Dan guntun murmushi Rayyern din yayi tare da gyara zamansa yace.
“Abba ba komai nayi sauki ai zan iya zuwa, kaga in mun je ɗin ma ba dadewa zamuyi ba, dududu bazan fi kwana ashirin ba zuwa da biyar zan dawo”.

D’an jim Abban yayi, kana cikin shakka yace.
“Kai gsky ni dai ban gamsuba.”

Da sauri yace.
“In sha Allah Abba ba komai fa, zanje lafiya nadawo lafiya.”

Kai Abban ya ɗan jinjina tare da cewa.
“Kayi shirin tafiyar ne?"
Da sauri yace.
“Ai na gama komai ma, nida Usman zamu je.”
Akaro na barkatai Abban ya sauke numfashi tare da cewa.
“Toh Allah ya kaimu, ya kuma bada sa’a.”

“Amin Amin.” yace.
Jin an fara kiran sallan magriba ne kuma, yasa duk suka mike sukayo al'wala suka wuce masallaci.


Yau jumma'a. Bayan an taso sallan jumma'a ne, kuma suna zazzaune a falon suna cin abinci.
Dan duk basu ci abincin rana ba.
Sabida gudun kada su makara.


A nitse ya turo ƙofar falon ya shigo.
Tare da sallama a saman lips ɗinshi, yayinda Usman PA kuwa, ke biye dashi a baya.

Riyyam-nsra ne ya fara mgn ba tare da ya haɗiye danwaken da yasa a bakinshi ba yace.
“Hamma Rayyern Mammy tace in gaisheka da jiki.”
Cikin alamun gajiya da ɗan yunwa ya gyaɗa kai.
Yana mai kallon Mamy da Usman da suke gaisawa.
Kana Mamy na sawa Usman din danwaken a plate.

Shi kuwa Usman kanshi ya ɗan juyo ya kalli Jannart dake bare dafeffen kwai.
“Hajia Barka da yamma.”

k’asa ta d’anyi da kanta, batare kuma da ta d’ago ta kalleshi ba, cikin mutumtawa tace.
“Barka dai PA ya gida.”
Tayi maganan tana bare kwan tana sawa a plate din da Mamyn ta turo mata.
Kana ta miƙa mishi.

Ramadan kuwa baki ya ɗan bude tare da ɗan yin shishitan yaji yace.
“Kai yajin nada zafi my Aunty ƙara min salat da tumatur da kwai ɗin zai ɗan kashe yajin.”
Ya ƙare mgnar yana turo mata plate din, murmurshi tayi tare da cewa.

“Toh sha ruwa kafin nan”.
Ba musu ya ɗauki cup din ruwa dan suna masifar tsoron yaji.

Riyyam-nsra kuwa sai ci yake yana tande baki kamar ɓera a gari.

Shi kuwa Rayyern a hankali ya ɗan muskuta tare da kwaɓe fuska.
Ido Mamy ta zuba mishi.
A hankali yasa hannunshin ya shafa cikinsa kana yace.
“Yunwa.”
Yayi mgnar can ƙasan makoshin sa.
Kai ta jinjina tare da jawo plate alamun zata zuba mishi.
Da sauri ya jujjuya kanshi tare da nuna mata Ramadan daketa shishitan.
“Abu sai kace cimar Mayu,mutun yanaci yana gigicewa.
Ai ni in nasa wannan a bakina suma zanyi Mamy.”
Yayi mgnar yana miƙewa tsaye.

Murmushi Mamy tayi.
Ita kuwa Jannart lips ɗinta duka biyu ta haɗe ta ciza.
Saboda yayi mgnar da ƙarfi kuma da gayya.
hakan yasa acikin ranta tace.
“Uhum ni dai ba mayya bace ato.”

Shi kuwa fara haurawa sama yayi tare da cewa Mamy.
“Please Mamy abu mai ɗan ruwa-ruwa.”
Ba tare da ta kulashi ba.
Ta kalli Jannart tare da cewa.
“Kici mana Jannart.”

Da sauri ta jujjuya kanta tare da cewa.
“Na koshi Mamy sai anjima.”

Juyowa sukayi suka kalli ƙofar ɗakin.
Jin ana bubbugawa.
Da sauri Riyyam-nsra dake ta hanyar kofar ya mike tare da zuwa ya buɗe.
Fahad ne telan Mamy da ta bawa kayan Jannart.
Cikin sauri Riyyam-nsra yasa hannunsa ya amsar masa jaka ɗaya tare da cewa.
“Bismilla shigo ciki, Mamy Fahad ne.”
Yayi mgnar yana shigowa Fahad na biye dashi a baya, yana dariya tare da rufe ido.
Da sauri Mamy ta juyo tana kallon Fahad tare da cewa.
“A Allah mai iko al'ƙawarin tela bai zuwa masallaci, nanfa ace min mako, biyu, har zance yayi yawa ma, amma nai shiru sai gashi kuma sai yau ka bullo.”
Dariya mai sauti Fahad din yayi tare da ajiye jakar hannunshi.
Kusa da inda Riyyam-nsra ya aje na hannunsa.
Kanshi ya ɗan shafa tare da zama gabanta kana anutse yace.

“Wlh akasi aka samu zazzaɓi ne ya...”

Da sauri Ramadan ya katseshi da cewa.
“Dan Allah kada ka daurawa kanka ciwo Fahad kai dai kawai kayi shiru.”

Dariya yayi tare da cewa.
“Toh Hajia buɗesu ki ganima zaki sha, mamakin kyansu da tsarinsu.”

Murmushi Mamyn tayi tare da cewa.
“Toh Jannart tattare plates din nan.”

Murmushi Jannart din tayi tare da fara tattare wurin.
Ita kuwa Mamy Fahad din ta zu bawa danwaken tare da sa mishi duk kayan haɗi.
Gyaran zamanshi yayi tare da fara ci.
Yayinda Jannart kuwa ta gyara wurin.

Riyyam-nsra kuwa kayan ya fara jawowa da sauri Fahad yace.

“A kai malam dakata ya kake figosu haka? a dinke a goge suke da ko wanne yana haɗe da ɗan uwansa cikin leda.”
Ya ƙare mgnar yana matsar da plate din gabanshi ya matso.
Kana ya fara fito dasu daya bayan daya saida ya fiddasu kab, kala ashirin da biyar.
Shadda biyar lace biyar atampa biyar material biyar shadda lace biyar.
A hankali ya fara ware ɗinkin wata shadda pink color, wacce akayiwa ɗinkin fent wok mai masifar kyau dan doguwar rigace.
“Masha Allah gsky ɗinki yayi kyau”.
mamy ta faɗa tana kallon rigar atamfar da ya kuma warewa.
Irin ɗin kin nanne na duwatsun shuwariski masu masifar kyau da akabi da kelleyen kolliyar.
Kasan cewar atampar koriyace sosai take daukar ido.
Medata yayi ya ninke tare da jawo wani shadda lace, mai azabar kyau pink and purple mai ɗan karen tsada.
Sai wani lace ya kuma fiddasa kalan yellow and orange, anyi masa ɗinkin gariyar mata mai masifar kyau.

Ita kanta Jannart kai ta jinjina dan ta gamsu da kalar kayyakin, da zafafan ɗinkuna na zamanin da suka samu.

Cikin jin daɗi Mamy tace.
“Kai sannu da aiki Fahad na huce, dan gaskiya kamana dinki mai kyau, ninkesu kawai medasu leda, dama
nasan ɗinkinka ai babu haifi”.

Murmushi yayi cikin jin daɗi kana ya medasu cikin leda.
Tare da ci gaba da cin danwaken.

Cikin jin daɗi Jannart tace.
“Gsky ɗinkuna sunyi kyau.
Allah ya saka da al'khairi Mamy.”
Amin Amin tace tare da kallon Riyyam-nsra tace.
“Yauwa ɗauki kayan kai matasu Bedroom in ta shigo sai ta kimtsasu.”
Da sauri yace.
“To.”
Kana ya fara jidansu.

Ita kuwa Mamy cikin kula tace.
“Nawane sauran kuɗinka Fahad?”

Gyara zama Fahad din yayi, tare da jinjina kansa yace.
“Ba ranan Hadi ya kai min 70k ba da fari kuma kin bani 50k
Yanzu saura 30k kenan Hajjajo.”

Cikin dariya Mamy tace.
“A'a fa Fahad kuke jin tausayin mutane mana kana nufin dubu dari da hamsin kenan a ɗinki kala ashirin da biyar.”
Da sauri yace.
“Allah ko Hajjajo ɗan ma kece kuma nasan ba adawo dasu da wuriba.”

Kai ta jinjina tare da cewa.
“Toh ba matsala Ramadan yi mishi transfer.”
Cikin sauran ɗan shishitan yace to.
Kana shi kuma Fahad ya fara gaya mishi ac no dinsa.

Haka dai yayi mishi send 30k din kana yaci yayi haniƙan kafin ya sallamesu ya tafi.

Usman ma tare suka fita.
Shi kuwa Ramadan anan ya miƙa sai bacci.

Mamy kuwa cikin alamun baccin itama tace.
“Yauwa Jannart jeki kimtsa kayanki.
Sai kizo ki samawa mijinki wani ɗan abu mai sauƙi.”
Kai ta jinnina kana ta miƙe.
Riyyam-nsra na cewa.
“Yauwa kiyi ki fito my Aunty zan tayaki.”
To tace kana ta wuce daki.
Itama Mamy dakin ta wuce.

Shi kuwa Riyyam-nsra nan ya zauna tare da fara sana'ar tasa.

Bayan ta gama kimtsa kayan nata kab da shiryasu cin drawer ne.
Ta fito a falon ta samu Riyyam-nsra.

Cikin alamun gajiya itama tace.
“Muje mu dama masa kunu.”
Tayi mgnar tana gaba.
A ranta kuwa tana cewa.
“Mutumin da ba'ayin masa gwaninta, zanyi mgninka ne kunu zan dama maka, idan kaga dama kasha in kaga dama ka bari cikinka ko nawa.”

Shi kuwa Riyyam-nsra yana biye da ita, har cikin store.
Shinkafa danya ta ɗiba gongoni biyu.
Ta miƙa mishi tare da cewa.
“Yauwa wonke wannan ka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login