Showing 198001 words to 201000 words out of 350584 words

Chapter 67 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

gaba da dan marin kumatunsa a hankali hankali, kana ta zuba idanunta kan kyakkyawar fuskarsa asanyaye takeyi masa komai, saboda har yanzu hawayen idanunta sun kasa tsayuwa.
So yake ya buɗe ido ya kalleta amman ya kasa.

Suna zaune ahakan ne kuma, yaji wani irin fitinanne kuma gigitaccen ciwo na taso masa, ciwon daya fi wanda ya taso masa abaya, ciwon daya sa shi jin duniyar na kifewa dashi.

Haka kuma ciwon da azabarsa yasa shi kasa tantance duniyar da yake, cikin wani irin azaban dake sukan naman jikinsa, ya soma fitar da wani irin numfashi mai kama da nishi, lokaci daya kuma duk jikinsa ya soma sakewa.

Sautin gurnanin numfashinsa da taji acikin kunnuwanta ne, kuma ya sata bud’e Idanunta amatuk’ar tsorace ta zuba masa idanu.

Baza ta tab’a iya jurewa ganinsa ahaka ba, wannan dalilin ya sakata sakin sabon kuka mai tsuma zuciya.

“A’a, A’a Naan Dan Allah karka rufe idanunka, karka tafi ka barni awannan duniyar da Bani da kowa sai kai, bansan kowa ba acikinta, Yah Allah ka taimakeni ka rufamin asiri Yah Allah ka taimaki bawanka ka sauk’a k’a masa wannan ciwon.”

Ta k’are maganan cikin matsanancin kuka tare da silalo da hawaye, kana ta sunkuyowa garesa, dai-dai lokacin kuwa idanunsa suka rufe rub.

Hannayenta duka biyu ta bud’e tare da rungumesa akan kirjinta, ta sake sakin wani sabon kuka, kuka kuma irin wanda bata tab’ayi ba arayuwarta.

Dai-dai lokacinne kuma Dr. Sulaiman ya turo kofar falon ya shigo.


Ita kuwa Jannart dake tsananin kuka kuwa, ko d’ago Kanta batayi ba, acikin kukan nata ne kuma ta sake rungume Rayyern din ak’irjinta.

Azauce take fad’in.

“Please Naan!! Please open your eyes please Naan don’t leave me please.....”

Ta kai k’arshen maganan tana me jijjigasa, Ahankali kuma takai yatsunta daidai saitin hancinsa.

Abunda taji ne kuma yasa ta waro Idanunta, amatuk’ar tsorace, cikin gigita da kuma tashin hankali, irin wanda bata tab’a samun kanta aciki ba, agaba d’aya rayuwarta.

Idanunta dake zubar da hawaye ta zubawa Rayyern din, tare da soma girgiza kanta da sauri, cikin firgici da kuma mugun bugun zuciyar dake dukan k’irjinta, muryar na rawa tace.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un...!

*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*

NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.

Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.


Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.

Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA)*




By
*GARKUWAR FULANI*


“Naan please ka bud’e idanunka, Dan Allah kayi numfashi!!”

Ta kare maganan cikin matsanancin kukan, dake bayyana karyewar zuciyarta da rauninta.

Hakan da Dr. Sulaiman ya ganine kuma ya sashi, k’arasowa cikin falon da sauri, hankalinsa amatukar tashe yace.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un, please Jannart stop crying, kiyi min bayanin abunda yake damunshi.”

Jin muryar Dr. Sulaiman acikin kunnuwanta ne kuma, ya sata d’ago Kanta da sauri cikin shasshshek’an kuka, kana murya asark’e tace.

“Ka taimakamin Doctor, Dan Allah ina tsoron ya rasa rayuwarsa, numfashinsa tafiya yakeyi, tun d’azu cikinsa keyi masa ciwo, kuma bansamu maganin da zan basa ba.”

K’arasowa wajen nasu Dr Sulaiman yayi, cikin kuma tsananin yanayin damuwa yace.

“Calm down Jannart, Insha Allah Rayyern zai samu lafiya, ki daina kuka kinji.”

Ya k’are maganar yana me lalub’o waya daga aljihunsa.

Rayyern dake rungume acikin k’irjinta kuwa, har yanzu da sauran numfashinsa, sannan kuma ahankali zuciyarsa ke bugawa, wanda kuma hakan na tafiya ne, da taimakon bugun zuciyar Jannart din da yake iya jiyowa acikin kirjinsa, kasancewar k’irjinsa da nata suna manne awaje d’aya.

K’warai yana so ya bud’e idanunsa da suke lumshe, amma kuma bashi da k’warin guiwar yin hakan, saboda zuwa yanzu komai na jikinsa yayi sanyi.

Jannart kuwa ahankali tasa hannayenta, ta sake matsetshi acikin jikinta, still kuma hawayen dake kwance akan fuskarta na d’iga ajikinsa.
Duk ta rud’e Yayinda Idanunta sukayi ja sosai.

Dr. Sulaiman kuwa Ganin yanda take arud’en ne yasa shi d’an rank’wafowa, kana cikin kulawa yace.

“Ya kamata mu kaisa asibiti mafi kusa, domin bashi taimakon gaggawa, amma firstly yanzu sakeshi bari na fara sakashi a mota.”
Ya ƙare mgnar yana matsowa kusa dasu,
Sunkuyowa yayi da niyar janye Rayyern dake jikinta.

Dai-dai lokacin kuma Rayyern ɗin ya fara wani irin numfarfashin masu nauyi.

Saurin girgiza kanta tasoma yi, cikin tsoro da kuma fargaban abunda ka iya zuwa tace.

“A’a Doctor Idan na sakeshi suma zaiyi fa.
Kalli yadda numfashinsa keyifa zai d’auke gaba d’aya, Ina jin tsoro ni dai bazan iya sakeshi awannan yanayin ba, Dan Allah kakira mana Dr yazo ya duba shi.”

Ta kai k’arshen maganan nata tana me, sake rungume Rayyern din acikin jikinta, Yayinda hawayen dake kwance akan fuskarta kuwa ke ci gaba da tsiyaya, tamkar ankunna famfo.

Baki Dr. Sulaiman din ya bud’e da niyar cewa wani abu, saidai kiran daya shigo cikin wayar tasa ne, yasa shi yin shiru tare da d’aukan wayan ya kara akan kunnensa.

Daga can b’angaren Ramadan jin Dr Sulaiman din ya d’aga wayan, cikin tsananin tashin hankali yace.

“Please Dr ya ake ciki, ya jikin Hamma Rayyern din? Kun kaishi asibitin Ina fatan babu abunda ya sameshi?”

Ramadan yayi tambayan duk agigice.

Kai Dr Sulaiman din ya girgiza, kana cikin yanayin damuwa yace.
“Ramadan ya zanyi Jannart ta rik’e sa gam, ta yanda babu yanda zan iya d’aukarsa, saboda tace wai Idan ta sakeshi suma zaiyi, na rasa makama Ramadan Domin ciwon nasa ya tashi sosai awannan karon.”

“Innalillahi wa’inna Ilaihirraju’un, Dr Sulaiman kayi wani abu mana, kayi wani abu kada Hamma na ya rasa ransa, Dan Allah ko Doctor ne kaje ka kira a waje.”

Ramadan ya fadi haka cikin tashin hankali.

Kai Dr Sulaiman ya jinjina, tare kuma da kad’a kansa cikin gamsuwa yace.

“Okay Ramadan amma inajin tsoron tafiya nabarsu awannan yanayin, Rayyern yana gab da suma, gashi Jannart kuma sai kuka take kamar zata shid’e, gaba d’aya na kasa iya control dinsu dukansu biyu.”

“Yah Allah help us.”

Ramadan ya fad’a cikin muryarsa da tayi rauni sosai, cike kuma da tausayin d’an uwan nasa, ga kuma Jannart dake ta kuka, domin daga cikin wayar yana iya jiyo sautin kukan da takeyi.

Jannart dake rungume da Rayyern din kuwa, kwata kwata bama tasu Dr Sulaiman din takeyi ba, damuwarta shine taga Rayyern din ya bud’e idanunsa.

Ahankali ta dawo da kallonta garesa, tare dasa hannunta d’aya ta tallafo hab’arsa cikin kuka tace.

“Dan Allah Naan ka bud’e idanunka, kada ka daina numfashi, kada kuma ka cire rai da rayuwa in sha Allah, ai zaka samu sauki ko, nasan zaka warke zaka samu lafiya mu koma Nigeria lfy en Mamynka da Abbanka su ganka lfy, za kayi rayuwa kamar kowa muna bukatar ka a tsakiyar mu, dan Allah ka bud’e idanunka yanzu, ka dawo cikin hayyacinka Dan Allah...”

Ta k’are maganan cikin tsananin kuka da kuma raunin zuciya, ahankali kuma tasa hannunta akan kumatunsa tana d’an bubbugawa, cike dason taga ya bud’e idanunsa.

Idanu Dr Sulaiman ya zuba musu, lokaci daya kuma duk jikinsa yayi sanyi, musamman da yaga yanda Jannart din ke kuka sosai da sosai.

Maida wayar tasa cikin aljihu yayi, cikin sauri kuma ya d’auki key din motar Rayyern din, da ya gani akan table, tamkar wanda zai tashi sama saboda sauri, haka ya sa Kai ya fice daga cikin falon.

Kaitsaye wajen da motar Rayyern din yake ya nufa, yana shiga kuwa ya cilla motar kan titi, tare da nufar babban hospital din garin, wanda kuma shine mafi kusa dasu.

Jannart dake zaune kuwa duk da taji fitansa, amma bata d’ago Kanta ta kalleshi ba, Idanunta har yanzu suna kan fuskar Rayyern, still kuma ko wani d’igon hawayenta d’aya, da zai fita akan fuskarsa yake sauk’a.

Ahankali take yawo da hannunta dake kan hab’arsa, har ta k’araso zuwa kan kirjinsa.
Lallausan tafin hannunta ta kife akan kirjin nasa, dai-dai saitin zuciyarsa, Jin zuciyar tasa na d’an bugawa ahankali ne kuma ya sata, lumshe Idanunta tare da motsa labb’anta cikin sanyi tace.

“Ya Allah ka taimaki Naanu na Yah Allah ka bashi lafiya, kasanya juriya acikin rayuwarsa, Allah kagani bamu da kowa anan saikai, Kai ke kulawa damu akoda yaushe, Ya Allah yauma ka kula damu, ka saukaka mana tsanani izuwa sauki ya Allah ka rufa min asiri ka bawa Naanu na lfy.”

Takai karshen maganan hawaye yana me shatata akan fuskar nata.

Rayyern dake kwance ajikinta kuwa, duk wani abu da take fadi yana jinsu acikin kunnuwansa, saidai kuma yakanji kalaman nata da sautin amon muryar nata tamkar acikin mafarki, saboda gangar jikinsa ne kawai take wannan duniyar, hankalinsa kuwa ya tafi izuwa wata duniyar ta daban.

Suna ahakanne kuma k’iran Ramadan ya shigo cikin wayar Rayyern din dake gefe, Ganin sunan Ramadan ne kuma, yasa ta d’aga wayar da sauri tana k’arawa akan kunnenta, ta sake fashewa da kuka, still cikin muryar sheshshek’a tace.

“Ramadan har yanzu baidawo cikin hayyacinsa ba, na shiga uku Ramadan banason wani abu ya sameshi, duk jikinsa rawa yakeyi, gaba daya ya fita ahayyacinsa, Ramadan ya zanyi....”

Sautin kukan nata ne yasa Ramadan d’an rumtse idanunsa, zuciyarsa cike da damuwa, da kuma tashin hankali yace.

“Zai dawo Hayyacinsa Aunty Jannart, Insha Allah nan bada jimawa ba Hamma Rayyern zai dawo hayyacinsa, ki daina kuka dan Allah, ki kula dashi kafun Dr. Sulaiman ya dawo.”

Cikin kukan ta jinjina kai, saidai ta kasa cewa komai sai sheshshekanta da yake tashi.

Acan Nigeria din kuwa Mamy dake gefen Ramadan, itama hawaye takeyi gaba daya ta shiga cikin damuwa.

Haka ma Abba wanda ya zauna yayi ta gumi, abubuwa da yawa yake sak’awa acikin zuciyarsa, kallo daya kuma zakayi masa kafahimci cewa yana cikin matsananciyar damuwa.

Kasancewar kuma Ramadan din a hands free ya saka wayar ne, yasa dukansu suke iya jiyo kukan Jannart din, harma da nishin Rayyern dake tashi k’asa k’asa.

Ahankali Abban ya d’ago ya kalli Ramadan, da hannu Yayi masa alama akan ya bashi wayar.

Ganin hakanne kuma yasa Ramadan mik’a masa, kara wayar Abban yayi akan kunnensa, cikin son b’oye damuwa da kuma tausasa murya yace.

“Jannart.”

Jannart dake zaune kuwa jin muryar Abban acikin wayanne yasa ta d’an zabura, cikin rawar murya tace.

“Abba Hamma! Hamma!! Abba jikinsa yana ta b’ari, ga numfashinsa ya kusa d’aukewa, ciwo yakeji sosai, Dan Allah Abba ka taimakeshi.”

Idanu Abban ya d’an lumshe saboda tsananin tausayin yarinyar da yaji, domin ayanzu kukan ta yafi komai d’aga musu hankali sabida yanaga tashin hankali da take ciki zai hanata yin abinda ya dace.

“Jannart, Jannart!!”

Abban ya kira sunanta ahankali.

Yanda taji sautin muryar Abban ne kuma yasa ta, d’an tsagaita kukan nata tare da amsawa.

“Kiyi shiru kinji ki kwantar da hankalinki, ki daina wannan kukan In sha Allah Rayyern zai samu lafiya, ki daina kuka ki zama mai juriya akan ciwon sa kinji ko Jannart, yanzu addu’a ya kamata ki masa, ki daina kuka domin yawan kuka zai iya jawo miki wata matsalar kema, saboda haka ki share hawayenki Allah nanan kuma zai Iyar muku.”

Abban ya fad’i haka cikin son bata k’arfin guiwa.

Jin hakanne kuma yasa ta sanya hannu ta share hawayenta, cikin nuna biyayyarta agaresa tace.

“To Abba.”

Kai Abban ya jinjina cike da yabawa halin yarinyar, kana Ahankali ya zare wayar akunnensa ya kashe, saboda shi d’inma dazai samu dama, kukan zaiyi Domin har abada bazai tab’a son ace wani abu ya samu Rayyern din ba, haka kuma bazai so ace Rayyern yabar duniya batare da ya sauk’e wani k’aton nauyin dake wuyansa ba, Lallai zaiso ace Rayyern ya rayu, har zuwa lokacin da gaskiya zatayi halinta.
Baya ga haka kuma Rayyern din shine komai nasu, shine AHALI’nsu kuma k’ashin bayansu.


Ahankali ta zare wayar daga kan kunnenta, tare da lumshe Idanunta tana mejin yanda Rayyern din ke sake shigewa cikin jikinta, Yayinda ya saka duka hannayensa biyu ya rungume cikinta gam.

Wanda hakan da yayi din kuma alamace dake, nuna cewar yanajin ciwo sosai.

Acan b’angaren Dr Sulaiman kuwa.
Koda yaje EUROUPEAN Medical senter mascow (E.M.S) din emergency Doctor ya nema, bayan ya shaidawa Doctorn matsalan Rayyern din ne kuma, suka nufo gidan kaitsaye.

Suna isowa kuwa ko gama dai-dai-ta parking ba suyi ba, direct suka nufi cikin gidan Dan bawa, Rayyern din agajin gaggawa.

Jin motsin shigowar su Dr Rayyern dinne, kuma ya sata d’ago da kanta ahankali ta kallesu.

Dr James ne wanda Sulaiman din ya d’auko, ya k’araso cikin falon tare da matsowa inda suke, Cikin kulawa da kuma harshensa na turanci yace.

“Madam ko zaki iya matsawa na dubashi, saboda akwai buk’atar sai nayi checking nasa sosai.”

Idanunta da sukayi jajur ta zubawa farin baturen likitan dake gabanta, kaman mai nazartar wani abu, Cikin sheshshek’an kuka kuma ta girgiza masa kai, murya araunace tace.

“Ka dubashi ahaka saboda bazan iya barinsa ba, inaji ajikina Idan na barshi mutuwa zaiyi, Dr ka kalla fa numfashinsa seizing yakeyi, Dan Allah kayi sauri ka dubashi ahaka kada wani abu ya sameshi.”

Kai Doctorn ya girgiza saboda yasan duba, patient din ahaka ba abu bane da zai yiwu, saboda akwai buk’atar dole sai anyi checking d’insa, saidai kuma da gaske yaga Jannart ba zata tab’a bari a dubasa, ba tare da yana jikinta ba.

Sanin cewar Idan aka k’ara wasu mintuna ahaka komai zai iya faruwa ne, yasa doctor din matsowa, ya d’aura hannunsa akan wuyar Rayyern, tare dasa wani abu mai kaman na’ura adai-dai kan cikin Rayyern din.

Bayan ya gama saka abunne kuma, ya d’ago ya kalli Jannart dake hawaye, shikam har acikin ransa yana me mamakin k’arfin halinta.

Wani k’wayan magani ya b’allo daga cikin wani sachet, mik’a mata maganin yayi kana Cikin harshen turanci yace.

“Kisa masa wannan ak’asan harshensa, saboda zaifi saurin yi masa aiki, zai kuma yi tasiri acikin jijiyoyin jikinsa.”

Da sauri ta jinjina kai tare da karb’an k’wayar maganin, kasancewar har yanzu Rayyern din na kwance ajikinta ne kuma, yasa ahankali ta juyo da fuskarsa, ya zamana suna fuskantar juna, fuskar tasa da tayi ja sosai ta d’an kalla, cikin sanyi da kuma tsananin tausayawa, tasa hannunta na dama ta saka mishi cikin bakinsa, d’aya daga cikin yatsunta tasa ta d’an d’aga harshensa, tare da tura k’wayan maganin ak’asan harshen nasa, kamar yanda doctor d’in ya buk’ata.

Ganin nan take maganin har ya soma narkewa, acikin bakin nasa ne yasa ta, zare yatsarta ahankali tare da zubawa kyakkyawar fuskarsa idanu.

Lokaci d’aya har rama ta bayyana akan fuskar tasa, Yayinda saman fatar idanunsa sukayi wani irin ja, haka ma labb’an bakinsa, da tsabar ja


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login