Showing 264001 words to 267000 words out of 350584 words

Chapter 89 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

sanyi ya kwabce masa shessheƙan tamkar zai fito da ransa.

Yayinda a cikin ɗakin itama Jannart kukan ne ya kwabce mata,
tanayi da zaton ko ciwon ne ya fiddashi cikin hayyacinsa.

Cikin yanayin tashin hankali ta tashi zaune, jin kamar shessheƙan kuka,
da sauri tasa hannunta ta jawo karamar wayarsa dake wurinta,

Number Ramadan ta dannawa Kira.

Cikin bacci Ramadan yaji rigging din wayarsa,

Kasan cewar bai jima da yin bacciba kasan cewar yana waya da Raihanansa ne yana shaida mata,
An gama haɗa kan aure nanda kwana biyu za'a kawo shiyasa suka raɓa dare.
A hankali ya miƙa hannunsa ya ɗauki wayar,
ganin Hamma Rayyern ne yasashi saurin tashi zaune duk da yasan yanzu Jannart ce ke amfani da layin.
Da sauri ya amsa kiran tare da kara wayar a kunne sa.
“Assalamu alaikum my Aunty ya dai?”.
Da sauri ya miƙe tsaye jin muryar Jannart ɗin tana kuka,
Cikin tashin hankali da tsoro yace.
“Innalillahi My Aunty meya samu Hamma Rayyern?”.
Cikin kuka tace.
“Ramadan Baida lfy ciwon cikinsa ya tashi kuma, gayican sai kuka yake tayi."
Cikin firgici da kuma mmki yace.
“Kuka kuma?. Yana ina yanzu”.
Da sauri tace.
“Yana falo”.
Cikin sauri yace.
“Sorry My Aunty ki nitsu keji kiji dashi, bari in kira Ya Sulaiman yanzu zaizo, kada ki damu kinji ko”.
Ta buɗe baki da nufin zatace tana tsoron yanayin sa na yaune kuma sai taji ya katse kiran yana katse kiran kuma,
ya dannawa number Dr Sulaiman Kira.
Yana mai mamakin kalmar wai yana kuka.
Ya sani iya tsawon rayuwar Hamma Rayyern ɗinsa da ciwon ciki bai taɓa yin kukaba.


Shi kuwa Dr a falo, wani masifeffen abu da yakeji wanda ya rasa me zaiyi ya magance masa abin,
yasa gaba ɗaya yake jinsa tamkar wanda ya rasa tunaninsa ji yake tamkar yayi ta ihu da karfi ko zaiji sanyin azalzalar da ruhi da jikinsa keyi, hakan yasa ɗan shessheƙan raunataccen kukan daya subce mishi fitowa.
Kuka yakeyi da hawaye sosai.
Allah ya sani yana son wani abu ya kuma gane abun a jikin Jannart yake so yake ya jishi a kwance a jikinta tanayi mishi irin abinda take mishi in ciwon mararsa ya tashi, so yake ya jisu a wuri ɗaya gado ɗaya borgo ɗaya manne da.
Ya kasa iya furta komai sai kukan tare da zamewa ƙasan ƙofar ya kife kansa bisa guiwowinsa.
Murya na rawa yake kiranta.
“J... Jan... Jannaaaaa”.

Dr Sulaiman ne zaune a hotel room ɗinsa video call yakeyi da matarsa.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Ɗazu fa Mamy ta kirani tace in gaya maka in Allah ya kaimu jibi zamuje mu kai kayan auren Ramadan”.
Cikin sakin fuska yace.
“Toh naji Allah ya kaimu Ni dai yanzu kiji dani”.
Cikin jin kunya tace.
“Toh Honey me zan iya maka kana can ina nan”.
Kanshi ya ɗan jujjuya tare da cewa.
“Wlh baki san halin da muke ciki bane maman Abdalla Mascow banzan garine mai masifar sanyi,
kawai muna rayuwane cikin begenku, dole in mutun baida karfin imani zaiyi zina, domin garine da yanayinsu kaɗai ke ingiza feelings ɗin mutane.”
Cikin tausasawa tace.
“Ayyah sorry mijina Allah dai ya baku Sa'a ku dawo lfy”.
Cikin sanyi yace.
“Uhum toh Amin amman dai wlh muna jin jiki, Ni dan sanyin kwanan nan yafi na kwanaki.
Dan wallahi yau oga Dr Rayyern Waliy ma najishi yana wani yanayi”.
Cikin tsokana tace.
“Allah ko ka sawa Dr Rayyern ido”.
Zai bata amsa ne kuma sai yaga kiran Ramadan a ƙaramar wayarsa.
Da sauri yace.
“Ramadan kuma a daren nan”.
Sai kuma ya kalleta tare da cewa,
Bari muyi waya zan kiraki bayan nan.
“Kayi bacci dai in kun gama dan numa bacci zanyi”.
Hararan wasa ya mata kana daga nan ya katse kiran tare da jawo karamar wayar ya amsa kiran Ramadan.

Shiru yayi yana sauraron bayanin da Ramadan key masa.
“Ba komai Ramadan kwantar da hankalinka dan Allah kada ka gayawa su Abba bari yanzu zan tashi in tafi in sha Allah ba matsala kaji ko”.
Cikin ɗan jin ƙarfin guiwa Ramadan yace.
“Toh”.
Kana ya katse kitse wayar.
Shi kuwa Dr Sulaiman da sauri ya kira Number Rayyern a ƙalla sau biyar ba'a ɗagawa,
Cikin fesar da numfashi yace.
“Uhum Namijin duniya waya sanima ko ciwon tuzuranci ne, dan dai wancan ciwon bayasashi kuka a iya sanina.
Kai ba wani ciwon cikima, sai dai in wani sabon ciwon cikin ne.

A nan gidan Rayyern kuwa wayarma na bedroom ɗinsa baima San ana kiraba.

Zuwa yanzu kuma muryarsa tana fita sosai.

Da sauri Dr Sulaiman yace.
“Yauwa bari in kira ɗaya layin”.
Ya ida mgn yana kiran layin Dr Rayyern ɗin dake wajen Jannart, bugu ɗaya ana biyu ta ɗauka ganin Dr Sulaiman a rubuce”.
Cikin sanyi murya mai tattare da kuka tace.
“Dan Allah Dr kazo Naan baida lfy, tun d’azu kuka yakeyi”.
Da sauri Dr Sulaiman yace.
“Kwantar da hankali ki kiyi haƙuri dena kuka nitsu ki gaya min. Meke damunshi!”.

Cikin sharce hawaye tace.
“Ba ɗazu kunyi wayaba yace, maka bashi da lfy cikinsa na, ciwoba kuna gama wayan ya tafi bedroom ko abinci baiciba,
Danaje kuma gaba ɗaya baya cikin hayyacinsa, ni dai na gudu kuma ya biyoni na rufe ƙofana gashi a falo yanata kuka, dan Allah Dr kazo ku dubashi”.
Da sauri ya danne dariyarsa tare da cewa.
“A'a Madam kije wurinsa kafin inzo”.
Cikin sauri itama tace.
“A'a wlh ni dai ina tsoronsa,".

“Tsoro kuma? Kullum ba kyace ke tare dashi ba!”.
Cewar Dr Sulaiman yayi mgnar yana mai murmushin dan tabbas ya fahimtar wani abu.

Ita Jannart ba tare da kawo komai cikin rantaba tace.
“Yaufa ba kamar na kullum yake mishiba, idan ina kusa dashi kamar baya hayyacinsa zai jimin ciwo”.

Cikin katseta yace.
“Ok kada ki damu, ba abinda zai samesa, zaiyi bacci a wurin”.
Daga nan ya katse kiran yana murmushin dan tabbas ya gano Rayyern.
Ya katse kiran ya saki dariyar mugunta.
“Uhumm Dakta ai su waɗannan ababen marmari ba'ayi musu taurin kai”.
Ya faɗa cikin dariya.

Ita kuwa Jannart shiru tayi tare da zuwaba wayar idanu.
Yayinda kuma ta kasa kunne jin babu sautin kukansa ne kuma yasata sakin ajiyar zuciya.
“Toh ko dai har yayi baccin nema,”.
Tayiwa kanta tambaya.

Shi kuwa Rayyern cikin fitinennen yanayin da yake cikine yayi bacci a zaune a wurin.
Sai ajiyan zuciya yake direba a hankali.

Itama Jannart a haka bacci yayi awon gaba da ita a zaune tana jingine da gado.

Yayinda Ramadan kuma ya kasa samun nitsuwa ya kira Jannart bata dagaba haka yasa ya kira Dr Sulaiman nan yace mishi ai sunyi bacci ne ciwon ya sakeshi.

4:51 na asuba, ya buɗe idanunsa a hankali tare da ɗago kansa.
Idonshi ya kuma lumshe a hankali tare da jujjuya kanshi da ya ɗanyi tsami,
Abubuwan da suka faru daren jiyan ne ya fara dawo mishi,
da sauri ya buɗe idonsa tare da jujjuya kai ya kalli inda ya kwana da kyau.

Wani irin takaicin kansa da kansane ya rufesa.
Mitsss yaja wani irin tsakin takaicin kunya.
Wani irin tsuke fuska yayi tamkar dai tana gabanshi wai kada ta rainashi.

Yunƙurawa yayi ya miƙe tsaye, tare da liƙawa kofar harara, sannan ya juya a hankali ya nufi ɗakinsa kai tsaye bathroom ya faɗa, tare da sakarwa kansa ruwan sanyi a gurguje yayi shirin salla ya fito ya tafi da mota dan lokacin ya kure masa.

Ita kuwa Jannart dirin tashin motarsa ne ya tasheta daga baccin kwanan zaune da sukayi.

A hankali ta zuro sawunta ƙasa, madadin tayi bathroom sai ta nufi ƙofar ɗaki.
Cikin sanɗa, ta iso a hankali ta murza key ɗin tare da janye kofar, ta ɗan leƙo da kanta, ganin baya nanne yasata sauƙe numfashi, kana a hankali ta fito falon ma baya nan.
Daga nan ɗakinsa ta wuce,
A hankali tace.
“Alhamdullilah yayi sauƙi”.
Daga nan fito falon har zata wuce sai kuma ta dawo baya, ganin katon ɗin magunguna ta, ɗaukar katon ɗin tayi kana nufi ɗakinta.
Tana shiga ta akiye katon ɗin kan dreesin meeror'n.

Bathroom ta wuce.
Brush tayi mai lafiya kana ta sulla wonka da ruwan ɗumi sabida sanyin da ake tsulawa.

Al'wala tayi kana ta fito.

Bayan ta idar da salla ne tayi addu'o'in ta kamar dai yadda ta saba,
kana ta miƙe ta isa gaban dreesin meeror tare da zare hijabin sallan ta ninkeshi, mai ta shafe jikinta dashi, kana ta ɗan murza pawder sannan
Lipstick ta dan gogawa pink lips ɗin ta.
Katon ɗin ta jawo ta fito da kayakin gaba ɗaya ta jerasu a kan meeror'n.
Kullacca ta lakata ta ɗan shafa.
Kana ta juya zuwa gaban wurin kayanta, wanu tattausan atampa ta zato riga da zabine orange color mai masifar kyau, ɗinkin rigar ɗan dai-dai. Anyi kolliyar zip ɗin ta gaba.

A hankali ta kimtsa kanta cikin kayan.
Masha Allah sunko yi mata kyau matuƙa gaya,
Rigar ta zauna ɗas a jikinta, irin ɗinkin nanne mai faɗin wuya, gashi batasa bra ba sabida har yanzu numfashin ta bai fita mata dai-dai tun tsoritan daren jiya.

Murza ɗan kwalin tayi a kanta tare fito da jelam gashinta data kitsa ta gefe,

Wayarshin ta ɗauka, tare da zama a bakin gadon.
“12 missed call harda kiran Abba ma”.
Ya faɗa cikin mamakin rashin jin kiran.
Number Abba ta fara kira.
Dai-dai lokacin kuma Abba yana mgn da Rayyern dake kan hayar dawowa gida.
Kanshi ya ɗan jingina da jikin kujerar motar tashi, tare da makala waya a kafaɗarsa, cikin ransa yace.
“Ya Salam wai wannan wacce iriyar yarinyace da komai sai ta gayawa su Abba,”.
A fili kuwa cikin sanyi yace.
“Abba na workefa”.
Cikin kulawa, so, tausayi, ƙauna, Abba yace.
“Ka tabbatar?”.
Numfashi ya ɗan fesar Allah ya sani baison yin kariya, ya zama ɗabi'arsa tunda gashi jiya yayi ɗaya baya son Kuma yayi ta biyu cikin sanyi yace.
“Abba matsalar da sauki in sha Allah zan samu sauki sosai kada ka damu kaji ko Abba na”.
Cikin gamsuwa Abba yace.
“Toh Rayyanu na Allah ya baka lfy ka kula da kanka kaji ko”.
Cikin son mahaifin nashi yace.
“Toh Abba na”.
Daga nan sukayi sallama.
Yana katse kiran kuma kiran Jannart na shiga,
da murmushin yace.
“Assalamu alaikum Jannart.”

“Wa alaikassalam Abba Barka da safi.”
Ta faɗa cikin girmamawa ,
“barka dai Ɗiyata ya mai jiki da sauƙi ko”.
Abba yayi mgnar cike da kulawa,
“Eh Abba da sauki ya tafi masallaci ma”.

“Masha Allah yanzuma ai munyi waya.
Allah dai ya bashi lfy, ya baki ladan jinya”.

“Amin ya Allah Abba”.
Daga nan nan kuma ya miƙawa Mamy wayar, tana jin muryar Mamy tace.
"Mamy”.
Cike da jin dadi Mamy tace.
“Ya mai jikin”.
“Alhamdullilah Mamy yaji sauƙi”.
cikin jin dadi Mamy tace
“Masha Allah, Allah ya ƙara sauki”.

“Amin ya Allah Mamy inata kewarku”.
Ɗan murmushi Mamy tayi tare da cewa.
“Ai kam nima ina kewarki kusa dani, yanzu dai ai na fara lisafin dawowarku, tunda auren Ramadan kafin Azumi za'ayi dudu wata ɗaya ne ya rage”.
Cike da zumuɗi tace.
“Naji daɗi Mamy na nakusa dawowa.”
Daga nan suka ɗanyi hirar yadda bikin Ramadan zai kasance kana sukayi sallama da juna.
Suna sallama kiran Aunty Fauziyya na shiga.
Bayan sun gaisane tayi mata dukkan bayanin yadda zatayi amfanin da magungunan, kana sukayi sallama.

Kai ta ɗan juya ta kalli ƙofar fita ɗakin nata, kana ta kuma kalli fuskar wayarta a fili tace.
“Har yanzu bai dawoba”.
Sai kuma ta miƙa a hankali ta nufo falon.

Shiru falon dama gidan baki ɗaya,
sai ƙamshin sa ɗaya gwaraye ko wanne kusurwa,
A hankali ta lumshe idanunta, tare da saurin ɗaga sawunta da takejin sanyin tayis na ratsa mata shi.
Kan kujera 2 str ta zauna kana a hankali ta zame tare da kwanciya, numfashi ta ɗan fesar tare da tafiya duniyar tunani.

A tsanake yakeyin driving yana mai jin sautin karatun Alqur'ani mai girma daya kunna, haka nan yake jin wata iriyar sassayar iska mai tattare da nitsuwa na ratsa mishi dukkan jiki,
A karo na uku ya kuma juyowa ya kalli wayarshi sabida kiran Dr Sulaiman daya kuma shigowa.

“Mitss”. Yaja gajeren tsaki tare da hararar wayar.
Kanshi ya juyo tare da shiga fuskantar kofar gidan nashi,

Yana kutsa kai cikin gidan kiran Dr Sulaiman na kuma shigo mishi,
Bai kula wayarba har saida ya dai-dai ta parking kana yasa hannunsa ya ɗauki wayar a kufule ya amsa kiran tare da karawa a kunne cikin jan tsaki yace.
“Uhum”.
Murmushi Dr Sulaiman yayi tare da cewa.
“Dr yau Ba sallama ne? Tun ɗazu ina kiraka baka amsaba”.
Buɗe marfin motar yayi tare da fitowa.
Hannunshi na dama ya zura cikin aljihun tattausan jallabiyar dake jikinsa,
kana ya saƙala wayar a kafaɗa hannunsa ɗaya kuma ya rufe motar,
Sannan ya juyo ya nufi cikin gidan.

“Wai har yanzu kukan kakeyine da bazakayi mgn ba?”.
Cewar Dr Sulaiman.

Shi kuwa Rayyern
Cikin kwaɓe fuska yace.
“Kuka kuma, wai kai Sulaiman wanne irin mutum ne kai kamar wani tsohon maye tunda ka kira ɗaya kaga ban ɗagaba ai sai ka sahirta min ko”.
Cikin dariyar ƙeta Dr Sulaiman yace.
“Uhum kai Akwai wani mayene sama da kai? Ni bana son wannan bauɗiyar taka, ka gaya min kukanme ka kwanayi daren jiya?
Me kakeso baka samu ba?".
Kanshi ya dafe da hannu ɗaya, dayan kuma ya buɗe ƙofar falon kana ya kutsa kai cikin falon a hankali.

Ita kuwa Jannart hankali ta buɗe idanunta jin muryarsa da motsinsa, ido ta zuba mishi tana ganinsa ras sai dai shi da yake yanzu ya shigo bai kula da ita a wajenba bare ya ganta.
Numfashi ta ɗan fesar a hankali tare da yunƙurawa ta tashi zaune, sai dai duk da hakan bai gantaba,
Meda hankalin ta garesa tayi, dan so take ta karanci halin da yake ciki.

Shi kuwa Dr Rayyern fuskarsa ya yamutsa ka murya a haɗe yace.
“Me kuma zanso?”.
Da sauri Dr Sulaiman yace.
“Mace mana”.
Idonshi ya rumtse jin abinda Dr Sulaiman yace, a ranshi yace.
“Ya sallam kai anya kuwa Sulaiman ba maye bane?”.

Ita kuwa Jannart hannu tasa ta tallaɓe habarta tana kallon Kekkyawar fuskarsa,

Shi Dr Rayyern A fili kuma cikin dakekkiyar murya yace.
“Mitsss an gaya maka ni mayen matane irinka?”.

Dariyar ƙeta Dr Sulaiman ya kece da ita cikin dariyar yace.
“Ai wlh kai babu wani mayen matama daya fika a nahiyar mu, tunda in dai baka samuba kuka kakeyi kamar wani ɗan shayi, ka gane abinda kakeso sai taurin kai tsiya da yake saka kana azabtar da kanka tuni fa na dade da ganeka,
To wallahi ka samawa kanka mafita don su waɗannan kayan marmarin ba'ayi musu girman kai domun su mata ai sune farin cikinmu in ka ƙi kuwa zaka kashe kanka”.

Cikin yanayin kufula da kuma kunyar saurin ganosa da akayi cikin son nuna ba hakan bane abinda suke nufib yace.
“Allah ya sauwaƙa ni ɗin? Ni Rayyern Kake tunanin mace tana gabana da har zanyi zaucewar da zata sani lalacewa a gaban wata halitta ƙaramar yarinya nayi mata kuka, kai Sulaiman Allah ya isarmin.
Dan wlh babu wanda ya taɓa yaɓa min bakar mgn irin wacce ka yaɓa min a duniyar nan, to ma wai a zatonka sauyawa nayi koko ka mance yadda nake ne da har kake faɗin hakan”.
Dariya harda buga cinya Dr Sulaiman yakeyi.

Ita kuwa Jannart idanu ta zuba mishi ko ƙeftawa batayi, jujjuya kalamansa takeyi dan tana son samar musu kekkyawan muhalli da cikekken ma'ana.

Tsaki yaja tare da cewa Dr Sulaiman.
“Kaga malam na mamajo kada ka fasa min kunne da wannan dariyan da bashi da tushe”.

Cikin sassauta dariya Sulaiman yace.
“Toh naji Malam waliyi kukan me kakeyi daren jiya?”.

Da sauri yace.
“Wai waye ce maka ina kuka? Inyi kuka abin haukane kuma mutuwa akayi min ne?”.
Ya ƙare mgnar yana juyowa ya kalli gafen da Jannart take Dan atishawar data subce mata yasashi sanin da ita a wurin,
Hannunshi yasa ya kunna wutan falon baki ɗaya sai gashi haske ya gauraye ko ina tamkar rana.

Da sauri ta yunƙura ta miƙe tsaye tare da yin ƙasa da kanta.
Shi kuwa Rayyern ido ya kafeta dashi sabida jin abinda Dr Sulaiman yake cemishi.
“Toh koma dai menene gwara ka faɗa min in sani dan in akwai taimakon da zanyi maka inyi maka, domin Ni dai jiya tsakar dare Madam ɗin ka ta kira su Ramadan ta gaya musu baka da lfy kuma kanata kuka, da ihu,
Shi kuma Ramadan ya gaya min kuma nayi ta kiran layinka baka ɗagaba wata ƙil kabar wayar a bedroom naka kabi Madam ɗakinta ko?
Sai kuma ta rufe maka ƙofa shine ka zauna a wurin kanata rusa mata ihu da magiya ko?
ka gigita yar mutane a banza itama tanata kuka a zatonta ciwon cikinka ne da ka fara karya ya taso, bata san cewa wannan na jarabar sha'awarta bane ”.
Wani irin kallo yakeyi Jannart wanda yasata jin duk tsikar jikin ta na mimmiƙewa shaidar idanunsa na yawo a jikinta,
A hankali ta ɗan ɗago kanta ta kalleshi da sauri ta kuma yi ƙasa da kanta ganin yadda ya tsareta da idanu babu alum wasa,
Fuska ya tsuke tare da fara takowa zuwa gabanta, Cikin Muryar gaskata kai da kai yace.
“To ni Rayyern me haɗina da mace, tun tuni da nake rayuwata na damu da wata halitta wai ita mace ne,
kai ka sani muddin inada chocolate wlh mace bata gabana, domin nasan duk daɗi da zaƙin dake tare da ita bazata kai min chocolate garɗi da daɗeen ciba”.

Da sauri Jannart ta rumtse idanunta koda bata san forkon mgnar suba, da kuma manufar zantukansa ba, kunya ta rufeta da maganarsa ta ƙarshe.

Shi kuwa Rayyern shida kansa ma wani irin yar-yar yaji da kalaman nasa a take yaji wasu irin fitinannun abubuwan jiya da daren nan suna dawo mishi, borin kunya ne ya sashi fadin koma menene.
A hankali ya kamo lips ɗinshi na ƙasan ya fara tsotsa ta ciki tamkar zai tsinkesu.

Shi kuwa Dr Sulaiman kai ya jinjina dan ya gamsu da ƙarfin halin Dr Sulaiman da har yake wannan cika bakin.
“Uhummm kayi kuskure Rayyern wlh na tausaya maka ranar da zaka shiga komar Jannart dole kayi azumi uku, na kaffaran rantsuwarka na fifita daɗeen chocolate aka mace.”
A kufule yace.
“Har abadako bazanyi wannan azuminba banza ɗan sa ido kai dolen-dole sai ka sani nayi mgn cikin fushi”.

Ya ida mgnar tare da katse kiran,
Kana ya zura wayar cikin aljihun tattausan jallabiyar dake jikinsa.

A hankali Jannart ta fara jan baya, sabida ganin yadda ya nufota haiƙan ƙadara,

Hannunsa yasa ya dafe ƙugunsa tare da ɗan kwantar da kanshi gefen dama, still yana tsotsan lips ɗinshi ta ciki,
Ita kuwa Jannart jin ta jingina da jikin ginine ya sata ɗago kanta ta kalleshi murya a raunace tace.
“Ya jikinka?”.
Tayi mgnar cikin rawan murya da kuma yin rau-rau da idanunta.

Numfashi mai nauyi ya fesar tare da zubawa pink lips ɗin ta da suka sha lipstick suna wani irin fitinennen sheƙi,
Fuskarsa a murtuƙe yace.
“Ke yaushe nayi kuka da kikayi ta shelantawa duniya na kwana kuka?”.
Yayi mgnar yana ƙara matsota kib da ita.

Kai ta fara jujjuyawa a hankali yayinda tsoronsa ya fara rufeta.
Mui-mui takeyi da ɗan bakinta tana jujjuya lips ɗinta alamun tana son yin mgn kuma ta kasayi,

Cikin ɗan ɗaga murya ya kuma cewa.
“Wato sharri zaki fara yimin kenan ko Janna, kuma har wurin su Abba da abokaina ko kunya bakijiba Janna kika faɗa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login