Showing 195001 words to 198000 words out of 350584 words
Turaren oud ta shafa ajikinta, cikin d’an hanzari ta fito falon saboda cikinta ya fara yi mata kukan yunwa.
K’arasowa cikin falon tayi ta zauna, tare da jawo ledan takeaway din gabanta.
Abincin ta tsurawa ido saboda taga kamar ba, alaman anci abincin sosai, da alamar Koda ancisa ma to bai wuce loma d’aya akayi ba.
D’an Jim tayi kamar meyin nazarin wani abu, sanin bai wani damu da cin abinci sosai bane yafi ta'ammali da kayan zaƙi, yasa ta share tunanin, abincin ta d’anci kad’an kafun ta tashi ta wuce d’aki, saboda yau din ana d’an tab’a sanyi sosai, gashi kuma bacci sosai takeji.
Rayyern shi kuwa Dr Rayyern.
Tun da ya shiga cikin masallacin bai fito ba, saida aka idar da sallan Isha, bayan ya d’an tab’a karatun Al’Qur’ani ne kuma ya d’auko hanyar dawowa gidan.
Ahankali yake taka k’afafunsa, tare kuma da kutso kansa cikin falon, gaba d’aya bayajin yana yanayi mai dad’i saboda ciwon cikin dake damunsa, duk da cewa ciwon nasa bai tsananta ba, amma dai yanayi masa kad’an kad’an, kaitsaye d’akinsa ya wuce batare da ya lura da ko Jannart din taci abincin ba, yana shiga kuwa ya fad’a kan gadonsa, tare dayin rigingine kana yaja blanket ya rufe jikinsa.
Cikin nutsuwa yake ambaton sunan Allah abakinsa, hade da lumshe kyawawan idanunsa da suka d’anyi ja, yana ahaka cikin ikon Allah bacci ya d’aukesa.
Washegari.
Kamar yanda ya saba tashi akowacce rana haka ma yau din ya tashi, saidai kuma tun tashinsa yaji cikin nasa na ci gaba da yi masa ciwo.
Duk da yana jin ciwon kuwa haka ya shirya kansa, cikin riga da wandon suit, sai kuma wani babban jacket daya d’aura akai.
Yana fitowa kuwa aka kawo breakfast, saidai ko ci baiyi ba haka ya tafi, saboda duk yana jin bakinsa babu dadi.
Jannart kuwa yau din bacci tasha sosai, Dan bata tashi ba sai k’arfe 10, bayan tayi wanka ne kuma ta fita zuwa falon.
Abincin ta d’auka taci, saidai bata wani ci sosai ba ta ture shi gefe, anan cikin falon ta kwanta, tare da d’aukan wayanta ta soma buga game.
Rayyern kuwa Koda ya shiga wajen meeting dinsu, gaba daya ya kasa nutsuwa, domin tun yana maida attension d’insa garesu, har dai abun ya soma fin karfinsa.
Fahimtar hakan da Dr. Sulaiman yayi ne kuma yasa shi, d’anyin k’asa da murya cikin kulawa yace.
“Gaskiya Dr. Rayyern ya kamata mufita mu nemo maganinka, domin naga har yanzu kamar you’re not okay.”
Idanu Rayyern din ya d’an rumtse, batare kuma da yace komai ba, ya jawo system d’insa ya soma latsawa.
shi dai kam Dr. Sulaiman yasan halin kafiyar Rayyern din Sarai, shiyasa ma baisake bi ta kansa ba, d’aya daga cikin manyan Doctors din da sukeyi musu, invigilators Dr. Sulaiman din ya samu, tare da gaya musu matsalan Rayyern din.
Wani magani d’aya daga cikin manyan Doctors din, ya rubuta tare da bawa Dr. Sulaiman yace ya nemo ya bawa Rayyern din yasha.
Sanin halin ciwon Rayyern din Idan ya tashi ne kuma, yasa babu wani b’ata lokaci Dr. Sulaiman ya fita zuwa sayo maganin.
Sosai kuwa maganin ya basa wahalan samu, Dan saida ya zagaye pharmacy har biyu amma babu, cikin sa’a kuwa a pharmacy na uku ya samu maganin.
Bayan ya dawo ne kuma ya bawa Rayyern din yasha.
Ahankali ya jingina bayansa da jikin kujera, tare da lumshe idanunsa, numfashi kawai yake sauk’ewa akai akai, Yayinda zuciyarsa kuwa ke bugawa da k’arfi.
Yana nan zaune ahaka har tsawon 30mn cikin, taimakon Allah kuwa ahankali yakejin ciwon nasa na lafawa.
3:30pm dai-dai yauma suka tashi daga meeting din nasu, inda suka tsaya wani d’an tattaunawa kuma wanda ya d’aukesu tsawon 30mn.
4 dai-dai amfanin maganin daya sha din ya k’are, Aikuwa ko mintuna biyu ba’a cika ba, yaji cikin nasa ya dawo da ciwo.
Ciwo kuma gadan gadan ba kaman yanda, ya tashi masa da safe ba.
Hakan yasa duk bayanan da sauran Doctors din keyi, baya fahimta.
Ahankali ya janye jikinsa baya, tare kuma da d’aukan car key d’insa.
Batare kuma daya tsaya sauraran wani abu ba, ya nufi inda ya ajiye motarsa.
Dr Nura dake ya dan zuba mishi ido ne.
Ya ɗan nunawa. Dr Sulaiman dake kula da duk wani motsinsa shi
Ganin ya juya ya fitane, ya biyosa saidai kafun ma ya iso, tuni Rayyern ya cilla motar tasa kan titi.
D’an Jim Dr. Sulaiman din yayi , acikin ransa yana me fatan Allah yasa kada ciwon Rayyern din ya tashi.
Rayyern kuwa tunda ya cilla motar tasa kan titi, ya daina fahimtar wasu abubuwan, murza steering motar kawai yakeyi, batare da yana tantance abunda yakeyi ba, saboda zuwa yanzu ciwon nasa ya tsananta sosai.
Wani irin gudun da yakeyi ne kuma, yasa cikin mintuna kad’an ya iso bakin k’ofar gidan nasa.
Yanayin yanda yakejin ciwon nasa ne kuma yasa, ko tsayawa saya musu abinci yau din baiyi ba.
Bayan ya dai-dai-ta parking ne kuma ya bud’e murfin motar ya fito, Cikin yanayin tafiyar dake nuna galabaitarsa, kaitsaye ya wuce cikin falon.
Yana shiga ya fad’a akan kujera, tare dasa hannayensa duka biyu ya rik’e cikinsa, idanunsa ya rumtse da k’arfi.
Domin har cikin jijiyoyin jikinsa yakejin rad’ad’in ciwon cikin.
Wani irin numfashi yake fitarwa, mai d’auke da tsananin wahalan da yakeji, saboda zafin ciwon da yakejin ne, yasa shi soma jujjuya kansa Ahankali, yake sakin nishi wanda yake fita daga bakinsa.
Jannart kuwa dake kwance a d’aki tana game, kwata-kwata bata ma ji koda motsinsa ba, saboda dama takan gane cewar ya dawo ne, ta hanyar k’aran motarsa.
Almost 1hour.
Ahankali ya bud’e idanunsa wanda yakejin sunyi masa nauyi, tare da soma sauk’e Ajiyar zuciya akai akai, lokaci d’aya kuma ya d’anji jikinsa na sakewa.
Anutse ya d’an d’ago kansa ya kalli agogon dake falon.
“6:19 pm Dai-dai da ya ganine, ya sashi yunk’urawa cikin k’arfin hali ya mik’e tsaye.
“Alhamdulillah.”
Ya fad’a k’asa k’asa saboda yanda yaji ciwon ya d‘an lafa masa.
Asanyaye ya nufi bedroom d’insa, Koda ya shiga kayan jikinsa ya cire, tare da shiga toilet yayi wanka had’i da d’auro alwala.
Duk way’annan abubuwan yanayinsu ne cikin rashin k’arfin jiki, da kuma tsananin dauriya saboda duk jikinsa babu karfi.
Fitowarsa daga wankan kenan ya saka wani, farin dogon wando da kuma farin riga, kasancewar bashi jin karfi ajikinsa sosai ne kuma yasa, ko gama mak’ala bottom din rigar baiyi ba, haka ya juya ya fita.
Adaddafe yake tafiya har ya iso waje, motarsa ya shiga tare da kunnata, kaitsaye ya nufi masallaci.
Yana zuwa kuwa ana shiga Sallah.
Hakkan yasa da d’an hanzari yazo yabi jam’i.
Bayan an idar da sallan magriban ne kuma, ya d’an matsar da jikinsa gefe tare da jingina bayansa ajikin bango.
Idanunsa ya lumshe tare da soma ambaton sunan Allah acikin zuciyarsa.
Sannu ahankali yakejin ciwon na taso masa, tamkar wanda ake yakutsa marar nasa haka yake ji.
Yana nan azaune kuma har aka kira sallan isha, Ganin anan kokarin tsaida sahu ne kuma, ya sashi mik’ewa shima ya gyara tsayuwarsa.
Komai nasa acikin k’arfin Hali yakeyi, saboda ciwon na k’ara taso masa akowanni second, hakan yasa Sallan kawai yakeyi amma ba tare da wani ishashshen nutsuwa ba, dai-dai sunkai Sujjadar raka’a ta uku ne kuma, yaji gaba d’aya duniyar na soma juya masa, Yayinda gaba d’aya jikinsa ya d’auki karkarwa, saboda wani irin matsanancin ciwo da yakeji, sosai yakejin ciwon wanda har hakan ya sashi kasa d’agowa daga sujjadan da yayi, har tsawon minti d’aya kafun ya iya d’agowa.
Adaddafe dai haka ya jure har aka idar da sallan, a sujjadarsa ta k’arshe ne kuma ya lumshe idanunsa, tare da mik’a neman taimakonsa wajen Allah.
Ana idar da sallan ya fice daga cikin jam’in, Cikin yanayin dauriya da cije baki, ya fice daga cikin masallacin, tare da nufan wajen da ya ajiye motarsa.
Acikin zuciyarsa kuwa addu’a yakeyi, ahaka ya shiga cikin motar tasa, ya nufo gida.
Kwata kwata ba acikin nutsuwarsa yake ba, wannan dalilin yasa shi yin wrong driving, ahaka har ya dawo gida.
Da k’yar ya iya shigar da motarsa cikin gidan, ko gama dai-dai-ta parking din motar baiyi ba ya fito, yana sako k’afarsa waje kuwa yaji ciwon cikin nasa na ci gaba da k’aruwa.
Ahankali yake taka k’afansa da yakejin kamar ba zasu iya jurewa d’aukan nauyinsa ba, Saboda ayanzu ciwon ya tashi masa gadan gadan, har takai ga ko bud’e idanunsa ya kasa yi, jikinsa yayinda gaba d‘aya jikinsa ke rawa sosai tamkar wanda aka jonawa shocking wani irin masifeffen zogi da raɗaɗin ciwon yakeji, ahaka ya nufi cikin gidan ido a rumtse dan in ya buɗesu ma jiri ke dibarsa duhu na rufe ganinsa.
*Jannart*
Ahankali ta zare hijab din dake jikinta, tare da mik’ewa tsaye.
Yauma sanye take cikin riga da wando na bacci, the same irin shigar daren jiya tayi, saidai kalan kayan na yau ya banbanta dana jiyan, saboda yau kayan nata pink colour ne, suna da matukar laushi kuma sosai, Yayinda suka bi jikinta suka kwanta.
Ahankali tasa hannunta ta d’an shafa cikinta dake kukan yunwa, saboda yau tun safe bata sake saka wani abu acikinta ba.
Sanin da tayi cewar zuwa yanzu baikai ga dawowa, amasallaci bane yasa kaitsaye ahaka ba tare da tasa wani mayafi ba ta nufi falon.
Dai-dai lokacin shi kuma Rayyern ya shigo, cikin juyawan kai da tsananin azabar ciwo, ya fad’a saman doguwar kujera, batare dako takalman dake k’afansa ya cire ba.
Hannayensa duka biyu ya d’aura akan cikinsa, tare da rumtse idanunsa da k’arfi yayinda gaba daya jikinsa ya debi karkarwa wani irin taune lips ɗinshi duka tamkar zai tsinkesu wata iriyar fitinenneyar zufa ce mai tattare da tsananin azaba da yanke rai da rayuwa yake tsastsafo mishi tako wanne hudan gashin jikinsa.
Cikin azaba yake fitar da numfashin wahala.
Ahankali ta bud’e k’ofar d’akin ta fito, hannunta rik’e da wayarta, sako kanta cikin falon da tayi, yayi dai-dai da sakin wani irin nishi da yayi.
“Hayhhhhhhhhh”.
Wanda hakan yasa cikin sauri ta d’ago Kanta ta kalli inda yake kwance.
Wani irin mummunan harbawa taji zuciyarta tayi, wanda hakan yasa ta tsura masa idanunta, cike da tsoro take Kallon yanda gaba d’aya jikinsa ke rawa.
ad’an tsorace ta shiga takowa cikin falon, har ta k’araso inda yake kwancen, idanunsa dake arumtse ta kalla, kana ta dawo da kallonta ga jajayene labb’an bakinsa, wa y’anda sukayi ja sosai, sai b’ari kuma sukeyi tamkar wanda yake fama da zazzafan zazzab’i.
Ahankali ta d’an sunkuyo da kanta garesa, cikin tsananin fargaba da kuma tsoron abunda zai faru ta k’ira shi da wani sunan da taji bakinta ya ambata kawai.
“Naan! Naan!!”
Sam baya cikin hayyacin da zai iya amsa mata, duk da yaji sautin muryarta acikin kunnuwansa kuma ya fahimci shi din take kira da da sunan Naan din, amma azaba da kuma zafin ciwon da yakeji ya wuce tunaninsa ayau din.
Jannart kuwa ganin bai amsa ta ba, ga kuma yanda jikinsa ke ta karkarwa yasa, ta sunkuyowa tare da matsowa kusa dashi sosai, Ahankali ta d’aura hannunta akan forehead d’insa, wanda jijiyoyin kansa suka bayyana rad’o rad’o.
Jin da tayi jikinsa babu zafi ko kad’an ne, yasa ta Kallon hannayensa daya daura akan cikinsa ya damƙe mararshi.
Duk jijiyoyin jikinsa sun mimmik’e, Yayinda fuskarsa tayi ja sosai.
Ahankali ta sake matsowa kusa dashi, lokaci d’aya kuma Idanunta suka ciko da hawaye.
Saboda ta fahimci cewar acikin biyu d’aya ne ya faru, ko ciwon cikinsa ne ya tashi, ko kuma ciwon kansa wani irin masifeffen raunine ya rufeta lokaci ɗaya ta tuno yadda hankalin ahlinsa ke mamummunan tashi in sun ganshi cikin makamancin wannan yanayin.
“Hamma Naan ka amsa mana meke damunka?.”
Ta fad’i hakan araunace tare dasa, hannayenta ta zare masa takalman dake k’afarsa.
Tana mai jin hawaye na silalo mata cikin rawan murya mai cike da rauni tace.
“Innalillahi
Naan me yake damunka? Kanka ne yake ciwo? ko cikinka? Dan Allah Hamma Naanu ka fad’amin kaji, please kaga duk jikinka rawa yakeyi.”
Jannart din ta fadi haka cikin yanayin tashin hankali, da kuma tsoro hadi da fargaban kada ciwon cikin nasa ne ya tashi.
Saboda taga yana dafe da cikinsa dayin murkususu, ga kuma wani irin numfarfashin da nishin yake sakewa akai-akai.
Ganin yanda yake ta had’a zufa ne kuma, yasa ta matsowa gab dashi, har hucin numfashinsa na dukan fuskarta.
Zip din dan Jacket din dake jikinsa ta zuge k’asa, tare dasa hannayenta duka biyu akan kirjinsa, wani irin rauni da tsananin tausayinsa takeji, d’aura hannunta da tayi akan kirjinsa ne kuma, ya sata jiyo yanda zuciyarsa ke bugawa da k’arfi-k’arfi.
Wannan dalilin yasa araunace ta fashe da kuka, cikin kukan nata ne kuma ta soma kokarin zare masa jacket din dake jikinsa.
D’an matsowa tayi garesa sosai.
Hannunta tasa ta tallaboshi da iya ƙarfinga ta d’an d’agosa daga kwancen tayi, tare da zama abakin kujeran, Ahankali ta d’aura kansa akan cinyarta, cikin sakin sheshshek’an kuka tace.
“Dan Allah Naan ka bud’e idanunka, ka kalleni kada wani abu ya sameka, ka bud’e idanunka dan Allah...”
Ta k’are maganan tana kuka sosai, tare da d’an jijjigasa saboda, zuwa yanzu ta tsorata sosai da yanda taji numfashinsa, na kokarin d’aukewa, ga kuma yanda jikinsa ke ci gaba da rawa, zufa kuwa ya keto masa takota Ina.
Ganin kukan bazai kaita bane kuma, yasa ta tashi kaitsaye ta nufi d’akinsa, Dan nema masa magani.
Saidai Koda ta shiga cikin d’akin, neman duniya tayi amma bata ga Koda kwayan magani ba, hakan yasa ta d’auko wayarsa ta fito.
Ganin abunda yakeyi dinne kuma yasa ta, sake rudewa atsorace ta taho kansa.
Saidai kafun ma ta k’araso har ya tafi k’asa zai fad’o daga kan kujeran, yanata jujjuya jikinsa hannayensa ko na dafe da cikinsa.
Wani sabon kuka ne ya sake kwance mata, cikin matsanancin tausayinsa da takeji, ta k’araso wajen, tare da durk’usawa ta zauna.
Hannayenta duka biyu tasa ta d’ago kansa zuwa kan cinyarta.
Arud’e take fad’in kalmar innalillahi wa’inna Ilaihirraju’un Hasbunallahiwani'imanwakil Naan! Naan!! Hamma Naanu!!!.
Shikuwa Rayyern da ya gama fita ahayyacinsa, jinsa acikin jikinta ne yasa shi sake matse jikinsa waje d’aya, tare da tura kansa acikinta, hannunsa na dama kuwa d’aurasa yayi akan cikin nata, duk ya zauce ya fita a hayyacinsa.
Wani irin numfarfashin azaba kawai yake fitarwa, duk da cewar yanajin duk abubuwan da take fad’a, amma bazai taba iya mayar mata da martani ba, saboda baya ko tantama yana bude bakinsa, gaba d’aya numfashinsa zai d’auke.
Jannart dake kuka kuwa Ganin yanda yake ta shigewa cikin jikinta ne, yasa ahankali ta d’aura hannunta akan cikinsa, rashin sanin abunda zatayi masa dinne kuma, yasa asanyaye ta soma shafa cikin nasa, tare da d’an dannawa kad’an kad’an.
Hakan da tayi d’inne kuma yasa shi jin, tamkar tana danne masa ciwon ne, amatuk’ar wahalce ya d’aura hannunsa akan nata, tare da sake tura hannun nata akan cikinsa, har yakai ga tana tab’o kan mararsa.
Kasancewar baya cikin hayyacinsa, shiyasa duk baisan me yakeyi ba, Haka ita Jannart dinma bata da wani nutsuwa, kuka kawai takeyi tare da sake ci gaba da danna masa cikin.
Almost 10mn suka d’auka ahaka, saidai har yanzu babu wani abu daya sanja, saima jikinsa dake k’ara sak’ewa, domin hatta numfashi yanzun da k’yar yake furgosa.
Ganin hakanne kuma yasa Jannart din k’ara rud’ewa, wayarsa dake hannunta ta kunna, cikin rashin sanin abunyi ta dannawa numbern Ramadan kira.
Adai-dai lokacin kuwa Ramadan din zaune, yake acikin falon sama yana aiki a laptop d’insa, Yana nan zaune kuma kiran wayan ya shigo, Ganin sunan Hamma Rayyern d’insa ne kuma ya sashi d’aga wayar da sauri, tare da cewa.
“Hello Hamma Rayyern.”
Idanu Jannart din ta rumtse, kana cikin tsananin rauni murya na rawa tace.
“Ramadan, Hamma Hamma ciwon cikinsa ya tashi, ya zanyi Ramadan tsoro nakeji.
Dan Allah
Ramadan ya zanyi.....”
Ta fad’i maganar cikin matsanancin kukan da ya riga yaci k’arfin ta.
Ramadan dake zaune kuwa jin abunda Jannart din ta fad’a ne, ya sashi tashi da sauri cikin tsananin tashin hankali yace.
“Innalillahi wa’inna Ilaihirraju’un, Jikin Hamm Rayyern ya tashi? Subahanallah Aunty Jannart yanzu kuna ina? ina Hamma Rayyern di yake? ciwon ya tashi sosai ko? kin basa magani?”
Ramadan din ya had’e mata duka tambayoyin, cikin tashin hankalin daya samu kansa aciki.
“Muna gida Ramadan, kuma na duba ko ina babu maganinsa ya shanye, bansan yanda zanyi ba Ramadan, numfashinsa d’aukewa yake.”
Jannart ta basa amsa murya adisashe.
Saboda kukan da tayi.
Ramadan kuwa jin yanda Jannart din ke kuka ne, yasa shi d’an dai-dai-ta nutsuwarsa a matsayin sa namiji, cikin tausasa murya yace.
“Calm down Aunty Jannart, Insha Allah Hamma Rayyern he’s will be fine, bari na k’ira Dr. Sulaiman nasan zaizo ya basa taimako, ki daina kuka Insha Allah zai samu lafiya.”
Ya kare maganan cikin lallashi.
Wanda hakan yasa Jannart din jinjina kai, tare da zare wayan akan kunnenta ta ajiye agefe.
Ramadan kuwa yana kashe wayan, Dr. Sulaiman ya kira, arude yake fad’a masa halin da Rayyern din ke ciki.
Jin hakanne kuma yasa Dr. Sulaiman tare taxi, Kai tsaye ya nufi gidan Rayyern din.
After 20mn.
Gaba d’aya Idanunta alumshe suke, saidai babu abunda suke fitarwa sai hawaye.
Har yanzu kuma Rayyern din kwance yake akan cinyarta, Yayinda ya mak’alk’aleta k’am, kansa da fuskarsa kuwa duk suna kan cikinta, wannan yasa duk wani numfashin azaba, da yake fitarwa akan cikinta yake sauk’a.
Har yanzu kuma jikinsa bai daina karkarwa ba, ga zufa dake feso masa tako ta ina.
Wani irin rik’o yayiwa Jannart d’in, tare da sake matse hannunta dake saman cikinsa, ahankali take yawo da hannun nata, tare da d’an mammatsa cikin nasa.
Wanda zuwa yanzu ya fara jin dadin hakan da takeyi masa, musamman yanda tausassan d’umin tafin hannunta, ke sauk’a akan mararsa.
Ahankali batare da ta sani ba kuma, hawayenta ke sauk’a acikin gashin kansa.
Duk da cewar baya cikin nutsuwarsa, amma hakan bai hanashi jin dumin hawayen nata acikin kansa ba da shessheƙan kukanta.
Wani irin fitinannen numfashi yaja, alokacin da yaji ta d’aura hannunta akan, faffad’an k’irjinsa wanda yake bud’e, kasancewar ta cire masa aninayen rigar tasa.
Ahankali ta tallabe habarsa cikin tafin hannunta.
Tare da d’an bubbugawa a hankali murya a sanyaye take kiranshi.
“Naan! Nasn!! Naan!!! Ka bude ido ka kada ka rufesu, gaya min dame zan taimaka maka, Naan ka bude idonka”. Take mgnar a raunace tana ci