Showing 27001 words to 30000 words out of 303099 words

Chapter 10 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1603

sai ce ma Umma nono sai ta baka ka sha, shi ma ya Yusuf sai na gaya masa tace an haifesa fiyot kamar kyanwa kamar bakwaini" Girgixa kai Mujaheed yyi ya bar wajen a mugun fusace Imaan ta bi bayansa da gudu tana kyalkyala dariya, Inna ta share kwallar idonta tace "Ni dai ba don gabana aka haifi muguwar yarinyar nan ba wllh sai ince ba jininmu bace, don gulmarta ya wuce hankali ya dauka, banda haka yaya xa ta dinga hada mutane fada a gida haka, shi kenan ni kuma bani da Ikon bada labari, ni daga yau ma kar ta sake xuwa min na yafe abincin, yarinya dai guda daya sai hada bala'i a gida, gashi ta hadani da Mujaheed xata tafi ta hada ni da isuhu kuma, ni dai bari Ahmadu ya dawo a ja mata kunne kar ta sake xuwa min, Bukar dai ya Haifi jaraba"

🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟

_By khaleesat Haiydar_ ✍️

10.....

A fusace Mujaheed ya juya ganin Imaan na bin sa yace "Kee Why are you following me?" Ta xaro ido tace "Ni ba gidanmu xan tafi ba toh??" kwafa yyi ya ci gaba da tafiyarsa tana kai wa bangarensu ta shiga tana dariya kasa kasa. Sai kusan karfe biyar Farida ta fito bangaren inna bayan ta cikata da abun arxiki, su sabulai, omo, malt har da bottle water duk ta xuba mata a leda, Inna ta rakota har bakin kofa tana cewa "Toh sai ki gaida iyayenki kinji, Allah maki albarka, nagode nagode, naji dadin turaren da kika kawo min duk da dai ba mai tsada bane, sai ayi ta hakuri da Mujaheed dai, Allah kuma ya nuna mana lkcn abun arikin nan" murmushi kawai Farida take ta wuce tare da Maimoon dake rike da ledan da inna ta bata, sai da suka isa bangaren su Imaan tace "Bari na shiga in duba imaan" Tare suka shiga parlon da Maimoon, imaan dake kwance tana kallo ta mike xaune tana murmushi tace "Har xa ki tafi Anty farida" farida tace "Eh xan wuce ya jikin fa?" Imaan tace "Ae na ji sauki" Farida tace "Toh Allah ya sauwake xan fito daxu inna tace kun tafi asibiti da Mujaheed" dariya imaan tayi tace "Ni dai naji sauki" farida tace "Toh ki dinga yawo da inhaler din ki amma" Imaan tace "Toh nagode" Ammi ta fito daga daki tace "Har xa ki tafi Farida" farida tace "Ehh Ammi yamma yayi" Ammi tace "Toh mun gode da ziyara, ki gaida mamarki da mutan gidan kin ji" farida tace "In sha Allah xa su ji" body spray uku Ammi ta sa mata a leda, ta amsa tana godiya suka fita tare da Imaan da ta sa hijab xa ta rakasu, xaune suka tadda Mujaheed a part dinsu kusa da parking space a kan farin kujera idonsa a kan wayar hannunsa, farida na daga inda take ta gaishesa ya kalleta sannan ya mike yace "Why did you come without telling me?" ta d'an buda ido tace "Saboda baka son inna ta bani labarin ka? To yau duk naji komai" Dariya Maimoon tayi har da imaan ya watsa masu wani kallo fuska daure, Farida tayi murmushi tace "Kawai na xo anguwar ne shine nace bari in karaso in gaida inna" yace "But da rana ai mun yi waya kuma baki ce kina anguwar ba" tace "Noo ban taho ba lkcn, nima fa ban san ma xan fito ba, I came on an errand for my mum" Kamar ance Mujaheed ya daga kai ya ga Ummar sa tsaye a balcony na sama tana kallonsu keenly, farida ta kalli sama ita ma, ganinta ta sunkuyar da kanta, murya can kasa yace "I think you have to go in ku gaisa tunda ta gan ki" Tace "Toh" imaan tace "Toh Anty farida sai wani lkci xan amshi number dinki gun yaya idan xai bani" ta gefen ido ya harareta, farida tace "Toh shi kenan imaan na gode sosai" Daga haka ta wuce Maimoon tayi leading din farida xuwa parlon Umma, Umma na xaune wayar ta a hannu suka shigo, Farida ta durkusa kasa tana kallonta tace "Ina yini Umma?" Murya can ciki umma tace "Lafiya lau" Farida na wasa da fingers dinta tace "Ya aiki umma" umma tace "Alhmdllh" shiru farida tayi, Maimoon dai na tsaye sai tabe baki take, Umma tace "Ya 'yan gidan naku?" Farida tace "Suna lafiya" Umma tace "To yayi" bayan kusan minti biyu farida ta mike tace "Toh xan koma umma nagode" umma tace "Toh a gaida gida" daga haka ta fita Maimoon na biye da ita, dakin Anty suka shiga, Anty taji dadin ganin ta, bayan sun gaisa ta tambayeta mamarsu farida tace "Suna lafiya Anty" Da ta tashi tafiya Anty ta bata dubu daya kudin transport, Maimoon ta amsar mata don kin amsa tayi suka fita dakin Anty, Mujaheed na tsaye parking space suka fito gidan, bayan sun iso inda yake yana kallon farida yace "Gida xa ki koma yanxu?" Tace "In sha Allah" yace "Ohk mu je in ajiye ki" har ya bude mota wayarsa ya fara ring, ya duba yaga umma ce ke kiransa, a hankali ya daga ya kai kunne, Umma tace "Ina jiran ka parlor yanxu" yace "Toh" daga haka ta katse wayarta, ya kalli Farida a hankali yace "Bari in baki transport kawai dear, akwai aikin da xan yi yanxu" daga haka ya fiddo dubu biyu ya mika mata, ta girgixa kai tace "A'a ka bar shi I have transport thanks" ya mika ma Maimoon yace "Ki bata plss" Maimoon ta amsa, yana kallon faridar yace "Sai mun yi waya dear" daga haka ya wuce ciki. Maimoon ta tabe baki tace mu je Anty farida. A hankali Mujaheed ya bude kofar parlon Ummarsa ya shiga da sallama, tsaye ya sameta ta rungume hannu tsakiyar parlon wandering about, ya karasa yace "Umma gani" kallon da ta dinga masa ya sa ya durkusa ya sauke kansa kasa, tace "Mujaheed dama ban raba ka da wannan yarinyar ba?" Ya kalleta da kyar yace "Umma ni ban fa san da xuwanta gidan ba, kuma...." Sai yayi shiru, Fuska a murtuke tace "Kuma me?" Yace "Umma don Allah me yasa baki so na da farida?" Tace "Ra'ayi! Wato dai har yanxu kuna tare duk jan kunnen da na maka kwanaki koh? To wllh ka kiyaye bacin raina Mujaheed, ka kiyaye ni a gidan nan, uban me xaka yi da diyar talakawa ka ja min bala'i, in xama abun magana gun kawayena, duk fadin kaduna ka rasa budurwar da xaka nema sai wannan yar, warce iyayenta ke xaune a ghetto ? Haba Mujaheed are you even alright?" Yace "But Umma I see nothing wrong with that, arxiki fa na Allah ne, beside suna da rufin...." Umma ta dakatar da shi rai bace tace "Da ca nayi arxikin na kanin ubanka Sadeeq ne? Ni xaka ma wa'axi? To wllh in dai kana son kwanciyar hankalin ka a rayuwa ka fita harkar yarinyar nan, su je can su samu wani kuma, abubuwan alkhairi da ka dinga masu a baya da ciyar da su da ka dinga yi Allah ya saka maka da alkhairi, ina ji ina gani baxa ka auri yarinyar nan ba ka xama mai bada charity su talautar min da kai, yarinya dai dai class dinka in sha Allah xan samo maka tunda naga ba saiti gareka ba, ba abun mamaki ba wataran ma ka xo min da yar talla kace ita kake so, kai ko kunyan kanka ma baka ji, dubi yarinyar da Yusuf yake nema xar sha'awa yar masu kudi ta ma fi ubansa kudi shi ne kai xaka makale ma yar ghetto ko, to wllh ka guji bacin raina a gidan nan, sannan don munafurci da kinibibi ta shigo sumui sumui ta nufi gun alakakan kakarka da ba so na take ba a gidan nan salon duk ta bata ni gunta ta hure mata kunne, don wllh da ban ganta a sama ba dama bata yi niyyar shigowa gaida ni ba, ta kama ta tafi gun kakarka da kanwar uwarka Aisha tunda ita ta haife ka, Allah kadai yasan me kakar taka ta k'itsa mata, wato Mujaheed tarayyar ka da yarinyar ba abu bane mai yiwu wa samm kayi ta kanka tun wuri, daga this very moment na raba ka da yarinyar na har Abadan abidina, tashi ka ban waje mara tunani kawai" mikewa yayi bai ce komai ba ya nufi kofa ta bi sa da harara har ya fita ya kulle mata kofar ta. Xaune yake cikin Lafiyayyen motarsa nesa da gidan, abokinsa dake gefensa yace "Look ni fa na gaji da xaunar da ni da kayi cikin mota tun daxu Sadeeq..." Sadeeq ya shafa cute Beards dinsa a hankali yace "You just chill Fahad... jikina na bani xata fito soon" Tabe baki abokin yyi yace "Have you changed ur mind about loving and dating only whites?" Sadeeq ya xaro ido yace "Of course No, wannan fa yar yarinya ce.... I think she is not even up to 18, she is....." Sai kuma yyi shiru yana murmushi, Fahad da ya saki baki yana kallonsa yace "Sweet eighteen kenan" Yar dariya Sadeeq yyi a hankali underneath his breathe yace "she is beautiful" Fahad yace "and why didn't you callect her digit?" Wani kallon gefen ido yyi masa yace "Sai kace nine kai? How on earth xan amshi numberta bata ce in bata nawa ba" Bude gate da suka ji aka yi yasa duk suka daga kai da sauri, Mujaheed ne ya fito, walking majestically ya nufi motarsa da yyi parking a waje. Imaan na xaune bakin kofar kitchen tana ta yi ma Amminta dake girkin dinner hira, Ammi tace "Daxu inna ta xo fa wai tana nemanki idan kin dawo schl" Imaan ta xaro ido tace "Ni??? Ba ruwana baxan je ba, ce ma Abba tayi fa kar in sake xuwa mata ina kwasan maganganunta ina yadawa a gidan nan, ita gaskiya xata gudu ta bar gidan idan naje mata" Ammi tayi murmushi tace "Toh tace kwana biyu bata gan ki ba ko jikin ne" Imaan tayi dariya tace "Xa ma ta fadi gaskiya ne, ba inda xanje ta sake cewa na mata laifi gwara dai Maimoon ta ci gaba da xuwa tana kai mata abinci" Ammi tace "Toh ke xa ki kai yau, kina ajiye mata ki gaisheta sai ki fito ba shi kenan ba" imaan ta bata fuska kamar xata yi kuka tace "Ni dai Ammi nayi alkawarin baxan sake xuwa part dinta ba fa" Ammi dai bata ce mata komai ba. Bayan magrib Imaan na Idar da sllh Ammi ta tilastata kai ma inna abinci sabanin Maimoon da ta dinga xuwa tana kai mata kusan kwana uku kenan, Imaan ta dau abinci ta fita fuska daure kamar mai shirin yin kuka, tana isa bangaren inna ta tura kofar ta shiga, Yusuf ne parlon suna hira, Inna na ganinta ta washe baki tace "A'a takwara ce" imaan ta ajiye abincin ba tare da ta kalleta ba tace "Ina yini?" Inna tace "Lafiya lau, ni kwana biyu ban ganki ba nace to ko jikin ne? Duk hankalina ya tashi na tafi sashin ku daxu Aisha tace ai kin ma tafi boko" Imaan ta tabe baki tace "Lafiya ta qlau kawai dai umarnin Abba nake bi" inna tace "Umarni kuma? Umarnin me ya maki?" Imaan ta buda ido tace "Ba ce masa kika yi kar na sake xuwa bangaren ki ba baki son ganina, shine ai na daina xuwa" Inna ta kalli Yusuf tace "Oh oh Allah, isuhu kaji wata magana irin na Ahmadu ko, dama an san babba da hadin fada, ni yaushe muka yi haka da shi, daga nace yayi mata fada ta daina haka gidan aure xata kuma ba halin xaman gidan miji kenan ba, shine xai ce nace kar ta sake xuwa min? To ina da masu xuwa ne idan ba ita ba ko shi xuwa yake yi ya xauna min, ni dai a dinga jin tsoron Allah gaskiya" Yusuf yyi murmushi yace "Toh ba ga ta nan dai ta xo ba" Inna na kallon imaan tace "Ni ban yi haka da shi ba gaskiya, ga soyayyen naman ki can na ajiye maki tun jiya a daki, naki ne da na Mujaheed shima kwana biyu ban gansa ba sai ki diba naki ki bar masa nasa" Imaan ta turo baki ta wuce cikin dakin, daukan bowl din tayi ta bude taga soyayyen naman cow din sai kamshi yake ta xubawa, ta xauna gefen gado ta kirga gaba daya taga yanka sha takwas ne, murmushi tayi ta fita don dauko leda a kitchen, Inna tace "Kin diba naki" tace "Leda xan dauko a kitchen" daga haka ta shiga kitchen din ta dau leda biyu ta boye daya, tana rike da daya ta fito ta koma cikin dakin, equal ta raba naman ta debi nata, cikin sauran da ya rage ta debe guda hudu ta xuba a daya ledan ta ajiye sauran, ta window ta jefar da guda hudun da ta dauka sannan ta fito parlor, inna na kallon hannunta tace "In ji baki kwashe naman ba nace naki da na Mujaheed ne, don gaskiya nasan halin ki" ta xaro ido tana nuna mata ledan tace "Duba ma ki gani, guda sha takwas ne na kirga na dau tara na bar masa tara" Inna tace "Yauwa kinyi dubara" Yusuf da ke ta kallonta yana murmushi yace "Are you sure imaan" da mamaki ta kallesa tace "Me that don't even like eating meat sef" murmushi ya kuma yi yace "Eh naga alama" Inna ta tabe baki bata dai ce masu komai ba, Ummi ce ta shigo parlon rike da abinci ta kawo ma inna, inna ta bude warmer din ta girgixa kai tace "Mayar masu, ce masu aka yi xaman abinci nake a gidan nan shekaranjiya a ban shinkafa da miya jiya a ban dafaduka yau kuma a ban koren shinkafa, maida baxan ci ba" Yusuf yace "Toh ae ba iri daya bane wannan fried rice ne fa" Inna tace "Toh Isuhu ni kenan a cin shinkafa xan kare, wlh na gaji da kaddararren shinkafar nan, Ahmadun baya ajiye abinci ne" tana fadin haka ta jawo warmer din da Imaan ta kawo ta bude, shinkafa ce da miya sai salad a gefe shi ma, Yusuf ya fara dariya, Imaan ma ta kyalkyale da dariya, inna tace "Toh Allah ya mana tsari" tana fadin haka ta kalli Ummi tace "Ke Mujaheed ya dawo ne ko yana can yana siyar da abinda ya kasa a titi?" Ummi tace "Ya dawo, tare muke tahowa kuma ya tsaya yana waya " Bata rufe baki ba sai ga shi ya shigo da sallama, farar 3 quatre ne jikinsa da bakar riga, Inna ta tura kulolin gabanta tace "Mujaheed don Allah irin wannan tuwon da ka taba siyo min nake so ni dai" ya karasa parlon ya ajiye ledan fruits din hannunsa yace "Ae sun tashi masu siyarwan" tace "Ni dai don Allah ka rufa min asiri ka tafi, su tashi su je ina?? Bayan ga maza masu fita titi cin abinci ta dalilin rashin iya girkin matansu" Yace "Ki tambayi Yusuf da karfe shidda suke tashi" yana fadin haka ya bude warmer din abincin kusa da ita yace "Wannan kuma fa" tace "Haba Mujaheed shinkafa dai shinkafa dai inje basir ya cafke ni, wa nake da shi da xai nema min magani, wllh baxan ci shinkafa jiya in ci yau ba, wannan ai mugunta ce ma" Mujaheed ya tabe baki yace "Toh ai sai ki sha tea ki kwanta" Ta maka masa wani kallo tace "Kai xaka gaya min abinda xan yi ko raini?" Yusuf ya mike yace "Toh bari a samo maki tuwon idan basu tashi ba" daga haka ya fita, Inna tace "Toh Allah yayi maka albarka, Ya baka abinda kake nema duniya da lahira, to dama? idan ba kai ba waye, Allah dai ya ma albarka" Mujaheed ya kalleta ta gefen ido xai fita inna tace "Ga namar ka can a daki, baxan biye ta halin ka ba ni dai" Ya juyo yace "Nama na me?" mikewa Imaan tayi ta nufi kofa ta fita sum sum, inna ta bi ta da kallo baki bude tace "Toh kuwa idan ba wani ikon Allah ba ta kwashe rabon naka, Ummi tafi daki ki dauko min roban naman, ai ni naga abinda ya isheni bai ishi ubangijina ba" Ummi ta tafi dakin ta dauko bowl din naman inna ta amsa ta bude tana kallo ta saki salati ta ajiye ta rike ha6a, Mujaheed ya dau roban yana kallon sauran naman, inna ta sauke ajiyar xuciya tace "Ta kwashe wllh, gaskiya dai wannan 'ya ta Bukar bata da hali, muguwa ce ta innanaha, ni wllh da xaka burgeni Mujaheed ka bi ta har gaban uwarta ka kwato min namana gaba daya na fasa badawa" Ya ajiye bowl din hannunsa bai dai ce komai ba, Inna tace "Idan kuma baxa ka ba ni sai in tashi inje, ya xata kwashe min nama gaba daya bayan na mata bayani, naman fa yyi yanka kusan ashirin shine ta bar maka hudu, ni dai rabona da a sani magana haka tun kwana uku da suka wuce, to bata xuwa.... yau kuma ban san uban me ya kawota ba" Yace "Sai da safe" bai jira cewar inna ba ya fita parlorn, motsin da yaji a bangarensu Imaan yasa ya tsaya duk da bai yi niyyar tsayawa ba, durkushe ya ganta a balcony dinsu tana tattara shoes dake wajen xata shigar da su ciki, yana kara taku daya xata gansa saboda hasken dake wajen hakan ya sa ya tsaya, mikewa tayi ganin alamar xata fito ya koma baya da sauri ya tsaya jikin flowers, socks dinta da ta shanya take kwashewa, da sauri ya nufeta tana ganinsa ta saki takalman hannunta da socks ta gudu xuwa balcony dinsu, Amma tuni ya kamata ta xaro ido kamar xata yi kuka tace "Yaya me nayi kuma?" Ya daure fuska yace "Ina naman da kika kwashe" tace "Yaya nama kuma, ni fa guda shidda na dauka" yace "Dauko shiddan"


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login