Showing 321001 words to 324000 words out of 350584 words

Chapter 108 - Tubali Book 1 Hausa Novel Complete

kamar tatsuniya bayan Jannart har ciki take dashi na wata ɗaya sannan kake ratsewa kaga ga shaidar gwajin da mukayi mata”.
Ya ƙare mgnar yana juyo masa takardar sikainin da sukayi mata.
Cikin wani irin yanayi mai wuyar ganewa ya fara jinjina kansa tare da cewa.
“Wallahi na rantse da girman zatin ubangijin ban kusancetaba ban rabata da budurcinta”.
Cikin tsananin tashin, hankali, tsoro, kiɗima, gigita, Barrister Kabeer yace.
“Kai dan Allah ka dena raina min hankali da rantsewu to cikin na uban nawaye kenan?”.
Cikin zubda hawaye ya fara jujjuya kai murya a raunace cikin gaskata wa yace.
“Na rantse da Allah da Manzonsa da kujerar al'arshi ban kusancetaba kuma cikin naw...!

Ba editing.


*GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.


GARKUWAR MA'AURATA






By
*GARKUWAR MA RUBUTA*



“Ciki kuma nawane kuma halatta ce".
Cikin zafin Barrister ya kuma daka mishi tsawa a hargitse yace.
“Kai tafi daga nan, ko a garin gaɓa-gaɓa ayi haka, yoh in ba mahaukaci ba wa zai ji wannan tatsuniyar taka ya yarda.
Kaida bakinka kace kayi min alƙawarin bazaka kusanceta ba, sannan kaje kayiwa yarinya ciki yanzu kazo kana wani cewa wai kai baka rabata da budurcinta ba, kuma ciki nakane”.
Cikin haƙiƙanin gsky Rayyern yace.
“Haba Barrister ni yarone koni mahaukacine da zanyi ta rantse maka a kan ƙarya.
Da Allah fa na rantse maka, wlh wlh wlh ban kusancetaba, ban rabata da budurcinta ba, kana ciki kuma nawane, domin ni nasan wacece Jannart nasan matata tana nan a cikekkiyar budurwa, kana amintacciya ce a gareni. Batun wani tsohon alƙawarin kuma ai yarintace tasa nayishi a bayan ma”
Toh fa mgna ta ɗau zafi.
Kowa ya kafe a kan gskyarsa.
Shi kuwa Dr Sajo komawa yayi ya zauna yana sauƙe numfashi domin yafi yarda da Rayyern sai dai ya bashi dariya da kalmar wai yarintace to acikin watanni takwas ɗin kenan ya girma.
Shi kuwa Barrister cikin asalin takaici da baƙin ciki yace.
“Rayyern yarinta ko”.

Da sauri ya gyaɗa masa kai alamar eh.
Shi kuwa Barrister cigaba yayi da ceea.
“To yanzu ka girma kenan.
baka kyauta minba, tunda kasan sharaɗinmu meyasa dakaji ka girman zaka meda min yata bazawara da sai ka barni in aura mata ɗan uwanta Azeez nasan shi yana sonta”.
A haukace Rayyern yace.
“Kai Barrister kace duk abinda kaga dama, ai koda na kusanceta matatace halaliyata sadaki na biya.
Kuma da aurena a kanta kake wani cewa zaka aura mata wani.
To mugani muga yadda za'ayi a aura mata wani
Magwaji ya gwoda ya mugani”.
Cikin fesar da numfashi Barrister yace.
“Ka manta sharaɗinmu ne da alkawarin daka ɗaukarmin”.
A fusace yace.
“Sharaɗin banza sharaɗin wofi, ni babu ruwana da wani makareren sharaɗi Mata matatace ciki kuma nawane, kuma wlh duk abinda ya samu matata da cikina za'a ga bala'i mai kai da ƙafa da fiffige yaseen ina son matata”.
Cikin sanyi Dr Sajo ya kamo hannun Rayyern dake wani rawa da karkarwa ya ajiyeshi bisa kujera.
Kana ya kamo hannun Barrister shina ya ajiyeshi.
Kallon kallo sukeyiwa juna.
Cikin nitsuwa Dr Sajo yace.
“Dr Rayyern mesa kace ciki nakane? Bayan kuma ka rantse baka kusancetaba”.
Cikin tarin fargabar ƙudurin daya gano Abbansa da Barrister Kabeer suke dashi yace.
“Dr in shi ba likita bane bai san cewa a duniya babu wani abu daya kai sperm sauri ba, to ka gaya mishi yasan da haka.
Jannart dai matatace kana cikin shaidun ɗaurin aurenmu.
Na sani nayi masa alƙawarin bazan rabata da budurcinta ba a wancan lokaci da nakega zan iya rayuwa babu mace.
To amman ai banyi mishi alƙawarin bazanyi wasa da ita, inji ɗumin jikinta ba,
Wallahi ban kusancetaba tana nan da budurcinta ko daren shekaran jiya na tabbatar da haka.
So amman lokuta da dama muna kasancewa tare da ita a matsayin mata da miji.
Ɗaki ɗaya gado ɗaya filo ɗaya, manne da juna.
A lukuta ma bambanta na samu nitsuwa a jikinta, wanda nakeda ilimin irin wannan kan iya samar da ciki.
Domin kai ka sani ciki saurin shiga ne dashi. Banyi kokonton cikintaba.
Na kuma yi imani cikin nawane halattacce, domin haƙiƙa sperm na kan iya wucewa jikinta da gudurin kasheta bamgiji.
Kuma Alhamdulillah wannan ma ya isheka ishara Barrister, nasan nayi kuskuren furuci a baya, amman haka ba yana nufin ni Rayyern wai zan saki matata bane”.
Murmushi mai cike da mamakin tsaurin idon Rayyern. Dr Sajo yayi tare da jinjina kai tabbas mgnar sa gsky ne a duniya sperp yana cikin abubuwan da sukeda masifar sauri.
Kana a duk sanda na miji ya kamo, yana kawowane da kwayayen haihuwa dubu, masu tsinin baki, yayinda na mace ɗaya ne.
Na macen zaiyi ta fafutuka har ya samu yayi karo da a bokin rayuwa su haɗu su liƙe, su zama ciki.
Tabbas wannan amintaccen bincikene da likitocin duniya suka yarda dashi.
Yana kuma faruwa a lokuta da dama, har a kan balagazzun ƴan mata masu buɗawa ƙazaman samarinsu ƙafa wai da nufin ai wasa kawai zasuyi baza'a shigaba.
Daga wannan wasan kuwa ubangiji keyin ikonsa, sai kaji ciki ya samu.
*Hattara gareku yan mata, dama zaurawa wlh ciki yana samuwa a haka, kuji tsoron Allah*

Cikin sanyi ya kalli Barrister Kabeer da yake murtuƙe da fuska kana a hankali yace.
“Barrister wlh kamar yadda ya gaya maka, ciki na shiga a wannan yanayi, muddin dai yayi inzali a kanta, har ta kai ga yana jin ɗuminta, kuma haka ba yana nufin ya ratsa budurcinta bane, ka yarda dani wlh tallahi haka na faruwa da iginin ubangiji”.
Wani dogon numfashi Barrister Kabeer ya sauƙe da ƙarfi tare da lumshe idanunsa.

Shi kuwa Rayyern a hankali ya sassauta murya cikin nitsuwarsa data fara dawowa yace.
“Dan Allah Barrister ina Jannart take, ina buƙatar kusa dani”.
Cikin haɗe fuska Barrister ya miƙe tsaye tare da cewa.
“Yarinyar da kace baka sonta ka tssneta bazaka kuma taɓa sontaba, ta yaya, zan bar marainiyar Allah a hannunka bayan nasan ba sonta kakeyi ba, ai wannan bazai taɓa yiwuwa ba”.
Yana faɗin haka ya fice
Shi kuwa Rayyern hannu biyu yasa ya dafe kansa tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi raji'un, dan Dr ka taimaka min, wlh Barrister zai azabtar damu, yasa Abba nama yana fushi dani, dan Allah ka taimaka min a matsayinka na waliyin aurenta gareni”.
Cikin sauƙe numfashi Dr Sajo yace.
“Nayi ƙoƙarin hakan tun kafin ka sani, to amman Barrister Kabeer da Abbanka sunƙi su saurareni, amman yanzu kayi haƙuri ka koma gida, muga abinda gobe zatayi”.
Da sauri yace.
“Dr ya zanyi in koma gida bayan Jannart bata tare dani, kuma batada lfy, ta yaya zan samu nitsuwa”.
Ya ƙare mgnar kamar zaiyi kuka.
Shi kuwa Dr Sajo cikin son kwantar masa da hankaki yace.
“Rayyern kabi mgnata ka koma gida, kaje kaji da iyayenka, ni kuwa nayi maka alƙawarin zan ji da Barrister Kabeer, ko dan cikin nan da Allah ya samar dashi a tsakaninku”.
Ina Rayyern fa ya kasa fahimtar Yaren.

Haka ya tasa Dr Sajo a gaba da magiya.
Karshe dai sukaje dakin da aka kwantar da Jannart amman sai suka samu Barrister Kabeer ya kulle ƙofar ya kuma ƙi buɗe wa.

Ranan haka dai Rayyern ya kwana kamar zautacce.

Ramadan kuwa, tunda ya kira Raihana ta shaida masa, tabbas Abbanta ya ɗaga aurensu.
Kuka yayi ta mata tamkar ɗan yaye, ita kanta taji ciwon abin to amman yaya zatayi mahaifinta ne, dole itan ta aro jarumta tana bashi haƙuri.

Riyyam-nsra kuwa falo ya fito yayi ta sana'asa ta bauɗewa Kekkyawar tarbiyya da akayi masa.

Mammy kuwa, da Zaiton baccinsu sukayi cike da farincin haɗuwar ahlinsu.

Mamy kuwa tunda Abba ya gaya mata abinda ke faruwa na sharaɗin auren Rayyern da Jannart, cikin sanyi tace.
“Amman dai yanzu duk wanda yaga Rayyern yasan yana son matarsa kuma suna zaman lfy, na sani lallai yayi kuskure amman kada a tsananta masa”.
Cikin tsuke fuska Abba yace.
“Da yake ba ke akayiwa cin fuskar bako”.
Da sauri ta jujjuya kai, kana a hankali kuma tace.
“Sannan kuma gsky ni kaina banji daɗin ɗaga auren Ramadan da akayi ba, kuma ma wai meyasa aka ɗaga fisabililahi fa?”.
Zamanshi ya gyara yana kallonta yace.
“Surkin nasa ya bani gamsassun hujjojinsa kan batun a ɗaga aure.
Domin ya lura da rawan kan Ramadan.
Yace tabbas kada muyi gamgancin yi musu auren nan a irin ya wannan lokaci da kwanaki goma kacal ne suka rage a ɗauki azumin watan Ramadan.
Yace iyaye da yawa suna wannan gangancin da sakaci a aurar da yara gab da Ramadan, suzo tun kafin su gama marmarin juna da sauƙe jarabar kuruciyarsu a kama azumi.
Sanadin wannan sai azo ma'aurantan suyi ta kusantar juna a cikin darare da rana duk da sunsan azumine, sai bayan salla ayi ta aikawa malamai tambaya ana cewa sabon aurene sunyi ta karya azuminsu.
To da za'ace iyaye su lura da wannan in dai azumi yazo sauran wata ɗaya ko kwana arba'in to a haƙura da auren a kaishi bayan salla domin kiyaye darajar watan.
Ya ƙara da cewa, yaga kan Ramadan yana rawa, zai iya yin komai, yace ya gansa daren jiya har sha ɗaya da rabi yana gidan sa.
Na kuwa gamsu dan wallahi Ramadan jarabebben yarone, marar haƙuri kinga idanun nan sa irin na Rayyern na fahimci duk jarabbabun yarane masu ɗan karen fitina, mace bazata samu sauƙi a wurinsu ba, kawai dai shi Rayyern ya iya takunsa ne.
Shi kuwa wancan ɗan jaririn Riyyam-nsra ɗin in dai ba dandatsen taure zamuyi mishiba, na fahimci tabbas zai iya aikata komai”.
Ya kare mgnar yana kwanciya tare da cewa.
“Bacci zanyi kin gamsu da hujjar mahaifin Raihana ko”.
Kai ta gyaɗa masa tare da kwanciya gefensa, ganin har ƙarfe biyu da rabi na dare.

Ana fitowa sallan Adusa.
Rayyern ya nufi ɗakin da Dr Sajo ya nuna masa daren jiya cewa, nan aka kwantar da Jannart.
Sai dai yana zuwa ya samu, babu kowa a ɗakin koda yaje Office ɗin Dr Sajo nanma sai ya samu a rufe.
Daya tambaya sai akace masa ai daga masallaci gida ya wuce.

Jiki a saɓule yaje ya shiga motarsa cikin sanyin jiki ya nufi gida.


A falo ya samesu gaba ɗayansu tea suke sha kamar kullum amman yau harda Baba Mauɗo kana dasu Mammy da Zaiton.
Amman banda Ramadan da yake durƙushe gaban Abba fuskarsa a kumbure,
Jiki a saɓule ya zauna gefen Mamy dake kallonsa cikin tausayawa duk ya rame a dare ɗaya.

“Mamy Mammy ina kwana”.
Cikin kulawa Mamy ta amsa, yayinda Mammy kuwa ta amsa a daƙile, sai kuma ya kalli Abba da Baba Mauɗo da ko inda yake basu kallaba, cikin sanyi ya gaidasu, a fakaice suka amsa masa,
Riyyam-nsra da Zaiton ne suka gaidasa.
Cikin sanyi ya amsa, kana ya juyo ya kalli Ramadan dake cewa.
“Dan Allah kuyi karoƙesu kada auren nan dan Allah Abba Baba Mauɗo ku taimaka min kugafa dun an gama komai sai ana gobe ɗaurin aure kuma ace an ɗaga.”
Cikin tsuke fuska Baba Mauɗo yace.
“Toh mu dai munyi iya yinmu, sarki mai gaggawa sai dai in kaine zakaje ka basu haƙurin”.
Da sauri ya kuma juyowa ya kalli Abba dake cewa.
“Ni ka tashi a gabana kasan bana son yawan magiyar banza da wofi”.

Miƙewa yayi tare da sakin kuka kamar yaro ya haura sama yana cewa.
“Na shiga ukuna”.
Abin nasama dariya ya basu.

Bayan sun gama shan tea ɗinne Baba Mauɗo ya fita.
Abba kuma yayi ciki.
Mammy ɗaki ta koma.

Ganin hakane yasa Rayyarn longoɓar da kai, cikin sanyi yace.
“Mamy kijifa wai rabani da Janna zasuyi, Mamy ki bawa Abba haƙuri dan Allah.
Kai ta jinjina masa tare da cewa.
“Kayi hakuri zomuje wurinsa.”
To yace kana yabi bayanta.

Shiru yayi gaban Abba ya kasa cewa komai.
Shi kuwa Abba kai ya kauda tare da cewa.
“Tunda baka da abincewa, tashi ka tafi, ka shirya dai ƙarfe takwas dai-dai zamuje gidan Kakanku Malam Mainasara.”
Da sauri ya gyara zamanshi tare dayin kasa da kansa kana murya a sanyaye yace.
“Dan Allah kayi haƙuri, wlh bata da lfy tana buƙatar kulawata”.
Da sauri ya dakatar dashi tare da cewa.
“Ficemin daga nan”. Dole ya tashi ya fita.
Daga nan side ɗin Baba Mauɗo ya nufa.

Ita kuwa Mamy cikin nuna tana fushi da mijin nata kan matakin da suka ɗauka kan Rayyern ɗin ta fito kitchen ta fara aiki.
Ganin haka Zaiton ta shigo ta fara tayata.


Shi kuwa Rayyern cikin sanyi ya zauna gaban Baba Mauɗo daya tsaresa da ido, cikin sanyi yace.
“Yah kai mahaifina ka taimaka wa zuciyata datake fuskantar abubuwa biyu lokacin ɗaya, farin cikin bayyanarku da warwarewar ko wanne ƙullin da kuma fargabar rabani da Jannart.
Dan Girman Allah Baba Mauɗo kayiwa Abba mgn ku dawo min datata, ko dan cikin da ke tsakaninmu.”
Cike da mamaki da kuma tarin farin ciki Baba Mauɗo yace.
“Ciki?”. Yayi tambayar a daƙile da danne farin cikinsa, shi kuwa Rayyern da sauri ya gyaɗa masa kai.
Sai kuma yayi saurin ɗago kansa tare da cewa.
“Ƴar tasu da kace bakaso, bazaka kuma taɓa sontaba, kayiwa ciki dan zalumci ka rabata da budurcinta, duk da yarjejeniyar da kukayi da ƙanin mahaifinta?".
Da sauri ya fara jujjuya kai tare da cewa.
“Baba Mauɗo ni ina son matata”.
Cikin danne murmushin sa, yace.
“Sai kaje ka gayawa Barrister ai tunda dashi kuka sharaɗin bada niba, maza bani wuri ka shirya zamuje gidanmu”.

Cike da ƙuna ya fita.

Acan wurin Barrister Kabeer kuwa, kasan cewar anyiwa Jannart duk abinda ya dace, kuma Alhamdulillah ta warware, haka yasa, ya ɗauketa suka koma gida.

Yayinda Aunty Dijat kuwa take bata kulawa ta musamman.
Suna zaune a falon ta ganshi ya foto da tarin tsoffin takardun da yake ta ɓoyewa, duk kwana biyu ya shiga silin ya dubasu kamar ɓarawo.
Cikin sanyi yace.
“Jannart kiyi haƙuri tun jiya anje an kaiwa Daddynki sammaci tare da takardar bada umarnin tsaresa, shida su Alhaji Abdu Tababa da kuma Dr Lukman, da sauransu.
Kuma duk an kamasu, suna tsare, domin nafi son ranar monday ayi komai a gama.
Waɗannan sune tarin shiduna tsoffi da sabbin.
Sannan kuma a ranar za'a saki Junaid sabida zamansa a can yayi nitsuwa ta haƙiƙa da tuba ma gsky.
Sannan Yah Azeez dinkima zai dawo a satin nan.
Kana Abdul da Mom sai randa Azeez ya dawo in yayi musu bayani zasu zo ki gansu.
Waɗanan kuma takardun kadarorin mahaifinki ne, domin na mahaifinsu Rayyern kam na bawa Alhaji Bala Tambari tun tuni ya kai mushi duk nima a lokacin ban san cewa Baba Mauɗo bane”.

Cikin zubda hawaye ta ajiye cup ɗin tea ɗin da take sha, murya na rawa tace.
“Abba yanzu kashe Daddy na za'ayi”.
Shima hawayen yake tsiyayarwa kana a hankali ya kauda kai tare da cewa
“Nima Jannart wannan kukan shi nake tayi tsawon shekaru, bana son rasa ɗan uwana duk da mugune ina sonsa, amman kuma sonsa bazai sa in karesaba”.
Daga nan kuma sukayi ta kuka, da kyar Aunty Dijat ta iya lallashinsu.

Ƙarfe takwas dai-dai duk suka fito cikin harabar gidan.
Suna cikin shiga ta musamman Baba Mauɗo yayi wani irin masifeffen kyau kamanninsa da Rayyern da Riyyam-nsra suka kara fitowa fili.
Ramadan da Zaiton da Mammy kuwa suma kamarsu ta ƙara fitowa.
Mamy da Abba ma sunyi matukar kyau.
Cikin motoci suka shiga.
Mammy da Riyyam-nsra suna bayan motar Rayyern, Baba Mauɗo kuwa yana gama kusa dashi.
Mamy kuwa da Zaiton suna bayan motar Ramadan.
Abba kuwa na gaba kusa da Ramadan ɗin.

A haka suka nufi gidan Baba Mauɗo.

A can cikin gidan Malam Mai Nasara kuwa, kusan duk a cike a falonsa.
Kamar yadda suka saba duk ƙarshen wata sunayin zama na musamman to yau ranar zaman tasune.

Ganin Rayyern ne a gaban mota yasa Mai gadin buɗe masa gate.
Haka yasa suka kutsa kai cikin gidan.
A hankali suka fara fitowa daga cikin motocin.

Wani irin sassayan numfashi Baba Mauɗo ya shaƙa lokacin daya sauƙe ƙafarsa a tsakiyar farfajiyar gidan.

A hankali Rayyern ya koma bayansa, ya tsaya ta gefen Mammy hakama Ramadan kana Riyyam-nsra da Zaiton.
Abba da Mammy kuwa matsowa sukayi kusa, dasu.
Shi kuwa Baba Mauɗo cikin wani irin raunin begen iyayensa da tsawon shekara biyu ɗaya dawo hayyacinsa kullum sai yazo ƙofar gidan.
A hankali ya farayin taku yana nufar ƙofar falon Mahaifin nasu da ya hango tarin takalma.

Cikin wani kaɗuwa, duk mutanen cikin falon suka juyo suka zubawa ƙofar falon idanu, sabida jiyo Muryar Baba Mauɗo da yayi sallama.
Da sauri wasu daga cikinsu suka miƙe suka nufi ƙofar falon a lokacin da yayi sallama ta uku.
Kusan a tare suka dawo cikin tsananin rawan jiki da kaɗuwa.
Lokacin da sukayi arba da fuskar babban yayansu. Da Aicha da zaratan samarin da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login