Showing 102001 words to 105000 words out of 350584 words
gyara tsayuwarsa yayi, tare da cewa.
”Ni ne Alhaji dama Barrister Kabir ne yace na nemama masa iso.”
Murmushi Abban ya fadada, tare da cewa.
“Masha Allah kace masa ya shigo.”
Da To Baba Maud’o ya amsa, kafun ya juya kaitsaye ya nufi wajen da Barrister din ke tsaye.
“Yace ka isa.”
“To To masha Allah Nagode sosai.”
Barrister Kabir din ya fad’a, yana me bud’e murfin motar, nan b’angaren baya inda Jannart din take.
Wanda kuma tad’an rufe gefen fuskarta, da tattausan hijabin dake jikinta.
Hannunta Abba Kabir din ya kamo, tare da cewa.
“Jannart fito, amma ki fito da kafar dama sannan ki rike addu’a a bakinki.”
Kanta ta Dan jinjina, cikin kuma sheshshekan kukan da yaso kwace mata ta fito daga cikin motar.
Sosai takejin kirjinta na wani irin bugawa, ga kuma wani nauyi da takeji acikin zuciyarta.
Yayinda hawayen dake cikin idanunta kuwa har yanzu suka kasa tsayuwa, shin wanni irin kulline acikin rayuwarta da har yasa akayi mata irin wannan auren?
“Masha Allah mu isa To.”
Baba Maud’o ya fad’a, yana me shigewa gaba, shikuwa Abba dake rike da hannun Jannart ya rufa masa baya.
Koda suka isa bakin kofar falon kuwa, Abba da kansa ya taso ya bud’e musu.
Tare da yi musu iso, cikin tsananin farinciki da jin dadi.
Karasowa cikin falon sukayi, Inda Abba Kabir din ya Zaunar da Jannart akan lallausan carfet din dake cikin falon.
Kana ya zauna asaman kujeran dake gefenta.
Abba kuwa Kallon Ramadan yayi, kana fuska asake yace.
“Ramadan jeka kiramin Rayyern.”
To Ramadan ya amsa, tare kuma da mikewa cikin sauri ya haura sama dan kiran Rayyern.
Rayyern dake kwance yana latsa system d’insa, jin muryar Ramadan dake knocking yasashi bada izinin shigowa.
Bud’e kofar Ramadan yayi ya shigo.
Cikin girmamawa, yace.
“Hamma Rayyern Abba na kiranka.”
Kai Rayyern din ya jinjina, Yayinda Ramadan kuwa ya juya ya tafi.
Koda ya dawo falon, cewa Abban yayi Rayyern din yana zuwa.
Kai Abba Ya jinjina, tare da cewa.
“Masha Allah to kaida Riyyam kudan bamu waje.”
Babu musu kuwa, duk suka Mike suka nufi steps din sama.
Suna haurawa kan steps din kuma Rayyern yana sauk’owa.
Kallonsa Ramadan yayi, tare da d’an gumtse dariyar farin cikin dake cinsa na sanin yanzu shine a layi.
Shikuwa Rayyern wani irin masifeffen kallon ya watsawa Ramadan, musamman alokacin daya sauke idanunsa akan Barrister Kabir da yake Zaune acikin falon.
Hakan yaji wani irin takaici ya cika masa zuciya sabida anfa dameshi matuka an hanashi salama.
Su kuwa Ramadan da Riyyam-nsra neman waje sukayi suka tsaya, Acan saman stairs din.
Yayinda shikuwa Rayyern jiki asanyaye ya karasa saukowa cikin falon.
Inda Barrister Kabir ke zaune agaban Abba, still kuma har yanzu yana rik’e da hannun Jannart wanda ta sunkuyar da kanta k’asa.
Abba kuwa Kallon Barrister Kabir din yayi, cikin tausasa Murya yace.
“Barrister daka koma sama ka zauna, Domin aduk sanda kazo gabana ka zauna akasa sai naji abun yamin nauyi.”
Murmushi Barrister Kabir din yayi, kana cikin mutum tawa yace.
“Babu komai Alhaji, zamana a k’asan bawai gazawa bace, kuma hakan yana da dalili.”
Kai Abban ya jinjina.
Tare kuma da kai dubansa ga Rayyern wanda ya karasa shigowa cikin falon.
“Zoka zauna anan Rayyern.”
Abban ya fada yana me nunawa Rayyern gefensa, kuma kusa da Mamy dake zaune.
Yayinda Jannart kuwa hawayen Idanunta, kwata-kwata sun kasa tsayawa, saboda yanda kukan ke neman cin karfinta ne kuma yasa har shashshekan kukan nata ya Dan soma fitowa.
Idanu duk suka zubawa Jannart din da kanta ke k’asa, Yayinda tsananin tausayin yarinyar ke sake lullub’e zuciyarsu, musamman ma Mamy da taji son yarinyar acikin zuciyarta, duk da cewar bata ga fuskar yarinyar ba, amma taji ta kwanta mata.
Rayyern kuwa yanda ya dauke kansa gefe, tamkar ma baisan da wata mai sakin sheshshekan kuka acikin falon ba.
Abba Kabir kuwa gyara zamansa yayi, tare da sake rike hannun Jannart kam, cikin muryarsa da tayi rauni sosai yace.
“Alhamdulillahi.
Yau gani na agabanka Alhaji Bashir, ga y’ata nan Jannart na kawota gareku”.
Sai kuma ya ɗan numfasa kana a hankali yaci gaba da cewa.
“Bansanku ba baku sanni ba, amma musulumci ya had’a mu kamar yanda manzon Allah yace, Almuslimu ak’ul muslim, musulmi d’an uwan musulmi ne, na nemi taimako kunyi mini, har lau kuma Ina sake neman taimakonku, akan kulawa da y’ata Jannart, da kuma rik’emin amanarta, Jannart amanace awajena numa kuma nima yau zan baku amana, arikemin Jannart Amana marainiya ce, Dan Allah ku rikemin amanarta, Jannart bata da laifi, jarrabawar rayuwace tazo mata ahaka.
Kana bata da tashin hankali, Jannart yarinyace mai tsananin biyayya, haka kuma mai tausasshiyar zuciya, Jannart yarinyace mai rauni, yarinyar da maraici ya cika gaba daya rayuwarta, Ina da tabbaci akan biyayyar Jannart.
Domin yarinya ce da take gudun bacin ran wanda ke kusa da ita, Idan tayi muku ba dai-dai ba ku hukuntata kamar yanda zaku hukunta y’ay’an cikinku.”
Dan tsagaitawa da maganan nasa yayi, saboda yanda Hawaye ke sauka akan fuskarsa.
Juyowa da kallonsa yayi ya kalli Mamy, cikin sanyin jiki yace.
“Hajiya ga Jannart nan na kawo muku Amana, Dan Allah ki rikemin ita, ki dauketa tamkar yar da kika haifa acikin cikinki, Dan Allah ku killacemin Jannart, banason ko k’ofar gida ta l’eka, Idan kuma akwai buk’atar fitar ta wanda ya kama da dalili a gayamin, saboda banason idanun wasu su sauk’a akanta.
Domin fataucin rayuwarta sukeyi, tamkar wanda yaje farauta yagaji bai samu komai ba, haka suke ayanzu, da zaran lokaci ya cika akanta zasu dire, suna son su kasheta, suna tsananin son ganin bayanta,
Alhamdulillah yau inajin na sauke wani nauyi akaina...”
Kasa karasa maganan nasa yayi, saboda kukan da yakeji na tasar masa.
Yayinda Jannart kuwa tuni kuka yaci karfinta, ba abunda ke tashi kuwa face sautin kukan ta.
Wanda hakan yasa gaba daya su Abba, Mamy, da Baba Maud’o duk jikinsu yayi sanyi.
Shikuwa Rayyern zuwa yanzu ya tankwashe kafafunsa, tare kuma dayin shiru, ya sunkuyar da kansa k’asa.
Haka kuma yakejin kansa na.
Dan sarawa, Yayinda yakejin jijiyon dake cikin kannsa nayi masa ciwo.
Badon komai ba kuma saidan saboda yanda yakejin kukan yarinyar na hawa kanshi.
Barrister Kabir kuwa Hannun Rayyern din ya kamo.
Da sauri Rayyern ya ɗago kansa ya kalleshi.
Sai kuma yayi ƙasa da ida nunshi ganin yadda mutumin mai girma yana kuka.
Shi kuwa Barrister Kabir.
cikin sanyin da jikinsa yayi yace.
“Rayyern ga amanar diyata matarka”.
Ya ƙare mgnar yana mai ɗago hannun Jannart ya saka acikin tattausan tafin hannun Rayyern din tare dasa nashi hannun ya rumtse tafin hannun Rayyern dake riƙe dana Jannart ya rumtse ya haɗe su...!
*Littafin TUBALI na kuɗine special Group 1k ne ƙaramin group 500 yawan posting ne banbanci su, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in baki da halin turawa ta banki to ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp na*
By
*GARKUWAR FULANI*
11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: Wani irin raunataccen kuka ne ya kwabcewa Jannart cike da rauni shessheƙan kukan yake fitowa, yana ratsa kunnuwansu.
Banda kukan Jannart dake tashi, shiru gaba d’aya falon ya d’auka.
Yayinda Rayyern kuwa ya sunkuyar da kansa k’asa, tare kuma da rumtse idanunsa gam dan jin fatan saman idonsa nata karkarwa.
Domin kuwa adai-dai lokacin da hannun Jannart din ya sauk’a acikin nasa hannun, wani irin harbawa zuciyarshi tayi tare da buɗewa da azaban ƙarfi.
Duk da cewar kuwa ba wannan bane first time nasa daya fara tab’a jikin mace, musamman Idan akayi duba da irin yanayin aikinsa, saidai kuma a iya tsawon rayuwarsa, bai tab’a rik’e jikin mace, da sunan wai dan yaji wani abu ajikinsa ba, yana rikewa ne kawai idan takama dole, enfact ma shi baicika son duba mata ba, sai idan abun yayi worst ya kuma zama lallai dole shidin ake da buk’atar ya duba su.
Sam bai tab’ajin wani abu makamancin haka ba.
Tamkar kuma yanda zuciyar tasa ke bugawa haka ma Jannart, da itama takejin wani irin bugun zuciya, badon komai ba kuwa saidan samun hannunta da tayi acikin nasa, haka kuma Wannan shine karo na farko a rayuwar ta, da wani d’a Namiji wanda bata sani ba kuma ba Muharraminta ba ya tab’a jikinta, domin kuwa Bayan Yah Junaid, Daddy, Abba Kabir, Abdull, sai kuma Dr Lukman wanda ya kasance Dr dinta ne, babu wani wanda ya tab’a kama Koda farcenta ne, sai wannan ayanzu da hannunta yake cikin nasa.
Wanda kuma hakanne yasa taji zuciyarta tayi mata nauyi, Yayinda duk wani rauni dake narke acikin zuciyarta ya sake hauhuwa, lokaci daya taji tamkar wani mafakan kuka ta samu.
Dan tsabar kukan dake cinta har wani seizing numfashinta keyi.
Cikin muryarta da ta dashe sosai, ta saki Sabon kukan da sauti da amonsa ya zarce na baya mai cike da rauni.
Domin ayanzun kuka take da duka zuciya da gangar jikinta, kukan dake bayyana tsananin tarin damuwa da maraicin rayuwarta, kukan dake bayyana rauninta, haka kuma kukan da yasawa kowannensu matsanancin tausayinta.
Musamman Mamy da gaba daya k’walla ya cika mata idanu.
Rayyern kuwa har yanzu idanunsa a rumtse suke, saboda yanda sautin kukan nata ke ratsa cikin kunnuwansa, yasa gaba d’aya yaji kansa na juyawa, Sam bayason wani hayaniya ko kuma yawan koke-koke, kwakwalwarsa bata iya jure hakan.
Abba Kabir kuwa wasu irin hawaye masu zafi ne, suka gangaro daga kan fuskarsa, sake matse hannunsu awaje daya yayi, cikin kuma muryarsa da tayi rauni sosai yace.
“Rayyern ga amanar y’ata Jannart na kawo maka, ayanzu kaine Mijinta majiɓamcin lamuran rayuwata, kaine kuma wanda nakesa ran zaka zame mata Garkuwa, Rayyern Jannart marainiyace, wacce tataso acikin kad’aici da tarin damuwa, Jannart batasan wani farinciki ba Rayyern.
Domin ako da yaushe damuwa da kuma fargaba suke cika zuciyarta, Karikemin amanar Jannart Rayyern, Domin ayanzu duk wani motsinta yana karkashin kulawanka ne da ikonka, Jannart ta rayu akan wata turba ta daban, sannan an tarbiyantar da ita akan biyyya da kuma karb’an umarni akan duk wani abu da aka sata, ko kad’an bani da haufi akan Jannart, Domin kuwa Ina da tabbaci akanta, nasani Jannart bazata tab’a sab’amaka ba Rayyern idan kuma ta saɓa maka to ajizancin ne da yake halittar ɗan Adam.
Dan Allah ka kula da ita, Koda ace bazaka dauketa awani matsa yi na musamman ba, To Ina fatan ka karb’eta amatsayin k’anwarka, Jannart tana buk’atar kulawa Rayyern, tana kuma buk’atar farinciki, saboda ita din Marainiya ce...”
Ya Kai k’arshen maganan cikin muryarsa dake rawa, hadi da alhinin sark’ak’iyar dake cikin rayuwar Jannart din.
Ahankali kuma ya dawo da kallonsa ga Jannart din, cikin matukar sanyin murya da kuma son kwantar mata da hankali yace.
“Jannart ga Mijinki nan, kiyi masa biyayya kamar yanda kika saba, ki kuma gujewa duk wani abu dazai b’ata ransa, Dan Allah Jannart ki kiyaye kinji, Insha Allah watarana zaki samu ingantaccen farinciki, watarana duhu zaiyaye inda haske zai cika cikinsa, ako wani bayan kunci akwai farinciki,sannan ako wani bayan k’addara akwai sauki, komai da muke yi yanzu da kuma wanda zamuyi anan gaba, rubutacce kuma tsararrene, wanda Allah ya tsara mana, babu wata damuwa da zata Tabbata Jannart nasan kinyi imani da hakan.”
D’an tsagaitawa Abba Kabir din yayi, cikin kuma hawaye dake zuba a idanunsa, ya zare hannunsa dake saman nasu, tare da tallafo fuskarta, ya sumbaceta akan goshinta.
“Zan tafi Jannart, ki kula da kanki, kada ki sab’awa kowa dake cikin gidannan, Domin ayanzu sune y’an uwa kuma Garkuwarki.”
Abba Kabir din ya fad’a yana me kokarin mik’ewa tsaye.
Jannart da kuka ya riga daya ci karfinta, saurin rik’o k’afafunsa tayi, tare da sake fashewa da kuka.
Domin hakanan takejin kamar Idan ya tafi bazai dawo ba, tayaya zata iya jure zama amatsayin matar aure?
Hakan wani rayuwane da bata sanshi ba, batasan wacce irin kalubale ne zata fuskanta ba, Tabbas ta sani acikin rayuwarta gaba d’aya duhu ne, ita da batasan menene cikakken fari ciki ba, tayaya zata iya bawa wani?
Rayyern kuwa cikin takaicin kukan nata dake shirin fasa masa kwakwalwa ya zare hannunsa, tare da kawar da kansa gefe, yana mejin tamkar yasa hannayensa ya toshe kunnuwansa ko bakinta.
Abba Kabir kuwa kukan da Jannart din keyi ne ya matuk’ar karyar masa da zuciya.
Ahankali ya d’an sunkuyo, tare da kama kafad’un Jannart din cikin tausasawa hadi da rarrashi yace.
“Jannart din Abba ki daina kuka, tafiyar da zanyi ayanzu bawai yana nufin bazan dawo bane, Lallai Zan dawo Jannart, ki saki ranki ki dauka nan tamkar gidanku ne, kuma suma iyayenki ne, kamar yanda muke kulawa dake haka suma zasu kula dake, ako da yaushe Ina miki fatan al'khairi da nasara Jannart, Allah ya sanya al'barka acikin rayuwar aurenki.”
Cikin matsanancin kukan dake addabarta, ta Dan soma jujjuya Kai.
Ganin hakanne kuma yasa Mamy da ta kasa tsaida ruwan hawayen daya zubo daga cikin idanunta tace.
“Zo Jannart kema y’atace kamar yanda su Rayyern suke yayana, ki daina kuka kinji, Insha Allah zan zame miki mahaifiyar dake share kukan yayanta, ki sa aranki kuma cewar kina tare da mahaifiyarki ce, ki kalleni amatsayin wacce ta haifeki, bawai matsayin suruka ba, ni kuma har abada zan rikeki amatsayin y’a, Domin dama Allah baibani y’a Mace ba,.
To yanzu gashi ya turo min ke amatsayin kyauta biyu, y’ata kuma suruka ta, Insha Allah bazamu bari kiyi kuka ba.”
Mamyn ta fad’a tana me jawo Jannart din jikinta, tare da kwantar da kan Jannart din akan cinyarta.
Hakanne kuma yasa Jannart din, lafewa ajikin Mamyn tana sakin sheshshek’an kuka akai akai.
Abba kuwa da Baba Maud’o duk mik’ewa tsaye sukayi, saboda Ganin Barrister Kabir din da sukayi ya mik’e.
Koda ya soma tafiya, Mara masa baya sukayi, Dan yi masa rakiya.
Suna fita daga cikin falon, kuwa Rayyern da yake jinsa tamkar akan k’aya ya mik’e tsaye, ko kallon inda Jannart din take kuwa baiyi ba, kaitsaye ya haura sama, yana Jin tamkar shi dinma ya fashe da kuka suyi tayi a tare tsabar takaici, haka kawai an takura yarinya.
Tazo da wani shegen kukanta tazo ta saukar masa da ciwon Kai.
Mamy kuwa, hannu tasa ta soma sharewa Jannart din hawayen dake kan fuskarta, wanda kuma saboda tsabar kukan da tayi, har saida idanunta suka zama jajur.
“Kiyi hakuri Jannart, ki daina wannan kukan kinji, haka rayuwar kowacce ya mace yake, Aranar da aka rabata da gidan iyayen ta, saboda haka hakuri zakiyi, da sannu kuma zaki saba da zama damu,
ba amatsayin surukata kawai kike ba, ke y’ata ce.”
Mamyn ta fad’a tana me shafa bayan Jannart din alaman rarrashi.
Saidai kuma duk da haka Jannart din ta kasa tsaida hawayen dake kwaranya daga cikin idanunta, kukan ya riga dayaci karfinta, duk yanda taso tsaida kukan nata ita kanta ta gaza, amma saidai jin kanta da tayi ajikin Mamyn, ya d’ansa zuciyarta tayi sanyi ko yanzu tasan ta samu madadin Mom.
Yayinda Acan waje kuwa har bakin mota Abba da kuma Baba Maud’o suka rako Barrister Kabir.
Ganin yanda shi kansa damuwa ke bayyane akan fuskarsa ne kuma yasa Abba da kansa yace.
“Ka kwantar da hankalinka Barrister, Domin kamar yanda ka aminta damu, ka d’auko Jannart ka kawo mana ita cikin gidannan Insha Allah, bazamu bari hawayenta su zuba ak’asa ba, zamu zame mata iyaye na gari, idan tayi rayuwar maraici abaya Ina mai tabbatar maka da ayanzu Jannart bazata sakeyin rayuwar maraici ba, Zamu zame mata Garkuwa da yardar Allah, ka bamu amana kuma zamu rik’e, Jannart ba zata sakeyin kukan kadaici da maraici ba, zamu bata duk wani farinciki.”
Kai Barrister Kabir din ya jinjina, tare da kamo hannun Abban yace.
“Nagode kwarai Alhaji Bashir, Lallai Tabbas yanzu na sake gamsuwa da cewar, na kawo Jannart inda ya dace, na kawota inda za’a bata kulawa, inda bakuma za’a bari tayi kunci ba, Alhamdulillah Allah ya tayaku rik’o”.
“Ameen.”
Abba da Baba Maud’o suka amsa.
Hannu Barrister Kabir din ya mik’awa, Abba da Baba Maud’o suka sakeyin musabaha.
Bayan yayi musu sallama ne kuma ya bud’e motarsa ya shiga, Ari ne kuma ya bud’e masa gate din gidan ya fice.
Har acikin ransa yana mejin gamsuwa na abunda ya aikata, Domin yasani acikin abunda ya aikatan Kwata-kwata babu kuskure, Allah yaga zuciyarsa da kuma kyakkyawan nufinsa.
Burinsa shine fito da gaskiyar da azzalumai suka b’oye, wanda kuma yake da tabbacin Allah zai bashi sa’a, akan dukkan komai, Domin Allah ba azzalumin kowa ba ne, saidai wanda ya zalunci kansa.
Su Abba kuwa ganin tafiyarsa ne, yasa Baba Maud’o wucewa makwancinsa kaitsaye, inda shi kuwa Abba juyawa yayi ya koma cikin gidan.
Barrister Kabir kuwa kaitsaye gidansa ya nufa.
Koda ya isa cikin gidannsa karfe 12:40 na dare.
Kaitsaye dakinsa ya wuce, bayan yayi wanka ne kuma Aunty Dijat ta kawo masa Coffee.
Sai-dai ganin yanda gaba daya jikin mijin nata ke sanyaye ne yasa, ta gyara zama tare da kamo hannunsa, cike dason basa kwarin guiwa tace.
“Ka kwantar da hankalinka Abban Hafeez, Domin nasan duk wani abunda ke damunka, ayanzu bai wuce akan Jannart, meyasa zaka damu Abban Hafeez, bayan kasan cewar wannan auren shine abunda zai kawo sauyi da farinciki acikin rayuwar Jannart, wannan auren shi zaisa Jannart tasan wacece ita, shi ne kuma zai warware mata duk wani k’ulli dake cikin rayuwarta, Tabbas wannan auren al'khairi ne, kuma Insha Allah akwai lokacin da Jannart zatayi al'fahari da wannan Auren, musamman alokacin da ta gano cewar ka zab’a mata miji, mai nagarta irin wanda bashida saukin samu, sannan ka ceci rayuwarta daga sharrin mak’iyan dake kewaye da ita, way’anda take kwana acikinsu, take tashi batare da ta sani ba.”
Kai Barrister Kabir din ya jinjina, Cikin samun karfin guiwa kuma yace.
“Insha Allah Jannart zatayi farinciki, komai kuma zai yaye, ayanzu duniyarta zatayi sanyi, Domin tafita daga cikin magauta, hakika ko ayau na mutu, nasan na mik’a Jannart ga inda za’a tsaya mata, inda babu wani maitsaurin ido daya isa zuwa yaci mutumcin ta, saboda Rayyern ba kanwar lasa bane ba kuma mutum bane kamar kowaba, shi na musamman ne domin naga tsoronshi cikin idanun Magautan nasa da Jannart.
Tun ran forko kuma dana ganshi ya tunomin wani ma irin zarrarsa a tsakiyar su Yaya idi wanda sukayi nasarar kaudashi a duniya.
Sai naketa kamar Allah ya turo Rayyern garesune dan ya tono jiyansu ya tsaida yau ɗinsu ya birkita gobensu yadda yake musu mgna kamar ɗan fansa ne, Insha Allah kuma