Showing 315001 words to 318000 words out of 350584 words

Chapter 106 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.

Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.


Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.

Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA)*


Hannunsa ya ɗaga, tare da nuna masa Jannart da yatsarsa.
Murya na rawa hawaye na kwaranya yace.
“Gata, itace abinda Zainab ta haifa, itace ƴar Yah Abdulkarim”. Sai kuma ya tallabe kansa da tafukan hannunsa duka biyu, yana sakin shessheƙan kuka.

Ita kuwa Jannart idanu ta zazzaro ta zuba musu, tamkar wacce bata gayyacinta,
Shi kuwa Rayyern da sauri ya rumtse ƙwayar idanunsa da yaji tauna tsastsafo wasu azabebben hawayen tausayin Jannart domin tuni ya gano inda mgnar Barrister Kabeer ta dosa.
Tafin hannunsa yasa kan tafin hannunta ya haɗesu kib, yatsunsu ya sarƙafe dana juna.
Wani irin masifeffen rauni, tausayi, jinƙai, Jannart ne suka rufe masa zuciya da jiki baki ɗaya.
Haka yasa tuni hawaye suke kwaranyo masa.

Yayinda tuni Aunty Dijat ma take wani kuka mai sassayan sauti.

Abba Rayyern kuwa, kanshi ya kife a jikin kujerar, domin dama ya zaci haka.

Mammy kuwa wani irin tausayi da son Jannart ya lulluɓe zuciyarta, a zahiri take ganin kamannin fuskar Zainab ɗin kan fuskar Jannart, domin kamace ta haƙiƙa.

Shi kuwa Baba Mauɗo, dafa kafaɗar Barrister Kabeer yayi tare da cewa.
“Kada ka cemin basa raye, kada ka cemin haka, bana son jin haka.
Amman batun Jannart yarsuce kam na gamsu, kuma na dade da tuna hakan tun randa naji sunanta, domin kamanceceniyarta da Zainab sun ƙazanta, kada ka cemin marainiyace.

Zuwa yanzu gaba ɗaya falon babu wanda rauni bai rufesaba.

Mamy kam itama tuni hawaye takeyi.

Dr Sajo ma kife kansa yayi, bisa hannun kujerar yana zubda hawaye.

Alhaji Bala Tambari, kuwa rumtse idanunshi kawai yayi yana mai jin rauni.
Riyyam-nsra da Ramadan kuwa, idanu suka zubawa Barrister.

Shi kuwa Barrister cikin Muryar kuka yace.
“Marainiyace, maraici mafi muni, marsicine da ban taɓa jin irinsa ba a duniya koda a littatafai da finafinai.
Domin maraicine da ita kanta bata saniba maraicine da aka hana ta amfani iyayenta bayan ransu, maraicine da ba'a bata ƙofar yiwa iyayenta addu'a ba, sabida masifar son duniya. Yah Idi da hannunsa ya kashe ɗan uwanmu ƙaninsa mai binsa ni kuma yayana da nakeki.”

Zuwa yanzu wani irin tsuma jikin Jannart ya farayi tare da jin wani irin tashin hankali yana ziyartota.

Shi kuwa Barrister Kabeer cikin rauni yaci gaba da basu lbrin kamar haka.
“Mu uku kacal iyayenmu suka haifa, Yan Idi shine, Babba sai Yah Abdulkareem, kana nine karami.
Iyayenmu sun renemu cikin aminci da bamu Kekkyawar tarbiyya.
Har muka girma, Yah Idi ya faɗa kasuwanci, cike da zalamar ganin ya zama shahararren mai kuɗi, shi kuwa Yah Abdulkareem ya bawa karatu mahimmanci, inda burinsa ne ya zama cikekken lawyer.
Allah kuwa ya cika masa burinsu.
To amman fa Yan Idi baya godewa Allah kan abinda ya basa, shiyasa kullum na wani yake hango, ya samu abokai masu irin zuciyarsa.
Haka yasa mugayen zuƙatansu haɗewa.

Yah Idi yayi aure, matarsa Amina mahaifiyar Junaid kenan.
Kana bayan ita, ya auri Momynsu Azeez amman ita a ƴar sokotoce kuma acan ya ajiyeta, shiyasa.
Basu wani san junaba.
Amina tunda ta aifi Junaid bata ƙara haihuwaba sai bayan shekaru goma, Allah ya bata ciki.

Momynsu Azeez kuwa ta Haifi Azeez wanda shekara uku ya bawa Abdul.

A lokacin kuma Yah Abdulkareem ma yayi auren, da ya kasance ba zata, domin aurene da akayi komi, da komai cikin ƙanƙanin lokacin.
Ya auri Aunty Zee, daga ranar kuwa.
Yacewa, iyayenmu zai ɗaukeni.
Zan dawo gidansa da zama.
Haka kuwa akayi basu hanaba.
A lokacin in secondary School.

A watan da akayi auren a watan Allah yayiwa iyayenmu rasu baki ɗaya su.
Dama ba yawan dangine da muba.
Yah Abdulkareem mutum ne mai jinƙai da tausayi da gsky.
Aunty Zee kuwa wata daya da aurenta ta fara laulayim cikin.
Wanda sam bata son taji duk wani abu na ƙamshin girki.
Toh dan lokacin mafi akasarin lokuta nikeyi mana girki.
Aunty Zee macece mai haƙuri da sanyin hankali.

A haka taita rainon cikinta har ya cika watannin haihuwarsa.

Wata rana da yamma Yah Idi yazo.
A falon Yah Abdulkareem din suka zauna.
Ni kuwa ina falon Aunty Zee muna kallo, sai take cemin, inje in amshi kuɗi in seyo mata, kifi, don lokacin cikin ya kai haihuwa Yau ko gobe amman bata iya cin komai sai kifi.

Da sauri na miƙe, na nufi ƙofar falon Yah Abdulkareem din.
Har nasa ƙafa zan shiga sai kuma na tsaya sabida jiyo muryar ya idi da abinda yake faɗa.
Abdulkareem ka bamu goyon baya, a kan wannan ƙudurin namu, domin shine kaɗai kwanciyar hankali ka, sabida shi kansa uban gidan naka, yace mana takardun suna hannunka ya baka ka dawo dasu, a soke aikin, dan haka ka bani su, tun muna shaida juna.
Shi kuwa Yah Abdulkareem sai naji yana mgnar cikin sanyi yace.
“Amman ai cewa yayi kawai a tsaida aikine bawai in baku, takardunba, ya za'ayi in baku abinda ba nawaba Kuma ba nakuba, inci amanarsa kenan.

Gyara tsayuwata nayi a bakin ƙofar jin Yah Idi na cewa.
Wallahi ina gargaɗinka Abdulkareem domin, shakka babu, zan iya yin komai a kanka, ba tare da duba alaƙarmu ba, muddin zaka hanani cika burina.
Da sauri naja da baya jin Yah Abdulkareem na cewa.
“Nasan zaka aikata, kuma nasan duk abinda zakayi bazai wuce, ka kasheni ba, to wlh koda kasheni zakayi bazan bada suba.
Hakan da yace ya fusata Yah Idi sai ji nayi yace.
Zaka ko gani ganin idonka.
Sai nayi saurin barin wurin sabida jin yana fitowa.

Saida ya tafi, na shiga na samu Yah Abdulkareem yayi shiru, cikin sanyi nace masa Meta faru,? Bai ɓoye min komaiba, kana ya ƙara da cewa.
Nasan son zuciya da rashin tsoron Allah irin na Yah Idi wlh zai iya min komai fa Kabeeru.
Naji tsoro sosai.

Dan haka, zan baka takardun nan, ka ajeyimen su.
Dan Kada in ya turo su sani in basu.
Cikin yarda dani yamin wannan bayani.
Kana ya bani takardun.
Sannan na gaya mishi mishi aiken da akayi min.
Ya bani kuɗi naje, na saya mata.

Muka dawo muka zauna a falon munata hira, tanacin kitinta.
Saida ta gama sannan na tattare Wurin Yah Abdulkareem na dariya wai ta medani kande.
Ita kuwa sai ta zuba mishi ido tare da cewa.
Shekaran jiya da zaka tafi Gembu naso in bika, muje, amman nasan hanyar gashi kuma yadda nake, sai nakeji dama na gaya munje nayi musu kallon karshe.
Da sauri yace mata.
Zainab kallon ƙarshe kuma?
Sai tayi murmushi tare da sunkuyar da kai, mu kuwa duk ido muka zuba mata, cikin sanyi tace.
Musamman Neena na, naso in ganta ta ganni. Amman ba komai Allah ya sadamu a darussalam.
Wannan kalma ta girgiza Yah Abdulkareem dan a take naga yana zubda hawaye.
Ita kuwa da sauri ta yunƙura zata tashi.
Sai kuma ta koma ta zauna tare da riƙe cikinta.
Wachhh Abban Jannart yau kam da alamun Jannart zata fito duniya.
Jin haka kuma ya samu murmushi domin haka take tanada, raha, shiyasa tun kafin ta haihu take cewa, in dai ya mace ta haihu Jannart za'a sa mata in kuwa na mijine Jalaladdeen. Haka yasa take kiran Yah Abdulkareem da Abban Jannart tana yawan cemin idan mace ta haifa dai to matar Rayyern ce, wai sabida tana son yaron ni kuwa a lokacin banma san waye Rayyern dinba.
Shi kuwa Yah Abdulkareem murmushi yayi tare da cewa.
Wai da gaskene Zainab? Kai ta jinjina masa tana matsa laɓɓanta kana zufa na tsastsafo mata tace.
Allah kuwa da gaskene.
Da sauri nace, bazaki jira in zama likita ba, in karɓi haihuwar da kaina. Dan a lokacin dani da Yah Abdulkareem duk burinmu in karanci likita, ita kuwa Zainba da sauri ta kamo hannun Yah Abdulkareem.
Ganin haka yasa muka tafi asibin Dr Lukman, duk da Dr Sajo abokinsa ne, to amman lokacin baya ƙasar.
Muna zuwa kuwa aka amsheta, ana dubawa ma, akace ai yanzun zata haihu.
Muko sabbin shiga dama bamuzo da kayan haihuwa ba, hakan yasa, nayi maza nace zan koma gida in ɗauko.

Ina fita kuwa, tana haihuwa.
Dr Lukman kuwa da kansa ya amshi haihuwar sabida, a lokacin babu yawan likitoci mata.

Cikin ƙankanin lokacin na dawo, ina dawowa, na samu.
Yah Abdulkareem a kiɗimi, yana bin Dr Lukman yana masa Dr Lukman, ka taimaka asan abin yi, jinifa ya ɓalle mata.
Shi kuwa Dr Lukman waya yakeyi, haka yasa sai hannu yake juya mishi alamun yana zuwa.

Ni kuwa sauri nayi na shiga, cikin ɗakin da naga sun fito.
A kwance na sameta da alamun har an gyara baby, da sauri ta yafitoni da hannu, ina isa, tasa hannunta ta ɗauko Jaririyar daga kwance cikin jan numfashin tace.
Kabeeru, ga Jannart ta samu, amman zata rayu marainiya, babu uwa, kuma ubanma babu tabbas, domin naji abinda Dr Lukman yake faɗawa Yah Idi a waya kafin ya fita, a zatonsa bana jin turanci tunda ni ba fulatar Gembu ce.
Jini nake zubarwa amman cewa takeyi bazai min allurar tsaida jininba, bazai kuma gayawa Abban Jannart ba sai yaga na kusan mutuwa, yace kuma yanzu zaiyi ƙoƙarin tura musu Abbab Jannart ya tafi gida, suje can su sameshi, wai in har bai basu takardun ba su kashesa kamar yadda sukasa aka kashe Alhaji Bashir Maigaskiya daren jiya,
Cikin tashin hankali nace. Yah Idi Kuma, to shi yana ina, cikin jan numfashin tacemin shima yana cikin asibitin nan ya kawo Aunty Amina itama haihuwa zatayi, kuma naji suna cewa, ta rasu, abinda ta haifama babu rai.
Kabeeru, nasan ni kam bazan rayuba, kuma inaji a jikina zasu kashe Abban Jannart, dan Allah ka zame mata Garkuwa bongo abin jingina, ka jiƙanta, ka bata dukkan kulawa, da Kekkyawar tarbiyya, in ta girma kayi mata zabi da miji na gari mumuni mai jin tausayin maraicinta, Dan Allah Kabeeru kada ka bari, rayuwarta ta taggayara ko ta wulaƙanta, ina tsoron kada magautan mahaifinta su dawo kanta.
Dan girman Allah Kabeeru kayi min alƙawarin kare min ita daga dukkan abin cutarwa, ka gaya mata ina sonta mahaifinta na sonta, tun kafin zuwanta duniya, ita kuma ta somu bayan barinmu duniya, tayi mana addu'a, ta zame mana al'waladussaliha.
Hankalina bai tashiba sai lokacin da na amshi yarinyar daga hannunta domin da ka gani kasan ɗiyarta ce.
Sai kuma ɗan ƙaramin yatsarta na hannun hagu da farcensa yake kamar a tsage kuma kala biyu, wanda irin farcen yatsar Yah Abdulkareem ne sak da sak.
Sai kuma na sunkuyo zan kalli fuskar Aunty Zee.
Nayi masifar gigitaccewa lokacin da naga idanunta na kafewa sunayin sama numfashin ta nayi ƙasa.
Cikin tsananin tashin hankali na kwantar da yarinyar, tare da tallabo kanta ina cewa.
La ha ila ha illahu Muhammadu Rasulullahi sallahu alaihi Wasallama.
Nayi kamar shadarne sabida firgicin ganin kamar ranta na barin jikinta ne, ita kuwa cikin sassayan murya ta amshi kalmar shahadar tana nanatawa, kira na fara aunawa Yah Abdulkareem lokacin da takai karshen kalmar shahada na ukun da kuma fitan ranta.

Ya salam naga tashin hankali a wannan ranar.
Domin a kiɗimi na fito, sai dai ina fita motar Yah Abdulkareem na barin wurin.
Ban san me Dr Lukman ya gaya mishi ba yasashi komawa gida.
Babur na hau a guje nabi bayansa.

Sai dai ya rigani shiga gidan,

Cikin kiɗima nabi, bayansa, bayan na sallami mai babu ɗin.
To sai dai bai tafiba ganin yadda nake kuka sai ya tsaya yana kallona.
Koda na shiga sai ya biyoni sabida bani canjina.

Ni kuwa da sauri na nufi falon jin wani irin masifeffen ihu mai haɗe da salatin da Yah Abdulkareem yakeyi.
Ina isa bakin ƙofar na hango Yah Idi ne riƙe da wuƙa, yanata caccaka cikin Yah Abdulkareem dashi. Alhaji Abdu Tababa na gefensa yana sheƙa dariya.
Ihu nasa da azaban ƙarfi zan shiga, cikin.
Cikin zafin nama mai Babur nan ya fincikoni tare da fara jawoni waje.

Su kuwa a cikin inaga ihun da salatin da Yah Abdulkareem yakeyi ne ya hanasu jiyo nawa ihun.

Shi kuwa mai Babur nan da yake babbane da ƙarfi ya jani ya hau kashin sani.
Bayan layinmu ya tsaya jikin wani kango.
Yana cewa.
Kada kaje zasu kasheka dan Allah kada ka shiga, zasu kasheka yadda suka kashe na cikin.
Ni dai daga nan ban kuma sanin ina nakeba na suma.

Lokacin dana farka kuwa Yah Idi na samu a kaina.
Ashe shi mai Babur din da yaga na suma asibitin ɗaya daukoni ya maidani, yayi komai aka bani gado sai ya gudu, sabida yana tsoro.
Toh da Dr Lukman yaga nine sai ya sanarwar Yah Idi.
Ashe kwanana uku ban dawo hayyacina ba sai ranan.
Ina farka sai na bushe kawai ina kallon Yah Idi sabida yadda ya ruggume ni yana wani irin masifeffen kuka mai tada hankali yana cemin. Wayyo Kabeeru mun rasa Abdulkareem sabida rasuwar matarsa Zainab da ƴar data haifa, shima zuciyarsa ta buga ya rasu, sannan Amina ma ta rasu, sai wurin haihuwa sai marainiyar ƴarta data bar mana, Kabir ina tsoron rasaka, in ka rasu bani da kowa nawa a duniya.
Tsoro mai tsanani ne da mamakin makircin Yah Idi ya rufeni ya hanani Koda motsi.
Wanda da haka ya yaudari mutane haka yasa ko jami'an tsaroma basu shiga mgnar ba.

A ranan aka sallameni dole gidansa muka koma, inda muna zuwa na samu ya ɗauko Mammynsu Abdul daga Sokoto ta dawo da zama nan gidan sa, ya kuma damƙa mata Jannart a hannunta, da cewar ƴar da Amina ta haifane.

Tsoro da fargaba ne yasa dole na kasa yin komai gashi bani da wani hujja bare shaida ga yarinta.
Sai dai nasan tabbas ɗan sa Aunty Amina ta haifa ya rasu dansu ɗa na mijine ba, kamar yadda Aunty Zee ta gaya min,
Sannan na gane Jannart, duk kuma wanda yazo sai aita mamaki ana cewa.
Wannan kam kamar ƴar Zainab, to wannan abinne yasani yin shiru domin nasan bani da ƙarfin da zanyin faɗa fito na fito dashi.
Haka yasa na shiga jikinsa na zauna a gidan ina kula da komai na Jannart da rainonta Junaid kuwa yana sonta sosai.
Sai dai tana girma daga shekarunta goma sha huɗu abin ya fara sauyawa.

Sai ya fara sha'awarta, ni kuwa a lokacin nayi aure babu yadda banyiba, Yah Idi ya bani ita amman sai yaƙi fir dole na haƙura Amman babu randa gari zai waye ban jeba.
Sai daga baya na fahimci ita kanta Jannart ya fara sha'awar kasheta sabida yaga sa hannunta irin na mahaifinta ne sak.
Toh sai yake rainonta dan ta cika shekara ashirun da biyu, tasa mishi hannu a dukkan takardun kadarorin mahaifinta, a matsayin ya mallaka masa su kafinma ya rasu, shiyasa ya rainentan kuma yake da gudurin kasheta.
Wannan dalilin ne yasa, na fara shirin neman inda zan boyeta.

Kwatsam ranar a wurin taron mu sai naga Rayyern, kamanninsa yasani tuno da Alhaji Bashir Maigaskiya, ashema mahaifinsa ne, ina kallonsa a lokacin tamkar wanda aka haifa dan ɗaukar fansane.
Daga nan nayi ta bibiyar rayuwarsa, na kuma gane shi asalin ɗan Alhaji Bashir Maigaskiya ne, saidai bani da hujja, da naga Baba Mauɗo kuwa naso in gane da tafiyarsa.
To amman bai bada damaba.

Wannan mai Babur ɗin kuwa yanzu haka yana cikin tawagar Yan Idi, shi Alƙali Baba,
Muna tsara komai tare, da hakane muka samu cikakkun hujjojin da Yah Idi ya rinƙa faɗa mana dukkan abinda yayi. Yayinda kuma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login