Showing 228001 words to 231000 words out of 350584 words

Chapter 77 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

shi dinma kallonta yakeyi ne, yasa idanunsu sarkewa acikin na juna.

D’anyin kasa da kanta tayi, Ahankali kuma ta mik’e tsaye, cikin sanyi,
ta nufi inda yake.

Ganin hakanne kuma yasa kashi zuba mata narkakkun idanunsa.

Jannart kuwa ahankali ta k’araso inda Rayyern din ke tsaye, cikin kuma yanayinta na sanyi, ta mika hannu ta karb’i ledan dake hannunsa.

Batare kuma da ta dago Kai ta kallesa ba, cikin sanyin murya tace.

“Sannu da dawowa.”

Kansa ya d’an jinjina mata ahankali, Cikin yanayin kasalan da ganinta ya haifar masa kuma, ya karasa shigowa cikin falon.

Ganin hakan kuwa shiya saka Jannart din rufa masa baya.

Akan daya daga cikin kujerun falon ya zauna, tare da lumshe gajiyayyun idanunsa, kana akasalance kuma yake shak’an daddad’an k’amshin turaren dake tashi acikin falon.

Jannart kuwa atsanake ta ajiye ledan daya kawo din akan table, Kaitsaye kuma ta wuce kitchine.

Ta k’asan idanunsa yabi bayanta da kallo, Yayinda acikin zuciyarsa yakejin wani irin abu nayi masa yawo, ga kuma kasalan daya saukar masa lokaci guda hannunsa yasa ya dafe kanshi yana mai sauke numfashi.

Jannart kuwa Koda ta shiga kitchine din, plate, cup and spoon ta d’auko, sai kuma fridge da ta bud’e ta d’auko drinks.

Atsanake ta nufo cikin falon, saidai kuma bata yarda ta saka Idanunta acikin nasa ba.

K’arasowa gabansa tayi, tare da jawo table ta ajiye plate da kuma cup din awajen.

Ledodin restaurant din daya kawo ta bud’e, tare da zuba masa abincin acikin plate din.

D’agowa tayi ahankali ta kalleshi, musamman kyakkyawar fuskarsa da ta sakeyin haske, ga kuma yalwataccen sajensa da yake kwance lub lub.

Zara zaran eye lashes d’insa da suke alumshe ta kalla, ahankali kuma cikin tausasa murya tace.

“Naan ga abincin .”

Kansa ya d’an jinjina mata, hade kuma da bud’e idanunsa, Cikin nutsuwa ya jawo plate din abincin gabansa ya soma ci.

Ganin hakanne kuma yasa ta zama ad’an nesa dashi, tare da sadda kanta k’asa, Ahankali take wasa da y’an yatsun hannunta, wanda ayanzu yin hakan ya zame mata jiki, saidai kuma azahirin gaskiya gaba, daya tunaninta ya tafi ne, izuwa wani waje na daban, saboda hakanan takejin maganganun Aunty Fauziya nayi mata yawo a kwakwalwarta.

Rayyern dake cin abinci kuwa, duk wani yanayinta yana lure dashi, time to time kuma yake yawan kallonta, saboda ba kad’anba bak’in kayan da ta sanya yayi mata kyau.

Suna nan ahaka dai harya kammala cin abincin.

Ahankali ta d’ago Idanunta ta kalleshi, ganin yana goge bakinsa da tissue ne kuma, yasa ta fahimtar cewa ya koshi.

Kasancewar kuma ita ba wani yunwa takeji sosai ba, shiyasa ta soma tartare wajen.

Ganin Rayyern din na kokarin mikewa tsaye ne kuma, yasa cikin sauri ta d’ago da Idanunta ta kalleshi.


“Naan.”
Takira sunansa asanyaye cikin kuma Dan yanayin shagwab’ar, da ta sashi tsayawa da abunda yakeyi.

Atsanake ya juyo ya kalleta, Ganin ta sunkuyar da kanta kasa ne, kuma ya sashi komawa ya zauna akan kujera.

Again idanu ya zuba mata, tare da soma karantar yanayinta.

Jannart kuwa hakanan taji ta kasa fad’an abunda takeson fadad’in, saima zuciyarta da taji tana bugawa da k’arfi.

“Kinyi shiru tell me what happened?”

Ya fad’a cikin wata irin murya mai sanyi, da kuma tausasawa wanda hakan ne ya bata wani confidence.

D’ago da kanta tayi ta kalleshi araunace, cikin cool da kuma son fahimtar dashi tace.

“Please Naan ka kawo mana abubuwan buk’ata saboda inason na fara girki.”

Ta kare maganan tana me tsaresa da idanu, tare da fargaba akan zai amince ko a’a...!






By
*GARKUWAR FULANI*



Idanu shima Rayyern din ya zuba mata, Ahankali kuma ya d’an nisa tare da gyara zamansa, atsanake yace.

“You’ll cooking why? Ko bakyason abincin restaurant din da nake kawo miki ne?”

Yayi tambayar Cikin kulawa, still kuma yana me kallonta.

Itakuwa Jannart Ganin irin Kallon da yakeyi mata ne, yasa tayi k’asa da kanta, asanyaye tace.

“A'a kawai dai inason na fara girki ne.”

“Okay shima girkin yana cikin aikin da yasa Abba ce mu taho tarene?.”
Kai ta ɗan ɗago ta kalleshi ganin yadda ya tsareta da idone yasata yin ƙasa da kai.
“Abba yace mu taho tarene dan ki kula sani, so in Kuma na liƙa miki aikin girgi ai baki da lokacin kula dani, in dai da gaske kike kula da nidin zakiyi”.
Yayi mgnar cikin kauda kai dan shi kanshi mmkin kansa yake a kwanakin nan.
Ita kuwa Jannart a hankali tace.
“Toh ai shima kula da kaine”.
Da sauri yace.
“Toh shi na yafe ki bari sai mun koma gida, a nan dai cewa akayi ki kuladani da gadina ko”.
Ya ida mgnar murmushi ya tsubce mishi.
Ita kuwa shiru, tai
“Kin ganeko?”.
Ya fada atakaice tare kuma da tashi, kaitsaye ya nufi bedroom d’insa, saboda dama bai shigo cikin gidan ba, saida yayi sallan Isha.

Da idanu ta bishi har saida taga shigewarsa, cikin dakin kafun ta tashi tare dakai plate and takeaways din kitchine, itakam yoghurt kawai tasha, tare da wuce wa dakinta ta soma buga game.

Yana shiga bedroom nasa,
ya rage kayan jikinsa kana nufi saman gadonsa ya kwanta.

Idanunsa ya dan lumshe saboda wani irin daddad’an kamshi, daya bugi hancinsa, wanda yake tashi ajikin bedsheet din.

Sake gyara kwanciyarsa yayi, tare da jawo laptop d’insa ya soma duba, sakonnin da suka shigo email dinsa.

Yana kwance ahaka kuwa bacci ya daukesa.

Yayinda a b’angaren Jannart ma hakanne ya kasance, domin tana tsaka da latsa waya, bacci mai nauyi ya dauketa.
Batare dako kofar d’akinta ta rufe ba.

Washegari.

Kamar yanda suka saba haka yau dinma, da sassafe kafun gari ya gama yin haske yayi musu ordern abincin.

Koda ya gama shiryawa kuma, abincin ya d’anci kadan, batare kuma daya jira fitowar Jannart d’in ba, ya wuce Azimut hotel Olympic Mascow inda zasuyi meeting.

Yayinda Jannart kuwa sai bayan ya tafin ta iya fitowa taci nata abincin.

*After 3days*

Ahaka suka ci gaba da rayuwa, Yayinda take iya kokarin ta wajen kulawa dashi, domin aduk sanda ya dawo takan fito ta bashi abinci yaci, sannan kuma akan Idanunta yake shan magungunan sa kana ta gyara masa ɗaki, a hankali wata iriyar sassayar shaƙuwa ta ɗan fara ratsa zuƙatansu.

Tun daga wancan ranan da sukayi maganan kayan abinci kuwa, bai sake dago mata maganar ba, har zuwa yau din kuma bai kawo kayan provision dinba.

Itama kuma ganin yayi shiru shiyasa bata sake ce masa komai agame da hakan ba, duk abunda ya kamata kuwa tana yi mishi.

Domin kullum bayan ya fita takan shiga ta gyara masa d’akinsa, tare da wanke masa toilet.

Saidai kuma dare nayi kowannensu yake kama gabansa.
Bata shiga d’akin nasa da dare ne kuma, gudun kada ya sake koranta kamar yanda yayi mata a wancan ranan duk da tana ganin sauye-sauye sa yawa daga garesa.

Ranar yau ta kasance Tuesday, kuma yaune zasu fara gwaji akan heart surgery, wannan dalilin yasa gaba d’aya, Doctors din a ankare suke.
Kowa ya shirya tsab tare da fatan samun nasara.

Kamar yanda ya saba kuma ordern abinci yayi musu, bayan ankawo yaci nasa ne kuma, ya d’auki briefcase d’insa ya wuce Hospital.

Koda ya karasa Hospital din already ya samu duka Doctors din, kasancewar shi kawai dama ake jira, shiyasa yana zuwa suka shiga theater room dan fara aikin.

Acan gida kuwa Jannart kwata kwata, ko fitowa yau din batayi ba, bacci tasha ta koshi, Koda ta tashi daga baccin kuwa game ta d’anyi awayanta, kana daga bisani bacci b’arawo ya sake d’aukarta.

Atak’aice dai haka ta k’are wunin ranan, batare da ta fito taci abincin da Rayyern din ya ajiye mata ba.

Asashin su Rayyern kuwa komai ya tafi musu yanda suke so, domin kuwa har sunyi surgery din, kuma komai yayi kyau, inda kowannensu ya fito da kyakkyawan result.

Bayan sun kammala duk wani abun da zasuyi ne kuma, kaitsaye ya nufo hanyar dawowa gida, saboda yau din duk agajiye yake jin kansa.

Kafun ya karaso gidanne kuma ya tsaya, a wani restaurant ya saya musu abinci.

Koda ya karaso gidan bayan ya gama dai-dai-ta parking din motarsa, anutse yake tafiya har ya k’araso cikin falon, yana shigowa kuwa ya soma kokarin zare, suit din dake jikinsa, yana acikin hakanne kuma idanunsa suka sauka akan takeaway din daya ajiye mata tun safe, Wanda kwata kwata babu alaman an tab’ashi.

Idanunsa ya d’an kankance cike kuma da mamaki yake Kallon takeaway din.

Ahaka har ya karasa shigowa cikin falon.
Saboda ya tabbatar da abunda yake zargi ne kuma, ya sashi bud’e takeaway din, Aikuwa abincin yana nan babu alaman ko cokali daya anyi.

Ajiyar zuciya ya d’an sauk’e tare kuma da juyawa, ya kalli kofar dakinta dake kulle.

Ahankali kuma ya janye idanunsa daga Kallon dakin, ledan dake hannunsa ya ajiye, Kaitsaye kuma ya wuce bedroom d’insa.

Yana shiga ya soma rage kayan jikinsa, tare da wucewa toilet yayi wanka hadi da dauro alwala, kasancewar ankusa kiran sallan magriba.

Yana fitowa awankan kuwa mai kawai ya shafa, sai turare wanda shafasa ya zame masa d’abi’a.

Anutse ya zura wata army green jallabiya ajikinsa, wayarsa da kuma key din motarsa ya dauka, kaitsaye kuma ya fice daga falon, bayan ya saka wasu slippers a kafafunsa.

Koda ya fito falon zama yayi Ganin akwai dan sauran lokaci ne kuma, yasa shi zama ya d’anci abincin kad’an.

Bayan ya kammala ne kuma ya shiga, kitchine ya kuskure bakinsa, batare da wani jinkiri ba kuma, ya juya kaitsaye ya fice daga cikin falon.

Cikin sa’a kuwa yana zuwa masallacin ana shiga sallan, hakan yasa da hanzari ya shiga jam’i.

Bayan sun idar da sallan kamar yanda ya saba, zama yayi a masallacin har saida suka sallame sallan Isha, Kafun ya kama hanyar dawowa gida.

Again Yana shigowa falon takeaway din abincin daya ajiye ya kalla, saidai ganin bataci abincin ba kamar yanda ya ajiye haka yazo ya samu, ya sashi d’ago kansa fuskarsa d’auke da yanayin mamaki yake Kallon kofar dakinta.

Inda yake jiyo sautin muryarta na tashi, wanda da’alama kuma waya takeyi.

Ahankali ya dan matsa kusa da kofar nata, dai-dai lokacin kuwa yaji sautin muryarta na fadin.

“Okay My Aunty Insha Allah zan kiyaye, eh zan bashi number Hajia Rabi'ah wata ƙil zai yarda ya amso min su.”

Ajiyar zuciya ya dan sauke, saboda Jin muryar nata ya tabbatar masa da cewar tana lafiya.

Kasancewar babu abunda zaiyi acikin falonne kuma, yasa shi juyawa ya wuce bedroom d’insa.

Yana shiga kuwa ya zare jallabiyan dake jikinsa, tare da komawa ya kwanta akan gadonsa, had’e da lullub’awa jikinsa blanket, kana ya jawo system d’insa ya soma latsawa.

Yana nan ahaka har bacci ya daukesa.

Jannart kuwa har dare ya raba bata fito taci abincin ba, tun tana buga game awayarta kuwa, har bacci b’arawo ya dauketa.

Washegari.

Yau dinma tun kafun ya fita yayi musu order.
Kamar yanda ta saba ay’an kwanakin kuma, ita da kanta ta zuba masa abincin a plate yaci.
Saidai ita bai ga alaman zata ci ba, Dan komawa can gefe tayi ta zauna.

Ahaka harya kammala cin abincinsa ya tafi.

Ita kuwa Jannart Ganin ya tafi ne, yasa ta tattare wajen daya ci abincin.
Batare kuma da ita taci ba ta koma d’aki tayi kwanciyarta dan fruits take dan ci in taji yunwa kasancewar akwaisu a Fridge.


*some hours ago*

Ahankali ya daura hannayensa akan waist d’insa, tare kuma da fesar da wani irin numfashi.

Abincin safe da kuma na daren daya ajiye mata, wanda duk bata ci ba ya kuma kallo, Cikin yanayin tsananin mamakin kwana biyu da ta dauka, bata saka abinci acikinta ba, ya dago ya kalli kofar dakinta.

Yayinda acikin ransa yake tambayar kansa, abunda zai hanata cin abinci har na tsawon 2days.

Wani tunani da yazo cikin ransa ne kuma, yasa shi juyawa ya nufi bedroom d’insa.

Jannart dake dakinta kuwa, tana sane bawai kuma tana kin cin, abincin bane saboda wani abu na daban, kawai dai tana yin hakanne saboda tana son, ya tuna da maganan kayan provision dinsu, ba ya ga haka kuma, ta gaji da cin kalan abubuwan da yake kawo mata din, shiyasa yanzun kawai take shan fruit.


Rayyern kuwa Koda ya shiga dakinsa, kwanciya yayi tare da lumshe idanunsa.

Ahankali yake sauke ajiyar zuciya, Yayinda acikin ransa yakejin, rashin Jin dadin cin abincin da Jannart din batayi ba.
Wani abu daya sake tunawa ne kuma, yasa shi tab’e bakinsa tare da d’age kafad’unsa, cikin halin ko in kula yace.

“Wannan damuwarta ne, bataji yunwa bane.”

Daga can wani b’angare na zuciyarsa kuwa, sai yaji kaman abunda ya fada din ba dai-dai bane, domin har abada bazai tab’a manta irin yanda tayi kuka sosai akansa ba, ta tsaya dashi alokacin da yake halin buk’atar taimako, ta kula dashi sosai more especially akan lafiyarsa ya lura tunda yayi ciwo take bashi kula ta musamman mai cike da tausayawa ta kula dashi fiye da yadda Abbanshi, da Mamy da Ramadan kan kula dashi in ciwonsa ya tashi.

Yanaji ajikinsa bai kyautu yayi mata haka ba, kodan abubuwan da tayi masa.

Ahankali ya fesar da wani irin numfashi, tare da mikewa atsanake ya karasa gaban drawern sa.

Wani riga da wando ya ciro, tare da saka kayan ajikinsa, kaitsaye ya nufi hanyar fita daga dakin.

*Nigeria.*

Alhaji Idi Sale Dakata ne ke zaune, acikin tamfatsetsen falonsa, Yayinda Abba Kabir ke zaune acan gefensa.

Zugum haka suka zauna kowannensu da irin abunda, yake sak’awa acikin zuciyarsa.

Dai-dai lokacin kuma Momy ta shigo, ta iskesu acikin irin yanayin, Dan jim tayi tana me nazartarsu, domin da dukkan alamu ta fahimci cewar, wani magana suka tattauna atsakaninsu, wanda hakan yasa duk sukayi jigum.

Ganin mood din nasu ne kuma, yasa Momyn juyawa ta koma, batare da ta ce kala ba, saboda ma ta lura kwata kwata su Abba Kabir din basu ganta ba.

Acan Mascow kuwa Jannart ne ke kwance, Yayinda wayanta ke sakale akan kunnenta, tana waya da Riyyam nsra, wanda ya hadata da Mammy da kuma Zaytoon suka gaisa.

Rayyern kuwa Koda ya fito daga cikin dakin nasa, sosai yayi kyau cikin shigar dake jikinsa.
Inda ya daura babban jacket akan shigar tasa, saboda wani irin matsanancin sanyi da akeyi.

Dan jim yayi tare da Kallon ƙofar nata, acikin zuciyarsa yake tunanin me zai fada mata, sanin bashi da wani abun cewa ne kuma, yasa shi nufar dakin nata kai tsaye.

Ahankali ya tura kofar dakin ya shiga, bakinsa dauke da sallama.

Jin alamun bud’e kofar dakinne kuma, yasa Jannart dake zaune saurin juyowa suka had’a idanu dashi.

Wayar dake kunnenta ta zare, tare da tashi ta zauna tana me fuskantar shi.
Cikin kuma Dan yanayin mamakin ganinsa acikin dakin tace.

“Naan.”

Idanunsa ya zuba mata, saboda ganin yanda duk saman breast dinta ya bayyana, kasancewar wuyan rigar dake jikinta ya zame batare da tasan hakan ba.

Ahankali ya karasa shigowa cikin dakin, tare da karasawa gaban dressing mirrorn ta, inda yaga wani cup ajiye agefe.
Lek’a Cikin kofin yayi wanda yake dauke da zuma.

Juyowa yayi ya kalleta, hakan ne kuwa yasa da sauri tayi kasa da kanta tana murza yatsun hannunta.

“Meye kike wani sunkuyar dakai, sai kace kinga Dodo.”

Kanta ta girgiza masa alaman “A’a.”
Still batare kuma da ta dago Kanta ta kalleshi ba.

Shikuwa Rayyern idanunsa ya cigaba da tsura mata, Ahankali kuma ya matso kusa da ita, tare dasa hannunsa acikin aljihun wandon sa, cikin tsareta da idanu yace.

“Meyasa bakya cin abinci, tell me mekike ci Janna?”

Kanta ta girgiza masa alaman “Babu.”
Still kuma bata dago ta kalleshi ba, haka kuma bata motsa labb’an bakinta ba.

Shikuwa Rayyern Ganin hakan ne yasa shi, bata fuska cikin tsare gida yace.

“Almost 2days baki ci abinci ba, meyasa ahaka kikeson kina rayuwa, bakisan cewar rashin cin abinci, yana haifar da Ulcer ba?”.

Saurin dan satan kallonsa tayi, saboda Jin abunda ya fada din, kasancewar tasan halinsa shine ma gwani wajen Kin cin abinci.
Amma wai yanzu da bakinsa yake fadin hakan.

Fuska tadan kwabe ashagwab’e kuma cikin narkar da murya tace.

“Nifa banason abincin ne, bayamin dadi kuma nace maka ka saya mana kayan provision amma kaki..”

Ta kare maganan tana me tura bakinta gaba.

Wanda hakan yasa shi dan lumshe idanunsa, ahankali yace.

“To kenan idan bake kika dafa abincin ba, bazaki ci ba?”

Sake kwabe fuska tayi, still a raunace tace.

“Ni fa yanzu ma yunwa nakeji sosai, kuma ni banason wancan abincin.”

Idanunsa yadan zuba mata, Cikin yanayin nazartar ta yace.

“Okay wani kalan abinci kikeso?”

“Nigerian Dishes nakeso, ba irin way’anda kake kawowa ba.”

Ta fada tana me karyar da wuyanta gefe.

“Nigerian dishes? a Mascow dinne zaki samu Nigerian dishes? like bakisan awacce k’asa kike ba ko?”

Yayi maganan yana me kallonta, Domin har yanzu idanunsa na gane masa saman breast dinta dake waje da nimples ɗin ta da suke tsaye cas.

Jannart kuwa Jin abunda ya fad’a dinne, yasa ta kwab’e fuska tare da yin rau rau da Idanunta.

“Alright Oya taso mu tafi.”

Rayyern din ya fad’a, yana me duba agogon dake daure atsintsiyar hannunta.

Itakuwa jin abunda yace dinne yasa ta tashi ta tsaya.

Kallonta ya somayi daga sama har kasa, inda take sanya da dogon wandon pencil jeans, sai kuma t-shirt mai fadin wuya, akanta kuwa hulan sanyi ne, sai kuma kafarta da ta sawa safa.

D’an soma Kallon dakin yayi, inda ya sauke idanunsa, akan wani shararan riga mai kaman abaya dake gefen gadonta.

Daukan rigan yayi tare da mika mata.

“Idan kinsa ki sameni a falo.”

Ya fadi haka yana me juyawa ya fice daga dakin.

Jannart kuwa jin hakanne yasa ta saka riga mai kaman abayan, tare da daukan wani karamin vail ta yane kanta dashi.

Cikin dan sauri ta saka wasu takalma sau ciki akafanta, wayarta ta dauka batare kuma da b’ata lokaci ba, ta rufa masa baya.


Koda ta fito falon hanyan waje taga ya nufa, wanda hakan yasa ta d’an tsayawa cikin sanyi tace.

“Naan Ina zamuje?”

“Restaurant.”
Ya fada atakaice batare kuma daya juyo ya kalleta ba.

Itakuwa jin hakanne yasa ta gyara mayafin jikinta, cike dajin dadin fitar da zatayi a karo na forko tunda suka zo, ta rufa masa baya, Dan hakanan sai taji wani farinciki, saboda tun da suka zo Mascow din bata fita ba ko sau daya.

Koda suka karaso wajen motar tasa, cikin zumudi ta bud’e murfin motar ta shiga.

Shi kansa Rayyern ya lura da irin farincikin da take ciki, wanda hakan yasa shi jin wani irin abu a Cikin zuciyarsa.

Yana shiga cikin motar ya tada ita kaitsaye suka fice daga Cikin gidan.

Suna hawa kan titi ne kuma karamar wayar tasa dake hannunta ta soma kara, Ganin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login