Showing 318001 words to 321000 words out of 350584 words

Chapter 107 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

muke naɗan hakan a video komai.
Sannan Alƙali Baba babban alƙaline da akeji dashi.
Kama kuma ga Alhaji Bala Tambari shima duk tawagar mu ɗaya.
Zuwa yanzu duk munada cikekkun hujjoji na musamman.

Da sauri duk falon suka juyo kan Jannart, da ta saki wani irin maraitaccen kuka mai cike da maraici da ƙunan rashin iyaye.
Faɗawa jikin Rayyern tayi tare da kife kanta bisa cinyarsa.
Wani irin masifeffen kuka mai tafiya da numfarfashi ta sake cikin shessheƙan raunataccen kukan take cewa.
“Innalillahi wa innailaihi raji'un, Hasbunallahiwani'imanwakil, wayyoooooooo Allah na, niyi asarar rayuwata ta, tsowon shekaru ban amfani iyayena da komaiba, kuma wai ina raye, banyi musu amfani ba ko kaɗan ban zame musu mai tunasu da addu'a ba, wayyoooooooo Naaaan zuciyata zata fashe,”.
Ya Salam shima kansa Rayyern fashewa yayi da ƙaƙƙarfan kuka mai sauti, ya jawota jikinsa ya ruggumeta da karfi.

Barrister Kabeer ma kukan ya saki kamar zai shiɗe,
Baba Mauɗo ma kife kansa yayi bisa sawun Alhaji Bala Tambari dake gefensa yasani kuka mai rauni.
Aunty Dijat kuwa itama ruggume yaranta tayi tare da sakin kuka.

Abba kuwa shima kukan yakeyi yana ɗan bubbuga kafaɗar Barrister Kabeer alamun yayi haƙuri.

Riyyam-nsra, Ramadan, Mammy da Mamy kuwa tausayin Jannart ne yasasu kuka mai ciwo.

Shi kuwa Rayyern cikin kuka yace.
“Nooo! Nooo!! A'a Janna bakiyi asarar rayuwaba kuma suma basu yi asarar haihuwar ki ba.
Tsinenne kuma la'annne Alhaji Idi Sale Dakata shine yayi asarar rayuwar duniya data ƙiyama.
Daya tauye miki maraicinki
Yabar azzalumi ɗansa yana cutar min da ke.
Baki da laifi domin a baibai ya barki kika rayu.”

Cikin kuka mai tafiya da numfarfashi ta kara ruggume shi tare da cewa.
“Naaan kaji fa Mamana ta bada yaƙini akan zan rayu, har tana cewa acemin suna sona tun kafin zuwana duniya.
Sannan tana bada wasiyan a sanarmin in sosu bayan barinsu duniya in rinƙa tunasu da addu'a.
Amman aka hanani wannan damar, Naan dame na amfanesu, me ribar haihuwata da sukayi? in banda cikin watannin nan daka nusar dani dayi musu addu'a a cikin dukkanin sallolina”.





By
*GARKUWAR MARUBUTA*



Ya salam kusan gaba ɗaya falon ɗibkewa da kuka sukayi.
Shi kuwa Rayyern kukan yakeyi har yana jin kamar kanshi zai buga, cikin tsananin tashin hankali ya tallabo kanta ganin yadda take kuka tuni idanunta sun kumbura sunyi jazir.
Hancinta yayi ja, numfashin ta sai korar juna yakeyi, hakan ne yasa ya jawota jikinsa ya ruggumeta da samun dai-dai ton numfashin ta.

Cikin tsananin tashin hankali Baba Mauɗo ya fara maimaita.
“innalillahi wa innailaihi raji'un Hasbunallahiwani'imanwakil”.
Hakan yasa suma kan suka fara maimaita hakan.
Wanda a take Allah ya fara sauƙo musu da sassauci cikin zuƙatansu.

Sai kuma duk suka fara sauƙe ajiyan zuciya amman banda Jannart da har yanzu maimaita innalillahi wa innailaihi raji'un takeyi tana kuma mai ci gaba da kuka.
Cikin sauƙe ajiyan zuciya Barrister Kabeer yace.
“Ki gafarceni Jannart ki dena kuka, na yi iya iyawata dan ganin komai ya tafi dai-dai.”
Shi kuwa Rayyern cikin sanyi yace.
“Barrister batar tayi kuka! Idan batayi kukaba a yau sai yaushe zatayi kuka, inama ace labarinki yazo kamar namu Janna ace iyayenki na raye, amman kash haka bata kasance ba.
Kiyi kukan rashinsu da kuma ɓoye miki da akayi, amman kada kiyi kukan maraici.
Nayi miki al'ƙawari zan cike miki dukkan gurbinsu.
Zan sama miki farin ciki.
Mammyn na zata zama madadin Mamanki Baba Mauɗo zai zama Madadin babanki.
Kisa a ranki Zaiton da Riyyam-nsra sune ƙanneki.
Ga Hafeez da Hafiza ga Abba Kabir ɗinki.”

Shiru Abba da Barrister Kabeer sukayi suna mai kallonsu da sauraron kalamansa.

Baba Mauɗo kuwa da Mammy kai suka jinjina mata alamun eh hakane.
Ramadan da Riyyam-nsra ba cikin tsananin tausayinta sukace.
“My Aunty kiyi haƙuri, ki dena kuka in Sha Allah bazamu sake barin kiyi kukaba”.

Shessheƙan kukan ta fara ja da ƙarfi.
Sai dai ina abin yaci tura.
Haka yasa Rayyarn kuma ruggume ta, Allah ya sani ya mance ma a cikin mutane suke, yana kuka yace.
“Janna ki kalleni in Sha Allah zan zame miki Nagartaccen miji mai jinƙai, tausayi, kulawa, sadakarwa, zan zame miki bongo abin jingina, kuma garkuwa ga duk wata cutarwa da izinin Allah.”
Kai kawai ta fara gyaɗa masa yana kwato numfashin ta, amman ina, cak numfashin ya tsaya ta lafe jikinsa a sume.

Cikin tashin hankali ya ɗan janye jikinsa, tare da jera mata kira.

Ramadan ne ya miƙa da sauri yana cewa.
“Ya salam Hamma Rayyern suma tayi fa”.
Gaba ɗaya hankainsu ya tashi, hakan ne yasa duk sukayi kanta.
Mammy ce tasa hannu ta amsheta daga jikinsa sabida ganin yadda gaba ɗaya jikinsa yake karkarwa, ya kasayin komai.
Aunty Dijat ce ta miƙa da sauri ruwa ta kuma ɗauki wa mai sanyi.
Tana miƙa musu, cikin sauri Mamy ta yayyafa mata a fuska an kuwa yi Sa'a ta farfaɗo da wani sabon kuka.
Ruggume ta Mammy tayi tana mai ɗan shafa bayanta da tausar zuciyarta da sanyaya kalamai.

Jin kiran sallan mangarib da akayi ne yasa, kab mazan sauƙe numfarfashi tare da miƙewa, suka firfita haraban gidan al'wala sukayi kana kab suka nufi masallaci.

Matan kuwa, cikin sanyi Mammy ta miƙa tare da kamo hannun Jannart daketa shessheƙa ta miƙar da ita.
Mamy ce ta nuna mata ɗakin.
Sai kuma Aunty Dijat da Zaiton subabi bayanta.
Cikin sanyi da lallashi Mammy ta kalleta lokacin da suka shiga cikin ɗakin cikin tausasawa tace.
“Jannart kiyi haƙuri kinji ki dena kuka, ki shiga bathroom ki watsa ruwan sanyi, zakiji sanyi a zuciyarka.
Sannan kiyi al'wala kizo kiyi salla, a karo na forko a rayuwarki, ki ɗaga hannunki, kiyiwa iyayenki addu'a shine abinda mahaifiyarki ta roƙa, kuma shine zai sasu farin ciki ba kukanki ba.
Kana kiyi sujjada ki godewa Allah da ya hana magautanka samun nasara a kanki ya rayaki har kika san gsky”.
Cikin sanyi ta gyaɗa mata kai.
Ganin haka yasa ta tallabeta suka shiga bathroom din.
Kana ta fito tare da ja mata ƙofar.

Su kuwa su Aunty Dijat da Zaiton main falon suka koma, a bathroom ɗin ciki sukayi al'wala, kana Mammy ma nan ta fito, al'walan.
Mamy kuwa sallayu ta shisshin fiɗa musu, kana duk suka kabbarta sallah.

Acan masallacin cikin gidan kuwa suna idar da salla, Baba Mauɗo yayi ta jerowa su Barrister Abdulkareem addu'o'in neman musu gafara da samun ni'imantaccen makwanci.

Ana shafawa Rayyern ya sulale ya fito ya nufi cikin gida.

Ido ya ɗan zuba musu ganin duk suna cikin falon, ganin bai ganta bane yasashi.
Wuce ɗakinta.
Jiyo shessheƙan kukanta a bathroom ne yasashi kutsa kai ciki.

Cikin bathtub dake cike da ruwa ya hangota tana zaune cikin sa babu komai a jikinta sai, kuka takeyi har jikinta na rawa.
Da sauri ya iso inda take, ita kuwa jin motsin mutum ne yasata ɗago kanta, ganin shine yasata, yin saurin matsowa bakin bathtub ɗin, hannunta tasa ta riƙe sawunsa tana daga ciki.
Kanta ta manna kan sawunsa, cikin tsananin rauni da kuka tace.
“Naan Zuciyata, ta ƙuntata, ruhina ya girgiza a sanadin rashin muradin zuciyata Naan bani da kowa duniya”.
Da sauri ya zauna bakin bathtub ɗin kanta ya manna da cinyarsa cikin sanyi yace.
“Kina dani Jannart, ki dena cewa haka, kina dami, kuma zamu samar da zuriya maigaɗi, zanyi miki ciki ki haifa mana yara da yawa, gani ga yaranmu ga Mammy ga Mamy ga Abba ga Baba Mauɗo gasu Abba Kabeer ga Zaiton kinaji Aunty Dijat da Mamy har sunayi mana kallon mai ciki, da ace haka zai tabbata da nayi farin ciki”.
Cikin sanyi ta fara sauƙe ajiyan zuciya jin yadda yake ɗan watsa mata ruwan sanyin a jikinta.
Ganin tayi shirune, yasa ya tasheta, ya zubda ruwan bathrobe ya zira mata, kana yasa tayi al'wala kana suka fito.
Shi ya taimaka mata ta, shirya kana yasa mata hijjabi.
Ta kabbarta sallah.
Shi kuwa falon ya fito.
Nan ya samu su Mammy na zaune, da alamun jira sukeyi isha tayi suyi salla kafin su tashi.

Shi juyowa yayi ya kalli Ramadan daya leƙo tare da cewa.
“Hamma Rayyern Abba yace kazo, muyi salla isha ta ƙarato”.
To yace kana yabi bayansa, so yake yayi sallan ya rabu da kowa yazo ya kula da Jannansa.


Bayan an idar da salla ne.
Mamy ta kai musu abinci falon Jannart.
Kana Mammy kuwa ta shiga ta fito da ita.

Su Abba kuwa a babban falon suka shigo baki ɗayansu, a nan inda Mamy da Zaiton suka jera musu abinci suka zauna.

Gaba ɗayansu babu wanda ya ci wani abincin kirki.
Ita kam ma Jannart kuka ta sawa Mammy data matsa mata taci, abinci sai Mamy ce ta tsoyayo kunu tare da miƙawa Mammy tace.
“Ai inaga gaba ɗaya ma cikin yanata cin abinci, dan tunda suka dawo in Banda kunu batasha sa wani abu a bakintaba sai ɗazune ma ta ɗanci a logoi alogoi.”
Cike da tsananin tarin farin ciki Mammy tace.
“Masha Allah! Masha Allah!! Masha Allah!!! Alhamdulillah! Allah ya inƙanta ya rabaku lfy”.
Sunkuyar da kai tayi tana mai tsiyayar da hawaye, ita kuwa Mammy miƙa mata cup ɗin tayi.
Amsa tayi tana mai zubda hawaye, sun sa mata son haihuwa musamman yadda Naan yake nuna mata in cikine zaiyi farin ciki da yadda ya nuna mata da haihuwa ne kawai zasu faɗaɗa ahlinsu.
A hankali ta kurbi kunun sabida yadda Aunty Dijat ke haɗata da Allah tasha
kurɓa takeyi hawayen na zubar mata.

Su kuma haka suka ɗan tsastsakali abincin sama-sama.


Acan falo ma haka mazanma basu wani ci abincin kirkiba.

Rayyern ya fara tashi ya haura sama sabida so yake yaje ya watsa ruwa.

Kafin nan sun watse a falon.

Ai kuwa tayarsa keda wuya.
Barrister Kabeer ya miƙe tare da cewa.
“To mu zamu tafi Hafeez kaje maza kace Mamanka da Aunty Jannart su fito mu tafi”.

Kai Ramadan da Riyyam-nsra suka ɗago tare da zuba mishi idanu tare da cewa.
“Barrister da Aunty Jannart Kuma?”.
Da sauri Baba Mauɗo ya ɗaga musu hannu tare da cewa.
“Wayasa bakinku”.
Yayi mgnar da alamun shima Abba da Barrister Kabeer sun sanar dashi yadda auren ya kasance.
Dr Sajo da Alhaji Bala Tambari kuwa kai suka jinjina tare da haɗa baki wurin cewa.
“Gsky ni ban goyi bayan raba yarannan cikin wannan yanayin da suke cikiba”.
Abban Rayyern ne ya ɗan jujjuya musu kai tare da cewa.
“Dan Allah kada kuce komai”.
Hakane yasa sukayi shiru.
Kana suka miƙe tare da yin sallama dasu suka tafi.

Dai-dai lokacin kuma Aunty Dijat da Jannart da Hafiza da Hafeez suka fito.
Wanda a tunaninsu Mamy Barrister Kabeer ya kiratane dan yayi mata nasiha shiyasa basu san me ake ciki ba.

Suna fitowa Barrister Kabeer yasa su Hafeez a gaba,
Abban Rayyern kuwa cikin tausasawa yace.
“Jannart kije wurin Abbanki akwai mgnar da zakuyi, gobe da safe zanzo”.
Cikin sanyi tace.
“Toh Abba”. Kana tabi bayan Aunty Dijat, ta rasa wanne irin yanayi takeji.

Su kuwa su Baba Mauɗo rakasu sukayi har waje.
A tare Dr Sajo da Alhaji Bala Tambari, da Barrister Kabeer suka fita gidan.

Suna fita Abba da Baba Mauɗo kuwa, suka wuce ɗakin Baba Mauɗo suka zauna.

Su Mamy kuwa jin shiru-shiru ne yasa suka, fito falo.
Ganin basa nanne yasa suka tambaya ina Jannart cikin sauri Riyyam-nsra yace.
“Uhumm su Abba sun sa, tabi Barrister Kabeer.”
Cike da mamaki
Sukace.
“Meyasa”. Kai suka jinjina musu alamun suma basu saniba.

Kai Mamy ta jinjina tare da zama a ƙasa gaban Mammy tace.
“Uhummm tabbas akwai wata matsala dan tun jiya naga alamun hakan amman ni kaina bansan menene ba, amman in sha Allah zan bincika mana a daren nan”.
Ita kuwa Mammy cikin sanyi tace.
“Toh ko dai ɗan naki yayi wani laifin ne”.
Kai Mamy ta jinjina kana ta juyo ta kalli Ramadan tare da cewa.
“Kaima ina zaton akwai matsala a lamarin aurenka nan da kyar in ba ɗaga bikin akayi ba”.
Cikin wani irin zabura Ramadan ya zazzaro idanu waje tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi raji'un dan Allah Mamy kada ki sake faɗan haka wlh zan iya suma”.
Cikin tsare fuska Mammy tace.
“Tafi daga nan ba kunya”.
Jin hakane yasa ma kawai ya haura sama, yayinda Riyyam-nsra yabo bayansa.
Ɗakin Ramadan ɗin suka shiga, yana mai kiran Raihanansa.

A can side ɗin Baba Mauɗo kuwa, cikin sanyi Abba yace.
“Daga yau zan dawo kwana nan Alhaji wanda akayi a bayama rashin sani ne”.
Cikin dariya Baba Mauɗo yace.
“Ni tashi ka barmin ɗakina, kaje kaji da rigimar Ramadan in yaji an ɗaga auremsa.
Kafin gobe kuma muga iya tsaurin ido da rashin kunyar Rayyanu”.

Kamar da wasa fa ma, amman ina fir.
Abba yaƙi komawa cikin gida. Saida Baba Mauɗo ya ɓata fuska yayi da gaske kafin Abba ya mike ya nufi cikin gidan

Jannart kuwa suna shiga cikin mota, Aunty Dijat ta ɗan kalleta jin yadda hannunta ɗaya taɓata yayi zafi.
Cikin kula tace.
“Jannart Zazzaɓi ko?”.
Kai ta jujjuya mata alamun itama bata saniba.
A haka dai suka isa gida.

Suna shiga Su Hafeez suka kwanta bisa kujeru, shi kuwa Barrister Kabeer, zama yayi tare da cewa.
“Dijat ki shiga kitchen ki ɗan dafa mata ko indomie ne taci”.

Jin haka yasa tana ajiye mayafinta ta shiga kitchen.
Ita kuwa Jannart kwanciya tayi bisa kujerar dake gefen Barrister Kabeer dan zazzaɓin takeji sosai.

Shi kuwa cikin nitsuwa yaci gaba da tausar zuciyarta.

Rayyern kuwa cikin sanyi yake tako steps din yana mai sauƙe ajiyan zuciya na kukan da yayi tayi,
Yayinda jikinsa kuma keta baza ƙamshi na musamman.
A hankali ya iso ɗan tsaya tsakiyar falon.
Kai ya ɗan sunkuyar ganin yadda Mamy da Mammy suka zuba mishi idanu.
Cikin sanyi yace.
“Mammy bakuyi bacciba”.
Kai ta jinjina masa, Mamy kuwa cikin sanyi tace.
“Ai yau kam kwanan zaune zamuyi, na yaushe gamo”.
Kai ya ɗan jinjina kana cikin wasiyya ya nufi kitchen.
Fridge ya buɗe Chocolate nasa ya ɗan ɗiba, kana yana fitowa ya nufi falon Jannart ɗin.
Su kuwa da ido suka rakasa.

A can gidan Barrister Kabeer kuwa, da sauri Jannart ta tashi zaune lokacin da Aunty Dijat ta ajiye mata plate ɗin indomie da kwai a gabanta, tururin su ya bugeta.
A gigice ta nufi Bathroom dake cikin falon, tana maiyi wani irin masifeffen kakari da yunƙurin amai,
Da sassarfa Aunty Dijat tabi bayanta.
Yayinda shi kuwa Barrister Kabeer cike da mamaki yake cewa.
“Subahallahi lfy kuwa”.
Ina babu mai bashi amsa, haka yasa ya rufa musu baya.

Tuni su Hafeez kuwa sunyi bacci.

Ita kuwa Jannart amai take cikin tsananin azaba, ga wani irin fitinennen zazzabin da takeji kamar zai kasheta.

Amai ɗin takeyi a gigice,
Wani irin duhune da jiri suka rufeta a tare,
haka yasa ta fita hayyacinta, sabida abubuwan sunyi mata yawa a wunin yauwa.

Da sauri Barrister Kabeer ya tallabeta tare da ɗagota cak, cikin kiɗima ya juya ya nufi waje yana cewa.
“Subahanallahi Dijat zauna da yara bari in kaita adibiti”.
Cikin tashin hankali Aunty Dijat tace.
“Ya ilahi Abban Hafeez muje tare”.
Yadda yaga har yanzu tana kakarin amai ɗin ne yasashi ƙara gudu.
Bayan mota yasata, kana ya shiga gaba da yana labubo car key ɗin a aljihunsa.
Kafinma Aunty Dijat ta idosu har yaja motar.
Mai gadi kuma ya buɗe mishi gate yaja ya tafi.

Dole Aunty Dijat ta koma cikin gida.

Asibitin Dr Sajo ya wuce da ita, cikin Sa'a kuwa ya samu Dr Sajon dama asibitin ya nufa ba gidaba.
Amsarta akayi cikin gaggawa tare da bata taimakon gaggawan da suka samu aman nata ya tsaya,
Sannan aka farayi mata dukkan gwaje-gwaje da suka dace.


Da ɗan saurinsa ya fito falon yana cewa.
“Mamy ina take ne?”.
Cikin kauda kai Mamy tace.
“Waye ɗin?”.
Da sauri yace.
“Jannart mana, na duba bata falo a bedroom nasu Zaiton kawai na samu tana bacci har bathroom na duba bata nan, Mamy ina take?”.
Da sauri duk suka juyo suka kalli ƙofar falon jin muryar Abba na cewa.
“Wa'adin ne ai ya cika, ba dama wata takwas ko shekara ɗaya kayi yarjejeniya da Barrister Kabeer cewa zaka sakar masa yarsaba, dan baka sonta ba kuma zaka taɓa sontaba dan haka yanzu sai ka rubuta takardar sakinta ka bani in kai mishi dan shi kam ya tafi da ƴarsa”.

Kamar sauƙar aradu haka yaji kalaman Abba.
Lokacin ɗaya suka ɗunguza mishi lissafi da nitsuwa, cikin yanayin diriricewa yace.
“Ni kuma?”.

Ido Abba ya zuba mishi, tare da tsareshi dasu.
Cikin tsananin kiɗima yaji wata zufa ta keto masa, murya a sarƙafe yace.
“Abba”.
Da sauri Abba ya daka masa tsawar da tashi zamewa ya zauna ƙasa da ɓas, hannunsa duka biyu yasa ya dafe kansa.

Shi kuwa Abba gefen Mammy yaje ya zauna, a ƙasa kusa da matarsa, sunkuyar da kai yayi a matsayinsa na karami a kanta, cikin nitsuwa ya kora mata dukkan bayanan da Barrister Kabeer yayi masa.
Ita kanta Mamy jikinta yayi sanyi.
Mammy kuwa Kai kawai ta jinjina ta miƙa ta wuce ɗaki inda Zaiton take ba tare da tayi mgn ba.
Shima Abba miƙewa yayi ya tafi.

Yana mai cewa Mamy ta biyoshi.
Haka ta miƙe ta bishi.
Ya zama sunyiwa Dr Rayyern watsiyar dila.

Wani irin tashin hankali yakeji mai gigitarwa.
Cikin fargaba ya miƙe da sauri ya haura sama.

Wayarsa ya ɗauka ya fara dannawa Barrister Kabeer Kira, sai dai wayar na shiga ba'a ɗagawa.
Sabida ya bar wayar a falon inda ya tashi.

A can asibiti kuwa cikin sauƙe numfashi Dr Sajo ya kalli Barrister Kabeer dake zaune a gabansa cikin murmushi yace.
“Congrat Barrister ka kusa samun jika nan da watanni takwas masu zuwa, dan Jannart nada cikene kimanin kwana ashirin da biyar zuwa wata ɗaya”.
Cikin wani irin mamaki da tarin al'ajabi Barrister Kabeer ya miƙe tsaye.

A gidan Barrister Kabeer kuwa, da sauri Aunty Dijat ta amsa kiran Rayyern daketa shiga wayar Barrister.
Shi kuwa Rayyern yana jin an ɗaga yace.
“Why! Why!! Whyyyyyyyyyy!? Barrister meyasa zakayi min haka”.
Da sauri Aunty Dijat tace.
“Rayyern ba shi bane,.”
Cikin sauri yace.
“Ina yake”.

“Ya tafi Asibitin SAJOS HOSPITAL din Dr Sajo ya kai Jannart bata da lfy, sai amai takeyi kamar zata suma”.
Cikin tsananin tashin hankali ya katse kiran.
Tare da zaran car key ɗinsa.
Gudu-gudu yake sauƙowa har yana taka steps din bibbiyu.

Babu kowa a falon haka yasa ya fita.
Shiga motar yayi yana danna Ari horn a gigice hakane yasa ya wangale masa gate.


Kai tsaye SAJOS HOSPITAL ɗin ya wuce.
Yana isa yayi parking kana ya kusa kai cikin asibitin.
Kasan cewar lokacin sha biyu tayi, shiyasa babu zirga-zirgan mutane.

Kai tsaye ya wuce Office din Dr Sajo bisa jagorancin wata Nurse.
Suma isa wurin tace masa.
“Nanne”.
Kai ya jinjina mata kana ya kutsa kansa ciki.

Cike da tashin hankali ya kalli Barrister Kabeer dake ɗagowa daga sujjadar da yaji.

Yana ganinsa yace.
“Barrister ina matata?”.
Cikin tsare fuska Barrister yace.
“Matarka adaba ai yanzu kam ɗiyatace, duk da kaci amanata ka karya alƙawarin da kayi min ka rabata da budurcinta”.
Cikin mamaki yace.
“Wallahi ni banyi mata komaiba ban rabata da budurcinta ba, amman ina son mamata dan Allah mu janye wanne sharadin amman wallahi tallahi billahil azeem ni ban kusancetaba ban keta budurcinta ba”.
Cikin tsananin tashin hankali da tsoro Dr Sajo ya miƙa tsaye tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi raji'un Rayyern me kake faɗa haka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login