Showing 171001 words to 174000 words out of 350584 words

Chapter 58 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

tsikarinsa sabida yadda yaji sauƙan Cabɓullenta bisa nasa ƙirjin.
Wani irin maraitaccen numfashin yaja can ƙasan maƙoshinsa tare cusa kanshi tsakanin wuyanta da kafaɗarta wani numfashin ya kuma sha sabida sassayan ƙamshinta da ya zuƙa.

Idanu Jannart ta d'an rumtse, cikin gajiya da kuma zafin da take d'anji ajikinta, ta d'an sake matsar da kanta saman kirjinsa, wanda kuma burinta shine ta samu ta zare d'an kunnenta daga jikin rigarsa.

Hakan da tayi d'inne kuma ya bata daman jiyo bugun zuciyarsa, wanda take tafiya da sauri sauri dib-dab-dib-dab.

Idanunta ta d'an lumshe tare da soma d'an jujjuya kannata, dake kwance saman kirjinsa, saboda ta kosa dan kunnen nata ya fita.

Shikuwa Rayyern dake kwance ak'asanta, hannunsa d'aya yasa ya kama gefen ba yansa, tare kuma da lumshe idanunsa, Ahankali k'amshin dake fita ajikinta, da kuma wanda ke fita acikin gashinta ke ratsa cikin hancinsa.

Sosai yake iya jiyo bugun zuciyarta daga cikin kirjinsa.

Idanunsa ya kuma rumtsewa adai-dai lokacin da yaji tana murza kanta akan chest d'insa.
Lokaci d'aya kuma yaji wani irin abu nabin kowani sashi na jikinsa.
Yaarrr yarrrrr haka tsikar jikinsa ke zubawa, Yayinda duk wani kofan gashi na jikinsa, ke bubbud'ewa.

Tun da yake aduniyarsa bai tab'ajin hakan ba, bai kuma san menene hakan ba, sai ayanzu da yaji yanda d'umin numfashin Jannart d'in, ke dukan wuyansa, ga kuma yanayin yanda yaji tana juya kanta akan kirjinsa, da wani irin salo.
Bugu da k'ari for the first time daya tab'a kasancewa da Mace haka, tunda yake aduniya hakan bai tab'a faruwa dashi ba sai yau, bai tab'ayin kusanci da Mace sosai haka ba bai tab’a sanin ya ake fuskanta ba in anyi kusanci da juna.

Idanunsa ya d'an sake rumtsewa, tare kuma dasa hakorinsa ya ciji jajayen labb'ansa.
Kwata kwata bazai iya jurewa kasantuwarsu ahaka ba, domin shi kam awajensa hakan bak'on lamari ne, da bayajin k'wak'walwarsa zata iya d'auka saboda abubuwan masu yawa ke ɗaurewa da kwancewa a sasan jikinsa.

D'an yun k'urawa yayi da niyar tashi, amma sai yaji ya kasa, saboda Jannart din dake kansa, da kuma bayansa wanda ya d'an rik'e.

"Wayyo Allah, ke ki tashi akaina mana, ko doki kika samu ne?"

Ya k'are maganan da wata irin fitinenniyar murya yana me taune lips d'insa.

Jannart dake kwance akansa kuwa, Jin abunda ya fad'a d'inne kuma yasa ta turo d'an k'aramin bakinta, gaba Cikin yanayin shagwab'a tace.

“Ni bazan iya tashi ba, d'an kunnena ya mak'ale ajikin shirt dinka, Idan na tashi da k'arfi kuma kunnena zai yage."

"To ya yage din mana sai meye, nidai da halla malama tashi akaina, da nauyinki zanji Koda zafin fad'uwan da nayi, Dan mugunta ma ai ke ya kamata ki fad'a k'asa ba niba."

Ya fad'a yana me yunk'urin tashi zaune.
Hakanne kuma yasa Jannart din sakin wani k'ara tare da manna kanta da ƙirjinsa da kyau kana ta kara rumtse damatsan hannunsa, saboda d'agowan da yaso yi ya sa tajin kunnenta zafi sosai.

"Auchhh kunnena."
Ta fad'a cikin wata irin shagwab'abbiya kuma kasalalliyar muryar, daya sashi komawa ya kwanta lib.

Hakan ko yasa ta ɗan ɗago, sai kuma tayi maza ta sake fad'awa jikinsa, saidai awannan karon atausashe kirjinta ya fad'a kan nasa.

Wani irin shocking yaji  tun daga k'asan k'afarsa, har zuwa tsakiyar madigan kansa wanda hakan yasa Rayyarn nasa wani irin masifeffen harbawar daya sashi furta.
“Aushhhhhyyyyyohhhhh”.
Yaja sautin da karfi dan abin yazo masa a bazata.

Taushi da kuma tudun tagwayen abu biyu masu kamar audugan da yaji
Akan kirjinsa ne,  yasa shi rumtse idanunsa da sauri, tare kuma da dunk'ule hannayensa.

Lokaci d'aya kuma numfashinsa ya soma wani irin fusga,  Yayinda zuciyarsa kuwa ta shiga bugawa a millions.

"Yah Salam wayyoooooooo Allah na ni mema ya shigo dani wannan jarabebben d'akinne? Why Rayyern Why?"

Ya fad'i hakan azuciyarsa, yana mejin tamkar yasanya hannayensa ya tureta, ko hakan zai sa ya daina jin abubuwanda yakeji na game dukkan sasan jikinsa gaba ɗaya, wanda kwata kwata arayuwarsa baima sansa ba to amman kuma haka nan sai yaji ya kasa baya son tureta, sai yakeji tamkar su tabbata a haka.

Jin sautin bugun zuciyartasa ne kuma, yasa Jannart d'an d'agowa, saidai bata wani Kallon fuskarsa da kyau saboda duhu.

"Meyasa zuciyarsa ke bugawa fast fast haka?"

Tayiwa kanta tambayar, dai-dai lokacin kuma Cikin ikon Allah ta samu ta zare d'an kunnenta daga jikin rigar tasa.

Hakanne kuma ya bata daman d'ago Kanta, tare da mirginawa cikin sauri ta sauk'a ajikinsa.

Jin ta sauk'a daga jikinsa ne kuma, yasa shi sauk'e wani irin ajiyar zuciya tare da mikewa tsaye cikin sauri wani irin haushin sauƙan nata daga jikinsa ne ya rufesa har kamar ya saki kuka.

"Mcheeeww mutun sai nauyi kamar dutse."

Ya fad'a abayyane yana me shafa bayan rigarsa, dake Jik'e da ruwan.

Jannart kuwa duk da cewar baya ganinta, sosai baki ta murgud'a masa, tare da d'aukan wayarta tamik'e tsaye.

Kaitsaye d'akinta ta wuce, domin shima Rayyern din yana tashi, baijirayi komai ba ya nufi hanyar fita daga cikin dakin.

Ahankali yake tafiya yana d'an ciccije bakinsa, har ya gama fitowa daga part din Jannart din.

Dai-dai ya fito falonne kuma idanunsa, suka sauk'a akan Abba dake zaune bisa kujera.

Hakanan yaji kirjinsa ya buga, lokaci d'aya kuma yaji wani irin masifeffen kunya Abban nashi ya kamashi, akaro na farko kuma kenan yanzun, agaba d'aya rayuwarsa da yaji kunyan Abban nasa ta kamasa.

Tamkar wani marar gaskiya haka yayi k'asa da kansa, kana cikin sanyi ya taho sad'ab sad'ab ya haura sama sam ya kasa ya mishi mgn, sai yakeji tamkar Abba yaga abinda ya faru.

Da kallon mamaki Abba yabi bayan Rayyern din, musamman da yaga yanda bayan rigar Rayyern din, ke jik'e da ruwa, wanda kuma shi a iya saninsa, ko digon yayyafi ba'ayiba balle ko yace shiya jik'a Rayyern din.

Ajiyar zuciya kawai Abban ya sauk'e, tare da mik'ewa shima yayi b'angaren sa.

Rayyern kuwa yana haurawa sama, rigar dake jikin nasa ya cire.

Tare da sanjata izuwa wata, Ahankali ya d'an zauna abakin gadonsa tare da jawo Laptop d'insa ya soma hidimar tafiyarsu Mascow.

Saidai gaba daya ya kasa daina jin k'amshin Jannart din acikin hancinsa.

D'an rumtse idanunsa yayi, tare kuma da bud'esu alokaci guda, cikin d'an yanayin k'osawa yace.

"Fitinanniya."

Acan b'angaren Jannart kuwa Koda ta shiga d'akinta, kwanciya tayi lub akan gado, tare da d'aukan wayarta ta soma buga game. 
Duk yanda taso maida hankalinta akan game din kuwa abun yaki, domin hakanan takejin k'amshin jikin Rayyern din, ya kasa barinta tayi sukuni, duk da cewar baya wajen amma mayen kamshinsa yana wajen.

Fuskarta ta d'an ya mutse, tare da shagwab'e murya, cikin kasa da murya tace.

"Ai duk shiya jawo muka fad'i, da wani k'amshinsa awajen."

Yanayin yanda tak'are maganan tana murgud'a baki, Idan ka gani zakayi tunanin agabansa take.

Almost 40minute kuwa ana tsula iska kana hadarin gaba d'aya ya washe, dai-dai lokacin kuma aka soma kiraye kirayen sallan magriba. 

Atare duk mazan gidan suka wuce masallaci, Abba, Rayyern Ramadan da kuma Riyyam-nsra.

Acan suka iske Baba Maud'o ma, wanda shi yakan riga ma kowa dake gidan tafiya masallaci.

Koda sukayi sallan magriban kuwa, basu fito daga masallacin ba har saida suka sallame sallan Isha. 

Koda suka dawo gida, anan kan dining table suka zauna, Yayinda Abba kuwa ya wuce sashinsa kaitsaye.

Mamy ne takai masa abincinsa, Ramadan da Riyyam-nsra kuwa Jannart ce tayi saving d'insu.

Ubangayyan kuwa bai hawo kan dining table d'in ba, anan cikin falon ya zauna, batare kuma daya ce akawo masa nasa abincin ba.

Itakuwa Jannart tana sane dashi, amma saita share batare da ta tambayesa ko yana buk'atar abinci ba, ta nemi waje ta zauna, tare da soma tsakalan abincin da ta zubawa kanta.

Rayyern dake zaune kuwa Ganin Mamy ta fito daga b'angaren Abba ne, yasa shi mik'ewa tsaye.

"Babana kai bazakaci abincin bane?"
Mamy ta tambaya da kulawa.

Fuskarsa ya d'an yamutsa, cikin kuma halinsa na rashin son yawan mgn daya tashi masa yau din yace.

“Ba'a bani ba”.
Yanayin yadda yayi mgnar yana kuma kallon Jannart ƙasa-ƙasa ne yasa, Mamy yin murmushi tare da cewa.
“To bari a kawo maka”.
Cikin kauda kai yace.
"No Mamy ni nakoshi."

"Amma Babana kafasan baka jima da tashi daga ciwo ba, Meyasa bazaka maida hankalinka wajen cin abinci akan lokaci ba?"

Mamyn ta fad'i haka cike da nuna masa, tsananin soyayyar da takeyi masa.

D'an marairaice fuskarsa yayi,  hakan yasa yayi tamkar k'aramin yaro.

"Seriously Mamy nak'oshi ne, kuma anjima zansha tea, yanzu bari naje wajen Abba."

Ya k'are maganar yana me nufan sashin, Abban kaitsaye.

Mamy kuwa da Idanu ta bishi har saida ya shige part din Abban, kafun ta janye idanunta tare da dawowa kan dining table din ta zauna.

Ahankali Rayyern ya tura k'ofar d'akin Abban ya shiga bakinsa d'auke da sallama.

Abba dake zaune akan carpet, yana cin abinci ne ya d'ago kansa, tare da amsawa Rayyern din sallaman, fuska asake yace.

"Rayyern shigo mana."
Abban ya fad'a cikin kulawa.

K'arasowa cikin falon Rayyern din yayi, tare da matsowa ya rusuna agaban Abban nasa, cikin girmamawa had'i da ladabi yace.

"Abba barka da warhaka."

Kai Abban ya jinjina, tare da d'aukan d'aya daga cikin spoons d'in dake, kan tray din abincinsa ya mik'awa Rayyern din.

"Muci abinci."
Abban ya fad'a cike da kulawa.

Kansa ya d'an rausayar gefe, tare dasa hannu ya shafa cikinsa, cikin sanyi yace.

"Abba nak'oshi."

Kallonsa Abban yayi kamar zaice wani abu kuma saiya fasa, saboda dama yasan halin Rayyern cin abinci akai-akai bawai ya wani damesa bane sai daifa idan ya ritsa abinda yakeso ba sauki.

Rayyern kuwa d'an gyara zamansa yayi, tare da fuskantar Abban nasa, cikin muryar dake nuna girmamawa yace.

"Abba dama akan maganan tafiyarmu Mascow ne”.

D’an zuba mishi ido Abba yayi kana ya dauki cup ruwa ya dan sha kana ya aje tare da cewa.
“Uhum ina jinka".
Gyara zamansa ya danyi tare da ci gaba da cewa.
“Yanzu mun kammala komai ranar tafiyan nata matsowa, kuma Ina d'aya daga cikin way'anda zasu tafi, saboda ni nema zanyiwa sauran Doctor's din jagora,  da nayi tunanin bazanje ba, amma kuma sai naga zuwan yana da muhimmanci, saboda akwai babban likita daya daga cikin malamaina nacan, daya nunamin dacewar zuwan nawa, tunda duk way'anda zasuje din ak'ark'ashin kulawana suke, To ya kamata na kasance tare dasu."

D'an dakatawa da cin abincin Abba yayi, tare kuma da d'ago kansa ya kalli Rayyern din, cikin gamsuwa yace.

"Masha Allah, ashe har tafiyar tayi kusa, zuwa nanda yaushe ne zaku tafi?"

"Nan da sati biyu Insha Allah."

Kai Abba ya jinjina tare da cewa.
"Allah ya kaimu, amma naji ku biyar zaku tafi, saidai ka manta masauk'inmu da yake can, wajen zaman mutum biyu ne kawai sai inga kamar zaku takuru a ɗan gidan tunda ba wani babba bane."

Kai Rayyern din ya jinjina tare kuma da gyara zamansa, cikin kwantar da murya yace.

"Eh Abba, su sauran staffs din namu, hotel zamu kama musu, nida Usman P.A ne kawai zamu zauna, anan gidan."

Kallonsa Abba yayi cikin dan yanayin mamaki yace.

"Kaida Usman P.A kuma?"

"Eh Abba, dashi zamu tafi saboda nasan zai d'an ragemin wasu ayyukan."

Rayyern din ya fad'a atausashe, daga cikin zuciyarsa kuwa yana tsoron kada Abban, nasa ya shigo da wata buk'atar.

Abba kuwa kansa ya girgiza, tare da cewa.
"A'a kam bada Usman P.A zaka tafi ba, da matarka zaka tafi."

Azabure Rayyern din ya d'ago kai, tare da zaro idanunsa ya kalli Abban, cikin yanayin kad'uwa yace.
"What Abba...."

D'aga masa hannu Abban yayi alaman dakatarwa, cikin nuna masa gaskiya da kuma hakikanin tabbacin maganansa yace.

"Na maimaita da matarka zaka tafi Rayyern, ba kuma zan sanja magana ba, saboda banason irin abunda ya faru dakai a China ya sake faruwa,   Ina da tabbacin cewa matarka zatafi kula dakai, fiye da Usman P.A, domin shi ba ad'aki d'aya zaku dinga kwana ba, kaga bai zama lallai yasan awani hali kake ciki ba a cikin dararen zamanku a can,  amma matarka fa tana tare dakai akoda yaushe, Dan haka za tafi kowa, sanin wanne hali kake ciki."

D'an numfasawa Abban yayi, kana cikin kulawa yaci gaba da cewa.

"Lafiyarka tafi mana komai Rayyern, akoda yaushe bama son duk wani abu na cutarwa dazai sameka, saboda haka bazamu tab'a barinka ka kasance awata duniya, Kai kad'ai babu wani mai baka kulawa ba."

Fuska Rayyern din ya kwab'e, lokaci d'aya kuma yaji komai duk ya daina yi masa dad'i, bakinsa ya bud'e ahankali da niyar yin magana.

Saurin dakatar dashi Abban yayi,  cikin tsare gida yace.

"Kada kace komai Rayyern domin wannan Umarni nane, bawai shawara ba."

Abban ya fad’i haka cikin tsare gida, tare kuma da jajjadada umarninsa.

K’asa Rayyern din yayi da kansa, tare kuma da d’an marairaice fuska cikin sanyi yace.

“Kayi hakuri Abba bawai Ina ja da umarninka bane, amma Barrister Kabir yace baya son kowa yasan cewar tana nan gidan, Koda kuwa zuwa nan da compound d’in gidan ne.”

“Nasan da hakan, shiyasa ma tafiyar da zakuyin babu wanda zaisan kun tafi tare, tunda bawai da kowa da kowa muke mu’amala ba sannan kuma tafiyarku tare kamar wani matakin tsaretane.”

Abban ya fad’a yana me gyara zama danci gaba dacin abincinsa.

Rayyern kuwa badon yaso ba, haka ya mik’e tare da yiwa Abban sallama, kaitsaye ya fice daga cikin falon.

Direct main falo d’insu ya nufo.
Dai-dai lokacin kuwa Mamy da Jannart d’in ke zaune, inda Mamyn ke kan sofa, sai Jannart dake zaune ak’asa tana latsa wayarta.

K’arasowarsa cikin falonne kuma, ya sanyashi kama k’ugu, tare da Kallon gefen da Jannart d’in take, k’asa k’asa ya watsa mata wani kalon da bai san manufarsa ba.

Cikin kuma yanayin shagwab’a ya kalli Mamynsa, tare da karyar da wuya, asanyaye yace.

“Mamy inason muyi magana.”

Jin abunda ya fad’a d’inne kuma yasa, Mamy d’agowa ta kalleshi.

“Magana kuma Rayyern, to inajinka.”
Mamyn ta fad’a tana me maida hankalinta garesa.

“No Mamy dake kawai nakeson magana.”

Ya fad’i hakan cikin gatse da kuma gayya, tare kuma da sake hararan Jannart k’asa k’asa, wanda ita batama san yanayi ba.

Mamy kuwa jin abunda ya fad’a d’inne yasa ta, Kallon Jannart dake zaune, ganin kuma gaba d’aya hankalin Jannart din ba akansu yake bane, yasa Mamyn mik’ewa, cikin nutsuwa tace.

“To mu haura sama.”

Ai kuwa kaman jira dama yake tuni ya shige gaba, Mamyn na biye dashi a baya.

Suna shiga cikin falon nasu kuwa ya juyo, tare da Kallon Mamyn nasa, cikin son isar mata da k’orafi yace.

“Eyyah Mamy kiji Abba fa, wai da wancan yarinyar yakeson naje Mascow, Mamy takurani zatayi Allah, ni kuma Mamy banason takura, yanzu meye laifi Idan na tafi da Usman P.A?.”

Murmushi Mamy tayi, tare da kallonsa Cikin kulawa tace.

“To meye abun damuwa acikin wannan Rayyern, ka tafi da ita mana, kuma kasan baka isa tsallake umarnin mahaifinku ba, Lallai dole abunda yace shi za’ayi, kuma nima bani da wani ja akan hakan.”

Fuskarsa ya shagwab’e tare da karyar da wuyansa gefe, cikin sanyi da rashin samun k’arfin guiwa yace.

“To yanzu Mamy Dan Allah kiyi wani abu mana.”

“Ni babu abunda zan iya Rayyern, kasan waye Abban ku Idan yayi magana baya tab’a sanjawa, nima kuma Ina goyan bayan hakan, saboda hujjar daya kawo hujja ce mai kyau.”

Mamyn ta fad’i hakan cike da son jaddada masa yiwuwar hakan.

Shikuwa Rayyern gane akan maganar tasu babu wani sauyi ne, ya sashi juyawa tare da neman waje ya zauna.

Mamy kuwa kanta kawai ta girgiza, tare da juyawa ta fice daga falon.

Kaitsaye falon k’asa ta nufa, anan. Ta iske Ramadan da kuma Riyyam-nsra wanda yanzu shigowansu, kasancewar bayan sunci abincin daren sunfita wajen su Baba Maud’o.

Ganin sunata hira ne kuma yasa Mamyn wucesu, kaitsaye ta nufi b’angaren Abba.

Su kuwa su Ramadan sun jima suna hira, kafun daga bisani Jannart ta wuce d’akinta, Ganin hakanne kuma yasa suma duk suka watse.

D’aki suka koma inda kowannensu ya rungumi wayarsa, Musamman Riyyam-nsra da ya sakeyin wata sabuwar budurwa, y’ar k’asar Nigeria kuma y’ar nan cikin garin kano, wanda ta nace masa akan cewar tana son su had’u.

Shikuwa Ganin yanda take tura masa wasu part, daga cikin body dinta ne yasa shi, bata duk wani attension d’insa.

Saidai kuma gaba d’aya ya kasa, sanin wani karya zaiyi, Dan samu ya fita ko zuwa hotel ne su had’u da yarinyar dan sam Rayyern ya saka masa takunkumi.

Acan b’angaren Jannart kuwa, tana shiga d’akinta kwanciya tayi, kasancewar ta gaji ne kuma yasa cikin mintuna kad’an bacci ya d’auketa.

Washegari
kamar kullum ita ta taya Mamy duk wasu aikace akace, bayan sun kammala breakfast bayan taci nata ne, kuma ta koma daki ta kwanta.

Ab’angaren Rayyern kuwa tun 6 ya wuce hospital, saboda akwai wasu patient da yake son dubawa.

Bayan kuma Rayyern din ya tafi ne kuma, Ramadan shima ya mara masa baya, saidai yau harda Riyyam-nsra suka tafi hospital din, saboda shi yace bayason zaman gida.

Ganin duk gidan yayi shiru ne kuma, yasa Mamy da Jannart watsewa afalon suma.

Rayyern kuwa bashi ya dawo gidan ba, sai bayan oppsallan magriba.

Bayan sunyi sallan Isha ne kuma duk suka shigo gida.

Bayan sun kammala Diner ne kuma, suka dawo cikin falon suka zauna.

Jannart ce ta fito daga cikin d’akinta, inda take cikin wani had’add’en doguwar riga navy blue, wanda yayi mata matukar kyau.
Musamman da ta yafa d’an siririn farin mayafi akanta.

Fitowan nata kuwa, yayi daidai da shigowar Rayyern cikin falon, karab kuwa ya sauk’e idanunsa akanta.

Duk da cewar ba akusa suke ba, amma hakan bai hanasa.
Ganin k’yallin da fuskarta keyi ba, still ga kuma bakinta, da yake fitar da shining na pink lipstick din da ta saka.

Janye idanunsa yayi daga kallonta, tare da k’arasowa cikin falon ya zauna.

Ita kuwa Jannart batare ma da ta lura dashi ba, kaitsaye kitchine ta wuce.

Koda taje ta samu sandwich d’in da take gasawa ya gasu.

Kashe oven din tayi, tare da d’aukan wani bowl, bayan ta saka poil paper aciki ne kuma, ta juye duka sandwich din.

D’aukan bowl d’in tayi ahannunta, tare da nufowa falon cikin takun ta na nutsuwa.

D’an tsayawa tayi ta d’auki tissue paper, kana ta k’arasa isowa cikin falon.

Da Murmushi Mamy ta kalleta, kana fuska asake tace.

“Jannart sarkin aiki, sannu duk kin cika mana gidan namu da k’amshin sandwich din naki.”

Murmushi Jannart din tayi, tare kuma da matsowa ta ajiye bowl d’in sandwich din agaban Mamy.
Cikin kuma d’an yanayin alk’unya tace.

“Bismillah Mamy kici sandwich din.”

“Haba My Aunty Mamy kawai, tun d’azu fa muke zaman jiran sandwich din, da k’amshinsa ya cika ko ina dake cikin falon nan, Allah tun kafun ki kammala yawuna yake ta tsinkewa.”

Ramadan ya fad’a yana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login