Showing 207001 words to 210000 words out of 350584 words

Chapter 70 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

nata, kana ta fesa sassanyan turarenta mai dadin kamshi, dangane da kwalliya kuwa powder kawai ta shafa akan fuskarta, sai kuma lipsgloss mai d’an shek’i.

Ahankali ta k’arasa wajen trolley dinta, tare da bud’ewa ta zaro wani had’add’en doguwar rigar engilsh wears, sai kuma hulan sanyi irin wanda ta saba sawa.

Koda ta zura rigar ajikinta d’as tayi mata, saidai duk da cewar rigar bata da tsawo sosai, amma tayi mata kyau ajiki, hulan ta saka akanta tare da d’aukan hijab mai girma ta saka.

Bayan ta shumfud’a sallayane kuma ta tada Sallah.

Adai-dai lokacin kuma Rayyern ke idar da nashi sallan, bayan ya d’anyi addu’o’i da azkhar ne kuma, ya gyara zamansa akan sallayan tare da maida kansa, ya jingina da jikin drawer.

Idanunsa ya d’an lumshe ahankali, acikin zuciyarsa kuwa yana me tunanin maganganun da Abba ya fad’a masa, har zuwa yanzun kuwa moment din daren jiyan ya kasa fita daga cikin tunaninsa, domin aduk sanda ya tuno da sautin kukanta, sai yaji tsikar jikinsa na tashi, zuciyarsa kuwa haka zata shiga bugawa da sauri.

Ga kuma wani irin shegen kasala da yakeji, musamman akan abunda tayi masa d’azun, har yanzu jin marar tasa yake wani iri, Yayinda penis d’insa ke maaifar harbawa, tamkar Wacce take fitar da numfashi wanda hakan ya kasance mishi bakon yanayin da bai san dashi ba idonshi ya lumshe sabida duk sanda ya tuna sai yaji wannan harbawar.

Ahankali Jannart din ta mik’e tsaye, bayan ta idar da sallah tare da sa hannu ta zare hijab din dake jikinta, baby pink jacket ta d’aura akan kayan nata, kana kaitsaye ta fice daga d’akin, tana me nanata fad’ar.
“Hasbiyallahu la’ila ha illahuwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim.”

Koda ta fito falo ledodin abincin da Dr.Sulaiman ya kawo mata ta bud’e, tare da zaro takeways din ta soma bubbudewa, Ganin duka abincin babu wanda ya b’aci ne, yasa ta d’aukan ledodin ta nufi kitchine.

Acikin plate ta juye chicken pepper onin sauce, da kuma saurce na liver sai kuma pancake, wanda aka yi masa gashi na musamman.

Warming abincin tayi bayan ta kammala ne kuma ta had’a musu coffee,

Acikin wani d’an tray ta saka musu abincin, kaitsaye ta nufi d’akin Rayyern din.

Ahankali ta tura kofar d’akin ta shiga, bakinta d’auke da sallama.

Jin motsin shigowarta ne kuma yasa, Rayyern din bud’e idanunsa, Ahankali kuma ya d’ago kansa ya kalleta.

Kyakkyawan shigan da tayi da kuma fuskarta ya zubawa idanu, wanda kuma tun kafun ta k’araso k’amshinta ya riga daya cika masa hanci.

Jannart kuwa cikin nutsuwa ta k’araso inda yake zaunen, batare da ta lura da irin Kallon da yakeyi mata ba.

Ahankali ta d’an durk’usa ta ajiye tray din agabansa, kana itama ta zauna tare da tank’washe k’afafunta, sai alokacinne kuma ta d’ago idanunta ta kalleshi.

Karab kuwa idanunsu suka had’e acikin na juna, saboda har yanzu Rayyern din kallonta yakeyi.

“Ina kwana.”
Ta fad’a tana meyin k’asa da Idanunta.

“Lafiya.”
Ya amsa mata asanyaye tare kuma da janye idanunsa daga kallonta.

Itakuwa Jin alamun ya daina kallonta ne, yasa ta d’an gyara zamanta, tare da d’agowa ta kalleshi, tray din abincin ta sake turowa gabansa, kana cikin d’an yin k’asa da murya tace.

“Naan ga abinci kaci sai kasha magani.”

Bud’add’un idanunsa ya lumshe, tare da fesar da numfashi ahankali, saboda Jin yanda sautin muryarta ke fita, yasa duk yaji tsikar jikinsa ya tashi.

“Nakoshi.”
Ya fad’a ta hanyar motsa y’an k’ananan lips d’insa.

Jin hakan ne kuma yasa Jannart din d’agowa, ta kallesa da sauri, lokaci d’aya kuma ta kwab’e fuska.

“Please Naan kaci abincin please.”

ta fad’i hakan tana me langwab’ar da kanta gefe.

Lips d’insa ya dan cije saboda, yanda yaji tayi maganan tamkar Wacce take tsokalo wani abu daga sashi na jikinsa, akaro na farko kenan da yaji sautin muryarta na neman zautar dashi, abunda bai tab’aji ba arayuwarsa.

“Banajin yunwa.”
Ya sake fad’a atak’aice saboda bashi da wani k’warin jiki.

“Please ko coffee kasha.”
Jannart din ta fad’i haka cikin tausasawa.

Jin hakan da yayi dinne kuma yasa shi, d’an ya motsa fuska, tare da mik’a mata hannunsa alaman ta bashi cofin coffee din.

Da sauri kuwa ta mik’a masa kofin, Ganin da tayi ya soma shan coffee din ne kuma ya sata tashi, Anutse ta cigaba da tattare masa d’akin, bayan ta kammala ne kuma ta wuce falo, magungunansa ta d’auko tare da dawowa cikin d’aki’n.

Kallon yanda yake sipping coffe din ahankali tayi, yanayin yanda bakinsa ke d’an motsawa ne, yasa ta jin wani iri ajikinta.
Ahankali ta k’araso inda yake zaunen.
Zama tayi agefensa tare da d’ago Kanta ta kalleshi.

“Naan.”
Takira sunanshi da wata irin unique voice, dinta Wacce tasa duk wani gargasan jikinsa mikewa.

Idanunsa ya kuma lumshewa, tare da Dan motsa bakinsa saidai bai iya amsa mata ba duk da zuwa yanzu ya gama fahimtar sunan data raɗa masa kenan (Naan) ya kuwa gane ƙarshen sunansa ta ƙawata ta bashi kekkyawan lafazi.

Ita kuwa Jannart dama bata damu daya amsa mata ba, plate din abincin ta d’auko tasa akan cinyarta, cikin dan tausasawa hadi da shagwab’a tace.

“Please Naan kaci abinci, ko kad’annne, kaga babu kyau mutum yasha magani batare dayasa komai acikinsa ba, coffee bazai rik’e ka ba, please Hamma Nanu karkace a’a.”

Ta k’are maganar tana me Kallon fuskarsa, tare kuma da karyar da wuyanta gefe.

Akasalance ya bud’e idanunsa ya kalleta, Ganin irin Kallon da yakeyi mata dinne kuma ya sata mik’a masa plate din.
Babu musu kuwa ya karb’a, saidai bawai Dan yanajin zai iya cin abincin ba, pancake d’aya ya d’auka yasa abakinsa, tare da soma taunawa Ahankali.
Idanu Jannart din ta zuba masa, domin daga Ganin yanda yake tauna abincin bayajin dadin bakinsa.

Amma duk da hakan taji dadi daya karb’a yaci, saboda magananin zaifi saurin yi masa aiki.

Lomansa biyu kacal ya zare hannunsa, tare da daukan tissue ya goge hannun sa.
Akasalance ya d’ago oily eyes d’insa ya kalleta.

“Jannah Nak’oshi.”
Ya fad’a yana me sake gyara zamansa.

Murmushi tayi tare dasa hannu ta karbi plate din, magungunansa dake hannunta ta b’are hade da daukan goran ruwa ta mik’a masa.
Babu musu kuwa ya karb’a yasha.

“Muje ka kwanta.”
Ta fad’a tana me mik’ewa tsaye.

Tare da mik’a masa hannunta alaman ya kama.

D’an Kallon hannun nata yayi, kamar bazai kama ba kuma sai ya cije labbansa, tare dasa hannun nasa acikin nata, Ahankali ya Mike tsaye bisa taimakonta.

Ganin ya tsaya ne kuma ya sashi zare hannunsa acikin nata, tare da d’an matsawa ya kwanta akan gado.

Kusan Atare suka sauke sassanyar Ajiyar zuciya, shida Jannart din, saidai kuma kowannensu da manufar sauke tasa Ajiyar zuciya.

Fararen tafin k’afansa ta zubawa ido, Yayinda shikuwa ya maida nasa idanun ya lumshe.

Dai-dai lokacin kuwa kunnuwanta suka soma jiye mata knocking kofar falon da akeyi.

D’an kallonsa tayi ganin ya rufe idanunsa ne kuma yasa kaitsaye ta nufi falon.

Ahankali ta daura hannunta akan handle din kofar tare da budewa.

Dr. Sulaiman da kuma su Dr. Sadiq ne tsaye, abakin kofar shigowa falon, ganinsu da tayi dinne kuma, ya saka ta sakin murmushi, kana cikin sakin fuska tace.

“Bismillah ku iso sannnunku da zuwa.”

“Yauwa Jannart.”
Dr. Sulaiman ya amsa mata shima fuskarsa d’auke da murmushi.
tare kuma da yiwa sauran Doctors din jagora, suka karasa shiga cikin falon.

Anan cikin falon suka zazzauna.
Yayinda Jannart kuwa Kai tsaye kitchine ta wuce, inda ta kawo musu ruwa da drinks.

Amutumce suka gaisa da sauran Doctors din, bayan sun gaisa dinne kuma Dr. Sulaiman ya kalli Jannart din, Cikin kulawa yace.

“Ya mai jikin, Ina fatan babu wata sabuwar matsala da ta kunno ko.”

D’an murmushi tayi tare dasa hannu, ta gyara zaman jacket din dake jikinta, murya asake tace.

“Jikinsa Alhamdulillah, tun jiya daya sha maganin dai ciwon bai sake tashi ba.”

Kai Dr Sulaiman ya jinjina, cike kuma da samun gamsuwa yace.

“Masha Allah ai haka akeso, amma daren jiyan ya samu bacci kuwa?”

“Eh ya samu, yanzu ma yana kwance inaga baccin zaiyi, but bari nayi mishi magana.”

Ta fad’a tana kokarin mikewa tsaye.
Saurin dakatar da ita Dr. Sadiq yayi, ta hanyar cewa.

“No basai kin taso sa ba, zamu dawo anjima da yamma nasan zuwa lokacin ya sake samun k’arfin jikinsa, ga wannan mu zamu wuce wajen aiki.”

Ya k’are maganan yana me ajiye wata babban ledan restaurant dake hannunsa.

Ganin hakanne kuma yasa sauran Doctors dinma duk suka mik’e.

“Mungode sosai.”
Jannart din ta fad’a, tare da taka musu har bakin kofar fita daga falon.

Saida taga tafiyarsu kuma kafun ta dawo ta zauna, ledan da Dr. Sadiq din ya kawo ta bud’e, tare da ciro takeway daya na African dishes ta soma ci.

Bata wani ci sosai ba kuwa ta ture abincin gefe, tare da daukan bottle water tasha ruwa, sauran ragowan abincin ta Kai kitchine.

Kana ta dawo kaitsaye ta wuce d’akinsa.

Ahankali ta murd’a handle din k’ofar ta shiga bakinta d’auke da siririyar sallama.

Yana nan kwance kamar yanda ta barshi, Yayinda kuma har yanzu idanuwansa ke lumshe.

Ahankali ta k’araso jikin gadon, tare da matsowa inda yake kwance.

Kyakkyawar fuskarsa ta zubawa ido, bata ko kyaftawa, daga gefe guda kuwa anutse kunnuwanta, ke jiye mata sautin fitar numfashinsa.

“Yayi bacci.”
Ta fad’a abayyane cikin kuma sanyin murya, yanda tasan bazai jiyota ba.

Zama tayi ad’an gefen gadon,
tare da d’aukan hannunta na dama, Ahankali ta kife tafin hannun nata akan goshinsa.

Wani irin b’oyayyar ajiyar zuciya ya sauke, tare kuma da d’an motsa hannunsa batare da ya bari taga hakan ba.
Taushi da kuma laushin hannun nata, hadi da daddad’an kamshin turarenta, shiyasa shi jin wani iri acikin jikinsa.

Itakuwa Jannart sanin da tayi cewar bacci yakeyi, shiyasa ta sauko da hannunta ahankali zuwa kan lallausan sajensa, wanda daga jiya zuwa yau take matukar jin dadin tab’ashi.

Ahankali ta d’an shafa sajen nasa, tare da lumshe Idanunta cikin sanyin murya tace.

“I pray wish you quick recovery Naan, soon zaka samu sauki Insha Allah, then babu wata cuta da take d’aurewa aduniya, you’ll be okay Insha Allah Naanu.”

Ta k’are maganan tana me gangaro da hannunta, kan wuyansa, tare da tura yatsun hannunta acikin wuyan rigar sa, wanda kuma hakanne ya bata daman jiyo sautin bugun zuciyarsa.

Idanunta ta lumshe ahankali, hade da sake saukar da hannunta k’asa, har ta iso kan mararsa.

Lallausan tafin hannunta ta kife akan mararsa, cikin kuma tsananin tausayinsa da takeji, murya araunace tace.

“I’m sorry Naan ai nasan zakaji sauki, maranka zai daina daurewa haka ma cikinka zai daina ciwo, so Sorry.”

Ta fad’i hakan ashagwab’e, tare da soma d’an shafa masa saman marar, wanda kuma ta nayin hakanne, da tunanin bacci yakeyi.

Shikuwa Rayyern saukan dumin tafin hannunta akan D d’insa, ba k’aramin tayar masa da tsikar jiki yayi ba, saboda yakanji hakanne amatsayin wani salo na musamman, sannan yakanji kansa acikin wani irin yanayi a duniya ta musamman.

Idanunsa ya d’an rumtse da k’arfi, tare da fusgar numfashin da ke neman k’wace masa.

Allah yasani bai tab’ajin irin abubuwan da yakeji ayanzun ba.
Musamman Idan hannunta na yawo asaman marar tasa, yakanji duk wasu jijiyoyi dake jikinsa sun motsa, haka ma Rayyern d’insa da yakejin na harbawa.

“Yah Salam.”
Ya fad’i haka acikin zuciyarsa, Yayinda abayayyane kuwa ya fesar da wani irin zazzafan numfashin da yasa Jannart din ta d’ago ta kalleshi.

“Naan.”
Ta d’an kira sunansa ahankali, tare kuma da zare hannunta dake kan marar tasa.

Duk da cewar ya jiya amma sai yayi shiru bai amsa taba.

Itakuwa Jannart shirun da yayi dinne, yasa ta tashi daga kan gadon.
Ahankali taja blanket ta rufe masa jikinsa.

Kana ita kuma ta koma k’asa nan kan carpet ta zauna.

Rayyern kuwa jin da yayi Jannart din tabar kusa da shi ne, yasa shi sauke Ajiyar zuciya, tare da d’an gyara kwanciyarsa, ta yanda ba zata sake samun daman tab’a saman marar tasa ba, domin yayi imani Idan taci gaba dayi masa hakan, zata iya d’aid’aita tunaninsa da nitsuwarsa dama rayuwarsa gaba ɗaya ya tabbata yana gab da sakin kuka idan har zatake sashi cikin wannan yanayin.

Jannart kuwa Koda ta zauna akan sofan, wayarta ta d’auka tare da soma latsawa.

Tana nan zaune kuma wayarsa ta soma k’ara, da sauri ta jawo wayar tare da saka ta a silent saboda, batason karan wayar ya tashe sa daga baccin da yakeyi.

Wani kiran ne ya kuma shigowa, cikin wayar tasa Ganin da Tayi sunan Riyyam na yawo, akan screen din wayarne kuma, yasa ta picking call din, tare da kara wayar akan kunnenta.

Daga can b’angaren Riyyam kuwa jin anyi picking call dinne, ya sashi gyara zama tare da cewa.

“Hamma Rayyern.”

Ajiyar zuciya Jannart din ta d’an sauk’e, kana murya ad’an sanyaye tace.

“Riyyam.”

“Na’am Aunty Jannart ya jikin Hamma Rayyern, yanzu Yah Ramadan yake fadamin wai jikin Hamma Rayyern ya tashi sosai jiya, Dan Allah ina yake ya jikin nasa kuma, Ina fatan dai ya samu sauki.”

Riyyam’n yayi mata duka tambayoyin, alokaci daya kuma cikin dan yanayi na rudewa.

Jin yanayin Riyyam dinne kuma yasa, Jannart sakin ranta, cikin son kwantar masa da hankali tace.

“Jikinsa da sauki Riyyam, yanzu haka ma ya samu bacci, saidai jiya na tsorata sosai Riyyam, naji tsoro kada ya mutu barni a wannan duniya da ban san kowaba.”

Ta fad’i hakan hawaye na cika mata idanu, lokaci daya kuma duk wani raunin ta ya bayyana.

Riyyam kuwa jin abunda ta fad’ane yasa jikinsa, yin sanyi asanyaye yace.

“Allah ya k’ara sauki, duk hankalinmu ya tashi ni da su Mammy, amma yanzu da naji ya samu relief Alhamdulillah, ga Mammy nan zaku gaisa.”

Ya kare maganan yana mikawa Mammy dake gefensa wayan.

“Jannart”
Mammy ta kira sunan Jannart din tana kara wayar akan kunnenta.

“Na’am Mammy Ina kwana.”
Jannart ta amsa mata cikin ladabi da matukar girmamawa.

“Lapia kalau Jannart ya mai jikin?”
Mammy ta tambaya cikin dan yanayin damuwa.

“Alhamdulillah jiki da sauki sosai, yanzu ma bacci yakeyi.”

“Allah ya kara sauki yasa kaffarane, ya kuma yaye masa wannan ciwon yasa kiyi farar jinya.”

Mammy ta fad’i hakan da iyaka gaskiyar dake zuciyarta.

Jannart kuwa cikin dan jin dadi tace.

“Ameen Mammy mungode sosai da kulawa, Ina Zaytoon.”

“Ganinan Aunty Jannart am ya jikin Hammana?”

Cewar Zaytoon da ta cafe wayar da sauri.

D’an murmushi Jannart tayi, kana murya asake tace.

“Jikinsa da sauki zaytoon ya school?”

“Alhamdulillah My beloved please ki kulamin da Hamma kinji, Allah ya kara masa lafiya .”

“Ameen.”
Jannart ta amsa tana me fadada Murmushin dake kan fuskarta.

Riyyam kuwa dake gefen Zaytoon k’wace wayar yayi, tare da maidashi kunnensa, cikin dan yanayin sigar tsokana yace.

“Gaskiya Aunty Jannart jiya kin tayar mana da hankali, duk kinsa muntsorata, Koda mukayi waya da Hamma Ramadan dazu, saida yayi ta miki dariya saboda yace, jiyan kuka kikeyi harda shid’ewa, irin bakyason mijinki ya mutu nan why?”.

Yanayin yanda ya kare maganan cike da tsokana ne, kuma yasa Jannart din shagwabe fuska, Cikin yanayin tura baki tace.

“Wallahi Riyyam banaso.”

Dariya gaba d’aya suka kwashe dashi, musamman Riyyam da Zaytoon din, harma da Mammy saidai ita nata kasa-kasa takeyi.

Jin yanda suke dariya ne kuma yasa Jannart din turo baki, ashagwab’e tace.

“Mammy ina kinajin su Riyyam ko.”

Da sauri Mammy ta kwace wayan, tare da cewa.

“Rabu dasu abunki, jeki kula da mijinki gaba dayansu duk rashin aikinyi ne ke damunsu, Allah ya miki albarka Jannart, kamar kuma yanda kika kula da Rayyern, kema Allah ya kula dake.”

“Ameen Summa Ameen.”
Jannart din ta amsa tana murmushi, tare da sunkuyar da kanta k’asa.

Mammy kuwa zuciyarta cike da nutsuwa, ta kashe wayan

Tare da watsawa su Riyyam din hararan wasa.

Cikin sakin fuska tace.

“Yarinya tana kulawa da mijinta zaku dameta, idan tayi kuka ai soyayyace ta kawo hakan, da bata sonshi bazatayi kuka akanshi ba.”

Murmushi Riyyam nsra yayi, cikin matsanancin farincikin da yakejin kansa aciki yace.

“Mammy ba auren soyayya fa sukayi ba, Hamma Rayyern bayaso itama haka, amma yanzu naga kaman rayuwar tasu tana ta juyawa, game din na canjawa, I cant wait ranan da Hamma Rayyern da Aunty Jannart zasu so juna.”

Murmushi Mammy tayi, tare da gigirza kanta, batare da tace musu komai ba kuma taci gaba da sabgoginta.

Jannart kuwa ajiye wayar tasa tayi, tare da maida kanta ta jingina da jikin gadon, ahankali take sauk’e numfashi, Yayinda zuciyarta ke cike da tunani kala daban daban.

Rayyern dake kwance kuwa, duk wani hiran dasu Jannart din keyi yana jinsu, harta k’are wayan kuwa bacci bai d’aukesa ba.

Ahankali yake sauke ajiyar zuciya, Yayinda kunnuwansa kuwa ke jiye masa sautin fitan numfashinta, kasancewar ta kashe AC’n dake d’akin, ko ina kuma yayi shiru shi yasa ko wanni sautin motsinta, akan kunnuwansa suke sauka.

Yana nan ahaka har bacci b’arawo yazo ya d’aukeshi.

Jannart dake zaune akan carpet kuwa, game ta d’an soma yi awayarta, tana cikin game din kuma itama bacci ya d’auke ta, inda tayi pillow da hannunta na dama.


1:30 pm.

Ahankali ta bud’e Idanunta, wanda tashin farko suka sauk’a akan agogon dake cikin dakin.

Da sauri ta d’an tashi zaune, tare da juyawa ta Kai dubanta kan gadon.

Idanunta ta sauke akan Rayyern, da har yanzu bacci yake, Yayinda ya sake nad’e jikinsa da blanket.

Yunk’urawa tayi Ahankali ta tashi, gudun kada motsinta ya tashe sa ne kuma, yasa cikin sand’a take tafiya, harta k’arasa bakin kofar fita, ahankali ta bud’e kofar dakin ta fice.

Tana fita kuwa ya bud’e idanunsa, saboda kusan Atare suka farka, kawai dai shi yayi jinkirin tashi ne.

K’ofar d’akin nasa yabi da kallo, kana ahankali ya zuro da kafafunsa k’asa, tare da tashi daga kan gadon ya tsaya akan k’afafunsa.

Ajiyar zuciya ya dan sauke, saboda kwarin da yaji ajikinsa, ba kamar dazu ba dako tsayuwa yayi sai yaji jiri na neman kada shi.

Direct bathroom ya shiga ya d’auro alwalan sallan azahar, bayan ya fito ne kuma ya shimfud’a sallaya tare da tada Sallah.

Acan gefen Jannart kuwa Koda tabar d’akin nasa, nata d’akin ta wuce, tare dayin alwala tazo tayi sallah.

Bayan ta idar da sallan ne kuma, ta tashi ta fice daga d’akin, direct dakinsa ta nufa Dan ta dashi yayi sallah.

Anutse ta tura kofar dakin ta shiga bakinta d’auke da sallama.

Bayan ta maida kofar dakin ta rufe ne, kuma ta juyo tare da kallon kan gadon.

Ganin gadon babu kowa ne kuma yasa ta, zaro Idanunta tare da k’arasa shigowa cikin dakin.

Karab kuwa Idanunta suka sauk’a akansa, Inda yake kwance akan sallaya, ya lumshe kyawawan idanunsa.

Ajiyar zuciya ta d’an sauk’e tare da k’arasowa inda yake kwancen.
Batare da tunanin komai ba ta zauna agefensa, tare da sauk’e idanunta akan lafaffen cikinsa.

“Naan.”

Takira sunansa in a silent voice din daya sashi bud’e idanunsa ahankali ya watsa mata su a narke.

Fuskarta tad’an shagwabe, cikin kuma son lallab’asa tace.

“Please Naan na kawo maka abinci?.”

Yanayin yanda ta kare maganan cikin sakalci ne, yasa Rayyern din zubawa lips


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login