Showing 249001 words to 252000 words out of 350584 words

Chapter 84 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

jikinsa.

“Nima yau Gadinki zanyi.”
Ya fad’i hakan da wata irin muryarsa, Wacce bata fita sosai, kana kuma take asanyaye.

Jin abunda ya fad’a d’inne kuma yasa Jannart din saurin bud’e Idanunta, tare kuma da kasala cikin shagwab’a tace.

“A’a nidai banason gadin, kuma ai na warke ni katafi kawai.”

Ta fad’i hakan batare da ta juyo da Idanunta ta kalleshi ba.
Saboda kwata kwata batajin zata iya Kallon, cikin idanunsa wanda suka juye izuwa wani kala na daban.
Hakan yasa ta sauke idanunta akan faffad’an kirjinsa.

“Ni babu inda zan tafi.”
Rayyern din ya fad’a yana me sauk’e idanunsa, akan kirjinta wanda ke tasowa da komawa.

“Meyasa Naan?”

“Saboda kema kinyi gadina alokacin da bani da lafiya.”
Ya fadi hakan yana me lumshe idanunsa, saboda wani irin harbawa da yaji Rayyern d’insa tayi, sakamakon Ganin shatin nipples dinta da yayi, way’anda suke tsaye tamkar zasu tsone masa idanu sabida sunji abokin rayuwarsu.

Lokaci daya kuma yaji duk jijiyoyin jikinsa na motsawa, ajikinsa yakejin bakon yanayi, wanda ke nuni da cewar yana buk’atar wani abu.
Saidai kasancewar bai tab’a jin feeling din wata mace ba, arayuwarsa shiyasa ayanzun baisan hakikanin abunda yake buk’ata ba amman dai koma menene ya tabbar yana jin daɗin wannan yanayin da suke ciki.

“Nidai banason gadin ai zan iya yiwa kaina komai, kuma kaima lokacin da nake gadinka ai korata kayi, harda min masifa da tsawa.”

Tayi maganan cikin yanayin tsoro da kuma bacci sosai, da kasala hadi da sakalcin da rashin lafiyan ya k’ara mata.

Fahimtar magungunan da tasha din sun fara yi mata aiki ne, yasa Rayyern din d’an sake rank’wafowa kanta ahankali, har ya zamana numfashinta da nashi Suna gauraya dana juna, haka ma faffad’an kirjinsa wanda kiris ya rage, ya sauk’a akan tsayayyun breast dinta.

Daddad’an kamshin turarenta da kuma kamshin numfashinta daya shak’a ne, yasa shi k’ank’ance rinannun idanunsa, tare da bud’e labb’an bakinsa, murya can k’asa cikin sanyi da kuma sabon yanayin da yakejin kansa aciki yace.

“Kinaso na tafi?”

“Ummm.”
Ta bashi amsa tana me sake gyara kwanciyarta, batare da ta sani ba kuma ta sake turo masa kirjin nata gaba.

Wanda hakan ya bawa kirjinsu daman had’ewa waje d’aya.

Take kuwa Rayyern din yaji jijiyoyin Rayyern d’insa na ci gaba da motsawa.

Numfashi yaja afusge tare kuma da d’an fesar da iska ta bakinsa,
Ahankali yace.

“Naji zan tafi amma sai kinyi bacci, oya close your eyes.”

Yanayin yanda yayi maganan da sexy sound ne, yasa Jannart din d’an bud’e bakinta, kamar meson cewa wani abu kuma saitayi shiru.

Domin akaron farko itama yanayin nasa da abun da yake mata, yasa taji wani iri acikin jikinta, duk da cewar akwai yanayin bacci atattare da ita.

Idanunta ta d’an lumshe ahankali, batare kuma da ta cewa Rayyern din komai ba, ta soma sakin Ajiyar zuciya akai akai.

Rayyern kuwa Ganin hakanne yasa shi d’an zamewa, tare da janye jikinsa daga kusan cin da suke dashi.

Acan gefe da ita ya kwanta, irin kwanciyarnan ta rub da ciki, hade da lumshe idanunsa, ahankali yake fitar da wani irin numfashi, wanda sautinsa ke tashi sama sama.

For the first time da yaji yana buk’atar mafaka, mafakar kuma da baisan ko na meye ba.
Idanunsa dake alumshe ya bud’e tare da sauke ganinsa, akan Jannart din.
Kirjinta dake dan tasawa ya kalla, kana anutse ya gangaro da kallonsa zuwa kan fuskarta, zara zaran gashin Idanunta dake akwance lub ya kalla.
Da’alama kuma bacci ya fara d’aukarta, saboda yanda yaji numfashinta na fita.

“Janna.”
Ya kira sunanta Ahankali da kuma muryar nutsuwa, Wacce tafi kama da rad’a.

Jin shiru bata amsa shi bane kuma, yasa shi yarda akan cewar bacci ya d’auketa.

Tashi yayi daga kwancen da yake, tare da jan blanket ya rufa mata ajikinta.
Dai-dai yazo wajen kirjinta ne kuma batare da zato ko tsammani ba yaji ta rik’e hannunsa.

“Naaan!”
Jannart din ta kira sunansa cikin magagin bacci, tare kuma da damk’e hannunsa, still cikin shaukin baccin nata ashagwab’e tace.

“Hamma Naanu kacewa Naan ya fitamin daga d’akina, ya dena taɓa min Caɓɓullena.
Kuma ai shima yana da d’aki kuma Idan na shiga korata yakeyi, kuma kace masa ya daina danneni nauyi ne dashi kaman doki....”

Ta k’are maganan tana me sake matse hannunsa, tare da gyara kwanciyarta dan da’alama ta fara jin dadin baccin nata.

Rayyern kuwa jin abunda ta fad’ane, yasa shi sakin murmushi tare da matsowa, ahankali ya daura hannunsa akanta tare da soma shafa gashin kanta wanda ke watse akan pillow.

Ajiyar zuciya ya sauke Yayinda daga cikin ransa kuwa, yakejin wani irin rauni mai dauke da tausayin Jannart din.

Tabbas yasan acikin rayuwarta akwai abubuwa da yawa wanda bata sani ba, baisan ya akayi rayuwar yarinyar ya kasance a haka ba, amma saidai koma meye yanzu yanajin tausayinta sosai, saboda ya fahimci cewar ita din wata kalan halittace mai raunin gaske.

Idanunsa ya kuma lumshewa, hade da zamewa ya kwanta akan gadon, hannunsa dake cikin nata ya soma kokarin zarewa, amma sai yaji ta rikeshi k’am.
Wannan dalilin yasa shi gyara kwanciyarsa.
Sanin da yayi cewar tayi bacci ne kuma, yasa shi d’aura d’ayan hannun nasa, akan saman mararsa Wacce yakejinta amatuk’ar kumbure.

Domin har yanzu Rayyern d’insa bata daina motsawa ba, aduk sanda murya da kuma kamshin turaren Jannart din zasu ziyarceshi kuwa, sai yaji duk wata jijiya dake kan Rayyern din nasa ta motsa.

Saman marar nasa ya dan soma shafawa ahankali, sai yakejin tamkar hannun Jannart dinne awajen.
Saboda moment dinsu na baya daya dawo masa.

Baisan Meyasa ba har yanzu wannan moment din, ya kasa barin tunaninsa.
Yana ahaka ne kuma bacci ya d’aukesa, batare daya cire hannunsa daga kan marar nasa ba.


*5: am*

Dai-dai alarm din wayarsa wacce ke kan gadon ta soma bugawa, wanda hakan yasa shi bude idanunsa, tare da daukar wayar tasa da sauri ya tsayar da alarm din gudun kada ya tasheta daga baccin da takeyi.

Juyowa yayi ahankali ya kalleta.

Kwance take ta mik’e duk jikinta, wanda hakan ya bawa kyakkyawar surorin jikinta bayyana, musamman santala santalan cinyoyinta, da kuma tsayayyun breast dinta, kasancewar tuni aninayen dake gaban rigar nata sun b’alle, saboda juyin da ta dingayi acikin baccin.

Ganin breast din nata kaman zasu tsole masa idanu, da yayi ne kuma yasa shi janye idanunsa, acikin ransa yake ambaton sunan Allah, saboda yasan matukar ya ci gaba da Kallon breast dinta ahaka, baisan abunda zai iya faruwa ba, domin sau d’aya tak da yaga nipple dinta, ji yayi gaba daya duniyar na juya masa, Rayyern d’insa kuwa jinta yayi tamkar zata bar gangar jikinsa daya taɓasu kuwa ji yayi kamar nfiffige yayi yana firewa samane.

Ahankali ya zare hannunsa dake cikin nata, Tare da sake rufa mata blanket kana cikin sand’a ya sauk’o daga kan gadon.

Kaitsaye batare kuma da yayi kwakkwaran motsin da yasan zai tashe ta, daga bacci ba ya fice daga cikin dakin.

Yana fitowa daga bedroom din nata kuwa dakinsa ya nufa.
Tare da soma rage kayan jikinsa, bayan ya daura towel akan waist d’insa ne kuma kaitsaye ya wuce bathroom, inda ya had’awa kansa ruwan wanka.

Kamar Koda yaushe atsanake yayi wankansa, bayan ya gama wankanne kuma ya d’auro alwala.

Koda ya fito daga bathroom din, karamin towel ne ahannunsa yana goge ruwan dake jikinsa.

Bayan ya kammala tsane jikin nasa ne kuma, ya bud’e sif din kayansa.
Wani riga da wando ya ciro tare da sakawa ajikinsa, batare da wani bata lokaci ba kuma ya d’auki key din motarsa, tare da bud’e kofar dakin ya fito kaitsaye ya wuce masallaci.


*5:40 am*

Ahankali Jannart din ta gama ware Idanunta, wanda suka d’an k’ank’ance saboda bacci.

Agogon bangon dake gefen gadon nata ta kalla, ganin lokacin Sallan asuba ya wuce ne kuma yasa ta tashi da sauri.

Blanket din da take lullub’e dashi ta kalla, lokaci d’aya kuma abubuwan da suka faru daren jiya suka soma dawo mata.

Da sauri ta waiwaya tare da soma k’arewa d’akin kallo, Ganin babu alamun Rayyern dinne kuma yasa ta sauk’e ajiyar zuciya, tare da d’an langwab’ar da Kai.
Tamkar yana gabanta tace.

“Aina d’auka anan ka kwana, nace maka ka tafi dakinka, ka tafi dakinka amma kaki, saida kaga nayi bacci sai ka lallab’a ka gudu, da ace anan ka kwana ainima dana jaka na fitar dakai da karfi, kamar yanda kayimin da naje dakinka kazo kana lallatseni.”

Ta k’are maganan tana me sakin k’wafa, lokaci daya kuma ta zare blanket din dake jikinta, tare da zuro kafafunta kasa kana ta Mike tsaye.

Direct toilet ta wuce tare da d’auro alwala, Koda ta fito kayan dake jikinta ta sauya, zuwa wani doguwar riga da hijab.
Bayan ta shumfud’a sallaya ne kuma ta tada sallah.

10mn ta d’auka wajen yin sallan, domin Koda ta idar bata tashi daga kan sallayan ba har saida ta kammala azkhar dinta.

Ganin Lokacin shida da yan wasu mintuna ne, kuma yasa ta koma kan gadon ta kwanta, take kuwa sabon bacci ya sake d’aukarta.

Acan b’angaren Rayyern kuwa tunda aka sallame sallan asuban, yake zaune acikin masallacin yana karatu.
Har saida yaga gari ya gama yin haske sosai, kafun ya rufe al’Qur’anin, tare da shafa addu’o’insa ya fito.

Dai-dai lokacin kuwa 7:10 ta cika.
Motarsa ya shiga tare da yi mata key, kaitsaye ya nufo gida, kamar yanda ya saba kuwa tun kafun ya karaso gidan yayi musu ordern abinci.

Kasancewar yau Monday ne kuma, yasa yana shigowa cikin gidan direct bedroom d’insa ya nufa.

Again wanka ya sakeyi, bayan ya fito ne kuma ya shirya kansa, cikin wani had’add’en black and white suit, wanda sukayi masa kyau sosai.

Takalmin Gucci mai kalan black ya saka ak’afafunsa, tare kuma da agogon rolex Golding ash.
Sosai kayan suka sake bayyana haske da kyaun fatarsa, Yayinda fuskarsa kuwa tafi komai d’aukar hankali atattare dashi, musamman k’awataccen sajensa dake sheki.

Car key and briefcase da kuma wayarsa ya dauka, kana cikin takunsa na nutsuwa ya fice daga cikin dakin, jikinsa na tashin dadd’an k’amshi.

Anutse yakai dubansa ga kofar d’akin Jannart din, duk da baisan cewar zuwa yanzu takai ga tashi ba ko a’a, haka ya nufi bedroom din nata kaitsaye.

Ahankali ya murd’a handle din kofar d’akin ya shiga bakinsa d’auke da sallama.

Dai-dai lokacin kuwa Jannart din, ta bud’e kofar bathroom ta fito, jikinta dauke da danshin ruwa, wanda da alama tashinta kenan taje tayi wanka.

Idanunsa ya tsura mata yana me kallonta daga sama har kasa, kasancewar tana sanye ne da Bathrobe ajikinta, sai kuma wani karamin towel dake rike ahannunta.

Jannart ko Ganin irin Kallon da yakeyi mata d’inne, yasa ta turo d’an bakinta.

“Ina kwana.”
Ta fad’a tana meyin kasa da Idanunta, Dan tun a kallon farko da tayi masa ta fahimci cewar yau din yayi kyau sosai.

Jin amo da sautin muryarta acikin kunnuwansa ne yasa shi lumshe ido, in a reality voice d’insa yace.

“Lafiya ya jikinki?”

“Nayi sauki sosai.”
Jannart din ta fad’a da d’an hanzarinta, wanda kuma tayi hakanne saboda tunawa da wani abu da tayi.

“Good Idan kin kimtsa inason ganinki afalo.”

Rayyern din ya fad’i haka, batare kuma daya sake cewa komai ba, ya juya kaitsaye ya fice daga d’akin.

Da kallo Jannart din ta bisa.

“Kullum sanjawa yake kamar wahainiya, yanzu zaiyi maka magana da tausasawa, amma anjima kuma saiya sanja kaman bashi ba.”

Ta fad’a abayyane tare da d’an murgud’a baki tamkar Wacce take gabansa.

Sanin yace yana jiranta ne kuma, yasa ta karasa gaban mirror, mai kawai ta shafa sai kuma powder, da lip gloss kamar yanda ta saba iya su kawai ta shafa.

Batare da ta kara wani abunba ta bud’e trolleyn kayanta.
Wani doguwar riga mai kalan red ta ciro, hade da zurawa ajikinta.

D’as haka rigar tayi mata, duk da kuwa cewar rigar bata kama ta ba, Dan irin boubou dinnan ne amma saida shape dinta ya bayyana, more especially hips dinta.

Hulan turban ta sanya akanta bayan ta sake dogon gashin kanta, wanda ya kwanta a bayanta.

Kwarai tayi kyau sosai domin red color din, ya bayyana hasken da fatarta ta kara.

Anutse ta murd’a handle din kofar ta fice.

Tana saka k’afarta acikin falon kuwa, daddad’an kamshin turarenta ya ziyarci hancinsa.

Ahankali ya ajiye spoon din dake hannunsa, tare da d’an d’ago kansa ya kalleta.

Tabbas yaso ya dauke kansa daga kallonta, amma saidai ganin yanda tayi kyau yasa shi kasa aikata hakan.

Itakuwa Jannart Ganin irin Kallon da yakeyi mata ne, yasa ta sadda kanta k’asa tare da karasowa cikin falon, ta zauna akan lallausan carpet din daya malale tsakiyar falon.

“Gani.”
Ta fad’a cikin sanyin murya.

Wanda kuma hakanne yasa shi, turo mata plate din chip and ketchup din dake gabansa.

“Kici.”
Ya fad’a atak’aice cikin kuma tsare gida, domin yasan abune mai sauki tace masa ta koshi.

Tabbas kuwa hakan da yayi mata din yayi aiki, Dan yanayin yanda taji muryarsa, yasa ta d’aukan plate din, batare da ta musa masa ba ta soma tsakalan chips din.

Duk da bata wani jin dadin abincin abakinta, amma yanayin yanda taga mood d’insa yasa dole ta d’anci kad’an.

Rayyern kuwa ganin ta d’anci abincinne, yasa shi d’auko ledan magungunanta dake bayansa, batare daya saki fuskarsa ba ya b’are magungunan, tare da d’aukan goran ruwa.

D’agowa yayi ya kalleta, karab kuwa suka had’a idanu da ita, ganin yanda Idanunta suka kawo ruwa ne kuma, yasa shi sake d’aure fuska, lokaci guda ya dawo asalin Rayyern d’insa.

“Meye kike wani kallona kona cinyemi ki wani abin ne?”

Ya fad’a yana me kokarin b’are injection din dake hannunsa.

Aikuwa kamar jira takeyi yayi maganan, hawayen dake cikin idanun nata suka soma gangarowa.

Cike da tsoron abubuwa biyun dake kusantota, murya na rawa tace.

“Dan Allah Naan karkamin allura, naji sauki tun jiya yanzu babu abunda yake damuna, Dan Allah kayi hakuri...”

Ta kare maganan tana me yayyarfa y’an yatsun hannunta, cike da tsananin tsoron abunda zai faru.

D’ago kansa yayi ya sake kallonta, adai-dai lokacin da yake zuk’an ruwan alluran, saboda yanda yaji muryarta na rawa sosai ne kuma, yasa shi sake had’e fuska.

In don’t care manner yace.
“Nasan kinji sauki, amma dole Idan anfara ak’arasa, ki tsaya Idan ba haka ba kuma nayi miki mai zafi.”

Da sauri ta zazzaro Idanunta tare da soma jan jikinta baya, cikin tsananin tsoron zafin da alluran ke dashi, tana me yayyarfa hannayenta tace.

“Dan Allah Naan kayi hakuri karkamin alluran, zansha maganin na yarda amma banason allura, Dan Allah karka min...”

Takai karshen maganan tana matso hawaye

Idanunsa ya d’an zuba mata saboda, shikam yanda yake hango tsananin tsoron alluran acikin Idanunta mamaki abun yake bashi.

Tabbas yasan cewa da gaske takeyi batason alluran, To amma tayayane zata warke Idan ba’ayi mata ba?

B’oyayyar Ajiyar zuciya ya sauke, tare da d’an zamowa ahankali ya soma kokarin kamo hanunta.

Ganin hakanne kuma yasa azabure ta tashi zata janye jikinta baya, saidai kuma kasancewar ya fita zafin nama, kafun tayi wani yunkuri tuni ya kamo hannunta.

“Ki tsaya ko kuma alluran ta karye ajikinki.”

Rayyern din ya fad’a yana me k’ok’arin nannad’e mata hannun rigarta.

Kanta ta soma girgizawa da sauri, lokaci daya ta fara shishita da ya yarda hannu, take ta soma kokarin kwace hannunta, cikin muryar shogoba tace.

“Please Naan Please......”

“Shiiiiiii.”
Ya katseta ta hanyar sanya y’ar yatsarsa akan labb’anta, baisan Meyasa ba sosai kukan nata yake tab’a masa zuciya.
Aduk lokacin da ta had’asa da Allah Kuwa, ji yakeyi zuciyarsa na ci gaba da karyewa.

To amma lafiyarta fa? Babu wanda yake son magani da allura, dole ce kawai take sawa mutum ya mika jikinsa ayi masa allura.

Ahankali ya sanya hannunsa ya riko dantsen ta, cikin yanayi na d’an shammata ya soka mata alluran acikin jikinta.

Take kuwa zafin alluran na shiga cikin jikinta, ta saki wani irin k’ara mai had’e da kuka.
Cike da tsananin jin haushinsa kuma, ta caka nails dinta akan wuyansa.

Sarai yasan tayi hakanne da gayya, duk da yaji zafi kuma amma bai nuna ba, tas kuwa ya juye mata ruwan alluran acikin jikinta.

Yana zare alluran tana k’ara sakin sabon kuka, tamkar Wacce aka daka haka take kukanta tsakani da Allah.
Wani irin yalwataccen murmushi ya saki, domin
Abun ya basa dariya sosai, saidai bai nuna mata ba ya fusge.

Tafukan hannayenta ya kamo tare da zuba mata magungunan acikin hannunta.

“Kishasu yanzu yanzu.”

Ya fad’a yana me mik’a mata goran ruwa.

Ko kallonsa batayi ba, balle yasa ran zata sha maganin, hasalima Kanta ta kifa da jikin kujera, ta shiga rera masa raki.

Rakin da yayi masifar yin tasiri acikin zuciyarsa, haka kuma rakin da yakejinsa har cikin Brain d’insa, ya haifar masa da rauni.
Ya kuma sake jefa masa tausayinta acikin zuciyarsa.

Idanunsa ya d’an zubawa kyakkyawar fuskarta Wacce duk ta b’aci da ruwan hawaye.

Ahankali ya d’an rank’wafo kusa da ita, tare da karyar da wuyansa gefe.

“Janna.”
Ya kira sunanta da muryar rad’a, tare kuma da d’aura tafukan hannunsa akan nata.

Kwarai taji amon muryar tasa, domin duk da kuwa kuka take, amma saita tsikar jikinta suka mimmike, sauti da kuma taushin muryar sun shigeta k’warai.

“Janna!!”

Ya sake kiran sunanta akaro na biyu, still da muryarsa dake kashe jiki.

Sanin da yayi cewar ba zata amsa shi bane kuma yasa, ahankali ya kamo hannunta ya d’aura akan bakinsa, again cikin rad’a yace.

“I’m sorry Jannart please stop crying kinji, alluran akwai zafi ne?”

Yayi maganan yana me goga tsakiyar tafin hannunta akan labb’ansa.

Hakan da yayi dinne kuma yasa duk tsikar jikinsu mimmikewa, musamman Jannart da takejin abun na yawo acikin jikinta, wanda hakan yasa ta nemi kuka da kuma zafin alluran da takeji din ta rasa, saidai sheshshek’a da take ta sakewa akai akai.

Rayyern kuwa idanunsa ya zuba wa, jajayen labb’anta wanda suka jike da ruwan hawaye.
Sunyi matukar yi masa kyau sosai, haka ma shagwab’a face dinta, wani abu yakeji na musamman acikin jikinsa.

Hakan yasa ahankali ya d’an sake matsowa kusa da ita, har ya zamana numfashinsu na gauraya dana juna.

Idanunsa ya lumshe adaidai lokacin, da yaji Sauk’an numfashinta akan kirjinsa, ahankali ya danyi kasa da kansa, tare da shakan kamshin Jannart din.

Jannart dake sakin sheshshek’an kuka kuwa, sautin numfashinsa ne yasa duk jikinta mutuwa, wanda hakan yasa ta lumshe Idanunta, tana me amsar sakon dake shiga jikinta.

Domin yanayin yanda Rayyern din ke goga labbansa, akan tsakiyar tafin hannunta yasa ta jin tamkar sumbatan tane yakeyi, musamman da ya kasance lallausan sajensa na gogan hannun nata.

Sake rank’wafowa yayi tare da lumshe idanunsa, wanda hakan yasa fuskarsu kusan had’ewa waje d’aya.

Dai-dai bakinsa zai Sauk’a akan kasan hancinta ne kuma,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login