Showing 180001 words to 183000 words out of 350584 words

Chapter 61 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

Rayyern din ya shiga jiya.

Ahankali ta sake gyara zaman babban abayan dake jikinta, Cikin yanayin takunta mai d’auke da nutsuwa ta soma takawa, kaitsaye ta nufi d’ayar k’ofar dake hannun hagu.

Koda ta k’arasa bakin k’ofar ahankali, ta d’aura hannunta akan handle din k’ofar, tare da d’an murd’awa, cikin sa’a kuwa taji k’ofar ta bud’e.

Ajiyar zuciya mai k’arfi ta sauk’e, tare da d’an tura kanta cikin d’akin.

Extra room ne mai kyau, wanda gaba d’aya aka malale k’asansa da wani lallausan carpet, Daga can gefe guda kuwa gado ne d’an madaidaici, sai kuma wani long mirror dake can gefe da gadon.
Bayan bedside carbinet kuwa, babu komai acikin d’akin.

Ajiyar zuciya ta kuma sauk’ewa, Ganin kuma akwai na urar dumama daki acikin dakinne, yasa ta juyawa ta koma falo, akwatinta ta d’auko tare da dawowa cikin d’akin.

Bayan ta ajiye akwatin nata ne kuma, tanu fi wani k’ofa dake cikin d’akin hannunta riƙe da miskil dahar ta nufi kofar, wanda take da yakinin cewa toilet ne.

Kamar yanda tayi zato kuwa hakanne, toilet ne me kyau sannan kuma akwai komai na amfani aciki.

Ganin da tayi kuma akwai shower mai bada ruwan dumi ne, yasa ta kwab’e kayan jikinta, Anutse ta sakarwa kanta ruwan d’umin bayan ta tabbatar da tsarkinta.

Wani irin dadi da nutsuwa taji alokacin da ruwan ya sauk’a akan fatar jikinta.
Sosai sanyin da takeji din ya ragu, bayan tayi wankan ne kuma tayi amfani da turaren miskin kamar yadda ta saba kana ta had’a da alwala.

Wani babban bathrobe ta saka, tare da bud’e kofar bathroom din ta fito.

Cikin d’an hanzari gudun kada sanyi ya dake shiga jikinta, ta jawo akwatinta tare da bud’ewa, ta zaro wata had’add’iyar riga mai kaman na sanyi, duk da kasancewar rigar english wears ce amma tana da kauri sosai, saidai bata da yawan tsawo domin da kad’an ta wuce mata guiwa, domin rigane irin fashion dinnan.

Koda tasaka rigar cas tayi mata, musamman da rigar ta kasance irin mai kwala dinnan ne.
Tubke dogon gashinta tayi, tare kuma da d’aukan safa mai kauri da tsawo ta sanya ak’afafunta.

D’aya daga cikin sallayun da tazo dashi ta shumfud’a, tare da zura wani dogon hijabin daya rufe mata duk jikinta, bayan ta kunna na’urar dake d’uma d’aki ne kuma, ta koma kan sallaya tare datada sallah.

Bayan ta idar da sallan tayi azkhar ne kuma ta koma ta kwanta akan lallausan gadon, tare da jan blanket ta rufe jikinta.
Wani irin ajiyar zuciya mai karfi ta sauk’e, badon komai ba kuwa, saidan nutsuwar da taji ta samu.

Acan b’angaren Rayyern kuwa Koda ya idar da sallah, karatun Alqur’ani yayi, bayan ya idar da karatunne kuma ya soma shirya kansa.

Saboda zuwa lokacin har k’arfe 7 tayi, hasken sararin samaniya ya bayyana ko ina.

Tsab ya shirya cikin wani had’add’en suit da yayi matuk’ar amsar jikinsa, takalmin Gucci da kuma Gucci parfume ya fesa ajikinsa.
Sosai yayi kyau yau din, Yayinda suit din ta k’ara fito dashi, amatsayin babban likita, yayi kyau ainun, briefcase da kuma wayoyinsa ya dauka.

Ahankali ya murd’a handle din kofar d’akin ya fito, yana me gyara agogon dake daure atsintsiyar hannunsa.

Wayarsa dake rik’e ahannunsa ne ta soma k’ara, alaman shigowar kira, picking call din yayi tare da kara wayar akan kunnensa, batare kuma da ya gama sauraran, abunda ake fad’a masa acikin wayan ba, cikin d’an yanayin gaggawa yace.

“I’m on my way.”

Yana gama fadin hakan ya zare, wayar daga kan kunnensa, cikin sauri kuma ya fice daga cikin falon.

Kaitsaye babban titin dake k’ofar gidan ya nufa, tsayawa yayi abakin titin tare da d’an soma lallatsa wayarsa, da alama sak’o yake turawa.

Bayan ya gama tura sak’onne kuma, ya maida wayar tasa cikin aljihun sa.

Almost 10mn kacal wata had’add’iyar mota ta k’araso inda yake, parking motar akayi, cikin sauri kuma baturen dake cikin motar ya fito, aladabce ya mik’awa Rayyern din key din motar.

Cikin muryar turanci baturen yace.

“We’ll come back Sir.”

“Thank you Jonas.”


Rayyern din ya fad’a atak’aice tare kuma da bud’e murfin motar ya shiga, wanda da dukkan alama dama, yana da motar Wacce Idan yazo k’asar yake amfani da ita, kasancewar ak’asar yayi karatun Degree d’insa na biyu, wannan dalilin yasa yake zaune a gidan da yake mmkin yadda akayi Abbansu ya mallakeshi anan k’asar ta Russia.

Jonas shine Wanda yake kula da komai na gidan dama duk wani abu nasu, duk da ya manyata.
Koda zuwa ya kamashi, shi yake gayawa ya gyara musu komai.
Jonas din ne ya rufe masa murfin motar, shi kuwa Rayyern cikin k’warewa yaja motar yayi gaba.

Ganin Dr. Rayyern din ya tafi ne kuma yasa, Jonas tare taxi ya koma inda ya fito.

Rayyern kuwa kaitsaye babban hospital din, dake cikin garin Mascow ya nufa, kasancewar tuntuni ya bawa sauran Doctors din, umarni akan su had’u acan hospital din, so already ma sunje shi kawai suke jira.

A hankali ya kusa hancin motarsa cikin farfajiyar.
*HSCT centre Mascow*
Cikin parking space na hospital din yayi parking, Cikin nutsuwa ya fito, tare da nufan cikin hospital din da tafiyarsa ta k’asaita...!







By
*GARKUWAR FULANI*

Yana isa farfajiyar asibitin su Dr. Sulaiman dake jiransa, suka k’araso garesa da sauri, hannu ya basu suka gaisa, bisa jagorancinsa kuma kaitsaye suka wuce, wani babban sashi na musamman dake Cikin hospital din.

HSCT centre Hospital ne me kyaun gaske wanda aka yi masa tsari mai kyau, komai dake cikinsa na musamman ne sabida shine babban asibitin horaswa da sukeji dashi a kasar.

Basu k’ara jaddada kyawun asibitin ba kuwa, saida suka shigo babban dakin ganawan manyan likitoti, wanda aka yi masa tsari na daban kuma na musamman.

D’akin taron da komansa ya kasance na glass, cike yake da manyan likitoti way’anda suka zo daga k’asashe sassan daban daban na duniya, kowanne likita kuwa ya amsa sunansa likita, wanda kuma sunzo ne dan k’arawa junansu sani.

Koda suka shiga cikin d’akin taron amutumce suka gaisa da junansu, anutse kuma kowanne ya zauna akan kujerar dake lik’e da sunansa.

Cikin girmama junansu, batare da wani babban cin k’asa ko addini ba suka soma gudanar da abunda ya kawosu.


Sosai suka b’ata lokaci wajen meeting, wanda ya d’aukesu sama da 6hours, domin tun 8:00 am suka shiga, basu fito ba kuma sai 2:00 pm dai-dai.

Nan ma bawai sun kammala bane, breaktime ne suka samu, wanda kuma hakanne ya baya musulman cikinsu daman yin sallah’n azahar.

Bayan sunyi sallan azahar dinne kuma, suka wuce wani cafe dake cikin hospital din, abinci mai kyau akayi saving nasu.
Saidai shi Rayyern bai wani ci sosai ba, duk da cewar baiyi breakfast ba yau din, amma hakan baisa yaci abincin sosai ba.

Bayan sun kammala cin abincinne kuma, suka sake komawa meeting din.

Basu suka fito ba sai sallan la'asar.
Koda sukayi salla kuwa, sashin da sabbin na'urorin aikin su suka nufa nan akai ta gwada musu ko wanne da kuma aikinsa
Basu fito ba har sai 5:30 pm, gaba d’ayansu agajiye suke, duk da cewar dukansu sun samu k’arin haske akan abubuwa da yawa, amma gaba d’aya sun jigata, saboda zaman waje daya babu dadi.

Fitowarsu din kenan kuma, Rayyern ya kalli su Dr. Sulaiman way’anda duk gajiya ya bayyana atattare dasu.

“I hope all yours. understanding the meeting?”

Yayi maganan yana me gyara zaman suit din dake jikinsa da rike jakar laptop nashi wanda shiyasa baya son Usman P.A yayi nesa dashi.

“Yeah we understanding.”

Gaba d’aya suka had’a baki wajen amsa masa.

Kai ya jinjina cike da gamsuwa, dai-dai lokacin kuma taxi din da suka tara suka k’araso.

Rayyern kuwa juyawa yayi ya nufi motarsa, shi kansa agajiye yake ga kuma wani irin kasala dake saukar masa.

Kusan Atare suka fita daga harabar asibitin, shida su Dr. Sulaiman way’anda suka shiga cikin taxi.

Suna hawa titi kuwa suka raba hanya, inda su masaukinsu Brosko hotel Arbat l, direct hotel dinsu suka nufa, shikuwa Rayyern hanyar gidansa ya nufa.

Cikin nutsuwa yake driving dinnasa, Dai-dai yazo wajen HALAL Sapiens RESTAURANT ne kuma ya tsaida motar, tare da fitowa ya nufi ciki.

Takeaway na african dishes yayi, sai kuma na salad and Chinese dishes.
Yayi hakanne kuma saboda sometimes yafiso yana mixing food.

Gaba d’aya acikin tsarinsa ma babu Jannart, domin kuwa kwata-kwata ma ya manta da cewar yazo da MACE.

Bayan ya karb’i takeaway dinnasa ne kuma, kaitsaye ya koma mota tare da nufar gidan nasa.

Koda ya iso gidan acikin compound yayi parking motar, Ahankali yake tafiya yana me zare suit din dake jikinsa.

Hannunsa ya d’aura ajikin kofar, tana bud’ewa ya tura kansa ciki.

Ahankali ya sauk’e Ajiyar zuciya, tare kuma da ajiye ledan Halal Restaurant din dake hannunsa akan kujera.

Direct bedroom d’insa ya wuce, yana shiga kuwa ya rage kayan dake jikinsa, tare da wuce bedroom in 20mn yayi wanka.

Bayan ya fito ne kuma ya shirya kansa, cikin wasu Sabin kaya.
Wayarsa ya d’auka kana ya kuma dawowa cikin falon.

Zama yayi akan sofa tare da tank’washe k’afafunsa, Ahankali ya bud’e ledar Halal restaurant din.

Chinese dishes din ya soma ci, Yayinda ya maida hankalinsa gaba d’aya kan laptop din dake gabansa.

Daga can cikin left side bedroom din kuwa, Jannart ce kwance tayi lub akan gado.

Wanda zuwa yanzu kuma tayi matuk’ar jigata, saboda wani irin yunwa dake damunta, kasancewar rabonta da abinci tun jiya da safe, Domin ko acikin jirgi wani dan cake kawai taci.

Tun tashinta yau din kuwa babu abunda takeci sai ruwa.
Wanda zuwa yanzu har ruwan ya soma murd’arta.
Ga kuma wani shegen sanyi dake damunta.

Hannu tasa ahakali ta dafe Kanta dake d’anyi mata ciwo, her know tasan babu kowa acikin gidan, kasancewar d’azu ta fito, ta kuma gama dube dubenta amma sam bataga alaman bayan ita akwai wani rai agidan ba, har kitchine din dake cikin falon ta shiga wai ko, zata samu abunda zataci amma babu komai.
Hakan kuwa shi yasa koda tayi sallan la’asar ta dawo daki ta kwanta.

Duk yanda taso bacci ya dauketa kuwa abun ya kasa, saboda yunwa ya hanata sukuni.

Shikuwa Rayyern baiwani ci abincin sosai ba, ya mik’e tsaye, saboda yaga lokacin sallan magriba tayi.
Direct dakinsa ya koma ya d’auro alwala.

Koda ya fito car key d’insa ya dauka, tare kuma da ficewa daga Cikin gidan gaba d’aya.

Kasancewar yana dan gudu ne kuma yasa, tafiyar 13mn ne ya kaisa babban masallacin.

Yana zuwa kuwa ko mintuna 3 baiyi ba aka shiga sallan magriba.
Bayan sun idar ma haka ya zauna acikin masallacin, har saida akayi sallan Isha.

Acan gidan kuwa Jannart adaddafe tayi sallan Isha, saboda yunwan da take cinta aciki, bayan ta idar da sallan ne kuma ta sake dawowa falon.

Aikuwa cikin sa’a ta samu sauran abincin da yaci ya rage, zama tayi awajen cikin yunwa, batare kuma da tunanin komai ba ta jawo takeaway d’aya ta soma ci, sosai taci abincin har saida taji cikinta ya kama, kana ta bi da ruwa.

Tana gama cin abincin kuwa lokaci d’aya, taji wani irin kasala ya sauk’ar mata azabebben sanyin da takeji ya ɗan ragu kaɗan.

Ahankali ta mik’e tsaye tare da wucewa d’akinta, tana shiga kuwa ta fad’a kan gado, tare da jawo blanket ta rufawa jikinta, lokaci daya kuma taji wani irin bacci na fusgarta.

Shikuwa Rayyern bayan an idar da Sallan isha’n, kaitsaye hanyan gida ya nufo.

A hankali yayi paking kana ya fito tare da rufe motar, cikin yanayin gajiya, Bacci da kasala ya nufi cikin gidan,
hannunsa ya ɗaura tsakiyar kofar lokacin ɗaya ta buɗe, cikin lumshe ido ya kutsa kansa cikin falon.
Yana taku cikin alamun bacci, gaban santer table ɗin ya nufa dan ɗaukar System ɗin sa daya bari a wurin.

Da sauri ya ɗan zubawa ledodin kan table ɗin idanu,
“Yah salam”.
Ya faɗi tare dasa hannunsa ya dafe kansa.
Allah ya sani shi ya ma mance da ita gaba ɗaya sai yanzu da yaga ledodin da ya bari an sauya musu tsarin zama ta fado mishi a rai, a fili yace.
“Astagfirrullah ba ga irinta nanba na gayawa Abba yaki fahimtata, ni yaushema na kula da kainama bare wata da aka lika min gashi nan wlh na mance da ita”.
Ya ƙarashe mgnar yana k’arasa isowa gaban table din.

Yana isa kuwa idanunsa suka sauk’a akan ledan abincin daya bari, ga kuma wani takeaway dake gefe wanda aka bud’e.
Da dukkan alama kuma yasan itace taci abincin.

Kansa ya d’an girgiza tare da lumshe idanunsa, cikin d’an yanayin gajiya yace.

“Sune suka ja miki Allah ya gani ba laifina bane, na fad’awa Abba cewar ni bazan iya kula da wata mace ba, amma yasaka dole saida nazo da ita, zata takurani nasani, then ba Lallai na iya kulawa da cinta ba, cause nima ban kula da nawa cin ba.”
Ya ƙare mgnar yana mai
D’aga kafad’unsa yayi tare kuma da bud’e hannayensa alaman ko oho, bai sake bi takan takeaway dinba kuma ya wuce zuwa bedroom d’insa.

Yana shiga ya kwanta tare da buɗe laptop d’insa yana dan latsawa, ahaka har bacci ya d’aukesa.

Yayinda ab’angaren Jannart kuwa tuntuni ma, ita baccin ya d’auketa.

Washegari.

The same 7:00 am dai-dai ya gama shirya kansa, still cikin wasu tsadaddun suit, saidai colourn ya banbanta dana jiya, Domin yau din ash colour suit ya saka, sai kuma wani babban jacket mai kyau daya d’aura akai, musamman Dan tarewa kansa, masifaffen sanyin da akeyi.

Fitowa falon yayi cikin shirinsa na office tsab, zama yayi akan d’aya daga cikin kujerun falon, tare da zaro wayarsa yayi musu ordern abinci.

Laptop d’insa ya bud’e tare da d’an soma tattab’awa, yana nan azaunen kuwa yajiyo k’aran intercom, da’alama kuma order’n abincin da yayi dinne ya iso.

Ahankali ya mike tsaye tare da k’arasawa ya bud’e kofar, kaman yanda yayi hasa she din kuwa hakanne, domin abincin ne aka kawo, karb’a yayi kasancewar kuma free delivery ne, shiyasa shi juyawa ya koma ciki.

Zama yayi tare da bud’e takeaways din, way’anda yaga zai iya ci ya d’an tsakala, batare kuma da yaci sosai ba ya tashi, ya wuce zuwa HSCT centre hospital domin yasan yauma 8:00 am dai-dai zasu shiga meeting.

Fitannasa da kamar 17mn Jannart ta bud’e kofar dakin ta fito, sanye take cikin wani riga da wandon jeans, da sukayi matukar kama jikinta, kasancewar kayan masu kauri kuma shiyasa, basu wani bayyana surar jikinta sosai ba, uwa uba kuma kaurin nasu ya rage mata kaso 30 acikin d’ari na sanyin da takeji.

Ahankali ta k’araso cikin falon, sauk’e idanunta akan abincin da tayi ne kuma yasa ta sauk’e Ajiyar zuciya, domin kafun yanzu harta fara tunanin wuni da yunwa.

Zama tayi acikin falon tare da kunna TV plasma, Anutse kuma cikin kwanciyar hankali ta soma cin abincin.

Bayan ta kammala ne kuma ta kimtsa falon, tare da dawowa ta kwanta akan wata cushion, din da musamman akayi ta dan shak’atawa.

Acan b’angaren Rayyern kuwa yauma taron nasu ya dau zafi sosai, Dan yau din kamar karantar dasu akeyi, akan sikila ta yanda za’a magance ta, da kuma yanda za’a iya sanjawa mai d’auke da cutar jini.

Sosai kuma duk Doctors din suke enjoying abunda ake koyar dasu.


*Nigeria*

Mamy ce zaune acikin falon tayi shiru, saboda duk haka takejin gidan nasu babu dad’i, domin hatta Ramadan yanzu ba zama yakeyi ba, gaba daya hankalinsa, ya maidashi akan hospital dinsu, Idan ya fita baya dawowa saida yamma.

Abba da shigowarsa kenan, ganin yanda matar tasa ke cikin damuwa ne yasa shi cewa.

“Ruk’ayya.”

Ya k’ira sunanta atausashe.

Hakan kuwa shiya saka ta juyo ta fuskancesa.

“Tunanin me kikeyi haka?”
Abban ya tambaya yana me k’arasowa cikin falon.

Mamyn kuwa Ajiyar zuciya ta sauk’e, cikin dan yanayin sanyin dake dauke da kewa tace.

“Kewar su Rayyern da Jannart nake, gaba d’aya kwana biyun nan gidan duk babu dadi, ga Ramadan ba zama yake ba, dama ace Riyyam bai koma ba, to danasan abun da sauk’i, gaskiya nima yanzu kam na matsu ayi batun auren Ramadan, akawo mana Wacce zata na d’an d’ebe mana kewa.”

Mamyn ta k’are maganan cikin dan damuwa.

Abba kuwa murmushi yayi tare da zama akusa da ita, Cikin kulawa kuma yace.

“To in bandake da abunki Ruk’ayya gaki ga mijinki kuma wani kewa ne ya rage miki?”

Murmushi itama Mamyn tayi, kana cikin dan sakin fuska tace.

“Hakane amma nima ai inason kusanci da y’ay’ana matsayin kewar miji da ban ta yarama da ban ina son yarana.”
Ta ida mgnar hawaye na silalo mata da alamun akwai wani babban abin data tuna wanda ke damun rayuwarta.

Kai Abban ya jinjina tare da gyara zamansa cikin tausasawa yace.

“Badamuwa maganar auren Ramadan, yanzu muna jiran cewa daga wajen iyayen yarinyar ne, Insha Allah za’ayi bikinsu nan bada jimawa ba,
Sannan yara kuma keda Allah ya bawa Rayyern, Ramadan, ai saikice Alhamdulillah.”
Uhummm taja wani dogon numfashi tare da zuba mishi ido alamun tuni.
Shi kuwa Abba kai ya jinjina mata, tare kauda zancen da cewa.
“Amma niko tunda yaronnan Riyyam-nsra ya tafi kunyi magana dashi kuwa?.”

Murmushin Jin dadi Mamyn tayi, cikin farinciki kuma tace.

“Masha Allah,eh munyi magana dashi, washegarin tafiyarsa Ramadan ya k’ira ya kuma bani wayar mun gaisa.”

Kai Abban ya jinjina.

Dai-dai lokacin kuma Ramadan ya turo k’ofar falon ya shigo.

Akusa da Mamyn nasa ya zauna, bayan yayi musu sannu da gida ne kuma, ya sake dagowa ya kalli Mamyn nasa, cikin sanyi yace.

“Mamy kina ta zaune duk gidan babu dadi ko?”

Kai Mamyn ta jinjina masa alaman “Eh.”

Hakan kuwa shiyasa Ahankali ya d’an gyara zamansa, tare da cewa.
“Ai Mamy na fad’a miki cewar gidannan bazai yi dadi ba, matukar babu su Hamma Rayyern, duk gidan ya rame mun zama abun tausayi.”

Murmushi Mamyn tayi tare da kallonsa, domin ita ta gama sanin ayanzun me yake nufi, wanda kuma yanzu suka gama maganan abunda yakeso din da Abba.

Cikin son kawar da zancen nasa tace.

“Yauwa kiramin Riyyam nsra mana.”

“To.”
Ramadan din yace tare dayin dialing numbern Riyyam, bugu biyu ya d’aga, bayan sun gaisa ne kuma ya bawa Mamyn waya.

Mamy na amsa Daga can b’angaren Riyyam nsra yace.

“Wallahi I miss you so much Mamy na, nayi missing girkinku keda Aunty Jannart.”

Murmushi Mamy tayi kana cikin danjin dadi tace.

“Muma munyi kewarka Riyyam ya Mammyn ka da kuma Zaytoon?”

“Duk Suna lafiya Mamy yasu Abba, da Hamma Rayyern


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login